Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
amince" Ta fada tana rufe fuska, miqewa yayi dai-dai Hafsat ta fito dauke da plate da kayan karyawa akai, " A'aa ina kuma zaka je baka karya ba," "Inaaa ai ni yanzu na ma fasa biyawa asibitin waya zan kawai su duban mara lafiyar nan, ba zan zame ko Ina ba Daga nan sai Kano, an ban damar zuwa neman aure ai ban ga ta zama ba," Eamaan ce ta miqe ta je kusa da shi ta dan shagwab'e fuska ta ce, "Yanzu tafiya za ka yi bamu ci abinci ba, da ni fa zamu karya ko baka son cin abinci da ni?" Ta qarasa maganar ta tana kallon shi, ai bai san sanda ya zauna ba ya karb'i babban tray din hannun Hafsat ya na mata godiya ya dire a gaban Eamaan ya na bin ta da kallo fuskar shi cike da annuri, bude plate din gaban shi ya yi, soyayyan kwai ne da chips, sai miyar hanta, da taji kayan lambu, ga tea a flask mai kayan qamshi, zuba masa tea Eamaan ta yi tace ya fara ci bari ta had'o nata Tea din, dan bata shan wannan irin me Madara, in ta dawo bai fara ba ta fasa ci da shi, yana jin haka ya gane so take yaci kawai, amma dama ba tare zasu ci ba, nan take ya yi murmushi dan a koda yaushe yana alfahari da Eamaan din shi, sai da ya gama tass ta dawo,zata kwanukan yace mata, " Ina Fatee na? Ko bacci take ne," "Ban sani ba gaskiya, dan ba dani take kwana ba," Kamal ne ya fito cikin shirin fita shima dauke da Fatee a hannun shi ko nauyin ta baya ji, Hafsat Kuma na  ɗauke da jakar shi kamar kullum, tana ganin Anwar ta hau tsalle-tsalle a jikin Kamal tana faɗin, " Daddy, Daddy oyoyoooo," Tana ta dariya shima cikin so da qaunar yarinyar ya isa ya karɓe ta, an mata wanka sai qamshi take yi, wannan aikin Kamal ne wato feshe ta da turare, da an mata wanka an shirya ta in zai saka tirare itama sai ya feshe ta da shi, har waje suka kai su, Kamal ya bawa Hafsat kiss kad'an a lips d'in ta, Anwar na gani ya radawa Eamaan a kunne, "Kinga gani ko, kin ga yanda ake yi in miji zai fita ko? Haka za mu dinga yi bayan mun yi aure, ni fa su Hafsat na bala'in burge ni,ko dayake muma nan da wasu 'yan watanni zamu fara irin nasu, ko dake namu ma sai yafi nasu ko," Kallon shi ta yi tare da qanqance ido,fuskar ta kuma na dauke da murmushi, dauke kai ya yi alamar yaji tsoron wannan kallon ya miqa mata Fatee wadda ta fara kuka saboda bata son su rabu, lallashin ta ya yi da sweets, ya mata wayo ya tafi, dik da haka sai da ta yi ta kuka sosai kafin ta hakura, addu'a Eamaan ta masa akan Allah ya kiyaye ya Kai shi lafiya ya dawo da shi lafiya,ta d'aga masa  hannu ya tafi, gida suka koma dikan su kowacce na kewar masoyin ta. ****************************** " Ni fa Iya aure zan yi, sai ke ki koma wancan d'akin na saka amaryar anan," "Dan qwal uban ka ni zan koma wancan dan tsukukun d'akin daga gani ma kiwon wani abun akai a ciki, dan kai tantiri ne ko baka san matsayin uwa a wajen ka ba ko?k.8" Sosa qeya ya yi ya gyara tsayuwar shi sannan  ya ce , "Ni fa Iya iya adalcin da zan miki kenan, ai dai gadon ki kin cinye shi a yan kwanakin nan, sannan ni aure zanyi na gaji da bin ƙadangarun bariki, yanzu ke bama zaki min murna ba kenan zan aure na bar yawon bariki" "Yaro duniya ce ka je ta ishe ka riga da wando, sai kai auren ai,ni ba zan hana ka ba, Amma ta ya za a ce ka Maida ni wancan d'akin kamar akurki kai da matar ka ku dawo nan?" Majina ta sharb'a alamun kuka ya zo mata, ta tattaka a hankali ta shiga d'akin ta hau  kwashe yan tarkacen ta tana sharar kwalla,tinawa da Alhaji da ta yi ya sa ta zauna ta saka kuka mai cin rai, shi da ko girki bai yadda ta yi da kan ta ba, miqo d'akko ma na yau da gobe sai da ya aje mata masu yi, matar shi ma sai da ta maida ita mai aiki a gidan mijin ta. A haka ta gama tattare komai ta je ta share d'akin da zata koma da zama Wanda da Gani kiwon tattabaru ko kaji akai a ciki, ba wata  iska Dake ratsawa sosai, haka dai ta tsara kayan ta ciki ta ja qofar ta ciki ta rufe, Bata sake fitowa ba sabida bacin ran Sahabee. Shi kuwa fita ya yi yaje wajen budurewar shi ya sanar da ita komai ya yi normal kamar yanda take so, murna suka dinga yi ta na qara masa pampo akan yanda zai kawar da Iya gefe su sha soyayyar su bayan aure, shi Kuma sokon ya na biye mata kamar be tab'a sanin mace ba se akan ta zai fara. Wata qwanqwararriyar yar bariki ya samo, ta gama barikin ta gida an ce ta fidda miji, kaf maneman nata sun San ita wace ce sosai dan haka sai suka gudu,Sahabee ne ya je sama  ta ka zai soyayya da ita, ta kuwa zage suke Shan soyayya dan tin Kan auren ma ba za a Iya qirga sau nawa su na keb'ewa ba,ko yanzun ma da ya kawo mata wannan labarin me dad'i se da suka  sheqe ayar su son ran su, a kwanaki goma cif cif  akai aure ba istibra'i ba komai aka kawo amarya ta tare a gida d'aya da Iya. Daren ranar Iya ta yi kwanan takaici ,kuka sosai ta sha ta tina sanda take Kiran Eamaan da jarababbiya dan ta ji ta na waya akan  had'in maganin mata da ake da rake da kaninfari da citta, ashe yau ne zata ji jarabar iyakar Jin ta kuwa dan kuwa komai akan kunne ta suke yin shi, amarya babu sirri ta na sane ta ke duk abinda take yi dan Iya taji, Wanda ban San ribar da zata ci ba tinda Iya dai ba kishiyar ta bace uwar miji ce. Wani ihu da ta zabga kuwa se da Iya ta toshe kunnen ta, nan take wani irin nauyi da kunya suka lullube ta,ita kuwa Amarya se sambatu take tana surutai na rashin d'a'a wanda tasan dole surukar ta ta zata ji, shikuwa Sahabee sai fadi yake yana kumawa "Ashe abun nan na aure ya fi daɗi ban sani ba nai ta yawo a titi ban aure da wuri ba? Oda na sani na yi aure tin Ina da sauran qurciya ta, wayyooo Iya kin cuce ni da baki min aure da wuri ba" (niko nace dan ma baku bi yanda tsarin ya ke ba da kun fi morewa) Salati Iya ta zabga ta miqe tsaye Dan zuwa ta buga musu qofa, ko ba su yi shiru dan ita ba, su duba maqota mana, Wani ihu da Sahabee ya saki tare da amaryar shi ne ya Maida ta ta yi zaman 'yan bori ta na zubar da hawaye, lallai kuwa za su yi ajalin ta nan kusa in dai haka rayuwar gidan za ta kasance ...... [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼      BIYAYYAH.  💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 24: Anwar ya isa kano bayan azahar, direct unguwar su ya nufa cike da d'oki, sai dai bai san me yasa gaban shi ke ta fad'uwa ba, addu'a ya fara yi akan Allah ya kare shi daga dikkan abun qi ya tabbatar musu da alkhairi, ta gaban gidan su Eamaan ya wuce, aran shi yana ayyana nan da yan kwanaki za a daura auren su da Eamaan din shi anan, Wani qayataccen murmushi ya saki, ya tarar da  mai gadin gidan nasu a qofar gate din gidan tare da abokan shi ya na ta hira,hango motar Anwar ne ya Sanya shi sheqawa a guje dan bud'e gate d'in, sallama ya wa abokan Mai gadin nasu sannan ya danna hancin motar shi compound din gidan su Mai d'auke da motoci kala-kala,daga inda yayi parking d'in motar shi ya na iya hango mahaifiyar shi dake cikin lambun gidan tana ta kaiwa da komowa hannayen ta hard'e a bayan ta cike da isa,da dikkan alama tana cikin wani yanayi ne na damuwa, fuskar ta sam babu walwala a cikin ta kamar kullum, tayi nisa sosai a cikin tinanin da ta ke yi shi yasa bata San shigar Anwar d'in gidan ba ma. Bude motar shi ya  yi sannan ya fita  tare da zagayawa ya  bude bayan motar ya ɗauki ledojin da ya tsaya a hanya ya yo tsaraba ya fara takawa zuwa ga mahaifiyar shi da suke Kira da Hajiyah, yana isa ta d'ago kan ta ta kalle shi tare da murmusawa kaɗan,sannan ta ce, " Sannu da zuwa mutanen bauchi qaya baku san na gida ba," Murmushi Shima ya mayar mata sannan ya ce, " Barka da hutawa Hajiya ta,akwai abinda ke damun ki ne? Na ga kin yi nisa cikin tinanin da kike yi har na shigo baki sani ba," Kama hannun shi ta yi suka fara takawa cikin gidan, " Muje ciki kai wanka ka ci abinci ka huta zamu yi magana mai mahimmanci da kai," 'Daga mata kai ya yi alamar to, amma zuciyar shi sai bugawa take da dikkan alamu abinda za su yi magana akai Mai mahimmanci ne, tinda Hajiyah ta gama nuna hakan a fuskar shi, bayan sun shiga ne ya kammala komai, ya kwanta da niyyar ya dan samu bacci, amma inaaa baccin nan ba zai samu ba, tabbas sai yaji me ke damun Hajiyan shi haka? Tashi yai ya saka qananan kaya marasa nauyi ya fesa tirare ya saka takalmin shi ya fita. A daki ya same ta tana kwance kamar mai bacci amma idon ta biyu, sallama ya yi ta tashi zaune tare da  amsa masa sallamar shi, nuna masa kusa da ita ta yi alamar ya zauna, zama ya yi yana fuskantar ta, ta shafa kan shi tare da murmusawa tace, "Anwar in baka yi wasa ba zaka zama babban tuzuru a layin nan, rashin auren ka na damun mu matiqa ni da Abban ku,shin wai yaushe ne za ka yi aure? Ka sani kai d'aya ne Wanda muke  da shi, ga shi girma ya fara kama mu ba kai aure ba balle mu sa ran samun zuri' daga wajen ka,bama ka da niyyar aure Anwar why? Yarinyar da ka kwallafawa rai ta yi aure mijin ya mutu,zawarci take yi yanzu, kaga ba sa'ar auren ka bace ita sai ka nemi wata, amma Anwar 8inaa ka qi sam, ko an nemo maka sai ka ce basu yi maka ba, ya kake8 so na yi ne Anwar," Ta qarasa maganar ta cikin damuwa sosai, Anwar ya fita shiga damuwa musamman da yaji tana neman condaming auren na su tin kafin ya fad'i me ya kawo shi, zufa kawai yake yi,a hankali ya saka hannu ya share, kallon shi ta yi cikin kulawa ta ce, " Son me ke faruwa ne na ga ka shiga halin damuwa? Ko na faɗi wani abu daya d'aga maka hankali ne haka," " Kwarai kuwa Hajiya ta,domin kuwa yanzu haka har mun daidaita da Eamaan akan maganar auren mu,kuma ta amince da ni nima na amince da ita, yayun ta dika sun yarda na faɗa wa magabatan na wato na fada maku a nemar min auren Eamaan, Hajiya na rasa ta a baya ba....." "Haka wannan karon ma zaka sake rasa ta, wai Kai Anwar wanne irin yaro ne Kai mai kafiya da naci? Ba ka ganin yanda mahaifiyar ta ta mallake mahaifin ta se abinda ta ce, so ka ke Ina zaune wata ta zo ta dinga juya ka se yanda ta yi da Kai ni na sha wahalar banza kenan? Ba zai Yu ba to! can gidan ma da ta bari Ina da labari har mijin ya rasu ita ke juya gidan,me ka ke tunanin zai faru anan gidan in ka aure ta?" Cike da fushi ta miqe tana fad'an hakan,a hankali Anwar yace, " Hajiya ban gane me kike faɗa ba, ina son Eamaan ke shaida ce, ban da macen da zan zauna da ita zaman aure ban cutar da ita ba saboda ba zan iya mata adalci ba tinda bana son ta,iin kk ce ba zan aure ta ba a karo na biyu, na rantse sai dai na zauna ban da aure har abada, don kuwa kowa zaku auran ba zan taba zama da itaba har abada,kai gida daya ma ba zan zauna da ita ba," Idon shi ya yi jawur saboda damuwa yake maganar da bai taɓa yi wa mahaifiyar shi irin ta ba,cike da mamakin maganganun Anwar Hajiya ke kallon shi, lallai Eamaan ta yi nasara, tin kafin ya aure ta ma ta fara juya mata Kan yaro to Ina ga ya aure ta? Anwar da ko kallon-kallo na rashin kunya be tab'a had'a ta da shi ba shi ne ke mayar mata da magana haka, cikin damuwa ta ce " Anwar ni nake fada kake faɗa, akan mace? Lallai dole ne na haramta maka auren yarinyar nan, domin bana jin zai haifar da d'a mai ido a gare mu dika anan gaba," Cikin fushi idon shi ya gama rufe wa da hawaye da jimanta wa zuciyar shi baƙin cikin kalaman Hajiya ya dau hanyar fita Daga d'akin nata, ko gaban shi baya gani saboda tsabar damuwa me Hajiyah ke so daga wajen shi ne wai ? wace iriyar biyayya ce baya yi musu, wasu ma koya musu yanda za su bi iyayen su yake yi balle shi, bai tab'a masu musu ba tinda ya girma ya San matsayin iyaye a wajen d'a,me yasa Hajiyah ke so ta rusa masa farin cikin shi,wannan karon zai tsaya tsayin daka dan ganin ba a raba shi da Eamaan d'in shi ba, Luuu yayi ya fara tafiya qasa sakamakon wani jiri da ya ɗebe shi, ji kake timm ya faɗi qasa, da gudu ta nufe shi, ta na k'walla masa kira tana jijji shi, amma inaaa ya suma be San ma ta na Yi ba, hawaye ta Gani ya na gangarewa ta gefen idon shi, da gudu ta fita waje dan neman taimako,kicibus sukai da Abban shi ya gan ta a gigice, kama kafadun ta ya yi,tana ganin shi ta qanqame shi ta na nuna masa hanyar d'akin ta,da hanzari ya janye ta ya nufi d'akin nata ta bishi a baya, yana shiga yaga gudan jinin shi yashe a qasa, hankali tashe ya d'aga shi, ya kwantar a gadon, Number ɗin likitan su ya danna yayi masa bayanin halin da ya tsinci  Anwar a ciki, likita cewa ya yi su kai shi asibiti kawai. Waje ya je ya samo matasa biyu suka ɗauke shi su ka nufi mota da shi suka saka a ciki, Abban shi da Kan shi ya ja mota suka yi asibiti, suna zuwa aka bashi gado, likita ne ya shiga duba shi da kyar ya samu nunfashin shi ya daidaita ya dawo hayyacin shi, allurar bacci suka masa ya samu bacci, a dan wannan tazarar ko wanda bai san shi ba ya kalle shi ya san yana cikin damuwa, saboda yanda fuskar shi ta koma, "Fada min me ki kayi masa? Kin nuna masa qiyayya akan Eamaan ko kamar yanda kika saba ko? Kin sanar da shi mummunar a qidar ki mara tushe da madafa akan yarinya Mai nutsuwa da kamun Kai tare da BIYAYYAH kamar Eamaan ko? Ke wai me yasa kike da qaramar ƙwaƙwalwa ne watarana? ko mai aka fad'a maki baki d'auka, ko nace kina da son kan ki, in ba son kai ba in kin manta bari na tina maki, Mubaraka qanwar ki, ba a bazawara kuka aurawa saurayi ba wata hud'u da suka wuce, wato ke kece mai d'a ba zaki bar d'an ki ya auri bazawara ba, tinda su ba su da gata ko wata cutar ce a jikin su, ko kuma wani mummunan d'abi'u ne da su da yayi fice, to in wannan kike hangowa da baku ba d'an uwana ya auri qanwar ki ba, mai shegen son kan tsiya,for ur information Hajiya d'azu-d'azu muka gama magana da mahaifin yarinyar akan had'a auren su, tinda ke baki da tarihin Annabin rahama akan ki, waya fara aure a rayuwar shi ne? Bazawara ce Nana Khadeejah mai yara,wadda ba aure ɗaya ma tayi ba kafin auren Annabi ,sannan ta girme shi ma ita,  kuma sun yi zaman da yake yabon ta har saida ya koma ga Allah,sannan ta haifa masa Yara Mafiya daraja a duniya da lahira, to shi Anwar wane ne shi? Wa ya fi da ba zai auri bazawara ba, musamman ma da shi ya kawo ta ya ce ya na so, Anwar ya kuma girmi  yarinyar nan ya bata shekaru d'ai-d'ai har bakwai, sannan ke da kan ki kk yabon halayen ta a baya dik da kina ƙin ta,amma yanzu kike son ki rufe idanun ki dan son zuciya ki ce ba haka ba, to bari ki ji aure babu fashi idan ki ka sake nuna masa qiyayyar auren nan zai zama a bakin naki auren, sannan in Wani abu mummuna ya samu yaro na ko....." Bai qarasa maganar shi ba ya zuba mata Wani mugun kallo ya kade rigar shi ya fice daga asibitin gaba d'aya, ta gama bata ran shi, ai ta magana d'aya amma bata gane komai? Zuciyar ta ta matuqar raunana, musamman na ganin gudan d'an nata a kwance kamar matacce,sai a lokacin ta gane ashe ma ran gaba d'aya shi ba abakin komai yake ba, da mutuwa ya yi da itama mutuwar za ta yi ai tin da ita ce sanadi , hawayen ta ta share ta goge majina da tissue, ta qura masa ido, a nan suka kwan, mai aikin su ta kawo masu abinci, da kayan Tea, Abban shi na son ya dawo amma so yake ya koya mata hankali, ya fita sha'anin ta, dan ya sani zasu wahala saboda ya San in ta shiga damuwa ta na tsananin buqatar tallafin shi, Dan haka dole ya nuna mata kuren ta musamman in bata yarda da maganar auren  ba har yanzu. ************ " Subhanallahi me ya same shi? "OK to shikenan, yanda kace hakan za ai," "Ba damuwa, zuwa goben sai a daura ɗin, Allah ya bashi lafiya, yau zamu zo duba shi da yardar Allah" Aje wayar Daddyn Eamaan ya yi, ya Maida  kallon shi ga matan shi da ke zaune gefen shi suna magana akan auren Eamaan d'in da Anwar. Bayanin Kiran da mahaifin Anwar ya Masa yanzu yayi musu suma, sun jimanta rashin lafiyar da yake sannan suka yi fatan Allah ya Sanya alkhairi da albarka a cikin auren,sun yanke cewar da an yi sallar magrib za su je duba shi,Amma tace ita kam sai dai a tafi da Mama ita za ta yi wasu abubuwan in basa nan, kuma ai ba a bar gida shiru ba sai masu aiki kawai, murmushi suka yi dan sun gano ta, Daddy ne yace, "To fullo ba komai munje da yayar taki Allah ya kaimu," Dariya suka yi dikkkan su, ita kuma kunya ta qara kama ta, dan tana tsananin son d'iyar ta ta, ga shi Allah ya had'a ta da abokiyar zaman da sai dai sabanin harshe da haqori amma Mama ba ta da matsala ta ja girman ta sosai, ita kuma tana bata girman nata,bar Mama dai  da son bin ra'ayin ta, bata yarda a yanke mata hukunci ba tare da an yi shawara da ita ba, ko Kuma ta yi niyyar abun, a wannan kam za a buga da ita sosai. Washe gari da misalin sha d'aya na safe aka daura auren Anwar da Eamaan, kan sadaki dubu hamsin, wanda Abban shi ya so su bada d'ari, Daddy ya qi,yace albarkar suke nema ba yawan ba,lokacin da labari ya iske Anwar tini ya ware ya miqe daga gadon asibitin ya na qoqarin cire qarin ruwan da aka masa,tangararau ya ke tafiya kamar ba shi ne ya sha jinyar love ba,har office ya Sami  likitan ya matsa Masa a sallame shi shi ya ji sauqi, likita ya shaida ya ji sauqin tinda ga shi tsaye rasss,dan haka ba shi da zab'in da ya wuce na ya sallame shi. Tinda suka koma gida Hajiyan shi ta kasa gane Kan shi Dan ko fara'a yake daya ga Hajiyar shi sai fuskar shi ta canja zuwa ba yabo ba fallasa, abun na matuqar damun ta, Abban shi ya tsime shima ya dauke mata wuta,ta rasa inda zata je ta ji dad'i a wajen su, gashi ta nuna musu ita fa ta sakko ta bi Allah ta bi mijin ta da abinda d'an ta ke so. Eamaan ke zaune sai juya cokali take a abinci tana murmusawa, ita d'aya,sabuwar wayar ta na gefe wadda Kamal ya sai mata a  jiya, Hafsat ce ta zauna gefen ta tare da dafa ta ta ce, "Wai ke albishir aka maki da makka ne kk ta murmushi haka? Kin ma qi taba abincin ki a bakin ki sai juya cokali kk, meke faruwa ban San da shi ba, ban labari na sha dear sis," Murmushin ta ne ya fad'ad'a, "Ban san me ke damuna ba Hafsy, kawai ji na nake ina cike da nishadi, tinda na sa qafa na sauka a gado, da  farko dai daren jiya cikin damuwar wani abun da ban san meye ba na kwana, amma yanzu zuciyata cike take da farin ciki kamar ance an mallaka min Anwar," Ta qarasa tare da dafe bakin ta lokacin da ta ji qarar takalmin Kamal na zuwa wajen su, qara gyara mayafin ta ta yi ta rufe jikin ta sosai, tana murmushi, "Kin ji da gulmar ki an jima shi zaki ta yi wa wannan rashin kunyar taki ai," "Albishirin ku, ko dake Eamaan albishir, me zaki ban inna fad'a maki wannan kyakkyawan labarin," Zaro ido ta yi waje cikin wata iriyar  murna kamar ta san me zai ce mata, " Yah Kamal sai abinda kk so zan baka," " kin tabbata?" " Eh na tabbata," "Ok dazu da misalin sha d'aya aka daura auren Anwar da Eamaannnnnn" Ya qarasa maganar shi cikin d'aga murya yana farin ciki,sai kama hannun Hafsat yana juya ta yana kallon Eamaan suna dariya, Idon ta ya cika da hawaye murmushi ɗauke a fuskar ta,daga  baya kawai se suka ga ta fashe da kuka ta miƙe zata bar wajen.......... [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼    BIYAYYAH.   💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 25: Kukan murna Eamaan ta yi sosai kan ta ɗago da idanun ta da suka sauya kala daga farare tas zuwa launin ja, haqoran ta farare wanda suke a jere ɗauke da siririyar hushirya sai haskawa suke, Hafsat da ta matsa kusa da ita tana shafa bayan ta da sigar lallashi ta kalla, itama murmushin ta sakar mata Fatee kuwa na ta kallon ta da mamakin dalilin kukan nata, Eamaan ce ta ce, " Yah kamal me kake so a matsayin goron albishir d'in da ka min yanzu?" " Ba abinda nake so illa kafin nan kafin ki tafi ki koya ma Hafsat duk girke-girke  da kike yi mana masu dad'i, sannan kuma a bar mana Fatee har tsawon lokacin da kuka gama cin amarcin ku sannan ku karɓe ta, ke in ma Anwar ba zai d'auke ta ba ni nayi tayin riqe Fateema har abada a matsayin ta ƴata" Farin ciki ne ya qara sanya ta kuka sosai mai cike da murmushi, lallai Yah Kamal na son Hafsat sosai, dan ta kula yana taya Hafsat son duk abin da take so, ko baya son abun nan indai ta na so to fa Shima abun nan ya zama abin son shi,lokuta da dama shi da Eamaan sukan zauna su yi ta gulmar Hafsat d'in, su Kan yi magana da Eamaan akan shi fa baya son kaza a da amma tinda ya kula Hafsat na so ya ji ya fara son abun. " Yah Kamal kome kake so zan yi maka,kai daga yau ma zan fara inshaa Allah, game da Fatee kuma shi fa Anwar cewa ya yi da ita za mu tare duk sanda Allah ya sa muka yi aure, amma dole zan lallab'a shi mu barta ko wata biyu muka yi an maida ta yanda dai ya amince,"

Chapter 16 of 20