Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Sojojin su na zuwa suka ce duk ku fito daga cikin motan nan, haka aka tsare su da tambayoyi, daga masu musu tsawa sai masu zaro musu jajayen idanuwa gaba ɗaya sun shiga cikin firgici, idon Asmeen ne ya sauƙa akan wata maroon jeep car, leƙa number motar tayi taga na gidan su ne, taɓa Nasreen tayi tana nuna mata motar Tasleem, Nasreen zaro ido tayi ga hawaye duk ya wanke mata fuska ta ce "Ya Abeesh motar Tasleem..." Shima gani ya yi tare da girgiza kai yana faɗin "da mun sani tin farko mun sanar musu gaskiyar abinda yake faruwa, gashi nan ƙarya ta jawo mana damuwa..." Asmeen ta ce "abu ɗaya ne kawai ya jawo mana wannan rikicin shine sanar musu da muka yi daga Kaduna muke, yanzu kuwa ba damar canza magana domin bazasu taɓa yadda damu ba...." Nasreen ta ce "ai kuwa dole zamu sanar musu gaskiya..." Abeesh ya ce "yanzu meye abun yi?..." Duk wannan tattaunawar da suke yi suna durƙushe ne da gwiwowinsu sun ɗaga hannu sama, ga sojoji a kewaye da su, a haka suka kwana har asuba hannu a sama, duk wacce ta rintsa to a tsawace za'a tayar da ita, Asmeen tasha kuka kamar ranta zai fita ga ta gaji sosai, hannu duk ya yi tsami, ƙafafuwa duk sun tutturje, kan gwigwarta ba ƙaramin ciwo yake mata ba, tana sauƙe hannu soja zai darara mata tsawa haka itama Nasreen gaba ɗaya ƙafafuwan ta kamar wanda aka sa ƙaton dutsi aka danne mata su ko rintsawa bata yi ba gaba ɗaya idanuwansu sunyi jajawur tsabar azaba da kukan da suka sha, Shi kuwa Abeesh kwana ya yi yana tsallen kwaɗo wani sojan yana binsa a baya da dorina, yana tsayawa za'a zabga masa dorinar, gaba ɗaya ya fita hayyacin sa.... Da Asuba misalin ƙarfe 6 da rabi gari ya washe sosai, sai a lokacin Tasleem ta samu damar farfaɗowa tana kame da goshin ta, ganin ta a kwance akan carpet ne yasa ta miƙe tana dudduba jikinta, taga ko ina yayi jawur kamar ƙonuwar wuta, tana cikin wannan halin ne sai ga Amaar ya fito daga toilet yana goggoge sumar kansa da towel da farar jallabiya a jikinsa wanda ya tsaya masa a iya gwiwa, dake shi ya juma da farfaɗowa har ya yi sallar asuba. Ganin ta farfaɗo ne yasa ya nufi yanda take tare da faɗin "kina lafiya, fatan kin tashi cikin ƙoshin lafiya naga jikin ki duk ya yi ja, ya kamata na duba lafiyar jikin ki..." Gaba ɗaya a ruɗe yake wannan maganar idonsa akan ta, domin ba ƙaramin tausaya mata ya yi ba, shima kamar wanda ya tashi daga jinya eyes ɗin sa a shashshanye. Tasleem tsabar takaici da haushi tama rasa bakin magana, ido kawai ta zuba masa hawaye kuwa ya gagara tsayuwa sai girgiza kai take, tana tunanin wani irin hukunci zata ɗau akan sa, suna cikin wannan halin suka ji yo knocking, Amaar idonsa akan Tasleem ya bada izinin shigowa, ɗaya daga cikin masu aikin gidan ne ta shigo tare da faɗin "Sir an kammala breakfast, za'a kawo muku nan ne ko a bar muku a dinning?..." Amaar hararar ƴar aikin yayi sannan ya ce "kin gaishe da Madam ɗina?..." Ƴar aiki haɗiyar yawu tayi kanta a ƙasi ta ce "ina kwana Madam ?..." Tasleem a fusace ta kalle ta tana faɗin "da ban kwana ba zaki ganni a gaban ki a tsaye?..." Ƴar aiki kai a ƙasi ta ce "Allah ya baki haƙuri..." Tasleem tsabar masifa har jijiyoyin wuyan ta sun tattashi, fuska tayi jawur ta ce "lokacin da akayi rabon haƙuri ba'a halicce ni ba..." Amaar murmushi ya yi sannan ya kalli ƴar aiki ya ce "je ki kawo mana nan ...." yana furta wa tayi waje domin Allah take ta bar room ɗin nan domin zata iya yiwa Tasleem rashin kunya idan ta musguna mata... Tasleem gaban Amaar ta je ta tsaya tana nuna shi da yatsa tare da faɗin "kai kuma Insha Allahu ni ce ajalinka, kana ji ba nace ni zan zamo ajalinka, a hannuna zaka mutu, wallahi ji nake kamar na shaƙe wuyan ka a yanzu..." Amaar ba abinda yake sai murmushi idonsa akanta, Mai aiki ce ta dawo da paranti kuloli a hannun ta, tsayawa tayi sannan ta ce "Sir aina za'a ajiye?..." Tasleem ce ta je har gaban ta sannan tasa hannu ta karɓi parantin sannan ta dawo gaban Amaar fuska a ɗaure ta ɗaga parantin sama ta sau a ƙasi, kulolin abincin duk suka tawarwatse, ƴar aiki toshe bakin ta tayi da hannayenta biyu tana zaro ido ta ce "ke kina da hankali kuwa? Abinci mai daraja zaki wulaƙanta?..." Wani irin juyi Tasleem tayi ta shaƙo wuyan Ƴar aiki tare da manne ta a jikin bango tana faɗin "meye to? saboda ba abinci a gidan ubanki shine zaki rikice kina so ki mun rashin kunya? daman haka ƴaƴan talakawa kuke da zaran kun samu wurin hutawa sai ku nemi ku falle..." Amaar cikin sassanyar murya ya furta "Tasleem...." Juyowa tayi tare da hankaɗa ƴar aiki saida ta faɗi ƙasi tayo kan Amaar tana faɗin "ehen ko zaka rama mata ne?..." Amaar kallon ƴar aikin yayi sannan ya ce "ke bar ɗakin nan..." Haka ta tashi ta karkaɗe jikinta tabar ɗakin... Amaar ya maida idonsa kan Tasleem sannan ya ce "me kike son ci? zan shiga kitchen da kaina na girka miki abunda kike so..." Dogon tsaki taja tare da furta "bani da lokacin ka ..." Nufan toilet tayi taje ta ɗauro alwala sannan ta tsayar da sallar asuba tare da lafula, Daga nan ta ɗauki handbag ɗin ta da wayar ta, tana duba wayar taga 100 missed call ƙiran Nasreen ne sai ƙiran Asmeen da na Abeesh zaro manya-manyan idanuwanta tayi tare da faɗin "innalillahi, ban taɓa kwana a wani wuri ba sai wannan lokacin ta dalilin ka, gashi yanzu na tayar da hankalin ƴan uwana, wallahi nayi danasanin saninka a rayuwata, ka shiga rayuwata da yawa...." Tana kuka tabar ɗakin, tana sauƙa falo ta tarar da ƴan aiki su huɗu a wuri ɗaya suna gulma, Tasleem tsarguwa tayi ta kasa yin haƙuri sai da ta same su, tana zuwa ta ce "duk kuyi mun kneel down..." Kallon juna suka shiga yi kafin suka ce "me muka miki da zaki ce muyi kneel down?..." Tasleem ta ce "ko baza kuyi ba?..." Suka ce "gaskiya ba zaman ki muke ba don haka baza muyi ba..." Tasleem jinjina kai tayi sannan ta ce "gaskiya ne..." Shima Amaar fito wa ya yi ya ce "meya faru?...". Ƴan aikin ne suka sanar masa abinda yake faruwa... Kallon Tasleem ya yi Sannan ya ce "meyasa zaki hukunta su? ni nayi miki laifi ni ya kamata ki hukunta ba su ba...." Tasleem ta ce "okay kai zo ka mun kneel down..." Duk ƴan aiki zaro ido suka yi tare da faɗin "a'a ki bari mu zamu yi, domin bai cancanci wannan wulaƙanci ba..." Ta ce "meyasa da farko dana saka ku bakuyi ba? saboda haka yanzu reshe ya juye da mujiya..." Tasleem kallon Amaar tayi sannan ta ce "kai zo nan, kayi abinda na saka ka...." Amaar bai ji komai ba haka yaje gaban ta ya yi kneel down. Ta ce "ka ɗaga hannun ka sama..." Hakan kuwa yayi kamar yanda ta umarce shi... Wata daga cikin ƴar aikin ce tayi murya ƙasa-ƙasa ta cewa sauran "Asiri fa tayi masa..." Wannan furcin ne ya sauƙa akan kunnen Amaar, murmushi ya yi sannan ya ce "ba Asiri bane, tsananin so da ƙauna ne..." Duk shiru suka yi da sauri suka bar falon, ita kuwa Tasleem zama tayi akan kujerar falon ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya tana karkaɗa ƙafa, sai faman danna wayar ta take, shi kuma idonsa akan ta ji yake kamar ana ƙara masa ƙaunar ta ne, yana kuma farin ciki ko ba komai ta yaye masa damuwa ɗaya, wato na matsalar ƙwaƙwalwa, yanzu yabar wannan matsalar... Suna cikin wannan halin sai ga wani soja ya turo ƙafa ya shigo, har ya buɗe baki zai yi magana idonsa ya sauƙa akan Ogansu, da sauri ya ƙarisa shigowa ciki tare da faɗin "Ogah ya haka kuma?..." Tasleem ko ɗagowa bata yi ba balle ta kalli yanda suke. Amaar ya ce "No kar ka damu faɗan cikin gida ne, wannan ɗin sarauniyata ce nayi mata laifi shine take hukunta ni..." Sojan ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba sai dai babu yanda ya iya, ya sanar da abinda ya kawo shi yana faɗin "Ogah wasu ne suka zo wurinka tin jiya cikin dare misalin ƙarfe 12 zuwa 1 amma bamu bar su sun zo nan ba..." Amaar ya ce "meyasa baku sanar mun ba a tin jiya?..." Shi har ya manta kwana yayi a sume. Sojan ya ce "sun ce daga Kaduna suke kuma mun san bakada kowa a Kaduna shiyasa muka riƙe su a can cikin quarters...." Amaar ya ce "su nawa ne?..." Sojan ya ce "mata biyu namiji ɗaya..." Amaar abun mamaki ya bashi jin har da mata, yana cikin tunani yaji Sojan ya ce "amma matan ƴan biyu ne domin kamar su ɗaya sak..." Tasleem tana jin haka tayi saurin ɗagowa tana kallon Sojan, Sojan yana ganin ta ya zabura tare da nuna ta da yatsa yana faɗin "Ogah inaga fa matan Aljanu ne domin kamar su ɗaya sak da wannan ta zaunen..." Sai a lokacin Amaar ya kawo a ransa cewa ƴan uwan Tasleem ne, itama Tasleem a zabure ta miƙe tsaye tana faɗin "Nasreen and Asmeen..." da gudu tayi waje ko tsaya ɗaukar jakar ta bata yi ba, Shima Amaar bin bayanta yayi da Sojan.... NEXT NEXT NEXT New Book 2025. *💋HASKEN RUHI💋* (Spiritual Light) A Fictional Story✍️ Writing and Organizing Asma'u Muhammad Auwal Which is best known as *Asmeetah writer* *WhatsApp 09065443871* 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ EP 23 to 24 Tasleem tana isa wurin da ƴan uwanta suke a durƙushe bata san lokacin da kuka ya yanko mata ba, itama durƙusawa tayi tare da rungumo Asmeen, daga lokacin Asmeen ta suma akan ƙirjin Tasleem, a ruɗe ta fara jijjiga ta tana ƙiran sunan ta "Asmeen! Aasmeen!! ke Asmeen dan Allah ki tashi babu abinda ya faru da ke..." Itama Nasreen hankalin ta ba ƙaramin tashi ya yi ba duk wahalar da tasha hakan bai hanata jijjiga Asmeen tana kuka itama. Tasleem ta ce "Nasreen kin sha wahala sosai dan Allah kuyi haƙuri...." Nasreen cikin fushi da takaici ta finciko Aasmeen daga kan Tasleem ta rungume ta sosai tana hararar Tasleem tare da faɗin "wannan tashin hankalin da muka shiga duk ke ce sila, hankalin mu ya tashi duk saboda ke, because of you mun kwana a haka yanda kika gan mu kamar wasu ɓarayi, ga can Abeesh yanda sojoji suka masa abin tausayi...." Tasleem tana hawaye ta ɗaga kai ta kalli Abeesh yanda yake ta tsallen kwaɗo a wahalce gaba ɗaya ya fita hayyacin sa domin mintuna kaɗan zai iya haɗiyar ransa, ɗan dakatawa ya yi yana hutawa Sojan nan ya ɗaga dorina ya zabga masa a baya, a zabure Tasleem ta miƙe da gudu ta nufi wurin sa tana ƙiran sunan sa cikin kuka, tana zuwa tasa hannu ta ɗago Abeesh wanda ya kife a ƙasi, zaunar da shi tayi tare da faɗin "Sannu Ya Abeesh, kayi hakuri dan Allah...." Sojan daka mata tsawa ya yi yana faɗin "ke wa ya baki umarnin ɗago shi? wace ce ke?..." Tasleem cikin takaici da cije leɓɓe ta ɗago tana masa wani irin kallo na raini kafin daga bisani ta ɗaga hannu ta zabga masa mari tana huci ta ce "baka da matsayin da zaka san ko ni wacece, idan kuma ka takura kanka akan sanin ko ni wacece to zaka mutu ne..." Sojan ya ce "whattt ni kika mara?..." Tasleem ta ɗago hannu zata ƙara masa marin ya yi saurin riƙe mata hannu yana zaro mata rikitattun idanuwansa yana huci kamar tsohon zaki, Tasleem tana ta yunƙurin ƙwace hannunta daga riƙon da ya yi mata amma ta kasa domin ba ƙaramin riƙo ya yi mata ba.. Ba tare da Sojan ya ankara ba ya ji shima an damƙe masa hannun da ya riƙe Tasleem da shi, ɗagowa ya yi yana kallon Amaar ya ce "Oga wannan yarinyar hannu tasa ta mare ni..." Fuska ba annuri ya ce "ka sake mata hannu..." Tasleem tana ta yunƙurin zare hannun ta daga riƙon da sojan yayi mata, sannan shima sojan Amaar ya riƙe masa hannu da gasken gaske domin ji kake hannun yana ƙaras ƙaras alamun ƙashin hannun ne yake goce wa, Sojan ya ce "Oga my hand please..." Cikin tsawa Amaar ya ce "na ce ka sake mata hannu..." Sojan yana sakin Tasleem wani irin naushi Amaar ya kai masa akan lips ɗinsa har sai da ya dungura... Tasleem itama cike da takaici ta ɗaga hannu ta zabga wa Amaar mari, ba tare da ya motsa ba ya lumshe ido kafin ya buɗe har ta ƙara masa marin ta ɗayan ɓangaren. Sojojin wurin ne suka motsa zasu zo wurin Amaar ya yi saurin ɗaga musu hannu yana girgiza musu kai alamar a'a... sauƙe idanuwansa ya yi akan kyakkyawar fuskar ta wanda ya hargitse tana huci ta ce "na tsane ka wallahi, duk da ban san ka ba, ban san asalin ka ba amma ji nake kamar na kashe ka, duk kai ka jawa ƴan uwana shiga wannan tashin hankali, meyasa ka shigo rayuwa ta? dan Allah na roƙe ka da sunayen Allah ka fita daga cikin rayuwata tin kafin ka jawo mun matsala...." Amaar ya ce "idan kuma ban fita ba fa? me zai faru?..." A gigice Tasleem ta furta "zaka mutu ne, duk wanda ya shigo mana rayuwa mutuwa yake...." Murmushi ya yi tare da jinjina kai cikin salo ya juyar da eyes ɗin sa kan Nasreen wacce take zaune Asmeen a kwance kan cinyarta itama su ɗin take kallo tana mamakin ta yanda suka haɗu har suka fara wannan cakwakiyar..." Amaar ya juyar da kansa kan Tasleem yana girgiza kai ya ce "bazan iya fita daga cikin rayuwar ki kai tsaye ba sai dai idan kece kika cire ni da ƙarfin gaske, ta hanyar kisa, na fison ke da hannunki ki rabani da rayuwata ba wai aga gawata lokaci guda ba..." Tasleem tana hawaye ta ce "inda inada halin kashe ka, to da yanzu ba wannan labarin ake ba..." Buɗe tafin hannunsa ya yi tare da faɗin "bindiga..." yana alamu a sojan sa ya miƙo masa bindiga, kafin mintina aka ajiye masa bindigar akan hannunsa ba tare da sanin abinda zai aiwatar ba, idonsa akan Tasleem ya ce "ga bindiga ki harbe ni a wurin da zan mutu Lokaci guda..." wurga mata ya yi ita kuwa ta cabke tare da kunna kunamar bindigar ta saita shi tare da faɗin "kana tunanin bazan iya bane..." Amaar ya ce "nasan zaki iya shiyasa na baki damar aiwatar wa..." Sojojin sa ne suka fara "Please Oga don't allow her..." Ɗaga musu hannu ya yi tare da faɗin "ku dakata mun..." Nasreen ta gama tsurewa tana tunanin shin Tasleem zata iya harbe shi ko kuma pretending ne, Shi kuwa Abeesh tinda ya kifar da kansa bai ƙara ɗagowa ba tsabar tsananin wahalar da ya sha.... Amaar idonsa akan Tasleem wacce ta saita shi da bindiga ya ce "ki saita kan goshi na kina harba wa a take zan mutu, ko kuma a saitin zuciyata nan ma ko minti ɗaya bazan ƙara shurawa a duniya ba..." Murmushi Tasleem ta yi sannan ta ce "da kuwa zan fi kowa farin ciki idan ka bar duniya, zan harbe ka a saitin zuciyarka ne saboda anan ka ajiye soyayyata, wannan soyayyar kuwa so nake na dagargaza ta..." Jinjina kai ya yi sannan ya ce "Go ahead my beautiful girl..." Tasleem kamar wacce aka bata umarni lokaci guda ta harba bindigar sai ga bullet ya fasa ƙirjin sa...." Amaar a zabure ya ɗora hannunsa akan wurin da ta harba wato kan ƙirjinsa ta ɓangaren dama... Nasreen a zabure ta da ka uban ihu tare da furta "Tasleemmmm...." Haka sojojin suka nufo shi, a ruɗe Amaar ya ɗaga musu yatsa yana karkaɗawa alamar kar su nufo shi, Jin ƙarar harbi ne yasa Asmeen farfaɗowa a tsorace ta rungumi Nasreen tana faɗin "wayyo sun harbe mu ko? mun shiga uku sun harbe mu..." Abeesh shima ɗagowa ya yi yana kallon Tasleem cike da mamaki ganin yanda ta harbe shi, duk a tunanin sa pretending take duk da ta farmake shi a gidan su, duk da ba shi aka harba ba amma ya ji zafin harbin har cikin zuciyar sa, yana motsi da lips

Chapter 14 of 34