Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Amaar yana tsaye shima sauran kaɗan hawaye ya yanko masa yayi saurin kawar da kan sa gefe tare da faɗin "Allah sarki! Ina so ku bani damar maye gurbin sa..." Asmeen da sauri ta furta "mun baka..." Nasreen kallon Asmeen tayi tana sakin murmushi, duk basu san lokacin da suka tsinci kan su cikin farin ciki ba, Shima yana murmushi ya basu damar shiga motar sa zasu bi bayan Tasleem ta hanyar connecting location da phone number ta.... Cikin lokaci ƙanƙani suka isa wurin da motar ta take a tsaye cakk, Asmeen ta ce "wannan ne motar mu, i think tana ciki..." A ruɗe Nasreen ta ce "Polo Grand Hotel?..." Sai a lokacin Asmeen ta lura da yanda suka zo, a zabure ta furta "Hotel kuma, me tazo yi?..." Amaar idon sa akan motar ya ce "tana cikin motar bata fita ba, ina tunanin tana jiran fitowar wani ko wata..." Su ma suna cikin mota basu fita ba, sai gani suka yi wani saurayi ya fito daga cikin Hotel ya nufo motar ta, yana zuwa ya fara knocking, saurayin irin masu jiji da kai ɗin nan ne, tantiran ƴan daba domin har da sigari a hannun sa yana zuƙa... Bayan wasu mintina sai ga Tasleem ta buɗe murfin motar ta sai da ta fara sauƙar da ƙafar ta ɗaya kafin wasu seconni ta fito da ɗayar cikin ƙasaita da izzah ta fito a cikin motar tana taku a hankali sai ƙarar sautin takalmin ta ake ji har ta zagayo yanda saurayin yake a tsaye yana busar taba, Tsayawa tayi a gaban sa tare da goya hannayen ta akan ƙirji, ga wani tsararren black glass akan dara-daran idanuwan ta suna facing juna... Cikin izzah ta furta "Sarkin ƴan daban yanki Arewa, gagara hukuma...." Wani irin mahaukacin dariya ya yi tare da hura mata hayaƙin tabar bakin sa, yana faɗin "ba iya hukuma ba gagara kowa ne..." Murmushi ta sau ko motsi bata yi ba balle hayaƙin tabar sa ya dame ta, ta ce "ban da kowa domin baka kai ka gagari kowa ba har yanzu da sauran ka..." Wani irin kallo ya yi mata yana faɗin "me ke tafe da ke murɗaɗɗiyar yarinya mai murɗaɗɗen tunani, ai da kin mun magana har wurin da kike zan je na same ki, amma yanzu ina cikin jin daɗi na da Babies ɗina akan gado kin zo kin takura mun akan na fito waje, shin meya hanaki shiga cikin Hotel ɗin?..." Tasleem tana tsaye fuska ba alamar annuri ta ce "kar ka yi kuskure dangantani da shiga cikin Hotel sannan ba wai jin daɗin kaina ne yasa na biyo ka har yanda kake ba, ba muhawara nazo muyi ba..." Nasreen suna cikin mota ta ce "me Tasleem take a wurin wannan mutumi marar ɗa'a?..." Asmeen ta ce "kamar tattaunawa suke akan wata magana, amma meye alaƙar dake tsakanin su, a sanin mu Tasleem bata tsayawa da kowa tayi zance saboda bata da lokacin kowa..." Amaar idonsa akan ta ya kasa furta komai... Tasleem cikin fushi ta furta "Meyasa kayi mata fyaɗe?..." Mutumin jin tambayar da tayi masa ne ya sa shi tintsirewa da dariya ya ce "Amma kin raina mun wayo yarinyar nan, yanzu don nayi fyaɗe har sai an tambaye ni Meyasa nayi? ka ji banza! jin daɗin rayuwata mana, wai ma tsaya kina magana ne akan waye? kinsan sunada yawa akwai yara sannan akwai ƴan mata akwai tsofi shin wa ye daga ciki?...." Haka zuciyar Tasleem yake hauro wa kamar ta murɗe masa wuya amma da haka ta daure cikin ɗaga murya ta furta "Yarinya ƙarama ƴar shekara uku marainiyar Allah wacce ake rainon ta a gidan marayu, fara zuwan ta makaranta kenam ka shiga cikin makarantar kayi mata fyaɗe saboda kaga babu wanda zai ɗauki hukunci akan ka, to wannan yarinyar tana cikin ƙarƙashin kulawa ta, duk ƙananun yaran da suke cikin gidan marayu tamkar jinin jikina nake jin su, da hannuna na yi rubutu na ɗauki yara 15 ƴan shekara 3 zuwa 4 na sanya su a makaranta, a cikin motata na ɗauke su na kai su makaranta na biya musu kuɗin makaranta, yau kwana uku da fara zuwan su, yau kuma aka ƙira ni ake sanar mun ta'addancin da kayi musu, kayi wa ƙananun ɗalibai biyar fyaɗe a lokaci guda kuma kana tunanin baza'a yi maka komai ba saboda kana yaron Minister, tirrrrrrr...." Tinda Tasleem ta girma bata taɓa yin kuka ba sai yau, ta cikin glass ɗin kan idonta hawaye yake tsiyaya kamar da bakin gora.... Duk waɗannan maganganu da tayi babu wanda bata ɗaga murya kowa ya ji ba, Su Nasreen dake cikin mota duk suna jin abinda take faɗi, haka hawaye yake tsiyaya a cikin idon Nasreen itama, Asmeen kuwa ba abinda take faɗi sai Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Shima Amaar ya jinjina wa rashin imani irin na wannan mutumin... Mutumin da ake ƙira da Firoj ɗan gidan Ministan garin ba abinda yake sai dariya, haka yake ɗaga murya shima yana faɗin "wannan ba sabon abu bane a wurin Firoj, ƙananun yara ya irin shekarun ta sun fi dubu waɗanda nayi wa fyaɗe, wasu sun mutu wasu sun warke wasu suna kwance ba lafiya duk na sa ni........" Kafin Firoj ya rufe baki har Tasleem ta zuciyo ta zabga masa mari akan fuskar sa, kafin ya ankara ta riƙe kafaɗunsa biyu tare da ɗago da ƙafarta tayi amfani da gwiwarta da iya ƙarfin ta ta buge masa tsuriya, ba shiri ya durƙusa ƙasi yana ihu tare da riƙe wurin, Tasleem ƙafa tasa ta canki ƙirjinsa ya faɗi ta baya yana kallon sama, kafin ya ɗago ta ɗora ƙafar ta da take sanye da takalmi mai bala'in tudu da tsini ta taka tsuriyar tare da miƙe wa tsaye akan sa, haka take ta tattaka tsuriyar da takalminta ta wurin tsinin. Firoj ba abinda yake sai ihu gaba ɗaya ƙarfin jikin sa ya ƙare sai buga hannayensa yake a ƙasi, Kafin ka ce mai mutane har sun taru masu video kowa yi yake, ana gulmar ɗan gidan Minister, Sai da ta gama lugwigwita masa masarrafai duk babu wanda ya dakatar da ita kafin ta sauƙa akan sa, tana murmushi ta nufi bayan both ɗin motarta ta buɗe ta ɗauki wani sanda na ƙarfe ta koma yanda yake kwance yana birgima, haka ta fara doka masa wannan ƙarfe a duk wurin da tasan zai raunana, da ta samu kan gwiwarsa ta fara kwaɗa masa sai da ta karya masa ƙafa ɗaya sannan ta gurɗa ƙafa ɗaya, ta koma kan hannayensa nan ma sai da ta karya masa hannaye biyu... Nasreen da Asmeen kuka suke suna so su fito su dakatar da Tasleem kar tayi kisan kai amma Amaar ya riƙe su, yaƙi barin su fita, sai roƙon sa suke amma yaƙi bari sai ma key da ya sa a motar gaba ɗaya yanda baza su iya buɗe wa ba, Har cikin zuciyar Amaar so yake sai yaron ya suma domin a faɗar sa bashi da amfani a cikin al'umma, in ma kashe shi tayi a cewar sa babu abinda za'a mata.... Nasreen a tsawace take faɗin "wai kai bakada imani ne? so kake ta kashe shi itama a rataye ta? shin kasan shi ɗin ɗan gidan waye ne? ɗan gidan Minister ne fa, kuma nasan dole sai an kamata...." Amaar cikin ɗaga murya ya furta "Tasleem bazata taɓa kamuwa ba koda kashe shi tayi, ko shugaban ƙasa bai isa kamata ba, a yanzu zan buɗe ku ne kuje ku dakatar da ita saboda kar ta shiga bakin duniya cewa tayi kisan kai, bazan so hakan ba...." Yana kaiwa nan ya buɗe motar sa, da gudu Nasreen da Asmeen suka fice, nufan yanda Tasleem take ta dukan Firoj suka yi domin a halin yanzu ko motsi ya daina yi, baya cikin hayyacin sa amma duk da hakan Tasleem bata daina kwaɗa masa ƙarfen nan ba, duk ta faffasa masa kai.... Nasreen da Asmeen ne suka rirriƙe ta tare da ƙoƙarin jawo ta gefe da ƙyar domin kokuwa suke, Tasleem ba abinda take furtawa illa "ku sake ni na ƙarasa ɗan banza, yau ni zanyi ajalinsa, ku sake ni nace shin kun san abinda ya aikata mun ne?..." Nasreen itama cikin ɗaga murya ta ce "baza mu sake ki ba Tasleem, bakida hankali ne zaki yi kisan kai..." A tsawace Tasleem ta furta "banida hankali Indai akan marayun yara ne..." tare da yin wurgi da Nasreen har sai da tayi dungure sau uku sai gata a gaban Amaar wanda fitowar sa kenan a cikin motar sa, A fusace ta juyar da ƙwayar idanuwanta kan Asmeen wacce ta gama tsorata da irin fusatar da Tasleem tayi har tayi wurgi da Nasreen, ba shiri kuwa ta yi baya da gudu... Amaar hannu yasa ya ɗago da Nasreen har goshin ta ya fashe sai jinin dake zuba, Tasleem kallace-kallace take tana neman abun da zata ƙara sa Firoj domin ƙarfen hannun ta duk ya lanƙwashe, idonuwanta ne suka sauƙa akan AMAAR, ta ɗau tsawon seconni tana kallon wurin da Amaar yake, sai dai abun mamaki ba Amaar ɗin take kallo ba, bindigar dake sokare a aljihun wandon sa take kallo, tana tunanin yanda zata je ta ciro shi, Kafin a ankara har ta tafi da gudu ta ciro bindigar, kafin Amaar ya ankara har ta kunna kunamar bindigar ta sai ta Firoj, Nasreen da Asmeen ihu suka fara yi suna bata haƙuri akan ta dakata, Amaar wani irin sufa ya yi tare da riƙo hannun ta ya ɗaga sama dai-dai lokacin ta danna kunamar bindigar sai ga bullet ya fita yayi sama, ga shocking ɗin da yabi jikin su wani irin ihu Tasleem tayi sai da suka ɗagu sama suka doku a ƙasi, bindigar hannun ta ya cillu gefe guda... Tasleem cikin ƙarfin hali ta ɗago da kanta tana ƙoƙarin juya bayanta tana son ganin wanda ya riƙe ta har wannan shocking ya same ta, kafin ta juya kuwa Amaar yayi saurin tashi jiki na ɓari ya ɓuya a bayan mota, Dafe goshin sa yayi domin ba ƙaramin juyawa ƙwaƙwalwar sa ke yi ba, Asmeen da gudu ta nufi yanda yake tana faɗin "Ya Amaar kana lafiya, zan iya taimaka maka?..." Itama Tasleem tunanin ta ne ya fara gushe wa, ƙwaƙwalwar ta na juyawa, wani irin sauti ta fara ji ana faɗin "Tasleem ki taimake ni, kar momynki ta kashe ni, Tasleem dan Allah, Tasleem ki taimake ni...." a cikin kwakwalwar take jin waɗannan sautin, itama dafe kanta tayi tana birgima.. Nasreen ganin ciwon Tasleem yana shirin tashi yasa ta tafi wurin da take kwance da gudu tana ƙiran sunanta, Dai-dai lokacin da motar Minister ta iso da wasu motoci na sojoji da polisawa sai jiniya ne yake ta tashi. Ta ɓangare guda itama Madam Nablah ta zo da motocin security ta......... NEXT....... New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 13 to 14 Minister yana sauƙa da gudun gaske ya nufi yanda yaron sa yake a kwance shame-shame, kafin ka ce mai sai ga Ambulance an zo ɗaukan sa, Madam Nablah wacce fitowar ta kenan daga cikin mota idanuwanta suka sauƙa akan Tasleem wacce take ta birgima tana riƙe da kanta sai sambatu take wanda ba'a jin abinda take faɗi, Madam Nablah ganin ƙwaƙwalwar Tasleem ne yake shirin motsawa ne yasa gaba ɗaya hankalin ta tashi, yanzu ba'a gida suke ba balle tayi mata abinda ta saba idan ciwon ya motsa, a yanzu nuna tsafin ta zai bada matsala, babu wanda yasan ita matsafiya ce still ga yaran ta a wurin, tana cikin tunanin yanda zata yi ba zato ba tsammani taji dirarren murya ya sauƙa akan dodon kunnen ta, Minister ne yake zazzaro idanu cikin fushi yake faɗin "Nablah kun wuce gona da ƙiri, shin ɗiyar ki tasan wa ta taɓa kuwa? to ki sanar mata cewa ta taɓo masifa da bala'i akan ta sai tayi nadamar tozarta Firoj da tayi...." Madam Nablah idonta akan Minister tana sakin murmushi cikin izzah ta ce "Hmmm! Minister kenan tabbas nasan yaron wa Tasleem ta taɓa amma ina so ka sani cewa ita ma Tasleem ƴa ce ga babban mutum wanda duniya ta san shi, idan ka manta zan tuna maka, iya ɗin ɗiya ce ga Governor wannan ƙayataccen garin da muke ciki, sannan mahaifiyar ta Madam Nablah wato ni ba ƙaramar mata ba ce da za'a taɓa mun ƴaƴa nayi shuru na ƙyale...." Minister ya ce "maganar banza! kina maganar ƴar governor shi da ya juma da barin muƙamin? shekara nawa da shafe shafinsa, a bayan sa govenoni nawa aka yi? to bari kiji wallahi tallahi sai na ɗau hukunci akan wannan al'amarin, zan sa a ɗaure ɗiyar ki a gidan yari har sai yarona ya samu isasshen lafiya..." Madam Nablah ta ce "Idan kuma ya mutu fa?..." A fusace Minister ya ce "itama dole zata mutum, sai ta girbi abinda ta shuka..." Madam Nablah ta ce "okay fatan nasara..." Daga nan Minister da mutanen sa suka tafi kai tsaye hospital suka nufa yanda aka kai Firoj... Madam Nablah kallon Nasreen ta yi sannan ta ce "ku kai mun ita cikin mota..." Nasreen da Asmeen ne suka yi ƙoƙarin ɗago ta suka nufi cikin mota da Tasleem, Shi kuwa Amaar tinda idanuwansa suka sauƙa akan Madam Nablah ya nemi wuri ya ɓuya amma idonsa yana kanta, ya gagara manta wannan kamannin tin shekarun baya... Madam Nablah shiga motar ta tayi ga Tasleem a back seat a kwance, da gudu Madam Nablah ta ja mota ta bar wurin sai security ta da suka bi ta a baya, Nasreen da Asmeen su ma motar su suka shiga zasu bi bayan su, cike da damuwa suka ja motar suka bar wurin, Amaar dake tsaye gaba ɗaya fuskar sa ta jagalgale ba alamun annuri a fuskar sa, tsananin damuwa ne a kwance a fuskar sa, yana kukan zucin abubuwa da yawa na farko ya rasa mahaifinsa wanda bai san meya faru da shi ba, a cewar mutane da yayi tambaya sun sanar masa cewa mahaifinsa ya daɗe da rasuwa, amma ba'a san mai ya kashe shi ba, Sannan ga damuwar rashin Ɗan uwansa Abeesh duk da ya ji labarin yana gidan Madam Nablah amma shi ko kaɗan baya ƙaunar zuwa gidan, saboda baya son kowa ya gane shi a yanzu sai ya gama binciken sa akan Madam Nablah... Shima motar sa ya shige tare da nufan yanda ya miƙa, abinda ya ra ya a ransa shine zai je can tsohon gidan su, wato gidan mahaifinsa wanda tin lokacin da aka rasa shi gidan yake kulle babu mai shigar sa... Madam Nablah su na isa gida tasa security ɗaya ya ɗauki Tasleem tare da bashi Umarnin ya kaita can part ɗin ta, itama ta bi bayan su, Nasreen da Asmeen bayan sun iso a falo suka zauna kowa da damuwa akan fuskar ta, su na cikin wannan halin su ka fara jin ringing ɗin telephone dake ajiye akan table ɗin falo, hakan na nufin ana ƙiran mutanen gidan ne, kowa zai iya ɗaukan ƙira ko a cikin ƴan aikin gidan ma, Nasreen idonta akan Telephone amma ta kasa motsawa tsabar jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba, Asmeen ce tayi ƙarfin ɗaukan wayar tare da karawa a kunne, tana faɗin "hello wa kake nema a cikin mutanen gidan?..." Ta cikin wayar ta ji an furta "Asmeen, Asmeen nake nema..." Cike da mamaki Asmeen ta ce "waye kai ɗin?..." Shima ya ce "ke ɗin wacece?..." Asmeen ta ce "naji ka ƙira sunana shin meke tafe da kai?..." Daga cikin wayar ta ji an furta "kin tafi kin barni da yunwa, uban wa zai yi feeding ɗina?..." Gaban Asmeen ce ya yi matuƙar bugawa da ƙarfin gaske jin Shaprees ne, A ruɗe ta ce "kayi hakuri gani nan zuwa, Allah ya huci zuciyar ka..." Tana kaiwa nan ta ajiye wayar cikin damuwa ta miƙe tana goge hawaye ta fice daga falon, kai tsaye part ɗin Shaprees ta nufa... Ita kuwa Nasreen kanta ta kwantar akan sopar kujera, da haka har bacci ɓarawo ya ɗauke ta a wurin, Bayan wasu mintina sai ga Abeesh ya dawo daga wurin aiki, har zai wuce idonsa ya sauƙa akan Nasreen dake ta shan bacci, murmushi ya sau domin ya gane cewa Nasreen ce, zuwa yayi gabanta ya durƙusa yana ƙare ta da kallo daga bisani ya ajiye jakar hannun sa akan kujera sannan yasa hannu ya ɗauke ta, kai tsaye upstairs ya haura ya nufi part ɗin su da ita, yana zuwa ya kwantar da ita akan gado sannan ya tofa mata addu'o'i ya fice a ɗakin yana sakin murmushi shi kaɗai.... Tasleem ce kwance akan gadon Madam Nablah an gama tsafe ta, an juyar mata da tunanin da yake shirin

Chapter 8 of 34