Reading SIRRIN YA'MACE COMPLT BY MRS ALKALI Chapter 3 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kauna Mujaheed yaci abincin sa, bayan sun kammala ne Marwat ta tattare wajen."

"Zama tayi akan cinyar sa cikin kontar da Murya tace ""Zauji """

"Uhuummm habeebty cewar Mujaheed daya ke shafamata gashin kanta, cikin salo tafara magana, Zauji baka ce komai ba akan matsalar nan."

"Mujaheed ne ya zuba mata ido yana karantar yanayin ta, sanda yagama nazarinta sannan yace to me kike son nace bayan a idon ki doctor yamana baya ni."

"Dan daburcewa Marwat tayi dan ita kanta ta na tsoron abun da zai fito daga bakin ta sai dai idan ta tuna wannan ne mafitar ta sai taji wani irin kwarin guiwa, cikin jarumtar da ta aro tace yanzu kana ganin bawata hanya da zamu bi kenan, cikin nitsuwa da ya zame masa ado yace ina ga sai mujarraba maganin da doctor ya daurani a kai tunda yace na 2 month ne, kinga in ansamu change shike nan dama haka ake fata."

"Kallon sa tayi tace dama ina son kasa mamini yan aiki sabida gaskiya ina bukatar su a gidan nan, sanna kuma ina son in fara fita MJ plaza daily in a week kaga dole na bukaci maid a gidannan don wlh nafara gajiya da zaman banzan nan, ba daba ba jika ba."

"Wani irin kallon mamaki Mujaheed yake mata, Amma ita Marwat ko ajikin ta , saima wani sanyi da ya ratsa zuciyar ta ganin ta fitar da abun da yake damunta, don tasha alwashi a wannan karan bazata bari son da takeyiwa Mujaheed ya rufe mata ido ba."

"Tazo tana tauye kanta sabi da shi, alhalin shi yana chan yana kula wasu yan matan awaje dan haka gara ta farka, tafara nemawa kanta yanci, ya za'ayi da karatun ta da komai amma ya hanata fita kullum tana gida a rufe sai kace wata kifin rijiya."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Cikin wani irin bacin rai ya ce Marwat ina ce tun ba yau ba munriga da mungama maganar fitan ki office,shin akoi abun da nagaza miki da shi ne acikin gidan nan ya tambaye ta tare da zuba mata idanunsa."

Cikin karfin hali tace babu abun da kagaza min dashi Jaheed kawai dai nima ina da ra'ayin fita office din ne.

"Cikin da kekkiyar muryan shi yace to ban amin ce ba yana gama fada yatashi yanufi bedroom din sa, cikin zuciyar sa kuma yana tunanin tabbas akoi wanda yake zuga Marwat amma bako mai zai gano waye ne."

"Wasu irin hawayen bakin ciki ne suka cika idanunta wata abun da zulaiha ta fadama ta da gaske ne su maza, kansu kadai suka sani toh in dai kuwa gaka ne wlh wannan karon ta shirya yin koma meye ne in dai Mujaheed yaki amincewa da buka tunta."

"Sai yanzu tagane soyayyar Mujaheed ta makantar da ita kamar yanda kawayen ta sukasha fada mata, yan zune ta tabbatar da maganar zulaiha, wato da ita ce take da matsalar tsinkewar maniyi da zai iya auren wata kenan ita kuma tazama yar kallo, wani irin haushin sa ne ya kamata."

"Sanda tagama kukan ta a parlour sannan ta tashi bedroom din ta tanufa direct don bata bukatan ganin sa a wannan lokacin, tayi masa wannan kolliyar ne da nufin ta gigita duniyar sa, sai gashi yayi wa kansa, konciya tayi ta rufe idanunta, amma tsabar bakin ciki baccin ma yaki ya dauke ta, wayan ta ta dau ka ta hau online nan ta duba taga zulaiha tana online."

Nan tashiga labarta mata abun da yafaru a tsakanin ta da Mujaheed.

"Nan fa zulaiha ta zage tayi tabata mugayen shawarwari , akan karta yarda wlh ai wannan shi ta taimaka ma da ta ci gaba da zama da shi, nan tashiga nuna mata haihuwa ai ita ce komai, zulaiha ta dauki shawarwarin da zulaiha ta bata don aganin ta gaskiya ne don taga alama Mujaheed yafara chanza mata, gara tun wuri ta takawa abun birki, sai kusan karfe 1:00pm sannan ta sauka a online konciya tayi abunta kamar ba abunda yafaru, sai dai acikin zuciyar ta tasha alwashi iri iri akan cikar burinta."

"Cikin dare Mujaheed sai juyi yakeyi, gaba daya ya gagara bacci kewar matar sa ya ishe shi , ganin bazai iya hakura ba ne yasa yatashi, bedroom din Marwat ya nufa."

"A konce yasameta sai sharan baccin ta takeyi hankali kon ce, pyjamas din jikin sa ya tube yarage daga shi sai boxer ajikin sa gudun AC ya rage ."

"A hankali ya haura kan gadon cikin nitsuwa ya jawota jikin sa, sleeping dress din yashiga cire mata, a hankali yafara sarrafata ya na aika mata da sakkonni."

"Tun shigowar sa Marwat ta farka sai dai tayi mirsisi kamar mai bacci, haka tabarshi yaci gaba da sarrafata san da taji alamar zai mata mai kankatt ne tawani yi juyi ta hanka da shi gefe cikin muryan bacci tace me haka ni dai kabarni bana so mutum yana cikin baccin sa mai dadi kawai zaka tashe ni."

"Wani irin kululun bakin ciki ne ya tokarewa Mujaheed wuya, yau shi Marwat zata ture sai kace wani kare, sabida ya zo da bukatar sa shida halal din sa, tun da yake da Marwat yau ne karo na biyu da ta hana shi kanta, cikin hali na bukatuwa ya matso yana kokarin sake jawota jikin sa."

"Sake matsawa gefe tayi tace haba Jaheed nace maka bana bukata ko a na dolene haba, abun da in anyima banga amfanin sa ba tun da bazai haifar mana da da mai ido ba, haba sai yanzu naga ne cewa da ace lafiyar ka kalau da kamin ciki yafi sau dari a gidannan,dan Allah ka barni ni bazan iya da jarabar nan ba, juya masa baya tayi tacigaba da baccin ta."

"Tun da yake bai taba tunanin akoi ranar da zata zo ba Marwat tafada masa irin wadannan kalamen yau shi Marwat takeyiwa gorin haihuwa, wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga bin kuncinsa akaro na farko arayuwar sa da yaji yana matukar son haihuwa."

San da yayi mai isar sa sannan ya tashi ya nufi bathroom din ta wanka yayi ya dauro alwala zuwa yayi ya shimfida sallaya yafara nafila.

"Yajima yana addu'a Allah ya kawo masa mafita, bayan ya shafa addu'ar ne, ya dauki wayan Marwat dama babu wani security ajiki nan yaga tabar datan ta abude, dubawa yayi yaga tana kan manhajar Facebook."

Nan fa yafara dubawa yaga tana duba post ne acikin group din SIRRIN YA'MACE bacci ya dauke ta.

"Alamar massage yagani a inbox din ta kamar bazai duba ba, wani zuciyar ta ja shi ya bude, massage ne zulaiha ta mata tana dada jaddada mata akan cewa kar ta yadda gara ta kwatowa kanta yanci."

Nan fa hankalin Mujaheed ya tashi yashiga duba charting din su tun daga farko.

"Wani irin zufa ne ya shiga karyoma sa, bai taba tunanin cewa Marwat zata aikata wannan shirmen ba , da ilimin ta."

"Ace daga haduwa a group shikenan sai ki hau daukan shawarwarin matar da baki ma san rayuwarta ba, wani irin zafi zuciyar sa take masa."

"Lallai wannan karon zai nunawa Marwat ta tafka babbar kuskure, cikin ruwan sanyi zai gasata, dakan ta zata dawo haiyacinta."

"Nan ya gama yanke shawara acikin zuciyar sa, Wani irin haushin gungiyar yakeji ganin ta silar ta ne yasa Marwat ta hadu da zulaiha, gashi har zaman kafiyar gidan sa yafara masa barazana."

"Wayan sa ya dauka, Data ya bude nan yashiga manhajar Facebook yafara creating new account da sunan mace."

"""MAMAN SADIQ"" nan ya tura request na joining din group din, bayan ya kammala ne ya yi addu'a n bacci ya konta."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Mujaheed ne ya shigo cikin parlourn, da alama daga masallaci ya fito , don abun yazamo masa kamar al'adar sa in dai ya yi sallah, toh sai yayi azkhar kafin ya shigo gida."

"Ganin parlourn wayam ba kowa, da 'alama Marwat bata fito parlourn ba."

"Idanun sa ya sauke akan dinning table nan ma wayam yagani babu ma alamar anfito parlourn bare kuma ya saka ran anyi girki, wani irin bacin rai ne ya ziyar ce shi, sai dai wannan karon yasha alwashin zai nunawa Marwat bata da wayo."

"Tunjiya da dare dayagane inda ta dosa sannan yagane zugata akeyi, shima ya daukanwa kan sa alkawarin sai ya gasata da ruwan sanyi."

"Direct bedroom din sa ya wuce dan a halin yanzu baya bukatan sanya ta a idanun sa, bathroom ya shiga wanka yayi a gaggau ce ya fara, shiryawa dan yana son yafita office da wuri, dan akoi aikin da zai kara sa, bayan ya kammala shiryawa cikin wasu suit Ash colour masu bala'in tsada necktie black colour yasaka, agogon sa me shegen tsada ya daura ,wasu Black cover shoes ya saka, turaren sa mai dadin kamshi da sanyaya zuciya ya fesa, rass yafito kamar dan shekara 30yrs , jakan sa ya dauka da wayan sa, drowern da yake ajiye keys din motocin sa ya bude key din wata range Rover ya dauka, a gaggau ce yabar dakin ko takan Marwat be bi ba haka yaja motar sa me gadi ya wangale masa gate ya fita."

"Marwat bata tashi daga baccin a saranta ba sai 11:00am, wani irin mika tayi , dan tsabaragen tajima tana baccin har ciwo take jin jikinta yana mata, sake mika tayi, tanajin yanda kasusuwan ta suke kara, dan ba karamin tsami takeji ba acikin jikin na taba."

"Tashi tayi ta nufi bathroom ruwa masu dumi sosai ta hada, tayi wankan ta, bayan tafito ne tashirya kanta cikin wasu Riga da wondo, bakaramin kyau suka mata ba."

"Fitowa tayi ta har ta wuce kofar bedroom din sa wata zuciyar ta rayamata ta leka, haka ta sa hannu zata bude kofan, amma sai taji kofar a rufe ruff da key."

"Wani irin tsaki tayi aranta tana ayyana wulakancin irin na Mujaheed wato yau ita ne yake rufewa dakin sa harda saka key, lallai maganar zulaiha gaskiya ne tabbas sai ta tashi tsaye ta kwatar wa kan ta yanci in ba haka ba tana gani kuwa wankin hula yana so yakai ta dare."

"Jin wani irin murdawa da cikin ta yayi ne yasata tayi saurin wucewa parlourn, kamshin turaren sa ne taji yagama mamaye lungu da sako na parlourn kai kace yanzu ya fesa turaren, ajiyar zuciya ta sauke, da alama har ya fita duddah dama tasan zai yi wuya Mujaheed ya kai kamar wannan time din a gida alhalin zai fita office."

"Wani irin bakin ciki ne ya tokare mata wuya, wato baima damu da ita ba shiyasa zai fita bai tashe ta ba, lallai ita kuma zata nuna masa ta cika jinin SIRRIN YA'MACE."

"Kitchen ta wuce snacks da tea mai kauri ta hada, dan yau bata jin yin girki, don daga yau ta dauki alwashin sauya rayuwar gidan ta daga yadda Mujaheed yake so zuwa ra'ayin ta, tunda ita ce matar gidan."

"Haka tazauna ta gama break fast dinta tsaff a parlourn tattare kwanukan data yi amfani da su tayi, kitchen ta kai su , ko wanke su bata yiba haka ta ajiye su ta fito, kallon cikin parlourn tayi, wani tsaki taja, aranta tace wlh sai dai kura ya kashe parlourn nan da daga yau na dai na wahalar da kaina , akan ka Mujaheed in ka gaji ai dole ka nemamin maid a cikin gidannan dan wlh bazan lamunci wannan wulakancin ba ,ni da gidana kasaka nazamo boyi boyi da sunan soyayyah."

"Wani tskin ta kara ja afili, Wani irin haushin kanta takeji, sai kace wacce ta farka a nannauyan bacci, yanzu ne take jin itama zata tsaya acikin gidan ta da kafafun ta kamar ko wace house wife."

"Bedroom din ta ta nufa, gado ta hau ta konta tare da bude wayar ta ta hau online."

"Nan ta tarar da zulaiha a online, hira sukeyi sosai game da halayyar mazan zamani nan fa zulaiha ta samu dama tayi ta sake daura Marwat akan keken bera."

"Wani irin kwarin guiwa ne ya ziyarci zuciyar Marwat jin yadda zulaiha take jinjina mata tare da kara bata kwarin guiwa akan abun da ta yiwa Mujaheed, ji takeyi yau sai dai yamata duk abunda yaga dama Amma wlh ko tsinke bazata dage ba a cikin gidannan bare kuma ace zatayi wani girki."

In yana bukatar hakan dolen sa yabi shawarwarin ta ya samu mata maid domin kula da gidan da kuma sauran aikace aikacen gidan da wannan ne ita kuma zata samu daman fara fita office din ta na MJ plaza.

"Haka Marwat ta wuni a bedroom inkaga ta tashi dai to sallah ne aka kira, sai kuma inta ji yunwa takanje kitchen ta dauko snacks da drinks, ba wani abu da takeyi sai danna wayar ta gashi yau tasamu zulaiha tana online haka suka wuni suna charting."

"Wannan sai yazamo dama da zulaiha tasamu ta kara daura Marwat akan wasu shawarwari , don har posting ta musu a group din SIRRIN YA'MACE da sunan abawa kawar ta shawara nan danan Yan group suka shiga bada shawarwarin da sukaga yakamat iya karfin su."

"Ganin comments din wasu daga cikin muta ne masu hali irin na zulaiha shi yakara karfafawa Marwat zuciya, ganin dai dai take aikatawa ."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Abangaren Mujaheed kuma tun da ya isa office ya zama busy, aiyuka sun masa yawa."

"Sai bayan yayi sallan azahar ne ya samu nitsuwa, wayar sa ya kunna, online ya hau, yana hawa yaga admin tayi approving din friend request din sa."

"Nan danan ya tsunduma cikin Page din SIRRIN YA'MACE yafara dubawa, acewar sa zaiga ireiren abubuwan da akeyi a cikin group din SIRRIN YA'MACE."

"Nan yaci karo da wata tayi posting kamar haka,,"

"Matan sirri kubani shawara ina cikin damuwa mijina dan iska ne ga shaye shaye ga neman mata dayagane nasani ya yi tabani hakuri, har rantsuwa , yamin akan bazai sakeba, yan'uwa kubani shawara, narasa yadda zanyi."

"Nan fa yayi taganin ruwan comment akasari cewa sukeyi tarabu da shi , ai baya hallatta zama da fasiki."

Wani comment ne ya dauki hankalin sa in da yaga wata mai suna Mufeedah Munir tace.

""" Sister kiyi hakuri kiba shi dama ta biyu, kici gaba dama sa addu'a , in kin rabu dashi kina da yakinin shi wanda zai sake auren ki ba mazanaci bane, sannan kuma ba mashayi bane ina mai baki shawari ki yawaita"

"masa addu'a sannan kirin ka azumin nafila gawasu addu'o i kiringa yi Insha Allahu damuwar ki zata yaye, Allah zai baki mafita nan yaga tabata wasu addu'o in dazata dinga yi domin samun sassauci."""

"Ajiyar zuciya ya sauke yana cigaba da bibiyan comments din mata wasu suna bata shawarwari mai kyau, wasu kuma akasin haka."

Nan yaci karo da comment din zulaiha in da tace.

"""Hmm wlh sister kirabu da shi kawai ina ke ina zama da fasiki mashayi to bari ya kwaso cuta ya sakamiki, kimin magana ta inbox akoi shawarwarin da zan baki ."

Mujaheed yaga ne username din zulaiha sabida ya bibiyi charting din su da Marwat.

"Wani tunani ne yafado masa arai nan yashiga Page din SIRRIN YA'MACE yafara typing , nan fa yayi posting akan matsalar da yake fiskanta a tsakanin sa da Marwat."

"Ba a dau dogon lokaci ba admin tayi approving din post din na sa, nan fa yafara ganin ruwan comment kowa yana tofa albarkacin bakin sa."

"Nan yaga wani comment da ya dauke masa hankali, massage yamata ta private."

"""Asslm sister ykk """

"Lpy qlu alhmdullah, cewar mufeedah Munir,,"

Sunana Maman Sadiq nice nayi posting a group din SIRRIN YA'MACE comment din ki ya burgeni hakika kina da zurfin tunani da hangen nesa in ba da muwa ina son murinka zumunci da neman shawarwari a wajen juna.

"Toh shikenan ba matsala, "" ni sunana mufeedah Munir"" kuma ni budurwa wa ce sannan ina garin zariya, naji dadin haduwa da ke."

"Wow nice to meet you nima agarin zariya nake da rabon watara na zamu ga juna, ""Insha Allahu"" cewar mufeedah."

"Nan fa Mujaheed ya shiga jan mufeedah Munir da hira, don ya lura a zancen yarinyar akoi hikima da basira a ciki."

A bangaren mufeedah kuma duk aza tonta da mace yar uwar ta take charting don a tunanin ta ma matar aure ce.

"Mujaheed ya shagala da yin charting da mufeedah, don bakaramin dadin hiran nasu yakeji ba haka kawai yakejin zantukan ta sun konta masa a rai."

"Sectary din sa ne yayi noking kofar office din,."

"Yes come in cewar Mujaheed, wani matashi ne yashigo yace sorry Sir time for meeting, jinjina masa kai yayi yace ok, fita sectary yayi domin komawa bakin aikin sa."

"Mujaheed ne ya duba time a a cikin agogon hannunsa mai shegen tsada, idon sa ya ware ganin yanda time ya tafi, shi kansa bai san ya dauki wannan time din ba, sai yanzu da ya duba time."

"Sallama yayiwa mufeedah tare da sauka a online din, shafa lallausan gashin kan sa yayi tare da sakin wani cute smile, tunani yakeyi wai yau shine da bude manhajar Facebook kuma da sunan mata, duk asanadin Marwat."

Tashi yayi ya fara shirin attending na meeting din da zai shiga da wasu company da suke son saka hannun jari a nasa companyn.

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Pageță

WACECE MUFEEDAH..?

"""Mufeedah Munir "" matashiyar yarinya ce mai kimanin shekaru 20yrs tana zaune da iyayenta a anguwar tudun wada dake cikin garin zariya."

"Malam Munir mutum ne me karamin karfi don yana aiki a wani government school anan cikin anguwar tudun wada, malamin secondary school ne."

"Yana da mata biyu da yaya biyar , uwar gidan sa hajiya shuwa mace ce mai kyau , sabida ta fito daga asalin tsatson shuwa arab ne iyayen ta yan maiduguri ne aure ne yakawo ta garin zariya, iyayenta suna da rufin asiri sosai, sai dai soyayyah yasa suka aura mata malam Munir, don bakaramin so sukeyiwa junan su ba, kafin kaddara ta chanza komai hajiya shuwa mace ce mai dottaku da kawai ci ga sanin ya kamata tana da yarinya daya mai suna Mufeedah tun awajen haihuwar mufeedah tasamu matsala a mahaifar ta, wanda yasaka aka cire mata mahaifar gaba daya, domin kuwa ta lala ce bazata moruba."

"Malam Munir da hajiya shuwa sunyi bakin cikin wannan lamarin, sai dai kuma kaddara tariga fata."

"Bayan tagama jinya ne tasamu sauki, suka ci gaba da renon kyakkyawan yar su mai suna Mufeedah."

"""Mufeedah kyakkyawan yarin yace mai shiga rai tun tana yar jaririyan ta take da farin jinin mutane ,dan dawuya mutum yagan ta bai daga ta ba ganin haka ne yasa daga malam Munir har hajiya shuwa suka tsayamata da azkhar da wasu addu'o in neman tsari."

"Bayan shekaru 7 da haihuwar mufeedah ne, mahaifiyar malam Munir tafara masa korafin yakamata ya kara aure, don bazai yiwu ya ci gaba da zama da wacce bazata sake haihu wa ba."

"Malam Munir baiyi na'am da zancen mahaifiyar sa ba, don shi anashi tunanin kamar yazama cin amana ne inyace zaiyiwa hajiya shuwa kishiya, kuma anasa tsarin babu auren mata biyu saiga shi kaddara tasame su wanda hakan yasaka mahaifiyar sa tirsa sa shi akan lallai lallai sai ya kara aure, acewar ta ba bu amfanin zama da juya."

"Ba irin magiya da roko da malam Munir baiyiwa mahaifiyar sa ba Amma haka tayi mirsisi tace ita batasan zancen ba indai bazai kara aure ba to zata yafe shi acikin yayan ta, jin wannan kalaman nata ne yasa hankalin malam Munir ya yi mugun tashi, yashiga matsanancin damuwa."

"Ganin halin da malam Munir ya shiga ne yasa hajiya shuwa ta keta karfafa masa guiwa, don duk abunda yake faruwa tasani, don baya boye mata da komai, shiyasa ta ce masa ba matsala yayi wa mahaifiyar sa biyaiya."

Badon ransa yaso ba sai don kaucewa fishin mahaifiyar sa sannan da kwarin guiwa da hajiya shuwa tabashi haka ya amince da batun auren da mahaifiyar sa ta zomasa da shi.

"Cikin kankanin lokaci mahaifiyar sa ta zabo masa mata acikin danginta acewar su auren zumunci za sumasa, don gani sukeyi hajiya shuwa tagama mallake shi, shiyasa ma suka matsa masa da batun karin aure."

Yar uman sa zuwaira ita ce mahaifiyar sa tazaba masa cikin sati biyu akayi biki Amarya zuwaira ta tare agidan mijin ta.

"Duddah bawani son ta malam Munir yakeyi ba, hakan bai hana shi kotanta adalciba, sabida ba karamin kwarin guiwa yake samu ba ata bangaren hajiya shuwa, don ita bata da wani matsala da batun auren sa, acewar ta ai mijin mace hudu ne kowa ya iya allon sa ya wanke."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Zuwaira yarinya ce me rawan kai gashi yar dangi ce , don haka ba irin huduba da ba'a mata ba akan inta shigo gidan tayi yanda zatayi duka tafitar da hajiya shuwa, acewar su ai matsafiya ce don inba aikin tsafi ba ba yanda za'ayi ace komai sai malam Munir yayi shawari da ita kafin ya aiwatar, kuma gani sukeyi batabar shi banza ba , ganin irin kaunar da yake nunawa Yar ta mufeedah."

"Jin irin hudubar da suka mata ne yasa zuwaira daura damaran fitar da hajiya shuwa daga gidan, sai dai abun ya citura don har yanzu Allah bai bata sa'a ba."

"Ayanzu haka zuwaira wace suke kira da baba zuwaira tana da yaya maza guda hudu a cikin gidan, ganin ita ce ta haifi maza agidan yasaka tafara kanainaye komai na cikin gidan cikin kissa da kisisi na da iyeyi, kai harma da malaman zaure, don acewar mahaifiyar malam Munir dole sai sun hada da neman taimako, shiyasa ma da kanta take zuwa ta karbo temakon ta kawowa baba zuwaira tana yiwa malam Muniru amfani da shi."

"Ganin irin son da dangi sukeyiwa zuwaira ne, yasa hajiya shuwa ta sake kama kanta, bata fiye shiga shirgin su ba, kuma hakan bai hana ta temaka musu ba, sabida familyn ta suna da rufin asiri sannan kuma itama tana aikin asibiti a wani private hospital acikin anguwar tudun wada, don ita ce ma in charge din hospital din."

"Ganin yanda hajiya shuwa ta share su ne bata taba nuna musu cewa ta san me suke aikatawa bane, yasa ka mahaifiyar malam Muniru tasake kullatar ta, acewar ta ai hajiya shuwa ta raina su ne tana ganin familyn ta suna da kudi sannan kuma tana ganin alwashin ta yafi na malam Muniru shiya sa take renasu."

"Ayanzu haka zuwaira gani takeyi kamar tagama mallakar zuciyar malam Muniru domin kuwa gani takeyi

Please Login or Register in order to submit comment