Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bashi lafiya ya dawo cikin iyalan shi lafiya daga qarshe ya godewa matan nashi akan qoqarin su a gare shi da dikkan d'awainiya da hidimar da suka yi tayi da shi a lokacin da yana kwance a asibiti,bayan nan ne ya sanar da su zai koma Abuja ana da buqatar shi a wajen hidindimun siyasar su. Kuɗi ya d'akko ya miqa wa kowa nashi kamar yanda ya saba, sannan ya jawa Sahabee kunne akan dad'ewar dare da yake yi. Niko nace wai kura ce za tace da kare maye,hannun Hajiya Babba ya kalla cikin mamaki ya ce, " Hajiya me ya samu hannun ki na ga kamar ya kumbura?" A ɗan razane ta kalli Eamaan da ta kauda kan ta daga kallon ta ta yi kamar ma ba ta ji tambayar da akai wa Hajiya Babba ba, nan da nan zuciyar dake shawartar Hajiyan akan ta faɗi me suka yi ta taso mata,cikin sauri Eamaan tace, " Alhaji ka gafarce ni d'azu na je gaishe  ta ne na buɗe qofar shiga tana wajen ban sani ba na buge ta," "Subhanallahi Allah ya kiyaye gaba, ke kuma kina k'wank'wasa qofa kan ki shiga waje gudun faruwar irin  hakan," Amsawa ta yi da zata kiyaye gaba sannan ta sake kauda kan ta daga barin kallon kowa a wajen, Sahabee da Hajiya kuwa zuciyoyin su babu dad'i dan hakan na qara sanya su a dogon nazari da jin tsoron me zai je yazo game da shirun Eamaan ɗin,muryar Alhaji suka ji yana faɗin, " Sahabee ka kai Hajiya Babba asibiti a duban hannun nata," " To Yayah," yace yana wani sunne kai qasa kamar na Allah. Daga haka sai Alhaji ya miqe ya fice zuwa ɓangaren Eamaan yana fita ba jimawa itama ta bi bayan shi, idanu suka zuba mata gaba ɗayan su har Iya, tana fita Hajiya qarama tace, "Ni fa ina ganin wani al'amari a wajen yarinyar nan, ban sani ba ko kun kula da hakan kuma?" Hankalin Sahabee da Hajiya Babba ne ya qara kid'ima suka faɗa tashin hankalin Allah yasa ba gano abinda suka aikata Hajiya Qarama tayi ba,cikin zumud'i Hajiya Babba tace, "Me kike nufi da maganar ki?" Iya ce ta karɓe maganar da cewa, "Tana nufin Eamaanii na ɗauke da juna biyu na haihuwa," A zabure Hajiya Babba da Sahabee suka had'a baki wajen faɗin, "Cikiii kuma?" Hajiya Babba ce ta dafe qirji da hannun ta me lafiya ta kalli Iya tace, " Iya ciki fa kika ce, yaushe ma tazo gidan har da zata yi ciki ni ina nan ina fama shekara da shekaru ban taɓa koda bari bane?to gwanda ma Hajiya Qarama ta ajiye waɗannan gajiyayyun yaran marasa jin magana, ni yanzu ina na kama babu d'a babu jika?" "Ya ko me zaki yi banda ki zubawa sarautar Allah idanu a yi abinda kike gudu babu ke? Ke kam yanzu in ba wani ikon Allahn ba ba wata haihuwa da zaki yi nan gaba tsufa ya riga da ya riske ki, dan haka kawai ki barmu masu sauran jini a jika mu yi ta haihuwar," Nan fa fad'a ya kaure a tsakanin su dama sun dad'e ba su yi ba,Iya data gaji da jin su ta daka masu tsawa, ta ce "To kaji kun fara ko? kai tashi ka d'ebo hatsin nan na watsa masu, ku tashi ku ban waje shashashan banza kawai,kuda bazaku taɓa zama ku samawa kan ku mafita akan komai ba sai faɗa da hauragiyar banza," Miqewa suka yi suka tafi sashen su kowa na harar 'yar uwar ta, Sahabee ne yabi Hajiya Babba ya ce mata zasu asibiti anjima ta shirya daga qarshe sai ya kashe mata ido ɗaya, d'aga masa kai kawai tayi sannan suka rabu, cike da murna ya shiga d'akin shi ya shirya don zuwan nasu asibiti, tin daga murnar da Sahabee yake yi mutum zai gane duk wanda ya Saba da bariki tana yi masa wuyar bari, har ya manta tashin hankalin da suka shiga lokacin da Eamaan ta kama su dumu-dumu suna aikata masha'a. Eamaan kuwa bayan sun koma ɓangaren ta da Alhaji ne ta samu akwatin da take haɗawa Alhajin kaya in zai yi tafiya Abuja, ta saka kayan duk da zai buqata wanda suka had'a da; manyan kaya da qanana,sai boxers da vest, man shafawa,brush, sai ta samu wani qaramin qur'ani Izu biyu ta saka a aljihun jakar,sannan ta saka turatuka, hula da dai duk abinda zai buqata, wata yar takarda na ga ta yaga guda biyu ta faki idon shi ta zauna ta yi rubutu a cikin su sannan ta saka ɗaya a tsakiyar wata babbar rigar shi, sai ta sa ka wata a wandon qananan kayan shi,bayan ta gama ne ta zauna ta kamo hanun shi ta zaunar da shi a bakin gadon su da ya sha gyara yana fitar da qamshi na musamman. Domin kuwa yanda take turara kayan ta da turaren wuta a kabbasa haka take turara zanin gadon ta da towels ɗin su na wanka shi yasa a koda yaushe qamshin su na musamman ne,kallon fuskar shi ta yi shima ya kalle ta cikin murmushi yace, " Eamaanii na wai meye sirrin ne kullum sai wani irin kyau kike qarawa,shin wai ma ni yaushe rabon ki da ki ga al'adar ki ne?" Gaban ta ne yayi wata muguwar fad'uwa saboda jin tambayar da yayi mata, nan take ta tuna cewar rabon ta da period yanzu ta kai wata uku, tana son ta faɗa masa amma sai ta fasa saboda halin da yake ciki, hankalin ta be taɓa kawo mata maganar ciki ba duba da tana yawan jin ciwon mara sai kawai ta sa a ranta maybe ta ɗan samu tsaiko ne amma zai zo, haka wata zai wuce ciwon marar ya lafa kuma jinin be zo ba, a sanyaye ta bashi amsa da, " Watana na uku kenan," Jan ta yayi jikin shi sannan ya ɗora ta a kan cinyar shi yana shinshinar wuyan ta da alamar murna ya zira hannun shi a rigar ta yana shafa cikin ta ba tare da ya ce komai ba, yana so ya more wannan yanayin da suke ciki me daɗi kafin Allah ya dawo dashi daga tafiyar da zai yi ya kaita a gwada ta a ga me yake faruwa da ita, a hankali Eamaan tace masa, " Sweet ! ina son nayi maka wata magana amma bana son ka ɗauki hakan ta fuskar na raina ka ko kuma ni na yi qanqanta na yi maka irin wannan maganar, dan Allah ka yi hakuri in a maganar da zan yi maka ka samu wata kalma da zata b'ata ran ka, sannan ina son ka dauka shawara ce ke fitowa daga bakin masoyiya zuwa ga masoyin ta," Gyara mata zama ya yi a cinyar shi yana kallon ta da wani irin kallon so da qauna, kenan tana nufin tana son shi a yanzu kenan tinda ta kira kanta da masoyiyar shi? Cikin farin cikin da maganar ta ta sanya shi yace, "Ina jin ki Eamaanii na," "Dan Allah don son Annabin Allah ka taimake mu ka daina aikata neman matan waje, ka ji tsoron Allah domin shi yana ganin ka idan kai baka ganin shi, sannan ka sani Allah ne ya baka rai da lafiya dan ka bauta masa, baka sani ba kana cikin aikata sab'on Allah se Allah ya zare rayuwar ka kaje gare shi kana mai aikata sab'on da ya hana, kaga ka mutu a cikin yan wuta kenan,za kuma a tada kai ne a cikin 'yan wuta, Sweet Haerbeebee ka ji tausayin mu a matsayin mu na matan ka,ka tausaya ma Iya a matsayin ta na mahaifiyar ka,sannan ka tausayawa yaran ka domin kai Uba ne na yara mata kar abinda kake yi da matan wasu ko yaran wasu a yi da naka, nasan ba zaka so haka ta faru akan zuri'ar ka ba to dan Allah ka dena taɓa zuri'ar kowa kaima,ka sani ita zina bashi ce dole idan kayi sai ka biya, ko da ranka ko babu ranka wani zai kusanci zuri'ar ka ta inda baka zata ba,dan haka Ina so ka tuba ga Allah sai Allah ya yafe maka ya kare zuri'ar mu, a qarshe ina yi maka fata da addu'ar Allah ya shiryar min da kai masoyi na Allah kuma ya bada sa'a ya dawo mana da Kai lafiya, wannan shi ne abinda nake so in fad'a maka dama idan na b'ata maka dan Allah ka yafe wa Eamaaniin ka kaji?" Gaba ɗaya kalaman yarinyar sun yi mugun kashe masa jiki, ga hawayen da take sharewa masu zafi a lokacin da take yi masa maganar wanda alamu ne na yanda zuciyar ta ke quna akan abinda yake aikatawa,wata kunya da nauyin ta ne suka dirar masa a lokaci d'aya, ga wani irin baqin ciki daya turniqe shi jin za a yiwa yaran shi abinda yayi wa na wasu saboda keta gonar da ba tashi ba da yake yi. Kalmar godiya kawai ya iya furtawa sannan ya yi wa goshin ta kiss ya share mata hawaye ya tashi tsaye tare da daukar jakar shi da akwatin shi ya fita, hijab ta saka dogo ta bi bayan shi ta amshi qaramar jakar tabishi zuwa waje,gaba ɗaya ji yake ba shi da laka a jikin shi, shagwab'a ta fara yi masa tana buga qafa a qasa ta dakata da bin shi da take yi, juyowa ya yi ya kalle ta cike da sha'awar yanda take masa shagwab'ar yace, " Eamaaniii na ya aka yi ne,ko rikicin ne ya motsa kuma a lokacin da kika san tafiya zan yi?" Fad'awa ta yi gefen qirjin shi ta fara murza jikin ta a nashi tana ci gaba da shagwab'ar ta son ranta,cikin kuka kamar na qananan yara take nuna masa yanda ta fara jin kewar shi tin yanzu,Eamaan kuwa a cikin ranta har mamaki take baiwa kanta idan ta aikata wani abun, a hankali ta sake furta, "Kuma ai kai ne naga kana ta b'ata rai kamar maganata ta ɗazu ta b'ata ranka, kuma gashi ka na fushi da ni za ka yi tafiya salon ka manta da ni idan ka tafi kace ka huta da mitar da nake yi maka kullum shi yasa baka amsa min magana ta ba d'azun," Dariya ta bashi sosai har yaji yana son kasancewa da ita a wannan yanayin da take zuba masa shagwab'ar dake matuqar burge shi, tinani ya yi akan maganganun ta sai ya quduri ko sau d'aya ne zai je ya dawo ba tare da ya taɓa diyar kowa ba, dan haka dole ya sauke wannan buqatar tashi da ta taso masa babu shiri. Janta ya yi suka koma sashen ta cikin yanayi na tsantsar buqatuwa Alhaji ya fara aika mata da zazzafan saqon da take jin zuciyar ta na cunkushewa saboda bata jin sha'awar hakan aranta, amma dole ta hakura ta taya shi sauke masa wannan buqatar,aiko nan da nan tai wurgi da hijab ɗin dake jikin ta ta fara aika masa da nata kalar saqon da take fatan ya mantar da shi aikata zina da dikkan abinda ya danganceta, Eamaan ta baiwa Alhajin mamaki sosai ba kaɗan ba, domin kuwa sai da ya yi mamakin dama Eamaan ɗin ta kware a harkar nan take qin baje basirar ta a baya su mori juna sai yau? Da ba a budurwa ya same ta ba tabbas da sai yace dama can ta san ya ake yin komai tin kafin aure, Eamaan kuwa bata bar Alhaji ba har sai da ta tabbatar da ta cire wa Alhaji hankalin shi ta aje a gefe, ta sa ya ji tinda yake bariki bai taɓa haɗuwa da mace mai iya salon ɗauke hankalin namiji a aza room ba irin ta, da kyar ya hakura ya barta saboda kar yayi dare,maganar bin jirgi ma tini ta tashi dan kuwa yasan yayi missing flight ɗin shi,dan haka dole mota zai bi, wanka suka shiga tare wanda a wajen wankan ma saida suka dad'a shan wata sabuwar soyayyar sannan ya fito ya sauya kaya, itama ta saka wasu qananan kayan sannan suka fito a tare suna sakar wa Junan su murmushin da su kaɗai suka san ma'anar shi,fuskar ta ta yi kyau a cikin dark green din hijabin da ta sanya,bata barshi ba sai da ta raka shi har jikin mota,shiga ta yi ta zauna a gefen shi kafin driver ya shiga, a jikin shi ta zauna ta hau sumbatar shi, kasancewar motar nada baqin gilashi ya sanya babu mai hango su ta waje,bata barshi ba sai da ta tabbatar ta dasa masa tunanin ta wanda zai ɗauke shi tsahon lokaci yana yi har yaje ya dawo daga tafiyar da zai yi,a hankali ta sauka daga jikin shi tana marairacewa ta furta, " I am going to miss u my Sweet baby," wayyoo Alhaji ji ya yi kamar zai suma saboda farin ciki da jin daɗi,yau kuma wai shine baby... Wohohooo lallai babu abinda yafi rayuwar aure daɗi da sanya farin ciki,cikin yaqe baki da nuna tsantsar farin cikin da Eamaan ta sanya shi yace, "Kar ki damu My dear inshaa Allahu da na gama abubuwan da zanyi zan dawo, ga waya zamuna yi kullum ke har video call ma sai muyi abun mu tinda yanzu Eamaanii na ta rage jin kunya ta," D'aga kai ta yi ta sake sumbatar shi a kuncin shi sannan ta fita tana d'aga masa hannu har suka bar gidan shi da driver, komawa ta yi bangaren ta kan ta shiga tana hango kishiyoyin ta na kallon ta ta window,ita kuwa ko nuna alamar ta gansu ma batayi ba ta shige,gaba d'aya yanzu haushi suke bata dikan su, ayi mata basu da aikin yi sai sa idon tsiya, su ɗin ma haushin ta suke ji dan sun kula ta gama janye hankalin Alhaji akan ta ita ɗaya. ************************* Tinda Alhaji ya tafi baida wani aikin da ya wuce na tinanin Eamaan, matan banzan da suka saba huld'a da shi a baya dik ya qi kula su tinda ya isa dan kuwa be kira kowa ba a cikin su kuma sun ji labarin shigar shi Abujan, gaba ɗaya haushi suke ji saboda ya qi sauraron kowa a cikin su,a yanzu ya saba da soyayyar da Eamaan ke yi masa da zaqin ta, ya saba da irin salon kulawar da Eamaaniin shi take bashi sosai, ga shi wannan karon kafin su rabu ta bashi soyayya mai tsayawa a rai, dan haka baya jin akwai wadda zata iya bashi wannan abinda ya samu a wajen Eamaan ɗin, ko da kuwa a cikin matan shi ne kuwa. Yau ya gama aikin da zai yi da wuri ya dawo gidan shi dake nan Abujan gaba ɗaya buqatuwar kasancewa da matan shi ta dame shi, ya rasa yanda zaiyi da ran shi a qoqarin shi na kare kan shi daga afkawa zina. Daga qarshe dai abun ya gagare shi sai ya yanke shawarar leqawa hotel ɗin da ya saba shanawar shi, dan yau d'aya dai ai Eamaan ba ganewa zata yi ba, sannan kwanan shi nawa da zuwa bai kwan da mace ba ai ya yi qoqari sosai ma. Dan haka wanka kawai yayi ya tsane jikin shi da towel ya shafa mayukan shi ya feshe jikin shi da tirare, sannan ya d'akko wata rigar shi daga cikin qananan kayan shi dan ya saka,kawai sai yaga takarda ta fad'o a cikin wandon kayan, buɗe wa ya yi ya ga an rubuta *MY SWEET BABY* murmushi ya yi ya zauna ya fara ware takardar gaba ɗayan ta dan ya karanta abinda ta qunsa.............[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼    BIYAYYAH  💅🏼   WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 11: *My one and only husband, ina roqon ka da kuma sake yi maka tini akan kaji tsoron Allah,ka sani indan kai baka ganin shi to shi yana ganin ka, ka kare mana mutuncin mu ta hanyar adana kan ka har sai ka dawo gare mu, zamu tarbe ka da tarbar da baka tab'a zato ba mijin mu, muna son ka,Allah ya dawo mana da kai lafiya..In kewa ta dame ka ka Kira d'aya daga cikin mu video call ko voice call za mu yi qoqarin taimaka Maka ta kowacce hanya da ta dace*          *Eamaaniin Alhaji shi kaɗai* Nan take Alhaji ji ya ji gaba d'aya an zare masa lakar jikin shi,tini ya nemi sha'awar shi ya rasa, miqewa ya yi ya je ya yo alwala ya yi ta nafilfulu,kamar yanda ya ji Eamaan tana yawan faɗa yin nafila yana kawar da mugun tunani da damuwa. Haqiqa Eamaan tayi gaskiya a maganganun ta domin kuwa Alhaji be gushe yana nafila ba face sai da ya ji wani qarfin imani na shigar shi, tsoron Allah da kunyar Allah ta kama shi, a nan ya zauna yana ta kuka yana neman gafarar Allah akan abubuwan da yayi a baya,sannan ya roqi Allah daya kare shi da zuri'ar shi daga zina,a haka ya fara gyangyadi sai kawai ya miqe ya yi shirin bacci, da asubar fari ya farka ya yi brush ya yi alwala ya yi sallah, tinani ne yazo masa na komawa gida ko kuma kiran Eamaan ta sama masa natsuwar da ta alqawarta masa, domin kuwa tinda ya tashi da safe yake jin shi wani iri. Nasihar Eamaan ce ta yin azumin nafila ta sake fad'o masa a rai a karo na babu adadi,tinda ya iso garin Abuja a komai zai yi sai ya tuna da ita da nasihar da take yi masa,kawai sai ya d'aura niyyar zarcewa da azumi. 'Yana da kyau wanda ba ya iya riqe sha'awarsa ya dinga yin azumin nafila akai akai,kuma ya gujewa dikkan abinda zai tada masa da sha'awa idan yayi haka zai kauce fad'awa sharrin zina' Yana gama tinawa da kalaman yarinyar sai ya saki murmushi mai kyau ya ce, " Da dikkan alamu an sanar da yarinyar nan dalilin aure na da ita shiyasa take yi min wa'azi cikin hikima da ladabi tare da girmamawa dik da ban cancanta da hakan ba,Yah Allah ka yi mata albarka ka bani iKon sauya halaye na domin ka ko iyali na za su samu natsuwa da kwanciyar hankali da ni," Tabbas yana tsananin jin kunyar yarinyar da ya San zai iya haifar wanda suka girme mata ma, akwai wani lokaci da Eamaan ta taɓa ce masa, 'Haqiqa Allah shine mafi cancanta kowanne bawa ya ji kunya ya bar aikata sab'on Allah ba mutane ba, domin kuwa Allah shine yake da wuta kuma yake da aljannah, shi yayi hani da zina da shirka,ya bada umarni a tsaida sallah a bi iyaye, kaga kuwa shi ne zai sanya wanda ya kyautata a aljannah ya jefa wanda ya munana a wuta, dan haka kar ka bar aikata zunubi domin mutane ka bar aikata zunubi domin Allah kawai sai ka rabauta duniya da lahira,' Hawaye ne suke gangara a kuncin Alhaji na tsananin tsoron Allah da yake jin yana shigar shi a lokaci ɗaya, yana cikin wannan halin wayar shi ta yi qara, yana dubawa sai yaga sunan *My Babee* na yawo a saman screen ɗin wayar,murmushi ya yi cikin hawayen da ke zuba a idanun shi ya d'aga wayar,kafin yayi sallama yaji zazzaqar muryar ta na faɗin, "I miss u so so very much my love, na kasa zaune na kasa tsaye saboda tsananin kewar mijina," Dad'i ne ya kama Alhaji tinda ya zo Abuja kusan a rana sai ta kira shi sama da sau biyar, a baya kuwa tinda yake a cikin matan shi babu wadda ta damu da ta kira ta ji ma ya ya isa lafiya balle a kai ga wai ta kira shi haka nan dan jin ya yake, sai dai shi ya kira su yaji ya suke,soyayya suka sha ta waya sosai, da ya ji muryar ta na kashe masa jiki kuwa sai ya ce mata yana ɗan gabatar da wasu ayyuka ne, kamar irin bayan magrib dinnan zai kirata suyi waya, addu'a ta yi masa  tare da fatan samun nasara akan ayyukan shi suka yi sallama suka kashe wayar. ************************** Hajiya Babba ce zaune tana shirya kayan ta na magungunan mata tana aje su inda ta saba, kawai ta ji an bude qofar shigowa bangaren ta, miqewa ta yi dan zuwa ta  ga waye,dik da cewa tinanin ta ya gama bata Sahabee ne ya zo, domin kuwa ta kwana biyu rabon ta da shi,tin sanda Alhaji yace suje asibiti a duba hannun ta bayan sun dawo daga asibitin sai suka je hotel suka yini suna abu ɗaya, da suka dawo ya ajiye ta ya sake fita to tin daga nan bata sake sanya shi a idanun ta ba, a 'yan kwanakin nan duk ta damu tana kuma kewar shi sosai, cikin k'warin guiwa ta buɗe baki tace, "Saha......," Maganar ta ce ta maqale saboda ganin Hajiya Qarama a sashen nata, "Ke kuma me ya faru zaki shigo min gida babu sallama? dan dai ke ba zuwa kike yi ba sai da kwakkwaran dalili," "Tabbas haka yake bana zuwa sai da ƙwaƙƙwaran dalili,to yanzun ma da kika ganni wani abu ne ya kawo ni mai mahimmanci, zuwa na yi ki tashi muje mu yi wa yarinyar can magana akan karuwancin da ta ɓullo mana da shi a gidan nan har ta janye hankalin Alhaji daga kammu," Yawu hajiya babba ta had'iya mai d'aci domin kuwa dik masifa da tijarar ta bata da qwarin guiwar tinkarar Eamaan da maganar komai,cikin jinjina kai Hajiya Babba tace wa Hajiya qarama, "Lallai baki san wace ce Eamaan ba ashe ke har yanzu,to bari kiji ba dani za ai wannan abun ba, amma in kin dage nima abun na ci min tuwo a kwarya na dai kasa magana ne kawai sai na raka ki ina gefe ki yi mata tatas ɗin mu dawo," " Eh na yarda muje ki rakanin ni zan yi mata Magana,haka kawai muna zaune yarinya qarama tazo ta janye mana hankalin miji? Ke ni fa na kula dake da Sahabee wani tsoron ta ma kuke ji, Iya ma kwana biyu ta yi sanyi akan yanda take yi mata masifa a da, to ni ba na tsoron ta, dama ina d'aga mata qafa ne saboda tana son yara na, amma yanzu ba wannan maganar," Tashi suka yi suka nufi hanyar sashen Eamaan,sun same ta ta na zaune ta ɗora qafafun ta a kan center table tana kad'a su a hankali tare da miqar da su ta kuma komawa ta lanqwashe su cikin salo,zaune take daga ita sai guntun wando pink da rigar wandon,wadda iyakar qirjin ta ta rufe sai dogon hannu da hula da take da shi,cikin ta da bayan ta duk a waje suke gwanin burge mai kallon ta,gashin ta kuwa ta d'aure shi wasu sun fito sun zuba a gefen fuskar ta suna reto gwanin sha'awa,dik wannan karairayar da take yi da kashe muryar ashe waya take yi da Alhaji, dan kuwa yanzu ko bata kira shi ba shi zai kira ta su sha soyayyar su. Wata iriyar mutuwar tsaye suka yi dan jin maganganun da take yi wa Alhajin na qarshe, shagala suka yi da kallon shigar da tayi da kuma kyakkyawar surar ta da yanda ta iya sarrafa jikin ta naturally ba wani iyayi da gwalangwaso, ashe haka Alhaji yake shan kallo a jikin wannan halittar mai tsananin kyawun diri? Lallai kishi ko faɗa da Eamaan abu ne mai matuqar wahala a wajen su dan kuwa sun kwana biyu ita kuwa a ganiyar quruciyar ta take,Eamaan kuwa tana ganin su sai ta kashe wayar ta duqa kaɗan ta na gaishe su,Hajiya Babba kam gefe ta yi dan har yanzu tana shakkar Eamaan,ba ma zata iya buɗe baki ta amsa gaisuwar da take yi mata ba balle tayi mata faɗa,Hajiya Qarama ce ta kalli Eamaan a sheqe cikin kishi da b'acin rai tace, " ke karuwar gida hawainiyar ki ta kiyayi ramar mu,kina daga cikin gida kina zabga karuwanci kina son karb'ar mana miji daga zuwan ki, yanzu gaba ɗaya hankalin shi ya tattara ya koma wajen ki, to bari kiji da kyau, ahir ɗin ki da shiga gona ta dan kuwa ni ɗin nan da kika ganni bani da kyau bani da mutunci, ki tambaya ki ji ba ragowa tsakani na da duk wadda zatai qoqarin rabani da Alhaji," Murmushi Eamaan take ta zabgawa, na ganin tsantsar haukan su da wautar su,cikin murmushin ta miqe daga durquson da tayi dan gaida su tace, " Hajiya Qarama kenan amma gaskiya na yi matiqar mamakin zuwan ku nan dan yi min gargad'i akan wai ina

Chapter 7 of 20