Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kamar... ya shuɗe ne a raina?” Ta dafe kanta. Da gaggawa, idanuwanta suka buɗe. “Sunansa ma... sunansa?” Kamar wata zararriya tana tunanin abubuwa da yawa a cikin zuciyar ta, Tana ƙoƙarin tunawa, amma zuciyarta na hana ta. Fuskar da ta saba gani duk lokacin da ta lumshe ido yanzu kamar hazo take gani Ta ce “Wayyo Allah... menene ke faruwa dani?” Ta miƙe daga inda take, ta nufi madubi tana kallon kanta. Amma da ta kalli fuskar ta sosai… sai kawai taga wata surar mace a cikin madubin tana murmushi. Amma wannan murmushin... bai da armashi, yana da shaiɗanci da ruɗani. Sai kwatsam, madubin ya fashe da wani irin ƙara, wani hazo ya fito daga ciki, ya rufe fuskar Tasleem. Ta ɗan zabura baya, tana girgiza kai tare da faɗin “Babu wanda zai iya... juya zuciyata... babu wanda zai manta mun da shi...” Amma a cikin zuciyarta, muryar wani da ba nata ba take ji ana furta “Babu Amaar. Bai taba wanzuwa ba. Wannan tunanin karya ne. Wani abu ne kawai da kike sawa a ranki... kuma lokaci ya yi da zaki manta da shi har abada.” A daidai lokacin, Nasreen da Asmeen suka dawo gida. Suna shiga cikin falo, suka ji sanyi mai ɗauke da warin wani abu kamar ƙonanniyar ganye. Suka kalli juna. Nasreen ta ce “Asmeen... kina jin wani abu?" Asmeen ta ce “Ina jin kamar tsafi. Dama kinsan gidan nan baya zaman lafiya.” Suka nufi ɗakin Tasleem, suna kiran sunanta. “Tasleem! Kina lafiya?” “Ki buɗe mana ƙofa...!” Amma Tasleem tana tsaye a gaban madubi, idonta baƙi ƙal-kal, tana kallon kanta kamar wata da bata gane kanta ba. daga nan sai hawaye suka fara gangarowa daga idonta. Ta kama kanta da hannayenta biyu tana faɗin “Ni wacece ne? Waye nake nema? Me nake tunawa ne...? Shin ina mafarki ne?” Nasreen daƙer suka buɗe ƙofar suka shige da sauri, suka ruga da gudu tare da rungumar ta. Nasreen ta ce “Tasleem! Menene ke faruwa?” Itama Asmeen tambayar ta tayi tana faɗin “Me ya sameki haka?” Tasleem ta kalle su, idonta cike da hawaye ta furta “Waye wanda na harba? Me yasa nake jin kamar na rasa wani bangare na zuciyata? Me yasa nake jin kamar an sace ni... daga ciki?” Asmeen ta kalli Nasreen, zuciyarta cike da tsoro. Nasreen cikin kuka take faɗin “Tsafi ne... wallahi tsafi ne ke kokarin karya ta. Amma bazan bari ba.” ** A gefe guda... Madam Nablah tana zaune a ɗaki mai duhu, tana jin murya cikin kanta na faɗin: “Zata fara mantawa... zata daina tunawa... lokaci yana tare da mu.” Amma kuma... wani canji ya fara tasowa daga zuciyar Tasleem. Wannan baƙin hazo da tsafi… yana samun cikas daga wani ɓangare na ruhinta da tsafi ba zai iya shafanta ba, tsatsan ƙauna da soyayyar Amaar da bata da izinin mantawa da ita. ★★★ Yamma ta ƙure. Rana ta narke cikin duhun dare. A cikin ɗakin Amaar, wutar fitila tana kunne da hasken rawaya, yana zaune kan gado, bandage har yanzu na manne a kirjinsa, idanunsa a lumshe, numfashinsa mai nauyi. Zuciyarsa na tafasa da abubuwa da dama, amma wani abu daban ya fara ƙona shi tun daga ciki… Yayi ƙoƙarin rufe idanu domin samun natsuwa, amma a zuciyarsa yana jin wani irin bugun bugun zuciyar wata – bugun zuciyar Tasleem. “Tasleem...” ya furta a hankali. “Ina jin kamar tana cikin haɗari...” Wani irin ƙamshi mai wari da tsami ya doki hancinsa duk da babu komai a ɗakin. Sai zuciyarsa ta fara bugawa da ƙarfi. “Ba daidai bane... zuciyarta na ƙara shigewa cikin duhu. Wannan ba Tasleem ɗina bace... an fara rugujeta daga ciki...” Ya miƙe a hankali, duk da jikin nasa har yanzu yana rauni. Amma zuciyarsa ta yi nauyi da damuwa. Ya isa gaban madubi yana kallon kansa, ya dafe gefen bango da hannunsa ɗaya, idanunsa sun canza launi, wani haske mai kama da ruwan sama ya fara bayyana a jikin sa. A hankali ya furta “Na sha alwashin kare ta... ko da da rai na ne...” Sai kawai ya fara jin wani murya daga cikin kansa – muryar wani wanda ya ceci rayuwarsa a lokacin da aka jefa shi cikin ruwa shekaru ashirin da suka wuce. “Lokaci ya kusa, Amaar. Ikonka yana dawowa, amma ƙiyayya da soyayya sun fara yakar juna a zuciyar Tasleem. Idan tsafi ya cinye zuciyarta bazata tuna da kai ba… sai dai ka rasa ta har abada.” Ya dafe kirjinsa. “A’a... bazan bari hakan ta faru ba. Ko da zata ƙi ni... zan kareta. Amma ban isa na bari ta mutu da bakar zuciya ba...” A cewar Amaar. Sai kawai wani haske mai ɗumi ya fara fita daga hannunsa na hagu, yana yawo a cikin ɗakin – wani ƙaramin iftila’i da ya nuna cewa ikon da aka ɗora masa a lokacin da aka ceci rayuwarsa yana dawowa a hankali. Ya furta cikin salo: “Dole in gane hanyar shiga cikin mafarkinta... domin a can za a yi yaƙin farko.” A wannan lokacin, wayarsa ta ɗauki kira – Nasreen ce ke kiran sa da gaggawa. “Amaar! Ka shirya, mun dawo gida... Tasleem na cikin wani mummunan yanayi! Mun iso yanzu amma ba zamu iya samun taimako ba… sai kai!” Cikin rawar jiki da ƙarfin zuciya, ya ce: “Ki ƙara riƙe ta, ban da kowa da zai iya fitar da ita daga wannan duhun sai ni.” Ya miƙe da ƙyar, ya ɗaura rigar sa, duk da jiki yana rauni, amma zuciyarsa ta fara sauya tsari – daga rauni zuwa azama yana faɗin “Tasleem... ba zan bar ki a hannun zuciyar tsafi ba. Komai zai faru, sai kin tuna da ni.”...... A ɗakin ta dake saman bene, Tasleem ta haye gado tana karkarwa, idanunta sun lulluɓe da hawaye, zuciyarta kamar zata tarwatse. Amma abun mamaki – tana jin wani abu a ranta, kamar ana tunkudata cikin wani wuri mai duhu, amma daga ciki akwai murya – muryar da ba ta san daga ina take fitowa ba. “Ki guje wa hasken zuciyarki, Tasleem… ki rungumi duhu… ki yarda da ƙiyayya, kin fi ƙarfi idan zuciyarki ta cika da tsana...” Tana riƙe kanta, tana girgiza kai: “A'a… ba haka nake ba. Ni ba mugunwa bace... Me yasa nake jin kamar zuciyata tana canzawa? Me yasa nake jin kamar bana ƙaunar kowa... har kaina ma?” Nasreen da Asmeen sun juma da barin ɗakin sakamakon tiririn wutar ɗakin, gaba ɗaya tsoro ne a cikin zuciyoyin su... Tasleem ita kaɗai ce a ɗakin kuma daman ita kaɗai ake buƙata. Wata ƙatuwar guguwa ta mamaye ɗakin ta – hasken wuta ya ɗauke, labule ya fara yawo akan iska, zafin daki ya hauhawa. Cikin wannan yanayi, ta fara ganin madubi a bango yana sauya launi – ya koma baƙin zurfi kamar ramin shaidanu. Sai kuma ta fara ganin hoton kanta a cikin madubin – amma ba Tasleem bace kamar yadda ta san kanta ba. Wata sigar ta ce – idanu jajaye, gashi a warwatse, tana murmushi da baki cike da jini. “Kece Tasleem na gaske... Kece zuciyar da aka daƙile. Ki zo ki karɓi ikona... Ki manta da Amaar, ki manta da kowa...” Tasleem ta ja da baya tana kuka, ta durƙusa a ƙasa, tana rokonsu su daina: “Ku barni! Ku bar zuciyata! Ni ba haka nake ba!” jikin ta ne ya fara rawa da ƙarfi, kamar wutar lantarki na shiga jikinta sai da ta saki wani irin ƙara mai ban tsoro – wani haske ya fita daga cikinta na dan lokaci, ta sake faɗuwa. Wannan tsafi na ƙoƙarin cire hasken da ya rage a ranta – ƙaramin haske wanda har yanzu bai mutu ba. A ƙasan falo kuma su Nasreen da Asmeen ne suna cikin firgici. Sai da suka yi yunƙurin hayewa sama, sai suka tsaya cak – saboda ganin Madam Nablah tana tsaye a tsakiyar falo da idanu kamar ba na mutane ba, tana kallon saman bene, tana karanto wata ruɗaniyar addu’a cikin yaren aljanu. Nasreen ta matsa kusa da Asmeen cikin muryar tsoro: “Asmeen... mece ce wannan murya haka? Kuma me ya faru da Mommy...? Kamar ba ita bace...” Asmeen ta ce: “Idan har Tasleem tana sama yanzu… to akwai buƙatar mu dakatar da wannan... Amma ba mu da iko...” A wannan lokacin ne su ka ji ƙarar motar Amaar ya tsaya a ƙofar gida. Lokaci ya ƙure ko Amaar zai iya tsallake duhun da ke hana kowa hawa sama, ko kuma Tasleem zata faɗa tarkon da Madam Nablah ta kulla tun tuni. “Tasleem... ki tsaya har zuwa isowata,” Amaar ya furta a zuciyarsa, yana kallon saman gidan da hayaki da hasken duhu ke fitowa… Amaar ya fito daga motar da sauri. Da kallo guda ya gane gidan na cikin wani yanayi da ba a saba gani ba hayaki mai duhu yana fita daga tagogi, iska tana kadawa kamar hadari na shigowa, kuma wutar rana ta ɓace daga saman gidan duk da gabar rana ce. "Tasleem..." ya ambaci sunanta da ƙasa cikin murya, idanuwansa sun cika da tsoro da damuwa. Kamar wani haske daga sama, sai Amaar ya fara jin wata irin ƙara a kunne, kamar ƙira daga wani ruhin tsarkaka – kira wanda ya saba jin sa tun lokacin da aka ceci rayuwarsa a cikin ruwa shekaru da suka wuce. A wannan lokacin ne wani murya mai zurfi ta dawo masa a rai: "Lokacinka yayi, Amaar. Ka fuskanci duhun da ya raba ku... Ka shiga da zuciya tsarkaka, domin kai kaɗai ne zai iya warware abinda aka daɗe ana gina wa." Amaar ya lumshe ido, ya dafa ƙirjinsa inda aka harbe shi. A wurin nan yake jin ƙarfinsa – ruhinsa yana ɗauke da haske wanda ke iya karya tsafin da Madam Nablah ta ƙulla. Sai da yaja numfashi, ya furta: “Bismillahir Rahmanir Rahim... Allah ka bani ikon tsallake duhun da zai hana ni ceton zuciyar da ta rasa kanta.” Da haka ya taka ƙafar sa cikin falo. Yayin da ƙafarsa ta taka ƙasa – kamar ƙasa ce ta wani duniya. Lokaci ya tsaya, iska ta tsaya, sai wata ƙara ta tashi daga cikin hayaƙi: “Wannan gida ba naka bane, ruhun wuta zai karyaka, ka janye Amaar!” Madam Nablah ce ta furta hakan da wata murya da ba kamar ta ɗan adam ba. Idanunta sun yi jajaye, tana tafiya a hankali zuwa ga Amaar, tana ɓalle masa karatu a harshen aljanu. Amma Amaar bai ja da baya ba. Ya matsa kusa da ita. Kowane taku yana fitar da haske daga ƙafarsa – kamar yana takawa a wani wuri na tsarki. Ya tsaya gaban Madam Nablah: “Na dawo ba don na yaƙe ki ba, sai don na ceci abinda kika kusan lalata... Ina neman ceto Tasleem daga duhun da kika jefa ta ciki!” Kafin Madam Nablah ta yi wani ƙari, Amaar ya furta kalmomin addu’a da aka koya masa lokacin da ya rayu bayan fadowa cikin ruwan nan, kalmomi da ke iya karya tsafi mai duhu: “Allahu Akbar kabīra, walhamdulillāhi kathīra, wa subhānallāhi bukratan wa aṣīla...” Haske ya buɗe daga jikinsa, ya haura sama, ya daki tagar da ke zuwa sama inda Tasleem ke kwance cikin suma. Wata ƙara ta tashi daga cikin bangon madubi — madubin tsafin ya tarwatse! Madam Nablah ta ja da baya tana kururuwa: “Kayi kuskure Amaar! Kai ne silar lalacewata... Amma ba zaka fitar da ita daga hannuna ba!” Sai ga Abeesh ya fito daga ɗaki, cikin fushi da ƙarfin zuciya. Ya tsaya gefen Amaar: “Zan tsaya tare da kai Yaya... Duhu bai isa ya cinye gaskiya ba.” Nasreen da Asmeen suma sun tsaya a ƙofa suna karanta Ayatul Kursiyy da Suratul Falaq a ƙasa cikin fargaba. Haske yana cigaba da bayyana... Saman ɗaki kuwa, Tasleem ta fara motsawa. Idanuwanta ya buɗe amma har yanzu tsananin hayaƙi da duhu ya rufe ta... Jirjirin iska ya fara kadawa cikin falon, ƙarar murya da karatun Ayatul Kursiyy daga bakin su Nasreen da Asmeen na karuwa, Abeesh ya tsaya gefen Amaar yana girgiza kai cikin kuka, zuciyarsa cike da jin zafin ƙaddara da yanda duniya ta juya musu, amma a tare da dukkan su guda hudu, haske yana fitowa daga ƙasan ƙafafunsu, yana tunkuɗe duhun da Madam Nablah ta shafa. Madam Nablah tana ja da baya, tana furta kalmomi cikin harshen da ba a fahimta, jikin ta yana ƙara canjawa – kamar ba ta mutum ba, ta fara ɓarin jini a bakinta da hancinta, hakan ya nuna cewa ƙarfin Amaar yana cin galaba akan tsafinta. Amaar ya kalli sama, inda ɗakin Tasleem ke sama – ya lumshe idonsa. A zuciyarsa ya ce: “Allah ka karya duk abin da ke tsakanin mu da ita. Ka warware igiyar da aka ɗaure rayuwarmu da ita ta ruɗu.” Sai da ya taka step ɗaya, ya fara hawa matakalar bene... Amma kafin ya kai ƙofar matakala – ƙarfin shocking ya saukar masa daga sama! Zuuuummmm!! Wutar da Madam Nablah ta haɗa shekaru ashirin da suka gabata don hana shi da Tasleem haduwa ta tashi daga cikin ƙasa ta buge shi da ƙarfi! Amaar ya durƙusa ƙasa da ƙyar, ƙirjinsa yana bugawa, numfashinsa yana fita kamar wani wanda aka yi masa lantarki. “Subhanallah…” ya furta a hankali. Sai Abeesh ya nufo shi, amma shi ma shocking ɗin yana so ya buge shi, sai dai Amaar ya daga masa hannu: “Kada ka kuskura ka taɓa ni yanzu… wannan shirme ne da aka haɗa shekaru da suka wuce... Sai ni kaɗai zan iya fasa shi.” Ya dafa ƙirjinsa. A can ya ke jin wani tsarki na waje da baƙin ciki na ciki – rikicin da yake cikin zuciyarsa yana neman karya masa ƙarfin ruhi. Idanunsa sun fara kadawa da hawaye, ya tuna yanda suka shaƙu da Tasleem tun suna yara... yanda suka rike hannun juna da dariya a bakin su... yanda take cewa masa: "Amaar, karka taɓa bari na..." Sai ya furta da ƙarfi ya ce “Na rantse da Allah albarkacin wannan rana... ba zan taɓa barin ki ba!” Da haka sai ya miƙe da ƙarfin zuciya, ya cigaba da hawa matakala, kowane mataki da ya taka – shocking yana bugunsa – amma haske yana ƙara fitowa daga jikinsa. Tsafi yana ƙonewa kamar ganyen busassu. Kafin ya kai sama, wani sabon salo ya bayyana a cikinsa – kalmar da ya daɗe bai furta ba ya furta a zuciyarsa: "Ya Allah, idan har ni ba zan iya ceton ta ba... ka tura wanda zai iya. Amma kar ka bar rayuwarta cikin duhu!" Da haka, Amaar ya isa ƙofar ɗakin Tasleem. Ya jawo handle ɗin ƙofar a hankali… ƙofar ta buɗe da ƙara kamar ana warware sarƙar duhu. Tasleem na kwance a kasa cikin wani zobe na hayaki, idanunta a lumshe, jikin ta yana rawa, sai wata murya daga cikin bangon dakin ke cewa: “Kar ka taɓata, Amaar... idan kuka kusanci juna – za ku ƙone tare!!” Amma Amaar bai tsaya ba. Ya tako a hankali, yana sauke ajiyar zuciya. Ya durƙusa a gabanta. Yana kallonta cike da tausayi. “Zan fi son in kone tare da ita, fiye da barin ta cikin duhu.” Da hannunsa ya mika ya dafa hannunta... Zuuummmmmmmm!!! Wani karfi na shocking ya fasa dakin gaba daya! Haske ya tashi daga hannayensu, duhu ya washe! Idanun Tasleem suka buɗe cikin wani irin girgiza... suka zuba ido cikin na juna… Shin zata gane Amaar ne? Shin ruhinta zai tuna da shi kafin tsafi ya sake mamaye ta? Shin Madam Nablah zata ƙara wani sabon farmaki? *GAREKU MASU KARATU ASHA KARATU LAFIYA ....* New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 29 to 30 ★★★ Tasleem ta zuba idanu cikin na Amaar, idanu masu cike da hawaye da hasken da ke tasowa daga ƙasan ruhinta. Wani sauti mai rauni ta fito daga bakin ta, kamar tana ƙoƙarin fadar wani abu, amma muryarta ya makale. Amma cikin zuciyarta, wata ƙwaƙwalwa ta fara motsawa... wani abu da ba a manta shi da sauƙi ba. “Amaar...” Kalmar ta fito daga bakinta cikin tattausar murya, Amaar ya ji ta kamar an buga gangar farin ciki a kunnen sa. Idanunta sun cika da hawaye. Wani ɓangare na zuciyarta na kokarin faɗuwa cikin duhu, amma wani ɓangare kuma – hasken da ke fitowa daga hannun Amaar – na tunasar da ita soyayya, amana, da wani alkawari da suka ɗaura tun suna yara. Madubin bangon ya fara fashewa gaba ɗaya. Wata murya mai ƙarfi ta fito daga cikin duhun: “A'a! Wannan ba zai faru ba! Zuciyarta ta nawa ce! Na shafe komai da kuke kira ƙauna! Babu wuri gare ka a zuciyarta!” Muryar Madam Nablah ne. Madam Nablah ta haura sama cikin siffar da ba mutum ba – idanuwanta jajaye kamar wuta, fuskarta na nuna zafin tsafi da haushin haske. Amma kafin ta karasa kusa da su, wata gagarumar igiyar haske ta haska dakin gaba ɗaya! Wani murya daga sama – mai laushi kuma mai ƙarfi – ta busa kamar iska, tana cewa: “Lokaci ya ƙare, Nablah. Tsafi ba zai iya shafe abinda Allah Ya rubuta ba. Zuciyar da aka haɗa da gaskiya ba za ta taɓa zama duhu dindindin ba.” A wannan lokaci ne Amaar ya daga hannunsa na hagu – inda ikon da aka ɗora masa ya fi ƙarfi. Haske ya bayyana daga can, kamar hasken safi ya bayan yanzu dare ne, Ya ce da karfi: “Ki bar mu haka Aunty Nablah! Tsafinki ya ƙare – zuciyar Tasleem ba wurinki bace!” Madam Nablah tayi ƙara mai tsayi da zafi – jikin ta ya fara tarwatsewa cikin hayaki. Wutar dake fitowa daga cikin jikinta ta dawo masa, Cikin wani kakkarfan ƙara ta bace gaba ɗaya cikin hasken da Amaar ya bayyanar, kamar ba ta taɓa wanzuwa ba. Zuuuwwwwww! Duhu ya ɓace. Gidan ya koma kamar yadda yake. Hayaki ya washe, Tsit ya sauka – tsit ɗin da ke bayyana ƙarshen gwagwarmaya.... Amaar yana riƙe da hannun Tasleem. Ita kuma, idanunta sun cika da hawaye, tana kallon sa ba tare da rudani ba. Tana jin numfashinsa, kuma zuciyarta na amsa kira – kira na ƙwaƙwalwa, soyayya, da alkawari. “Amaar… na tuna. Na tuna komai, na tuna wallahi, kai ne Mommy na ta jefa cikin ramin ruwa sannan ta canza daga mutum zuwa dabban daji, innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Allahumma ajurni mi musiba ti wa aklif li khairan min ha..." A lokacin ta fashe da kuka. Ya jawota jikinsa, duk da har yanzu yana ɗan jin karamin wutar shocking har yanzu, amma bai bar riƙonta ba. "Ki kwantar da hankalin ki, ban mutu ba, na dawo gare ki my Tasleem, kuma nace miki ba zan taɓa barin ki ba, na dawo kenan....” Tasleem tana kuka ta ce "Ya Amaar nayi kewar ka sosai, ka dawo gare ni amma nayi kuskure rashin fahimtar ka, kayi hakuri Ya Amaar na aikata kuskure..." Toshe mata baki ya yi tare da faɗin "ki dakatar da wannan shirmen nakin, ki kwantar da hankalinki babu abinda zai ƙara faruwa da ke, sai dai mu tsara yanda zamu gudanar da sabuwar rayuwa ...." Tasleem tana kuka ta rungume shi sosai... Asmeen, Nasreen, da Abeesh sun hau bene da sauri. Da suka gan su riƙe da juna cikin dakin da aka cika da duhu kafin yanzu, suka tsaya cak da hawaye a idanu, zuciyoyinsu cike da mamaki da farin ciki. A ƙasa kuwa, wani ƙaramin wuri ya buɗe – kamar ƙofofin aljanu – daga cikin falo. Amma kafin wani abu ya fito, wani sautin ƙaho na haske ya buɗe sama, yana hana duhun sake hawa. Haske ya cigaba da cika gidan, kamar ana wanke dukan ƙwayoyin cutar da suka jima a can. Tsafaffen gida ya dawo gida. Haske ya dawo. Gaskiya ta yi nasara akan tsafi. --- Kwana biyu bayan haka... Tasleem na zaune a gefen ruwan swimming da ke bayan gida, tana kallon ruwa, hannunta na cikin na Amaar. Sunyi shiru na lokaci mai tsawo, kafin ta ce cikin sanyi: “Duk lokacin da zan fara mantawa da wacece ni... kai kake tuna min.” Amaar ya ce, yana kallon ta da murmushi: “Saboda zuciyarmu daya ce. Kuma idan ina da rai – zan kasance a kusa da ke.” A wannan lokacin wuni suka yi a tare wuri ɗaya..... ★★★★★ Ɓangaren Shaprees Duk abubuwan da yake faruwa a gidan Madam Nablah ya sani amma sai dai bai ɗauki hakan a matsayin damuwar sa ba, abinda ya kawo shi cikin ahalin su shine ɗaukar fansa, har yanzu akwai wannan ƙudirin a zuciyar sa, kuma ya shirya akan mallakan tsafi shima, yana son ya karɓi ikon tsafi saboda wata manufar sa, kuma ya sa a ransa cewa sai ya dawo da Sophia rayuwa..... Madam Nablah ta ajiye makamin yaƙin ta akan Amaar a wannan lokacin domin sai ta yi shiri na gaske amma har yanzu ƙiyayyarsa ruruwa yake a cikin zuciyar ta, ta koma kan Shaprees domin amsa ƙiransa, kallo ɗaya tayi masa ta gama karantar sirrin zuciyarsa na son karɓan tsafin wuta domin dawo da Sophia matar sa, Madam Nablah maimakon taji wani abu a ranta sai ma ta ƙarfafa masa gwiwa akan karɓa masa tsafi a wurin shugabanta ZULQARNAIN. Bayan kwana biyu ta shirya kai shi wurin tsafin ta. Idan ya tuna wannan ranar, yakan ji kamar ya haukace Daren da Shaprees ya rasa Sophia, zuciyarsa ta mutu kafin jikinta ya mutu. Wani murɗaɗɗen baƙin ciki ya shaƙe zuciyarsa. Bai gane yadda aka kashe matarsa ba, amma wata mata mai idon zinariya ta bayyana a lokacin da zuciyarsa ke tsaka da faɗuwa. Ita ce Madam Nablah. A yayin da yayi shiru zuciyarsa tana tuna masa da wasu abubuwa da yawa, kwatsam ya ji Madam Nablah ta furta "Ka rasa? Ina jin wannan azabar," ta ce cikin wata murya mai zuma amma mai daɗin daci. "Amma akwai hanyar da za ka ƙwato darajarka—da ikon fansa." Shaprees bai ce komai ba. Amma ido ya cika da shakku da hasarar da yake son mayar da fansa. “Zan kaika wajen wanda ya bani iko. Idan ka dace, zai baka wuta.” --- A Ƙasar Tsafi Sun sauka a wani wuri mara rana, inda haske ke fitowa daga harshen wuta da ke yawo a ƙasa kamar kogi. Wani katafaren mutum mai jikin toka da ido kamar gawayi yana zaune akan wani tsafaffen kujera, kujerar hawa-hawa ne da igiyoyin zinariya ke zagaye da shi. Wannan shi ne ZULQARNAIN, shugaban tsafin wuta. ZULQARNAIN ya duba

Chapter 17 of 34