Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ƙeta da raini ta sakar, sannan ta juya gefe kaɗan, ta matsa gaban kujera ta zauna tana ta kallon yatsun kafarta kamar wata budurwar zinariya Ta ce “Yana fushi dake… ko baki lura ba? Na shiga ransa a cikin mintuna kaɗan, ke da kike da shekaru da shi baki iya riƙe zuciyarsa ba…” Wannan magana tamkar sara ne a kunnen Nasreen, Zuciyarta ta buga da ƙarfi, Hannunta har ya ɗago kamar zata daki Catrina, amma sai ta tsaya, Kuka ya hana ta magana, numfashinta ne yake hawa da sauƙa... Nasreen maganar zuci take “Me na yi wa Abeesh har ya tsane ni haka? Har ya zama haka?” Ta juya da sauri, hawaye na sauƙa daga idonta, sannan ta nufi ɗakin su, Da ƙyar ta taka ƙafarta har ta kai ɗakin, ta rufo ƙofa da ƙarfi, ta zube a ƙasa tana kuka kamar karamar yarinya. --- A falon kuwa Catrina ce ta miƙe tsaye cikin natsuwa. Wani ƙaramin murmushi ya bayyana a fuskarta, na gamsuwa da cigaba da rikita soyayya tsakanin Abeesh da Nasreen. Tana jin daɗin ganin kishin ya fara cin zuciya. Catrina a cikin zuciyarta ta furta "Idan ransu ya karye, zuciyoyinsu za su samu girgiza. Idan zuciya ta rikice, ina da damar shigar da duhu..." Ta tafi da natsuwa zuwa wani ɗaki na baƙi inda Madam Nablah ta tanadar mata wuri, amma kafin ta shige, ta sai da ta kalli saman upstairs mataki na ƙarshe yanda zata ɗauka.... Tana tafe tana maganar zuci “Zan iya ɗaukar zuciyarsa gaba ɗaya… idan Nasreen ba ta farka ba.”..... Da haka ta shige ɗakin masauƙin ta. ★★★★★ Daren ya sauka da natsuwa, amma zuciyoyin gida sun cika da hayaniya. A ɗakin baƙi, Catrina ta zauna a bakin gadonta, tana shan ruwan sanyi a cikin kofin gilashi mai tsada. Hasken fitilar dakin na haskaka gashinta mai sheƙi kamar zinariya mai siffar duhu. A cikin zuciyarta kuwa, akwai fassarar dabaru. Akwai shiri. Catrina ta furta a hankali "Zuciyar Abeesh… mai ƙarfi ce, amma tana da rauni idan yana fushi, Nasreen ta manta cewa soyayya ba kyauta ba ce idan ba a kula da ita..." Ta miƙe. Tana tafiya kamar sarauniya, Ta zura rigar bacci mai launin azurfa, wacce ke kwance a jikinta kamar ruwa. Sai dai ba domin son burge Abeesh kawai ba, har da saƙo: tana son ya manta da Nasreen gaba ɗaya. --- A gefe guda kuwa... Nasreen tana kwance a kan gado, idanuwanta cike da hawaye. Tana tunanin kalaman da Abeesh ya faɗa mata. Kamar wuƙa suka ratsata. Nasreen a cikin ranta take faɗin "Shin ya manta da yadda muka fara? Da yadda na tsaya masa? Me yasa yanzu yake ƙoƙarin canza mun?" Tana tashi, ta nufi kofar ɗaki da niyyar komawa wurinsa. Amma ƙafafunta suka tsaya cak. Wani murya daga cikin zuciyarta ta ce “Ki barshi! Idan har zai iya juya miki baya da wacce bai ma sani ba, to ya dace ki ƙyalle shi!” Sai kuma wata murya mai taushi ta ce “Ki fahimce shi, ki yi haƙuri, ki nemi yafiyarsa…” Tana tsaye a tsakiyar waɗannan muryoyi, zuciyarta na sarƙe da alhini, idonta na kaɗa wa da hawaye. --- A ɗakin Abeesh kuwa, yana zaune a bakin gado, tunani fal cikin kansa. Ko da yake yana jin jiki da zuciyarsa sun gaji da Nasreen saboda wata ɓacin rai da ta haifar masa, amma a ƙasan zuciyarsa akwai soyayya mai zurfi da baya iya musawa. Amma yaƙin da ke zuciyarsa ya ruɗe, musamman da wannan sabuwar halitta mai kyau da ƙamshi kamar sararin samaniya ta fara ƙoƙarin shigar masa rai – Catrina. Yana da tsattsauran ra'ayi a kan soyayya, ya yarda da gaskiya, biyayya, da sauƙin hyiali. Amma yanzu ya fara ji kamar Nasreen ta canza. Catrina kuma tana nuna masa salo dabam. Abeesh a zuciyar sa ya furta “Ta bani kulawa, ta nuna mun soyayyar gaskiya bazan iya juran ganin Nasreen a cikin hawaye da zargi ba... Ba haka nake so ba…” Misalin ƙarfe 2 na dare.... WURIN ABEESH… Dare ya tsinke da shiru. Kamar kowane dare, an jima da kashe fitila, sai hasken farin wata daga tagar ɗakin da ke daddarewa a bango, Amma ba barci a idon Abeesh. Sai juye-juye yake yi a gado, yana tunani. Tunani ne cike da rikici da soyayya, fushi, ruɗani, da sabon abu mai kama da jaraba. Ji ya yi an buɗe ƙofar ɗakin sa a hankali, juyowa ya yi yana kallon bakin ƙofar. Catrina ce ta zo masa a hankali, tana daɗa rage tazarar dake tsakaninsu, tana sanye da rigar baccin ta... Abeesh ya tashi zaune tare da faɗin “Ke kuma? Me kike nema a nan cikin dare?” Catrina ta dafe ƙofa tana dariya ƙasa-ƙasa sannan ta ce “Na kasa yin bacci, Sai naji kamar zan fi samun kwanciyar hankali idan na ganka... King Abeesh....” Ya runtse ido. Wannan sunan da ya ji a bakin ta tamkar sabon wata ne ya ratsa cikin zuciyar sa da wani salo mai ɗauke da wani sirri, mayar da idonsa ya yi kanta tare da kama bakinsa, Ya ce “Wannan ba daidai bane. Ki koma ɗakinki.” Catrina ta matso kusa da shi sannan ta ce “Ban zo da mungun niyya ba. Kawai ina so ka san cewa ba kai kaɗai bane a cikin jin zafi…” Abeesh bai ce komai ba. Sai dai yanda take kallonsa, kamar ta fahimci komai cikin zuciyarsa. Cikin daddadan murya da dabara, ta matsa kusa da shi sosai. Hannunta ya sauka a kan hannunsa, Tana son jin irin karfi ko rauni dake cikin rayuwarsa. Zuciyarsa na yawo. Bai tura hannunta ba. Amma kuma bai kama ba. Abeesh ya ce “Kin san inada rauni Catrina... Kuma ni... ni ba mutumin da ke saurin yarda da sababbin mutane ba ne...” Catrina ta saka murmushi sannan ta ce “A lokacin da waɗanda ka yarda da su suka raunata ka, wani lokacin, sabon mutum na iya zama mafita…” Yayi shiru. Zuciyarsa tana tafasa da ruɗani. Cikin zuciyarsa, yana jin kalamanta suna ratsa shi. Sai dai a lokaci guda yana jin kamar wani ɓangare daga cikinta yana ɓoye wani abu. Shiru ya shiga tsakaninsu. Catrina ta miƙe tsaye cikin salo, ta zuba masa idanu. Sannan ta ce “Zan tafi… Amma zan dawo. Kuma in Allah ya yarda, wannan zuciyar taka zata dawo da murmushinta.” Ta juya. Sai kuma ta tsaya a ƙofa, ta ce: “Nasreen ta rasa hanya. Amma ni zan iya nuna maka sabon titi... Titi na gaskiya... ko kuwa na mafarki.” Tana kaiwa nan ta fice a ɗakin, tana fita ta ɓace cikin duhu. --- A GEFE GUDA – NASREEN… Nasreen tana zaune a gefen gado, hannunta ɗauke da littafin addu’a. Amma ba karatu take ba – kallo ɗaya kawai take wa shafin, Zuciyarta na cike da ƙuna. Wani abu yana ƙona ta fiye da zafin kalmomin Abeesh: yanda ya kalle ta kamar bai taɓa sonta ba, da kuma yanda bai damu da halin da take ciki ba... Sai dai Nasreen ba mace bace da zata zuba ido ta bari soyayyarta ta rushe. Ta miƙe, ta saka mayafi, sannan ta furta da ƙarfi: “Zan kare soyayyata. Ko da zan rasa komai. Ko da zan tafka kuka. Amma ba zan bari wata yarinya ta kwace min miji ba.”..... NEXTTTTTT........ New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 41 to 42 A DAKIN ABEESH… Tsakar dare ne. Shiru ya mamaye gidan. Daga wani ƙaramin fitilar bango ana iya hango Abeesh zaune a gefen gado, da labulen window a buɗe yana kallon duhun dare yana tunani. Tunaninsa cike yake da abubuwa biyu: Catrina, wacce ke da wani jan hankalin da ba zai iya fassara ba… da kuma Nasreen macen da ya fara soyayya da ita da zuciyarsa gaba ɗaya — amma ta raunata shi. Ya dafe kansa. “Me yasa komai ke rikicewa haka?” Yayi tambaya cikin zuciyarsa. Ƙaran ƙofa ya ji Ya juyo da sauri. A hankali ƙofar ta buɗu, Nasreen ce, cikin doguwar riga mai launin ruwan hoda da hijabi a kafada. Idonta cike da hawaye, fuskar ta sharaf da damuwa. Ta tsaya a ƙofar ba tare da ta shigo ba Abeesh cikin mamaki da ɓacin rai ya ce “Ke kuma... me kike nema a nan?” Nasreen cikin murya mai rauni ta ce “Ina son magana da kai, Abeesh... ka bani minti daya... na roƙeka.” Ya ɗan kalle ta, yaja numfashi mai nauyi, ya ɗan matsa gefe a gefen gado, bai ce komai ba yayi mata alamar ta shigo. Nasreen ta shigo a hankali kamar wacce take takawa akan ƙaya. Zuciyarta na bugawa, idonta na kallon sa har ƙasa. Sannan ta ce “Na san baka shirya ji daga gare ni ba... kuma gaskiya ne, na yi maka babban laifi. Amma zan mutu cikin nadama idan baka yafe mun ba...” Abeesh ya ɗago kai ya kalle ta sannan ya ce “Wani laifi kika aikata har ya sa kika zo da dare neman gafara?” Nasreen ta durƙusa ƙasi, idanunta cike da ƙwalla ta ce “Na mare ka, kuma na goyi bayan mahaifiyata, wacce ta raɗa maka azaba har ka rasa komai da ka sani... kuma da zuciya ɗaya nake cewa na tafka kuskure...” hawaye ne suka zubo daga idonta. ta ci gaba da cewa “Nayi kuskure na zaɓar tsoron mahaifiya akan gaskiyar da zuciyata ke gani. Kuma zuciyata ta san kai ne hasken da nake nema. Amma tsoronta da karfinta ya sa na tsorata… nayi maka rashin adalci...” Abeesh ya kalle ta. fuskar sa a washe Amma zuciyarsa bata sake ba. Ya daɗe yana kallonta ba tare da ya ce komai ba. Daga bisani yace: “Kin san mene ne ya fi komai zafi a rayuwa?” Nasreen ta girgiza kai Sannan ta ce “Mene ne?” Ya ce “Kin fi jin zafin mari da kalma, amma ni, na sha wahala cikin duhun da mahaifiyar ki ta jefa ni a ciki, na rasa tunani, na rasa imani... kuma da kika mare ni, ba wai fuskata kika mara ba — rayuwata kika ƙara jefa cikin ƙunci.” Nasreen ta fashe da kuka. Ta ce “Idan zan iya komai don in gyara kuskuren nan, zan yi. Zan tsaya a gabanka kullum in zubar da hawaye na har sai zuciyarka ta huce. Zan yi komai don in dawo da kai… Abeesh... kar ka bar ni.” Shiru ya yi ba tare da ya furta komai ba, Ya tuna kukan da yayi a lokacin da ya rasa komai. Ya tuna yanda zuciyarsa ke son Nasreen... amma yanda ya tsani abinda tayi masa ya wuce misali... Ya juyo gareta, cikin murya mai sanyi da kuma karfi yace: “Zan iya gafartawa… amma bana iya mantawa da azaba cikin sauri. Ki bar ni na zauna da zuciyata. Idan da gaske kina sona, ki bani lokaci… ki bani sarari...” Nasreen ta gyaɗa kai da hawaye, ta miƙe a hankali, ta fita da zuciyarta cike da fargaba da fatan nasara... ★★★★★★ *WASHE GARI* Ana shirye-shiryen bikin Abeesh da Nasreen, da kuma Shaprees da Asmeen. Gidan Madam Nablah ya cika da shirye-shiryen biki — kallo ɗaya zaka yi ka fahimci ana shirin wani babban abu. Falo da tsakar gida sun sha ado da launuka masu ban burgewa. an rataya fitilu da fure a jikin bangon gini, ƙamshi na turaren wuta da bakhoor yana yawo har cikin sararin gidan.... Abeesh Kwance yake a cikin ɗakinsa, yana kallon saman ceiling ... zuciyarsa taƙi nutsuwa. Catrina dai ta riga ta fara nasara wajen ɗaga masa hankali — duk da bai gane asalinta ba, Yana jin sonta a cikin zuciyar sa amma yana jin hakan laifi ne, yana jin laifi ne saboda Nasreen ta nemi afuwar sa da hawaye a fuskarta, har ya haƙura da Auren ta amma saboda umarnin Abul, da kuma shawarar Yayansa Amaar, sai ya amince da wannan auren domin su gyara rayuwa. A wunin yau kowa yana cikin shirye-shiryen gobe. Nasreen na cikin ɗaki tare da Asmeen suna shiryawa, amma zuciyarta cike take da ƙunci. Tana son zuwa ɗakin Abeesh domin ta sake magana shi — ta san ba a gama warware komai ba, har yanzu akwai dusar da bata narke ba a cikin ransa. A gefe guda, Catrina kuwa tana zaune a wani lungu na falon gidan, cikin shiga mai zaman kansa. Bata fito fili ba, amma tunanin ta yana kan Abeesh ne — gaba ɗaya ta gama karantar zuciyarsa. Tana murmushi a hankali, tana cewa a zuciyarta: “Zan bar ku kuyi Aure Nasreen, Amma zuciyar mijinki ba taki bace gaba ɗaya... ba sai na kwace shi daga gareki ba, tunda nayi nasarar shiga cikin ransa.”...... TSARIN BIKIN YAU An tsara biki da sassafe. An kira limamai da shaidu, ana sa ran za a yi aure da safe kafin rana ta bayyana sosai. Ana shirin yi a cikin babban filin gida, inda aka jejjera komai na ƙayatar da bikin.... An tsara komai, an ƙawata gidan tamkar sabuwar duniya, ƙamshi na turaren wuta da na fure sun haɗu sun ba da wata irin annushuwa ta musamman. A yau ne za a ɗaura auren Abeesh da Nasreen, da kuma Asmeen da Shapreen... A ɗakin Abeesh... Yana zaune a gefen gado yana kallon tagar da ke fuskantar rana, yana ta tunanin yadda zuciyarsa ke cike da ruɗani. Soyayyar da yake wa Nasreen ta fara dusashewa, amma zuciyarsa baza ta iya fitar da ita gaba ɗaya ba. Har yanzu yana jin raɗaɗin mari da kalaman da ta furta masa a lokacin da ya bayyana gaskiyar halin Madam Nablah. Kwatsam sai ga ƙofar ɗakin ta turo a hankali, Catrina ce, ta sha ado kamar bazawara daga wata masarauta. Ba ƙaramin kyau tayi ba. Rigar da ke jikinta na launin zinariya mai kyalli, tana fidda haske da kwalliyar da ta bayyanar da surar jikinta, gashinta yana yawo har gadon baya, idonta cike da kwaɗayi da nuni. Tsaya wa tayi a bakin ƙofa sannan ta ce “Zan iya shigowa ko?” ta faɗa cikin wata murya mai sa nutsuwa da girgiza zuciya. Abeesh ya ɗan juyar da kansa yana kallon ta, duk da a yanzu bai da ƙarfi sosai akan Nasreen, yana jin wata ɓangare na zuciyarsa yana ja da Catrina. Ya gyara zama amma bai ce komai ba. Catrina ta matso a hankali, kamar wacce take jin kunyarsa, amma da mugun nufi take tare dashi, ta zauna gefensa tana kallon sa kai tsaye. Ta furta “Na san rana mai kamar ta yau kana bukatar nutsuwa, amma na zo ne in tayaka murna.” Ta ɗan ɗora hannunta a saman kafadarsa, tana shafar sa a hankali. Abeesh ya kama hannunta da nufin cirewa, amma sai ya tsaya. Ganin yanda zuciyarsa ke sauya yanayi, sai ya ce da ita: “Catrina… me kike nema a wurina?” “Ka sani ai,” ta ce da murmushi, sannan ta kuma cewa “Ba zan tsaya ba sai na samu zuciyar da nake nema…” Abeesh kallon ta kawai yake ba tare da ya furta komai ba, har ta gama yinta ta tashi ta fice... --- A can ɗayan ɓangaren part ɗin su Tasleem... Tasleem tana tare da Nasreen da Asmeen a ɗaya daga cikin ɗakunan kwana. Ta kama hannun Nasreen tana ƙoƙarin kwantar mata da hankali. Cikin kulawa ta ce “Nasreen… ki manta da baya, ki tuna da yanda kike ƙaunar Abeesh. Na san zai dawo ya darajar ki.” Nasreen tana hawaye ta ce “Amma Tasleem, zuciyarsa ta riga ta fita daga wurina… ina jin yana sonta… waccan Catrina.” Tasleem ta share mata hawayen fuskarta ta ce “Wallahi in har Catrina ba ita ce uwar ƙaunarsa ba, ba zata shige zuciyar sa ba. Ke ce ta zuciyarsa... karki bari wani ya maye miki gurbi.” A gefe guda kuwa, Asmeen ce ta saki ajiyar zuciya tana kallon madubi wacce ata sanadiyar Auren nan Mommynsu tasa aka ɗauko ta daga part ɗin Shaprees Tana hawaye ta ce “Ni kuwa Tasleem, wallahi bana jin Shaprees mijina ne. In dai auren dole ne, to zuciyata ba zata taba yarda da shi ba.” Tasleem ta matso kusa da ita tare da cewa “Kada ki karaya, Asmeen. Kullum haske yana da hanya, har cikin duhu. Ni zan ci gaba da neman mafita, domin ku samu kuɗi, ku sami lafiya, kuma ku samu soyayya.” ' Tasleem wuni take tare da ƴan uwanta tana basu kulawa ta musamman.... --- A yau ne za a kai Amare ɗakin mazajen su dake cikin gidan Madam Nablah saboda tsaro Kowa yana cikin girmamawa da farin ciki a zahiri, amma a zuciya akwai sirrin da bai da mafita. Kuma a gefen wannan soyayya da ƙaddara, Catrina tana ta ƙoƙarin cin nasara da kwaɗayin zuciya... ★★★★★ Daren da aka ɗaura aure, gidan Madam Nablah ya ɗauki kyan da ba a taɓa gani ba. Wutar fitilu tana haskakawa kamar taurari sun sauko ƙasa. Turaren ƙamshi ya cika ko’ina, yana yawo cikin iska kamar harshen soyayya. Amma duk wannan ƙyalli na waje bai iya ɓoye tsananin rikici da girgizar da zuciyoyi ke fama da su ba. A ɗakin sabuwar Amarya Nasreen tana zaune a gefen gado cikin shigar bacci mai launin shudi da zinariya. Idanunta sun cika da hawaye duk da fatar da ta yi na wannan ranar, tana ƙoƙarin kare kanta tana maganar zuci “na samu soyayyar rayuwata amma zuciyata ta san gaskiya...." Abeesh bai zo ɗakin nata ba. Yana can a ɗakinsa yana kallon madubi, yana duban fuskar kansa da ido mai zurfi kamar yana tambayar kansa: “Ni waye ne yanzu? Mijin Nasreen? Ko dai ƙaunataccen Catrina da zuciyata ke bugawa saboda ita?”... Kamar daga sama, ƙamshin turaren Catrina ya karade ɗakin. Kafin ya kammala tunani, ta turo ƙofar cikin natsuwa, cikin shigar mayafi mai launin ja da zinariya. Fuskarta cike da annuri, idanunta kuwa na walƙiya da sirrin duhu. Ta tsaya a gabansa. “Abeesh...” ta kira sunansa da murya mai sanyi kamar ruɗin murya daga wata duniya. “Ka yi aure yau, amma zuciyar ka har yanzu bata samu natsuwa ba. Ni na fahimta.” Abeesh bai iya cewa uffan ba. Kamar mai shaƙuwa da ƙamshin sihiri, ya matsa kusa da ita. Ta kai hannunta ta shafa sajen fuskarsa da tausasawa, tana murmushi ta ce “Na san baka manta da ni ba. Kuma zan kasance tare da kai — ko da ka auri Nasreen. Ba zan bar ka ba.” Yayi ƙoƙarin cewa wani abu, amma muryarsa ta makale. Zuciyarsa a rikice — ba ƙyale Nasreen gaba ɗaya ba, amma zuciyarsa na karkata ga Catrina. ** A part ɗin Asmeen kuwa.... Tasleem na cikin ɗakin Asmeen, tana rarrashin ta kamar yadda uwa ke rarrashin ɗa. Asmeen tana zaune da mayafi a bisa kafadarta, hawaye na sauƙa daga fuskar ta. Asmeen tana kuka ta ce “Tasleem, kada ki ce mun Shaprees mijina ne. Zuciyata na tsoro, kuma hankalina ba ya kwance da shi.” Tasleem ta kamo hannunta tare da faɗin “Na san... na san wannan auren ba shine burinki ba. Amma ki yi haƙuri. Kada ki manta da hasken da ke cikin ki. Ki riƙe shi, kada ki bar duhu ya ruguza miki rayuwa.” Asmeen ta kalli Tasleem sannan ta ce “Kina nufin... Shaprees ba wanda muke zato bane?” Tasleem ta ɗan yi shiru, sannan ta ce, “Ina jin akwai abubuwa da yawa da muke buƙatar sani. Amma yanzu... ki kasance da tawakkali. Zaki buƙaci ƙarfin zuciya sosai.” Tana cikin rarrashin Asmeen sai ga ƙiran wayan Nasreen, Tasleem ɗaga ƙiran tayi tare da faɗin "Nasreen lafiya kuwa?..." Nasreen tana kuka ta ce da Tasleem "Dan Allah ki zo yanda nake yanzu akwai matsala...." Tasleem kallon Asmeen tayi sannan ta ce "Ƴar uwa Asmeen ki kwantar da hankalin ki Insha Allahu babu abinda zai faru, yanzu zanje Nasreen tana ƙira na...." Daga nan ta bar part ɗin Shaprees da Asmeen, ta koma can part ɗin su yanda Nasreen take .... ***** A gefe guda kuwa, Nasreen ta kai karar zuciyarta wurin Tasleem tana faɗin “Kin ga yadda yake, ko? Bai zo ba. Babu soyayya... babu daɗin aure... Catrina ce matsalar nan, ban san ko wacece ba amma... tana son ruguza ni!” Tasleem ta rungume ta sosai tare da faɗin “Na fahimce ki. Ki kwantar da hankalinki. Zuciyar Abeesh ba a wuri guda take ba. Amma ki sani — ke ce matar aurensa. Kuma Allah zai daidaita zuciyarsa idan kika dage da addu'a.” ** A ɗakin duhu kuma, Madam Nablah na zaune tana juyawa a kujerar sarautarta, tana dariyar cikin zuciya. Tana jin daɗin yadda abubuwa ke tafiya dai-dai.... Kwatsam, wani hazo mai duhu ya bayyana a gabanta — Catrina ce. Tana siffar aljana yanzu, ba mutum ba. Ta sunkuyar da kai. “Uwar Wuta, komai na tafiya daidai. Na kusa mallake zuciyar Abeesh gaba ɗaya.” Madam Nablah ta murmusa da mugunta ta furta “Da kyau, Catrina... Idan muka mallaki zuciyar Abeesh, za mu iya karya ruhin Abul da kuma shanye hasken da Tasleem ke ƙoƙarin kawo wa.” ★★★★★★ Falon ya ɗauki salo mai zafi, wutar fitila na haskaka fuskokin da ke cike da motsin zuciya. Amaar yana zaune cikin natsuwa, hannunsa a kan na Tasleem wacce take ta sharar hawaye cikin tausayi da ƙunci. “Ya Amaar,” Tasleem ta ce da muryar da ke rawar zuciya, “meyasa mommyna bazata amince da kai ba? Ta Aurar da Nasreen da Asmeen amma ni... ita ce ta hana ni farin ciki na. Na gaji da jurewa.” Amaar ya riƙo hannunta cikin tausayawa tausayi yana kallon idanunta cikin kwantar da hankali “Tasleem,” ya ce cikin murya mai laushi, “ki kasance mai tawakkali. Allah yana jarrabar bayinsa da wanda yafi dacewa da su. Ranar aurenmu na zuwa, ko da duniya ta ƙi, sammai zasu yarda. Kin cancanci soyayya mai tsarki kuma Allah bazai bar ki ba.” Tasleem ta sauke ajiyar zuciya, tana ƙoƙarin daidaita numfashinta. Suna cikin wannan tattaunawa ne sai ga ƙofar falo ta buɗe — Catrina ta shigo. Sai ta tsaya, a jikin lulluɓe da atamfa mai launin zinariya da baƙi, tana kallon su da wani murmushi wanda ba’a gane ko da gaske bane ko yaudara a hankali ta furta “Masoya... sannunku da hutawa,” ta faɗa da murya mai saukar da sanyi amma cike da nufin karya nutsuwa. Tasleem ta ɗaga kai da sauri, kamar wata wuta ce ta kunno kai a zuciyarta. Ta miƙe tsaye cikin hanzari kamar bazata jure ganinta ba “Kece Catrina ko?” ta ce cikin tsawa. sannan ta cigaba da faɗin “Ke da kika zo mana a matsayin baƙuwa amma kina ƙoƙarin ruguza soyayyar ƴar uwata da mijinta? Wace irin halayya ce haka?” Catrina ta ɗan saki dariya — wadda ke cike da wani irin kwanciyar hankali. Ta taka zuwa tsakiya cikin falo, ta tsaya gaf da gaf tana kallon Tasleem da ido masu walƙiya. “Soyayyar Abeesh?” Catrina ta ce. Ta kuma cewa “Na rigada na mallaki zuciyarsa. Kin ce Nasreen ce matar sa, amma zuciyarsa ba ta wurinta. Shi kansa yasan hakan. Ina sonsa... ko da zuciyar ku bata so...” Amaar dai bai ce uffan ba, yana zaune yana nazari, zuciyarsa na hararar wannan sabuwar halitta da ba ya ganewa. Amma a hankali yana lura, Catrina ba kamar kowa bace. Tunaninsa na barazanar cewa akwai wani abu mai zurfi da ke ɓoye a bayanta. Tasleem ta matso kusa da ita, fuskarta cike

Chapter 23 of 34