Reading SIRRIN YA'MACE COMPLT BY MRS ALKALI Chapter 8 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan yasan baya dauke da wata kwayar cuta ta HIV dan haka baiji komai aran sa ba .

"Doctor ne yayi jaran murya ya kalli Mujaheed yace yallaboi an muku gwajin HIV kamar yadda ka bukata sai dai kasani duk wani bawa baya wuce kaddarar sa dan haka kai da madam kuyi hakuri da abun da zakuji dama shi mumini cike yake da jarrabawa kuma babu wata kwayar cuta da bata da magani, Allah bai saukar da wata cuta ba face san da ya saukar mata da maganin ta hakika in an daure za ' aci jarrabawa."

"Ba Marwat ba hatta Mujaheed wani irin dumm dumm gabansa ya buga, ko dai da gaske Marwat ta ke fada masa yana da HIV inkuwa haka ne to a ina ya samu, wani irin gumi ne ya shiga yanko masa duk sanyin AC dake cikin office din bayaji wani irin zafi yakeji, a hankali jikin sa ya shiga rawa, da kyar ya iya karan to innalillahi wa'inna ilaihirraji'un haka yayi ta nana ta kalmar acikin zuciyar sa a hankali yafara jin relief din mood din daya ke ciki."

Marwat kam ji takeyi duniyar ta tsaya mata chak bata wani fahimtar komai ji takeyi kamar ma taje ta shako wuyar doctorn dan jakar uba ya fada musu me results din yake dauke aciki amma ya tsaya yana musu wani kewaye kewaye da nasihan da bashi da wani amfani.

"Cike da karfin hali ta kallah Mujaheed da tafahimci yana cikin wani irin yanayi, hakan ne yasake tabbatar mata da cewa tabbas zargin ta yazama gaskiya, cikin murya mai rauni da sheshsheqan kuka tace Mujaheed ka cuce ni ka gama dani kaga abunda son zuciyar ka ta jawo mana ko, wayyo ni Marwat nashiga uku shikenan kuwa tawa ta kare, nazo duniya a banza gashi zan koma a wofi niba da'ba kuma ba jika ba."

Ganin irin yanayin da suka shiga ne yasa doctor yace yallaboi results yanuna da kai da Madam ba kwa dauke da cuta mai karya garkuwar jiki.

Wani irin ajiyar zuciya suka sauke atare wanda hatta doctorn san da yaji hakan.

"Muryan doctorn ne ya katse su da cewa sai dai ita madam mun samu tana dauke da cutar hypertertis B amma ba wata matsala bace cutan bata riga tayi nisa ajikin ta ba zamu iya shawo matsalar, ayanzu zamu daura ta akan magani sanna kuma akoi abubuwan da yakamata ta kiyaye cinsu dakuma wa'dan da ya kamata taringa ci domin samun lafiyar ta."

"Kai kuma zamu fara maka rigakafin cutar tunda oready baka riga da ka dauke ta ba, nan dai doctor ya shiga musu bayani game da cutar dakuma matakan kariya da zasu bi domin gujemata."

"Marwat dai tagama daskarewa akan kujeran da take zaune wannan shi ne ana wata ga wata, ji takeyi kamar ma kofofin hancinta sun toshe dan bata shakan iska yanda ya kamata."

"Ita ce ma take dauke da hypertertis B kai ina bazaiyiwu ba wannan doctorn ya rena mata hankali, wato shi Mujaheed lafiyar sa ma kalau kenan bayan yagama biye biyen matan banzan sa a waje ita ce zata dauki consequences din abun da ya aikata, kai ina bazai ma ta ba yiwuwa ba, ai itama hypertertis B din ana daukan ta true body contact dan haka wlh bazata taba yarda ba Mujaheed ne ya kwaso ya yaba mata inba haka ba ya za'ayi doctor yace shi bashi da kowacce irin cuta amma ita tana dauke da wannan cutar , ita da ba wani da namiji da ta sani bayan Mujaheed kenan ma doctor ya nufin ita ce ta kwaso cutar, to a ina yake nufi, cikin zafin"

nama ta tashi tana kuka kallon Mujaheed tayi cikin bacin rai tace bazan taba yafe maka ba mugu kawai cikin matsanancin kuka ta bar office din.

"Cikin rashin fahimta doctorn yake kallon Mujaheed din , cike da kunyan abunda Marwat ta aika ta agaban doctorn Mujaheed yace karka damu doctor ta shiga damuwa ne."

Haka doctor ya rubuwa Mujaheed magun gunansa tare da wanda Marwat zata fara sha haka ya sa akayiwa Mujaheed rigakafin hypertertis bayan angama ne Mujaheed yamasa godiya ya nufi pharmacy acikin hospital din magungunan da aka rubuta ya saya bayan ya kammala ne yanufi motar sa da tunanin Marwat tana ciki tana jiranshi dan yasan ba inda zata tafi ta barshi yasan tashiga rudani ne amma zaimata bayanin yanda cutar take cikin hikama don shima tausayi ta bashi

"Bude motar sa yayi amma wayam ba Marwat ba alamarta harta jakan ta da tabari acikin Motar bata nan da alama ta dauki jakan ta ta tafi kenan, ajiyar zuciya ya sauke cike da matsanancin damuwa ya ciro wayar sa numbern Marwat yashiga kira tana ta ringing ba a dauka ba sanda yakira sau biyar a karshe ma kashe wayar akayi."

"Bakaramin damuwa Mujaheed ya shiga ba,jiki ba kwari ya shiga motar sa cikin mutuwar jiki yake tukin yarasa ma me yakeyi masa dadi."

"Yadanyi tafiya mai nisa tunani yakeyi ina Marwat ta wuce yasan dai bazata koma gida a wannan yanayin ba don ya tabbatar da a fusace take da shi wayarsa ce tayi ringing da sauri ya dauka yana tsammanin Marwat ce, sunan hajiya yagani akan screen din wayar dauka yayi a hankali ya shiga gaisheta."

Hajiya bata amsa gaisuwar saba tace masa baba na kana ina ne meya samu Marwat tazo ta nata kuka tundazu nake tambayan ta amma taki cemin komai.

Ajiyar zuciya ya sauke jin Marwat gidan hajiya taje cikin murya mai dauke da damuwa yafara briefing ma Hajiya abunda ya faru a hospital din.

"Cikin tausayawa danna tan hajiya tace ka karyane yanzun a hankali ya ce hajiya bana ma jin yinwan, aa baba na ka daure ka karaso kayi break fast komai yayi zafi maganin sa Allah kamikawa Allah al amuranka shi zai isarmaka insha Allahu."

"Cike da kaunar mahaifiyar ta sa yace ba komai hajiya zanci a office yanzuma na makara, toh shikenan Allah ya kare itama Marwat din zan lallasheta ba komai kaje Allah ya tsare da ameen ya amsa mata ."

Reverse yayi da motar ya dauki titin da zai sadashi da office din sa

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

Misalin qarfe 1 30pm na rana doctor ne ya gama duba jikin Mufeedah kallon su baba da ummah ga Kamal a tsaye a gefe yayi yace alhmdullah yanzu bawata matsala baba zamuyi discharge din ta yanzu sai yan magungunan da za a rubuta mata sai kubi pharmacy kukar ba su zata ci gaba da sha agida Allah ya sauwaqe da ameen su baba suka amsa.

"Nan doctor ya rubuta musu discharge, magungunan yarubuta ya mikawa baba takardan cikin hanzari Kamal ya matso yasa hannu ya karba, kallon su baba yayi yace barin je in sayo maganin a pharmacy kafinnan ummah ta gama tattare kayan ,baba ne yace to kamalu Allah yayi albarka da ameen ya amsa tare da wucewa pharmacy domin sayo magungunan."

"Ummah ce tashiga tattara musu yan tarkacen su duddah bawani kaya suka kwasoba, Mufeedah dai tana zaune shiru tara sa me yake mata dadi, gashi dai bata wani jin zazzabi amma kuma chan kasan zuciyarta takejin kamar akoi abun da take kewar shi."

"Muryan baba ne ya katseta yace to sai ki sakko ai zaman asibitin ya isa haka, ummah ce tayi dan murmushi tace in ba dole ba ai malam zaman asibiti kam ba dadi."

"Mufeedah ce ta sauko sanye da katon hijabin ta , Kamal ne ya turo kofar dakin , baba ne yace har ansa yo maganin ko, cikin nuna rashin jin dadi ya mikawa ummah ledar pharmacy din yace gashi ummah basuma karba kudin ba sunce wai wanda yakawo ta ya biya kudin komai."

"Basu ummah ba har mufeedah san da ta zubawa Kamal idanu jin abun da Kamal ya fada , dukan su sun san wayake nufi."

Cike da dan fara'a baba yace Allah sarki bawan Allah dagani mutumin kirki ne Allah ya saka masa da alkhairii kai samun irin su a wannan zamanin yana da matuqar wahala yakara maganar yana kallon ummah.

"Ummah ce tace wannan haka yake Allah ya biyasa da mafificin alkhairii da ameen baba ya amsa, gashi kuma zamu tafi gida ba musamu muka sanar masa ba kodai wajen likitan zanje na barmasa sallahu ne cewar baba dayake kallon ummah."

"A'a malam kabari kawai in munkoma gida basa Mufeedah ta kira min shi awaya sai a sake masa godiyar dawainiyar da ya shiga, toh shikenan hakan ma yayi Masha Allahu cewar baba da ya nufi kofar fita."

"Kamal kam a yau hakurin sa yagama zuwa karshe akan wannan mutumin da yaji su baba na yabonsa yasan mutumin da suka hadu anan jiya ne yaukam in sun koma sai yaji mene alakarsa dasu baba dan bazai taba yarda ace saura sati daya bikin sa da Mufeedah ba ace wani chan daban yafara lallabowa ba, dama ance ana samun late commer a aure to shi bazai yi sake ba wlh ."

"Tunda su baba sukafara jerawa Mujaheed addu'a takejin wani irin sanyi acikin ranta ji takeyi kamar kar su dai na maganar sa, muryan ummah ne ya katsemata tunanin ta sai ki wuce muje cewar ummah databi bayan baba dauke da sauran kayan su."

"Cikin rashin kuzari Mufeedah ta fara takawa Kamal ne ya matso kusa da ita jerawa sukayi, cike da kulawa yace sannu beb ko dai akoi inda yake miki ciwone har yanzu, girgiza masa kai tayi batace masa uffan ba don haka kawai taji bata son masa magana, haka suka bi bayan su baba kafin su fito har baba ya tare musu adaidaita sahu nan fa ummah da mufeedah suka shiga baya baba ne yace suje shi zai taho da Kamal haka kuwa akayi bayan su ummah sun wuce ne Kamal ya sake tare musu wani adaidaitan shida baba suka shiga suka bi bayan su ummah."

"Kamal irin gajerun mutanen nan ne dan dumurmur da shi dan yana da dan kiba, baki ne yana da dan siririn gemu, yana da ba'in kishi musamman akan Mufeedah, ya gama NCE har yanzu bai samu aikin gomnati ba shiyasa yanemi koyarwa a wata private school dake cikin anguwar su."

Baba zuwaira tana aikin abincin rana su ummah suka shigo gidan ganin idon baba ne yasa tayiwa Mufeedah ya jiki.

Ummah da Mufeedah ne suka wuce daki yayin da baba ya tsaya a tsakar gida yana jiran shigowar Kamal domin kuwa ya tsaya sallamar mai adaidatan da yakawo su.

"Kamal ne ya shigo cikin gidan bakin sa dauke da sallama baba zuwaira ya gaisar nan take tambayar sa su umman shi, baba zuwaira kanwar maman shine kuma matar bapphan shi dake auren zumunci ne aka musu da baba da baba zuwaira shiyasa shi ba bako bane acikin gidan."

Baba ne yakalli shi yace Kamal samu waje kazauna dama ina son muyi wata magana nan Kamal ya zauna akan taburmar dayaga an shumfuda a tsakar gidan.

Cikin nitsuwa da hikama baba yashiga yimasa bayanin abunda ya hada su da Mujaheed san da ya tabbatar da Kamal ya gamsu da bayanan sa sannan ya wuce turakan sa domin agajiye yake so yakeyi ya huta.

Dukan maganganun da baba yayiwa kamal akan kunnuwan baba zuwaira domin kuwa ta labe abakin kofar dakin tana sauraran su.

Ajiyar zuciya Kamal ya sauke bayan tafiyan baba sai yanzu yadan ji sassauci Jin cewa bawani abu a tsakanin su da mutumin tashi yayi ya nufi dakin ummah so yake yayiwa Mufeedah bankwana sai dare yake son kara shigowa dubata .

"A kwance yasa meta ummah namata fifita ummah zan wuce Allah ya kara sauki cewar Kamal, dake tsaye a bakin kofar dakin."

"To angode da dawainiya kamal agaida mutanen gidan, zasuji Insha Allahu cewar kamal da ya juya domin yaga mutuniyar tashin bacci ya dauke ta ."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Misalin qarfe 8 00pm Mujaheed ya baro office, Mufeedah ce ta fadoma sa arai kota kota ya sha'afa yau baije hospital ya duba ta ba."

"Tsayawa yayi a bakin wani babban plaza sayaiya yayi sosai kayan tea da su chocolate, su arabian oud, wata abaya yagani mai shegen kyau har zai wuce haka kawai yaji Mufeedah ta fado masa arai, daukan rigar yayi nan yashiga kwasan abaya sanda ya dauki son ransa sannan ya je ya biya kudin, a mota suka loda masa kayan haka ya shiga motar sai alokacin ya shiga tunanin ko dai sun samu sallama ne ganin bazai samu amsar tambayar sa bane yasa ya dauki wayar sa numbern ummah yakira bugu daya kuwa ummah ta dauka, cikin nitsuwa ya gaisheta tare da tambayar ta ya mejiki, nan ummah take sanar da shi ai sun samu sallama suna gida ta sha'afa ne shiya sa bata sanar masa ba, sallama yamata tare da juya akalar motan ya dauki titin da zai kaishi tudun wada."

Da kyar Hajiya ta lallaba Marwat bata sake tambayar ta abunda ya faru tunda Mujaheed ya mata bayani.

"Cike da hikima take yiwa Marwat nasiha mai ratsa jiki, duddah haka Marwat jinta kawai takeyi dan ita kadai tasan halin da zuciyar ta take ciki."

Haka ta wuni a gidan hajiya duddah bawani sakewa tayi ba amma ta dan samu relief na damuwar da take ciki.

"Bayan sallan la'a sar ne tace wa hajiya zata wuce gida , nan hajiya tace tajira Mujaheed mana , firr Marwat taki acewar ta zata je ta daura girki ne haka Hajiya ta hakura ta barta ta tafi."

"8:00pm Mujaheed ya yi parking a kofar gidan su Mufeedah baba ne zaune akofar gida tare da kannen Mufeedah yaran baba zuwaira dukan su maza ne akoi Ahmad,Musa, Ibrahim sai umar, zaune suke tare da baba suna taya shi hira dama haka al'adar baba take akoi sa da son yara, ganin mota tayi parking ne ya sa baba ya maida hankalin sa wajen."

"Mujaheed ne ya fito cikin shigar sa ta office wato suit ne sanye ajikin sa, wajen da baba yake zaune ya nufa don tun acikin motar ya gane cewa baba ne yake zaune awajen."

Ayau sai yake jin kunyar saka kananan kaya haka kawai yaji baya son baba yagan shi cikin wannan shigan sai dai ba yadda zaiyi yariga da ya kara so.

"Cikin nitsuwa yayi Sallama baba ne ya amsa cike da sakin fiska dan kuwa shima ya gane shi, gaisawa sukayi Mujaheed ne ya tambayi ya maijiki ,baba ne yayi ta godiya akan dawainiyar da yayi musu."

Cike da kunya Mujaheed ya ce bakomai baba ai Mufeedah kanwa na dauke ta.

"Ba karamin dadi kalaman sa sukayiwa baba ba , nan baba ya ke cemasa ai auren ta saura sati daya wanda suka hadu a asibiti ne zai aure ta kuma cousin din ta ne , wani irin dummmm Mujaheed yaji saukan maganar baba cikin kunnen sa May be maganar ce ta zo masa a bazata , Allah Sanya alkhairii Mujaheed yayi ,baba ne ya kalli su Ibrahim yace ibro tashi kashiga gida kace wa su umman ku anyi bako zai shigo ya gaida Mufeedah, yaron ne yatashi da gudu ya nufi cikin gidan domin isar da sakon baba."

"Ummah tana tattare kitchen domin ita ce tayi girkin dare, ibro ne yashigo da gudu yana kwalamata kira amsa masa tayi, sakon da baba yafada masa ya isar mata, juyawa yayi yakoma wajen baba."

"Ummah ce ta nufi dakin ta domin sanya hijabin ta a zaune ta samu Mufeedah tana tilawar haddan ta na islamiya, bata cemata komai ba ganin tana sanye da hijab din ta, kuma bata son ta katse mata karatun nata."

"Jin anyi sallama ne yasa ummah tace Bismillah ka iso, cikin nitsuwa Mujaheed ya bi bayan su ibro da suka nufi dakin ummah hannunsu dauke da ledojin shopping din da yayiwa Mufeedah."

"Baba zuwaira ce takama baki ganin irin kayan da su ibro suke wucewa dakin ummah da shi, tun lokacin da ibro yasanarwa da ummah sakon baba anyi bako ya sa ta labe a bakin windown dakin ta."

Ido baba zuwaira ta zubawa Mujaheed tsaff take kare masa kallo dake tana labe tacikin daki ne shiyasa shi bazai iya ganin ta ba amma ita tana kallon sa rass dake akoi wutar NEPA a tsakar gidan.

"Chap wanna Alhajin fa a ina yasan Mufeedah don dai tasan wannan ba dangin su ummah bane ganin duk dangin su ummah masu zuwa ta san su, ko dai shine mutumin da naji dazu malam yanayiwa Kamal bayani inkuwa shine tabbas akoi gagarumar matsala, nan zuciyar baba zuwaira tashiga sake sake."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Cikin sassanyan murya yayi sallama a bakin kofar parlourn ummah, ummah ce ta amsa tare da masa iso, cike da kunya ya karasa shigowa parlourn a kasa ya zauna ummah ce ta ce a'a karmuyi haka da kai tashi kazauna a saman sofa , duk yanda ummah ta yi da Mujaheed amma yaki ya zauna yace kasan ma yayi."

Ita kanta ummah kunyar sa takeji ganin yanda yake wani bata girma kuma tasan May be ma ya dan girmeta dan daga nin sa kasan ba na yau bane.

Tashi ummah tayi ta nufi cikin bedroom din ta inda Mufeedah take tilawar haddan ta.

"Mujaheed ne ya bi parlourn da kallo komai tsaf tsaf da shi duddah dakin bawani mai girma ba ne amma komai a gyare yake a muhallin sa kuma ba laifi kayan cikin parlourn masu tsada ne baza ace na talaka bane, gawani turaren wuta mai shegen kamshi da yake tashi, lumshe idanunsa yayi jin wani irin kira'a dayake fitowa daga cikin dakin dayaga ummah ta shiga, har cikin kasan zuciyarsa yakejin kira'ar, jiyakeyi kamar kar a daina."

Jin andakata da kara tun ne yasa shi bude gajiyayyun idanunsa dan bakaramin gajiya yake jiba gakuma yunwa dayake ji tana damun sa.

"Cikin wata zazzakar murya yaji anmasa sallama, wani irin faduwar gaba yaji amma ya dake amsawa yayi a hankali ta kara so ta zauna akasa chan dan nesa da shi."

"Mujaheed ne ya zuba mata idanu kamar mai son fahimtar wani abu, cikin nitsuwa ta fara gai sheshi."

"Jim bai amsamata bane yasa ta dago kanta idanunta ne suka sarke acikin na sa, Wani irin yanayi sukeji a hankali Mufeedah ta janye idanunta bata sake cewa komai ba haka shima Mujaheed bai ce mata uffan ba saima sake zuba mata narkekkun idanunsa dayayi hakan kuma ba karamin takurata yayi ba."

"Ummah ce ta fito daga cikin bedroom din ta kiran Mufeedah ta yi suka wuce waje tare, wajen minti biyu sai ga Mufeedah ta dawo hannun ta dauke da tiren silver mai shegen kyau ajiyewa tayi a ganan Mujaheed gefe ta koma ta zauna a inda ta tashi dazu."

"Mujaheed ne ya kalleta yaga tawani ta kure waje daya ga wani uban hijab din ta da tunda ya santa acikin ire iren su yake kallonta, shikam dariya abun ya basa sai dai ya dake baiyiba."

"Cikin dakekkiyar muryansa yace come and sarve me, bawai dan yana da niyar cin abincin bane yasa yace ta yi saving din sa kawai dai haka kawai yakejin yanaso yaganta akusa da shi."

"A hanakali ta matso ta bude flasks din silvern wani irin daddadan kamshi ne ya bugomasa hanci, atake yaji yunwar cikin sa tana dawowa sabuwa,babu shiri ya hadiye wani yawu mukuttt."

"Mufeedah ce tashiga saving din sa a plate din silver wanda ya kasance set ne da flaks da tiren, cikin nitsuwa ta ajiye plate din agaban sa jug din zobon ta dauka ta zubamasa a cup ta ajiye."

"Ta zo zata tashi taji ya rike mata gefen hijab din ta cikin fargaba ta dan kalle shi, shima ita ya zubawa ido, fiskar sa ba alamar wasa yace haka ake saving din mutum abinci kin wani ciki wa mutum plate sai kace wani rumbu, haka zaki je kinayiwa gajeren saurayin ki inya aure ki kenan dama ga shi dan lukuti inkika cigaba da loda masa abinci irin haka nan gaba kadan zai zama wada yanzuma kingan shi daf da kasa, yana gama fadan haka ya sake mata gefen hijabin ta."

"Agefe tasake rakubewa kamar wata bakuwa , ita dai yau tana ganin ikon Allah awajen wannan mutumin, jiyan da yawani hada rai yana yabawa Kamal bakaken maganganu Allah ma dai ya taimaketa Kamal din baya nan."

"Mujaheed kam spoon din ya dauka yayi Bismillah yafara cin dambun shinkafa da ummah tayi, yasha zo gale da gyada, ga albasa da cabbage da aka yanka su yan sirara akasaka aciki sai kamshin man kuli yakeyi kunsan in ansoya mangyada matsar hannu yasha albasa abun ba acewa komai gashi ummah ta zuba garin kuli dakar hannu, ai Mujaheed baisan san da ya lumshe idanunsa ba dayakai abincin baki ba, Wani irin magana disun dadi ne yake ratsa kunnuwan sa."

"Jiyakeyi yunwar sa ta dawo sabuwa , baisake bi ta kan Mufeedah ba haka ya zage ya kwashi girkin ummah, san da ya cinye dambun da tayi saving din sa tass sannan ya dauki zobon da ta zuba masa a cikin cup mai sanyi ya kai bakin sa."

"Ya Allahu shine abunda Mujaheed ya iya ambata jin wani irin gardi dayaji acikin bakin sa, don dai karyayi karya ne da yace tunda yake baitaba cin abincin da ya kai wannan dadi ba,don akoi shi da son abincin gargajiya."

"Tass ya shanye zobon jug din ya dauka yakara zuba wani haka ya shanye shi tass, hamdala yayi, sannan ya kalli Mufeedah dake rakube ta wani sunkuyar da kayi kamar ace mata ass ta arce a guje kanta akasa yake batama san wainar da Mujaheed yake toyawa ba ita dai taji yayi shiru bayan yagama ciwa habibinta mutunci."

"Abazata taji saukar muryansa come and pick this things, tasan da ita yake hakan ne yasa ta tashi ta matso ."

Hannunta ta sa zata dauki plate din da tasaka masa dambun idon tane yasauka akan sa wayam ba komai dan tsayawa tayi kamar mai nazarin wani abu.

"Uhuummm kinwani duramin abinci so kikeyi nima nadawo gajere nai tumbi kamar boyfriend dinki ko, ki cuci mata ta, cewar Mujaheed dayaga tana kallon plate din."

"Fara tattare wajen tayi ita dai batace masa uffan ba inbanda karfin hali wai ta cuci matar sa sai kace dole tamasa yacinye abincin, haka ta tattare kwanukan ta fita da su waje gurin ummah."

"Bayan tashigo be ya kalle ta yace shekarun ki nawa abazata taji tambayar tazo mata, cikin sanyin murya tace nima ban sani ba sai dai

Please Login or Register in order to submit comment