Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
lokaci guda zuciyar ta ya hauro ga manya-manyan idanuwanta yanda take zaro su ta ce "impossible Mom! bazan taɓa durƙusa gwigwowina a gaban halittar da muke matsayi ɗaya a wurin Ubangiji ba..." Madam Nablah ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba cikin fushi ta miƙe tsaye tana faɗin "Tasleem idan bazaki bi umarni na ba zaki shiga uƙuba ta..." Tasleem haka ta tanƙwashe ta ce "Mom no one like me haka zuciyata take bata tanƙwasuwa sai dai kawai kiyi haƙuri ki barni a yanda kika ganni, zuciyata ta dabance...." A tsawa ce Madam Nablah ta furta sunan ta cikin fushi, har yanayin ta ya fara canzawa, ƙwayar idanuwanta sun canza launin green, kafin yaran sun ankara Shapris ya yi saurin miƙe wa tsaye ya nufi Madam Nablah yana bata haƙuri akan ta sauƙo, ya tare ta yanda yaran baza su ganta ba domin ya fahimci basu san halin da mahaifiyarsu take ciki ba, Cikin ɓacin rai Madam Nablah ta rufe idanuwanta sosai sai da ta koma normal kafin ta ratsa ta gefen Shapris ta je har yanda Tasleem take tsaye gira a haɗe, hannunta ta cabko tare da wurga ta saman kujera tana faɗin "ki nutsu ki saurare ni..." Nasreen sarkin shiga damuwa tin tinin har hawaye sun fara zubo mata, ganin yanda mommy da Tasleem suke musayar yawu, ta rasa gane wannan matsalar har sun fara zargin cewa Tasleem ba lafiyar ta ƙalau ba... Asmeen kuwa asalin matsoraciya kenan, yanda ta ji Momminsu tana darara tsawa kamar wata dodonniya yasa jikinta ɗaukar rawa, ga yanda ta rurrungumi Nasreen tsabar tsoro.. Madam Nablah juyo wa tayi tana kallon su Nasreen sannan su ma ta basu izinin zama, ba mu su haka suka zauna dab da Tasleem kowacce jikin ta kamar wacce aka watsawa ruwa ba ƙwari sai Tasleem da take ta huci idonta akan Shaprees tana jin haushin sa domin saboda shi ake tsawatar mata... Shapris haƙuri yake ba wa Madam Nablah tare da faɗin "Sorry Madam control your self, ki daina biye wa yaran nan domin yarinta ke damun su..." Madam Nablah sauƙe numfashi tayi sannan ta ce "okay Shikenam yanzu inaso nayi abinda ya tara mu anan..." Su na cikin wannan halin sai ga Abeesh ya shigo da sallama a bakin sa, cikin nuna farin ciki Nasreen tayi saurin amsa masa tare da faɗin "your welcome my lovely bros..." Murmushi ya sau mata tare da shafa sumar kanta yana faɗin "Allah ya miki albarka my gimbiya..." Itama Asmeen masa sannu da dawowa tayi, ya amsa mata cikin kulawa tare da sanya mata albarka itama, Idonsa ne ya sauƙa akan Tasleem wacce ko ɗagowa bata yi ba balle yasa ran zata gaishe shi, murmushi yayi domin tin tinin yasan halin ta haka take a ko ina ma, bai biye mata ba haka ya sa hannu ya shafa gefen fuskar ta yana faɗin "my juju..." Itama hannu ta ɗora akan nasa tana jinjina masa kai amsuwar ta kenam, shirin barin falon yake ba tare da ya kalli yanda Madam Nablah take ba balle baƙon ta, Madam Nablah ce tayi saurin ƙiran sunan sa "Abeesh ba kaga baƙona bane?..." A slow Abeesh ya juyo yana kallon Shapris daga bisani ya ce "your welcome..." Shapris ɗaga masa kai kawai ya yi ba tare da ya furta komai ba, Abeesh juyawa ya yi zai wuce Madam Nablah ta ƙara dakatar da shi tana faɗin "Abeesh ka zo ka zauna ina son yin magana da ku gaba ɗaya..." Ko kallon ta bai yi ba ya ce "ba ki ga yanzu na dawo daga wurin aiki bane? ina buƙatar hutawa..." Madam Nablah ganin zai iya tizgata a gaban Shapris wanda yake matuƙar jin maganar ta ne yasa ta sauƙar da muryar ta tana faɗin "Abeesh just two minutes please..." Cije lips ɗinsa ya yi ta ƙasi sannan ya juyo cikin falon, samun kujera ɗaya yayi ya zauna shima.... Shapris abun mamaki ya bashi ganin Madam Nablah ta kasa control mutanen gidan ta hatta ƴar cikin ta amma sai tana bayyana tsoron ta da kwarjinin ta a mutanen waje, ya rasa gane dalilin haka, ta wani ɓangaren kuma yana tunanin har yanzu a cikin yaran gidan ta babu wanda yasan asalin wacece Madam Nablah ba, tana ɓoye musu kan ta shiyasa ta kasa hukunta su, Haka yake ta wannan tunanin har Madam Nablah ta katse shi da wata iriyar tambaya da ya daki dodon kunnen sa, Wannan tambaya ba shi kaɗai ba hatta sauran mutanen wurin tambayar ya girgiza su... Nasreen da Aasmeen zaro ido waje suka yi suka kallon Momminsu, tunani suke ayya kuwa wannan tambayar daga bakin mahaifiyar su ta fito?... Tasleem wacce take sunkuye da kanta ƙasi jin tambayar da mommy tayi ne yasa ta watso da gwala-gwalan idanuwanta kan Madam Nablah, idanu kamar zasu faɗo ƙasi domin duk ta fi sauran ƴan uwan nata manyan idanu sosai, sai take ƙara gwalalo su kamar wata aljana... Madam Nablah ƙara maimaita tambayar tayi idonta akan Shaprees tana faɗin "Shapris kai nake tambaya, shin a cikin waɗannan ƴan mata uku wacece ta fi burge ka? ina nufin ka zaɓi wacce tayi maka kamar yanda nayi maka alƙawarin zan baka ɗaya daga cikin triplets ɗina, to yanzu zaɓi nake baka domin ka cancanci haka...." Shapris haka yake bin ko wacce da kallo gaba ɗaya ya kasa gane wa zai zaɓa a cikin su domin duk kamannin su ɗaya, ya so ya nuna Tasleem amma sai dai duk sun hargitse kayuwan su bazai iya gane ta ba domin fuskar ko waccen su ba annuri jin wannan batun sai fuskokin su ta zama kamar na mutum ɗaya, Ganin bazai iya ware guda ɗaya a cikin su ba yasa shi kallon yanda Madam Nablah take yana girgiza kai ya ce "Madam kawai ki zaɓa mun da kan ki..." Madam Nablah ta ce "okay tinda kai ka buƙaci haka zan zaɓa maka..." Shapris ya ce "amma sai dai kiyi musu alamar shaida ta yanda zan rinƙa banbance su ..." Girgiza kai Madam Nablah tayi sannan ta ce "babu wata alamar shaida da zan musu, kai da kan ka zaka rinƙa banbance su..." Madam Nablah idonta ta sauƙar kan wacce take ƙarshen kujera ta furta "Aasmeen..." Aasmeen wacce take last sopa sai dai ƙirjinta ya buga jin ta ambaci sunan ta tana tsoron kar ita ce zata yiwa kyauta... Madam Nablah ta ce "inaso kiyi mun dariya yanzu..." Asmeen kallon Nasreen tayi wacce take gefen ta daidai lokacin da itama Nasreen ta kalle ta suka haɗa ido su na kallon juna, Lokaci guda Aasmeen ta fashe da kuka. Madam Nablah ta ce "dariya nake so ki yi mun ba kuka ba, kar ki ɓata mun lokaci..." Asmeen tsabar kuka ya ci ranta sosai kasa buɗe bakin tayi sai da Madam Nablah ta darara mata wata uwar tsawa tukun ta shiga taitayin ta ba shiri ta washe bakin ta tana dariyar dole... Madam Nablah kallon Shapris tayi sannan ta ce kaga wancan ita gushiryar haƙorin sama gare ta, ita ce Aasmeen kuma rabin raina, ina matuƙar ji da ita..." Shapris jinjina kai ya yi alamun ya gamsu. Madam Nablah kallon Nasreen tayi sannan ta ce "ke kuma ki mun murmushi..." Nasreen kallon mommy tayi sannan ta ce "Mom murmushi kuma?..." Madam Nablah ta ce "ko baza kiyi bane?..." Ta girgiza kai tare da faɗin "a'a Mom ban isa nayi jayayya dake ba..." Saida Nasreen ta rufe idanuwanta sosai kafin ta sau wata iriyar murmushin dole mai kama da kuka... Madam Nablah ta kalli Shapris sannan ta ce "ka ga wannan kuma dimple gare ta, ko magana take zaka ga kyawawan dimple su na lotse wa..." Madam Nablah ɗagowar da zata yi ta kalli Tasleem sai karaf suka haɗa ido, har sai da gaban Madam Nablah ya yanke tsabar ta tsorata da irin kallon da Tasleem take mata ga fuska a murtuƙe ba annuri, da sauri Madam Nablah ta kawar da idonta tana faɗin "Shapris ita kuma wannan ta hanyar idanuwanta masu firgitarwa zaka gane cewa Tasleem ce da kuma yawan fushi domin rabon da Tasleem tayi murmushi tin tana yarinya ƴar shekara 10 a duniya...." Madam Nablah tuna lokacin da Tasleem ta daina murmushi a rayuwar ta tayi, tin lokacin da ta jefa Abokinta Amaar Junaid cikin ƙaton rafi wanda yake cike da ruwa daga lokacin aka daina ganin farin cikin Tasleem, da zaka kwana kana nuna mata abun farin ciki bazata taɓa nuna wa ba, domin ba'a san farin cikin ta ba kullum sai baƙin ciki... Madam Nablah ta cigaba da cewa "ita ɗin sam bata nuna farin cikin ta a kowa kullum a cikin wannan yanayin za kana ganin ta, Tasleem Kenam...." Shapris jinjina kai yayi idonsa akan Tasleem sai yanzu ya gano ta.... Madam Nablah ta ce "Shapris na zaɓa maka ɗaya a ciki wato ita ce Aasmeen my lovely daughter...." Cikin tsoro da fargaba Aasmeen ta ce "why Mommy?...." Madam Nablah ta ce "Yes Aasmeen, bazan taɓa zaɓa miki abinda zai cutar da ke ba, saboda haka na ri ga da na yanke hukunci na, na mallaka wa Shaprees ke a matsayin matar sa ta Aure...." Sannan ta maida idonta kan Shaprees ta ce "Shapris ga Aasmeen na mallaka maka ita, inaso ka riƙe mun ita amana, na baka amanar ɗiyata Aasmeen..." Shapris ya ce "insha Allahu Madam zan riƙe ta kamar yanda kika umarta..." Shapris har cikin zuciyarsa bazai taɓa haƙura da ɗaukar fansar matarsa Sophia ba, dole sai ya ɗau mummunan hukunci akan jinin Madam Nablah ko wacece kuma yayi alƙawarin bazai taɓa ƙyale wannan ahalin ba..." Madam Nablah idonta akan Aasmeen ta ce "shi ɗin mutumin kirki ne, bazai taɓa cutar da ke ba..." Aasmeen tana kuka ta ce "Mom wani abu yana faruwa da mu, kin kasa sauraron mu a duk lokacin da muka kawo miki kukan mu, duk wanda ya fara Soyayya da mu mutuwa yake, dan Allah kar ki jefa rayuwar sa cikin hatsari..." Madam Nablah da Shaprees kallon juna suka yi domin Shapris yasan dole da hannun Madam Nablah akan abinda yake faruwa da ƴaƴanta, itama tasan ita take ai watar da hakan sai kawai ta wayance akan maganar tana faɗin "duk wanda kika ga ya mutu to lokacin mutuwar sa ne yayi, don haka ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru da Shapris..." Nasreen riƙo hannun Aasmeen tayi tana ƙoƙarin rarrashin ta... Madam Nablah ce ta kalli yanda Abeesh yake sannan ta ce "sai kuma Nasreen da Abeesh..." Nasreen da Abeesh duk ɗago kansu suka yi suna kallon juna daga bisani suka mayar da kallon su kan Madam Nablah, ta cigaba da cewa "na daɗe da tsara hakan a raina cewa Abeesh da Nasreen zasu zamo ma'aurata, don haka ya kamata ku ƙara fahimtar juna, na riga da na yanke hukunci na, hukunci na kuma shine dai dai, Nasreen da Abeesh ku fara tsara rayuwar ku kafin lokacin bikin ku..." Daga nan Madam Nablah ta miƙe tsaye tana faɗin, "Ke kuma Tasleem zan ji dake daga baya..." "Aasmeen idan kun kammala fahimtar juna ke da Shaprees ki kaishi order part na musamman yanda zai zauna sannan daga yau ke zaki na masa gyaran room ki kai masa abinci part ɗinsa, gyaran gado da wanke toilet room duk ke ce, kar ki kuskura naga kin yi masa ba dai dai ba, sannan bana son ganin house worker a part ɗin Shaprees domin shi ɗin naki ne, babu macen da ta fi cancanta taje part ɗinsa in ba ke ba, Wannan shi ake ƙira da training kafin Aure..." Kema Nasreen daga yau ke za ki na gyara part ɗin Abeesh ba ƴar aiki ba, idan naga ba kiyi abinda nace ba haƙiƙa zaki ga ɓacin raina, kina ji ba..." Nasreen gaba ɗaya ta ɗauke wuta domin bata taɓa tunanin zata Auri Abeesh ba, bata taɓa jin soyayyar sa ta Aure a cikin zuciyar sa ba, sai kuma tunanin Ayub ya faɗo mata a rai... A tsawace Madam Nablah ta ce "kina jin abinda nake cewa ko Nasreen?..." A firgice Nasreen ta amsa mata.. Madam Nablah bata tsaya ta ji daga bakin Abeesh ba kawai tayi tafiyar ta, kai tsaye upstairs yanda room ɗin ta yake ta nufa... Abeesh kallon ta kawai yake gaba ɗaya ya rasa abin cewa, yanda kasan an sa masa kwaɗo ya gagara yin magana,. Shima a fizge ya miƙe gudu-gudu sauri'sauri ya bar falon, domin haɗa shi da Nasreen da akayi ba ƙaramin nauyin ta yake ji ba, har kunyar haɗa ido yake da ita samm bai so wannan haɗin ba..... Tasleem ganin irin rainawa ƴan uwanta wayo da akayi ne yasa ta tashi cikin takaici ta haura saman upstairs zata shige room ɗin su, Nasreen tana kuka itama haka ta tashi ta haura upstairs room ɗin su... Aasmeen itama kuka take da sauri ta miƙe tare da shirin barin falon Shapris ya dakatar da ita yana faɗin "Amaryata shin baza ki kaini wurin mazaunina bane?..." Asmeen tsayawa tayi idonta akansa yanda suka yi jawur domin haɗin yazo mata a bazata, tsoro da fargaba duk ya ratsa ta bugu da ƙari bata san shi ba, bata taɓa ganinsa ba lokaci guda ace an bayar ta a shi, abun yana ƙona mata rai...... NEXT NEXT NEXT New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 9 to 10 Shapris miƙe wa ya yi tare da tako wa har yanda Asmeen take a tsaye, a gaban ta ya tsaya yana ƙare fuskar ta da kallo a yayin da ita kuma take kallon ƙasi ta kasa haɗa ido da shi, hannu yasa ya ɗago da haɓarta a hankali ta sauƙe kyakkyawan idanuwanta akan fuskar sa tana bin sa da kallo daga bisani ta kawar da kanta gefe tare da faɗin "mu je na kai ka part ɗin ka...." Sauƙe numfashi ya yi tare da bin bayan ta suka bar falon, sai dai suka fita can compound na gidan kafin suka hau wani beni mai hawa uku acan aka tanadar masa da tsararren part site ɗin sa, Su na shiga falon suka tarar an tsara komai, komai da komai na rayuwar duniya an zuba a falon, ba abinda zai nema ya rasa, falon kaɗai ma abun kallo ne, Murya ciki-ciki Asmeen ta furta "inaso zan koma part ɗin mu..." Murmushi Shaprees ya sau tare da faɗin "baza ki rakani ciki ba ne?..." A ruɗe ta furta "ciki kuma?..." Ya ce "eh! ko baza ki iya ba? sai na ƙira Mommyn ku a waya tazo ta shigar dani ciki..." Aasmeen kamar zata yi kuka ta ce "Shikenam! four bedrooms ne a site ɗin nan, ka zaɓi a wannan kake son zama?..." Sai da ya baza eyes sannan ya ce "aina bedrooms ɗin suke?..." Idonta na kallon gefe ta furta "duk su na upstairs, 2 su na hawa na biyu, 2 a hawa na uku..." Goya hannayensa ya yi akan ƙirji yana hura iskar bakin sa da alamun akwai abinda yake tsarawa a cikin ransa, Ya ce "Ok mu je hawa na ukun, domin bana son zama a farko-farko, kinsan mijin ki matsoraci ne..." Su na cikin wannan halin sai ga wasu security su biyu sun shigo da kayayyakin sa, daga nan ya sallame su, gyaran murya ya yi sannan ya ce "my Bride zaki iya taya ni ɗaukan jakakkunan nan?..." Ba tare da ta furta komai ba tasa hannu ta ɗauki kaya biyu tabar masa sauran biyun ta haura saman upstairs, Shima murmushi ya yi ya ɗauki sauran ya bi bayan ta.... Sai da suka hau saman upstairs ta uku sannan suka buɗe room ta ƙarshe suka shige, ga wantalelen gado da kujeru ata gefe guda har da plasman da ƙaramin frig, ta wani site guda dake cikin bedroom wardrobe ne da mirror and drowers, da kuma bathroom, su na shiga ta ajiye masa kayayyakin sa tayi saurin juyawa zata fice yayi saurin dakatar da ita, ba tare da ta juyo ba ta ce "na gama maka komai ai yanzu..." Goya hannayen sa ya yi akan ƙirji tare da murtuƙe fuska kamar bai taɓa yin murmushi ba, zuciyar sa kawai take haurowa da zaran ya tuno da matar sa Sophia, Cikin ɗaga murya ya furta "Keee!..." Cike da mamaki Asmeen taji wannan

Chapter 5 of 34