Reading SIRRIN YA'MACE COMPLT BY MRS ALKALI Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng ÿþ SIRRIN YA'MACE

*Gidauniyar Zuciyar Mace*

Na

Ummuh Eyshal

~Mrs Alkali ~

GABATARWA

"Wannan labarin na sadaukar dashi ga kungiyar mata na SIRRIN YA'MACE ( WOMEN ONLY) by Jiddatulkhairii &Maijiddah Bello, wacce aka kafa domin bayar da shawarwari da tallafi ga mata masu matsaloli na rayuwar aure, lafiya, da tarbiya."

"Daga cikin dubban manbobi wasu sun rayu ta dalilin wannan kungiyar , wasu kuma sunbata rayuwar aure da sunan ta."

"Maza da yawa naganin kungiyar barazana ce ga zaman lafiya, amma akoi wani sirri wanda ba kowa ne yagane hakan ba."

Kubiyo alkalamina danjin wanne irin sirri ne wannan.

GARGADI

"*Labarin littafin SIRRIN YA'MACE, ™ir™irarran labari ne, idan yayi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata, arashi ne.*"

"Wannan littafin mallaki na ne Ban lamunci a juya mini littafi, ta kowace irin siga ba, sai da izinina "

Page

GARIN ZARIYA

Anguwar Sabon Gari

"Misalin qarfe 1: 30pm na dare wata ham matashiyar mata ce mai kimanin shekaru 35yrs, zaune take agefen tafkeken gadon ta, wannan shi ne karo na 5 kenan tana ta faman kiran wayar sa, amma bai daga ba, a karshe ma da ta matsa da kiran, sai ya danna mata user busy , ganin haka ne haushi ya kamata , tayi jifa da wayar, akan gadon ta, tsaki taja mai karfi, afili ta furta, ban san me yasa ka chanza ba Jaheed, wannan ba halin ka bane, why!why!!whyyy ta karasa maganar cikin wani irin zafin rai da ihu."

"Wassu hawaye ne masu zafi suke gangarowa agefen kuma tunta, cikin dacin murya mai amo ta furta, Allah ka kawomin dauki."

"A hankali tashiga ambaton Sunan Allah a cikin zuciyar ta a hankali ta ke sauke ajiyar zuciya, wani irin sanyi ne yake mamaye cikin zuciyarta bayan wani lokaci tasa hannun ta ta share hawayenta, wayanta da ta wurgar akan gado ta dauka, datan wayan ta tabude ta hau dandalin sadarwan ta na Facebook, tana hawa taci karo da wani group da ake kira da SIRRIN YA'MACE (WOMEN ONLY)by Jiddatulkhairii &Maijiddah ."

"A hankali ta kutsa cikin group din nan tafara cin karo da posting din mata dasu ke da matsala a harkar zaman takewar su da mazajen su, cikin nitsuwa tafara bibiyan su, ganin irin shawarwarin da ake basu a comment section ne yasa a hankali zuciyar ta tafara rayamata cewa, shin mai zai hana itama tanemi shawari game da halin da take fiskanta a zamanta kewar aurenta da mijin ta, wata Kila zata iya samun mafita ,zuciyar ta ce tayi na'amm da wannan shawaran, nan take tashiga ta fara typing."

Typing tafara yi kamar haka;

"""Asslm barkanmu da warhaka sister, kuba ni shawari miji nane baya dawowa gida da wuri, yanzu haka danake typing dinnan bai dawo, ba nakirashi 10 times baiyi picking call dinaba a karshe ma user busy ya ke danna mini, plz kubani shawari ko Zuciya ta zatayi sanyi"""

"Bayan tagama typing din ne ta tura sakon ba jimawa admin tayi approving din post din, nan danan matan group suka hau zuba comment, fara karanta comment din su tayi, watace tace sister yakamata kizauna da mijin ki akan matsalar ku tattauna a tsakanin ku kufiskanci juna, inda wata mai suna , zulaiha tayi comment akasan , wannan rubutun kamar haka,"

"""Hmmm ai bazaki gane halin da take ciki bane ko da yake bake akayiwa hakan ba, shiya sa ke bazaki san zafin abun ba , plz sister inkinga comment dina kimin magana ta inbox dina , Insha Allah,zanbaki shawarwarin da suka dace da ke"""

"Wani irin ajiyar zuciya ta sauke, nan take tabita ta private,"

"""Asslm sis nice wacce kika ce in miki magana ta inbox,"

"""Ok ai sister kifita a harkarshi kawai, don yaga kin damu da shi ne , a duk san da zaki nunawa namiji kin fiye damu wa da shi toh fa daga nan ki shirya karbar wulakan ci awajen sa kinsan fa maza zumane sai da wuta, dole sai ana hada musu da gashin kuma, ina mai tabbatar miki inyaga kinfita sabgarshi, zakiga yanda zai dawo cikin ruwan hankalin sa, ina dalili Zaki zauna bakin cikin namiji ya kasheki,"

"Wataqila ma yana chan wajen wata budurwar sa ke kuma ya barki, da bakin ciki, gara kikoyawa kanki , fita sabgar sa,, don kinga nima haka ta taba faruwa da ni amma dana bi wannan hanyar, ai ba shiri ya shiga ruwan hankalin sa."

"Ajiyar zuciya ta sauke bayan tagama karanta message din da zulaiha ta rubuta mata, a hankali taji wani bangare na zuciyar ta tana aminta da shawarwarin da zulaiha ta bata, tabbas haka halin maza yake, ko ita kawayenta sun sha fadamata takiyayi kanta da lamarin rijalu, kartaga kamar mijin ta salihi ne, don namiji ba dan goyo da zani bane, Amma kullum takan ce musu banda nata mijin , sai gashi yau maganar da suke fadamata ya tabbata tun da gashi nan zulaiha ta nana ta mata , typing tashiga yi kamar haka."

"""Ok sister nagode da shawarwarin da kika ba ni insha Allah zan gwada hakan"""

"Ganin karfe 2:00pm tayi yasa ta kashe datan wayan ta ta konta, bata jima ba da konciya wani bacci mai nauyi yayi awungaba da ita."

"Hajiya Marwat kenan, kyakkyawar matashiyar mata mai kimanin shekaru 35yrs aduniya, Marwat kyakkyawa ce ajin farko, Allah ya mata baiwar kyau da ba ko wacce mace ba ce tasamu irin sa ba, tana da matsakaicin jiki mai daukan hankali, fiskar ta na dauke da wani irin kwarjini, da haiba, gawa su irin idanu masu dan zurfi da ke dau ke da launin fari da dan koren haske aciki, hancinta dan madai dai cine , siriri, kamar na larabawa, gawani irin irin lips jajaye da bakinta ke dauke da shi, Allah ya azurta ta da dogon gashi baki mai santsi, in kaganta zaka dauka yar shekara 20yrs ce tsabaragen yanda take kula da jikinta."

"Tana zaune da mijin ta Alhaji Mujaheed agarin zariya a anguwar sabon gari, yau kimanin shekaru 10yrs da auren su kenan , Allah baitaba basu haihuwa ba, suna zaune cike da soyayyah da kaunar junan su, kafin alkalamin kaddara tashigo ciki ta chanza komai, a yanzu Mujaheed baya dawo wa gida dawuri don sai ya kai 1:30pm a office ,wannan shine gagarumin matsalar da ta kunno kai acikin zaman takewar auren su, abun yana damun Marwat, tayiwa Mujaheed korofi amma yace mata takara hakuri sabida akoi muhimmin aikin da yake tsayar da shi a office din shiya sa , amma da zarar ya warware matsalar, komai zai koma normal kamar da ,tun Marwat tana yadda da batun Mujaheed har zuciyar ta tafara mata was wasi game da hakan ,wanda hakan ne yasa a yau ta baiyana wa group din SIRRIN YA'MACE domin neman mafita."

"Wannan Kenan kubiyoni danjin yan da zata kasan ce wasan bai faraba, domin kuwa hausawa sun ce wasa farin giki, muje zuwaa..."

"Dare ya tsala sosai ba abunda kake ji sai karar iska dake kadawa na sanyin damina ,wani irin iska mai dauke da ni'ma ne yake kadawa misalin qarfe 2:50pm wata farar mota ce kirar Roll Royce ce kitafiya cikin nitsuwa, a cikin anguwar sabon gari dake cikin garin zariya, tafiya motar takeyi cikin nitsuwa daganin yanayin tukin kasan mamallakin motar ya mallaki hankalin kansa, a hankali ya iso kofar wani makeken mansion, horn yayi, bai wani jima ba aka zuge gate din, cikin nitsuwa ya cillah hancin motar sa wani farfajiyar aji motoci ya nufa, parking yayi yaka she motar, ya dau kusan 3min kafin ya zuro fararen kafafun sa waje, a hankali, ya fito gaba dayan sa, ya Allah, Wani kyakkyawan matashin magidanci ne mai kemanin shekaru 45yrs, fari ne sosai dan har fatarsa tana daukar ido da wani irin kyalli, idanun sa ruwan kasa ne wanda hakan ya kara baiyanar da kyan sa da korjinin fiskar sa, hancin sa siriri ne mai tsari, fiskar sa bata cika kauri ba kuma ita ba siririya bace, yana dauke da wani irin siririn gemu baki mai kayatarwa, dogo ne so sai yana da fadin kirji, kana ganin sa kaga ingarman namiji, don daganin tsarin halittar sa kasan yana kashewa jikin sa kudi ba na wasaba, don bazaka ce yakai 45yrs ba azahiran ce."

"Wani irin kamshin turaren sa mai sanyi da shiga rai ne ya mamaye farfajiyar gidan, baba maigadi ne ya rugo da gudu dan rusu nawa yayi yace barka da dawowa alhaji cikin wata irin murya mai kauri, da taushi acikin ta yace yauwa baba barkan ka dai mun sameku lpy, baba maigadi ne yace lafiya kalau alhaji bai sake magana ba"

",farfajiyar gidan yafara ratsawa, da ke dauke da wani haske kai kace da rana ne, cikin wani irin takunsa na kasaita da cikakkun maza, yanufi kofar part din sa, wani irin Black suit ne sanye ajikin sa, daganin kayan kasan anyi barin kudi wajen sayan su, rike yake da brief Case din sa, kai daganin sa kaga namijin duniya, wanda yasha gwagwarmayan rayu, anga jiya anga yau, kuma ana sa ran ganin gobe da izinin Allah."

"A hankali ya saka yatsar sa manuniya ajikin kofar, wani irin kara na'uran jikin kofar tayi tare, da cewa welcome Mr. Mujaheed, budewa ta shiga yi da kanta, a hankali yasanya kafafun sa dake sanye cikin wani irin Black cover shoes masu uban tsada, wani irin ajiyar zuciya ya sauke a lokacin da hancin sa ya shakomasa daddadan kamshin turaren Airfreesher da parlourn keyi, wani irin lumshe kyawawan idanun shi yayi,"

"A hankali ya shiga takawa zuwa stairs din parlourn, direct bedroom din sa ya nufa dan yasan warhaka, Marwa tana can tana jiranshi sanin da yayimata baza ta iya bacci ba batare da yadawo ba, a hankali yashiga tura kofar dakin, ya Allahu, kai kunga cikin bedroom dinsa kuwa sai kace a kasar turai, turus yayi ya tsaya idanunsa ya shiga bazawa a cikin dakin, da alama wani abu yake nema,"

"Rufe kifar yayi, aransa yana tunanin toh yau mai yahana Marwa zuwa dakin sa kamar kullum yadda suka saba, ajiyar zuciya ya sauke a hankali, shi kansa abun yafara damun sa, to Amma ya zaiyi, komai lokacine dan in bai tsaya ya kula da kamfanin sa ba komai na shirin tabarbare masa, besan maiyasa ba wannan karon Marwa ta"

"gagara fahimtar sa, dazuma yana ganin kiran ta, bai dauka ba sabida meeting da sukeyi, a cikin companyn su, shiyasa ya danna mata user busy,"

"A hankali ya shiga rage kayan jikin sa, ya Allahu kunga wani irin building body na ingarman namiji da yake dauke dashi kuwa, bathroom ya nufa, bayan yagama rage kayan jikin na sa,"

"Bayan kamar 10minutes yafito daga bathroom din daure da towel a kunkumin shi, dressing mirro, wani body lotion ya dauka, yashiga shafawa ajikin sa bayan yagama ne ya dauki turarukan sa masu uban tsada ya fesa, wani dan lungu ya nufa acikin dakin, ya, Allah, Waldrop ne awajen , kai kace boutique ne aka bude tsabaragen kayan dayake wajen, pyjamas din sa masu taushi ya dauka, wandon kawai ya saka, dan yazama kamar al adar sa baya son saka rigar pyjamas din yafi jin dadin konciya a haka acewar shi."

"Wayoyin sa ya dauka, yanufi kofar fita, a hankali yake tafiya kamar mai tausayin taka kasan , kofar dakin ya bude a hankali, idon sa ne ya sauka, akan ta tana konci sanye da nata pyjamas din, bacci takeyi cike da nitsuwa da konciyar hankali."

"Wani irin murmushi ne ya subce masa, ya Allahu kunga yanda murmushi yamasa kyau kuwa, a hankali yashiga nufo gadon nata, hawa yayi yazauna, gashinta daya barbaje a fiskarta yashiga jaramata cike da nishadi, kyakkyawan fiskar ta ne ya baiyana, atake yaji wani irin kasala ta na kamashi, wani irin sha'awa da bukatuwa ne suka taso masa, cikin nitsuwa ya kai hannunsa yafara shafa ta , Marwa ce ta bude idanunta a hankali ta sauke su akansa, wani irin sanyi ne ya mamaye zuciyar ta dan ba karamin so takema sa ba, kanta ta daga ta kalli agogon dake manne a saman dakin ganin agogon ya nuna qarfe 3:00pm nadere ne ya sa ranta kara baci wato ma sai yanzu ya ga daman dawowa gidan, bayan yagama da budurwarsa shine yanzu zai zo yatashe ta cikin baccin ta, shawarar da zulaiha ta bata dazu ne ya shiga dawo mata,jin yacigaba da shafata ne yasa ta saka hannunta ta buge masa nasa hannun , cikin nitsuwa ya dago idanunsa da suke nuna bukatan mace yace habeebty, come here i want you badly, wani irin juyawa Marwa tayi tacigaba da baccinta ganin haka ne yasa mujaheed kara matsawa jikin ta, dan shi tunda yake da Marwa bata taba masa abu makamancin wannan ba, duddah tafara masa korafi akan yacika kai wa dare a office yanzu, amma bata taba bacci inbai shigo gidan ba sabanin yau da yasameta har ta kwanta,"

"Sake matsawa jikin ta yayi, a hankali yafara zare mata rigan jikinta, wani irin buge masa hannu Marwa tayi tare da jan wani uban tsaki,"

"A hankali Mujaheed ya cire hannunsa ya dai na kokarin cire mata rigan nata, me Marwat take nufi da shine da take jamasa tsaki haka, kenan ma ba bacci takeyi ba, tana sane da shi, kenan ma wulakanci takemasa, a hanakali yaji sha'awar tana gushewa, don ya tsani reni arayuwar sa ,addu'an konciya yayi ya kwanta agefen ta tare da jan blanket ya rufe zuwa kunkumin sa."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Kiran sallan asuba ne ya tashe shi don indai kula da addini ne akoi shi da kokari a ta wannan fannin, mika yayi tare da karanto addu'ar tashi daga bacci, tashi yayi ya nufi toilet wanka yayi tare da dauro alwala, fitowa yayi, ya dauki farar jallabiyarsa yazura, farin hula tabani kasha hadisi ya saka akanshi, nan ya dauki turarukan sa masu uban kamshi yashiga fesawa,"

"Bayan yagama ne ya nufi bakin gadon a hankali ya shiga buga bakin gadon yana kiranta cikin taushin murya, habeebty, habeebty, ahankali ta shiga bude idanunta, sauke su tayi akan kyakkyawan fuskar sa , murmushi mai kashe zuciya ya sakarmata, tare da sunkuyawa ya sumbaci goshin ta, a hankali Marwa ta lumshe idanunta wani irin sanyi na ratsa zuciyarta, atake maganar zulaiha ta dawo mata, ""Maza Zuma ne sai da wuta"""

"Wani irin haushin sa ne yakamata atake ta kawar da kanta gefe, ganin abunda tayi ne yasa Mujaheed yaji zuciyar sa ta sosu, sai dai yakusan makara a sallah don haka ya nufi kofa, yana cemata sai nadawo kitashi kema kiyi sallah, ko kallon sa batayi ba bare yasaka ran zata amsa masa,"

"Shima bai sake bin ta kanta ba yafita abunsa, Amma ya kudur ce aransa idon ya dawo zai zauna da ita, su fiskan ci lamarin, don yasan shima bai kyauta mata ba."

"Kamar kullum bayan Marwa tayi sallan asuba ne, ta sauko kitchen domin hadawa mijin ta Mujaheed lafiyeyyen break fast, duddah yaudin fishi takeyi da shi bana wasaba, cikin kwarewa da himma tashiga aikinta hankali kon ce, dan duk kudi da wada ta irin na Mujaheed bai sa Marwa ta yadda ya kawo mata yan aiki ba, acewar ta ai yan aiki husband snatchers ne, ita kuma yanda take kaunar Mujaheed bazata taba iya sharing din sa da wata ba shiya sa take jurewa buka tunsa na yau da kullum."

"Bayan tagama hada masa break fast din ne ta shiga jera masa akan table, haka ta shirya komai staff staff, ba abunda yake tashi a parlourn sai kamshin turaren wuta dana abinci."

"Stairs tanufa cikin nitsuwa da class take taka matakalar, bedroom din ta tashiga, toilet ta wuce direct don wanka take bukatar tayi, bayan wassu mintuna tafito daure da towel, mirror ta nufa ta hau shafe shafen ta, san da tagama shirya kanta tsaff a cikin wani riga da skirt na wani leshi mai uban tsada kai kace gasar kyau na duniya zataje, wajen da take ajiye gwalagwalan ta tanufa, nan tashiga sakawa, sarka da dan kunne tasaka, sannan ta saka aworworo na gold masu shegen tsada da daukar idanu, wassu zobunan Gold tasanya a yatsun ta guda biyu, nan tanufo kasa, sai baza kamshi takeyi,"

"Tasan warhaka Mujaheed ya shigo ,gidan dan al'adar sa ne in yadawo daga masallaci ba zai hauro samaba sai yacika cikin sa da abinci, dan irin muta nennan ne masu kaunar abinci, baya wasa da cikin sa."

"Cikin takunta na jan hankali da class ta nufi dining table din da tagama jera masa abincin, ganin hakane ya sa Mujaheed binta, abaya kujera yaja ya zauna, a hankali cikin sanyin murya tace, good morning Zauji, bai kulata ba bare tasa ran zai amsa, domin tasan halin sa , yana nufin sai dai taje tayi hugging nasa yadda tasa ba gai she shi, ita kuma bazata iya ba dan wlh fishi takeyi da shi sosai, kuma ta dau alwashin sai ta goda amfani da shawarar da zulaiha ta bata a kansa."

"Mujaheed ne ya daga kansa ya zuba mata narkekkun idanunsa, jin idanunsa na yawo akanta ne yasa taki kallon position din da yake zaune, plate din abincin da tayi saving ta ajiye agaban sa, jollof din couscous ne yasha vegetables da hanta sai kamshi yakeyi ganin taki kallon sa ne yasa ya dauki spoon dinsa ya yi Bismillah yafara cin abincin, sa hankali konce wani irin lumshe idanu yayi, a lokacin dayaji dandanon abincin acikin bakinsa, a hankali yacigaba da cin abincin sa cikin nitsuwa, da class."

"Sanda ya cinye na plate din tass sannan ya dauki coffee data hada masa ya daura, akai hamdala yayi, tashi yayi yanufi cikin parlourn, ba tsammani taji saukan kakkausan muryansa yana cewa meet me at your room daga haka kuma ya wuce stairs abun sa."

"Kwanukan abincin tashiga tattarewa bayan tagama ne ta wuce stairs din, a hankali ta tura kofar dakin, akishingide ta hangoshi akan gadon, yacire jallabiyarsa dagashi sai dan boxes ne ajikin sa ganin fiskar sa ba alamar wasa ya sa ta shiga ta kowa a hankali har ta iso bakin gadon zama tayi ,tana facing din sa cikin zazzakar muryanta tace ""Zauji "" I'm here cikin dan shogwaba shogwaba, yarrrrrrr yaji ajikin sa, wani irin sha'awar tane yake taso masa,amma sam baya son ta fahimci hakan, don har yanzu yanajin haushin abun da tamasa jiya da dere ,duddah haka, ya danne bai nunamata ba, cikin kaushin murya, mai laushi, yace what wrong with you,,"

"Marwa ce ta daga idanu ta kalleshi jin wani irin tambayar renin hankalin dayake mata, wato ma shikam ya manta da abun da yamata, ita yabari da bakin ciki, wani irin kuka tasake, mai tsuma Zuciya."

"Mujaheed ne ya tsaya yana kallon ikon Allah daga tambaya kawai zatawani saka masa kuka, sai da yaga tayi mai isarta a hankali ya matso yafara bubbuga bayanta alamar rarrashi, ajiyar zuciya ta fara saukewa ajere ajere."

"Cikin sanyin murya yace habeebty nasan ban kyautamiki ba yanayin office ne ya rikene jiya, sanda na karasa"

",aikin gashi muna meeting kikayi ta kirana shiyasa kikaga ban daga ba,"

"Wani sanyi Marwa taji acikin ranta jin ba wajen budurwa Mujaheed yaje ba duddah tasan abune me wuya, amma hausawa sunce ba a yabon dan kuturu sai ya shekara goma da yatsu, turomasa baki tayi gaba, cikin murya mai taushi yace mata please habeebty i apologize, wani sanyi ne yake ratsa zuciyar Marwat a hankali ta ce apologize accepted, ""Zauji ""murmushi Mujaheed yayi a hankali salon maganar yashiga sauyawa, don zuwa yanzu kam Marwat tagama birkita masa lissafi."

"A hankali yashiga rabata da Kayan jikinta cikin salo da kwarewa, ya shiga sumbatar ta wassu irin sakonni masu wuyar fassarawa yake aikamata, nan da nan Marwat tafara sakin layi , dan Mujaheed ba bayaba wajen iya bama mace kulawa, haka suka faranta ran junan su, bayan komai ya lafa ne sukayi wanka tare, bayan sungama shiryawa ne Mujaheed ya ce mata bacci yakeji zai kwanta, haka ya dale gadon yayi kwanciyar sa, Marwat kuma ta dauki wayar ta ta bude data ta hau Facebook din ta, nan taci karo da massage din zulaiha kamar haka,,"

"""Sis ykk hope dai shawarwarin da nabaki yayi aiki"""

"Marwa ce ta mata reply kamar haka,,"

"""Ehhh wlh ai naga amfanin shawarwarin kinnan, ai bakiga yadda ya nemi sulhu ba, cikin gaggawa dan har munshirya , nagode sosai da shawarwarin ki sister."""

""" Hmmm dama bana fada miki ba maza zuma ne ai sai da wuta wlh, ai barin baki lbr sufa maza dole sai kin nuna musu kema fa jar wuya ce, Amma gaskiya sister kinyi giving up da wuri waya ce miki ana neman sulhu da wuri haka ai kibari ki waina masa hankali tukunna, kai bari kiji , su fa maza a duk san da suka ga kina musu biyaiyah,to wlh sunfi renaki, dan haka gara kifita safgar sa kawai ki nunama sa ko babu shi zaki iya rayuwa."""

"Wannan haka ne , na gode da shawarwarin da kika bani cewar Marwa da tagama karan ta massage din da zulaiha ta turo mata,"

Nan fa Marwa ta tsunduma cikin Page din SIRRIN YA'MACE ta ciga ba da duba wa.

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Zulaiha, zulaiha haka wata yar dattijuwar mata take ta kwalawa zulaiha kira, wai ni ko bakyajin ana kiranki ne kam,"

"Zulaiha ce taja wani irin dogon tsaki, kallon kawar ta habiba tayi, tace ni wlh nafara gajiya da wannan takura na yakumbo wlh, ace mutum bai isa ya sarara ba sai ta hau shi da kira sai kace wani abun zata tsinana masa, in banda ma Allah bai kawo mijin aure da wuriba ai da mutum yana gidan sa yana hutawa wlh baruwan sa da takura."

"Habiba ce ta ce uhumm haka

Please Login or Register in order to submit comment