Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mutum ba ce kawai — ke rabin ruhi ce, rabin jini. Kuma zuciyar ki na ɗauke da makullin rugujewar Madam Nablah.”... Tasleem cikin rashin fahimta ta ce “To me ake nufi da hakan?”.. Dattijon ya ce “Dole ne ki fuskanci mahaifiyarki da gaskiya. Kuma idan Amaar yana tare da ke, ku shiga ƙugin zuma kafin Duhu ya maye gurbin Domin kuna da alaƙa da juna fiye da yadda kuke tunani.” Tasleem tana motsi da lips a hankali ta furta "menene ƙugin zuma?...." Dattijon ya ce "Hmmm... Ƙugi na zuma wannan ba kalma ce da yara ke taɓa ambatawa ba, sai wanda ya san asalin wani sirri, Idan baki manta ba a nan ne kika taɓa ganin wani dattijon mutumi a tsare babu haske a yanda yake saboda tsananin tsafi, to nan ne gefen ƙugin zuma, asalin ƙugin zuma kuwa sai kinyi da gaske kafin kin san wurin, idan kika shiga nan ne gaskiya zata bayyana kanta, nan ne komai zai ruguje na tsafi, rayuwa zata dawo sabuwa..." Tasleem a ruɗe take faɗin "a yaushe wannan al'amarin zai fara aiki?..." Dattijon yayi murmushi sannan ya ce "dalilin da yasa zamu wakilce ki akan tsarin tafiyar mu, zalunci ya yi yawa, muna son haske ya kawo ƙarshen duhu, daga yanzu ke ce sarauniyar Haske, mun riga da mun naɗaki akan wannan mulkin, na kuma isar da saƙo a gareki...." Tasleem ta ce "taya za'a ban sarauniyar Haske alhalin ban san komai game da haske da duhu ba?...." Dattijon ya ce "a sannu a hankali zaki gane komai da idon sarauta, akwai wasu baiwa da muka zuba miki bayan bayyanar gaskiyar mafarkin ki, matakin da muke so ki kai a wannan zango shine ki bayyana gaskiya, domin haske tana tafiya ne da gaskiya, idan ba haske to ba gaskiya haka kuma idan ba gaskiya to kuwa ba haske, ki bayyana wa su Amaar yanda mahaifinsu yake, kuje ku cece shi daga halin da yake ciki na tsawon shekara ashirin, kada ki wuce awa 24 baki taimakawa tsohon nan ba.... Sarauniyar Haske....Ku hadu da wanda aka ɓoye – ku ƙaraɗe duhun da haske – kafin lokaci ya kure.”.... Tasleem tana hawaye tare da faɗin "Insha Allahu zan taimake shi, a yau ...." Dattijon haske ya ɓace ba tare da ya sake cewa komai ba, daga nan Tasleem ta dawo baccin ta, a ruɗe ta tashi zaune tana jero addu'o'i...." Itama Nasreen tashi tayi jin yanda Tasleem take ta addu'a cikin fitar hayyaci, tambayar ta take tayi tana faɗin "lafiya kuwa Tasleem? wani irin mafarki kika yi haka ..." Sai a yanzu Nasreen ta lura da sumar gashinta da ya koma fari tass kamar furfura, babu alamun ɗigon baƙi, a tsorace ta ce "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un Tasleem ya sumar gashin ki ta koma fari?.." Tasleem bata damu ba kawai hannu tasa ta shafa kanta, sai a lokacin gashin ya fara komawa baƙi kamar yanda yake... Tasleem cike da mamaki take maimaita wa Nasreen abinda ya faru a cikin mafarkin ta, ta sanar cewa "an bata mulkin sarauniyar Haske...." Ta cigaba da cewa "Nasreen....taya zan fara gudanar da wannan al'amarin?...." Nasreen ta matso kusa da ita tare da rungumar ta ta ce "ki bi gaskiya sai ki cigaba da kasancewa a cikin haske shine abinda wannan mafarkin yake ƙunshe dashi da kuma sarautar ki, duk wata gaskiyar da kike ɓoyewa ya zamana kin bayyana ta, kada ki ɓoye sirri sannan kar kiji tsoron duhu wannan shi ake nufi da sarauniyar Haske...." Wannan bayanan Nasreen ya ƙarfafa mata gwiwa sosai, ta jinjina kai sannan ta furta "dole gaskiya zata yi nasara akan ƙarya dole haske ta wargaza duhu, yanzu ne daidai lokacin da zan buɗe wata gaskiyar da na daɗe ina ɓoyewa...." Nasreen ta miƙe tana faɗin "meye wannan gaskiyar?..." Tasleem ta miƙe tsaye tare da faɗin "UNCLE JUN mahaifin su Amaar da Abeesh...." Nasreen itama miƙewa tayi tsaye tana faɗin "haƙiƙa wannan al'amarin babba ne, kuma ya rataya a wuyan sarauniyar Haske ta ceceshi daga cikin duhun da yake domin zuciyarsa haske gare ta...." Tasleem jinjina kai tayi sannan ta ce "naji an fara ƙiran asuba muyi sallah kafin naje na samu Ya Amaar da wannan batun...." A cikin safiyar yau mai cike da shiru, wanda iska ke kadawa a hankali, Tasleem ta sauko daga saman bene Idonta cike da hawaye, zuciyarta kuma kamar ta fashe da sirrin da ta dade da boyewa. Tana shirin shiga ɗakin Amaar. Bayan Tasleem ta je ɗakin Amaar bata same shi ba ya tafi masallaci shi da Abeesh, zaman jiran sa take har ya dawo, ganin ta a zaune cikin damuwa yasa ya ƙara sa wurinta da sauri yana faɗin "lafiya kuwa Baby Tasl?..." Tasleem miƙe wa tayi ita tana hawaye ta ce: "Ya Amaar..… idan na faɗa maka gaskiya, zaka cigaba da sona?” Amaar ya tsaya yana kallonta daga bisani ya ce “Soyayya ba ta dogara da sirri ba. Amma gaskiya tana ƙara ƙarfinta.” Tasleem ta furta cikin kuka “Ni ba cikakkiyar mutum bace. A yanzu na zama sarauniyar Haske wacce aka bata ragamar rushe tsafin Madam Nablah wacce take ƙoƙarin ruguza gaskiya akan ƙarya, Na zama haske ne domin na sanar da duk wata gaskiyar da ake ɓoyewa....” Amaar ya rungume ta da ƙarfi. Yana faɗin “Tasleem… duk da haka, ke ce kike jaddada min farin ciki, ina mai farin ciki domin kin zo da haske, ba duhu ba.”... Tasleem tana hawaye ta ce "akwai wata gaskiyar da nake ɓoye muku amma a yau kuma a yanzu zan sanar maka koda wuta zata ƙone ni... Amaar ya jinjina kai sannan ya ce "wuta bazata taɓa cin sarauniyar Haske ba...." Tasleem ta ce "idan na lumshe idanuwana ƙwaƙwalwata takan kawo mun abubuwan da ke ɓoye, a cikin idanuwa nake iya ganin komai tamkar video nake gani koda mutum yana cikin ƙasin ƙasin ƙasa ne, na samu wannan baiwar ne sakamakon ɗaurani da akayi a matsayin sarauniyar Haske...." Ta kalli Amaar sannan ta kuma cewa "aikin da zan fara yi da wannan baiwar tawa shine zan gano sirrin dake zuciyar Shaprees ne, shin yana son Auran ƴar uwata da zuciya ɗaya ne ko kuwa shima akwai shirin da yake shiryawa yanzu nayi ƙoƙarin dakatar da shi.... Tasleem ta lumshe idanuwanta lips ɗin ta ne ya fara motsi a hankali tana faɗin "bayyana mun sirrin zuciyar Shaprees...." Amaar kuwa zuba wa kyakkyawar fuskar ta yayi da kallo, ji ya yi ta fara faɗin “Wannan… wannan shine Shaprees… da Sophia a zane a cikin zuciyar sa, Amma me yasa yake zaune da Madam Nablah yana dariya, bayan ta aikata masa mummunan laifi, ta ruguza masa farin ciki ta hanyar kashe masa matarsa Sophia.?”.... Da sauri Tasleem ta buɗe idanuwanta tana zazzaro su, tare da faɗin "kenan ɗaukar fansa ya kawo shi gidan nan? har yana shirin Auran ƴar uwata da niyyar cutar wa ?..." Ta kalli Amaar wanda shima abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba... Da sauri Tasleem ta ɗauko biro da takarda ta fara rubutu kamar haka: "Shaprees zaiyi amfani da ke ne, yana son janyo ki cikin shirin da zai iya sa ya dawo da matarsa wacce ta daɗe da mutuwa, ko da kuwa hakan shi zai halaka.... Ta gama rubutun tana furta wa a fili, sannan ta furta "Chuchu...." Sai ga wani tsuntsu ya bayyana ata window ɗakin Amaar yanda yaji ƙiran kenan, tsuntsu fari tass shine ɗan amanan Tasleem, tana matuƙar ji da wannan tsuntsun nata in zata yi aike da ya shafi letter shi take aikawa, da sauri ta nufe shi tana faɗin "wannan saƙon ka kai mun zuwa ga Asmeen yanzu...." Ta lanƙaya masa a wuya lokaci guda ya fura zuwa aiken.. Amaar kallon ta kawai yake cikin tausayawa, sannan yayi matuƙar farin ciki da wannan muƙamin da aka bata domin su zata amfana, zata kare su daga faɗawa cikin hallaka.... Tasleem ta tsaya a gaban Amaar cikin tausayawa ta ce "akwai wata gaskiyar da nake son sanar maka kuma ya shafe ka sosai, amma kafin nan sai na duba halin da yake ciki da kuma hanya mafi sauƙi yanda zamu gano shi...." Amaar a ɗan ruɗe ya ce "shi wa?...." Tasleem ta ce: "Ya Amaar, don Allah ka saurare ni. Zan faɗa maka wani abu mai girma… wani abu da zai iya canza rayuwarmu gaba ɗaya." Amaar yana tsaye idonsa akan fuskarta, ya ga wani irin tsoro da damuwa akan fuskarta a hankali yace: "Na saurare ki, Tasleem. Kar ki ɓoye komai." Tasleem lumshe idanuwanta ta yi tare da furta: "Naga wani tsoho a cikin wani duhun ɗaki dake can cikin ƙasa yana ɗaure da igiyoyi na tsafi, yana neman taimakon haske, wannan gaskiyar idan na bayyana shi Madam Nablah zata iya cutar da shi ko ma ta kashe shi gaba ɗaya..." Amaar cikin rashin fahimta yake faɗin "waye shi ɗin? meyasa yake cikin tarkon Mahaifiyarki?...." Ta kuma maimaitawa tana hawaye a yayin da idanuwanta suke buɗe furta: “Na ga wani tsoho... Yana cikin ɗakin ƙasa a kulle, Na ga idonsa suna kallo kamar yana magana da ido. Amma idan na faɗa, Madam Nablah zata iya hallaka shi!” Cikin damuwa da fusata Amaar ya danna hannayensa cikin sumar gashinsa kamar zai yi hauka yana faɗin "oh my god! what is wrong with you Tasleem ki sanar mun who is him?...." Tasleem murya na rawa ta furta: " Wannan tsohon shine Mahaifinku, Tabbas na san inda mahaifinku yake a ɓoye... yana raye.".... Amaar a ruɗe yake kallon Tasleem ya ce "Wane mahaifi?" Tasleem ta ce "Mahaifin ka da Abeesh — mahaifinku yana can ƙasan gidan Mahaifiyata, an tsare shi shekaru ashirin da suka gabata. Nasha ganinsa a cikin mafarki na amma ban taɓa tunanin shi bane, sai wata rana da na bi bayan Mommy a ɓoye har zuwa yanda yake amma tsoro ya hanani faɗa. Madam Nablah bata ma san cewa na sani ba." Amaar gaba ɗaya ya rikice haka yake fitar da numfashi daƙer yana faɗin "Na... na dade ina mafarkin wannan abun nima. Kuma yanzu ke kike sanar mun cewa gaskiya ne?" Ya girgiza kai ya ce "Ya kamata na je yanzu. Wannan na nufin rayuwarmu na cikin haɗari...." Tasleem ta riƙe hannun Amaar sosai, tace: “Zamuyi wannan tafiyar tare, ni kaɗai ce nasan yanda yake kuma sai da ni ku samu hasken hanya..." Amaar yana zubda hawaye haka yasa hannu ya rungumo Tasleem jikinsa tare da sumbatarta ta ko ina tsabar tsananin farin ciki, haka yake jin ƙaunarta yana ƙara shige cikin zuciyar sa.... Abeesh yana zaune a falo shi kaɗai sai murmushi yake ta zuba wa, a wannan yayin Nasreen tazo ta same shi cike da mamaki itama ta zauna kusa da shi idonta akan fuskar sa wacce ta gagara gane ma'anar wannan murmushin... Abeesh a ruɗe ya juya yana fuskantar Nasreen tsabar farin ciki bai san lokacin da ya rungume ta sosai a jikinsa ba yana faɗin "wannan ranar nake jira daman, gaskiya ta bayyana, bazan iya faɗan a yanda mahaifin mu yake ba amma muddin wani ya sanar a yanda yake kuma ake ƙoƙarin ceto shi to tabbas zan ji hakan a jikina, Nasreen gaskiya ta bayyana, daman nasan mahaifina yana raye domin akan idona akan ɗaure shi a cikin wani duhun ɗakin ƙasa amma bazan iya bayyana hakan a zahiri ba, an kurmantar dani ta yanda bazan taɓa faɗan gaskiyan abinda na gani ba amma hakan bai sa na manta ba, saboda ƙarfin addu'a dana riƙe....." Yana bayani cikin hawaye da nuna farin cikin, itama Nasreen hawayen take tana share masa hawayen sa da tafin hannunta... Ta gefe guda kuma Amaar da Tasleem ne suke tsaye wanda tin farkon maganar Abeesh suke tsaye suna riƙe da hannun juna, daga Amaar har Tasleem duk kowa hawaye yake, Amaar ba ƙaramin tausayawa ƙaninsa yayi ba... Abeesh yana ganin su ya taso da sauri ya tsaya a gaban Tasleem yana hawaye ya ce "my Juju nagode sosai, ta sanadiyar ki yanzu bakina ya buɗe wurin faɗan gaskiya akan zaluncin da aka yiwa mahaifina.... Yana girgiza kai yasa hannu ya rungumeta yana kuka, itama tana kuka tana rarrashin sa.... Amaar ya ce "a yanzu zamu je wurin da mahaifin mu yake zamu ceto shi daga hannun hallaka... Abeesh ya ce "ina tare da kai Yaya, tare zamu wannan tafiyar..." Tasleem ta kalli Nasreen ta ce "ki zauna mana anan nasan Mommy bata nan a halin yanzu, idan har ta dawo kafin mu fito ki riƙe mana ita please..." Nasreen ta ce "yanzu ina zaku nufa?..." Tasleem ta ce "dole ta ɗakin ta zamu shiga domin nan ne kawai hanya mafi sauƙi...." Nasreen ta ce "ki mallaki key ɗin ɗakin ta ne?..." Tasleem girgiza kai tayi sannan ta ce "ban mallaka ba amma yanzu zan gado yanda key ɗin yake..." Ta lumshe idanuwanta cikin lokaci ƙanƙani ta buɗe tana faɗin "ba da key ake buɗe ɗakin ba, sai da jinin jikinta ɗakin yake buɗuwa amma kar ku damu jinin mu ɗaya da ita, zanyi amfani da jini na...." Daga nan suke nufi room ɗin Madam Nablah, suna zuwa Tasleem tasa reza a hannun ta sai ga jini ya ɗiga akan ƙofar ɗakin, sai da ƙofar ta shanye jinin kafin ta karɓi jinin a matsayin mai mallakar ta, sai ga ƙofa ta buɗu da kanta, a take suka yi saurin shiga, ɗaki kamar aljannar duniya domin ba ƙaramin tsaruwa ya yi ba sai dai ko wani ɓangare da ajiyar tsafi a jiki mai ado da kwalliya.... Tasleem kai tsaye ta nufi wani ƙaton photon mahaifinta wanda ta nan ne ƙofar take, Amaar da Abeesh kallon photon suka yi sun san cewa photon mahaifin su Tasleem ne domin da wayon su ya mutu, gani suka yi Tasleem ta rufe ido tare da wasu karatun yaren aljanu kamar yanda taga Mommynta tayi domin bata manta wannan sirrin ba, gani suka yi photon ya rabe biyu sai ga wani ƙofa nan ma ƙofar ta buɗu, cike da mamaki Amaar ya ce "kenan ana amfani da wannan photon wurin tsafi?...." Tasleem ta kalle shi cikin damuwa sannan ta ce "al'amarin Mommy ba sauƙi...." A haka suka kutsa ciki da addu'o'i a bakin su, baƙin duhu ne a wurin ko gaban su basa iya gani, Tasleem rufe ido tayi tare da furta wata kalma ta haske sai ga sumar gashin ta wanda yake a kwance har gadon baya ya bayyana da wani irin haske, haske mai sheƙi wannan ya haska ko ina na wurin, haka suke kallon wurin kamar hasken rana, Amaar murmushi kawai yayi domin kaɗan daga cikin baiwar haske, Abeesh kam gaba ɗaya ya cika da mamaki ganin yanda Tasleem ta koma, sumar gashin ta ya koma fari tass kamar furfura sannan ya bayyanar da haske, a ruɗe ya furta kema tsafi gare ki?..." Tasleem tayi murmushi sannan ta ce "ba tsafi ba, baiwa ce ta haske..." Amaar ya dafa kafaɗarsa ya ce "ita ɗin sarauniyar Haske ce kar ka damu da hakan...." Shima Abeesh murmushi ya yi suka cigaba da tafiya, sai da suka yi tafiya mai nisan gaske har sun zo dab da wurin suka tarar da wani ƙofar ƙarfe anyi katanga da wurin da Mahaifin su Amaar yake, wanda babu bil'adama da zata tsallake wannan ƙofar.... Cike da mamaki Tasleem ta ce "yanzu kuma? amma lokacin da nazo nan babu wannan ƙofar...." Amaar ya ce "ta gane cewa akwai wanda yasan da wurin shiyasa ta kafa tsaro..." Abeesh ya ce "yanzu taya zamu ratsa nan wurin?...." Amaar ya kalli Tasleem sannan ya ce "kiyi amfani da ƙarfin ikonki ki sama mana hanyar wuce wa...." Tasleem gaba ɗaya ta rikice ta soma faɗin "ban san ta yanda zan fara ba..." Amaar ya ce "Tasleem zaki iya, kiyi ƙoƙarin ganin cewa zaki iya, ke fa sarauniyar Haske ne kar ki karaya da wuri haka...." Tasleem cikin ƙwarin gwiwa ta rufe idanu ta fara motsi da lips ɗin ta alamun akwai abinda take faɗi a cikin zuciyar ta, wani haske ne ya bayyana a cikin tafin hannunta lokaci guda ta da fa jikin ƙofar da hannaye masu ɗauke da haske, nan ta fara ƙoƙarin tura wannan ƙofa da ƙarfin haske, gaba ɗaya haske ne ya mamaye ƙofar... Ta jikin ƙofar suka ji murya na tashi a rikice ana faɗin: “Kuna son sanin gaskiya? Toh ku ji: Amaar ba irin mutumin da kuke tunani bane. Kuma Tasleem... ke 'yar wanda ke jini da Madam Nablah ba wai jinin haske ba. Idan gaskiya ta fito, ƙaunar da kuke yiwa juna zata koma ƙiyayya.” Tasleem ta tsayar da abinda take ta kalli Amaar tare da faɗin “Me ake nufi? kenan har yanzu haske bai gama karɓata ba saboda ni jinin Madam Nablah ce? sannan wani irin gaskiya in ta fito soyayyar mu zata koma ƙiyasta?..." Amaar girgiza kai ya yi sannan ya ce "wannan kalmar ɗorata akai akayi domin a tsoratar da mu amma soyayya da aka ginata ta hanyar gaskiya bata taɓa komawa ƙiyayya, ke Sarauniyar Haske ne bakida wani alaƙa da duhu..." Amaar ya kalli jikin ƙofar cikin ƙwarin guiwa ya ce “Komai gaskiya ce, zamu fuskance ta....." ★★★★★ A gefe guda kuwa, Shaprees yana cikin mawuyacin hali. Ruhinsa na cike da damuwa da rikicewa. Ganin mahaifin wani dattijo (mahaifin su Amaar) cikin gilashin asiri ya jefa shi cikin rudani. Shaprees yana zaune a wurin da yake gudanar da sirrin sa yana kallon cikin wuta ya ce: “Madam Nablah ta ɓoye gaskiya. Wannan ba dai-dai bane. Wannan tsoho… yana da alaƙa da hasken da Sophia ta ke kira.” Zuciyarsa ce ta fara ɓallewa daga duhun da Madam Nablah ta jefa shi ciki. A hankali, harshen soyayya da gaskiya ya fara haskaka cikin zuciyarsa. Shaprees a hankali ya furta: “Asmeen ba zata cancanci wannan hukunci ba... kuma Sophia ba zata so haka ba.” ★★★★ Madam Nablah kuwa, tana zaune a cikin ɗakin tsafinta, ta fara jin karfi yana kubucewa daga jikinta. Ta juya cikin madubi, amma madubin ya fara hayaƙi. Madam Nablah a rikice ta furta: "Wani yana shirin tono sirri... wani yana tasowa daga ƙasa?" Sai wani baƙon haske ya fito daga madubi. Fuskar Abul Abeesh ne. ta tintsire da dariya amma cikin zuciyarta ta fara jin tsoro da faduwar gaba. Madam Nablah a ruɗe ta miƙe tsaye tana faɗin: “Bai kamata ka rayu ba! Na tsare ka da tsafin da babu wanda zai iya warwarewa! Amma a yanzu ana shirin ruguza wannan tsaron da ƙarfin haske shin waye wannan mai ƙarfin ikon shiga makomata?....." Sai wani murya daga cikin madubi ya furta: “Idan haske ya haɗu da gaskiya, komai na duhu zai fāɗi...” Madam Nablah ta firgita. Ta fahimta cewa hasken da take ƙoƙarin hana wa shi ya fara fitowa. Kuma wannan haske, ba daga waje yake ba — daga cikin waɗanda ta cuta da hannunta ne..... *NEXT PAGE.....* New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 35 to 36 Tasleem da ƙarfin tsafin hasken ta take ƙoƙarin buɗe ƙofar nan, cikin ɗaga murya da azaba take faɗin "Ya Amaar ku taimaka mun..." Amaar da Abeesh hannu suka sa zasu ture ƙofar, ba shiri suka ja da baya tare da yarfe hannayen su sakamakon wutar ƙuna da suka ji, ƙofar ta ƙone musu hannu, Abeesh tsabar azaba sai da ya

Chapter 20 of 34