Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Kamal ne ya kalli Hafsat da farin ciki ya bayyana a fuskar ta ya matsa jikin ta ya dora kan ta a gefen jikin shi dan itan tana zaune a hannun kujera ne kusa da Eamaan da ke kukan farin ciki sannan yayi kissing goshin ta, a tare suka yiwa Eamaan godiya tare da fatan Allah yasa Anwar ya bar musu Fateema su riƙe ta na tsawon lokaci. ************************** Anwar na qara murmurewa ya sa aka je gidan shi sabo aka gyara shi fes, dan ba abinda bai zuba ba na more rayuwa dai-dai qarfin shi, komai yayi masa yanda yake son shi, gidan na ɗauke da d'aki hud'u ne sai palour biyu, dinning area ɗaya, kowanne d'aki da toilet ɗin shi, sai Kuma toilet guda d'aya a harabar gidan, gidan ya na da  farfajiya mai girman da zata Iya d'aukan a qalla mota uku, a can bayan gidan Kuma ya yi dan garden me d'auke da kayan wasa na yara wanda manya ma zasu iya hawa lillunan wajen, gidan yayi matuƙar haɗuwa gwanin sha'awa,yana tafe ya na kallon  yanda aka tsara gidan ne ya ji qarar saqo a wayar shi, daya duba sai yaga No Kamal ne ta turo mai wata Number waya a qasa an  rubuta *Ur sweetheart No* wani dad'i ne ya kama shi, dan dama yana son ya aika kuɗi yace kamal ya sai mata waya mai kyau amma da alama Kamal d'in ya riga shi, shi kuwa me zai yi ya biya Kamal kyautatawar da yake yi masa, saving ya yi da 'My one' ai ko yana gamawa ya shiga ɗaya daga cikin palourn ya qame a kujera ya danna kiran layin na ta, Eamaan na can na ta faman koyawa Hafsat girki ta ji wayar ta na ringing wanke hannun ta tayi ta d'aga tare da yin sallama a zuciyar ta tana mamakin waye wannan da ya samu No ta sabuwa haka? Iya sanin ta ba kowa ne yasan tana da waya ba. Ajiyar zuciyar da ya sauke ne da ƙarfi ya sanya ta dafe jikin cabinet na kitchen ɗin ta jingina dashi tana murmushi mai sauti, Hafsat na ganin haka ta daki kafadar ta ta ce, "Sarakan soyayya bari na kwab'a na yau na tara  a gaba, na San yanzu ko wuqa zan caka maki ba ji Zaki yi ba," Fita ta yi ma daga kitchen d'in kwatakwata ta tafi d'aki ta kwanta a gado ta mimmiqe ta na sauraron muryar Anwar d'in da ke ratsa dik wata kafa ta jikin ta. "Kin san me?" " A'a sai ka fada" " Ina gidan mu yanzu haka,inda zamu zauna ni da ke da Fateema nake nufi,ina kan doguwar kujera a kwance nace bari na kira ki naji muryar ki,yanzu iwar haka inshaa Allah wani satin kina gefe na a kwance muna hira ko?" Cike da jin kunya kamar yana ganin ta ta rufe idon ta, " Kaii Daddan Fatee, ni dai ba ruwa na, babyn ka na jin ka, gata a kwance tana bacci" Dariya ya yi dan ya san wayon ta,gani yake kamar kunyar ta tama qaru ne akan tada da take budurwa, anya zasu sha amarcin da yake hango masu kuwa da wannan kunyar tata? "Ita ma Fateeman ai ta shaida Daddyn ta na son Mummyn ta sosai, dan in ba ita ba zai iya rayuwa ba, sauran qiris na mutu Abbana ya taimaka ya yi ma Daddyn ku magana aka daura auren mu," Nan ya kwashe komai ya sanar da ita har halin da suke ciki shi da Hajiyan shi, " Allah ya qara maka lafiya Daddan Fatee, amma gaskiya banji dad'in yanda ka yi wa Hajiya magana ba, waya faɗa maka ana jayayya da iyaye ta yanda ka yi? Ko kuma kai fushi da su? Kar ka manta fa dik BIYAYYAHr da na yi wa iyaye na Kai ne sila, tarbiyyar da ka dinga d'ora ni a Kai ta yin BIYAYYAH wa iyaye ita ta Kai ni ga auren Alhaji, gashi yanzu alhamdulillah naga ribar BIYAYYAH Anwar, ko kasan sanadin BIYAYYAH ne yanzu zamu yi aure? So kake in mun samu yara muma in mun musu fada suna fushi da mu? idan baka son haka ta kasance damu ka baiwa Hajya hakuri ka daina mata yanda kake yi mata kaji nawan," duk abinda take fada yana yi yana bata amsa da A'a da eh ne tare da d'aga kai kamar tana ganin shi, "Inshaa Allah yanzu dana koma zan bata hakuri na gode sosai, kuma ki fara shiri nan da sati zaki tare, me kike gani zamu yi na bikin, dinner ko walima?" "Ni gaskiya bana son yin wani bidi'a na fi son auren mu ya yi albarka,domin kuwa auren da aka yi cikin ƙanƙanin kashe kuɗi yafi albarka,sannan auren da ba a sab'awa Allah ba wajen nuna murna Shima ya fi albarka, dinner din yanzu da ake Banda nuna tsiraicin amarya, se rashin kunya da fitsara da ake yi, ga kad'e-,kad'e na mutanen da ba addinin mu d'aya da su ba, ga Raye-Raye da zaka ga mata da maza ana yi, dan haka mu yi walima a cikin gida kawai, yan uwan mu da abokan arziqi su hadu aci a sha kowa ya sa mana albarka shikenan, ko ya kace?" Yaji daɗin maganganun ta sosai dan ta nuna mai tana aiki da ilimi, shiko zai bata mamaki wajen sata ta ji dad'i a rayuwar ta, "Shikenan yanda kk ce haka za ai gimbiya ta, jibi ina hanya," "Ko kazo ba zaka ganni ba,dan kuwa ba zan fito ba, sai sanda aka kaini za ka ganni," Yana kwance ya d'ago ya zaro ido, " lallai da kin azabtar da mu kuwa, habaa ke kuwa kar mu yi haka da ke manaaa," Dariya ta yi ta masa ta jaddada masa ba fa zai gan ta ba,haka ya hakura yace to kuwa ba zai dawo ba, har sai an kai masa ita, haka suka yi ta soyayyar su ta waya, suka ci gaba da tsara yanda zasu yi zaman su in Allah ya kaisu ranar da zasu kammala mallakar junan su. Amarya ta sha gyara sosai, da kan ta take gyararrakin jikin ta, wanda da dama da kayan da muke dasu ne na cikin gida take amfani dasu irin su fruits, madara, baking soda, da sugar gishiri da sauran su( ku duba novel dina na baya 'YAN ABUJA, WATA UWAR,DA KAINE JARUMI, 'YAR RAWA zaku samu kayan gyaran jiki inshaa Allah, ko kuma ku sayi littafin MAIDA TSOHUWA YARINYA za ku ga yanda ake gyaran jiki da natural abubuwan da muke dasu a tare damu 09031416423) Eamaan ta yi kyau sosai, ba kad'an ba, Kamal kullum sai ya tsokani Anwar ta waya akan irin kyan da yaga Eamaan tayi, shi kuma ya yi ta jin kamar ya yi tsunstu ya zo ya ɗauke ta, wataran in ya ji yabon ya yi yawa, yakan ce masa, "Malam she is my wife oo,ya kamata a dena kallon ta da yawa haka," Kamal ya kan yi dariya sosai sannan sai ya bashi amsa da "Ni da nake da Hafsat me zan da Eamaan?" Anwar da kamal sun zama manyan abokai fiye da yanda sukw a baya,a dik sanda Anwar zai ga kiran kamal to fa zai ɗauka cikin sauri da gaggawa dan yaji yanda Eamaan ɗin shi take. ************************* Wanka Sahabee da amaryar shi suka fito a tare, daure take da towel iya guiwa duk qafar ta da tasha man bleaching ta yi kala biyu nan baqi can fari, sai gwaguis ɗin gashin ta da ya sha relaxer qeyar duk ta cinye, sai kad'a jikin ta da yake a sake shakaf take faman yi ita a dole ga wayayyiya ƴar bariki, sai buɗe gajeren hancin ta mai faɗi take yi kamar salansar babur. Amaryar Sahabee ba kyakkyawa bace, sannan ba za a kira ta da mummuna ba a tashin farko,shi kuwa a wajen shi babu macen da ta kai ta kyau a idanun shi dan haka duƙawa yayi ya dakko bokitin wankan da kwandon wanka ya biyo bayan ta, Iya na ciki bata San ma sun shiga wanka tare ba, zafi dik ya ishe ta ga warin kashin kaji be gama sakin d'akin ba,dan haka sai kawai ta ɗauko tabarma da matashin Kai ta  fito ta shinfida a tsakar gidan dan ta shaƙi iskar ƴanci. Tafe suke Amarya na gaba angon ta na biye da ita riqe da bokoti da kwandon wanka a hannu,tana ganin Iya a tsakar gidan kwance sai ta koma da baya ta rungumo shi tana wani shafa qirjin shi, Iya da ke kwance ce miƙe zaune ta hau tari babu qaqqautawa, amarya kuwa ƙin sakin Sahabee tayi dik da ƙoƙarin da yake na son zuwa wajen Iya,cikin takaici Amarya tace, "Baby meye haka kuma ina zaka je? Ko kana nufin ba zata yi tari ba saboda gata yayi mata yawa? Wuce mu je ka shafa min mai ni kar na bushe." Gaba suka yi abin su suna shiga ta ɗakko mai ta bashi ya shafa mata sannan ya sanya mata kaya, daga karshe sai ta hau yi masa magana cike da kirsa da shagwab'a tana faɗin taso yin wanki gashi ta yi wanka bata so ta b'ata jikin ta, "Kar ki damu zan wanke maki mene a ciki, ai duk a cikin soyayya ne," Tulo masa kayan ta masu datti ta yi dan tinda aka yi auren su ko tsinke bata taɓa wankewa ba,dan haka kayan wanki gare ta masu yawa, aiko ya na ganin su ya zaro ido yana ayyana anya wannan ba tin daga gidan su tazo masa da masu datti ba? Kan dole babu yanda zai yi ya d'ebi kayan ya je yayi ta wankew. Ita kuwa zaman yin kwalliya tayi a d'akin ,bayan ta gama ta fita tsakar gidan ta dasa kujera ta zauna a gefen shi tana yi masa fari da sun haɗa ido,hannun ta riƙe da mafici tana firfita fuskar ta da ta dame da powder da zufa, data ga alamar ya gaji zata zaro zancen batsa ta watsa masa,nan da nan zai qara qaim wajen yin wankin yana washe baki,Iya da ta ga abun na neman fin ƙarfin ta sai ta tattare shimfidar ta koma ɗakin ta,tana shiga d'akin ta zauna a bakin katifa tai ta kukan baƙin ciki da dana-sanin rashin tarbiyyar da bata baiwa yaran ta ba musamman sahabee, nan take zuciyar ta ta tuno mata Eamaan baiwar Allah da irin muzgunawar da ta dinga yi mata dik tsananin biyayyar da ta dinga yi mata. A ɓangaren amarya Eamaan kuwa........ [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼      BIYAYYAH   💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 26: A hankali Amarya ta maida Sahabee tamkar wani bawan ta, domin kuwa dik wani aiki da ya kamata a ce itace take yin shi sai ta mayar masa da shi aikin shi,shine shara, wanke-wanke,girki, d'iban ruwa da wankin kayan su,a dik sanda yayi girki taci taji bai yi mata daɗi ba yanda take so sai ta sa shi ya siyo a waje. Yana matuƙar wahala wata yazo ya wuce bata je biki ba, babban abinda yafi ƙayatar da ita a zuwa biki shine ɗinka anko,wannan shine babban dalilin da yasa ta ƙware wajen yawan roqon kud'i,abinda dik ya bata da shi zata sayi anko tayi ɗinki idan ya ragu ta kaiwa bokan ta ya qara kafe mata shi ta yanda sai abinda tace yayi kawai zai yi, dik kuma abinda bata so to fa bai isa ya aikata shi ba. Wajen shaye-shayen magungunan mata kuwa an bata lambar yabo dan kuwa ƙwararriya ce a wannan fannin tinda ta gama gano lagon sa,indai  zai samu biyan buƙatarsa to fa komai zata yi masa baya gani,kan kuce me Sahabee ya tashi daga d'an gaye ya koma Wani iri da shi kamar d'an aikin gidan dama can shi ba me kaurin jiki bane se ya sake jemewa ya rame sai uban tsawo kamar igiya,gaba ɗaya ya zama wani abin tausayi da shi. Tsakanin uwa da ɗa sai Allah,ganin halin da ya shiga ne ya sanya ciwon Iya yake yawan tashi, Sahabee bai ma san tana yi ba balle ya sai mata magani, watarana har kasa tashi take yi ta fita koda yin alwala ne. Idan abun ya yawaita ne yaga be ga gilmawar ta ba na kwanaki sai ya ɗaga labule daga bakin ƙofa zai yi mata sannu sannan ya kama gaban shi ya shiga sabgogin shi kamar bai ga halin da take ciki ba,matar shi kuwa sai suyi kwanaki bata leqa ta ba balle ta duba ya jikin ta yake, lokacin da ta ga damar gaishe ta kuwa to daga bakin qofa take d'age dan buhun labulen itama ta ce mata sannu ta yi gaba abunta,a cewar ta ai uwar miji ba uwar ta bace. Babban abinda yafi baƙantawa Iya rai bai wuce yanda matar nan zata kalli idanun Iya ta dinga kiran ta da ƙazama wadda bata share ɗakin ta balle tayi wanka taji dad'in jikin ta,Iya ta yi nadamar abubuwan data dinga yiwa Eamaan a baya, gefe ɗaya kuma ta yi nadamar yanda ta dinga yiwa Alhaji Abdullah da yake tsananin tausaya mata da taimaka mata tare da yi mata ladabi da BIYAYYAH,a kullum ba shi da burin da ya wuce na ya ganta cikin walwala da farin ciki, duk dan kar ran ta ya baci da girman shi haka zata sa shi a gaba da fad'a kamar yaro qarami, ga masu aiki wajen uku ya zuba mata ita kaɗai a sashen ta dan su kula da dikkan buƙatun ta, amma dik da haka ta takurawa matar shi mai tsananin BIYAYYAH dik da cewa ba auren soyayya suka yi ba, idan tace masu abu fari ne komai baqin shi basa yi mata musa haka zasu yarda da abinda tace ɗin.kuka shine ya dawo abincin Iya Kuma ya zamto abin Shanta. Idan ana girki a gidan haka hayaƙin zai shiga ta ɗan ƙaramin windown nata tai ta tari tana neman iskar shaƙa mai kyau, dik randa tayi gigin fita dan ta shaƙi iska amaryar sahabee sai ta nuna mata bariki ta hau taɓa shi a gaban idanun ta shi kuwa yana biye mata,tsananin da Iya ke ciki yayi tsanani har ya kai ga yanzu bata gani sosai saboda hawan jini da yayi mata yawa da kuma hayaƙi dake addabar ta kullum. Muryar Amaryar Sahabee ke tashi kamar wata gardi a cikin gidan cikin ɓacin rai take magana. " Yanzu honey kana nufin bashin da na ciwo saboda ankon bikin qawata ba za ka samu biya ba? kai fa ka yi min alqawari kafin auren mu ba zan tab'a neman abu na rasa ba kace min babu ni babu wahala aikin gida da komai ba nawa bane naka ne, sannan ka jaddada min kar na damu da maganar kud'i ko nawa ne baka da matsala akan su zaka dinga bani,ni ba ma abinda ya fi min ciwo ma sama da alqawarin zama a qaton gida bayan d'aura mana aure sai na ga an kawo ni nan, hakuri kawai na yi na rufa Maka asiri wajen dangi na da qawaye na muke zaune a wannan akurkin, domin rufin asirin ka shine nawa,se yanzu na gane duk Kalaman ka a gare ni qanzon kurege ne,tin yanzu gashi ka fara karya alƙawarin ka na bani kud'in anko a duk sanda na buƙata,to ka buɗe kunnen ka da kyau kaji ni,wannan ankon da na ciyo bashi se ka biya ba zaka sa na ji kunya ba,dubun nan talatin da bakwai cassss se ka kawo su,sannan ga kudin ɗinki dubu biyar da aka yo min,dole ne ka biya kud'in takalmi da jaka da mayafi da na sa qanina ya amso bashi a shagon abokin shi, ba zaka sa na ji kunyar qanne na ba a dinga raina ni ana zagin miji na ana kiran ka talaka,sarqa da dan kunne da abun hannu da zan yi amfani dasu Kuma ka siya daga baya kafin ranar bikin tazo. Kai dama zaka godewa Allah na samu bashin?  Yanzu a wannan zamanin bashin ma ai se ka yi da gaske zaka same shi, ni yanzu na gama gane inda ka dosa dik ƙarya ka zuba min lokacin neman aure na,gashi yanzu ka gaza a kula da ni, dama ko a gadon ma hakuri nake da Kai yanzu," fashe wa ta yi da kuka har da shessheƙa kamar shine ya gama yi mata rashin mutunci ba ita ba, duk maganganun da take yi sun shiga kunnen Iya sun zauna a zuciyar ta daram, kad'a kai Iya ta yi alamar muje zuwa yanzu aka fara tinda na hana ka auren ta ka kafe, to ga irin ta nan ai. Sahabee kuwa duqawa ya yi a gaban ta ya na bata hakuri da tabbatar mata ze biya kud'in ko nawa ne, murmushi ta fara yi masa ta na wani kakkama shi, Sahabee na ganin ta sakko ya tallabe kan ta zai yi mata kiss, cikin nuna qyanqyamin shi ta janye jikin ta tace, "Haba my baby ki yi hakuri mana na ce maki inna samu zan baki, kinga a wajen aikin mu ni ke ajiyar kud'i, inna je zan ranta na baki, a albashina sun dinga d'auka a hankali har na gama biya, ba dai dubu tamanin bane dika kud'in? kar ki damu zan baki ni dai ki min murmushin ki me kyau na gani ko naji dad'i a raina" Murmushin ta masa ta rungume shi tana boye fuskar ta a bayan shi tare da murgud'a masa baki da harar shi, shafata ya soma yi cikin b'ata rai ta ture shi tace, "A'a gaskiya ciki na babu komai me zan iya yi maka yanzu? ni yunwa na ke ji kamar banci komai ba nake jina, gaskiya ka samo mana yar kaza yau mu d'an ci a gidan nan mu maida mugun yawu, kaima kasan kullum sai na ci kaji bama kaza ba sanda Ina gidan mu,amma ka duba ka gani sai na yi sati ko kwana hudu ban ganta ba anan gidan." Hawayen munafurci ta share ta fyace majina ita a dole zaman haƙuri take yi a gidan Sahabee, jikin shi na rawa ya fita ya amso bashin qatuwar kaza guda d'aya,wanda da kyar ma aka bashi bashin kazar saboda dama can akwai tsohon bashin kusan dubu bakwai da Mai kajin ke bin shi, yau d'in ma dan ya gilla qaryar a gobe zai kawo masa har na baya ne sannan ya yarda ya bashi, Sahabee ya qudurta a ran shi gobe zai je wajen aikin nasu ya d'akko kud'in ba Wanda ya sani tinda a office ɗin shi suke. Koda ya dawo sai ya baje mata kazar a gaban ta yana murmushi, zama tayi kamar mayya tana washe baki, a tare suka hau cin kaza tana zuba surutu kamar tsohuwar redio, yawun Iya gaba ɗaya ya gama tsinkewa saboda tana jin dik abinda ke faruwa,hawaye take zubarwa tsabar kwad'ayin da ya addabe ta, tinanin gidan Alhaji Abdullah kuwa ya zame mata ibada dan kuwa kullum sai tayi,yanzu da acan ne ko kaji nawa take so se ta sa a gasa mata ta ci,a rayuwar nan dama dik wanda yasaba cin dad'i tofa shi yafi begen dad'in, haka suka gama tass suka sha ruwa basu sammata koda fuffuke ba, da kyar Sahabee ya samu had'in kan ta ya sauke buƙatar shi dik da faranta mata da yake ƙoƙarin yi a kullum. Washe gari da sassafe ya shirya bayan ya gama yi mata aikace-aikacen gidan da ya saba,sai ya leqa Iya ya mata sallama, bai ji ta amsa ba ya wuce dan bai damu daya ga lafiya take ba ko akasin hakan, yana fitowa ya sa kai ya tafi. Lokacin da ya isa office bai tarar da mutane ba sosai sai ya zauna  ya gaggaisa da mutanen da ya tarar,sannan ya tashi zai shiga office ɗin shi d'auke da jakar shi a hannu,sauran ma'aikatan kuwa yana tashi suka hau qulmar shi suna cewa tin da ya yi aure ya rame kuma yake makara,ko kuma ma ya yi fashi gaba d'aya yaƙi zuwa,yana ji bai kula su ba ya wuce, sai da qafa ta d'auke lokacin cin abincin rana ya yi ya buɗe wajen da ake aje kud'in ya kwasa,da har ya dauki dubu d'ari ya rufe, daga baya kawai yace bari ya ɗauki dari biyu zasu masa amfani a gaba, sun dinga zara a albashin sa a hankali har ya gama biya, yana gama d'iba ya rufe ko ina ya tafi gida hankalin shi kwance, yana zuwa gida ya zaro dika kud'in ya zube a gaban ta tin kafin ya cire kaya ya huta, amarya kuwa na ganin wannan uban kud'in sai rawar kai ta tashi, tana ta yi maaa sannu da zuwa harda tashi ta ɗora girki tana faɗin ya gaji ya zauna ya huta zata yi musu abincin. Bayan sun ci abinci sun gama ne ya shiga wanka ya fito yayi alwala saboda gabatowar sallar magariba, koda ya je masallaci yayi sallah ya dawo da isha'i Amarya ta maqale masa,ranar Sahabee ya samu kulawa ta musamman a wajen matar shi har bai san sanda dare yayi nisa ba,bata barshi ba har sai da taga bashi da sauran qarfi a jikin shi, tana ganin ya yi bacci ta ɗauki wayar ta ta kira qawar ta tace mata, "ke shegiyar ga fa kayan ki nan zan dawo maki da su, ni kam na samu kudin da na dan samu zan qara gaba, na gaji da qaddararren auren nan, dama ace yana d'an samu ne  kuma yana da qarfi sosai a gado to da na hakura, amma ba komai daga sama har qasa komai a bushe me zai zaunar da ni? Ina nan tafe yanzu ki saurare ni nan da awa ɗaya, dan haka ki fito bakin hanya na baki kayan ki na ƙara gaba." Dariya kawai waccan take kwasa tana ta hura mata kai, tana ziga ta,cikin shewa tace, "To muguwar sai kinzo, ai ita bariki haka take dama, wanda bai zo bama jiran shi take gashi ya faɗa hannun ki kin kwashi rabon ki zaki arce,ina nan ina jiran ki sai kin zo." Sallama suka yi ta aje yar rakani kashin ta ta fara haɗa kayan ta a hankali,sahabee kuwa na nan washarere jiki a bude dik ya gaji, ta kalle shi ta tofar da yawu a gefe tace, " Allah ya kiyaye na ci gaba da zama da wannan lagwanin, ba kuɗi ba biyan buƙata, ga mazaje can a waje na jira na a biya min buƙata kuma a bani kuɗi  amma ina nan a rakub'e kamar ƴar karo? dama ai dan na zaci har lokacin yana tare da wannan yayan nashi ne mai kuɗin da yake kashe min a baya,wanda shima na ji ana ta rad'e rad'in d'an hannu ne,(Matsalar zina kenan yan uwa, Alhaji dai ya mutu amma ga wata tana tino da labarin shi kuma tana maimaita ai dan hannu ne, wanda ana so in za a tina ka a tina ka da aikin alkairi, Allah ya kyauta ya samu aikata dai-dai, ya yafe mana a inda muka yi kuskure, Allah ya shiryar damu da zuriar mu) tana gama mitar ta ta kwashe kud'in ta d'ure a jaka ta sa kai ta bar gidan, d'akin Iya ta leqa taga yanda ta barta tin safe tana nan kwance a haka har a wannan lokacin, sakin labulen ta yi ta kyab'e baki tai gaba tana mitar sai shegen son jiki kawai tsohuwar ta sani da sa ido, tana fita gidan qawar ta ta nufa ta miqa mata kayan da dubu biyu kamar yanda suka yi alqawari tai gaba. Sahabee kuwa sai da ya kai awa d'aya bayan fitar ta ya na bacci kafin ya farka, kallon d'akin ya yi yaga kamar anyi yasa, shiru ya yi ya ɗauki gajeran wandon shi irin na ƴan ball ya saka,neman ta ya fara yi amma babu ita babu dalilin ta, ɗan murmusawa ya yi sannan ya ce, "Wataqila tana can tana gasa kan ta, dan yau na more ta sosai ba kad'an ba , yaushe rabon da ta barni nayi irin na yau? Muguwar ai haka zan nayi mata kuwa daga yau." Yana nan har aka kira la'asar yaji shiru bata dawo d'aki ba,sai ya tashi ya leqa band'aki dan yaga me take yi haka, yana shiga yaga wayam, hankalin shi ne ya fara tashi cikin sauri ya koma d'akin ya hau bincike, nan fa yaga babu kud'i babu dalilin su Kuma ba kayan ta na sawa,sai wata dubu buyu da ya gani da

Chapter 17 of 20