bazai misaltu ba...
Tana kammalawa ta haura saman upstairs can room ɗin ta, falon kamar babu abinda ya faru a cikin sa,
Bayan awanni Asmeen ce ta sauƙo falo ganin yanda falon ta koma ne kamar wacce tayi ɓatan kai, haka take ta kallace-kallace ta kasa gane wa shin a gidan su take ne ko kuma ƙasar waje aka fita da ita, tsabar ta gama tsora ta da gudun gaske ta koma room ɗin su, tana zuwa ta jawo hannun Nasreen suka fito falon a tare, itama Nasreen abinda ta gani ne ya tada mata da hankali, a ruɗe ta ce "a yaushe aka sauya komai na gidan? hatta fentin an sauya launin sa.
Tasleem itama fitowa tayi, tsaya wa tayi tana bin falon da kallo daga bisani ta ce "Aljanun nan sun iya gyara kam..."
Nasreen da Asmeen kallon ta suka yi tare da faɗin "Aljanu kuma?..."
Tasleem ta ce "eh in ba su ba wani bil adam ne zai iya wannan aikin a wuni guda?..."
Nasreen gaba ɗaya itama abun ya ɗaure mata kai...
Madam Nablah tana kallon su ta cikin ɗakinta ta mirror, yanke hukuncin kawar musu da tunanin taya akayi aka maida falon na musamman tayi, tana cikin room ɗinta ta ƙirƙiri skeleton robot kamar mutane sannan ta sanya musu Aljanun da zasu zauna a jikin robot suna aiki kamar mutane, duk abinda aka sanya su suyi zasu yi, bayan ta gama ƙirƙiran su ta kuma basu umarnin su koma falo, haka robot suka fara motsi su biyar suka fita daga cikin room ɗin Madam Nablah suka nufi falo,
A jere su biyar suka fara sauƙo wa falo,
Asmeen ce ta fara ganin su a tsorace ta nuna su da yatsa ba tare da tayi magana ba, su ma sauran kallon wurin da take nuna wa suka yi, Nasreen ganin su yasa ta zaro ido waje tana faɗin "ƙalu innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, meye waɗannan skeleton?..."
Tasleem kuwa tana ganin su kanta yayi wani irin sarawa kamar wanda aka kwaɗa mata guduma,
Madam Nablah ce ta biyo bayan su tare da faɗin "ku kwantar da hankalin ku waɗannan robot ne kamar yanda ku ke gani ana showing ɗin su a TV, duk siyan su nayi daga yau zasu rinƙa rage ayyukan gida, har girki su zasu na yi, gyaran gida su ne, komai da komai sannan duk abinda ku ke buƙata ku sanar musu zasu yi muku..."
Asmeen cike da mamaki ta ce "Mom irin robot ɗin da muke gani a Film yau su ne a gidan mu? ...."
Madam Nablah ta ce "eh su ne, musamman nasa aka kawo mun su daga China..."
Nasreen ta ce "Mom kina nufin kice su suka tsara falon nan? amma kuma naga komai na falon an chanza..."
Madam Nablah ta ce "daman ina ajiye da kayan furnitures, yau kuma nasa aka kawo mun waɗannan robot suka tsara mun falon kamar yanda na umarce su..."
Asmeen ta ce "wow so beautiful, abinda nake gani like dreams yanzu kuma gasu nan a realty...."
Tasleem gaba ɗaya hankalin ta bai kwanta da waɗannan robot ba, ji take ƙirjinta yana bugawa sannan kanta kamar ana buga mata guduma,
Tasleem nufan wurin robot tayi yanda suke a jere ta tsaya a gaban su tana ƙare su da kallo, idonta tasa a cikin ɗaya daga cikin robot tana kallon can cikin idonsa, gani tayi a cikin eyes ɗin sa wuta ne yake ta ci, haka tabi duk sauran da kallo su ma haka suke, lokaci guda taji wani irin hajijiya yana shirin ɗaukar ta...
Madam Nablah idonta akan Tasleem tana tunanin ita ce kawai zata kwabsa mata, tana da saurin gane sihiri shiyasa Madam Nablah bata yinta sosai duk da jininta ce,
Tasleem ce ta fara faɗin "ni gaba ɗaya hankalina bai kwanta da su ba, bana son su gaba ɗaya, dan Allah a fitar da su daga cikin gidan nan, bana son ganin su..."
Madam Nablah ce tazo ta tsaya a gaban Tasleem tare da faɗin "Kinga Tasleem sai dai daga yau kar ki ƙara fito wa falo ki rinƙa zama acan cikin room ɗin ku domin babu yanda zan kai su, kamar yanda na tsara haka zasu cigaba da gudanar da aikin su a cikin gidan nan, sannan zasu rinƙa mun recording duk abinda yake faruwa, don haka ki koma can bedroom ɗinki, abinci da komai duk za'a rinƙa kai miki can...."
Tasleem cikin fushi da tashin hankali ta bar falon ba tare da ta furta komai ba, saman room ɗin su ta haura tana kuka domin zaman gidan nan ya fara isar ta....
Shima Abeesh yana tsaye a saman upstairs ɗin sa yana jin duk jawaban Madam Nablah akan robot ɗin ta, shima tsabar ɓacin rai koma wa yayi cikin room ɗin sa......
New Book 2025.
*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)
A Fictional Story✍️
Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal
Which is best known as
*Asmeetah writer*
*WhatsApp 09065443871*
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
EP 19 to 20
Yau kwana uku da ƙirƙiran robot, yanzu su suke komai a gidan, Madam Nablah duk ta kori ƴan aikin gidan ta, hatta girki yanzu robot ne suke yi sannan su shirya akan dinning, Asmeen kuwa an samu abokan wasa, sai dai ta sa su a gaba taita kallon su tana dariya, robot ɗin burge ta suke shiyasa take taya su aiki,
Nasreen kuwa da zaran sun kammala girki zata ɗauki kulolin Abeesh ta kai masa can room ɗin sa,
Tasleem kuwa kamar ta hallaka idan tayi ido huɗu da robot domin bata ƙaunar su sam,
tana room ɗin su ta gama shirin ta zata fita, ta feffesa ko ina na jikinta da turaruka kamar yanda ta saba, sannan ta ɗauki handbag ɗin ta da waya tare da key ɗin motarta ta fice,
A falo ta tarar da Madam Nablah akan dinning da Nasreen da Asmeen, fuska a ɗaure tana kallon gefe ta ce "zan fita..."
Nasreen ta ce "an kammala girki fa, yanzu nake shirin ta shi naje na ƙira ki..."
Tasleem kallon ta tayi sannan ta ce "yau kwana nawa rabon da kiga na ci abincin gidan nan?..."
Nasreen kallon Mommyn su tayi wacce take ta cin abincin ta ko kallon su bata yi ba.
Tasleem ta cigaba da faɗin "har duniya ta naɗe Indai waɗannan Aljanun ne zasu cigaba da yin girki a gidan nan wallahi bazan ci ba, idan inaso zan iya shiga kitchen na girka abinda raina yake so, idan kuma naso zan fita naje restaurant ne.."
Hanyar fita ta nufa taji Madam Nablah ta furta "ina zaki je?..."
Tasleem tana yamutsa fuska ta ce "restaurant..."
Madam Nablah ta ce "ki zo ki kaiwa Shaprees abincin sa kafin ki tafi..."
Tasleem cike da mamaki ta furta "whattt? Mom ni kuma? why shi bazai rinƙa zuwa yana yin lunch ɗin sa anan ba?..."
Madam Nablah ta ce "kiyi abinda na saka ki bawai umarnin ki zan bi ba, haka na tsara ..."
Tasleem sai da ta ɗan tsaya na mintuna kafin ta nufi kitchen tana turo baki ta ɗauko jerin kuloli a paranti tayi waje, kai tsaye part ɗin Shaprees ta nufa, tana zuwa ta tura ƙofa ta shige, cikin sa'a ta tarar da shi a falo yana zaune akan sopa idonsa akan plasman da remote a hannunsa, ba tare da ta furta komai ba ta wuce shi ta kai masa dinning,
Shi kuwa tin shigowar ta ya gane cewa Tasleem ce domin ba haka ɗabi'ar Asmeen yake ba, duk san da zata shigo da sallama a bakin ta cikin tsoro da fargaba sannan zata durƙusa har ƙasi ta gaishe shi..
Tasleem har zata fita ya dakatar da ita ta hanyar furta "Ke!..."
Tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba ta ce "Keke na kasuwa, kawo maka za'a yi ne?..."
Ganin tana shirin raina masa wayo ne yasa ya miƙe shima ya nufo yanda take tsaye, bata ankara ba taga ya zagayo da hannayensa biyu ta sai tin cikin ta tare da mannota jikin sa yana faɗin "ki sauƙe wannan girman kan naki domin ni ne shugaban ki..."
Tasleem cikin ɓacin rai da salon mugunta da iya ƙarfinta ta gwara masa kanta akan lips ɗinsa, ba shiri ya sake ta tare da toshe bakinsa da hannayensa biyu har sai da ya durƙusa, kafin kace mai har lips ɗinsa ya fashe sai jini,
Tasleem juyo wa tayi tana kallon sa gira ɗaya a ɗage ta ce "Tasleem ce ba Aasmeen ba, kayi kuskure da baka gama tantance mu ba, wannan ɗin da kake gaban ta tafi guguwa iskanci...."
Tasleem zaro black glass ɗin ta tayi tare da toshe wa tana masa wani irin kallon up and down ta cikin glass ta ce "daga yau Tasleem ce zata cigaba da kawo maka girki ba Asmeen ba sai ka kiyaye, ka rinƙa kwantar da tsuriyar ka domin tana harin abinda yafi ƙarfin ta ne...."
Daga nan tayi ficewar ta....
Shi kuwa Shaprees har zuwa yanzu yana durƙushe gaba ɗaya jini ya gama wanke masa hannu domin ba ƙaramin bugu tayi masa akan lips ɗinsa ba, ga lips ɗin laushi kamar auduga shiyasa bashi da ƙarfi abu kaɗan ne zai fasa shi, wani irin ɓacin rai ne ya ziyarto cikin zuciyar sa, wani irin mugunta yake shirya ma ta....
Tasleem kuwa a gaban sa ta jefar da duk wani tunanin sa da ɓacin ransa domin ba shine a gabanta ba, yanzu abinda ta tinkara shine Amaar, da shi take kwana take kuma tashi a ranta, tsananin haushin sa take kamar ranta zai fita, babu wanda zai mata laifi bata ɗauki fansa ba hakan yasa tasa aka nemo mata address yanda yake, yanzu haka akan hanyar ta na zuwa gidan sa take....
Ita kaɗai tana driving tana tunanin abinda yayi mata a gidan su, duk duniya babu wanda ya taɓa sumbatar ta a ko ina sai shi mai ƙarfin hali da zuciya, hakan ma a cikin gidan su bayan ya furta kalmar soyayya da ta haramta wa kowa, ga laifin yasa an kore ta a ɗakin jarabawa...
Tana cikin driving bata san ma ta iso gidan sa ba sai ganin ta tayi a ƙofar bakin gate, wasu sojoji ta gani a tsaye kusan su biyar ko wanne da bindigar sa, tunani ta fara yi shin wannan mutumin babban soja ne ko kuwa? a labarin sa da ta binciko an sanar mata shi ɗin sojan Bangladesh ne, yazo gudanar da wasu ayyuka kafin ya koma.
Ƙarfin hali tayi ta sauƙa daga cikin mota ta ƙarasa wurin da sojojin suke a tsaye da ƙafa, tana isa wurin su ta tsaya Tare da furta "excuse me..."
Wani soja ne ya ce "Ke cire glass ɗin fuskar ki..."
Murmushi ta yi sannan ta ce "ba abin ta da hankali idan har glass ne matsalar ka ga shi nan zaka iya kaiwa Madam ɗinka domin nasan baka da arziƙin siyan wannan glass..."
Tana kammalawa ta wurga masa shi,
Wani sojan ne ya buɗe baki zai darara mata tsawa tayi saurin ɗaga masa hannu tana faɗin "Uhm uhm tsaya mana, ba'a ɗaga mun murya domin ni ba ƙaramar mace ba ce, ga can motata na parker ta acan, ba wurin ku nazo ba, nazo wurin ogan ku ne..."
Ya ce "Ogah bai san kowa a wannan ƙasar ba don haka ki juya, idan kuma neman taimako kika zo nema sai ki bari idan ya fita ki tare shi a hanyar sa ta wuce wa, nake ga zai fi miki..."
Tasleem kallon sa tayi up and down sannan ta ce "ka ga nayi maka kama da masu neman taimako? sannan babu ruwana da ko yasan wani a ƙasar ko bai sani ba nidai burina ka ƙira shi a waya yanzu ka sanar masa cewa ya yi baƙuwa..."
Sojan ganin ita ɗin bata wasa bace yasa ya yi dialing call number Amaar,
Shi kuwa har yana shirin shiga bathroom zai yi wanka towel a ɗaure a kunkumin yaji ringing, ɗaga wa yayi aka sanar masa cewa ya yi baƙuwa bai tsaya jin ko wacece ba ya sanar cewa a barta ta shigo, daga nan ya shige toilet domin a tunanin sa ko wacece tazo zata iya jiransa ya fito daga wanka sannan ya gama shirin sa....
Tasleem bayan an sanar mata cewa ta shiga dogon tsaki taja tana taku kamar wata sarauniya sai ƙarar takalmin ta kake ji ƙwas ƙwas ƙwass ta shige, a mashigar babban falo ta ƙara tarar da wasu sojoji munana marasa fara'a da jajayen idanuwa, har zata ratsa su ta shige suka dakatar da ita tare da faɗin "Ke tsaya mana ..."
Tasleem cikin ɓacin rai ta ce "meye kuma du? sai kace wanda na shigo gidan shugaban ƙasa...."
Wani soja ne yazo gaban ta yana shirin jona mata na'ura a jikinta wanda zai bayyanar da abinda ta shigo gidan da shi,
Tasleem ta ce "wai meye haka zargina ake ne?..."
Sojan ya ce "kowa ma ba abin yarda bane, haka ake yi duk wanda zai shiga ciki sai an auna shi anga da mai zai shiga..."
Sauƙe numfashi Tasleem tayi cike da takaici, wani ƙara suka ji a cikin jakar ta nan suka fara faɗin "ciro abinda yake cikin jakar ki..."
Tasleem hamdala tayi a cikin ranta domin har tayi tunanin ta tafo da bindigarta ta fasa, haka ta sa hannu a jaka ta ciro waya tana faɗin "wayata ce dai ba komai ba sai key ɗin motata..."
Sai da suka bincika sosai kafin suka barta ta shige ciki, tana shiga falo ta fara jin wani irin sanyi mai ratsa jiki, sai da ta gama ƙarewa falon kallo da kuma ƙaton photonsa dake manne a jikin bango da kakin sojan sa, ganin abinda take kallo bashi ya kawo ta ba yasa ta ja tsaki tare da kallon saman upstairs wanda take tunanin nan ne bedroom ɗinsa, har zata hau taji muryar wata mata ta fito daga kitchen tana faɗin "Malama ina zaki je ne, ki jira shi anan falon mana..."
Tasleem kallon matar tayi taga tana sanye da kayan aikatau a jikinta sannan ta ce "shin zan iya tambayar ki?..."
Matar ta ce "ina jinki..."
Tasleem ta ce "meye matsayin ki a cikin gidan nan?..."
Matar ta ce "ni mai aikin gidan ce, bani kaɗai ba mu huɗu ne a gidan masu aiki..."
Tasleem jinjina kai tayi sannan ta ce "dakyau wato ya ajiye zuƙa-zuƙan mata a gida har ku huɗu kamar wasu matan sa...."
Sauran ƴan aiki guda uku ne suka fito falo su ma tare da faɗin "wannan fa daga ina?..."
Tasleem ta ce "lallai kun dace da matan gidan..."
Duk murmushi suka fara saki tare da dudduba kan su tare da faɗin "Allah yasa mu zama matan sa, wayyo farin ciki, in haka ta faru ni ce farkon matar sa..."
A cewar wata daga ciki, haka duk suka fara mita kowa a cikin su so take Amaar ya ce yana sonta shiyasa koda yaushe basa zama cikin ƙazanta kuma kullum da kwalliya a fuskokin su...
Tasleem ganin batada lokacin su yasa ta barsu a wurin ita kuma ta haura saman ɗakin sa, tana zuwa ta shige bedroom, gani tayi babu kowa sai ƙarar ruwa da take taji a toilet alamun wanka yake, kana shigo wa room ɗin kasan ɗakin sa ne saboda tsananin ƙamshi da room ɗin yake koda yaushe baya rabuwa da turaruka, ga photunan sa a mammanne a jikin bango,
Cike da mugunta tana sakin murmushi ta zaro wayarta a cikin jaka tana maganar zuci "tinda har ka nuna mun cewa kai ɗan iska ne to ni yau zan nuna maka cewa ni oganniyar ka ce...."
Ajiye jakarta tayi akan gadon sa sannan ta nufi toilet tsayawa tayi a bakin toilet sai da ta kunna Camera wayanta kafin ta tura ƙofar toilet da ƙafarta cikin ƙarfi sai ga ƙofa ta buɗu anan ta saita Camera wayanta akan sa yana wanka,
Da sauri ya ɗago da kansa yana kallon bakin ƙofar, ga yanda ruwa yake ta zubowa a kansa dake shower ya kunna,
Tasleem murmushi take tana masa video tare da faɗin "ina kai ɗan iska ne ko? to yau zanga ƙarshen iskancin ka..."
Amaar cike da mamaki yake kallon ta daga bisani ya ce "daman ke ce baƙuwar tawan?..."
Tasleem ta ce "eh..."
Amaar murmushi ya yi ko girgiza bai yi ba yana tsaye tsirara haihuwar uwarsa ya ce "to yanzun mai kike yi haka?..."
Ta ce "video nake maka..."
Ya ce "mai zakiyi da video?..."
Murmushi tayi sannan ta ce "posting zanyi a social media, saboda iskanci irin taka kaje har gidan mu ka sumbace ni to yau zan nuna maka ranar ka kaima, zan kawo ƙarshen iskancin ka, facebook, TikTok, Instagram, Twitter duk zan tura videon tsirarar ka kowa ya gani, daga nan za'a fara raina wayon Soja..."
Amaar bai san lokacin da ya tintsire da dariya ba yana faɗin "ai da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 34