da Baƙin hayaƙi....
Cikin murya mai taushi wacce ke cike da haɗari, aljanar ta ce:
"Ni ce Bahrasha, uwargidan duhu uwa ga kowace mugunta.
Catrina ‘yata daga jini, na jiyo kiran ki... yanzu lokaci ya yi da zamu yaga sararin haske tare."
Tasleem ta ja baya da sauri, idonta yana haskawa, jikinta ne ya soma rawa saboda ƙarfinta yana raguwa.
Catrina ta miƙe daga ƙasa kamar halitta wacce aka rina da jini, ta ce:
"Hah! Kina tunanin ke kadai kike da gata daga haske?
Ni ma ina da nawa gata daga duhu.
Tasleem... yanzu faɗan ba tsakanin ki da ni kadai bane.
Yanzu Bahrasha ce zata koya miki yanda ake narkar da zuciya mai yawan gafara da ƙauna!"
A take Bahrasha ta miƙa hannunta zuwa cikin iska – sai wata zobe ta bayyana – zobe mai cike da jinin halittun da ba a san su ba. Ta miƙa wa Catrina, ta ce:
"Sa zoben jinin hauka domin ki jujjuya ki zama mace ba mutum ba
Ki zama Zarimar Duhu!"
Catrina ta amsa ta saka zoben, tana yin haka sai jikinta ya canza ta girma ta zama babbar halitta wacce jikinta ke huda sararin sahara da ƙura.
Tasleem kuwa ta dafe ƙirjinta, jikinta yana rawa, Haske yana ƙoƙarin ɓacewa, runtse ido tayi tana magana a cikin zuciyarta.
Ta ce cikin ranta:
"Haske ba iko kawai ba ne
Haske shi ne zuciyar da bata yarda da zalunci ba,
Shi ne idon da ke ganin mai laifi amma ya farka da addu’a...
Amma yau... Na yarda in tsaya domin kare aiki na ."
Haske ya sake ɓarkewa daga jikinta kamar wani tauraro da ya fashe a cikin duniya. Ta miƙa hannunta, ƙasa ta buɗe, wata garkuwar haske ta taso – tana fuskantar Bahrasha da Catrina.
Bayan Catrina ta sha zoben jinin hauka daga Bahrasha, ta canza zuwa wata baƙar halitta, gashinta ya tsawaita har zuwa ƙasa, fuskarta ta haɗu da wani irin tsufa da kwalliya mai ban tsoro.
Idonta huɗu ne yanzu – biyu masu jini, biyu kuma kamar hantsi a cikin duhu.
A bangaren Tasleem kuwa, bayan ta taso da hasken zuciyarta, ta miƙa hannu cikin iska ta furta da wata murya tana faɗin:
"Ya hasken ruhi,
ku buɗe ƙofofin ceto, ku aiko ma'abotan haske."
Sama ta tsage. Wata murya mai tsarki ta sauka daga sama:
"Anji kiran ki Sarauniyar Hasken Ruhi.
Kiyi maraba da ’Yan Agaji na Hasken Tabbas!"
Nan da nan haske ya fashe a sararin Sahara. Daga cikin hasken suka sauko:
Jundum – Wani babban halitta mai siffar mutum yana tafe da fuka-fuki masu walƙiya.
Rayyaa – Mace mai siffar haske gaba ɗaya, idanunta masu kukan adalci.
Sabeeh – Yaro ƙarami da jiki mai murɗaɗɗen haske, yana tafe da takobi wanda duk sanda ya buga shi ƙasa, ruhi mai kyau yana fita daga ƙasa.
Bahrasha da Catrina ganinsu yasa duk suka tsorata. Bahrasha ta furta:
"Toh, shima hasken yana da mabuƙata? Lallai yau sahara zata sha jini!"
Catrina kuwa ta ɗaga hannunta, ta saki wata ƙira kamar kukan dodo tana faɗin:
"Masu tarin duhu, ku fito daga ɓoyayyen duniya!
Ya ku halittun da na raya da kishi da tsoro, ku tsaya gaban haske yanzu!"
Wani irin ƙara ne ya sa ƙasa ta tsagei! Daga cikin ƙasa suka fito:
ZAKFURA – Halitta mai jikin maciji da fuskar mutum da wuya.
MAYURIN ZUCIYA – Wata halitta da ke ciyar da kanta da fushin mutane.
GALMASH – Halitta mai numfashi mai kone numfashin haske, tana rayuwa cikin kishi da munafunci.
FAƊA YA FARA CIKIN GASKIYA
Sabeeh ne ya ruga da gudu, takobinsa na walƙiya ya ɗaga sama tare da buga shi ƙasa ya haifar da rami mai kakkarfar haske ya bugi ZAKFURA a take ta faɗi haske na ƙone ta tana ihu...
Rayyaa kuwa wacce take fafatawa da Aljani Mayurin zuciya ta kifa fukafukanta ta fitar da murya mai ɗaukar ruhi mai duhu.
Mayurin Zuciya ya soma rawar jiki – yana ɓari – ya faɗi sumamme.
Jundum ya daka ƙara, ya bugi Bahrasha da wata garkuwa mai nisan haske, har sai da ta faɗi gefe tana tari jini.
Tasleem da Catrina sun sake haɗa ido. Catrina cikin murya mai ƙasƙantar zuciya da mugunta ta ce:
"Wannan ba faɗar ƙaramin iko bane.
Wannan faɗar zuciyarmu ce Tasleem.
Ki bani zuciyarki, mu raba haske da duhu...
Ki bani zuciyarki, in bar miki Abeesh..."
Tasleem ta amsa da karfi:
"Zuciyata tawa ce kuma na san darajarta, bana son in rasa abin da nake tsaye akai
Ina tsaye akan gaskiya, ƙauna da yanci!
Kuma a yau – ba za ku ƙara shan nasara ba!"
Cikin wannan lokaci ne wata ƙara ta buga daga nesa alamar cewa wani babban halitta daga haske ko duhu yana isowa...
Guguwar iska ta tashi cikin Sahara da hayaniya, lokacin da rana ta mai launin zinariya ta bayyana a sararin sama, wani haske ne mai sanyi da kwantar da zuciya ya sauka daga can…
Wannan ba kowa bace fa ce MIEMIE...
Miemie ce!
tana sauƙowa, gashinta na tafe kamar ruwa mai tsarki, fatar jikinta na haske kamar zinariyar dare. Idanuwanta sun cika da tausayi amma sukan ƙone dukkan duhun da suka kalle su da ƙyashi.
Kafin kowa ya ankara, ƙasa ta sake bugawa da ƙasa! Wani ƙaho na wuta ya huda sararin sama, zafi da hayaƙi da ƙamshin turaren ja suka mamaye saharar.
Madam Nablah ta bayyana.
Wuta tana tashi daga dukkan sassan jikinta. Hannunta biyu suna ci da harshen wuta, idanunta masu launin wuta sun cika da ƙarfi da ikirari.
Zuciyarta cike da mugunta domin tana ƙaunar 'ya'yanta, amma ba ta san tausayin duniya ba.
Lokacin da suka haɗa ido da Miemie, sahara ta girgiza....!
Miemie ta ce da murya mai taushi amma da nauyi kamar ruwa mai zurfi:
"Na zo ba domin ki ba, Nablah. Na zo domin kare gaskiya daga hallaka,
Amma yau zan tsaya gaban ki — domin ke da kanki kin zama hatsarin duniya."
Madam Nablah ta kalli Miemie da murmushi amma idonta na hura wuta ta ce:
"Kin zo ne domin kare gaskiya amma ki sani cewa wannan gaskiyar da kuke ƙoƙarin karewa jini na ne,
Ina da abin da ba ki da shi, Miemie. Ina da ƙiyayya da yaƙi.
Kuma yau zan nuna miki cewa wuta ba ruwa ba ce."
Nan faɗar ta ɓarke.
Miemie ta ɗaga hannu ta ƙira ruwan sama daga wani duniyar ruwa, ruwa mai daraja kamar lu'ulu'u ya sauƙo ya fara zagaye ta.
Madam Nablah kuwa ta fitar da harshen wuta daga zuciyarta, yana huda sanyi yana ƙone duk sanyin da ke kusa, a lokacin ta addasa zafi mai tsanani.. a yayin da sanyin ruwan Miemie ke ƙoƙarin kawar da zafin wuta....
Harshen wuta da ruwa ne suka haɗu ya fashe da wani irin ƙara wanda ya tarwatsa tsaunuka a gefe.
Tsuntsaye a sama suka fāɗi matattu. Rana ta dushe....
A gefe guda:
Tasleem tana fuskantar Catrina da Bahrasha.
Bahrasha ta fitar da kaho, tana ƙara tare da faɗin
"Na ɗauki zafi daga ruwan jini! Wani haske bazai iya kankare ni ba!"..
Tasleem kuwa ta kalli Bahrasha da dariya mai izza ta ce:
"Ke ne ake tsoro a cikin duhu? To, yau ki tsorata da hasken zuciyar wacce ku ke son cin amanarta!"
Ta fitar da wani garkuwa mai launin haske ta buga ta a ƙasa, wata walƙiya ta fito ta sare ƙafafun Catrina, tayi sama kafin ta faɗo ƙasi, Catrina ta zama gungume domin ƙafafun ta da hannayen ta ne duk suka watse gefe guda tana ihu domin ba ƙaramin raunana tayi ba....
Amma dake Aljana ce sai ta ƙara haɗe gaɓoɓin jikinta suka dawo normal...
Bahrasha ta ruga da gudu kamar giwa tana shirin yaƙar Tasleem, amma kafin ta iso yanda Tasleem ta ke, itama Tasleem ta yi tsalle tare da buga thunder hannunta ƙasa, har sai da Brahrasha ta tashi sama kamar guguwa ta faɗi gefe tsabar ƙafin haske...
ƘARFI DA ƘARFI: HASKE DA DUHU
A yanzu, halittun haske (Jundum, Rayyaa, Sabeeh da wasu sabbin) suna fafatawa da Galmarsh, Zakfura, da Mayurin Zuciya waɗanda suka farfaɗo da sabbin ƙarfi.
Faɗar da ba’a taɓa gani ba – faɗar da take canza nau’in duniya.
Sahara ta yi shiru.
Wuta da ruwa sun haɗu suka zama hayaƙi mai haske.
Madam Nablah da Miemie suna tsaye a sararin sama, jini da gumi na ratsawa jikinsu...
Tasleem tana ƙasa cikin kallo mai cike da mamaki — tana kallon Mahaifiyarta Madam Nablah, ba ta taɓa sanin cewa ikon mahaifiyarta ya kai wannan matakin ba.
A hankali take furta
"Shin wannan ita ce uwata wacce ta haifeni? Ita ce ta tsare ruhi da haske da duhu a jiki guda? Shin ita ce ta fi wuta zafi?..."
Zuciyar Tasleem na bugawa, yayin da hawaye suka cika idonta.
Kaff Aljanu da Jagororin hasken duk tsaya kallon faɗan manyan shuwagabannin suka yi,
Madam Nablah da Miemie...
Miemie cikin ƙarfin iko ta haɗa ruwa ta jefa Madam Nablah a ciki...
Tasleem har zata ruga da gudu wurin Madam Nablah ganin yanda aka jefa ta a ruwa mai yawan gaske, kafin ta motsa taji an riƙo hannun ta, tana juya wa ta haɗa ido da Miemie...
Miemie ta tsaya kusa da Tasleem, tana kallonta da idanuwanta masu launin ruwan sanyi.
Tasleem ta runtse ido, tana jin wani irin nutsuwa daga halittar da ba ta taɓa ganinta ba, amma zuciyarta ta yarda da ita gaba ɗaya.
A hankali ta furta
"Ke ba irin su bane... Ke haske ne..."
Miemie ta ɗora hannu a kan kafadar Tasleem, ta ce da murya mai sa hankali ya mutu:
"Haske bai faɗi ba. Amma idan haske da wuta suka ƙone juna, babu abinda zai rage sai ƙura. Don haka... sai a yi ƙoƙarin dakatar wa ta hanyar sadaukar da ɗaya.....
A gefe guda
Madam Nablah tana gefe, wanda fitowar ta kenan daga cikin ruwa tana huci da zufa, sai kuma ta fara nazarin ƴarta Tasleem, yanda zata ɗauke ta, ta rabata da ahalin haske gaba ɗaya....
Wata murya daga cikin zuciyarta ta ce:
"Zan rasa ƴaƴana gaba ɗaya idan na ci gaba da wannan yaƙi... Nasreen tana hannu na a killace..... Asmeen tana gida duk da nasan baza'a taɓa samun matsala daga ɓangaren ta ba domin yarinya ce marar wayo, so nake ta kasance da mijinta har su sama mun yaro wanda zai yi sanadiyyar ɗaukaka ta....sannan kuma Tasleem a yanzu zata faɗa tarkona....."
A can ɓangaren gida...
Amaar ya dawo gida cikin hanzari, tare da Asmeen da Shaprees da Abul.
Gidansu na cike da alhini, saboda duk sun tabbatar da cewa Abeesh ya ɓace.
Asmeen ta zauna cikin firgici, tana tunanin Tasleem da babu labarinta, itama basu san yanda ta je ba, ga samuwar rashin Nasreen...
Shaprees ya yi tagumi fuska a hargutse yana bin kowa da idanu masu ɗauke da mamaki, da jinjina lamarin da ke faruwa...
Abul kuwa, yana kuka a hankali, yana cewa:
"Na san wannan ƙaddara ce… amma a ina Abeesh yake? Wane ne zai iya ɗaukar shi daga asibiti har a ɓoye shi kamar iska?"
Amaar ya lumshe ido, yana jin wani abu ba daidai ba...
---
Yayinda Miemie ta fuskanci Madam Nablah bayan ta bayyana musu kamar iska, domin sun san ba zata taɓa mutuwa ba, su na so ne su kawo ƙarshen yaƙin
, ta ce:
"Nablah... Ƙiyayyarki ta cutar da duniya, amma so da kika ɓoye ya ceci ƴarki... Kuma zan baki zaɓi: ko ki daina, ko kuma ki rasa ta."
Madam Nablah ta ce da murya mai kaifi cike da izzah ta furta:
"Ba na jin tsoro... Amma ina jin zafin rasa ƴa... Idan hakan zai ceci Nasreen, Asmeen da Tasleem, zan tsayar."
Ta dakatar tare da jan yo Tasleem jikinta tana faɗin
"Wannan ƴata ce ta jini, bazan taɓa sadaukar da ƴata a gareku ba..."
MIEMIE ce take shirin yowa kan ta domin ƙwatar Tasleem, kafin ta motsa Madam Nablah ta kunna wutar tsafin ta mai ƙarfin gaske da tsananin zafi ya busa kowa dake wurin, tsabar tiririn wutar sai da Miemie tayi baya a gigice tare da faɗuwa ƙasi, duk babu wanda bai yi sama ya doku a ƙasi ba tsabar tiririn wuta..
A take Madam Nablah ta ɓace da Tasleem a cikin wannan wutar...
Catrina da Bahrasha ne suka kama kayuwansu tare da saki ƙara domin ƙwaƙwalwar baƙaƙen Aljanun ne suke tafarfasa tsabar tsananin zafin wuta su ma a take suka bace cikin duhu....
Halittun haske kuwa su ma ɓace wa suka yi cikin haske mai ɗauke da sanyi da iska mai daɗi...
Miemie ta zama ruwa itama ruwan ya ɓace..
Haske ya wanke sahara.
Faɗa ya tsaya.
Kowa ya kowa yanda ya fito, domin ba a yanda zasu samu Madam Nablah a halin yanzu, ga tana shirin hallaka su da wuta mai tsananin ƙuna...
★★★★★
A can bayan duniyar da mutane ke rayuwa, bayan saharar haske da duhu, akwai wani tattakeƙen lambu, da itatuwa masu baƙin ganye kuma rana bata fito wa a wurin sai wata mai launin ja.
A tsakiyar wannan wurin akwai ƙaramar dafaɗɗiyar alfarwa, wadda take gefen wata tafkin ruwa...
A cikin wannan alfarwa, Nasreen ce ke kwance.
Ita ba matacciya ba.
Ita ba kuma rayayya ba.
Sai dai kamar ana tsare da ruhinta cikin wani yanayi na barci mai zurfi....
💤 NASREEN CIKIN BARCI MAI RAI...
Nasreen wacce take bacci da duk motsin zuciyarta.
Idonta a rufe, amma murya tana fitowa daga cikin zuciyarta tana cewa:
"Abeesh... ina jin ka... amma ba zan iya miƙa hannuna ba... Ina jin sanyi... amma na kasa tashi... Waye ya tsare ni a nan?"
Ruwan tafkin yana zagayawa da ƙamshi mai sanyi da ƙara kamar kuka.
A gefe guda,
Madam Nablah ce ke zaune tana saka rawaya a cikin ruwa, tana ambaton wasu kalmomi cikin harshen da babu mai iya fassara wa sai halittu.
Ita kaɗai tasan a yanda ta ɓoye Tasleem, sannan ta bayyana a yanda ta ajiye Nasreen..
A lokacin da Catrina ta so kashe Nasreen da duhu, Madam Nablah ce ta karɓi ruhin Nasreen ba tare da barin ta mutu ba, ta kaita wannan wuri domin tsare rayuwarta har ta ci galaba akan haske....
Madam Nablah ta ce cikin wani sanyin murya da kuma ƙarfi, tana faɗin
"Ance mata zata mutu, amma ni nace a’a. Nasreen zata yi rayuwa, ba sai da kujerar mijinta ba… Sai da zuciyarta da ƙaddara.
Ta ci jarabawa, amma har yanzu akwai sabo a zuciyarta. Sai na goge komai, sai na shafe komai, sai na miƙe domin magance matsaloli... sannan zata tashi daga bacci, ki cigaba da hutawa ƴata Nasreen......"
💔
A cikin barcinta, hawaye suka gangaro daga gefen idonta.
Zuciyarta tana kiran sunan Abeesh, kuma tana jin laifin da ta yi masa lokacin da ta fara zargin sa da Catrina...
A cikin baccin take maganar zuci
"Idan na tashi daga wannan wuri, zan nuna soyayya kamar yau ce rana ta ƙarshe... Amma idan ban tashi ba, ku faɗa wa ƴan uwana cewa ina ƙaunar su.... Ku faɗa wa Abeesh cewa na yarda da shi har karshen numfashi..."...
★★★★★★ Kai tsaye Tsaunin da ta ajiye Abeesh ta nufa dake wata duniyar da bana mutane ba...
A wani tsauni mai hayaƙi da turɓaya, wanda wuta ke fita daga ƙasa kamar ana hura shi daga zuciyar duniya, Madam Nablah ce tsaye — jikin ta na ƙuna da harshen wuta, idonta kamar ƙarfen da aka ƙera domin hukunci.
A ƙasan wannan tsauni, a cikin wata ƙaramar rami da duhu ya lullube shi, Abeesh ne kwance yana fitar da numfashi mai rauni, jikinsa babu ƙarfi, ba motsi, amma zuciyarsa har yanzu tana bugawa da ƙauna, damuwa, da ruɗani.
Madam Nablah tana tsaye tana jiran zuwan wadda ta ƙira.
🌑 CATRINA CE TA BAYYANA
Cikin wata walkiya da iska mai mugun ƙamshi, Catrina ta bayyana.
Jikinta a gajiye daga faɗan da suka yi da Tasleem, amma idanunta na cike da jaraba na rudani.
Da ta hango Abeesh a ƙasa cikin yanayin rashin lafiya, ƙirjinta ne ya buga,
Sai ta ɗan yi baya, tana fadin:
"Wannan... wannan Abeesh ɗin ne...?"
Madam Nablah ba tare da ta ce komai ba sai da ta juya kanta a hankali, ta ɗauko ƙaramar wuƙa mai kaifi daga bayanta, wacce take walkiya da jini, sannan ta miƙa mata tana cewa:
"Kamar kin fara jin tausayin kauna ko? Kin manta cewa ke sarauniyar duhu ce, Catrina. Ya kamata ki wargaza ƙauna, ba wai ki gina ta ba..."
Catrina ta ɗauki wuƙar da hannunta yana rawar jiki.
Ta kalli fuskar Abeesh, ta runtse ido, hawaye na cika idonta duk da bakinta yana dariya, domin ita a koda yaushe a cikin dariya take ko da tana kuka..
Madam Nablah ta ce:
"Ina buƙatar ki yanke dangantakarki da zuciyarki, domin a wannan darasi, zuciya rauni ce. Ki nuna cewa kin fi zuciyar ki ƙarfi, Kashe shi... kafin ya kashe ki da ƙaunar sa."
Catrina ta ce:
"Na ƙi. Na ƙi! Banza nake kiran kaina sarauniyar duhu idan bazan iya amfani da duhun ba, zan yi amfani da duhu domin tarwatsa kowa amma ba zan iya cutar da Abeesh ba, Kullum idan na gan shi zuciyata tsinke wa take... Ban san yaushe na fara jin sa a cikin raina ba... Hakan yasa ba zan iya kashe shi ba!"
Madam Nablah cikin ɓacin rai ta ce:
"Kin gaza, Catrina! Kin zama rauni, kin koma mace mai ciwon ƙauna... Kin manta ni na gina ki! Ni na kore ki daga mutunci zuwa iko! Kuma yanzu ke kin kasa... akan wani ɗan adam?!"
Catrina ta ce:
"Na ƙi zama yanda kike so. Na ƙi zama wuta Saboda hatsarin ta. Ban son zama kamar ki. Kuma idan zaki kashe shi, ki fara kashe ni tukun...."
Madam Nablah karɓan wuƙar daga hannun Catrina ta yi tare da faɗin:
"To... na fahimta.
Amma ki sani... da zarar kin ɗauki hanyar ƙauna, shikenam kin zama ƙaramin haske... kuma ina ci gaba da ganin haske a jikinki. Wannan zai zama ƙarshen ki, Catrina, idan kin ci gaba..."
Sai ta juya da wuƙar, ta buga ta ƙasa, ta ɓace cikin wuta.
Itama Madam Nablah ba har cikin zuciyar ta take faɗin ta kashe Abeesh ba, akwai abinda take son shirya wa...
Catrina ta zauna a gefen Abeesh tana kuka.
Ta riƙo hannunsa a hankali tana cewa:
"Ka tashi, ka yi magana dani... Ka ce min ka yafe min... ko aƙalla ka ce min baka yafe ba..."
Sunkuyar da kanta a kan ƙirjinsa tayi, hawaye suna sauƙa.
Duhu ya ƙara rufe tsaunin, da alama wani sabon abu yana gab da faruwa...
Catrina na zaune gefen Abeesh, hannunta na dafe da goshinsa, hawaye na gangarowa daga fuskarta mai cike da wulakantacciyar soyayya da nadama. Duk da ta kasance cikin duhu, duk da ta rayu a ƙarƙashin horo da umarnin Madam Nablah, akwai wani abu a ranta da ke bijirewa — wanda ko ita kanta ba ta fahimce shi ba:
Abeesh.
Tana kallon shi, sai ta furta da murya mai sanyi :
“Me yasa baka da taurin zuciya kamar mu? Me yasa soyayyarka ke da sauƙin ƙona ruhin wanda bai san me ƙauna take nufi ba? Abeesh... ka karya mun zuciya da soyayyar ka...”
Iskar tsaunin ta ƙara zafi, kamar tana ƙona hawayen da ke zubowa daga idonta. Duk da haka, ta cigaba da magana, tana shafa fuskarsa da ƙaramar ƙarfinta domin ƙarfin ikon ta ƙara raguwa take a yayinda take zubar da hawaye...
Ta ce:
“Na ga duhu, kuma ni duhu ce, na ji daɗin sukar mutane. Na yi nesa da zuciyata... amma kai ka ja ni na fara dawo da ita. Na fara jin yadda zuciya ke bugawa idan tana cikin ƙauna.”
Ta kalli hannuwanta waɗanda suka saba azabtar da zuciya, yanzu suna rawar sanyi da tsoro. Sai ta ɗaga kanta, ta kalli sararin tsaunin, tana fadin:
“Idan hukuncina mutuwa ne saboda ƙaunar wanda nake zaton maƙiyi na, to na yarda. Amma kar ku ci gaba da cutar da shi... don Allah, kar ku taɓa shi...”
Cikin ɗan lokaci, wani ƙarar numfashi ya fito daga cikin ƙasan tsaunin. Abeesh ya motsa. Hannunsa ya dan motsa kamar wanda aka kwantar da shi tsawon lokaci.
Catrina ta zaro idonta cike da farin ciki, numfashinta ya tsaya cak.
ta ce da murya mai rauni:
“Abeesh... Abeesh? Ka na jina?”
Abeesh bai buɗe idonsa ba, amma ƙirjinsa na tashi da sauƙa. Wannan ne karo na farko da numfashinsa ya sauya tun da aka kwantar da shi.
Catrina ta matso da fuskarta kusa da kunnensa, tana fadin:
“Na sani... ka ji ƙiyayyata. Na sani... Na taɓa Nasreen. Na jefar da mafarkinka, Amma na fara yin nadama... kuma ko zan mutu saboda haka, na amince..... Ka yi shiru, Abeesh! amma zuciyarka ta gaya min komai.”
Kamar dai wani abu na faruwa daga nesa...
Catrina ta juyo da sauri.
Ba a iya ganin wanda ke zuwa ba, amma da alama wani abu ne ke matsowa kusa.
Idanunta ne suka cika da ruɗani, tana girgiza kai tana cewa:
“Kada ku zo ku ɗauke shi. Ku bar ni in gyara kuskurena. Ku bar ni in nuna masa cewa zuciya na iya tuba, koman zurfin duhu.”
Ta sunkuyar da kanta bisa ƙirjin Abeesh, ta cigaba da fadin:
“Idan har zaka tashi, ko da zaka ce bani da amfani a gareka, zan karɓa. Ko da zaka watsa ni da kalmomin ƙiyayya, zan saurara. Amma kayi min alfarma... ka tashi. Dan Allah, ka tashi…”
Da wannan kalmomi, hawaye suka zubo daga idon Abeesh — a hankali, ya buɗe idonsa...
Sai ya ce cikin murya ƙasa-ƙasa
“Ke ce...?”
Catrina ta girgiza kai cikin hawaye, tana murmushi mai raɗaɗi ta ce:
“Ni ce... kuma ban cancanci amsarka ba.”
Madam Nablah tana tsaye a saman wani dutse mai kaifi a cikin tsaunin da aka ɓoye Abeesh. Gashinta yana motsi kamar harshen wuta, idanunta kuwa suna lumshewa a hankali. Amma zuciyarta na girgiza ganin Catrina ta tsugunna jikin Abeesh da hawaye, tana tunanin taya Aljana zata kamu da ƙaunar bil adam na tsanani....
Ta furta da siririyar murya mai cike da iko da izzah:
“Catrina… Catrina… Ba ki zama ni ba, kuma bazaki taɓa zama kamar ni ba....Amma ki sani cewa ke duhu ce, kuma kina kokarin dauƙo haske? Da Soyayya? Lallai… kina kuskure, yarinya.”
Catrina ta ɗago idonta, jini na zuba daga hancinta da idanuwanta Tana kallon mahaifiyar ruhi da girmamawa da tsoro ta ce:
“Na rasa meye gaskiya… amma yanzu na san me nake so. Ba ku bane. Ba cutarwa ba. Na san cewa zuciya zata iya rayuwa da ƙauna.”
Madam Nablah ta tintsire da dariya mai cike da haushi, tana sauƙowa ƙasa daga kan tsauni cikin hayaƙi, ƙasa na ƙonewa da wuta a inda ƙafarta ke taka wa. Lokacin da ta tsaya gaban Catrina, ta ɗaga hannunta, wata wuƙa mai kamar an harhaɗa ta da wuta da jinin halittu ta bayyana.
Ta furta da murya mai ƙarfi:
“Ga zaɓi: ko ki tafi ki ɗauko Abul, mahaifin Abeesh da Amaar ko kuma... ki kashe Abeesh da kanki.”
Zuciyar Catrina ta tsaya. Kamar an fesa ruwan sanyi a jikinta. Sai ta girgiza kai a hankali ta ce:
“Kada ki jarraba ni da hakan. Bazan iya kashe shi ba, wallahi bazan iya ba... koda kuwa duhu zai ƙona ni, koda kuwa kin cire ni daga hallita ne bazan iya kashe shi ba.”
Madam Nablah ta ɗan lumshe ido. A fili ta nuna bacin rai, amma a zuciyarta baza ta taba bari a cutar da Abeesh ba balle ta sa a kashe shi, barazana ne kawai....
Domin Madam Nablah... tana son Abeesh.
Jin sa take kamar ita ta haife shi, duk da yana da ɗabi’a mai kyau, Ƙwazo. Tausayi. Gaskiya. Kuma hakan ya sa ta tsani wannan halin, amma tana ƙaunarsa....
Cikin barazana take faɗin:
“Idan bazaki kashe shi ba, ki tabbatar kin kawo min Abul. Idan ba haka ba... ke da shi zaku hallaka tare.”
Catrina ta juyo, tana kallon Abeesh, tana shafa goshinsa da yatsanta, wanda a halin yanzu baya cikin hankalinsa, haka yake binsu da kallo ba tare da yasan abinda suke faɗi ba..... Zuciyar sa Nasreen kawai take ƙira.
Catrina ta ce:
“Zan kawo miki Abul... Amma idan na dawo, kar ki kuskura ki taɓa shi. Na rantse da wutar da kika raina ni da ita, zan juyar da ita akanki idan kika ƙetare haddi.”
Madam Nablah ta bace da harshen wuta ba tare da ta furta komai ba...
A nan ta bar Abeesh bata ɗauke shi ba, ta bar shi, saboda wani abu a ranta . Ba zata taɓa iya kashe shi ba…
Catrina
Ta kalli hanyar sama, ƙarfin zuciyarta yana ƙaruwa, duk da hawaye na gangarowa ta ce:
“Wannan ba faɗa ce ta duhu kawai ba... Yanzu zuciyata tana ƙoƙarin ƙin kowane mungun aiki. Amma zan kare
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 34