Reading SIRRIN YA'MACE COMPLT BY MRS ALKALI Chapter 9 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

in tambayi ummah, dan murmushi yayi ya dan shafa sajen sa idanun sa na kanta, yace ahakan ne baba zai miki aure baki ma san shekarun ki ba."

"Haka zaki je kinayiwa dan dumurmur din saurayin ki shirme anyway shi yaga zai iya, ya karasa maganar tare da shafa dan gemun sa da sake kawata fuskar sa."

Mufeedah ce ta turo bakin ta gaba cike da shogwaba tace nikam nikam ba yarinya bace I'm 20yrs.

"Dariya tabawa Mujaheed ganin yarinta karara tattare da ita, yanzu tagama cemasa bata sani ba sai kuma gashi da taji ance mata yarinya ta fada."

Cike da zolaya yace uhuummm da alama ana son dan dumurmur dayawa tunda gashi dagjin zan afasa auren har kin tuna da shekarun ki.

"Cike da kunya ta rufe idanunta, ita kam yau taga ta kanta awajen Mujaheed tarasa me kamal ya tare masa daga dan gajere an dawo dan dumurmur kuma du."

"Babu zato baba zuwaira ta hankado labulen dakin tare da sallama sanda ta isa tsakiyan parlourn sannan tabuga sallamar, hannunta dauke da katon kofin silver ruwa ne acike aciki."

"A gaban Mujaheed ta ajiye kofin ruwan tace sannu bawan Allah ashe bako mukayi, ke Mufeedah shi ne baki sanar min nazo mugaisa ba."

Cike da kunya Mujaheed ya gaishe da baba zuwaira duddah ashekare zai girmemata nesa ba kusa ba.

"Washe baki baba zuwaira tayi tace Allah sarki bawan Allah sannu da dawainiya, an gode Allah ya saka da ameen Mujaheed ya amsa ."

"Tashi tayi ta fita , ita dai Mufeedah bata ce uffan ba dan tasan halin baba zuwaira angulu ce bata jiyuwar banza"

", dan da biyu tazo parlourn nan."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Baba zuwaira ce ta wuce ummah dake zaune a tsakar gida tanajin radion ta ,ko kulata ummah batayi ba dan kuwa akan idanuwan ta tazo ta wuce duk wani abu da baba zuwaira ta keyi ta san da biyu tayi shi shiyasa ma ta mannamata hauka, dan itakam bata da lokacin batawa akanta."

Baba zuwaira ce tashiga cikin dakin ta wayar ta Techno wanda ake cewa burin dan garuwa ta dauko numbern kamal ta lalubo.

"Kiran sa tayi ringing daya kuwa ya dauka, cikin kasa kasa da murya tace Kamal kana ina ne ba dazu naji kace zaka dawo da dare ba to kuwa ka hanzarta kazo gidannan don kuwa munafurtan ka akeyi."

"Gawani alhaji yazo hira harda abinci aka basa, jin yanda baba zuwaira take koromasa bayani ne yasa cikin bacin rai Kamal yace ai gani akofar gidan baba zuwaira yanzuma kuwa zan karaso, kit ya kashe wayar sa baijira cewar ta ba."

Wani irin makirin murmushi baba zuwaira tayi afili ta furta hmmm yaro bai san wuta ba saiya taka.

"Muje zuwa hajiya shuwa kina mini kallon biri ina miki kallon ayaba, Insha Allahu burina na shekara da shekaru yana daf da cika acikin gidannan kizuba ido kigani yanda zan kwace gidan nan a hannunki, nana ba da jimawa ba komai zai dawo karkashin Iko na, wani dariyar mugunta takeyi."

"Kamar daga sama ummah taji an fado tsakar gidan, dan tsorata tayi tare da kashe radion ta, ganin Kamal ne yasata sauke ajiyar zuciya, mamaki takeyi meya korosa yafadu musu gida haka ba ko sallama."

"Baiyi tsammanin ganin ummah a wajen ba, sabida haka yasa shi dan dakatawa a daddafe ya samu ya gaishe ta, kafin ma ummah ta gama amsa masa har ya tashi ya nufi hanyar parlourn ummah."

"Mujaheed na zaune yana duba wasu muhimman sako da aka turomasa ta Gmail din sa , kawai yaji mutum ya fado musu cikin parlourn ba ko sallama."

Mufeedah ce tadan razana ganin irin yanayin da Kamal ya shigo dan tasan halin kishi irin nasa shiyasa ma batafiye fita waje ba daga islamiya sai gida.

"Tsayawa yayi yana kare musu kallo duddah baiga wani abun zargiba amma baiji dadin yanda su ummah suka fita waje suka barta da wannan zindikin katon mai kama da mongoro nunar rana ba, ina dalilin hakan mutumin da ba muharramin ta ba, aganin sa hakan bai kamata ba ai shikadai ne yake da wannan damar, ajiyar zuciya ya sauke tare da nufar inda Mufeedah take zaune."

"Zama yayi a gefenta daf da ita sosai, dan matsawa baya Mufeedah ta yi, mika mata ledan hannun sa yayi yana cewa beb ya jikin naki ungo wannan lemo ne na sayomiki kinsan mai zazzabi sai da lemo bakin ba dadi yakarasa maganar tare da dan sake matsota."

Wani irin kunya ne ya rufe Mufeedah anya kuwa Kamal yana lafiya wani irin abu yakeyi haka agaban Mujaheed.

Ko inda suke Mujaheed bai kallaba haka yacigaba da duba wayar sa bayan yagama ne ya mayar da wayar aljihun sa.

"Tashi yayi sai a lokacin yadan kalli inda Mufeedah take zaune zaune , ya wani hada rai kamar bashine yake tsokanar ta ba dazu."

"Ganin irin kallon dayakemata ne yasaka Mufeedah ta taso a hankali ta dan tsaya nesa da shi kadan, Wani irin kallon dake narkar da zuciya Mujaheed yake mata ganin ta dan tsaya nesa da shine yasa shi dan matsowa daf da ita."

"Cikin wata irin murya mai taushi kamar mai mata rada yace dake ni dodo ne shiya sa kika tsaya a nesa amma da dan dumurmur ya matsoki ai baki matsa ba, anyway ni zan tafi gud night Allah ya qara afuwa duddah naga kin ji sauki."

A hankali ta ce nagode Yaya har yajuya zai tafi yadan tsaya juyowa yayi ya kalleta yace baki ce nagai da mata ta ba.

"Turomasa baki tayi a hankali ya furta matsoraciya kawai rufe fuskanta tayi da hannunta tana dan murmushi, juyawa yayi Murya kasa kasa yace kisamu kisha lemon kinsan bakin mai zazzabi ba dadi yana gama fadar haka ya fita, sallama yayiwa ummah."

"Wani irin murmushi Mufeedah ta keyi wato da Kamal yake kenan dazu yaji me Kamal ya fada amma yanuna baima san yana cikin dakinba, Wani irin blushing tayi tare da dan rufe fiskanta irin ta dan ji kunyar nan juyowa ta yi ta dawo wajen Kamal da yagama kuluwa wlh badon dare yayi ba da baba zai kira ayita takare dan ba zai yarda da wannan renin wayon ba kiri kiri agaban idanunsa za a nemi rena masa wayo, amma Allah ya kaimu goben wlh bazai yarda ba."

Wani dogon tsaki yaja tare da tashi ya nufi kofar fita batare da ya sake kallon Mufeedah ba.

Mufeedah ce ta sake baki tana kallon ikon Allah dan itakam bataga abun da akama sa ba.

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"10:30pm na dare Mujaheed ya isa gida , yanda yabar parlourn a hargitse haka ya dawo ya tarar da shi bai bi takan komai ba ya wuce bedroom din sa kayan jikin sa ya shiga ragewa, bayan yagama ne yawuce bathroom wanka yayi yafito ya shirya cikin pyjamas din sa masu mugun tsada da taushi."

"Har zai kwanta Marwat ce ta fadoma sa arai, dan yayi magana da hajiya a waya ta sanar masa da dawowar ta gida."

"Idon sa ne ya sauka akan ledan pharmacy ta shi yayi ya dauki magungunan da yasaya mata, dakin ta ya nufa ."

"Cikin sa'a yasamu kofar bedroom din ta abude , a hankali ya tura ya shiga bakin sa dauke da sallama akasan makoshi duddah baya tsammanin samun ta ido biyu."

Ga mamakin sa kuwa tana kawance akan makeken gadon ta wayar ta take dannawa jin anyi sallama bai sa ta ta dena abun da takeyi ba sabida tariga da tasan wanda zai iya shigowa dakin a wannan lokacin.

"Ganin irin halin ko inkula da tanuna masa ne yasa Mujaheed jiki a sanyaye ya karasa bakin gadon zama yayi a kusa da ita, Marwat ne ta dan matsa gefe hakan baisaka Mujaheed ya tashi ba."

"Kokari yakeyi ya danne bacin ransa, cikin sanyin murya yace habeebty ga maganin ki tashi kisha, in ginin dakin yayi magana to fa Marwat ta kula Mujaheed."

Ganin bata da niyar kula sa ne yasa Mujaheed ya dan warce wayar da take dannawa.

Cike da tsiwa da masifa dama kamar jiran sa takeyi tafara zazzaga masa ruwan masifa.

"Kaban wayata Mujaheed kafita daga daki na bana son sake ganin ka, azzalumi kawai, wato kaje ka hada baki da family doctorn ku yace baka dauke da HIV hakan bai isheku ba saida kasa ka ya makalamin sharrin cutar hypertertis B to wlh baku isa ba infact ma ni ban yarda da results din test din ba, magani kuma bazan sha ba ka kwashe kayan ka dan ni lafiya ta kalau bana son muna furci, tana gama fadan haka ta juya masa baya tare da rufe kanta a cikin blanket din da yake lullube a kunkuminta."

"Bacin ran da Mujaheed ya ke ta kokarin dannewa ne yaji yana taso masa, tsaki yaja tare da ajiye mata wayar ta."

Cikin bacin rai ya nufi dakin sa anan yabar mata ledan maganin.

"Konciya yayi yana tunanin mafita dan Allah ma yagani wlh Marwat yafara kaisa makura, haka yaciga ba da tunanin mafita har wani nannauyan bacci yayi awun gaba da shi."

Tun ran da Mujaheed yaje gidan su Mufeedah da dare bai sake zuwa ba.

"Haka ma a bangaren Marwat ba abun da ya sauya saima karuwa dan duk ta zaiyanewa zulaiha halin da ake ciki, nan fa zulaiha ta yi ta bata gurguwar shawara."

Ayanzu haka zaman doya da manja akeyi a tsakanin ta da Mujaheed.

Tun wanchan ranan da Mujaheed ya kusan ce ta bata sake barin wani abu yashiga tsakanin su ba duddah ta sake zuwa wani hospital din anmata test the same results din yanuna bata dauke da cutar HIV sai dai hypertertis B hakan ne yasaka tafara amfani da maganin da Mujaheed ya kawo mata.

"A yanzu Marwat kazanta takeyi fafafa bakama kafar yaro domin kuwa, bata damu da gyaran gidan ba bare kuma girki sai taga dama takeyi, 247 zaka sameta tana kon ce tana Danna wayar ta in tagaji tasha baccin ta."

"Acewar ta yanzu gashin kanta take ci dan bazata zauna Mujaheed ya kashe ta da hawan jini ba, shi yasani yaje chan yaci gaba da neman matan banza, ita dai tana kan bakan ta office ne dai bazata janye ba sai tafara fita kamar yanda tayi niya."

"Mujaheed kam ido ya zubawa Marwat don yaga abun nata ya wuce misali, shima a yanzu matsanancin fishi yakeyi da ita shiyasa ma ko takanta baya bi, baidamu da dawowa gidan bama bare kuma cin abincin ta da ba kullum take girkawa ba, haka dai suke zaman doya da manja dan tun wanchan lokacin bai sake nemanta da aure ba , duddah yana da bukatar ta haka yake dannewa ya hakura dan kuwa alkawari yayiwa kan sa bazai sake neman ta ba sai tagane kuskuren ta."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

Yau takama ranar laraba wanda yarage saura kwana biyu a daura auren Mufeedah da Kamal.

Mujaheed ne zau ne a cikin garden na gidan aminin sa Imam tattaunawa sukeyi akan matsalolin da Marwat ta tsiro da su.

Imam ne yace inaga zanyiwa ramlart magana inya so kaga saita je tasameta kasan su mata wani lokacin sunfi fahimtar yan'uwan su inaga idan ramlart tasame ta da maganar za a samu chanji.

Mujaheed ne ya sauke ajiyar zuciya yace toh shikenan Allah ya sa.

"Kallon Imam yayi yace barin zo in wuce, kallon sa Imam yayi yace da wuri haka nazaci zamu sha hira ne ai."

"Mujaheed ne ya ce akoi inda nake son na wuce ne Imam ne yace to barin yiwa Madam sallama kaga sai in maka rakiya, munkwana biyu bamu fita tare ba, Mujaheed ne ya danyi murmushi tunowa da yanda suke a da ba sa rabuwa."

"Imam ne ya wuce bayan wasu mintuna ya fito a cikin mota yasamu Mujaheed, shiga yayi Mujaheed ya ja Motar."

Imam ne yake tambayar ina ne zasu je ganin Mujaheed ya dauki wani layi acikin anguwar tudun wada.

"Name kake sauri kazuba ido zakagani, cewar Mujaheed da ya ke tukin, Imam ne yace kodai kayi sabuwar beb ne a anguwar mu don dai nasan baka da wajen zuwa ata wajen nan, kasani ko wajen business partner dina zanje, cewar Mujaheed daya ciga da tukinsa yana kokarin karya kwana a kofar gidan su Mufeedah."

Haba wani irin business partner a wannan layin haba Jaheed dake wataran haka Imam yake kiran sa da Jaheed kamar yanda Marwat ta saka masa tun suna saurayi da budurwar wa.

"Mujaheed bai bashi amsa ba ganin sun iso kofar gidan parking yayi yakashe motar, kallon sa Imam yayi yace don't tell me cewa anan gidan business partner din nakan yake."

"Mujaheed ne ya ce and so, gani nayi cewa gidan bai yi kama da wanda kace ba ne, dariya Mujaheed ya kyalkyale da shi ganin shifa Imam bilhakki ya yarda business sukazo yi bai sake tamka masa ba ya bude marfin kofan yafita gani iskancin da Mujaheed ya masa ne ya sa Imam din fita shima."

"A kofar gidan suka tsaya, ibro ne yafito da alama aika zaije ganin su Mujaheed a kofar gidan ne yasa shi ya gaishe su , Mujaheed ne ya tambaye sa baba ibro ne yace masa yana cikin gida ai, toh kace ana masa sallama, juyawa ibro yayi cikin gidan ."

"Ba'a jima ba baba yafito hannunsa dauke da tabarma, ganin su Mujaheed ne yasaka ya fadada fara'ar sa."

"Mujaheed ne yakarbi tabar mar ya shumfuda, sanda baba ya zauna sannan suma suka zauna."

Zuwa yanzu Mujaheed ya jefa zargi acikin zuciyar Imam sai dai kuwa babu damar yin magana tunda agaban baba suke.

"Cikin nitsuwa da jin kunya Mujaheed ya shiga gaishe da baba, shidai Imam yau yana ganin ikon Allah awajen aminina sa, business partner ne ake yiwa wannan biyaiyar har da sunkuyar masa da kai kasa infact ma wannan mutumin baiyi kama da Abokin business din Mujaheed ba gakuma alamar sunjima da sanin juna ,kodai kodai Mujaheed uhuummm to bari dai yaga gudun ruwan sa ."

"Mujaheed ne ya dan zunguri Imam ganin ma hankalin sa baya tare dasu, ya tsunduma kogin tunaninsa, Imam ne ya dagawa baba gaisuwa cike da fara'a baba ya amsa kallon Mujaheed yayi yace hala dan'uwan ka ne."

Dan murmushi yayi tare da jinjina wa baba kai cike da kunya Mujaheed yadan sosa kai yace dama nazo gidan dan'uwa nane nace barin kara so mugai sa .

"Masha Allahu ka kyauta sosai Allah sarki Allah ya bar zumunci da ameen suka amsa baba ne yatashi yace barin zo, cikin gida ya wuce yabar su a wajen."

"Imam ne ya kaiwa Mujaheed naushin wasa kaucewa Mujaheed yayi yana dariya, imam ne yace kodai kodai, kodai me cewar Mujaheed uhuummm nidai bakina da goro zakayi bayanine wlh, ganin baba yafito ne yasa sukayi shiru."

"Jug din kunun aya mai sanyi baba ya ajiye musu yace BISSIMILLAH, Mujaheed ne ya sunkuyar da kai shikam Imam cup ya dauka ya zuba kunun ayan yafara sha, Wani irin lumshe idanunsa yayi tunda yake baita ba shan kunun aya mai shegen musulmin dadi kamar wannan ba tass ya shanye na kofin kara daukan jug din yayi yasa ke zuba wani shi dai Mujaheed sai kyafta masa idanu yakeyi amma Imam yayi buruss da shi kamar bai gansa ba."

"Baba ne ya mikawa Mujaheed wani envelope guda biyu yana ce gawannan katin auren kanwar kane nan da jumma'a in Allah ya kaimu, sai kabawa Dan uwan ka daya."

Kamar saukan guduma a tsakiyar kan sa haka Mujaheed yaji saukan maganar baba Imam ne yayi saurin saka hannun sa ya karba yana dan murmushi yace toh baba mun gode Allah ya sa ayi da mu da ameen baba ya amsa.

Mujaheed ne ya tashi kamar an tsikare shi yace toh baba mungode zamu wuce baba ne yace nine da godiya alhaji nagode da ziyara Allah ya kara sutura da ameen suka amsa.

"Bayan sun shiga mota ne Mujaheed yabude wani waje acikin motar kamar akwati kudine awajen bunch na 1k ya dauka guda goma yayi making 1 million kallon Imam yayi yace ina zuwa, fita yayi yanufi inda baba yake zaune dan kuwa haryanzu bai tashiba."

"Sallama yayi ya tsuguna ajiye kudin yayi agefen baba yace baba ga wannan gudun mawa nane , cikin Wani irin mamaki baba yace ai wannan kudin sunyi yawa alhaji, bakomai baba Mufeedah ai kanwa tace zan iya mata fiye da hakama baba, to alhaji an gode sosai Allah yajikan magabata, nan baba yayi ta masa addu'o i, sallama yamasa ya wuce wajen mota inda Imam yake jiran sa dan shikam Mujaheed yana neman ya goge masa haddah yasaka shi a cikin duhu, dole ma yazo yamasa bayani dan bazai bar kan sa yayi murfiba."

"Mujaheed ne ya ja motar sanda suka bar kofar gidan Imam yace kacemin aure kake nema mutumin, hararan sa Mujaheed yayi yace kamar yaya aure kuma don kawai na basa 1 mil gudun mawa nabasa na auren yar sa , Imam ne yace toh a ina ma kasan mutanen nan ne, yaushe kazama dan jarida cewar Mujaheed ganin irin iskancin da Mujaheed ya ke masa ne yasa ya kama bakin sa yayi shiru don kuwa yasan miskilancin irin na aminin nasa in baiso magantuwa ba bawanda ya'isa ya saka shi, haka Mujaheed yaje ya sauke Imam a kofar gida , shikuma ya wuce ."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

Rana bata karya saidai uwar diya taji kunya a yau jumma'a ake shirin daura auren Kamal da Mufeedah bayan an idar da sallan jumma'a a babban masallacin jumma'a dake anguwar su.

"Baba ne yake sanye da babbar riga ya sha hulan sa na zanna kana ganin kayan kasan sababbi ne, kallo daya zaka masa kasan cewa yana cike da farin ciki, yana tsaye ne a harabar masallacin inda yake tare da yan'uwa da abokan arziki."

Wata zazzafar mota ce kirar BMW X7 tashigo harabar masallacin duk mutanen dake haraban masallacin hankalin su ne ya koma kan motar kusan 3min kafin aka bude marfin motan.

"Mujaheed ne ya fito sanye yake da farar gezner me shegen tsada anmasa dinkin jamfa da babbar riga bakaramin kyau yayi ba dagani kasan sabon kaya ne , sassanyan kamshin sa ne ya mamaye harabar wajen, Imam ne ya fito a gefe mai zaman banza, shima yasha gezner sai dai shi babu babban riga."

"Cikin nitsuwa da kamala suka nufi inda su baba suke, haka kawai yau Mujaheed ya kejin sa Wani iri shikan shi baisan me yake damun sa ba, wannan daurin auren ma kawai dai daurewa yayi yazo baya son su baba suga kamar bai mutun ta su bane."

"Sallama sukayi nan suka shiga gaisawa da sauran mutanen, baba ne yamikawa Mujaheed hannunsa alamar suyi musabaha cike da Jin nauyi Mujaheed ya mika masa hannu suka gaisa nan fa sukaji anfara kiran sallah cikin masallacin suka shiga dukan su Mujaheed da Imam suna bayan su baba."

"Bayan an idar da sallah ne akafara gudanar da daurin auren da akeda su a cikin masallacin, me shelane yafara kiran malam Muniru baba ne ya tashi cike da fara'a ya matsa kusa da liman nan akashiga kiran alhaji garba waliyin ango, amma shiru babu shi babu alamar sa, nan fa hankalin baba yadan tashi dan tun dazu sukayi waya"

"da alhaji garba yayan mahaifiyar kamal dan shine waliyin sa, sabida mahaifin Kamal ya jima da rasuwa dazu dai baba yakira sa a waya yace masa suna hanya sunku san karaso wa to alokacin ne liman ya tada sallah."

Baba ne yashiga waige waige amma bai hango alhaji garba ba sai yanzu ya lura da cewa babu kamal ba alamar sa kuma babu wasu yangidan su awajen.

"Baba ne ya dubi liman yace amin afuwa malam inaga a daura wani auren barin je in dubo luwalin angon Allah dai yasa lafiya, da ameen malam liman ya amsa."

"Baba ne yata shi tare da tattare babbar rigan sa tashi yayi ya nufi hanyan fita haraban masallacin cikin hanzari ya zare wayar sa keypad numbern alhaji garba yakira ringing takeyi amma ba'a daga ba san da takusan katsewa sannan ya dauka cikin sanyin murya alhaji garba yayi sallama baba ne yace alhaji garba Allah dai yasa lafiya ku aketa jira awajen daurin auren, cike da jin nauyin baba alhaji garba yace kayi hakuri malam Muniru dama yanzu nake kokarin kiran ka don sanar da kai cewa kayi hakuri yaronnan Kamal yace yafasa auren yar'uwar sa Mufeedah bisa ga wassu dalilai da in ka dawo gida za'a zauna a warware su don ba maganar waya bace."

"Cikin bugawar zuciya da magiya baba yace dan Allah alhaji garba kuzo a daura auren nan inyaso ko wacce irin matsala ce za'a warware ta daga baya, kudubi girman Allah kar mutuncina ya zube, baba ne ya karasa maganar cikin magiya da bugawar zuciya dan har wani jiri jiri yake gani, bai taba tsammanin faruwar hakan ba."

"Cike da tausayawa baba alhaji garba yace kayi hakuri malam Muniru kasan ni wakili ne kawai ban isa nakarba wa Kamal auren yarka ba , batare da izinin sa dana mahaifiyar saba, baba ne yace bangane zancenka ba alhaji garba kana son kace mini zainabu ma bata amince a daura auren ba ."

"Wannan haka yake cewar alhaji garba, cikin Wani irin yanayi baba ya katse kiran, ba abun da yake ambata sai innalillahi wa'inna ilaihirraji'un."

"Ganin baba yafita tun dazu ne gashi kuma shiru haryanzu bai dawo ba yasa Mujaheed ya kalli Imam yace barin zo tashi yayi yabi bayan baba, kalaman karshe da baba ya furta acikin kunnen Mujaheed."

"Ganin Mujaheed ne yasa baba ya nufoshi cikin karfin hali yace kuyi hakuri alhaji nataraku anan sai gashi Allah ya nufa auren ba mai dauruwa bane mutum yana nashi Allah na nasa, sai dai na Allah ne daidai."

"Mujaheed bai fahimci zancen baba ba sai dai yagan sa cikin yanayi na rashin natsuwa ga wani uban zufa dayake yanko masa, Mujaheed ne yace baba me yake faruwa, cikin bakin ciki baba ya sanar da shi abunda alhaji garba ya fada masa."

"Shikenan yanzu sun gama kunya tane , sun zubarmini da mutunci acikin jama'a meya sa tunjiya basu sanar dani maganar fasa auren ba cewar baba da wasu hawaye masu zafi suka zubo masa kawai tunanin yanda zaifara sallaman jama'a dasunan anfasa auren yakeyi, abangare guda kuma gachan gida acike makil da mutanen biki wasu sunyi tafiya mai shegen nisa ."

"Mujaheed ne ya ji saukan zancen har cikin ransa toh me yasa dan gajeren saurayin nata fasa auren ganin hawaye na sakkowa a idanun baba ne yasa yaji jikin sa na masa sanyi, lallai kuwa sun so tozarta baba, cikin nitsuwa ya kalli baba Wani irin nauyi ne

Please Login or Register in order to submit comment