sauri ta ɗauke idon ta ta kalli gefe, cikin ranta tace,
'shifa wannan tsohon sam naga kamar bai san kunya ba, ko dan yaga ina mai haka ne? Shi bai san daurewa nake yi bane? Haka kawai yau yanda ya wuni baya gida zan barshi ya hau min gado ba wanka,ai bazan iya bacci ba,gashi ya ci abinci kuma be yi brush ba zai kwanta,aiko yau dana shiga uku in yayi min irin abun d'azu da safe kafin ya fita,amai zan yi na tabbata'
Tana maganar zuci take gyara jikin ta,wata rigar bacci ta saka mai ɗan kauri kuma ba wata mai nuna jiki ba, amma duk da haka ta yi mata kyau,rigar fara ce sol, sai ta hannu da wuyan ne aka yi musu ratsin blue me haske, zani ta daura a saman kayan ta ɗora hijab, ta shimfid'a masu sallaya ta zauna zaman jiran shi, sai tashin qamshi take yi, yana fitowa ya gan ta a zaune a sallaya sai ya kauda kai, ya shirya cikin kayan bacci riga da wando kalar fari shima, kallon ta ya sake yi yaga abun salla biyu ta shimfid'a, sai yace mata,
"Me zaki yi ne na gan ki anan a zaune? daman baki yi salla bane?"
Kad'a ido ta yi ta kifkifta su sannan tace,
" A'a na zaci zaka ce muyi nafila ne irin na sabon aure da na ji ana yi tinda na ga ba mu yi ba mu,bana son sai ka fito ne sannan kace na shinfida abun sallah, nafi son na dinga yin abu mai kyau kafin ka bada umarnin yin shi,"
shi dai bai ce komai ba ya nufi inda take zaune,amma shi bai san wata sallar sabon aure ba, abinda ya sani baya wuce kawai akai masa mata ya kwanta bacci ya biya buqata ya miqe shikenan,
"To miqe muyi sallar raka'a nawa zamu yi babyn Alhaji?"
Sanar da shi tayi komai tayi a lokaci ɗaya dan ta yi saving kanta da tambaye-tambayen da zai ta yi mata, sallar suka yi,bayan sun idar ne yayi mata addu'a yanda ta koyar da shi da Hausa,dan ta kula se su kwana be riqe larabcin ba,sannan suka miqe suka hau gado, kashe fitila za ta yi,yace sam bai san zance ba, tsoron duhu yake yi, dariya tayi ta masa yanda ya nuna da gaske tsoron duhun yake, dama tin da ta zo sai sun yi wannan dramar kashe fitilar da dare, komawa ta yi ta kwanta ya matsa ya dauke ta cak ya dora a jikin shi, daga haka Alhaji Audu ya sauya salon tsokanar da Eamaan ke yi masa......
Kafin ya gama abinda yake yi idon ta da zuciyar ta sun kumbura kamar su fashe ,ba dan komai ba sai dan kukan zahiri da badini da take yi, ga kunya da ke addabar zuciyar ta da wanne ido zata kalle shi da safe kuma? Mutumin nan fa sa'an Daddyn tane,amma ya zauna ya baje basirar shi a kan ta.
wayyooo ina zata sa kanta da wannan lamari yau? Alhaji Audu kuwa lallashin ta yake tayi sosai, tare da mata alqawurran jin daɗin rayuwa kala-kala, shi a zaton shi kayan more rayuwa sune a gaban kowacce mace, bata ce masa komai ba, ta miqe da kyar ta yi bayi,ruwa mai d'umi ta shiga ta zauna,sai da ta ji jikin ta ya yi mata dai-dai sannan ta bari, tai wankan tsarki ta fito d'aure da alwala,lokacin qarfe 2 na dare ne, nawafil tai tayi tana kumawa, a sujjadar qarshe ta samu tai addu'a akan neman zaman lafiyar su, da roqon Allah ya bata jimirin yi mai biyayya,sannan ya yaye mata soyayyar Anwar a ranta ko za ta ji dad'in zaman gidan mijin ta, tana haka taji ya saki wani wawan minshari, addu'a ta ci gaba da yi ta na kuka a cikin sujjadar ta, ta sauke babban nauyin da Auntyn ta take ta mata nuni akai d'azu, ta tabbata a yanzu Anwar yayi mata nisa,dan haka dole ne ta yi hakuri ta rungumi mijin ta da auren ta tin kafin lokaci ya qure mata, Wani shiga damuwa da tashin hankali ba nata bane,a hankali ta miqe ta haye gado ta kwanta ta rintse ido da fatan bacci ya ɗauke ta dena jin rad'ad'in da zuciyar ta ke yi mata.
Asubar fari ta tashi tai sallah amma Alhaji Abdullah yana nan kwance yana bacci, dabara ce ta faɗo mata a ran ta,wayar ta ta sa ta kunna karatu ta ajiye a gefen kan shi, karatun ne ya tada shi,nan take kuwa ya buɗe ido yana guntun tsaki, ita ya gani kusa da shi tana yi masa murmushi tare da sunne kai qasa alamar jin nauyin shi, nan da nan abinda ya faru a daren jiya ya bijiro wa ƙwaƙwalwar shi, shima murmushi ya saki wanda be shirya wa, a can qasan ranta kuwa tana jin haushin shi saboda barin ta da ya yi tayi jinyar kan ta, shi Kuma ya baza ciki da baki yana bacci, sake murmusawa ta yi ta sunne kai qasa sosai, cikin murya cike da shagwab'a tace,
"My Sweet yau ma zaka makara sallah fa, ni bana son kowa na samun lada ana wuce mijina gaskiya,"
Sai juya baya irin na shagwab'ab'b'un nan, bacci ne fal idon shi amma baya Jin zai iya jure wannan salon nata, ga wata iriyar shagwab'a da juya jiki da take yi wanda be saba ganin hakan ba a wajen matan shi da sauran karuwan da yake mu'amala da su saboda ya gama yarda Eamaan ta daban ce a cikin mata, tashi ya yi bai kula ta ba ya shige bathroom ya yi wanka sannan ya zo ya yi sallah,ko addu'a be tsaya yi ba ya koma gado abin shi tare da Janta jikin shi dan su koma bacci,shafa fuskar ta ya yi a hankali sannan yace ,
"To na yi sallah lada be wuce mijin ki ba , mu koma bacci dan ni bacci nake ji,"
Ba tare da ta musa masa ba kuwa suka koma baccin su.
Tin daga ranar Eamaan ta zama kwararriya wajen yi ma Alhaji wayo na sa shi yin duk wani abun da ba yayi a da musamman ta bangaren ibada, wajen wanka da brush ɗin dare dana asuba kuwa yanzu shi da kan shi in bai yiba ma zai ji ba daɗi, matan shi ma sun ga sauyi sosai a tattare da shi, Iya ma uwar sa ido sai da ta ga ɗan nata gaba ɗaya ya sauya, har masjid yana fita yanzu, amma taurin kai na tsohuwar nan ba abinda ke haɗa su kuma ya raba su da Eamaan sai zagi, da kyara,ita ko bata nuna mata wata alamar ta ji haushi dangane da yanda take mata a gidan, iyaka in ta mata abinda ya mata zafi sosai,sai ta dawo sashenta ta sha kukanta ta bawa Kan ta hakuri, sannan ta Kuma tina wa Kanta cewar dama zaman BIYAYYAH take yi a gidan ba zaman soyayya ba,Dan haka zata jure komai watarana sai labari.
Babban abin da ke damun ta yanzu be wuce matsalar neman matan shi ba da ya dawo da shi, dan kuwa har yanzu bai dena ba, tana yawan ganin condom a kayan shi, rannan ma da yaje Abuja girki ya fad'o ta wajen ta used condom ta gani a aljihun sa na babbar riga,abun na matuqar bata mamaki wai shin wannan jaraba har ina, kuka take yi sosai in ta ga hakan, ace mata har uku amma ba zaka daina neman mata ba? ta qudurta indai ita mace ce da yardar Allah sai ya daina bin matan banza.
A cikin wata na uku da auren su Eamaan bata taɓa zuwa gida ba dan ganin iyayen ta da ta yi kewa sosai, dan haka yau ta roqi Alhaji da ya barta taje ganin Ammaahn ta, kullum sai dai su yi waya ta gaji da hakurin rashin ganin mahaifiyar ta,Mama Kareema ma ta matsu ta gan ta tana son zuwa amma basa shiri yanzu da matan Alhaji shi yasa bata zo ba,sunce da munafurcin ta aka haɗa baki aka yi masu kishiya da d'iyar su, da kyar ya yarda dan Alhaji ba dai kulle ba.
To fa dama kunsan mai aikata zina ko wani mugun hali, kullum tsoron shi kar nashi su fita ayi da su, bai san in dai kana yi ba sai an yi da naka komai kullen ka, sai dai in ka tuba ka bi Allah, Allah ya yafe maka ya kuma kare zuri'ar ka.
Gaye tasha sosai na zuwa gida tana gamawa ta rufe wajen ta ta bi wajen Iya dan yi mata sallama, bayan ta gaida ta ne ta sanar da ita cewar Alhaji ya bata izinin zuwa gaida Ammaahn ta.
"To in ya baki izini ni ban bayar ba ba zaki je ba,kina ganin ai gidana ya yi datti amma ba zaki taya a gyara ba, maza jeki d'akko kayan gyara ki gyara min sashe na dika, zan je wancan ɗan filin kan ki gama sabida qura,"
Sake baki Eamaan tayi idon ta fal hawaye tana kallon tsohuwar,tin da tazo ita fa ke gyara ma Iyan bangaren ta, ba kuma wanda ya saka ta, ita ta saka kanta da kanta,amma yau da zata je gida ace ba zata ba saboda mugunta?wata zuciyar na cewa ki ajiye mata kar ta share ta kwana a dattin, wata zuciyar kuma na cewa ki yi hakuri ki gama mata sai ki tafi,duk wanda ya girmama uwar wani za a girmama tashi, balle ma wannan kaka ce a wajen ki ba iyawar zatai ba kiyi ki samu lada, umarnin ta kamar na Ammaahn ki ne, dan kuwa uwar miji itama uwa ce,
"Zaman me kike yi har yanzu baki tashi daga gaba na ba? Ko amsa kike ban akan ba zaki yi ba Na saka mijin ki yayi min?"
Da sauri ta girgiza kai ta miqe tsaye ta yi hanyar waje inda kayan shara da goge-goge suke, hawaye wani na korar wani haka suka dinga zuba daga idanun ta, haka Eamaan ta fara shara ta gama ta hau goge-goge sannan ta yi mopping,kan ta gama ta gaji sosai, bangaren Iya ɗaki biyu ne sai babban Parlorn nan da suke taruwa su ci abinci ko a zauna hira a duk sanda ta so, sai toilet a kowanne d'aki, duk haka ta gyara ta wanke su, sai qarfe biyu da rabi na rana ta gama tinda dama bata fita da wuri ba, ganin gida zata je shi yasa bata sani damu da fita da sassafe ba sab'anin wasu matan dake doka wa iyayen su sammako kamar wanda gidan su ya gundire su ko ake yi musu wani abun, sallama ta yi mata zata tafi Iya tace,
"Ina kuma zaki je kamar mai daukar wuta, shin wai ni saurin na meye haka, ba dai Audun bane ya barki? Na sa shi ya qara barin ki watarana yau Sahabee zai zo ke nake so ki yi mai abincin nan naki mai dad'i, dan taryar shi,"
Fashewa Eamaan tayi da kukan da take ta dannewa, dan ba qaramin baqanta mata rai Iya ta yi ba, ace duk ta san da wannan, bata faɗa mata ba tin jiya da ta zo ta gyara mata gidan sai yau da take d'okin zuwa gida? amma gaskiya ba a kyauta mata ba sam,Iya na ganin haka sai ta qanqance ido tace,
"kuka fa naga kina yi tsohuwar ki na zaga ko tsohon ki? Ko salon munafurci wani ya shigo yace na sa matar d'a a gaba da baqin hali ko, to baza ki jazan masifa ba, miqe kije tinda bazaki yi ba na saka masu aiki suyi masa girkin,ko na kira Audun na faɗa mai banda ikon sawa ko hanawa agidan shi,"
Da sauri Eamaan ta share hawayen ta har yanzu ta kasa furta komai, kitchen taje ta fara aikace-aikacen da za ta yi, ba ita ta gama komai ba sai wajen huɗu da kwata na yamma, direct bayan ta jera komai jakar ta ta dauka da mayafin ta tai bangarenta ta bude ta shige, daki ta shiga da gudu ta faɗa gado tai ta kuka tin qarfin ta, sai da ta yi mai isarta sannan ta miqe taje tai wanka ta sauya kaya, ta saka dan gajeren wandon ta mai kama qugun ta da kyau ya fidda mazaunan ta yanda ya kamata da half vest,sai ta d'aure gashinta ta nade shi,kitchen taje ta d'akko ice creem ta zauna a kujerar parlour tana sha tana ajiyar zuciya, Ihun yara ta jiyo sai ta miqe kaɗan ta leqa window,daga nan ta hango shi yana fitowa daga motar shi,lallai sun yi kama sosai da Alhaji dan kuwa ba laifi kyakkyawa ne,amma Alhajin su ya fi shi kyau, fari ne dogo sosai har ranqwafawa yake saboda tsaho da siranta, sakin labulen ta yi ta koma ta zauna tana ci gaba da ajiyar zuciyar kukan da ta sha, da robar ice cream a hannunta tai bacci a doguwar kujera,bata san iya lokacin da ta ɗauke a haka ba, taji kamar kallon ta ake yi, tana bude ido suka sauka a saman fuskar shi da ta firgita ta.........
*wane na yasshigo mana gida babu ko sallama jama'a?*😱
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
RUBUTAWA:HAERMEEBRAERH
Page 5:
"A'udhubillahi minasshaid'anirrajeem,waye kai? Meye haka zaka shigo ba ko sallama, ko an faɗa maka nan ɗin gidan arna ne, dalla malami fita daga nan,Kuma koma waye kai baka da d'a'a, FITA MANA NACE NA SUTURCE JIKI NA"
Da fari Ido ya zuba mata ya na Jin sautin muryar ta kamar busar sarewa a kunnuwan shi,tinda yake tsalle-tsallen shi daga gida Nigeria har waje be tab'a gamo da mace kamar Eamaan ba, a zaton shi ko baquwa amaryar sashen ta yi kyakkyawa haka, dan be tab'a ganin makamanciyar shigar qananan kaya a jikin kowacce mace a gidan ba sai yau,tsawar ta ta qarshe ce ta bashi tsoro ya dawo cikin hayyacin shi,kallon idanun ta ya yi ya tabbatar da wannan fuskar ba alamar wasa a cikin ta, fita ya yi salalo-salalo da dogon wuya ya koma bangaren Iya,yana shiga ya zauna dabar yana dogon nazari, Iya kuwa bin shi kawai ta yi da ido, tinani ya hau yi shin wai wannan 'yar yarinyar ce ta daka mai tsawa kuma ya bi umarnin ta kamar Wani soko? Lallai sai ya koya mata hankali ko ita wacece, sai ya nuna mata bariki fa sune iyayen ta, dan ta yi shigar 'yan bariki take zaton ita wata ce? Lallai rashin sani ya fi dare duhu in ji bahaushe, kwafa ya yi ya janyo jug ɗin da ke cike da juice ya tsiyaya ya sha,wani gard'i ne ya buge masa kunne sai ya d'aga glass cup ɗin yana kallo, duk abinda yake Iya na kallon shi sai kawai tayi murmushi tace,
" Labartan abinda ya faru daga fitar ka zuwa dawowar ka yanzu,"
kwafa ya sake yi a karo na ba adadi tin shigar shi parlourn sannan ya zayyana mata haɗuwar shi da budurwar sashen amarya, ya qara da cewa,
"Har ni zata kora da kakkausar murya, wai na bar mata waje ta suturce jikin ta? Ni wanne kalar jiki ne ban gani ba kuma ban taɓa ba,daga na turawa har larabawa zuwa baqaqen fata namu na nan,ni zata faɗawa jikin ta?"
"Dole ta faɗa maka jikin ta mana d'anneman lalatacce( ita take lalata shi kenan tin da ga sunan da ta faɗa masa wai lalatacce)kai da ko kunyar faɗin kai mazinaci ne ba ka yi, a gabana kakr faɗan wacce kalar mace ce baka taɓa ba ko?,saboda ka gawurta, na rasa me yake damun ku Kai da d'an uwan ka, kamar Waɗanda na tsugunna na haife su a gidan magajiya,mtsss maza d'auki abinci kaci soko kawai,Kuma ka sani wannan yarinyar da ka ke magana akai matar Yayan ka ce,dan haka ka kula"
Tashi ta yi ta na ta surutai har ta shige d'akin ta.
Abincin shi ya ɗauka ya na ci siffar Eamaan da surar jikin ta da ya gani a kashingid'e a kujera nayi masa yawo a kwanya da zuciyar shi, ba wai tsananin kyau ne da ita ba, ah ah kyau ne wanda yake da ɗaukar hankali, sura ce da ita ta daban me ban mamaki ,da tinanin ta ya kammala cin abincin shi da yake Jin dad'in shi har tsakiyar Kan shi.
Eamaan kuwa bayan fitar shi ne ta tashi ta sako doguwar riga akan kayan,ta yafa dankwalin rigar ta d'akko wayar ta ta duba lokaci ta ga lokacin da ta saba yin Chatting da qawar ta ne saboda yanayin aikin ta bata so tana shiga lokacin aikin ta tafi so sai ta tashi daga aiki su sha hirar su a nutse,cikin sa'a kuwa ta ga Aishan online sai kawai suka hau hira.
Eamaan :'Assalamu alaikum Babe y kk'
Aisha :'Gud..sarkin qa'ida tin dazu nake jiran ki hawo online mu sha hira sai in ga time din hawan ki be ba, ni ki na bani mamaki fa sosai Eamaan, a wannan zamanin wa ya damu da wani amfani da lokaci irin haka? Ko ni da nake aikin ma na ce miki ki dinga hawa online zaki same ni a kowanne lokaci amma se ki qi kice sai na taso aiki,',
Eamaan : 'Hmmmm Ayshaa kenan, kiyaye lokaci kuwa na da matuqar mahimmanci a wajen d'an Adam, a kalla ko ba ka zama me tsananin kula da lokaci ba ka zama ka San me ka yi da lokacin ka, kar ya zo ya wuce a banza baka mora ba ba a more ka ba, sannan in bama kula da shi sai ajalin mu ya riske mu bamu tab'uka komai ba, bamu Samar wa kammu mazauni me kyau ba a aljannah,ke ni raina ne ma a b'ace'
Aisha : Haka ne kuma...amarya da b'acin rai? meke faruwa?😱'
Eamaan: 'Allah wani wawa ne kawai ina zaune ya fad'on min cikin parlour ba ko sallama, gashi ba wata suturar azziqi a jiki na, daga ni sai qananan kaya, dadikkan alamu Qanin Alhaji ne da ake fad'ar zai dawo, Dan kuwa yanzu da nake tuna fuskar shi a raina na ga kamannin shi da Alhaji,akan shi aka hana ni zuwa ganin Ammaahna,in Alhaji ya dawo zan Sanar da shi me ya faru'
Kamar Aysha na gaban ta haka take magana, cike da shagwab'a.
Aisha: 'Babe kar ki damu,kar ki sakar mai fuska ko da wasa,ki yi hakuri kuma kar ki fad'awa kowa ya shigo maki Kai tsaye Kuma ki gyara yanayin Sanya suturar ki a gidan, tinda kin ga yanzu ba ku kad'ai bane, ko Kuma in kin san kin yi irin shigar nan ki na kulle sashen ki'
Eamaan : 'Eh na gane na kuma gode, dan da har na fara tinanin sanar da Alhjin,'
Aisha: Kar ki fara, daga zuwa ki fara Kai qarar qanin miji ba tare da kin san matsayin shi wajen mijin ba, ke dai kawai kar kina sakar masa fuska ko ki bashi damar zuwa bangaren ki ma kwata kwata, sannan ma baki da tabbas ko qanin shi ne ko ba qanin shi bane"
Eamaan: To na gode sai anjima bari mu je mu gana da ubangijin mu,dan an Kira sallah, kin san gwanda komai kana yi kana kula kar ka shiga haqqin Allah"
(ba dan chatting aka halicce mu ba dan bautar Allah aka halicce mu, ya kamata 'yar uwa ki ribaci lokacin ki, kar ya lalace a banza, ya zamana kina da lokacin yin komai, ko da a online kike kullum kuma ko wanne lokaci, to ya zamana aikin da zaki samu lada wajen Allah kike yi, balle akwai Application na Qur'ani a waya zaki iya kunnawa ko ki bude ki karanta, in baki karanta shi kina tasbihi, in baki tasbihi kina fad'akarwa akan aikin Allah, banda zaman banza sisters)
Miqewa ta yi tayo alwala, tai sallar magrib, ta zauna a nan inda tayi sallar tai azkar,tana nan zaune har aka kira isha'i ta dora sannan ta ninke kayan sallar ta, wanka ta sake yi na dare, sannan ta saka kayan bacci, ta haye gado in da sabo ta saba dad'ewar Alhaji a waje, cikin ranta ba qaramin qyamar shi take ba saboda sai yaje wasu sun gama jagwalgwala shi ya dawo ya sauke masu dattin zina a jiki, hawaye ne suka zubo mata.
" Yah Allah ka sani ban kasance daga cikin mazinata ba, Allah ka shiryar da mijina, ka yaye mishi neman matan waje qazamai da yake yi, Allah ka sa ya zamo daga cikin bayin ka tsarkaka masu tsoron ka a duk inda suka sami kan su, su dinga tunawa da cewa kana ganin su idan su basu ganin ka,"
Alhaji Abdullah ba qaramin jin kunyar addu'ar da ya riske ta tana yi da qarfi yayi ba, a hankali ya koma baya dan a zaton shi ta yi bacci a wannan lokacin, zama ya yi a kujerar parlorn ya dafe kai, yau ce rana ta farko daya taɓa jin nadamar wata aba wai ita zina, dan kuwa a baya shi bai ɗauke ta a komai ba, a hankali ya miqe yayi sallama a d'akin dan ta san da dawowar shi ya shiga, da sauri ta goge idon ta ta rintse Ido kamar me bacci,bai ga laifin ta ba dan tana ma qoqari a shekarun ta, direct band'aki ya shiga,dan a halin janaba ya shigo gidan, yana wanka yana saqe-saqe a zuciyar shi, bayan ya gama ne ya yi brush ya fito, kaya ya saka ya ɗan shafa mai da turaruka sannan ya hau gadon, janyo ta ya yi yanda ya saba akan su yi bacci ta juya fuskar ta jikin shi, idon ta fall hawaye, a hankali ta rintse Idanun ta suka zubo,kallon ta yake da so da qauna tare da girmamawa, dan ba wanda ya taɓa jin yayi mai addu'a irin haka,ko da mahaifiyar shi ce kuwa, a kullum sai dai ta zage shi ta sake aibanta shi akan halin nashi mara kyau.
" Na San idon ki biyu i am very sorry for everything, inshaa Allah zan dena ne, ba lokaci ɗaya na zama mazinaci ba, amma da yardar Allah ina sa ran dainawa wata rana, but i need ur help,"
Cikin kukan da take riqewa tace,
"And i promise to help u in any way possible, ni dai fatana ka dinga qoqarin bari, kan ka bar zina sai ka bar sabab ɗin ta, sabab ɗin ta kuwa sun haɗa da daina halattar wajen da ake yin ta, daina kula abokan yin zinar, da abokan da suke saka ka aikata ta,sannan sai ka kiyaye jin ka da ganin ka ma'ana,sauraron duk abinda zai ja hankalin ka zuwa aika ta zina,kamar misali hirar banza da waɗanda ba muharraman ka ba ,da kuma kallon surar macen da ba muharramar ka ba,ina fatan zaka qoqarta yin wadannan abubuwan,kaga ba ma wasu yawa ne da su ba"
D'aga mata kai ya yi kamar yaro, tallafe fuskar shi ta yi ta sumbace shi tare da murmusawa , hawayen ta ya share mata, sannan ya mannata da qirjin shi, a haka suka yi bacci.
Da safe kuwa bayan kammala duk Wani abu na al'ada da suka saba, Eamaan shiri ta yi me kyau, suka jera zuwa sashen Hajiya Iya, dan yace da kan shi zai kai ta gida yau tinda jiya bata je ba, sannan shi zai je ya dawo da ita, ta yi matuqar jin dad'in hakan da ya faɗa, suna shiga sashen Iya suka ga mutum ya baje daga shi sai gajeren wando, duk jikin shi a waje sai latse-latsen waya yake yi, da sauri Alhaji ya maida Eaamaan baya ya ce,
" kai tashi kaje ka saka kaya, meye haka zaka zauna tsirara,"
Miqewa ya yi ya na sosa qeya ya fad'a dakin shi,Iya ce ta d'ingiso ta fito, yau ciwon qafar ta ya motsa, Alhaji ne ya matsa Eamaan ta bayyana bayan shi,
"Toooo 'yar jakar Audu, ina kuma zaku da sanyin safiyar nan, qarfe sha daya?,"
" Iya barka da safiya,"
"Baka amsan tambaya ta ba, nace ina zaku,"
"Iya zan kai ta gida ne, jiya na ji bata je ba,"
"Ohhhh bayan tijarar da ki kai wa Sahabee jiya, shine kenan yau ki ka tasan d'a gaba sai ya kai ki gida ko?"
Da sauri Alhaji ya d'aga kai daga duqen da yake a gaban Iya yace,
"Me ki ka yi wa Sahabeen jiya?"
Idon ta fal hawaye ta kasa magana, dan dai ta san ita tsakanin ta da wannan zalb'en
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 20