A ruɗe ya zo gunta yana faɗin "a'a kar kiyi kuka Tasleem, zamu yi wa Mommy wayo kema ki biyo mu, kawo kunnen ki na gaya miki wata magana..."
Kama kunnen ta yayi ya mata raɗa a kunne, tana dariya ta ce "yeee haka zan yi wa mommy wayo..."
Tana faɗin haka ta tafi da gudu ta je ta buɗe bayan both ɗin mota ta shige, shi kuma ya buɗe back seat ya zauna, ba jumawa ta dawo itama ta shiga taja motar suka tafi, tafiya taƙi ƙarewa saida sukayi tafiya mai nisan gaske har sai da bacci ya ɗauke Tasleem a bayan both,
Basu tsaya a ko ina ba sai a cikin daji kusa da bakin wani rami mai ɗauke da ruwan gaske wanda ba'a iya ganin ƙarshen ruwan, tana huci ta ce "Amaar sauƙa..."
Cike da tsoro da fargaban wurin yana kallace-kallace ya fito daga motar, babu kowa sai kukan tsuntsaye da kuma ƙarar tafiyar ruwa...
A ruɗe ya kalli Madam Nablah wacce itama fitowar ta kenan ya ce "Mommy ina ne nam?..."
Tasleem itama tashin ta kenam daga bacci taji Amaar yana tambayar ina ne nam, cike da zumuɗi ta haura saman kujerun motar ta fito ta ƙofa, kallace-kallace ta fara yi itama, tana tsaye a jikin mota ta bayan Madam Nablah, Amaar yaga fitowar Tasleem amma sai ya nuna bai ganta ba saboda a ɓoye tazo ta, sai ji suka yi Madam Nablah ta furta
"Amaar nan ɗin wurin mutuwar ka ne, anan zaka mutu..."
Amaar yana zazzaro ido waje cike da tsoro ya ce "waye zai kashe ni?..."
Dariya Madam Nablah ta yi sannan ta ce " Ni mana, waye zai kashe ka in ba ni ba, Ni ce ajalinka..."
Kuka Amaar ya fara yi yana faɗin "me na miki zaki kashe ni?..."
Madam Nablah ta ce "baka kai nayi maka bayanin abinda nayi niyyar yi ba..."
Lokaci guda idanuwanta suka chanza colour sai ga fiƙoƙi sun fito waje nan ta zama Kura, Amaar ja da baya yake har ya faɗi ganin Kurar tana yo wa kansa yasa ya miƙe da gudun gaske, itama Kurar bin bayansa tayi, Tasleem ganin abu yana shirin fin ƙarfin idanuwa sun ƙafe baki ya gagara rufuwa, kamar wacce aka zabure ta tayi wani irin ihu tare da furta "Amaaaaarrrrrr...."
Itama ta bi bayan su da gudu, gudu kaɗan tayi ta rinke su Amaar yana kwance a ƙasi yanda ya faɗi sai Kurar da take ta huci a gaban sa, Tasleem tana kuka ta ce "Mom daman ke ce a cikin mafarki na, shine kika ce mafarki ba gaskiya bane ashe ke ce mai ƙarya..."
Jin maganar Tasleem ata baya ne yasa Kurar juyowa dai dai lokacin da ta dawo asalin mutum ɗin ta tana sanye da baƙaƙen kaya ga idanuwa yanda suka canza launin kore, Madam Nablah mamaki take ta yanda Tasleem ta biyo su,
Tasleem da gudu ta je wurin Amaar ta faɗa jikin sa tare da rungumar sa sosai tana kuka tana faɗin "Mom bazan bari ki kashe mun Amaar ɗina ba, ke ke ke ɗin ba mutum ba ce..."
Amaar shima kuka yake ya rungumi Tasleem sosai yana faɗin "Tasleem dan Allah kar ki bari Mommyn ki ta kashe ni, ita ɗin ba mutum ba ce, zata kashe ni..."
Murmushi Madam Nablah ta yi taje yanda suke zata raba su, haka suka ƙanƙame juna suna ihu, duk da yara ne amma ta kasa ɓanɓare su ga ihun da suke yi gaba ɗaya sun takura ƙwaƙwalwar ta sam bata ƙaunar ƙara ko ihu ko kiɗa mai sautin gaske....
Wani dabara ne ya faɗo mata a rai, ta lumshe ido tare da tsafe musu jiki da tsafin hannunta, nan suka fara jin shocking yana ratsa jikin su kamar electric, ba shiri suka rabe da juna duk suka watse gefe guda, Madam Nablah riƙo hannun Amaar tayi ta ɗago shi tsaye tare da jan sa suka fara tafiya, ganin haka yasa itama Tasleem ta jajirce ta miƙe ta bi bayan su da gudu tana faɗin "Mom kar ki kashe mun Amaar dan Allah, Amaar! Amaar!! Amaar!!! wayyo Allah, Mom kiyi haƙuri...."
Shima haka yake waiwayo wa yana miƙa wa Tasleem hannu tare da faɗin "Tasleem dan Allah ki taimake ni, kar ki bar mominki ta kashe ni, Tasleem ki taimake niiiii...."
Madam Nablah sai da tazo bakin ramin ruwa tukun ta ɗaga Amaar sama zata jefa shi ciki,
Tasleem tana ihu ta ce "Mommmmm! kar ki jefa mun shi cikin ramin nan, ruwa ne a ciki zai mutu mommy...."
Ai kafin Tasleem ta rufe baki har Madam Nablah ta sau shi ciki,
Tasleem a ruɗe tasau wani irin ihu ta taho da gudu itama zata faɗa Madam Nablah tayi saurin riƙo ta suka koma baya, haka Tasleem take dukan mommynta aka ta sake ta zata bi Amaar, ganin bazata sake ta ba yasa ta kafa hakwaranta ta garzaya mata cizo anan ta kuɓuce tayi bakin rami da gudu itama tayi tsalle ta faɗa cikin rami,
A gigice Madam Nablah cikin tsoro da fargaba tayi wani tsafin ta sai ga hasken green yana fita daga cikin tafin hannayenta guda biyu da wannan tsafin ta ɗago da Tasleem sama kafin ta ƙarasa cikin ramin, haka ta miƙar da hannayenta sai ga Tasleem ta tafo gare ta cikin iska, a ruɗe ta kamo ta tare da rungumar ta sosai tana faɗin "ki dakata da wannan shirme nakin..."
Tasleem gaba ɗaya ta fita hayyacinta ko motsi bata iya yi sai bakin ta dake furta "Amaar! Amaar!! Amaar!!!...."
Da wannan sunan ta sume akan cinyar mahaifiyar ta, a lokacin Madam Nablah ta wallafa wani tsafin ta tana shafar sumar kan Tasleem tare da faɗin "ki manta da wannan al'amarin da ya faru akan idonki, ina so bakin ki ya rufe akan ƙiran sunan Amaar, bakin ki ya toshe, tunanin ki ya gushe yanda bazaki iya tuna duk abinda ya faru dake ba, Tasleem! ko a mafarki bana son wannan al'amarin ya dawo miki...."
Haka take ta wannan surutan tana shafa kanta, duk sai da ta mantar da ita komai har Amaar a cikin ƙwaƙwalwar ta, daga nan ta ɗauke ta tare da nufan mota ta kwantar da ita a back seat, sannan itama ta shiga ta ja mota suka tafi.......
New Book 2025.
*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)
A Fictional Story✍️
Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal
Which is best known as
*Asmeetah writer*
*WhatsApp 09065443871*
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
EP 11 to 12
Cigaban labarin......
Wata zurariyar mota ce GLK 350 4matic ta parker a wurin parking beside Supermarket.
Wacce take back seat ce ta fara fito wa kana ganin ta kasan ƴar hutu ce, tana sanye da Swiss Lace mai bala'in tsada da ɗaukar ido, komai nata two match ne sai black glass mai designer da ta toshe eye ɗinta da shi,
Tana rufe murfin motar sai ga wata ta ƙara fito wa ta front seat the same irin kayan wanca ne a jikin ta, sai ga ta uku wacce take driving itama ta fito still irin shigar sauran biyu, Ƴan uku masu kamanni ɗaya sun jeru komai nasu iri ɗaya sai taku suke irin na sarakuna, mutanen wurin kowa idonsa akan su, wasu har da video domin kowa ya sha'awance su amma kowa fargaban tinkarar su yake domin babu wanda bai san ƴaƴan Madam Nablah ba ce, Yaran da duk wanda ya kulasu ƙarshen rayuwar sa kenam sai dai a gani da ido a ƙyale..
Tasleem tana tafiya tana juyar da key ɗin mota dake hannun ta, kai tsaye cikin supermarket suka shige, su na shiga ko wacce ta bi layin kayan da take son ɗauka,
Nasreen layin kayayyakin drinks ta bi domin idan ta shigo abinda take fara ɗauka kenan kayan fruits, tana taku a hankali tare da duba abubuwan da take so ba tare da ta duba gaban ta ba ta yi tuntuɓe da wani Basket da yake ajiye akan hanyar da zata wuce sauran kaɗan ta kife a ciki, mutumin da ya ajiye kuwa shima yana tsaye ya juya bayansa yana ta waya, jin motsin mutum ne yasa shi juyo wa yana faɗin "oh my god sorry my sister, fatan baki ji ciwo ba..."
Cikin murmushi Nasreen ta ɗago tana faɗin "No kar ka damu, ban ji komai ba..."
Ɗagowar da zata yi suka haɗa ido, zaro ido tayi cike da mamaki tana faɗin "kamar na taɓa ganin wannan fuskar koh..."
Cikin rashin fahimta ya ce "aina kenam?..."
Nasreen ta ce "nasan daman bazaka iya tuna da mu ba amma mu kam a duk inda muka ganka zamu gane ka, domin zuciyoyin mu basa manta wanda ya kyautata musu..."
Mutumin murmushi ya yi sannan ya ce "naji kamar jam'i kike, wata ƙil ba ke kaɗai kika gane ni a yanda muka haɗu ba ko?..."
Nasreen jinjina kai tayi sannan ta ce "Ni da ƴan uwana, amma nayi mamakin rashin gane mu daka yi, amma ba abun mamaki bane domin duk wanda yake soyayya baya taɓa ganin fuskar mace in ba ta masoyiyar sa ba...."
Bai san lokacin da ya saki dariya ba
Ya ce "ke da kanki kinyi tambaya sannan kin bawa kan ki amsa, oh daman haka duk wanda ya faɗa soyayya yake? to wata ƙila nima hakan ne shiyasa na kasa gane ki..."
Jinjina kai Nasreen tayi sannan
Ta ce "Okay! akwai wasu ƴan mata uku da ka cecesu daga hannun Kura a filin school of UNIMAID..."
Amaar Junaid cike da mamaki ya ce "Okayyy! Na tuna, kune ƴan ukun nan?..."
Da sauri Nasreen ta amsa masa cikin fara'a...
Su na cikin wannan halin sai ga Asmeen ta nufo wurin su tare da faɗin "Nasreen da wa kike tsaye ne shin kin kammala ɗaukan abinda zaki ɗauka ne?..."
Nasreen ta ce "Asmeen shin kin gane wannan bawan Allah?..."
Buɗe baki Asmeen ta yi cike da mamaki ta ce "laaa! wannan ba wancan sojan da ya taimaka mana a school ba ne?..."
Nasreen ta ce "shine mana..."
Amaar da murmushi akan fuskar sa ya ce "a cikin ku wacece marar lafiya?.."
Asmeen ta ce "kana magana akan ɗayar ƴar uwar tamun ne? babu ita a cikin mu, ni sunana Asmeen wannan kuma Nasreen, munyi farin cikin haɗuwa da kai, shin ko zamu iya sanin sunan ka?..."
Nasreen kallon ta tayi ta ce "Ke fa kin cika surutu, kin san irin waɗan nan basa son surutu da yawa..."
Asmeen ta ce "An gaya miki shi ɗin kamar Sister mu ta gida ne..."
Amaar ya ce "kar ku damu I'm a simple Man, ni ɗin ba kamar yanda ku ke tunani bane, na kan iya rayuwa da kowa cikin mutunci da daraja,
ni surutu na ma har ya zarce na Sis Asmeen..."
Asmeen tayi wani irin tsalle ta ce "wow to kin ji fa, zamu zo ɗaya da shi, please zaka iya bamu number wayan ka, ai zamu na gaisawa...."
Nasreen ta ce "Da farko dai mu fara jin sunan sa..."
Sauƙe numfashi ya yi sannan ya ce "Sunana Major A.J..."
Nasreen ta ce "Ma sha Allah..."
Asmeen ta ce "wow kin ji fa suna mai daɗi wai Major A.J, am to number waya..."
Ya ce "okay bari na baki..."
Asmeen ta ce "tsaya tsaya kafin nan zamu iya yin selfie?..."
Amaar ya ce "why not..."
Nasreen ta ce "Asmeen abin nakin ya fara yin yawa, ki bar shi haka kar daga yanzu mu gundure shi..."
Asmeen ta ce "haba one selfie kam wani gundura..."
Kafin su ankara suka yi wani mutumi ya yi magana yana faɗin "Ɗan uwa kayi nesa da waɗannan yara domin zasu zamo Ajalin ka, su ɗin Mayu ne duk namijin da ya tsaya da su sai ya mutu...."
Nasreen zaro ido waje tayi har eyes ɗin ta sun cicciko da hawaye cikin tsoro da fargaba ta riƙo hannun Aasmeen...
Itama Asmeen jikin ta ba ƙaramin sanyi ya yi ba, lokaci guda farin ciki ya ɗauke akan fuskar ta, ƙararar damuwa ne akan fuskar..
Amaar cikin rashin fahimta haka yake kallon mutumin daga bisani ya ce "ban fahimci abinda kake nufi ba..."
Mutumin ya ce "inaso ne na ceceka daga munguwar hallaka, waɗannan ƴan mata su ɗin Annoba ne, basu da aikin yi sai kisa da shan jinin matasa duk wanda yace yana son su ko ya yi gigin tsayawa da su..."
Amaar maida idonsa yayi kan su yana mamakin irin furucin da ake akan su, cikin sassanyar murya ya furta "wai da gaske ne?..."
Asmeen girgiza kai ta fara yi tana kuka, a razane Nasreen ta riƙo hannun Aasmeen tare da faɗin "kin ga zo mu tafi..."
Ba shiri suka bar wurin...
Amaar kallon mutumin ya yi sannan yasau murmushi yana faɗin "shin akwai wata hallakar da zanyi a gaba wanda ya wuce na baya??..."
Mutumin ya ce "Ni dai na gaya maka gaskiya yauwa sai anjuma..." daga nan yayi tafiyar sa...
Amaar tsayawa yayi wuri ɗaya tare da lumshe idanuwansa, ƙwaƙwalwar sa ce ta fara tariyo masa abubuwan da suka faru da shi kamar a mafarki,
Fuskar Madam Nablah da bazai taɓa manta kamannin ta ba ya fara gani lokacin da ta zama Kurar daji, da idanuwanta da suka canza zuwa wani launi da ban, da lokacin da Madam Nablah ta ɗaga shi sama ta sake shi a cikin ramin ruwan hallaka dai-dai lokacin da Nasreen da Asmeen suka ƙwalla ƙiran sunan Tasleem,
A ruɗe ya buɗe idanuwansa jin wannan sunan da bazai taɓa manta shi a cikin ƙwaƙwalwar sa ba, jin suna ta ƙiran sunan Tasleem yasa ya nufi wurin su da gudun gaske, domin a duk yanda yaji mace mai suna Tasleem sai ya neme ta sannan ya yi ƙoƙarin taɓa koda hannun ta ne domin tabbatar da asalin Tasleem ta hanyar jin shocking,
A yanzu ya samo asalin Tasleem ɗinsa wato ƴar uwar su Nasreen da Asmeen...
A bakin titi ya iske su suna tsaye su biyu Nasreen da Asmeen ko wacce da damuwa akan fuskar ta,
Muryar Amaar suka ji yana faɗin "lafiya kuwa??..."
Nasreen da Asmeen a tsorace suka juya suna kallon sa tare da kawar da idonsu suna kallon mutanen wurin, kowa idonsa akan su ana nuna su alamar maganar su ake.
Amaar ne ya sake furta "me yake faruwa ne?..."
Nasreen ce tayi ƙarfin halin cewa "Ƴar uwar mu ce ta fito cikin damuwa ta shige mota ta tafi, bamu san ina ta tafi da motar ba..."
Asmeen ta ce "naga an ƙira ta a waya kamar wani magana aka sanar mata, daga nan ta tafi da sauri cikin fushi..."
Nasreen ta ce "ke ma dai kinsan koda yaushe a cikin fushi take, yanzu aina zamu same ta?..."
Amaar ya ce "ga can mota ta shin zan iya kai ku yanda take?..."
Nasreen ta ce "a'a bama son wani abu ya faru da kai, mun gode zamu jira ta..."
Amaar ya ce "ku na nufin kuce na gamsu da abinda wancan mutumin ya faɗa akan ku?..."
Asmeen ta ce "ka yadda da shi tabbas abinda ya faɗa maka gaskiya ne, shiyasa muke rayuwarmu mu kaɗai, babu wanda yake shiga shirgin mu..."
Amaar ya ce "kar ku damu akan abinda mutane zasu ce akan ku, Indai kuna da kyakkyawar zuciya babu wanda zai ci galaba akan ku, ni ina tare da ku babu abinda zai cutar da ni..."
Nasreen da Asmeen har zuwa wannan lokacin basu dawo normal ba, ko wacce da hawaye akan fuskar ta...
Amaar ya ce "a matsayina na ɗan uwanku Musulmi inaso ku mun wata alfarma dan Allah..."
Nasreen ta kalle shi cike da mamaki ta ce "wani irin alfarma?..."
Da murmushi akan fuskar sa ya ce "inaso ku bani dama na zama abokin ku na amana, wanda zai rinƙa saka ku cikin farin ciki sannan mai tare muku faɗa a koda yaushe..."
Nasreen da Asmeen kallon juna suka yi sannan suka mayar da eyes ɗin su kan sa, Nasreen ta ce "har ka tuna mun da wani ɗan uwan mu wanda muka rasa shi tsawon shekarun baya, ya kasance shine mai tare mana faɗa kuma mai kishin mu, mun rasa shi har abada..."
Asmeen tana hawaye ta ce "YA AMAAR..."
Nasreen itama tana hawaye ta jinjina kai...
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 34