Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ƙugiya ce ta rufe ƙofar kogon ruwan. Wani murya a cikin ranta ke faɗa mata: "Ki dage, ki nemi mafita, saboda soyayya da kauna na gaskiya ba ta mutuwa cikin wahala." Tasleem ta kwanta, hawaye na zubo mata. Amma zuciyarta bata yarda da duhu ba. Ta san cewa akwai wanda ke nemanta, wanda zuciyarsa zata iya bugawa da nata... A hankali ta furta "Ya Amaar, ka bar ni ne, ko kuwa?..." ta furta a ƙasan murya, kamar numfashinta ya ɗauke da bege. ___________________★★★ A gefe guda, Madam Nablah ta na satar kallon ruwan sihiri da ke ɗakin sihirinta. Tana murmushi a hankali tana kallon Tasleem da ke kwance cikin wancan wurin sirri. Cikin izzah ta furta "Kin ga yadda nake tafiyar da al’amura ko? Babu wanda zai iya gano yanda kike. Kuma kafin komai ya bayyana, zan mallaki zuciyoyin da nake buƙata.....Ba wanda zai iya shigowa, balle ya cece ki... Sai ni kadai," ta faɗa cikin dariyar mugunta. "Amaar da zuciyarsa mai tsarki, ba zai taɓa gane ina ba. Kuma kafin ya gane, zan canza tafiyar duniyar nan gaba ɗaya." Washegari, garin ya farka cikin sabuwar rana, amma zuciyar Amaar tana ci gaba da ɗauke da rana. Ya zauna kusa da mahaifinsa yana kallon fuskar tsohon cikin kwanciyar hankali. Ya ce,: "Abul..." Amaar ya furta cikin murya mai taushi. "Shekaru ashirin da suka gabata, ban san kana raye ba. Amma yanzu da na sanka, sai zuciyata ke so ta bayyana komai. Amma me zai faru idan sirrin nan ya ɓalle gaba ɗaya?" Abul bai ce komai ba, sai ya ɗaga hannu a hankali, kamar yana so ya taɓa fuskarsa. Amaar ya kama hannunsa, yana jin wani sanyi mai kama da ta'aziyya ya lullube shi. Kamar hannun mahaifi yana ƙarfafa masa zuciya: "Ka nemi abinda ya ɓace... Ka cece ta kafin dare ya mamaye komai, domin ita ɗin Hasken ruhi ce..." Amaar ya lumshe idanuwansa yana faɗin: "Na rantse da mahalicci na, albarkacin soyayyar mu... Zan same ki Tasleem. Ko da kuwa zan faɗa cikin ruwan da ba mai tsira." Bayan kwana biyu.... Falon Madam Nablah ya ƙayatu da fitilun kristal masu walƙiya, kowane lungu da saƙo ya sha ado kamar ana shirin babban taro. Amma ba shagali ake ba—damuwa da shiru sun mamaye zuciyoyin kowa... Ana Alhinin rashin ƴan uwa wato Tasleem da Abeesh da Nasreen har yanzu ba a samu labarinsu... Amaar yana zaune da Shaprees da Asmeen a gefe guda, Abul kuma yana room ɗin sa, suna zaune cikin yanayi na ɓacin rai. Madam Nablah dai tana ta danna wayarta kamar wacce bata damu da damuwar duniya ba... Kafin kowa ya iya sake numfashi, ƙofar babban falon ta buɗe da ƙara mai ɗaukar hankali. Kamar walkiya, wata haske mai launin ruwan sanyi ya lullube wajen na ɗan lokaci kafin ta bayyana... Gaba ɗaya suka ɗago kansu, suka sauƙe idanunsu kan wata kyakkyawar halitta da babu kamarta. Matar da ta shigo kyakkyawa ce tamkar ba a duniya ba, tana sanye da doguwar riga mai ƙirar gold, Sumarta doguwa ce kamar siliki tana lanƙwashe har gadon bayanta. Fuskar ta tsab ce, kamar ba'a taɓa samun ɓacin rai a rayuwarta ba. Idanunta shuɗa ne, amma suna da wata annuri da ke jan zuciya. Kamar ruwan rafi ne mai rai.... Amaar ya miƙe tsaye nan da nan. zuciyarsa ta ɗauki bugun farin ciki. A hankali, kamar yana magana da kansa ya furta: "Miemie..." Madam Nablah ta ɗago kai cikin tsoro. Ba kowa bace wannan da ta shigo—ita ce MIEMIE, Sarauniyar Ruwan Aljanu. Halitta mai iko da daraja a tsakanin makaman tsafi da haske. Miemie ta zauna cikin tsayin daka, tana kallon kowa cikin salama da iko. Cikin izzah take faɗin: "Lokaci ya yi da gaskiya za ta fara tunkarar haske," ta ce da murya mai laushi da raɗaɗi, kamar ana karanta waƙa a cikin ruwa. Shaprees ya gyaɗa kai a hankali, zuciyarsa na bugawa. Ya san wannan ba ƙaramin abu bane. Idan Miemie ta bayyana, to kuwa akwai gagarumin sauyi da zai zo. Madam Nablah kuwa ta ɓoye damuwarta tana ƙoƙarin murmushi, amma Miemie ta hango ƙiyayyar da take ƙoƙarin ɓoye wa. Miemie ta ce: "Nazo ne domin sauƙe nauyin da nake da shi tun shekaru ashirin da suka wuce... lokacin da aka jefa ƙaramin yaro cikin ruwan halakar tsafi, na ceci shi, na bashi kariya da haske. Wanda nake magana akai, shi ne... AMAAAR." Wata guguwa ta tashi a cikin zuciyoyin ɗakin. Kowa ya kalli Amaar, wanda yanzu yana fuskantar Miemie da idanu masu cike da alhini da tambayoyi. Miemie ta cigaba da magana: "Kuma yanzu na dawo... domin tsare zuciyoyin da haske ya taɓa. Ku shirya, domin akwai sirrin da zai girgiza kowa nan ba da jimawa ba." Wani irin sanyi mai daɗi ya bayyana cikin ɗakin lokacin da Miemie ta kammala maganarta. Kamar ana busa iska mai ƙamshi daga rafin aljanna, aka ji zuciya na kokuwa da ƙalubale da kuma tsoro. Amaar ya matso kusa da ita a hankali, idanunsa cike da tambayoyi. A yau ne ya sake ganinta a zahiri bayan shekaru masu tsawo da suka gabata, lokacin da yake ƙaramin yaro, yana cikin hadarin nutsewa cikin ruwan tsafi da Madam Nablah ta jefa shi. Sai Miemie ta bayyana wancan lokacin — kamar haske cikin duhu — ta fitar da shi, ta rufe shi da sihiri mai tsabta, wanda har yanzu ke yawo a jikinsa, duk da ba shi da cikakken sani akan hakan, amma tana yawan zuwa masa a cikin mafarki... A hankali ya furta: "Kina da labarin komai... kin san wacece Tasleem? Kin san inda take? sannan ƙanina Abeesh shima kin san a yanda yake? shin da gaske ke Nasreen ta mutu?...." Amaar ya tambaya da murya mai nauyin kewa. Miemie ta dubi kowane fuska kafin ta ce, "Duk da ikon da nake da shi a cikin ruwa da haske, ba zan iya nuna maku inda aka ɓoye Tasleem ba. Wannan sirrin na cikin zurfin duhu ne da aka ƙarfafa da jinin zuciya. Sannan Abeesh shima yana wani duniyar da banida ikon zuwa wurin Amma zan iya taimaka maku ku ji hanyarsu idan kun tsaftace zukatanku, kuma ku jure gaskiyar da zata bayyana." A wannan lokacin ne zuciyar Madam Nablah ta fara karaya. Ta san cewa idan Miemie ta shiga cikin lamarin, ba ruwanta da tsafi ko dabara. Tana ƙoƙarin ɓoye fargaba ne, amma idon Miemie — waɗanda suka fi ruwa tsarki — sun riga sun karanto dukan damuwar da ke ɓoye a zuciyarta. Madam Nablah ta ce: "Kin iso ne saboda Amaar? Ko akwai wata manufa?" Ta tambaya tana ƙoƙarin nuna ƙwarewa da sarauta.... Miemie ta ƙaraso kusa da ita, ta dubeta cikin idanunta masu ƙasaita ta ce: "Kin shafe shekaru da dama kina amfani da duka ikon da aka baku don girbe fansa da iko, amma kin manta... da tsarkin zuciya ake buɗe ƙofofin aljanna. Kuma idan zuciya ta ƙafe da ƙiyayya — to ruwan tsarki ba zai iya wanke ta ba." Sai ta waiwaya gun Shaprees, wanda tuni zuciyarsa ta fara kaɗawa. Ta ce da shi "Ka kasance kana da zaɓi: ko ka zaɓi bin gaskiya da haske, ko ka cigaba da ɓoye kanka a cikin ruwan duhu. Amma ka sani, ba za ka iya fansar matar da ka rasa ba ta hanyar cutar da wata ba." Shaprees ya sauƙe numfashi, ya kau da kai. Kalaman Miemie sun taɓa jikin sa fiye da yanda ya zata. A hankali ya ɗago yana kallonta— yana mamakin yanda wannan kyakkyawar halitta ke tafiya da ikon da ba mutum ke da shi ba, kuma bai taba ganin kowa yana karantar zuciya kamar yadda take ba. MIEMIE ta matso kusa da Amaar, ta ce a hankali: "Zan taimaka maka neman Tasleem. Komai zai iya faruwa, amma ina jin zuciyarka na ƙiranta da gaskiya. Kuma nasan duk inda take... tana fatan sake ganin ka." Miemie ta sake juyo wa ta dube su duka, sannan ta ce da murya mai ƙarfi: "Na bar haske a cikin ɗaya daga cikinku... wanda zai iya bayyana mafita daga duhun da Madam Nablah ta lulluɓe. Lokaci na kusa. Amma har yanzu akwai sirri mai girgiza zuciya da bai bayyana ba." Idanunta sun ɗan tsaya kan Amaar, ta ce: "Ka tuna hasken da ke cikinka, Amaar... shine zai tsine duhun dake kewayen zuciyarka. Kuma shine zai bayyana Tasleem." Asmeen kallon Mahaifiyarta kawai take, ganin ko wani magana idan ya taso akanta za'ayi... Madam Nablah, duk da tana ƙoƙarin nunawa kamar bata damu ba, amma jikinta yana rawa. Tana tsoron su sauka can inda ta ɓoye gaskiya da tarihi, inda ta adana wani sirri da zai iya rushe komai da ta gina tsawon shekaru ashirin. Zuciya cike da mamaki da firgici kowa ya kasa motsi a cikin falon. Bayyanar Miemie ta zame musu tamkar mafarki. Amma ga Amaar, tamkar wani kaho ne aka buga masa — kaho na kiran tarihi, na farkon rayuwarsa. Wata irin sanyi da haske ya lullube zuciyarsa yayin da yake kallon Miemie... Madam Nablah kuwa ta ƙafe Miemie da ido kamar yadda maciji ke kallon kwallon wuta. Tana jin wani iska mai sanyi yana ratsa ta, alamar cewa karfin da Miemie ke da shi yana cikin nau’in da ke rushe dukkanin duhun tsafi. Sai kawai Miemie ta furta da muryarta mai taushi da ƙarfi, “Lokaci ya yi.” “Lokaci na me?” inji Madam Nablah, tana ƙoƙarin ɗaga ƙirjinta da kangararta kamar yadda take yi a duk lokacin da take son rufe laifinta da iko. “Lokacin da gaskiya zata fara bayyana, ko da kuwa an binne ta cikin dutse tsawon shekaru.” Miemie ta ɗaga hannunta sama, sai wata iska ta kaɗa labulen falo, fitilu suka ɗan yi rawar jiki alamar wani abu mai girma yana gab da faruwa. Amaar, wanda yake ta kallo yana ci gaba da tuna wani abu daga rayuwarsa — ya tuna da ruwan da aka jefa shi a ciki lokacin yana yaro, ya tuna da hannun da ya zame shi daga halaka, ya tuna da muryar da ta ce masa “Zaka girma, zaka fuskanci duhu, amma ka kasance da haske.” Sai kawai ya furta, “Ke ce kika ceci rayuwata, ina matuƙar Alfahari dake…” Miemie ta gyada kai cikin murmushi. Sai ta juya ido zuwa ga Madam Nablah, sannan ta ce: “Na zo ne domin janye garkuwar duhu daga zuciyar ‘ya’yanki kafin abin ya kai ga wuce gona da iri.” Sai ta juya zuwa wani ɓangaren falon. Ta danna kafarta ƙasa sau uku, sai wani ginin ƙasa ya buɗe a hankali. Duk suka zuba ido. Akwati ne _ akwatin gawa mai ɗauke da tambarin tsafi da dutsen haske a jikin murfin sa. Kowa yayi shiru. Miemie ta ce: “ Madam Nablah... kin ajiye gawar mijinki shekaru da dama amma ki sani ruhi ba zai bar duniya ba, saboda tsafin da kika tofa masa kafin ki kashe shi.” Asmeen ta rausa ihu daga gefe, zuciyarta na harbawa. Ta ce: “Mahaifinmu? Ashe da gaske ne kina da ikon kashe shi?” Madam Nablah ta juya da hargowa. Tana faɗin: “Na yi hakan domin ikon da nake nema! Ku da kuke nan da babu shi, babu ni!” Amaar ya ƙureta da ido. Shaprees ya ƙafe ta da kallon da babu wanda zai fassara... Miemie ta durƙusa ta shafi akwatin — wani haske ya fito daga cikinsa... Mahaifin su... yana nan, gawarsa na kwance a cikin akwatin... Gaba ɗaya zaman falon ya koma shiru. Kamar an danna abin dakatar da lokaci, kowa na kallon akwatin gawar da Miemie ta bayyana. Haske yana ci gaba da fita daga cikin akwatin, yana fizgar zuciyoyi da nau’in sanyi wanda babu wanda ya taɓa ji. “Wannan shi ne mijinki, Madam Nablah. Wanda kika daɗe kina ɗauke da gawarsa don ki rufe laifinki. Amma ruhi ba ya mutuwa, musamman idan aka kashe shi da zalunci,” Miemie ta faɗi tana kallon Madam Nablah da idanuwanta masu zurfin gaskiya. Madam Nablah ta miƙe tsaye da sauri tana faɗin: “Ba laifi bane idan domin iko ne!” ta hargitse da murya tana kallon kowa da wani irin kallon hauka... “daman da gaske ke kika kashe mahaifinmu?” Asmeen ta furta da kuka murya na kakkarwa domin abun ya tsaya mata a rai, ta nufi akwatin da zafin zuciya tana fadin: “Kin ɓoye wannan shekara da shekaru, kin hana mu jin ƙaunar uba..” Shaprees ya ja baya a hankali. Ya riga ya san cewa Madam Nablah ba mace ce da za a yarda da ita ba, amma ya kasa tsammanin za ta aikata haka a mijinta, uban ‘ya’yanta! Amaar ya durƙusa kusa da akwatin. Ya kura wa fuskar mai kwance a ciki ido, kodayake an daɗe da rasa numfashi, amma kwanciyar fuskar da sakon ruhi da Miemie ke aika masa suna tada jinin jinƙai da mamaki. “Ya kamata a kawo ƙarshen wannan duhu,” Miemie ta ce, tana matsowa kusa da akwatin. Ta ɗauko wata ƙaramar ƙaho wacce ke haskawa da ruwan zinariya, ta zuba ruwa a jikin akwatin. Sai kuma wani abu ya fara girgiza… Kwatsam, sai jikin gawar ya fara fitar da haske – haske mai launin shuɗi mai ƙyalli – da kamar wani abu yana ƙoƙarin farka daga dogon barci! Gaba ɗaya suka miƙe tsaye da firgici, Asmeen ta tsaya jikin Shaprees... Miemie ta juya tana fadin: “Ruhi yana da ƙarfi idan aka kashe shi da zalunci. A yau, wannan ruhi zai ɗan farka — domin ya bada shaidar gaskiyar da kika ɓoye.” Madam Nablah ta ja baya tana girgiza kai tare da faɗin: “A’a, ba zai iya farfaɗowa ba! Na kulle shi da jinin kansa! Na ƙulle shi da alkawari da tsafi!” “To," inji Miemie, "da haske muke warware duhu.” A wannan lokacin aka fara jin muryar mutumin da ke cikin akwatin, yana fadin... “…Nablah... me kika yi min…? Ƴaƴana… Ina ku ke, ina son ganin ƴaƴana…” Asmeen ce ta fashe da kuka, haka Amaar Idanun sa biyu na cike da ƙwalla — suna kallon jikin mahaifinsu wanda tsawon shekaru suka rayu ba tare da saninsa ba... Kuma Tasleem — ita ce kawai ta san da wannan sirri… amma yanzu tana ɓoye a wani ɓangaren duniya da babu wanda zai iya ganinta. A nan labari ya ƙara ɗaukar sabon salo. Madam Nablah ta fara girgiza tamkar mai hauka. “Ku tafi! Ku barni! Baku fahimta ba, banyi hakan don son raina ba!!” Miemie ta kalle ta da murmushi mai taushi amma mai nauyin hukunci ta ce: “Kina da sauran damar tuba... Amma gaskiya ba zata ƙyale karya ta cigaba da mulki ba.” Falon ya yi tsit, kowa na kallon akwatin da Miemie ta bayyana. Cikin ɗakin akwai Amaar, Asmeen, Shaprees, a cikin wannan falo akwai wata zuciya wadda ke shirin fashewa da tsoro wato Madam Nablah... Suna cikin wannan halin Sai ga takun ƙafafu da numfashi mai nauyi yana karatowa daga saman beni. Kafin kowa ya gane me ke faruwa, sai ga tsohon mahaifin su Amaar, ya shigo cikin rawar jiki da hawaye a idanuwansa. Ya durƙusa a gaban akwatin, yana kallon fuskarsa cikin halin da ba'a taɓa ganin sa ba. Yana faɗin: "Ahmed..." ya furta da kyar, yana maimaita sunan. "Kai ne? Kai ne ƙanina da na rasa shekaru ashirin da suka shuɗe? Nablah... me kika yi masa?!" Kallon kowa ya koma gareta. Miemie ta ɗan matsa gefe, tana kallonsu cikin nutsuwa kamar wata sarki mai hukunci. Madam Nablah kuwa ta kasa motsawa. Sai idanuwanta suka haɗu da na tsohon mijinta cikin akwatin—mutumin da ta kashe saboda ya gaza amincewa da shaidanci da muguntar ta. Tsohon mijin da ta ɗaure da sihiri, sannan ta ɓoye gawar tasa a ƙarƙashin wani lungu na gidan da babu wanda ke iya ganowa. Asmeen ta shige jikin Shaprees tana hawaye.. Amaar kuwa ya ɗan matso kusa da mahaifinsa, yana kallon gawar mutumin – ƙanin mahaifinsa da aka kashe a asirce. "Wannan gawar... shi ne mahaifin su Tasleem, Nasreen da Asmeen?" Amaar ya furta da mamaki. Miemie ta jinjina kai tare da faɗin "Na kwance sihirin da aka ɗaura a jikinsa. Ya cancanci a girmama shi, ba a ɓoye shi cikin duhu ba. Amma akwai wata ƙarin asiri da ba a saniba..." Shaprees ya ɗago kansa da sauri, zuciyarsa na harbawa. Madam Nablah na nan zaune, ba ta motsi kamar wanda ruwa ya cinye, amma idanunta sun cika da wani irin ƙiyayya da tsoro na ɓoye gaskiya. "Wace irin halitta ce ke, har za ki aikata haka ga mijinta?" Abul yace, yana girgiza kai, yana mai tuna irin soyayyar da Ahmed ya nuna wa matarsa – amma a ƙarshe, ta ƙare da kisa.... Amaar ya matso kusa da Miemie ya ce: "Kina da ikon gaya mana gaskiyar komai yanzu, ko akwai wani abin da har yanzu ana ɓoyewa?" Miemie ta kalli Amaar, sai kuma ta juyo zuwa ga Madam Nablah. Sai ta ce da ita: "Na bar wannan dama a hannunki. Kifadi gaskiya da bakinki, ko kuma ni da hasken ruwa na mu karasa tone komai..." A cikin falon da aka cika da zazzafan numfashi, hasken Miemie na kara kyalli a tsakiyar dakin, sai aka ji tamkar duk iska ta tsaya. Idanun kowa sun zube kan Madam Nablah, wadda yanzu zuciyarta ke dukan ƙirjinta kamar za ta fasa. Kamar ba ita ba — uwar da ta jima da ɓoye gaskiya, da ɓoye jikin mijinta na tsawon shekaru, yanzu tana cikin fargaba tamkar wani ƙwararren ɗan laifi da aka cafke a wurin laifi. Amaar yana kallonta, yana ɗauke da tambayoyi a idanuwansa.... "Ki faɗi gaskiya yanzu!" inji Abul murya na ɓarke da ɗaci. "Me kike da shi a wannan lokacin? Me ya faru da ɗan uwana?" Madam Nablah ta ƙi kallon kowa. Sai dai ta ja tsaki ga taurin kai, ta ɗaure fuska ta ce: "Kuna so ku ji gaskiya? To ku saurara..." Sai ta tashi tsaye. Ta ɗan gyara mayafinta kamar wata sarauniya da ba ta yarda ta sunkuyar da kai ba, duk da an kama ta da laifi. "Ahmed ya yi kuskure. Na so ya bani ikon mulkin ruhin aljanu da sirrin nasaba... amma ya ƙi. Ya ce ba za a haɗa duhu da haske ba. Na gargaɗe shi, ya ƙi sauraro. Kuma saboda ƙin yarda da ikon da na samu, na kawo ƙarshen sa. Na kuma ɓoye gawarsa a ƙasan gidan nan domin kada wani ya san cewa ni ce na kashe shi." Zuciyar kowa ta ɗauki bugawa. Asmeen ta rufe fuska da tafin hannu. Shaprees ya ɗan jinjina kai, yana jin tsantsar muguntar da ke cikin zuciyar matar da har yanzu ba ta da kunyar bayyanar gaskiya. "Kin kashe mijinki?" Miemie ta furta cikin daƙilewar murya. "Kin hana 'ya'yanki su san yanda uba ke nan? Kin ɓoye rai da gaskiya saboda kuɗi da iko?" Madam Nablah ta saki murmushin ƙiyayya. "Ni Sarauniya ce. Kuma Sarauniya ba ta roƙon gafara. Ban taɓa nadama ba. Duk wani da ya tsaya a gabana, to ya sha keɓaɓɓen hukunci." Kamar wuta ta faɗa cikin zuciyar Abul mahaifin su Amaar. Ya juya da sauri ya kalli Miemie yana faɗin: "Kada ki bar wannan ta tafi ba tare da an hukunta ta ba!" Amma Miemie ta ɗan dafe ƙirji, sannan ta kalli Amaar da Asmeen da Shapreen ta ce: "Hukuncin wannan ba daga gare ni zai fara ba. Sai zuciyar 'ya'yanta da danginta sun gane hakikanin darajar abin da suka rasa." Nan take wata guguwa ta shigo cikin falon – amma ba iska bace – ruhi ne mai sanyi, mai tsarki, mai haske, wanda ya dudduba kowa ya shiga jikinsu kamar wani abun lura. Nan take kowa ya fara ganin hoto a zuciyarsa – na kisan Ahmed, na ƙiyayya da fushin Madam Nablah, da irin sihirin da ta taɓa yi. Sai Amaar ya ɗauki numfashi mai zurfi. Ya ce da Miemie: "Duk wannan... amma Tasleem ba ta cikinmu. Shin akwai alaƙa tsakanin abin da Madam Nablah ta ɓoye da ɓacewar Tasleem?" Miemie ta jinjina kai a hankali. "Wani ƙarin sirri yana jiranku... Kuma har sai kun nemi da gaske, za ku gano."... Cikin ikon Allah duk abinda ke faruwa Nasreen tana cikin tafkin ruwan MIEMIE tana kallon duk abinda ke faruwa a gidan su, domin Miemie ta bar mata wani madubi yanda zata na ganin video abinda ke faruwa, itama tana nan sai rausa kuka take tana Allah wadai da halin mahaifiyar su, har Idanunta sunyi jawurr.... Itama Tasleem Miemie ta san dabarar da tayi ta bayyanar mata da video abinda ke faruwa ba tare da sanin Madam Nablah ba, Tasleem tana zaune a ɗaure tana ganin abubuwan da ke faruwa, ga mahaifinsu da basu taɓa gani ba yau ya bayyana a matsayin gawa, tasha kuka itama kamar ranta zai fita.... Daga cikin numfashin duhu da tsantsar ruɗani, dakin falon gidan Madam Nablah ya shiga shiru mai nauyi. Miemie ta ɗan yi tsuru-tsuru da idanuwanta masu hasken ruwa, sannan ta juya ta kalli Amaar wanda zuciyarsa ke ƙuna da rasa ƴan uwansa da kuma mamakin makircin Madam Nablah. “Wannan gawar,” Miemie ta nuna akwatin da Ahmed ke kwance ciki, ta ce: “ba kawai jikin mataccen mutum bane. Wannan wuri da aka binne shi ya zama makabarta ce ta ƙiyayya da sihiri, soyayya da jinƙai.” Madam Nablah ta yi dariya mai sauti, tana takawa a hankali kamar wata zakanya mai jin ƙarfinta. “Gawarsa tana nan, so what? Kwana nawa zai canza rayuwar ku? Ko dai na kashe, ko dai na ɓoye – amma na rayu, kuma ina da iko!” Sai wani abu ya girgiza cikin falon. Tagogi suka fara motsawa. Fitilun ruwan hoda suka ɗan ɗauke, sannan aka ji murya – kamar ta sama, mai sanyi da mai nauyi: Ruhin Mahaifin su Tasleem ne ke magana yana faɗin: "Ba wanda ya mallaki zuciyar duniya. Ko kin kashe gaskiya, za ta dawo da rai. Kuma ko kin ɗaure sirri, dare zai zo da rana." Gaba ɗaya suka zuba ido suna kallon sama. Idanun Asmeen sun cika da hawaye. Shaprees ya rufe baki da tafin hannunsa, tamkar yana tunanin wani abu mai girma da ke dawowa masa a hankali. “Ya Allah…” mahaifin su Amaar ya furta. “Na bar ɗan uwana cikin mugun gidan mace da ba ta san mecece ‘yanci ba.” Miemie ta ɗan juya kamar wata sarauniya, ta miƙa tafinta zuwa ga Amaar, sannan ta ce da shi da murya mai laushi: “Idan kana son ku samu Tasleem, to sai kun zurfafa cikin ruwan da ke ɓoye mafita. Amma ku sani — ba ƙarfin jiki zai fito da ita ba, sai ƙarfin zuciya.” Amaar ya runtse ido. Wani zafi na tsananin ƙauna ya zuba masa a zuciya. Bai san yanda yake ji ba — kamar ruwa, kamar wuta, kamar iska. Amma ya san abu ɗaya: Tasleem tana kiransa, duk inda take. A gefe kuwa, Madam Nablah ta wuce zuwa ɗakinta, tana kuka… amma ba kukan nadama ba — kukan fushin da ta tsinci kanta a ciki. Ta na tafiya a hankali, tana jin Miemie ta zo mata da barazana. Kuma wannan ba zata yarda da shi ba. Ta rantse a zuciyarta tana faɗin: “Bari su ci gaba da neman Tasleem. Wuta ce za su tsinta a ƙarshe.” A wannan ranar ne aka sitirta Mahaifinsu Tasleem, Abul da Amaar da Shaprees ne suka yi jana'izar sa a cikin gidan ba tare da sun gayyato kowa ba, cikin dare suka je su ka binne shi.... Bayan sun dawo, Abul yana fama da zazzabin damuwa... Amaar wanda ke zaune a gefen mahaifinsa, yana lulluɓe shi da bargo. Kamar dare ne ya zo masa da nauyin tunani. Amma daga can cikin kunnensa, sai ya ji wata murya mai laushi tana cewa: Miemie ta bayyana cikin hasken ruwa a kusa da tagar ɗakin.. “Amaar, lokaci yana tafiya. Duk da an bayyana gawar da Madam Nablah ta ɓoye, akwai babban sirri da ke can cikin ruwan da ta kulle Tasleem.” Amaar ya ce: “Ina Tasleem take? Ina matata? Me ya sa zuciyata ba ta huta ba har yanzu?” Miemie ta ce: “Kuna bukatar ku shiga tafkin madalla da hasken rana — tafkin da babu wani sihiri da zai iya kare ku sai zuciyar ku. Amma sai kowa ya haɗa hannu — kai, Shaprees, Sirrin wannan tafki yana cikin zanen bango da ke ɗakin Madam Nablah.” Amaar ya zabura. Wannan zance ya birkita masa tunani, amma ya bashi ƙwarin gwiwa. Ya san lokaci bai da yawa kuma yasan ba zai bari Madam Nablah ta ci nasara ba. --- A wannan daren, Madam Nablah ta shiga wani ɗaki mai duhu a ƙarƙashin beni, ɗakin tsafinta mafi ɓoyuwa. Ta ɗauko wani kwanon ruwa mai haske, ta zuba wani ruwan tsafi a ciki. Ta ga fuskar Tasleem a ciki — tana kwance a cikin wata dunƙulalliyar madatsar ruwa, tana numfashi idonta a rufe. Madam Nablah cikin dariyar mugunta ta ce: “Ke Tasleem, ni na haife ki, ni kuma zan hukunta ki. Idan na rasa iko akan sauran ‘ya’yana — ke ba zaki gudu ba.” Washegari da safe ..... Amaar, da idonsa jajaye, ya fito daga ɗakin mahaifinsa. Kamar jarumin da ya taso daga makogwaron

Chapter 32 of 34