sai dan abinda ya mallaka,a kullum takan nuna masa ta fahimtce shi ya daina saka damuwa a ranshi.
Watan da zai kama ne za a yi bikin Hafsat dan haka ta koma gida dan fara shirin biki,ranar da zata tafi Eamaan kuka ta dinga yi domin kuwa ba ta son rabuwa da yayarta ta,lokacin da aka fara gudanar da bikin kuwa Alhaji ya sakar masu kuɗi sosai da su suka qarasa yin siyayyar da basu yi ba, angon Hafsat kuwa idan suna waya Eamaan dariya take yi musu sosai, dan da ganin yanda yake abubuwa zai yi naci,Iya ko yanzu jikin ta ya qara yin sanyi, ba safai take zagewa ta yi ta yiwa Eamaan masifa ba,Eamaan ta dawo da yi mata abinci kamar yanda take yi ada dan tace albarka take nema.
Tin safe Eamaan ke shirin tafiya gida saboda gobe za a fara bikin Hafsat, Alhaji bai so ba amma babu yanda zai yi haka ya barta ta tafi,shi kuma ya sanar da ita zai koma Abuja dan bai ga abinda zai zauna yayi ba a gidan bata nan.
Hajiya Babba da Sahabee kuwa sak hakan yayi musu daɗi saboda sun samu freedom ɗin yin abinda suka ga dama a gidan babu mai sanya musu ido, fatan su ma shine idan ya tafi ya dad'e wannan karon bai dawoba.
Alhaji ba qaramin warning din Hafsat yayi ba akan ta kular masa da Eamaan da abinda ke cikin ta kar a wahalar masa da mata da aikace-aikacen biki sannan ya qara da cewa,
"A kuma dinga bata abinci akan lokaci, kar kuna damun ta idan tana bacci, banda yawan sata aiki Hafsat, kinga dai bata jin dadi,i don't want to lose my baby pls"
Cike da tausayawa Eamaan ta kama hannun shi ɗaya ta kwantar da kan ta a gefen jikin shi tace,
" Ba zaka rasa komai ba Alhajina, kwana biyar kawai zanyi ko ka dawo ko baka dawo ba zan dawo gida ni, ka sa wa ranka salama kar wani ciwon ya zo yana damun ka ka ji?"
D'aga mata kai ya yi tare da manne ta a jikin shi ya na sumbatar ta, Hafsat rufe fuska ta yi da hannu d'aya tana fad'in,
"Oh ni Hafsat ina ganin rayuwa a wajen bayin nan na Allah ! Thank god na baro gidan ku na dena ganin wannan rayuwa da kuke bani kunya da ita,"
Alhaji ne ya kalle ta yace,
" kinyi magana ne ?"
'Aaa'aa ni ban ce komai ba,"
Dariya suka yi gaba d'ayan su, sannan Hafsat ta taya Eamaan shigar da kayan ta cikin gidan.
Aqofar masallacin gidan su ta gan shi yana saka takalmin shi, suna haɗa ido suka ji wani abu daga kan su zuwa qafar su mai nauyi qarshe ya danne zuciyoyin su, saurin kauda kai ta yi tare da yin a'u'ziyya tai maza ta shige gidan su, shi ko tsayawa ya yi kyam ya bi hanyar da ta shige gidan nasu da kallo,gaba ɗaya ya can ja yayi kyau yayi fresh da shi ya aje gemu irin na samarin yanzu, sai dai duk wannan kyawun da yayi be hana a gane irin ramar da yayi ba......
*Eamaan na gayyatar ku auren Hafsat, zamu ci rangyam💃🏻💃🏻💃🏻 who is going with me ? zan maku kuɗin mota*💃🏻
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 15:
Shigewa suka yi da hanzari nan suka tadda gidan a cike da mutane maqil, kowa ya ga Eamaan sai ya yi sha'awar ta ya yaba saboda ta yi kyau ta qara cika dumdum da ita, ga dan cikin ta daya fito gwanin sha'awa, sai yalwataccen gashin ta da bai boyuwa a dik shigar da zata yi, gaishe da 'yan uwa da abokan arziqi Eamaan ta dinga yi suna amsa mata cikin sakin fuska da raha, wasu qannen Mama na ganin Hafsat suka saki gud'a har wata a cikin su tace to ai amaren biyu ne tinda Eamaan ma bata gama cin nata amarcin ba gud'a suka sake saki akai ta shewa ana raha.
An sha biki lafiya an gama inda aka kai Hafsat garin Bauchin Yakubu gidan ta madaidaici daidai rayuwar da take sha'awa, ba qaramin godiya ga Allah ta yi ba na samun gida mai kyau haka, Hafsat da Eamaan sun sha kukan rabuwa da junan su,sai bayan kwana biyu Babbar yayar su zata zo ganin gida dan kuwa ta yi missing bikin ba da ita aka yi ba, a haka suka taho suka bar amarya da kewar 'yan uwan ta, direct gida Ammaah tace a ajiye Eamaan, dan ba ta ga me zata koma ta yi masu ba tinda mijin ta ya dawo daga Abuja ya na gari sai waya yake faman yi yana tambayar an gama bikin kuwa?Eamaan taci kuka sosai haushin Alhajin take ji da yayi mata haka, dan bata taɓa yi masa musu ko rashin da'a ba amma zai hana ta ɗan zama a gidan su ta huta gajiyar biki,dika-dika kwanan ta nawa a gidan nema da zai damu da rashin ta shi ba tafiya yake yi ya bar ta ba,a gaskiya be kyauta mata ba ta so ta d'an huta a gidan su itama kafin ta koma, cike take famm da haushin shi aka ajiye ta a wajen gate ɗin gidan nasu,a zaton su mai gadi ne zai buɗe gidan tinda aikin shi kenan sai ganin Alhaji suka yi da kan shi, ya fito ya buɗe yana ta washe baki, kananan kaya ya sanya kan shi ya sha aski ya yi kyau sosai kamar wani matashi, tsabar gayun Alhaji yawancin mutane basu yarda da cewar ya haura shekaru hamsin a duniya, cike da murna ya gyra zaman farin gilashin idanun shi a fuskar shi ya tinkare ta, su kuma 'yan uwan Eamaan suka yi mata sallama aka tada mota suka wuce kowa na sha'awar dacewa da miji dan k'walisa da tayi,a hankali ta ɗan sassauta fushin ta ta gaida shi, daga nan bata qara cewa komai ba ta wuce shi ta shige cikin gidan haka Alhaji ya bi bayan ta riqe da akwatin ta a hannun shi sai surutu yake yi mata ita kuwa ko A bata ce masa ba, suna shiga ya janyo ta ta fada jikin shi, cikin kashe murya yace mata,
" Wai me ya faru ne my baby naga kina fushi fa ni,"
kuka ta sake masa sosai tana buga qafa a qasa cike da shagwab'a tace,
"Yau fa aka gama biki zaka matsa se na dawo, na so na je gida na kwana da Ammaahna yau d'aya dai shine za kai ta waya kace a dawo da ni gida,"
kukan ta ci gaba da yi shi kuma yana aikin lallashi, can qasan ran shi kuma yana dariya, gashi dai kuka take yi amma duk ta bi ta manne masa a jiki tana wani shaqar qamshin jikin shi da take so tin bayan da ta samu cikin jikin ta,dik da bata taɓa faɗa masa ba saboda kunya da tazarar shekaru da ke tsakanin su ya gane da kan shi tana tsananin son qamshin jikin shi, wanda a zaton shi turaren da yake sanya wa take so sai ya siyo mata irin shi sak, qarshe cewa tayi ita ya ɗauke ya dinga shafawa kawai ba irin shi take son shafawa ba, har ta kai ta kawo da kanta take fesa masa ta zauna a jikin shi tana shaqar qamshin, d'aga ta a jikin shi ya yi yace mata,
"Wash Allah baya na baby kin ji nauyin da ki ka yi kuwa? Washhh kar ki karya wa Iya yaron ta fa ki haɗu da ita dan naga kwana biyu tana ji dake kun dena faɗa..... to shikenan zo na maida ki gidan ki kwana kin san dik abinda kike so shi nake so nima"
Narke wa ta sake yi a jikin shi tana shinshina qirjin shi tace,
" A'a sai da na dawo gida kuma zaka wani ce na koma na kwana,wato salon ka ja amin faɗa a wajen Ammaah ko"
Dariya ya yi sosai ya ci gaba da lallashin amaryar shi cike da kulawa,su na qarasa shiga sashen ta ya nufi d'aki da ita ya ajiye ta a gado ya hau cire mata mayafin jikin ta da riga da d'ankwalin ta dan ta sha iska, ita kuma tsananin gajiya ya sa ta fara hamma, juyi tai zata gyara kwanciya,yana ganin haka ya san bacci take ji sosai dan haka sai ya kunce mata zanin jikin ta dan ta samu sakewa sosai d'ago ta yayi suna fuskantar juna yace,
" A'aa sai fa anyi wanka za ai baccin nan, na san halin ki cikin dare sai ki tada ni kice min zaki yi wanka, muje na yi maki in kin gaji ne,"
Cike da shagwaba ta ce
"Ni dai ka barni na yi bacci na,bacci nake ji sosai idona har yaji yake yi min,"
D'aga ta ya yi cak ya nufi toilet da ita,cikin nishi yace
"Wai Eamaanii na ba dai nauyi ba,kinji nauyin da ki ka qara kuwa, sai ki karyawa ɗan tsohon mijin naki baya ai,"
Dariya ta yi masa sannan ta qara sake mishi nauyin ta, dan kuwa ta gaji da rakin da yake yi mata kullum akan nauyin da ta qara kamar ita ta sa shi d'aukan ta, da baya amfana da d'aukar ai ta San ba zai yi ba,a haka ya mata wanka da ruwa mai zafi, ta gasu kuwa sosai ana gamawa ta d'aura towel ta tako wajen sink tayi brush, sannan suka fito a tare, mai ya shafa mata tace,
"Sweet nima yau ka shafa min irin tiraren ka na dinga qamshin ka ka ji,"
D'akkowa ya yi ya fesa mata yana mamakin hali irin na masu ciki tinda da dai ita tace bata so yau kuma gashi tace a fesa mata, yana fesa mata taji kamar ba turaren ba taso yin qorafi akan qamshin ta dai daure,kayan bacci ya d'akko mata ya saka mata rigar zai saka mata wandon tace ita fa ba zai saka mata ba zata takura a barta haka ta sha iska ai kuwa a haka suka kwanta, ganin yanda ta gaji yasa bai damu da sai ya nemi haqqin shi ba a wajen ta, ita kuma ta saddaqar in ya nema ba zata yi masa rashin BIYAYYAH ba zata bashi haqqin shi, da ta ji shiru kawai sai ta yi baccin ta cikin natsuwa da kwanciyar hankali.
Hajiya Babba dai likkafa ta ci gaba, dan kuwa yanzu Sahabee har kwana yake yi a wajen ta, tin da Eamaan da Alhaji suka yi tafiya ya daina kwana wajen Iya, sai ya shirya kamar zai fice yawon shi sai ya zame ya yi bangaren Hajiya, a haka Sahabee ya maye gurbin Alhaji a wajen Hajiya, yau ma Alhaji na wajen Eamaan shi kuma yana wajen Hajiya, ga su kamar inji ba sa gajiya da yin abu ɗaya.
Iya kuwa kullum haka zata yi ta faɗa akan yawon da Sahabee yake yi a bayan idon shi,amma a gaban shi ba ta iya yi masa maganar,sai dai in shi ne ya yi wani zancen barikancin a gaban ta,sai tace masa kai yanzu baka jin kunyar fad'amin kai dan iskane ko? Ita sam bata san ya ake tarbiyya ba sai shegen son nuna ita fa wannan d'anta ne, ko 'ya'yan ta ne, amma tarbiyya kuwa wala.
Eamaan ta riga Alhaji tashi kamar kullum sai ta yi wanka ta wanke baki ta saka doguwar riga da d'ankwalin kayan, ganin yanda qirjin ta ya fito sosai a cikin rigar ne ya sanya ta saka qaramin hijab da ya wuce qirjin ta, gyara wajen ta dan yi dan ba datti sai qura, sannan ta fice wajen Iya, daga bangaren Hajiya Babba ta gan shi yana fitowa, ta bishi da kallon ta mai kid'ima shi, daga baya ta ɗauke kan ta irin ko a jikinta din nan rayuwar ku ce, ta shigewar ta wajen Iya,rasa ina zai koma ya yi, in ya koma wajen Hajiya Babba Alhaji ya shigo fa? In ya shiga wajen Iya su kacame a hanya da Eamaan kuma, salin alim ya wuce wajen driver ya karb'i key ɗin mota ya bar gidan abun shi, ita kuma mamakin qarfin halin su take gani sosai, dan ta tabbata a wajen Hajiyar ya kwana, aikace-aikacen ta ta fara yi har ta gama be dawo gidan ba, sai ta je d'akin Iya ta tarar ta farka daga bacci har tayi wanka tana zaune tana sauraren redio,durqusawa tayi ta gaida ita sannan ta sanar da ita abincin karyawa ya kammalu,Iya kuwa fuska babu yabo babu fallasa ta tambayi Eamaan ya gajiyar biki sannan ta yi fatan alkairi.
Qarshe dai Iya har da godiya domin yanzu ko ba komai ta gano wacece Eamaan ba kamar sauran matan Alhaji bane ita, yarinya ce data ɗauke ta a matsayin Uwa ba suruka ba, dan haka itama zata qoqarta ta d'auke ta a matsayin d'iyar ta,tashi ta yi taje ta wanke hannu a band'akin dake d'akin ta ta fito parlour, anan ta tadda Eamaan tana haɗa mata kokon da ta dama mata,koko yayi fari qal saboda ya sha madara da pineapple flavour da kayan qamshi sai qamshi yake yi, gefe kuma ga qosai ta yi mata,dan Iya na son wannan haɗin matuqa, sai dan farfesun naman rago da ya ji kayan qamshi da albasa,cikin yatsina fuska Iya tace,
" Wai ni ina Sahabee ne? Rabona da shi tin jiya kafin isha'i da yai wanka ya fita ban sake ganin shi ba,duban d'akin shi ki kiran shi, d'annema mai kan buta kawai,"
Eamaan da ta riga ta san inda yake kawai sai ta tashi ta leqa d'akin ta dawo tace baya nan,Iya sallamar ta ta yi tace taje ta daukar masu nasu ta tafi kawai, shi ya sani, ( Iya ba ta iya yiwa yaran ta addu'ar shiriya ba sai zagi da kiran su da sunayen da in suka bi yaro sai ya qara lalacewa)
Eamaan ta tarar da Alhajin ta ya gama shirin shi tsaf na zaman gida da yake yi idan yana gida ba fita zai yi ba,dan kuwa shi mutum ne me yawan gayu a cikin gida dan kawai iyalin shi su gani su ji dad'i, abinda ke baqanta masa rai kenan a baya da Hajiya Qarama, ta na gani shi da yake namiji zai yi wanka ya yi gayu, amma ita ba wannan a tattare da ita sam, ya na Kuma da qoqarin taya matan shi aiki, musamman Eamaan da itama ke yi masa komai da yake so Kan jiki Kan qarfin ta, shi yasa ma da ya tashi be gan ta ba ya ga Kuma ta gyara ko Ina se ya gyara gadon daya tashi akai, yana riqe da cup da ya hada coffee yana sha ta shigo,
"Wai ke ba zaki daina wahal da kan ki ba ko a wannan yanayin da kike ciki ko? yanzu na je na hana ki Iya taga laifi na, bakiga kina dauke da ciki ba ne, so kike ki ja mana matsala ne,"
Cikin murmushi ta ce masa,
" Inshaa Allahu bama tare da matsala,wanda basu kyautatawa iyayen su ma basa tare da ita balle ni da nake yi wa uwata aikin lada, ai sai dai na ga alkairi ba dai matsala ba, so kake na zo na jibge kamar kayan wankin da suka rasa mawanki su jiki na ya yi ta ciwo ba dalili?"
Kad'a kai ya yi alamar Ah ah tace
" To ka gani... ai yi ma Iya abun karyawa ba wani aiki bane mai yawa nima yana sawwaqe min sake zuwa na yi maka naka na daban, tinda bana so kana cin na masu aiki kana da mata,nima kuma dama ba son cin nasu nake ba ,tinda ba zuwa ko ina nake yi ba kaga girkin zai taimaka min na samu k'warin jiki na,dan haka kar kana damun kan ka akai na,"
Ya gamsu da bayanan ta amma da kam gani yake yi kawai wahala take yi.
A kwana a tashi Eamaan ciki ya shiga watan haihuwar shi, komai Alhaji ya fita ya gani na jarirai zai siyo ya kawo mata, murna yake yi sosai saboda za a haifa masa ɗan shi na halal mallakin sa, in yana wa Hajiya Babba karad'i da zumud'in haihuwar sai ranta ya na ɓaci kishin ta ya bayyana ta kauda kai, a haka ya gane itama ba son babyn take ba, Sahabee ma bai wani damu ba ko a haihu ko kar a haihu oho,Iya ce kawai ke taya shi murna kusan kamar tafi Alhaji son wannan abinda za a haifa d'in ma, duk shekarun ta ace bata taba ganin jikan ta ba ai dole ta yi ta d'okin ganin wannan da za a samu yanzu.
Eamaan girki take yi a kitchen din Iya hankali kwance, juyawa tayi ta d'aga qafa zata dakko muciya ta tuqa tuwon shinkafa da take yi ta ji qafar ta riqe ta kasa gaba da ita ko baya, abu kamar wasa sai da ta kwalawa mai aiki kira, da kyar ta taimaka mata suka shigo parlourn Iya ta zaunar da ita a kujera, zaune Iya take ita da Alhaji suna hira suka ga an zaunar da Eamaan a kujera, miqewa suka yi da sauri suka isa wajen ta suna tambayar lafiya? Ita kuwa babu abinda take yi da ya wuce kiran sunayen Allah, Alhaji ne ya kama ta suka fita sai wajen mota, da kan shi ya ja su suka tafi asibiti, ba a jima ba kuwa Allah ya sauke ta lafiya, ta samu yarinya kyakkyawa qatuwar gaske ga ta fara fat kamar iyayen ta, se kuka take zabgawa, da fari Iya ta ma zaci namiji ne saboda kukan da take tsalawa saida aka bata jinjirar taga ashe mace ce sai tace,
" Sannu ci mu ci acici kajin binni,to bismillahi daga zuwa duniyar mu an fara wage mana baki ana son a ci abinci dan wannan kukan da ji na yunwa ne"
Nurses ɗin da suka miqo musu jinjirar kuwa dariya suka Sanya, Iya kuwa tace,
" Yo Allah yarinya sai d'anneman cin tsiya,Kai da gani wannan se an aje wa uwar ta buhunan gero da farar shinkafa da gyad'a dan yin kunu kawai" Dariya suka sake sanyawa suna tsokanar Iya da kishi ne kawai ke damun ta.
Suna nan zaune ana duba lafiyar baby da Eamaan dan haka ba a sallame su da wuri ba sai dare,asibiti kamar zata tsage dan mutane dake zuwa taya su murna,ba a bar Ammaah da Mama wajen bayyana farin cikin su,har da kukan farin ciki Ammaah ta yi sanda labarin haihuwar ya riske su, likitoci ne sika yanke zasu sallame ta kawai tinda an haihu lafiya.
Sun dawo gida cike da murna da farin ciki, Sahabee da ya ga yarinyar sai da ya yi tasbihi ga Allah dan ganin kyaun ta, a zuciyar shi ya nema mata tsari da haɗuwa da maza irin su shi da uban ta, yarinyar ta kwanta masa a rai sosai.
An yi suna yarinya taci suna Fateema suna kiran ta da Fatee, yarinyar da alama za ta yi wayo da wuri duk wanda ya wuce sai ta bi shi da ido.
Gaba ɗayan ahalin gidan na zaune a sashen Iya har Baby Fatee suna ta hirar duniya suka ji an k'wank'wasa qofa, Sahabee ne ya je ya buɗe qofar, abinda ya gani da mutanen da ya gani sun firgita shi ba kadan ba hankalin shi ya tashi, dan yasan yau kam ta Alhaj ta qare, da baya-baya ya koma parlourn yana nuna masu hanya da hannun shi, Alhaji fad'a ya fara yi masa yace,
" Meye haka ne ka dawo kana abu kamar wanda ya yi gamo? Su waye ne suka zo? Matsa ni na ga ko su waye zasu shigo man gida kai tsaye cikin iyali su rikita ka ha.........."
Maganar shi ce ta maqale da ya yi arba da su, har wani dan tintsirawa ya yi kamar an hankada shi ya yi baya kamar zai faɗi.......
*Hahaiiii casssss gamo ya yi da mutan boye hala*🤣🤣🤣
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 16:
Ganin hukumar EFCC a gidan Alhaji ba qaramin tada wa kowa hankali yayi ba, jikin shi har rawa yake yi a lokacin da ya koma ya zauna,suna shiga suka samu waje suka zauna suma kamar gidan su tare da gabatar da kawunan su da kuma abinda ya kawo su,babu b'ata lokaci suka fara binciken Alhaji daga fatari har fataari, duk wata dukiyar shi sai da aka karɓe da sunan za a yi bincike akai idan haqqin shi ce za a dawo masa da ita, idan kuma ta gwamnati ce to fa gwamnatin zata karɓe wataqila har hukunci ma ya biyo baya,ganin yanda suke yi masa abubuwa cikin cin zarafi da wulaqanci ne ya koma tunanin anya wannan hukumar EFCC ne ma kuwa?
Amshe dikkan kadarorin shi da hukumar tayi ne ya sanya jikin Alhaji ɗaukan rawar sanyi, Eamaan kam ta dad'e da fara kuka saboda matsanancin tausayin mijin nata da ya kama ta,abubuwan da suke samun shi akai-akai na musibu sun yi yawa.
Eamaan da Iya sai kuka suke zabgawa babu mai lallashin wani a cikin su,Alhaji kuwa yana zaune shiru banda karkarwa babu abinda jikin shi ke yi, ma'aikatan hukumar da kansu suka dinga shiga lungu da saqon gidan suna ɗaukan takardu da dik abinda yayi musu, Hajiya Babba kuwa takaicin kwashe mata sarqoqin zinaren ta dik shi yafi damun ta har ya sanya ta kasa yin kukan ma, shi kuwa Sahabee baqin cikin yanda aka k'wace komai ba tare da ya samu wani abu daga wajen yayan nashi ba shi ya sanya shi zabga tagumi yana bin kowa da kallo,daga gidan da suke ciki sai motoci biyu kawai aka bar musu.
Suna cikin wannan halin na jimami aka sake k'wank'wasa qofar parlourn Iya,nan take Alhaji yaji k'wank'wasawar har cikin tsokar zuciyar shi,gani yake yi kamar wata musibar ce ta sake tinkaro shi da iyalan shi,babu wanda yayi jarumtar amsawa mai k'wank'wasawar daga qarshe dai da kan shi ya buɗe ya shiga parlourn cike da isa da taqama, Alhaji Saminu ne yake ta zabga murmushin da yafi dacewa a kira shi da sassanyar dariyar samun nasara kafin yace,
" Alhaji Abdullahi kenan a zaton ka zaka samu kuɗin gwamnati ka sace ka killace dan ka mora kai da iyalan ka ba tare da gwamnati ta k'wace abinta ba? to bari kaji wani sabon albishir da zan yi maka dan na kula baka kalli news ba jiya kana nan kana shanawa da wannan kyakkyawar matar taka ko? Albishir ɗin shine majalisa ta sauke ka daga muqaminka yanzu haka ana can ana jefa quri'ar samun madadin ka,kai kuma kana nan a nade wajen mata,"
Ya na gama faɗin maganganun nashi dake kama da shaqiyanci ya kwashe da dariyar mugunta harda tafa hannayen shi,a harzuqe Alhaji yayi kan shi da niyyar yi masa dukan tsiya,kafin ya qarasa gaban Alhaji Saminu ya yanke jiki ya fad'i a qasa yana ta wani abu kamar mai bugun iska.
Ihu Eamaan ta sanya ta ajiye Fatee ta nufe shi tana jijjigawa, Iya kuwa jinin ta ya jima da hayewa ganin ta gaba ɗaya yayi rauni jinta take yi kamar ba zata kai gobe ba saboda tsananin ciwon kai da bugawa da zuciyar ta keyi dan haka ko yunqurin zuwa wajen Alhaji bata yi ba,dan kuwa ta riga ta san da ta miqe se dai a yi biyu,sunan Allah kawai take ambata dan shine mafitar ta a wannan halin da suke ciki.
Eamaan kuka take tayi sosai ta na yima Sahabee magana akan ya rabu da Alhaji Saminu daya dunqunqunewa wuya ya zo akai Alhaji asibiti,amma ya qi sai naushin Alhaji Saminu yake yi yana zagin shi, shi kuma yana dariya kamar ba jikin shi ake duka ba.
Jikin Alhaji Abdullah ne ya saki ya daina motsi Eamaan kuwa sai ta fasa ihu da qarfi wanda ya ja hankulan Hajiya Babba da Sahabee,Waje Sahabee yaje ya hau kiran masu gadi da driver akan su zo su taimaka masa, suna zuwa kuwa suka hau ciccibar Alhajin suka fita dashi suka sanya shi a mota .
Asibiti suka kai Alhaji nan da nan likitoci suka duqufa akan shi dan duba lafiyar shi, ba shi ya farfado ba kuwa sai da asubar washegarin ranar da suka kaishi asibitin, Eamaan ta ci kuka ta gode Allah har ta hakura ta barwa Allah komai, Fatee kuwa sai kallo take bin kowa da shi,lokacin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 20