Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Nasreen addu'o'i take ta tofa mata ko zogin zai ragu mata, suna cikin wannan halin sai ga Madam Nablah ta shigo tana riƙe da wani glass cup, zama tayi a kusa da Tasleem tare da miƙa mata cup ɗin ta ce "kar ɓi ki sha, zaki daina jin ƙunar wutan..." Tasleem karɓa tayi takai bakin ta zata sha, ta tuno da kalar tsafin da Mommyn ta take yi, tana tsoron kar ta mata tsafi a cikin ruwan, a ruɗe ta ɗago kanta ba tare da tasha ruwan ba, ta miƙa wa Madam Nablah cup ɗin ta tashi da gudu ta shige toilet, tana shiga ta kunna shower a kanta, haka ruwa yake ta zuba, ta ɗau tsawon minti 15 a cikin ruwan, fuskar Amaar ne yake ta mata gizo, ta kasa daina tambayar zuciyar ta waye shi ɗin? daga ina yake?...." *NEXT NEXT NEXT.....* New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 17 to 18 Tasleem sai da ta watsa ruwa a jikin ta kafin taji sanyi a ranta... Bayan sati guda da kammala Exam itama Tasleem Mommyn su taje har makarantar tayi magana an dawo da Tasleem ta ƙarasa exam ɗin ta cikin sauƙi... Yau ranar hutu ne duk sun hallaru a falo hatta Abeesh shima a zaune yake a falo yana danna computer sa, Nasreen da Asmeen kuma suna zaune su na kallon plasman, Tasleem kuma tana kan dinning table da cup ɗin Lipton a gaban ta sai pressing phone ɗin ta take, su na cikin wannan yanayin sai suka ji an fara knocking, Asmeen ta bada umarnin shigo wa, turo ƙofa akayi security ya sanar cewa "mai feshin maganin sauro da ƙwari ne ya zo..." Nasreen ta kalli Asmeen ta ce "wa ya turo mai feshi kuma?..." Asmeen kafaɗa ta ɗaga alamar bata saniba itama, suka kalli Tasleem tare da faɗin "Oganniya ke kika turo shi?..." Tasleem sai da ta kurɓi ruwan tea kafin ta basu amsa da cewa "Oganniya tana can room ɗin ta, sai ku je ku tambaye ta..." Security ya ce "Indai babu wanda ya turo shi bari na je na kore shi..." Nasreen ta ce "Ya Abeesh ko kai ka turo shi?..." Abeesh yana zauna ya ce "kin dai san bana shiga shirgin gidan nan..." Nasreen kallon Security tayi sannan ta ce "ka ce ya shigo wata ƙil Mommy ce ta ƙira shi..." Security ya ce "Ok..." sannan ya fice... Bayan wasu mintina sai ga wani matashin mutum ya shigo falon da sallama a bakin sa, duk amsa masa suka yi tare da kallon yanda yake yana sanye da facemark a fuskar sa, kayan jikin sa irin na ƴar feshi yana ɗauke da abun feshi akan kafaɗar sa, Sai ga Madam Nablah itama ta sauƙo daga saman room ɗin ta tana riƙe da key ɗin mota tana son fita unguwa, ganin mutum a tsaye yasa ta tsayawa tana ƙare shi da kallo ta ce "from where?..." Nasreen da Asmeen sun yi mamakin tambayar da mommy tayi masa domin a tunanin su ita ta ƙira shi, Mutumin kuwa yana tsaye zuciyarsa ce take ta faman bugawa domin Madam Nablah ba ƙaramin tsoro ta sanyawa zuciyar sa ba tin yana yaro ƙarami, ƙarfin tsafin da take amfani dashi ya so yafi ƙarfin ƙwaƙwalwar sa, murya ciki-ciki ya ce "am nima turo ni akayi akan nazo nayiwa gidan nan feshin ƙwari..." Madam Nablah ta ce "iya aikin da kake yi kenam?..." Girgiza kai ya yi sannan ya ce "eh a'a ehhh ina gyaran nepa da sauran abubuwa..." Ta ce "okay dalilin da yasa na tambaye ka kenam, daman inaso naji ko kana gyaran wutar nepa inaso zaka gyara mun wutan ɗakunan gidan nan..." Mutumin da yayi covering fuskar sa da face mark ya ce "okay ba damuwa..." Madam Nablah ta kalli yanda Nasreen take zaune ta ce "a ɗakunan gidan nan ina ne wutar ta ɓaci?..." Nasreen ta ce "Mom nepar ɗakin wardrobe ɗin mu ya lalace, sannan na ɗakin Yaya Abeesh nan ma ya lalace sai kitchen, ina tunanin iya su ne...." Madam Nablah kallon mutumin tayi sannan ta ce "yau kayi na feshin gobe kuma sai ka dawo kayi gyaran nepa...." Jinjina kai yayi tare da faɗin "okay Maadam..." Sannan ta miƙi hanyar fita tana faɗin "ku kai shi yanda zai yi aikin feshin, duk wani lungu ya feffeshe wurin..." daga nan tayi ficewar ta. Asmeen ce ta miƙe tana faɗin "muje na nuna maka..." Idonsa kuwa akan Abeesh yanda yake ta daddanna computer, Asmeen tsaya wa tayi a gaban sa tana faɗin "lafiya kuwa? Malam mai feshi ina ta maka magana..." Amaar hannu yasa tare da janye face mark ɗinsa, Asmeen cike da mamaki ta buɗe baki ta ce "Ɗan uwaaaa..." Nasreen jin haka yasa ta ɗago itama ganinsa yasa tayi saurin miƙe wa tana faɗin "laaa kai ne a gidan mu Ɗan uwaa, meya haɗa ka da feshi kuma?..." Da sauri Amaar yayi mata alamar tayi shiru saboda Abeesh yana wurin... Nasreen murmushi tayi tare da faɗin "kar ka damu Ɗan uwa, Ya Abeesh bashi da matsalar komai, kuma baya shiga abinda bai shafe shi ba..." Asmeen tayi saurin cewa "Ɗan uwa wannan shine Yayan mu kuma shine wanda Nasreen zata Aura, ba ruwan sa, shi ɗin salihi ne..." Amaar ya kasa daina sakin ƙayataccen murmushi, idonsa akan Abeesh, Abeesh yana jinsu amma ya kasa ɗagowa, sai gani ya yi an miƙo masa hannu, Abeesh kallon hannun ya yi tare da kai idonsa kan fuskar Amaar sai murmushi yake ta sau masa, shima murmushin yayi tare da miƙa masa hannu suka gaisa. Juyawar da zai yi ya hango Tasleem tana zaune akan kujerar dinning ko kallon yanda suke bata yi ba, nufan yanda take yayi yana zuwa ya ce "hello akwai sauro a yanda kike ne?..." Shiru Tasleem bata bashi amsa ba, tana magana a cikin ranta "lallai wannan ba ƙaramin rainani ya yi ba, haka kawai ina zaune zai wani mun yi bahagon tambaya..." Ba tare da ta bashi amsa ba ta miƙe tana mai jan dogon tsaki zata bar wurin, miƙewar da tayi kwatsam idanuwanta suka sauƙa akan fuskar Amaar, wani irin kallo take masa sama da ƙasa daga bisani tasau murmushi itama tana faɗin "kafin ka kora mun sauron wurin, ka fara wanke dattin jikin ka...." ta ƙarasa maganar tana mai ɗaukan cup ɗin ruwan tea ta ɗaga sama tana tsiyaya masa a tsakiyar kansa, haka ruwan tea yake zubo masa ta fuska har cikin rigar sa, ba abinda ya ji a ransa sai ma ƙara tu sa ta da yayi a cikin zuciyar sa, haka yake ta sakin murmushi a hankali ya furta "ke ɗin ta musamman ce, duk abinda kika yi dai dai ne, kuma fushin ki na ƙara miki kyau sosai da sosai...." Nasreen a cikin ranta take faɗin "tabbas akwai alamar tambaya a tsakanin su..." Asmeen ta ce "Ɗan uwaa daman ƙaunar ƴar uwar mu kake shiyasa a supermarket kake tambayar ta?..." Tasleem fuska a murɗe ta wurga wa Asmeen harara, cikin fushi ta bar wurin, har zata haura saman upstairs taji Amaar ya furta "I love you Tasleem, ina matuƙar ƙaunar ki..." Tasleem tsaya wa tayi tana sauraron sa zuciyar ta ce take ta hargutsuwa, ji tayi bazata iya haƙura ba haka ta juya da gudu ta nufi yanda yake zata shaƙo shi, shi kuwa ganinta yasa ya ware hannayensa biyu tare da faɗin "come and hug me..." Sai da ta zo dab da shi ta ja burki domin ta tuna shi da zaran ta taɓa shi wuta ne yake cin jikin ta, tsaya kallon sa tayi daga bisani ta furta "waye kai?..." Yana murmushi ya ce "I'm your lover..." A tsawace ta ce "shirmen banza, idan baka sanar ko kai waye ba sai na shaƙe ka..." ta kai hannun ta kusan wuyansa kamar zata shaƙe shi ta fasa, girgiza kai tayi tare da juyawa ta nufi upstairs, haurawa tayi ta shige room ɗin su... Amaar kamar zai yi kuka haka yake bin ta da kallo, tsananin tausayinta yake sakamakon abinda ya faru dasu tin basu mallaki hankalin kansu ba. Nasreen ce tayi magana ta ce "Ɗan uwa me yake faruwa ne?..." Murmushi ya yi tare da faɗin "zan miki baya ni da zaran mun nutsu..." Asmeen ta ce "wani bayani zaka yi bayan mun fahimci komai, amma kayi kuskure da ka fara sanar mata kana sonta, da ma ta hannun mu kazo zamu fi jawo maka hankalin ta amma kaga yanzu zata saka ka a jerin maƙiyan ta...." Ya ce "ba komai zan sa ta dawo dani masoyinta na musamman kamar yanda take a cikin zuciya ta..." Asmeen ta ce "ai kuwa idan kayi haka ka cika jarumi na musamman..." Nasreen ta ce "kar ka damu Ɗan uwa ina tare da kai kuma zan taya ka jawo maka hankalin ta..." Amaar murmushi ya yi sannan ya kalli yanda Abeesh yake a zaune ya zuba musu ido yana tunani a ransa cewa "daman saboda masoyiyar sa wannan mutumin ya shigo gidan nan? lallai ya cika jarumi kenam ba mai feshin magani ba ne ?..." Yana cikin wannan tunanin sai gani yayi Amaar ya nufo wurin da yake yana faɗin "Please Boom boy ka taimaka mun kaima wurin shawo mun kanta, ita ɗin rayuwata ce..." Abeesh yamutsa fuskar sa yayi tare da faɗin "who is Boom boy?..." Nasreen hannu tasa ta toshe bakin ta tana ƙoƙarin haɗiye dariyar ta, Asmeen kuwa kwashe wa tayi da dariya tana faɗin "Boom boyyyyy...." Suna cikin rahar su sai ga Tasleem ta sauƙo daga saman upstairs da gudu tana riƙe da ƙaramin bindiga a hannunta, tsayawa tayi ta saita shi tana faɗin "wato ka raina ni koh? har kana da ƙwarin gwiwar shigowa gidan mu ka furta mun soyayya? to yau sai dai a fita da gawar ka domin bazan ƙyale ka ba..." Tana kaiwa nan ta harba bindigar daman already ta kunna kunamar bindigar da sauri Amaar ya sunkuya ƙasi bullet ta wuce ta saman sa sai akan plasman, plasman ne ya dagargaje haka Asmeen ta shige ƙarƙashin dinning tana zunduma ihu, Nasreen kuwa bata san lokacin da tayi tsalle ta faɗa kan Abeesh ba, Abeesh shima rungumar ta ya yi sosai yana tunanin ta yanda bullet zai fara shigan sa domin ba ƙaramin tsorita ya yi ba, itama Nasreen tana rungume dashi sai zabga ihu take tana faɗin "dan Allah azo a taimaka mana, Tasleem ki daina kar tsautsayi yasa ki harbe mu wayyo Allah..." duk toshe kunnuwa suka yi tsabar ƙarar bindiga sai farfasa abubuwan falo ake irin su glass da su flowowi, ta ko ina Tasleem harbi take tana bin Amaar da gudu, duk yanda yayi da gudu haka take binsa tana harbi, har yanzu bata yi nasarar samun sa ba, nufan wurin dinning ya yi Asmeen ta kwarara ihu tana faɗin "dan girman Allah ɗan uwa kar ka yo ta nan ka taimaki rayuwata..." Abeesh riƙo hannun Nasreen yayi tare da ɗagota suka nufi upstairs da gudu, cikin sa'a suka shige bedroom tare da rufe ƙofa... Iya Amaar ne da Tasleem suke ta zarya a falo gaba ɗaya sun yi kaca-kaca da falon, sun farfasa komai na falon, hatta kujeru duk sun fuffuje da harbin bullet, daƙer Amaar ya ɗauki pillow kujeru guda biyu ya yo kan Tasleem da gudu kafin ta ankara ya yi tsalle ya faɗa kanta, gaba ɗaya faɗuwa suka yi akan carpet tana ƙasi shi kuwa yana saman ta ya danne hannayenta da filellikan kujerun da ya ɗauko yanda bazasu ji shocking ba, ya sakata a tsakiyar sa ba tare da ya danne ta ba sai iya hannayenta da ƙarfin sa yanda bazata samu ƙarfin ture shi ba, tana ƙoƙarin tashi amma ta kasa har ƙarfin ta ya ƙare haka tana ji tana gani ta kwanta tana kallon sa fuska a murtuƙe sai sauƙe numfashi take, shima kallon cikin ƙwayar idanuwanta yake tare da sakin murmushi ya furta "saboda tsananin ƙaunata da kike ne yasa zaki kashe ni?..." A fusace ta furta "na tsane ka wallahi ni ka ɗaga ni..." Kan sa yake matso dashi saitin fuskar ta zai sumbace ta, ganin abinda yake shirin yi ne yasa ta fara jujjuyar da kanta tana faɗin "bana so, kar ka sumbace ni, bana so, na gaya maka zan tsine maka albarka, ja'iri kawai..." Numfashin su ne yake haɗe wa yana shirin haɗe musu baki, ta ce "wallahi kana kawo bakin ka zan cije ka..." Sauran kaɗan ya haɗe musu baki ya yi saurin kawar da lips ɗinsa zuwa kan sumar gashin ta, cikin so da ƙauna ya sumbace ta akan gashin ta a hankali gudun kar su ji shocking...." A hankali yake hura mata iskar bakin sa ta ko ina, haka yake bin fuskarta da iskar bakin sa, ita kuwa ganin ba yanda ta iya ne yasa ta lumshe idanuwanta, ji tayi yana mata magana a sai tin kunnen ta a hankali cikin sexy voice "calm down! calm down!! calm down!!!...." Sai da ya fahimci ta samu nutsuwa tukun yayi saurin miƙe wa tare da ɗaukan abubuwan da yazo da su ya fice kafin ta ankara ta tashi.... Asmeen tana ƙarƙashin dinning idonta a kansu baki ya gagara rufuwa tsabar yanayin da suka shiga ne ya sanya ta nishaɗi.... Abeesh tinda suka shiga room ɗin sa suka tsaya a bakin ƙofa Nasreen kuma ta kwantar da kanta akan ƙirjinsa tayi lumuuu, shima kansa ya ɗora akan tsakiyar kanta ya lumshe ido gaba ɗaya basa cikin hayyacin su, Abeesh ƙamshin sumar kan Nasreen ba ƙaramin hargutsa masa ƙwaƙwalwa ya yi ba... Tasleem har zuwa yanzu bata buɗe eyes ɗin ta ba, bata ma san Amaar ya tafi ba sai dariyar Asmeen ce ta dawo da ita cikin hayyacin ta, a zabure Tasleem ta tashi daga kwancen da take a ƙasin carpet ta lalumo bindigar ta tana jujjuyawa tare da faɗin "yana ina? yana ina? yau sai nayi maganin sa..." saita Asmeen tayi da bindigar tana faɗin "ina wannan ja'irin mutumin yake?..." A tsorace Asmeen ta ce "kin ga dan Allah ki ajiye bindigar nan kar tsautsayi yasa ki harbe ni, shi kam ya daɗe da tafiya..." Tasleem ta ce "kashhhh! naso na ragargaza masa ƙwaƙwalwa..." Suna cikin wannan yanayin sai jin sautin motar Mommyn su suka yi ta dawo, A ruɗe Asmeen ta ce "innalillahi Mommy ta dawo..." Tasleem haura saman upstairs tayi tana riƙe da bindigar ta, Da gudu Asmeen ta haura saman upstairs room ɗin Abeesh taje tana bubbuga ƙofar, sai a lokacin Abeesh da Nasreen suka dawo hayyacin su, sai ji suka yi Asmeen tana faɗin "Nasreen mommy ta dawo..." Nasreen zaro ido tayi tana faɗin "mommy ta dawo?..." Cikin jin kunya Abeesh ya nufi cikin room ɗinsa ita kuma ta buɗe ƙofa ta fice, a tare suka sauƙa falo ita da Asmeen daidai lokacin da Madam Nablah ta shigo falo tana taku kamar bazata taka ƙasi ba, ganin yanda falon ya koma ne yasa ta tsaya cakk tana bin falon da kallo, cike da mamaki ta ce "whattt! me nake gani haka?..." Nasreen da Asmeen bakin su a haɗe wurin faɗin "your welcome Mom..." Madam Nablah ta ce "ba wannan ba taya falo na ya koma haka? wasan dambe ku ka yi ne? ko an mayar mun da falo kasuwa ne ban saniba..." Duk girgiza kai suka yi alamar a'a, Ta kuma cewa "shin yaƙi akayi ne? ko farmaki aka kawo muku?..." Ganin basu da amsar da zasu bata ne yasa suka ce "Mom ɓera ne..." Asmeen ta ce "ɓera ne ya fito falo saboda jin warin feshin magani da akayi, shine muke ta gudu..." Madam Nablah ta ce "Amma harbin bindiga nake gani ata ko ina, har a jikin bango, da kujeru ga plasman bullet ya fasa mun shi, flowowin ɗakin duk sun ragargaje, jikin frig alamar bullet, wai shin wani irin asara ku ka tamka mun ne haka? kayayyakin ɗakina masu bala'in tsada kun mun asarar su duk a saboda ɓera..." Asmeen ta kuma cewa "bindigar mu muka ɗauko zamu harbe ɓeran shine yake ta guduwa ko ina shiga yake, tsautsayi ne a yafe mana..." Madam Nablah fuska ba annuri tana kallon gefe ta ce da su "ku tafi ku bani wuri..." Haka suka ja jiki a sanyaye suka koma can room ɗin su... Madam Nablah ganin ba kowa a falon ne yasa ta lumshe idanuwanta, ta ɗago da hannayen ta sama sai ga wani irin haske mai launin green sai ga falon ya fara juyawa, a hankali a hankali har ya fara juyawa da gudun gaske, itama Madam Nablah haka take juyawa a cikin falon har sai da falon ya koma duhu ƙirin baka iya ganin abinda yake ciki, har ya koma normal, sai da falon ya ɗau tsawon mintina sha biyar daga bisani sai ga haske ya bayyana, Innalillahi wani irin tsaruwa falon yayi kamar ba'a Nigeria ba, komai da komai an canza kayan furnitures, kujeru na musamman masu bala'in tsada wanda babu mai irin su a doron ƙasa, plasman kuwa daga ƙarshen bango har ƙarshen bango tsabar girman sa, tsaruwar falon

Chapter 11 of 34