Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da farfatsin wuta, Cikin sassanyar murya ta furta "Shaprees..." Kafin ta ankara har ya damƙo hannunta suka ɓace a tare, basu sauƙa a ko ina ba sai a gaban Madam Nablah wacce take zaune a kan katafaren kujerar ta na sarauta wanda sai ka taka matakala kafin ka iso kan kujerar dake sama, Madam Nablah ganinsu yasa ta tintsire da wata irin mahaukaciyar dariya.. Sophia idonta akan Madam Nablah ta ce "daman nasan aikin ki ne, shin lokacin rabani da rayuwata ce ya yi?..." Madam Nablah girgiza kai tayi sannan ta ce "bazan barki kiyi mutuwar sauƙi ba, sai naga yanda Ruhinki zai wulaƙanta a cikin fada ta, sai na nuna miki yanda ƙarfin ikona yake, sai na shafe labarinki a doron ƙasar nan, zan ɓatar da gangan jikin ki yanda babu wanda ya isa ya san yanda kike, Ruhinki kuma haka zata rinƙa zagaye cikin hayaƙin uƙuba ta..." Sophia cike da jarumta ta ce "haka kuma Ruhina saita hanaki sukuni, sai ta hanaki bacci, Ruhina da hannunta zata sheƙe ki, a shirye nake da ganin duk wani ƙalubalen ki Shaiɗaniyar Uwa..." A fusace Madam Nablah ta fitar da wani haske daga cikin tafin hannunta tare da wurga mata shi, da wannan hasken Madam Nablah ta ɗago ta sama tana juyar da ita, sai da ta gama wahalar da ita kafin ta fara raba Ruhinta da gangan jikinta, daga sama gangan jikin Sophia ta faɗo ƙasi yaraf sai Ruhinta da Madam Nablah ta sauƙar da ita ƙasi da wannan hasken hannunta, Ruhi tana tsaye Madam Nablah ta ce "yau zan nuna miki cewa Devil Mom ba sa'ar kowa bace, ki biyo ni..." Madam Nablah ce tayi gaba sai Ruhi da take binta a baya, sai da suka yi tafiya mai ɗan nisa a cikin fadar ta kafin ta buɗe wani ƙofa mai bala'in girma tana buɗewa sai ga wani irin iska mai ƙarfin gaske ya ɗauke Ruhin Sophia zuwa ciki, ciki kuwa wani irin haske ne ga hayaƙi kamar gajimare baka iya ganin abinda yake ciki tsabar tsafin da Madam Nablah tayi a wurin, ana shiga da Ruhin Sophia ƙofar ta rufu da kanta, murmushi kawai Madam Nablah tayi sannan ta juya... Shaprees yana dawowa hayyacinsa ba abinda ya fara tarar wa sai gangan jikin Sophia dake yashe a ƙasi, a ruɗe ya yo kanta yana ƙiran sunan ta, "Sophia! Sophia!! Sophia!!! ki tashi dan Allah kar ki mutu ki barni dan Allah..." Madam Nablah ce ta bayyano lokaci guda tana faɗin "ka kwantar da hankalinka na kilacce maka matar ka, wannan gangar jikin ne babu amfanin da zata yi maka..." tana kaiwa nan ta ɗauki jikin Sophia ta hanyar iska ba tare da tasa hannunta ba ta buɗe wani akwati ta jefata a ciki tare da rufe ta sannan ta tura ta cikin ƙasin ƙasin ruwa... Shaprees haka yake kuka yana faɗin "Matata! Matata shin mezan ce wa iyayenta da suka bani amanar ta? na sanar musu cewa gobe Sophia zata koma Nigeria why?..." Madam Nablah zama tayi akan kujerar ta tana faɗin "kai kana cikin Secret society Amma sam babu jarumta a tattare da kai, duk abinda na buƙata sai na same shi, saboda haka yasa hatta mijina ban bar shi ba, sai da jininsa ƙarfin ikona ya ƙara wanzuwa sannan tsafina ya ƙaru haka yasa na yi sadaukarwa da jinin mijina kuma na jure hakan, why you bazakayi hakan ba, daman matar ka ce matsalar ka yanzu babu ita zaka iya gudanar da aikin ka, yanzu inaso ka shanye mun jinin dake ajiye a gefenka Shaprees..." Kamar yanda ta ce haka ya ɗauki cup zai kai bakinsa yaji kansa yayi wani irin sarawa lokaci guda ya yanki jiki ya faɗi, bai ƙara sanin halin da yake ciki ba... NEXT NEXT NEXT.... New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 3 to 4 Shaprees bai tsinci kansa a ko ina ba sai akan katafaren gadonsa, farfaɗowarsa ke da wuya maimakon ya tarar da matar sa Sophia sai yayi ido huɗu da Madam Nablah zaune akan kujerar ɗakin tana jiran farfaɗowarsa, a zabure ya tashi zaune yana ambatar sunan Sophia, haka ya tashi a gurguje ya je gaban Madam Nablah yana faɗin "Please where is my wife? kar ki ce ta mutu dan Allah..." Dogon numfashi Madam Nablah ta sauƙar tare da faɗin "So sorry Shaprees a wannan lokacin ka rasa matar ka domin ni ba'a ja dani kasan da haka, amma kar ka damu zan baka kyautar wacce zata maye maka gurbin Sophia, domin ina matuƙar ji da kai hakan yasa bana iya cutar da kai duk da tarin laifukan da kake mu, kyautar da zan baka shine abu mafi soyuwa a rayuwa ta, duk duniya babu abinda nake so sama da abinda zanyi maka kyautar sa..." Shapris leɓɓensa na kakkarwa ya furta "wani abu ne?..." Madam Nablah tasan murmushi sannan ta ce "Ɗaya daga cikin triplets daughter na, Ƴan mata uku sune ɓangarorin jikina, to na mallaka maka ɗaya daga cikin su duniya da lahira kuma zata haifa maka kyawawan ƴaƴan da kake so..." Girgiza kai Shaprees ya yi sannan ya ce "a duniyan nan babu macen da zata kai Sophia a wuri na, kinyi kuskuren cutar mun da ita Devil Mom, domin ita ɗin rayuwata ce..." Madam Nablah ta ce "ga shi lokaci guda na sauya rayuwarka Shaprees, yanzu sabuwar rayuwa zaka cigaba da gudanar wa..." Tana kammalawa ta miƙe tare da faɗin "daga nan airport zan wuce domin a yau zan koma Nigeria..." Bata jira wata amsa ba tayi ficewar ta, Shaprees ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba ganin yanda ake juyar da kwakwalwarsa, haka ya cije lips ɗinsa na ƙasi acikin ransa yake furta "Madam Nablah a yanzu wasan zai fara, idan kin san wani baki san wani ba, kin taɓo mun tabon da bazan taɓa warkewa ba, kin rusa mun farin cikina, kin rabani da rayuwata, bazan barki ba sai na ɗau fansa akan ɗiyarki da kika mallaka mun, zan nuna miki waye Shaprees Shattima...." Haka ya gama maganganu a cikin zuciyarsa idanuwa duk sun yi jawurrr, A lokacin ya ƙira waya ya sanar cewa yana buƙatar yin transfer zuwa Nigeria. Domin yasan duk abinda Madam Nablah tasa a gaba sai ta kai ƙarshen shi, tinda har ya kasa ceto rayuwar Sophia to yasan ya rasa ta har abada kenam, shiyasa zai yanke hukuncin komawa Nigeria sai dai abu ɗaya yake shakka shine sanar wa iyayen Sophia cewa ya rasa ɗiyarsu... Haka yake ta wannan tunanin... *NIGERIA...* Wasu maka-makan motoci ne guda biyar suka yi parking a harabar wani makeken gida mai upstairs hawa huɗu, bodyguards ne a tsatstsaye sun fi goma kowa yana riƙe da bindigar sa wanda ya kasance sune masu gadin gidan, wani daga ciki ne ya buɗe murfin mota wanda a ciki wata miskilalliyar mata ne mai ɗagun kai haɗe da girman kai, ƙafarta ɗaya ta soma sauƙo da shi wanda yake ɗauke da wani irin takalmi mai tsinin gaske, a hankali ta sauƙo gaba ɗaya a daidai lokacin da wasu ƴan mata su uku masu kamanni ɗaya suka nufo wurin parking, haka suka jeru tsayinsu ɗaya, kamanni kuwa kamar mutum ɗaya, kyau kamar su suka halicci kansu ga farin fata kamar ƴaƴan turawa, amma sai dai kowacce da kalar zuciyar ta. Madam Nablah ce ta fito tana kallon su ɗaya bayan ɗaya daga bisani ta farkon tazo dab da Madam Nablah sannan ta rungume ta tana faɗin "your welcome Mom..." Madam Nablah murmushi tasau tare da shafa gefen fuskarta ta ce "my big daughter Tasleem, god bless you...." Jinjina kai Tasleem tayi sannan ta koma yanda take ta tsaya sai kuma ta biyu wato Nasreen itama rungumar mahaifiyarsu tayi sannan ta ce "your welcome Mom..." Madam Nablah sumbatar ta tayi akan goshi sannan ta ce " I Appreciate you my lovely second daughter...." Sai ga ta ukun itama ta zo ta rungumi mamanta tana faɗin "Mom I really missed you..." Madam Nablah itama rungumar ta tayi sosai a jikinta tana faɗin "Ohhhh so sorry my heart partner Asmeen ..." Sannan ta kallesu gaba ɗaya daga sama har ƙasa ko wacce dressing ɗin ta ba ƙaramin yi mata kyau yayi ba, kowa da kalar dressing ɗin ta... Cikin nuna farin cikin ganin ƴan matan ƴaƴanta ta ce "my triplets daughter I missed you..." Su ma duk murmushi suka sake cikin jin daɗi da haka duk suka wuce ciki, a babban falo Madam Nablah ta tarar da wani matashin saurayi kyakkyawa mai ji da kansa yana zaune yana fuskantar television, yana ganin Madam Nablah ya yi saurin kawar da kansa gefe domin ko kallonta ma baya son yi, haka ya yi kamar bai ganta ba. Madam Nablah tsaya kallon sa tayi ga triplets a ta bayanta su ma suna tsatstsaye, murmushi tayi sannan ta ɗauki remove ta kashe tv idonta akan matashin ta ce "Abeesh shin baka ga shigowa ta bane?..." Miƙewa yayi tare da wurga mata wani irin kallo sannan ya ja dogon tsaki yabar falon, kai tsaye upstairs ya haura yanda room ɗinsa yake. Cikin ɓacin rai Madam Nablah ta kawar da idanuwanta daga kallon hanyar da yabi itama haura wani upstairs tayi ta nufi room ɗin ta ba tare da ta furta komai ba... Triplets duk kallon juna suka shiga yi ko wacce da saƙe-saƙen da take a ranta daga bisani su ma suka wuce room ɗin su dake can saman upstairs na ƙarshe hawa na huɗu, babban room ɗin su ne wanda manyan gado uku ne a ciki, ko wacce da gadonta, sai other room wanda ya kasance nan ne wurin kayayyakin sakawar su wardrobe da mirror sai wasu ƙofofi guda biyu bathroom and toilet room... Nasreen zama tayi a bakin gadonta hankali a tashe kamar zata yi kuka ta zabga tagumi bisa alamu kamar ta tafi dogon tunani, Asmeen ce ta zauna kusa da ita tare da dafa kafaɗarta ta ce "Nasreen!.." shiru bata amsa mata ba still ta sake ƙiran sunan "Nasreen!!..." Tasleem wacce ta gaba cire kayan jikinta ta zauna daga ita sai short jeans da singlet ko kallon yanda suke bata yi ba ta nemi gadonta ta kwanta tare da lalumar wani littafin English... Asmeen da ƙarfi ta sake ambatar sunan Nasreen a saitin kunnenta, a firgice Nasreen ta juyo tana furta "Na'am ABEESH...." Asmeen zaro manya-manyan idanuwanta tayi tare da faɗin "Abeesh kumaaaa?...." Tasleem wacce ta fara karanta littafi a ruɗe itama ta juyo tana kallon Nasreen, Aasmeen wacce take kusa da Nasreen dafa kafaɗarta tayi cike da tausayawa ta ce "Nasreen wai me yake damunki haka? Abeesh fa naji kin furta, mutumin da yake zaman ƙiyayya da mahaifiyar mu, kinaga ko zama baya yi a wurin da take amma kin ɗauki damuwa kin ɗora masa, meye matsalar ki ko dai son sa kike?..." Nasreen da sauri ta juyo tana kallon Aasmeen haɗe da girgiza mata kai tana faɗin "ko kaɗan wallahi, indai so na soyayya ne bana jinsa a raina amma ina son sa a matsayin ɗan uwantaka domin shi ɗin jinin mu ne, kin san da cewa mahaifinsa da mahaifin mu marigayi uwa ɗaya uba ɗaya suke, bashi da kowa bayan mu idan bamu ja shi a jiki ba ina zai shiga? ƙiyayyarshi da mahaifiyar mu kuma Allah ne kaɗai yabar wa kansa sani, bamu san me ya haɗa su ba haka muka tashi tin yarinta muka gan su a haka, na farko bamu isa mu tuntuɓi Mom akan abinda ya faru ita da Abeesh ba kuma shima Abeesh da zaran an kawo masa maganar Mom barin wurin yake baya tsayawa ya saurare mu, abun yana damu na wallahi...." Tasleem dogon tsaki ta ja sannan ta ce "meye to abin damuwa bayan haka kika tashi ki ka gansu, idan baki cire wannan damuwar ba wata rana sai dai a samu gawar ki, ni ban yadda dake ba son sa kike..." Nasreen murmushi tayi sannan ta ce "kin dai san inada wanda nake matuƙar ƙaun..." bata ƙarisa fitar da maganar ba Aasmeen tayi saurin toshe mata baki da hannu tana girgiza mata kai... Nasreen cikin fushi ta zamar da hannun Aasmeen daga kan bakinta ta miƙe tsaye tana faɗin "wai har yaushe za'a daina hukunta mu haka ne? nifa na gaji so ake mu mutu babu Aure ne? mun kai minzalin fara soyayya amma kullum a cikin daƙushe mana farin ciki ake, babu abinda muka nema muka rasa a duniyan nan sai abu ɗaya wato farin cikin soyayya, har yanzu bamu san daɗin soyayya ba, kullum a cikin ɓoye soyayya muke saboda kar a cutar da wanda muke so haba dan Allah...." lokaci guda Nasreen ta fashe da matsananci kuka mai azabtar da zuciya... Aasmeen itama hawayen take ta miƙe tsaye tare da dafa kafaɗarta tana faɗin "Nasreen idan bamu ɓoye soyayyar mu ba shin ya zamuyi? kina ga fa duk wanda muka fara soyayya da shi a cikin kwana ɗaya sai an samu gawarsa a jikin gawarsa kuma sai an samu takarda mai ɗauke da rubutun sunayen mu gaba ɗaya, Tasleem, Nasreen, Aasmeen duk a rubuce kuma hukuma babu abinda zata iya yi akan mu duk da bamu muke yin kisan ba, nasan a ɓangaren ki Nasreen an samu gawar samari kusan 50 waɗanda suka baki saƙon soyayya, haka nima a ɓangarena an samu gawar samari waɗanda suka ce suna sona da yawa, Tasleem ce kawai take yiwa samari kwarjini haɗe da yi musu wulaƙanci amma duk da hakan har da sunanta a rubuce a jikin takardar da aka samu a jikin ko wani gawa indai ya furta mana kalmar soyayya, Nasreen ba wai soyayyar ce matsalar mu ba, babban matsalar mu shine kashe waɗanda zamu yi soyayya dasu, kashe waɗanda basu ji ba basu gani ba duk a saboda mu...." Nasreen share hawayen fuskar ta tayi tana fuskantar Aasmeen ta ce "anya kuwa bamu da baƙaƙen aljanu?..." Aasmeen ta ce "i think so but bakya tunanin Ayub student ɗin school ɗin mu da ku ka fara soyayya dashi akan abinda zai faru da shi?..." Nasreen ta ce "Insha Allahu babu abinda zai faru dashi domin na tsayar da addu'a ta sosai akan sa, kinga sauran duk basa wuce kwana ɗaya ake kashe su shi kuma Ayub yau satin mu guda dashi, shiyasa nake da hope akan sa...." Aasmeen jinjina kai tayi sannan ta ce "amma naga ƙoƙarin Ayub da har yake da ƙwarin gwiwar zuwa wurin ki alhalin yanzu kam school kowa gudun mu yake, ba wanda yake son tsayawa a kusa damu balle har soyayya, har sun sa mana suna Mayu, nidai a yanzu bazan ƙara karɓan soyayyan kowa ba domin bazanyi sanadin mutuwar Ɗan mutane ba..." Nasreen sauƙe numfashi tayi sannan ta kalli wurin da Tasleem take sai faman karatun ta take, Ta ce "Tasleem ke babu abinda zaki ce a wannan al'amarin ne?..." Tasleem ɗagowa tayi fuska ba annuri ta ce "kin taɓa jin na tsoma baki na a cikin zancen soyayyar ku? ko kun fiso nima a rinƙa rubuta mun alhakin ɗaukan rai? kun san abinda yake faruwa damu amma kun kasa fahimtar komai, ta sanadiyarku ake hallaka bayin Allah amma ku bakuda imanin da zaku dakatar...." Nasreen ta katseta da cewa "inda munada halin dakatarwa da tin yaushe mun dakatar..." Aasmeen ta ce "taya zamu dakatar alhalin bamu san lokacin da abun yake faruwa sai dai mu ji labari..." Cikin fushi Tasleem ta ce "ehen zaku iya dakatarwa ta hanyar daina soyayya da kowa, hakan ne zai ceci waɗanda ake hallakarwa, soyayyar banza da wofi dole sai anyi ta ne? kuma kunsan in kunyi ta ma ba samun soyayyar ku ke ba sai jawa kan ku zargi ko kuma jawa kan mu gaba ɗaya tinda nima ba'a barni ba, Ni da bana kula kowa babu ruwana da kowa amma sai an samu sunana a rubuce a takardar gawar samari ku, ni yanzu akwai mai zarrah da ikon da ya isa ya tuntuɓeni da maganar soyayya ne? duk da ba kowa yake gane kamannin mu ba amma ni na fita daban saboda mata ma basu ishe ni kallo ba bare maza...." Nasreen ta ce "Uhmmm Tasleem kenam kin manta ne, amma lokacin da muke primary duk cikin mu kece kawai mai shiga shauƙin soyayya, ke da Amaar Junaid bakwa rabuwa kullum kuna tare duk da a lokacin abokai za'a ƙira ku domin baku kai minzalin Aure ba duk da a lokacin shi yana Jss 3, nasan in badan kin rasa shi ba da yanzu kam sai dai a ƙira ku da Julleit and Romeo tsabar soyayya...." Nasreen da Aasmeen tafa hannayensu suka yi suna kwashewa da dariya, sannan suka juyo da ganinsu kan Tasleem, abinda suka gani ne ya tayar musu da hankali lokaci guda, ganin Tasleem a wani irin hali ta riƙe kanta sosai da hannu biyu tana faman shiɗewa, ƙwaƙwalwarta ne yake wani irin juyawa yana hargitse wa gaba ɗaya ta fita hayyacinta lips ɗinta ne yake kakkarwa a hankali take furta "Mom! Mom!! Mom!!! Mom!!!!..." hannunta riƙe da kanta sai juyi

Chapter 2 of 34