har kina so na da gaske to ki guji jefa ni a cikin wani halin da zai sa na kusanci macen da ba muharrama ta ba, ina nufin zina...."
Catrina jinjina kai ta yi ta ce "nayi maka alƙawarin babu abinda zai shiga tsakanin mu sai alkhairi, amma dan Allah ina so a wannan daren ka zauna dani, ko zan iya bacci...."
Abeesh ya ce "yanzun ya kike jin jikin nakin? na taho da allurai..."
Catrina zato ido tayi ta ce "ni kuma meya haɗani da allura bayan nace cutar kewar ka ke damuna, kaine magani na, ka kwana dani sai na fi samun nutsuwa...."
Abeesh kwanciya ya yi a bakin gado, itama kwanciya tayi a gefen sa tare da rungumo shi tana kallon kyakkyawan fuskar sa....
Nasreen kuwa har misalin ƙarfe 3 ta kai na dare tana jiran fitowar Abeesh daga ɗakin Catrina amma shiru har bacci ya ɗauke ta akan kujerar falo...
Daren ya gangara cikin nutsuwa da ɓoyayyun ruɗani. Abeesh ya kwana a ɗakin Catrina zuciyarsa cike da rikice-rikice, amma jikinsa yana masa jagora cikin natsuwa kamar yana bin saƙon da zuciyar sa ke masa.
-------Ƙiran Asubar Farko akan kunnen Abeesh, buɗe idonsa ya yi yana bin ɗakin da kallo, a hankali ya maida idonsa kan Catrina wacce take kwance akan ƙirjinsa bata samu farkawa ba...
A hankali Abeesh ya ture ta gefe sannan ya tashi jiki a sanyaye ya fice a ɗakin, yana sauƙa falo ya tarar da Nasreen a wurin da ya barta tana kwance akan kujera idonta a lumshe kamar mai yin bacci, sai dai ba baccin take ba, da sauri Abeesh ya wuce gudun kar ta buɗe ido ta gan shi, yana wuce wa Nasreen ta buɗe ido tana jinjina wannan lamarin, tasan Abeesh ne ya wuce domin tin sauƙowar sa ta gan shi, ganin sa ne yasa ta lumshe idonta....
A yau bata tanka masa ba, kuma bata nuna masa cewa tasan a ɗakin Catrina ya kwana ba, haka ta zuba masa ido,
Ganin haka yasa a kwana na biyu Catrina ta ƙara neman sa, a wannan lokacin ƙiran sa tayi tana kuka, ganin haka yasa ya fita nan ma da daddare ne misalin ƙarfe 10...
Fitarsa ke da wuya ya fara leƙe-leƙe gudun kar ya tarar da kowa a falo, duk wannan lelleƙawar da yake Nasreen tana tsaye a bakin ƙofar kitchen tana kallon sa, hannun ta riƙe da kofin tea zata sha domin yanzu bata iya cin komai, da haka ya wuce ɗakin Catrina, a yau ma acan zai kwana....
A wannan ranar Nasreen kwana tayi bata yi bacci ba, tana kwance a ɗakin ta tana kuka kamar ranta zai fita. Idonta ya kumbura, zuciyarta cike da raɗaɗin kishi da bakin ciki. ita kaɗai sai juyi take a gado gaba ɗaya kwanciyar hankali ya ƙaurace mata....
Da safiyar gari, kafin kowa ya farka, Nasreen ta tafi ɗakin Tasleem.
Tasleem tana kan sallaya yanda ta idar da sallar asuba, ganin Nasreen a cikin wani hali ne yasa tayi saurin miƙe wa tsaye tare da faɗin
"lafiya kuwa Nasreen? me yake faru wa?...."
Nasreen sai da ta rungumi ‘yar uwarta Tasleem kafin ta fashe da kuka, tana sharar hawaye cikin muryar kuka take faɗin
“Tasleem... na gaji! Kamar a cikin mafarki nake, yana kwana da wata a yayin da ni nake matsayin matarsa! Kuma ya kasa fitar da ita daga zuciyar sa... kina ganin zan iya ci gaba da wannan zaman?”
Tasleem ta saki numfashi da ƙarfi, baƙin ciki da tausayin Nasreen ne suka shige zuciyarta.
Ta dafa kafadarta tana faɗin
“ Na fahimce ki, Nasreen kiyi haƙuri... amma ki barni da ita. Wallahi sai ta gane cewa gidan nan ba na raini bane. Wata iriyar ‘yar bariki ce haka? ko ita ɗin mutum ce ko ba mutum ba ce—wallahi sai na tunkare ta!”...
Tasleem ta share mata hawaye tana faɗin "ki yi haƙuri ki sa salama a cikin zuciyar ki, ki daina bayyanar da damuwar ki a wanda yake son ganin bayan ki, yanzu ki je ki huta zan neme ki...."
Nasreen jinjina kai kawai tayi tare da ficewa daga ɗakin....
---.
Shaprees yana ɗakin su yana kallon Asmeen wacce ta fara narkewa a hankali. A wannan ranar, ta zauna kusa da shi a cikin dakin su na ma'aurata, tana tausayin yadda yake kokarin kyautata mata ba tare da nuna tsana ko kishi ba.
A hankali ta furta
“Shaprees... baka san yadda nake jin ba a raina, na jima ina tunanin kai wani ne dabam, amma yanzu ina ganin... ka cancanci ka samu farin ciki.”
Shaprees ya kama hannunta, yana kallon ta cikin kulawa ya ce:
“Ina so ki yarda dani, Asmeen. Na cire duhu daga zuciyata domin Allah. Soyayya da alheri nake nema yanzu. Kiyi ƙoƙarin bani dama dan Allah...”
Asmeen wasu zafafan hawaye ne suka gangaro mata tare da rungumar sa tana kuka...
Shima rungumar ta ya yi yana rarrashin ta cikin so da ƙauna..
Haka kawai yake jin tausayinta, especially jin ƙudurin mahaifiyar ta akan su....
★★★★★★★
A yau...
Tasleem ta tunkari Catrina da fuska ɗauke da zafin zuciya da tsantsar fushi...
Tarar da ita tayi a zaune a falo tana kallon wani Film na horror..
Tasleem tsaya mata tayi a kai cikin tsantsar matsifa take faɗin
“Ke! Na gaji dake, Kina wasa da zuciyar ‘yar uwata, da mutuncin mijinta. Ko kin manta wannan gida na mutunci ne? Kin raina mana hankali?”....
Catrina ta ɗaga kai tana kallon Tasleem cikin kwanciyar hankali, murmushinta bai gushe ba. Ta ce da ita:
“Wannan gidan ne na mutunci ko kuma mutanen cikin ta?
Hmmmm! Idan zuciyar mutum ta mallaki wani abu, ba laifi bane. Shin idan mijin ‘yar uwarki yana nuna mun soyayya... hakan laifi ne?”
Wani irin cakuma Tasleem tayi wa sumar gashin ta tare da ɗago ta tsaye, Catrina daƙer ta fizgi gashin ta tana faɗin "Ashhhh!! kina hauka ne?..."
Tasleem tana zaro ido waje ta ce
"Yau zan nuna miki yanda ake asalin hauka, Indai zaki cigaba da bibiyan mijin ƴan uwata to sai na gurɓata miki rayuwa, shaiɗaniyar banza, karuwar gida, idan mazajen mutane kike so ki fita can bariki suna jiran wanda bai zo duniya ba ma, amma ba'a cikin gidan nan ba, domin kaf babu la'anannu, da mutuncin mu da darajar mu haka kuma da kimar mu mun kuma san kunya..."
Tintsirewa da dariya Catrina tayi tare da faɗin "da farko dai ki fara zuwa ki tuntuɓi mijin ƴar uwar takin, ki bashi zaɓi shin yana so nane ko kuwa, idan ya baki amsar eh yana sona to kuwa sai dai kuyi haƙuri domin ba bu yanda zaku yi da ni, na zamo muku ciwon ido a cikin gidan nan...."
A fusace Tasleem ta shaƙo wuyan ta tana faɗin "aww haka ma kike cewa? ai kuwa zaki bar gidan nan tinda ba gidan uban ki bane...."
Itama Catrina riƙo ta tayi nan suka fara kaurewa da faɗa...
Tasleem da Catrina sun shiga faɗa mai zafi. Gidan ya ɗauki ƙarar fashewar glashe yanda suke ta faffasawa duk a cikin faɗan, kayan ado da fitilu na falo duk suka faffaɗo ƙasa suna tarwatsewa kamar hayaki, kowa yana ji da ƙarfin sa domin akwai sirrin ƙarfi a jikin su wanda yake ɗauke da Haske da Duhu....
Catrina ta fisgi labulen taga, ta wurga wa Tasleem ta faɗi ƙasi ita da labulen, itama haka ta zuciyo ta miƙe tare da janyo kofunan glass dake jejjere akan dinning ta wurga wa Catrina sai akan goshin ta, nan da nan goshin ya fashe, a ruɗe Catrina ta sau wata ƙara....
Tasleem nuna ta take da yatsa tana faɗin:
"Kin raina mana hankali Catrina! Ke ba mutuniyar kirki bace. Kawai kin zo da niyyar ruguza soyayya ne! Kin fi karfin mu ke?!"
Catrina ɗago wa tayi tare da ɗaga gira, tana goge jinin da ke zubo mata akan goshi, fuska ɗauke da murmushin da ke ɗora wuta a zuciyar Tasleem. Ta ce da ita:
"Na fi karfin zuciyoyin ku gaba ɗaya, Ke ki ke taya ƴar uwarki faɗa akan mijinta, ni kuma na riga da na mallake shi. Na shiga ransa yanda bazai iya manta ni a rayuwar sa ba...."
Tasleem ta furta
“Ukkk!” sannan ta nufi Catrina da niyyar fin karfin ta, suka kama juna da faɗa mai zafi, tana jan gashinta, tana hura hanci cikin fushi tana faɗin
"Sai kin fice daga gidan nan da kanki!"
Catrina kuma ta riƙe rigar Tasleem tana janta itama, har suka faɗi saman kujerar falo nan kujerar ta dungura da su, faɗa suke na gaske, Catrina ganin Tasleem tana shirin fin ƙarfinta yasa ta kafa haƙwaranta akan breast ɗin Tasleem ta garzaya mata ciwo, ba shiri Tasleem ta sau wata iriyar ƙara mai rikitarwa, sai da falon ya ɗau sautin....
Falon ya koma kamar wurin faɗan aljanu.
Amaar da Abeesh jin ƙarar ihu yasa suka shigo falon a guje.
Amaar ya damƙe Tasleem yana kokarin jan ta gefe, yana rarrashi ta...
Tasleem tana kuka tana faɗin "wallahi mayya ce yau saina yi maganin ta, ka barni na zubar mata da haƙora....."
Amaar cikin tashin hankali yake faɗin
“Tasleem! Dan Allah ki bari! Wannan ba hanya bace. Ki duba kanki fa!”
Abeesh kuwa ya ja Catrina yana faɗin:
“Catrina! Enough! Ki dakata! Wannan ba shine nake so ba.”
Tasleem ƙwace wa tayi daga hannun Amaar ta sake nufo Catrina. Gaba ɗaya gidan ya cika da hayaniya da tashin hankali...
Daƙer Amaar ya sake riƙo ta tare da rungumar ta sosai....
A cikin wannan rikici, sai ga Nasreen ta fito daga kitchen hannunta rike da wuƙa mai kaifi. Idonta jajir, zuciyarta na tafasa kamar ruwan zãfi. Ta nufi Catrina kai tsaye da nufin caka mata tana faɗin:
“Kina son kashe mun aure ko? Zaki kashe rayuwata ko? Wallahi sai na nuna miki ni matarsa ce ba ke ba!”
Abeesh da ya hangota da wuƙar ya yi saurin tarar ta da ƙarfi ya damƙe hannunta yana faɗin:
“NASREEN! Ki sauƙe wannan wuƙar! Wannan faɗa ba mafita bace. Kar ki zama mai laifi akan soyayyar da ke rikitar da kowa.”
Nasreen fashe wa tayi da kuka tana ƙoƙarin ƙwace wa tana nuna Catrina da wuƙar, tana faɗin
"Wallahi yau babu abinda zai hana na kashe ta, sai na rabata da rayuwar ta...."
Amaar ya nufi wurin da Abeesh yake riƙe da Nasreen yana faɗin
"Kin ga Nasreen ki kwantar da hankalin ki, ke ce mai hankalin cikin ku ki saurara...."
Kafin Amaar ya rufe baki Tasleem ta tafi da gudu ta damƙi wuyan Catrina tare da girban sawayen ta sai yaraf a ƙasi, Tasleem danne wuyan ta tayi sosai a ƙasin carpet tana faɗin:
"Nasreen zo ki huda cikin ta da wuƙar nan, umarni nake baki yanzu...."
Ai kafin a ankara itama Nasreen ta nufi yanda suke da mungun gudu tare da ɗaga wuƙar zata caka wa Catrina a ciki, Abeesh ya yi wani irin sufa ya cabki hannun Nasreen kafin ta kai ƙasi, fizgar wuƙar ya yi tare da rungumar ta sosai yana faɗin
"Please! Please!! Please!!! NASREEN don't do that...."
Nasreen fashe wa tayi da matsanancin kuka..... tana faɗin
“Ni ce matarka, amma ka zaɓi kwana da ita! Kayi min adalci kenam?! Me na maka, Abeesh?!”
Kwantar da kanta ya yi akan ƙirjin sa yana rarrashin ta...
Ita kuma Tasleem Amaar ne ya yi mata ɗaukan luɗa daga saman cikin Catrina yanda take ta naushin ta...
Catrina tashi tayi a ruɗe ta ɗan ja baya da murmushi mai wuyar fassara. Tasleem na gefe tana jan numfashi da ƙyar, yayin da Amaar ke rarrashinta...
Abul mahaifin su Amaar da Abeesh wanda yake zaune a can ɗakin sa jin hayaniya a falo yasa ya fito falo yana faɗin
"me yake faruwa anan?..."
Tasleem ce zata faɗa wa Abul abinda yake faruwa sai Nasreen ta katse ta da cewa
"dan Allah Tasleem kar ki sanar.."
Tasleem ta ce
"wallahi sai na faɗi abinda ke faruwa"
Amaar ya ce "Nima ban san meke faruwa ba haka na tarar dasu suna faɗa amma Tasleem sanar mana abinda yake faruwa..."
Tasleem ce ta tsaya a gaban kowa, ta ce da ƙwarin guiwa:
"Catrina ce take soyayya da Abeesh, tana shiga ɗakin Abeesh dare da rana, yanzu ma suna kwana tare kamar miji da mata, kuma a gaban Nasreen duk hakan yake faruwa, Wannan ai wulakanci ne ba ƙauna ba!"
Lokaci guda fuskar Amaar ta canza, Zuciyarsa ba ƙaramin ɓaci tayi, bai ce uffan ba sai kawai ya nufi gaban Abeesh cikin ɓacin rai ya zabga masa mari mai ƙarfi wanda kowa yaji ƙarar sa a dakin, yana faɗin:
"Kai munafuki ne?! Ka ɓata tarbiyyar ka! Ka ɓata sunan gidanmu! Wace irin rana ce wannan da zaka bar matarka ta sunnah kana kwana da wata macen banza?!"....
Abeesh ya yi shiru, yana kallon ƙasi, hannu a dafe akan kunci bai iya kallon kowa ba...
Catrina taji matuƙar ciwo a ranta jin marin da aka yi wa Abeesh, jure wa kawai take...
Itama Nasreen sai da ta rufe idanuwanta sosai tana jin zogi a cikin zuciyar ta, bata so wannan al'amarin ya faru ba...
Abul juya wa ya yi yana kallo mai ɗauke da ɓacin rai da mamaki yana duban Catrina. Cikin murya mai nauyi ya ce:
"Ke... baƙar kuliya ce! Mai bakar Aniya!"
Catrina ta kafe shi da ido, ta ɗan saki murmushi, kamar wata jaruma mai raina kowa. Amma bata ce uffan ba. Sai dai cikin zuciya ta tasan cewa Abul ya gane ta! Ya gane asalin ta — Sarauniyar Duhu.
Amma Abul bai faɗi wannan gaskiyar ba, domin yasan dole wata rana asirinta zai tonu, yasan ko zai faɗa musu cewa Catrina ba mutum ba ce, akwai wasu da ba zasu iya jurewa ba. Ya sake juyowa ya ƙara daka wa Abeesh tsawa tare da faɗin
"Ka raina mutuncina kenam? Abeesh.... haƙiƙa na raina tarbiyyar ka, Ka ɗora ma kanka laifi da ba zaka iya ɗauka ba. Ka bar matar aure ka rungumi wata iska..."
---
🔥 Cikin Zuciyar Catrina:
A lokacin da suke zagin ta da fushi da kuma faɗa, Catrina ta rufe idonta, ta furta a zuciyarta:
"Kun yi faɗa da ni amma Sai dai... ku sani, ban zo da niyyar ɗaukar mijin wata ba, na dawo ne don na ɗauki haske daga gare ku."...
Tana kammala maganar zuci ta bar falon tare da nufan ɗakin ta....
Abul ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, a fusace ya bar falon yana mai yin fushi da Abeesh...
A wannan ranar wuni akayi cikin ɓacin rai...
---
A ɗakin Abeesh...
Nasreen na zaune gefen gado, kanta a ƙasa, tana kuka kamar ruwan sama. Abeesh yana tsaye kusa da taga, yana kallon sararin sama. Yayi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce da muryar dake nuna cewa shi ma zuciyarsa cike take:
“Na kasa control zuciyata Nasreen... Ki yarda da ni. Ban taɓa so in cutar da ke ba. Amma bazan iya fitar da Catrina daga zuciyata ba.”
Nasreen ta ɗago kai, idonta jajir ta ce:
“Ka ƙi ka zaɓe ni Abeesh. Na fahimta. Amma bari na faɗa maka abu guda... Duk da cewa zuciyar ka tana tare da ita, ni ce matarka a bisa doka da addini. Ni ce kake da alhaki akai. Kuma wallahi, zan tsaya tsayin daka akan aurena.”
Abeesh ya juyo yana kallonta cikin tsananin damuwa ya ce:
“Na san haka. Amma Catrina... kamar akwai wani abu a tsakanin mu da bana iya bayyana wa. In na kalleta, zuciyata na bugawa...”
“Zuciyar da ta buga shin tana manta ƙauna?” Nasreen ta katse shi, hawaye na gangarowa. “To ka zauna da ita. Amma ka sani, bazan bar aurena haka nan ba.”
---
Washegari da safe...
Falonsu ya lafa, amma ba a cire kayan da suka tarwatse ba. Tasleem ta fito daga ɗakinta cikin riga mai laushi da ɗan gashi a rataye akan wuyanta, tana fitowa ta iske Catrina zaune kan kujera tana shan shayi, cikin fara’a kamar ba ita aka kusan cakawa wuƙa jiya ba.
Tasleem ta tsaya cak tana kallonta, sannan ta ce da ƙarfin zuciya:
“Ke fa baƙuwar da aka ba wurin zama ce. Amma ina sane da niyyarki... Soyayya dai za ta fito da gaskiyar ta, kuma wata rana za a gane wacece ke, Catrina...”
Catrina ta ɗan saki murmushi, tana ɗora kofi a leɓenta sannan ta ce
“Idan zuciyar mutum ta amshi abu, ko wane hali yake ciki, sai ya rasa kwanciyar hankali. Bani ce na tilasta masa soyayya ba. Shi ne yazo gare ni...”
Kafin Tasleem ta bata amsa sai ga Asmeen ta shigo, cikin farin ciki da annashuwa —kamar wata sabuwar wata...
Tasleem ta kalleta da mamaki ta ce:
“Asmeen... me nake gani haka? ke ce yau a part ɗin nan? yau Ango ya barki kenam tin Aure rabon ki danan, ga shi har mun shiga sati na biyu...”
Asmeen tana dariya ta ce
"wallahi nazo ziyara ne, nayi farin cikin ganin ki sosai...."
Tasleem ta ce "Asmeen ya dai nake ganin ki cikin farin ciki kodai yanzu ba wata matsala tsakanin ki da Shaprees?..."
Asmeen rungumar Tasleem ta yi tare da faɗin
"yanzu mijina bashi da wata matsala, ya zamo tamkar waliyi, shiyasa kika ganni cikin farin ciki, mu da duhu har abada munyi hannun riga...."
Tasleem cikin farin ciki ta ce "Alhamdulillah Ƴar uwata haka nake son ji..."
Catrina tana kallo Asmeen da mamaki, amma bata ce komai ba. Amma wannan haske da ke dawowa cikin Asmeen, wani sabon babi ne da zai iya karya ƙa’idar da Madam Nablah ta kafa.
---
Kiyi shiri...
Madam Nablah na gab da dawowa daga tafiyarta. Kuma za ta dawo ta tarar da gidan nata yana karkarwa da rudani—soyayya da ƙiyayya, barazana da mafita suna yaki a cikin gida guda.
Catrina na zaune tana maganar zuci....
Suna cikin wannan halin sai ga Nasreen ta shigo falo, ganin Asmeen yasa ta tafo da gudu suka rungumi juna, haka suke farin cikin ganin juna...
Su uku sun haɗa kayuwansu guda suna farin cikin kasance da juna... Yayin da
Catrina na zaune cikin izza kamar itace uwar gidan. tana gyara yatsun kafarta da reza tare da tauna cingam tana ƙararas...
Su ma duk zama suka yi...a falon.
Nasreen tana kallon Catrina cikin kishi da zafi kamar zuciyarta na tafasa da ruwan zãfi.
Asmeen tana kallon su cikin fara'a, tana riƙe da wani ƙaramin ledar kayan zaƙi domin tasan ƴan uwanta suna matuƙar son kayan zaƙi na ƙwaɗayi...
Ta ce:
“Tasleem! Nasreen yau na ce bari in zagaya na gaishe ku… Amma… kamar sabuwar fuska nake gani…”
ta kalli Catrina sannan ta dawo da kallon ta ga Tasleem da Nasreen ta kuma cewa
“Wacece wannan baƙuwa muka yi ne? Ban taɓa ganinta ba.”...
Tasleem ta lumshe idonta, zuciyarta na ƙoƙarin kwantar da kai, kafin ta ɗan jinjina kai sannan ta ce:
“Ƴar baƙunci ce daga can waje. Tazo gaisuwa ne ga Momy, sai ta tsaya.”...
Catrina ta saki murmushin da babu laifi amma akwai shashanci a ciki ta ce:
“Ni kuwa sai dai in ce nazo sadaukar da zuciya… Gidan da na samu kulawa da kwanciyar hankali. Ina jin kamar nan ne nawa gidan.”...
Asmeen ta ƙara kallonta, cikin nazari da tsananin shakku, tace:
“Kwanciyar hankali da kulawa…? Hmm, an ci sa’a. Sai dai kamar kin fi dacewa da ɗakin baƙi, ko ba haka ba?”
Catrina ta ɗan kwashe da dariya, tana ɗan karkada gashinta ta ce:
“Wani lokacin zuciya ta fi gini zama gida, Asmeen…”
Nasreen ta miƙe tsaye, tana tafa hannunta kamar wacce ta gaji tare da faɗin:
“Kina nufin zuciyar mijin wasu? Tunda ai kin sami sabuwar matsuguni, ko ba haka ba?”
Asmeen ta kallesu duka biyu cikin mamaki, bata fahimci inda zancen ya dosa ba. Amma kafin tayi magana, sai wayar Catrina ta yi ƙara. Ta ɗauka, ta yi wata hira da ba a ji ba, sannan ta miƙe kamar wacce zata bar falon.
Ta ce da su .
“Zan wuce yanzu. Sai an jima...”
Ta juya cikin izzarta, tana tafiya kamar sarauniya, gashinta yana kyalli kamar zinariya. Bayan ta fita, Asmeen ta juya ga Tasleem cikin damuwa tana kallon Nasreen da Tasleem ta ce
“ Ku gaya min gaskiya, wacece wannan? Kuma me take nema a gidan nan?”
Nasreen ta ja numfashi, idonta na ƙoƙarin cikowa da ƙwalla ta ce:
“Ta karɓe zuciyar Abeesh, Asmeen. ita ɗin kamar mayya ce… Ba a san asalinta ba, ba a san inda ta fito ba, amma ya kasa rabuwa da ita.”...
Asmeen ta ɗauki salati, ta dafe goshi tare da faɗin
“Innalillahi... yanzu ita ce wannan ke jefa ki Nasreen cikin damuwa? Kuma Momy bata san komai ba?”...
Tasleem ta girgiza kai sannan ta ce:
“Momy tayi tafiya, kuma kamar da gangan take gujewa auren mu ni da Amaar. Ba komai Asmeen, komai sai dai muyi addu’a… Amma ke fa? Shaprees yana kula dake kuwa?”
Asmeen ta yi shiru na ɗan lokaci, sai kuma ta ce da sanyi:
“E… Yana kokari. Kullum sai ya tambayi yadda nake ji, yana kula da Ni, Na fara jin kwanciyar hankali tare da shi, duk da zuciyata bata gama buɗewa ba.”
Tasleem ta riƙo hannunta cikin nata, tace:
“Ina fatan ke zaki samu farin ciki, Asmeen. mu cigaba da addu'a sauƙi na nan tafe Insha Allahu..."
Suka rungume juna a hankali. Amma a bayan labulen falon, wata inuwa ce ta ke kallon su — Catrina — ta dawo, ba tare da su ankara ba. Idonta ya ƙanƙance, kamar wacce ta ji wani abu da bai mata daɗi ba.
“Soyayya ba ta da sauƙi ...”
ta furta da siririyar murya.
“...amma bazan bar shi ba. Ko da kuwa sai nayi amfani da zuciyarsa gaba ɗaya...”
Bayan Sallar Isha’i
Shapreen ne yazo ya ɗauki Asmeen suka tafi can part ɗin su...
Daren ya zo da natsuwa,
Kowa ya shiga sashi-sashinsa,
Amma zuciyar Nasreen cike da raɗaɗi kamar zuciyar mace da take numfashi a cikin wuta.
Abeesh yana ɗakin Catrina. A cewar shi, “zai je ɗan gaishe da ita ne” — amma Nasreen ta san cewa wannan ƙarairayi ne, domin sau nawa yanzu da take tsintar sa a ɗakin Catrina cikin dare?
Ta zauna a gefen gado tana danna wayarta amma kallo ɗaya zaka mata kasan ba duba wayar take ba — zuciyarta na ambaliya da hawaye ne kawai.
Sai taji numfashinta yana ƙoƙarin ɗagewa....
Tasleem ne ta shigo ɗakin cikin gajiya, tana ɗauke da wata ruwan zafi da lemon zaki. Ganin Nasreen a ɗakin ta cikin damuwa yasa ta ajiye kofin a gefe saman frig sannan ta zauna kusa da ita tana faɗin
"Nasreen, wallahi ni ba zan ci gaba da kallon
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 34