Abeesh yana kokarin koya wa Nasreen yadda ake harba kibiyar mashi,
tana dariya ta saita yanda zata harba tazo yin harbi hannunta ya kuɓuce ta harbi kibiyar kan Abeesh kibiyar ta makale a turken rigarsa, dake kibiyar wasan yara ne kamar na roba, har ta tsorata kamar tana tunanin zai ji ciwo sai kawai taji yana dariya,
Ta ce:
"Na harbi zuciyarka fa, karka ce kibiyarta ta wasan yara ɗaya ne da ta farauta.!"
Abeesh yana dariya ya ce:
"Allah ya tsare! Na fi jin tsoron kibiyar ki fiye da na farauta...!"
Zaro ido Nasreen tayi tare da faɗin "kibiyata ta roba ce faa..."
Ya ce "eh duk da hakan..."
A wannan ranar wuni suka yi suna yawo cikin lambun gidan, suna ta kwasar dariya da soyayya kamar yara. Sau da yawa Nasreen tana tsokanar Abeesh da cewa:
"Idan har zaka zama gwamna na zuciya. Bazan kaɗa kuri'a ba idan baka iya girki ba!"
Abeesh ya ce "dole na kuwa na iya girki domin mallakar zuciya mai tsada da haske...."
Ɓangaren Asmeen...
Madam Nablah ta riga da ta mallaka wa Shaprees ita, yanzu a ɓangaren Shaprees take rayuwa, ta raba ta da ƴan uwanta gudun kada wani matsala ya gibto wanda zai sa a fasa Auren da tayi niyyar haɗawa...
Asmeen na zaune cikin daki da aka ware mata a part ɗin Shaprees tana kallo ta tagar ɗakin inda Shaprees ke zaune a bakin gadon ta yana kokarin nuna mata kulawa, amma zuciyarta cike take da shakku. Tana jin motsin ruhi a gabanta.
Wata rana kafin wannan lokacin Asmeen ta samu mahaifiyarta Madam Nablah tana kuka, tace:
"Mommy, kince za ki ba ni miji. Amma kin yanke hukunci akan ruhina ba tare da sanina ba."
Madam Nablah a tsawa ce ta ce:
"Shaprees shine mafi cancanta. Bai kamata kina tunanin cewa zan iya cutar dake ba ko wani daga cikin ku...."
Asmeen ta juya cikin damuwa, tana jin kamar zuciyarta zata fashe. A zuciyarta tace:
"Zan bar jikina gare shi, amma ruhina ba zai taba karbar sa ba."
Tana tsaye abunda take tunawa kenan ta rasa gane dalilin da yasa mommynta take son haɗa ta da Shaprees wanda ya nuna cewa shi wuta ne...
Shaprees yana zaune duk da duhun zuciyarsa, yana jin wani abu daban daga Asmeen. Daga lokacin da ya fara ganinta tana kuka a ranar da yazo gidan nan sai ya soma jin tsoro – tsoron cewa zai iya faduwa cikin soyayya da ita. Amma a zuciyarsa, Sophia ce kawai ke zaune. Sai ya daɗa kuduri cewa:y
" idan har zaki ceci ruhin Sophia daga Madam Nablah, to tabbas zan tsinci kai na cikin soyayyarki ko da bana so......"
Wata rana a cikin gida, Tasleem da Nasreen sun tsara zasu yi girkin masoya, suna kitchen suna dafa delicious abinci tare. kafin su kammala abincin ya kone ƙurmus saboda Tasleem ta tsaya tunanin neman abinda zata zuba don ƙara wa girki ɗanɗano, Nasreen kuma tana haɗa wani abu daban ganin yanda girkin su yake ta ƙone wa ne yasa tayi saurin sauƙe wa tana faɗin
"Innalillahi yau mai zamu ce wa masoyan mu, ga shi mun yi musu sosai akan cewa mun fi su iya girki..
Kafin Nasreen ta rufe baki sai ga Amaar da Abeesh suka shigo suna faɗin "Subhanallahi ƙonannen Abinci masoya zasu ci?..."
Nasreen ta ce "bani bace Tasleem ce...
Amaar yace:
"Beb Tassl baki iya girki ba daman?"
Tasleem tana turo baki ta ce "Nasreen ce fa bani ba..."
Abeesh ya sake baki yana kallon Nasreen ya ce "Mar'atussaliha daman kema baki iya girki ba,...?
Nasreen ta ce "Ya Abeesh idan ban iya girki ba shin girkin da nake kai maka waye yake yi?..."
Abeesh ya ce "Robot manaaa...."
Duk suka kwashe da dariya...
Amaar ya ce
"Idan wannan ne abincin masoya, to mun yafe wallahi, mun bar muku kayan ku Alhamdulillah a ƙoshe muke.....!"
Suna wasa da dariya da haka har suka koma falo, Nasreen tana tsokanar Tasleem akan bata iya girki ba,
Cikin fusata Tasleem ta kamo Nasreen suka fara kaure wa da faɗa,
Amaar da Abeesh kuwa zama suka yi suna kallon su tare da tinzira su suna faɗin "duk wacce ta kayar da ɗaya to wacce aka kayar ita ce bata iya girki ba..."
Tasleem da Nasreen kowa so yake ya kayar da ɗan uwansa domin su ci gasar iya girki,
Har zuwa wannan lokacin babu wacce ta yarda taje ƙasa saima ƙara kaurewa suke da faɗa, a ƙarshe dai a tare suka faɗi a ƙasin carpet suna sakin numfashi daƙer....
Amaar da Abeesh ihu suka danna suna faɗin "wayyo 0 0 duk basu iya girki baaa..."
Tasleem da Nasreen ƙara miƙe wa suka yi zasu ƙara dambe a lokacin Amaar da Abeesh suka miƙe kowa ya janye nashi jikinsa suna faɗin "A'a ya isa haka, kar ku raunana mana kan ku....."
Suka yi dariya gaba daya, cikin nishaɗi...
A nan ne labarin ke kara rikicewa, yayin da Asmeen ke neman mafita daga auren da bata so, Shaprees na fama da rikicin zuciya, Abeesh da Nasreen suna jindadin soyayya, yayin da zuciyar Tasleem da Amaar suka sake haɗe wa....
Amma wani mummunan sirri daga Madam Nablah na dab da bayyanuwa wanda zai canza komai...
Nexttttttt......
New Book 2025.
*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)
A Fictional Story✍️
Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal
Which is best known as
*Asmeetah writer*
*WhatsApp 09065443871*
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
EP 33 to 34
A wannan lokacin da yamma, hasken rana ya kusan faɗuwa Asmeen tana tsaye a gaban window tana kallon waje tun safe ta kasa cin abinci, ta kasa aiwatar da komai, Kullum cikin zuciyarta tana son fita daga wannan gidan. Amma babu inda zata je, babu wanda zata roƙa, sai hawaye masu dumi dake zubo daga cikin idanuwanta...
A ɗayan ɓangaren gidan, Abeesh da Nasreen sun shirya tafiya zuwa bakin ruwa domin shan iska da tattaunawa na musamman da ya shafi Auren su. Nasreen tana ɗauke da kwando cike da 'ya'yan itatuwa (fruits) da kayan ciye-ciye...
Sun zo fita Abeesh ya tsaya a gaban ta tare da zuba mata ido ko ƙibtawa ba ya yi, domin ba ƙaramin kyau ta sha ba,. A hankali ya furta
"Idan na faɗa cikin ruwa saboda kyawunki, za ki zo ki cece ni ko sai na jira malam kogi?"
Nasreen tintsirewa tayi da dariya tana faɗin
"Ni kuwa sai na ɗauko kwalba, na ajiye kyawunka a ciki, kada ka lalace!"
Yana dariya ya ce "kyawuna ba ma ni kaina ba?..."
Itama cikin nishaɗi take dariya tare da faɗin "a'a kyan ka zan adana, daga baya sai na jan ko..."
Suna dariya har suka fice daga falon,
zasu shige mota Abeesh shi da kansa ya buɗe mata murfin motar ta ɓangaren da zata shiga, har zata shige tsinkar jikinta ya tashi sai wani yaarrrr ta ji, ƙirjin ta ne ya fara bugawa a hankali...
Abeesh ya ce "lafiya kuwa? Meta faru ne Mar'atussaliha?..."
A jikinta taji cewa akwai abinda ya shafi jinin ta a nesa da ita tana kallon ta cikin damuwa da tashin hankali....
Nasreen a hankali ta ja da baya tare da juya bayanta ta ɗaga kanta saman Benin part ɗin Shaprees, gani tayi Asmeen tana tsaye ta tagar window ɗakin da take a part ɗin Shaprees dake ba nisa a tsakanin su, itama Asmeen su ɗin take kallo tana hawaye, ganin a halin da ƴar uwar ta take ciki ne yasa Nasreen kuka, lokaci guda hawaye suka wanke mata fuska, haka suke kallon juna, ita Nasreen ba halin ta je yanda Asmeen take haka itama Asmeen ba halin ta zo yanda ƴan uwanta suke,
Daƙer Abeesh ya ja Nasreen suka tafi.....
Shaprees yana kallonsu daga nesa yana kallon farin ciki yana ƙona zuciyarsa. A lokacin yana tare da Madam Nablah, wadda ta zo da wani shudi-shudin littafi a hannunta, koda yaushe tana kan karanta littafi abinda ya shafi spell-spell, itama tana kallon yanda Nasreen da Asmeen suke kewar juna, suna zaune a wurin shakatawa wanda yake kewaye da bukka, sai wasu tsararrun kujeru da table ta tsakiya, da duk kan alamu tana nuna masa yanda ake gudanar da wasu tsafe-tsafe ta cikin littafin ...
Madam Nablah ta ce:
"Shaprees, lokaci ya yi. Za ka auri Asmeen nan da kwana uku. Idan kana da wata damuwa — riƙe ta."
Shaprees yana buɗe littafi a hankali lips ɗinsa na motsi cikin sassanyar ya furta
"Akwai wani abu da kike ɓoyewa, Na san ba soyayya ce tasa kike son haɗani da ɗiyar ki Aure ba... na bincika cikin nawa salon tsafi kina so ne na ɗauki wani abu daga jikinta — wani sashi na asali."
Madam Nablah ta sau murmushi mai haɗarin gaske. Ta juya tare da faɗin
"Asmeen bata san cewa tana ɗauke da sirrin iko da nake da burin samu ba... kuma ita kaɗai zata iya dawo da Sophia — matarka — daga mutuwa."
Madam Nablah ta furta hakane domin tabbatar masa da gaskiyar lamari amma a cikin zuciyar ta bazata taɓa barin ya dawo da Sophia rayuwa ba...
Shaprees ya ɗan ɗago yana kallonta a ruɗe Zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri,
Me zai yi? Zai auri Asmeen don samun iko? Ko zai bijire wa Madam Nablah don kare wacce ba ta san komai ba?......
A gefe guda kuwa Tasleem tana kwance akan ƙirjin Amaar akan gadonsa bayan ta gama gyara masa ko ina na ɗakin, haka take sauraron bugun zuciyarsa na harbawa a hankali cikin nutsuwa, haka kawai take ji a jikinta cewa abinda ta aikata masa ta cancanci hukunci, idan ta nuno cewa da hannunta ta harbi Ya Amaar ɗin ta sai taji ta tsani kanta, idan ta tuno da Tasleem ɗin da ta tsani wanda take muradin ƙaunar gani da bege sai taji cewa ina ma zata iya canza kanta ta koma wata ɓangare da ban,
Lokaci guda hawaye suka gangaro mata a hankali ta furta
"Yaa Amaar...."
Yana pressing wayansa ya amsa tare da shafa fuskar ta.
Ta ce:
"Na san bana da ikon canza abin da ya faru... amma zaka iya bani dama in gyara. Ka koya min yanda zan daina zama irin Tasleem ɗin nan da nake tsana."
Amaar ya kalle ta da ido masu nuni da jinƙai da gargaɗi. Sai ya ce:
"Idan kina son gyara, ki fara da gaskiya — fada min komai game da mahaifiyarki."
Tasleem ta tsaya. Hankalinta ya tashi, a ruɗe ta tashi daga kansa tana kallon sa, domin babu abinda yake firgitar da ita irin a kawo mata maganar mahaifiyar ta, sai ta rinƙa jin tana tuno da wasu abubuwa na sirri,
A lokacin ne Abul Abeesh ya faɗo mata a rai, mahaifin su Amaar da Abeesh, haka take jin hawaye na ƙoƙarin zubo mata a ranta take furta
"Shin lokaci ya yi da zata tona babban sirrin Mommy?...."
Tana tambayar kanta...
Tasleem ta tsaya kamar mutum-mutumi, zuciyarta na bugawa da karfi.
Amaar ne ya sake furta
“faɗa min komai game da mahaifiyarki”
Ta ɗan juya kai gefe, sai kuma ta dawo da kallon ta cikin idon Amaar.
Sannan ta ce
"Yaa Amaar… mahaifiyata ba ta yadda da haske ba. Amma bamu san da haka ba domin dukkan mu mun girma muna ganin ta tamkar tauraruwa ce mai kare mu daga duhu. Har zuwa ranar da na fara jin wasu kalmomin tsafi daga gare ta a cikin mafarki na....."
Amaar ya runtse idanu yana sauraron ta, zuciyarsa na baƙin cikin halin da mahaifiyarsu ta shiga na rashin son haske.
Tasleem ta ci gaba da bayani cikin rawar murya:
"Tana da wani ɗaki a cikin ɓoyayyen ɓangare na gidan nan… wanda ba kowa ke sanin hanya zuwa ba. A can take tara jini, fure, da wani zane da muke tsoro mu kalla. Kuma ina jin tana amfani da wani sashi na rayuwarmu wajen ƙarfafa kanta."
Amaar ya ce
"Shin kin san dalilin da yasa take so Shaprees ya auri Asmeen?"
Tasleem ta girgiza kai tare da faɗin
"Na ji sau ɗaya tana cewa "'idan asalin Asmeen ya yanke, sai na dawo da ikon da aka ɗauke min shekaru ɗari. Ban fahimta ba. Amma yanzu ina tunanin… akwai abu mai girma da ke tattare da Asmeen."...
Cikin rashin fahimta Amaar ya ce "ikon da aka ɗauke shekaru ɗari kuma?...."
A lokacin Tasleem ta nutsu tare da daidaita tunanin ta cike da mamaki ta ce "shekaru ɗari ai ba'a haifi Mommy bama...."
Amaar ya ce "tabbas akwai abinda ke wakana, ina tunanin ba asalin mahaifiyar ku ba ce...."
Tasleem cikin rashin fahimta ta ce "ban gane mai kake nufi ba..."
Amaar ya ce "kar ki damu zamu gano komai nan bada jumawa ba..."
★★★★★
Washe gari da sanyin safiya
A can ɗayan ɓangaren gidan, Asmeen na zaune a gaban madubi, tana kallon fuskarta wacce ke ƙara haskakawa a duk dare. tana tunanin meyasa a duk lokacin da Shaprees ya zo kusa da ita, sai gabanta ya fadi. Zuciyarta na cika da damuwa—ba don ta tsane shi ba, sai don saboda tana jin wani abu daga jikinsa yana ɗauke da wuta na al'ajabi.....
Tana cikin wannan tunanin sai ta hango wani haske a dakin, Ruhin Sophia ya bayyana, murya kamar ƙara amma tana motsi cikin nutsuwa.
Ruhin Sophia ta ce
"Asmeen… ki saurara. Ki kiyayi Mahaifiyarki Ba Auren ki da Shaprees take so ba — ikon dake jikin ki take nema.
Sannan Mijina Shaprees ba azzalumi bane kuma baya cutarwa, tsautsayi da ƙaddara yasa ya shiga tarkon Mahaifiyarki Madam Nablah, kuma ita ta rabani da duniyan na, sannan ta datse farin cikin mijina don cikar burin ta, hakan yasa mijina yake ƙoƙarin jefa kansa cikin haɗari na tsafin wuta Amma a zuciyarsa akwai abin da ba zai iya shawo kansa da shi ba — soyayya da azaba sun yi masa kututture, amma nayi alƙawarin bazan taɓa barin mijina ya dawwama a cikin wannan wutar tsafin tsiyar ba, wanda babu komai a cikin sa sai zalunci da ƙonewar zuciya, zan kasance a cikin zuciyar mijina Shaprees kiyi haƙuri saboda zaki zama matar sa zuwa gobe...."
Asmeen ta miƙe da sauri, jikin ta yana rawa.
Ta furta
"Ni dai ban san komai game da rayuwar ku ba, a barni na zauna cikin kwanciyar hankali kamar yanda nake a baya, kada a sako ni a cikin tsafi domin banida alaƙa da shi,
sai dai na tabbata bana jin kwanciyar hankali da wannan auren."
Sophia ta juya kafin ta bace, ta furta wata kalma mai zurfi:
"Ke ce mafi alaƙantuwa da tsafi amma ki dage da addu'a hasken zuciyar ki zai kore duhun da ke ƙoƙarin mamaye ki...."
Daga nan Sophia ta ɓace,
Cikin firgici da tashin hankali Asmeen ta zauna a bakin gado tana sakin numfashi daƙer tare da faɗin "ke nan bayan Tasleem muma ana bibiyan ikon hasken mu? innalillahi wa inna'ilaihi raju'un....."
★★★★★
Abeesh da Nasreen kuwa sun dawo daga yawon su cikin dare, amma kafin su isa ƙofar gida, suka ci karo da wani tsoho mai launin fata kamar gawayi, yana tafe da sandarsa, yana fadin:
"Mai dauke da sirrin zuciya, kada ka manta… masoyi na gaskiya ba ya ɓoye sirri mai wuta, ruwan da kuke sha, yana iya zama madara ko guba."
Suna kallon juna cikin mamaki.
Nasreen ta ce
" Ya Abeesh… kana jin akwai wani abu da muke wulakanta gani?"
Abeesh yana kallon tsohon ya ce
"Ka sanar mana gaskiyar abinda kake nufi, nasan maganarka bazai wuce akan Madam Nablah ba..."
Tsohon ya nuna Nasreen sannan ya ce "ina magana ne akan wannan yarinya, ki kula da kan ki domin akwai sirrin tsafi...."
Abeesh ya kalli Nasreen cikin damuwa ya ce
"Zan tona komai daga yanzu. Idan akwai sirri tsakanin ki da tsafin Madam Nablah, wannan daren zai zama farkon haskenmu ko ƙarshenmu."
Tsohon ya ce:
"Akwai wani ƙugi a ƙasan gidan nan, an rufe shi da tambarin zinariya. A can ne aka binne asalin wutar Madam Nablah. Kuma, idan wani daga zuriyar gidan ya shiga ƙugin nan da zuciya mai tsabta, zai ga gaskiya gaba ɗaya...."
Daga nan tsohon ya ɓace ɓatt,
Nasreen cikin tsoro da fargaba ta rungumi Abeesh tana ihu, da sauri ya toshe mata baki zuciyarsa na ɗar-ɗar yana tunanin maganganun Aljanin tsoho da ya fito musu, cikin tashin hankali suka shige gidan, a lokacin misalin ƙarfe 12 na dare....
A falo suka tarar da Madam Nablah zaune akan sofa tana facing plasman alamun kallo take, ba komai ne yasa ta zauna a falo a wannan lokacin ba sai jiran dawowar su Abeesh, kallon su tayi cikin izzah da ƙasaita tana yamutsa fuska kamar bazata yi magana ba ta ce
Meyasa kuke hidimar gaban ku ba tare da bin umarni na ba, you support to tell me idan zaku fita wani wuri and then bana son yawon dare...."
Abeesh gyara tsayuwar sa yayi yana kallon ta tare da goya hannayensa akan ƙirji ya ce "bin umarnin ki dai-dai yake da faɗawa cikin wuta, shiyasa muke tsarkakakkiyar rayuwa cikin haske, bama buƙatar duhu ya shigo rayuwar mu...."
Madam Nablah murmushi tayi sannan ta kawar da kanta daga ganinsa, tana jinjina kai ba tare da ta furta komai ba,
Abeesh yana gamawa ya bar falon kai tsaye upstairs ya haura zai nufi bedroom ɗinsa.
Nasreen tana tsaye kanta na kallon ƙasi duk da halin da mahaifiyarta ke ciki bata daina mata biyayya ba, sannan kuma tana matuƙar jin shakkar ta saɓanin Tasleem,
ta juma a tsaye a gaban Madam Nablah ba tare da kowa ya furta komai ba, sai yanzu Madam Nablah ta samu bakin furta "ki bar gabana, like kije ki kwanta..."
Nasreen godiya tayi tare da barin wurin har zata hau saman beni ta hango Amaar ya shigo falo yana ɗauke da Tasleem wacce tayi bacci, yayi mata ɗaukar luɗa alamun a ɗakinsa tayi bacci, yana sakin murmushi idonsa akan Nasreen wacce ta zuba musu ido tana sakin murmushi itama..
Madam Nablah a firgice ta miƙe tsaye tana kallon su, idanuwanta kamar zasu faɗo tsabar zazzaro su da take cikin fushi gasu manya ne daman, tana huci haka Amaar ya wuce da Tasleem ko kallon yanda take bai yi ba, duk a tare suka haura saman upstairs da Nasreen tana masa dariya....
Itama Madam Nablah a fusace ta bar falon ta nufi bedroom ɗin ta,
Ba jumawa Amaar ya sauƙo bayan yaje ya kwantar da Tasleem, ya nufi room ɗin sa shima.....
A gefe guda kuma, Shaprees ya ƙara fusata. Duhu yana ƙara karfi a jikinsa. Amma cikin zuciyarsa, muryar Sophia tana ƙara bayyana, tana damunsa da tunanin gaskiya. Ya fito daga ɗakinsa da dare, ya nufi gidan ƙasa da ya ƙirƙira domin gudanar da tsafin sa, A can ya zana zane a ƙasa ya kira ruhin da ke ƙunshe da sirrin rayuwa da mutuwa.
Yana zaune ya furta cewa:
“Na yarda da duhu don in dawo da Sophia. Amma yanzu gaskiya tana fara rikita ni. Ina so in san, shin ina kan hanya?”
Wani murya ne ya bayyana, da suffar mutum kamar ruhi da idanuwa jajawur
ya ce:
“Ka rasa hanyar gaskiya tunda ka rungumi wuta saboda soyayya. Amma yanzu, akwai hanya ɗaya – idan Asmeen ta san gaskiya to zaka cimma burin ka, Idan kuma ka ci gaba da ɓoye gaskiya komai zai ƙone.”.........
A gefe guda.
Tasleem tana cikin bacci ta faɗa cikin wani mafarki mai ɗauke da haske, lokaci guda ta ganta a cikin gajimare wanda ba koda kukan tsuntsu ne, iya zallar haske ne sannan tana sanye da fararen kaya har ƙasi da mayafin kai wanda aka rufe mata sumar gashi, sai waiwaye take tayi amma bata tarar da kowa ba, bata wani tsorata ba domin tasan haske ne ke bibiyan ta ba abun cutarwa ba..
Tana tsaye taga wani mutumi fari da farin gemu yana sanye da fararen kaya shima a jikinsa, haka yake kamar ruhi domin ba mutum bane hakan yasa ya fito mata a mafarki domin ya tunatar da ita gaskiya,
Tasleem murmushi ne a kwance saman fuskar ta ganin tana tare da haske,
Cikin muryar nutsuwa dattijon nan ya fara magana kamar haka:
“Kin taɓa sha ruwa daga ruwan da aka gauraya da wutar ruhi. Ke ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 34