Reading SIRRIN YA'MACE COMPLT BY MRS ALKALI Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fa nake ta fama da su ummah a gida, ace sam mutum bai da sukuni, Allah dai ya bamu maza je masu kudi muma muje inda zamu huta."

"Zulaiha ce ta ce ameen ke dai bari kawai kawata ai miji mai kudi duniya ne, jiya ai na hadu da wata mata a group din SIRRIN YA'MACE tana neman shawarwari game da mijin ta, nan fa na jawo ta ta inbox ina bata shawarwari,"

Chap di jam yanzu ke zulaiha wa ce irin shawari kika bata bayan kin ce matar aure ce.

"Hmm ai tunda naga profile pic nata naga alamar matar mai kudi ce , shiyasama naja ta ta inbox don inbata shawara kuma fa abun mamaki dazu ta ke cemin ta gode don taga amfanin shawarwarin da na bata,"

"Habiba ce ta daka mata duka acinya tace chap lallai matar nan tana ruwa, wani abu sai waya, da kuwa zata ganki a zahiri watakila ko yar aikinta baki kai ba,."

"Hmmm ai tun da baza suji kunyar kawo sirrin auren su a group ba, haka kuwa zamuyi tayin maganin su, muna basu shawarwarin da basu dace ba kinga kuwa in yagaji da mugun halinta ai ya sakota, kinga mukuma ta hakane zamu samu shiga, kin san fa yan zu mazan ma tsada su keyi."

"Zulaiha wai nikam ba dake nake magana bane, kam cewar yakumbo da tagama fusata don tasan zulaiha najinta sarai amsata ne bazatayi ba, zulaiha ce ta tashi tana yatsuna fuska, tace uhuummm habiba ta shi muje don wlh kinga yakumbo, ba mutun ci bane da ita , ba akan kudi , tunda tafara jaraban kiran nata ba hakura zatayi ba."

"Nasan yanzu akan fita tallar kuli kuli da mangyada take ta kwalamin wannan uban kiran, sai kace, wacce taci mata bashi."

"Habiba ce ta ce toh muje inrakaki, fita tsakar gidan sukayi in da suka samu ya kumbo tagama jera kuli kuli da mangyada acikin kwanon fita tallar,."

"Kallon su tayi tsaf daga sama har kasa, tace ai duk wannan wayar ce take shiriri tar da ku ba, toh wlh zanyi maganin ku, tun da sanyin safiya nake binki kizo kizagaya ko zamu samu cinikin safe amma sam kinki kin je kin kule a kuryar daki ,kinta faman latse latsen waya."

"Zulaiha ce tadauki kwanon tallar ta ta aza shi bisa kanta, wayar ta kirar VEVO ta dau ko kunna waka tayi ta kure volume din kana ta soke wayar a kunkuminta, kallon yakumbo dake ta faman sababi tayi, tace to mukam munfita,neman halak, yakumbo ce tace toh adawo lafiya,haka su zulaiha suka wuce ita da kawar ta habiba."

WACECE ZULAIHA...?

"Zulaiha dai marainiya ce gaba da baya, iyayen ta duka sunrasu tun bata da wayo, hakan ne yasa rikon ta ya dawo hannun kakan ta ta wajen mahaifin ta wato yakumbo,"

Zulaiha ta taso a anguwar hausawa in da yakumbo take sana'ar kuli da mangyada domin su samu na rufawa kai asiri.

"Zulaiha ta yi makarantar primary da secondary, sai dai fa duka asha ruwan tsuntsaye ta yiwa karatun don ba ko da yaushe take zuwa ba,tafi bawa sana'ar kuli muhimman ci sai tafi sati biyu bata jeba, dama ita yakumbo kam bason wannan bokon takeyi ba acewar ta wai barnar kudi ne, amma ganin zulaiha ta dage ne yasa ta hakura ta barta, a hakan har Allah yasa ta kara sa."

"Zulaiha budurwa ce mai shekara 28yrs doguwa ce baka ce sosai irin wulak din nan tana da kiba irin matan nanne direrru ga kiba ga tsayi, tana da gajeren hanci, inka ganta dai masha Allahu da ita , bata taba aure ba tana da kawar ta mai suna habiba, itama sa'ar zulaiha ce, komai tare sukeyi, tun suna kana na, akoi shakuwa sosai a tsakanin su."

"""Mujaheed ne ya tashi daga bacci jin ana kiran sallan azahar, Marwat yagani zaune a kan gado tana ta faman latsa wayanta, sai wani shekewa da dariya takeyi, ganin hankalin ta ma baya kan sa ne ya sa shi tashi ya nufi inda take, jin motsin mutum akusa da ita ne yasa ta ankara ,"

"Haba Zauji ai sai kabani tsoro, ashe kata shi shine ko magana babu,,"

"Uhuummm keda kin mai da hankalin ki gaba daya akan wayanki tayaya ma zakisan na tashi,, cewar Mujaheed,,"

"Hmmm ai wlh bazaka gane ba ne wani posting nake karantawa a group din SIRRIN YA'MACE, duk yabi ya daukemin hankali shiya sa ban lura da tashinka ba,,"

Uhuummm yayi kyau ina fatan dai kinyi sallah ko..?

"A'a yanzu zanyi, bai sake kulata ba haka ya wuce toilet ya dauro alwalar sa, yanda ya barta haka ya dawo ya sameta tana rike da waya sai murmushi takeyi, bai ce mata kala ba, haka ya wuce masallaci."

"Bayan kamar 10minutes ne ya shigo gidan direct dinning table ya wuce, me zai gani wayaam ba komai akayi, juyawa yayi , cikin takunsa na ingarman namiji yake taka stairs din, bedroom dinta ya nufa direct,,"

"A zaune ya sameta kamar yadda yafita ya barta, da alama ko sallan ma bata tashi tayi ba kenan,, ranshi yaji yayi mugun baci,,"

Marwat ce ta dago kanta jin alamar anshigo dakin hada idanu sukayi da shi.

"Zauji harka dawo, cewar Marwa,danne bacin ransa yayi, cikin kaushin murya yace kinyi sallah ne, no zauji Amma yan zu zanyi, wani abune ya dauke hanakali na a waya, taba shi amsa tare da cigaba da latsa wayanta abunta,,"

"In ran Mujaheed yayi dubu to ya baci, ganin wasu irin halaye da Marwat tafara tsiro da su wanda shi bai san ta dasu ba,"

"Cikin dakekkiyar muryansa yace and were is my lunch na duba saman dinning table Banga komai ba akai,,"

"Hankalin ta nakan wayar ta, tace barin yi sallah yanzu sai inzo in sama maka ko noddle ne, kafin ma yace mata kala, ta ajiye wayar nata tanufi toilet, zama yayi yana tunanin sauyi dayaga ni awajen Marwat."

"Yana zaune ta fito daga toilet din sallayar ta shimfida, hijab dinta ta saka, sallah ta tayar, cikin minti biyu ta sallame, ba ta tsaya yin wani addu'a ba ta tashi abunta, hijab din tacire, juyowa tayi ta kalleshi ganin irin kallon tuhuman daya kemata ne yasata saurin cewa, naga kanajin yunwa ne shiya sa ban tsaya yin addu'a ba, ganin bai ce komai ba ne yasa ta juyawa tanufi hanyar fita zuwa kitchen din."

"Bayan ta daura noddles din ne, ta tuna da wayanta , cikin sauri ta nufi dakin, wayan ta dauka , wannan karon bata samu Mujaheed a cikin dakin ba sai dai taji alamar yana toilet maybe wanka yakeyi."

"A mai makon ta nufi kitchen din, sai ta samu sofa tazauna a parlour abun ta tashiga group din SIRRIN YA'MACE taci gaba da dubawa, kusan 5 minutes ta tuna ta daura noddles a wuta da sauri ta ajiye wayar ta nufi kitchen din kashe gas din tayi , tukunyar tabude taga ruwan cikin noddles din yagama tsotsewa, har yafara kama kasan tukunyar, plate ta dauko mai shegen kyau ta juye aciki, drink ta dauka ta jera a tire din , dauka tayi ta nufi daki da abincin ."

"Mujaheed ta samu cikin shirin fita ,sanye yake da wata gezner da ta sha dinkin jamfa da wondo ba karamin kyau yayi acikin kayan ba, gawata hula da yakafa akan sa, saibaza kamshi yakeyi, ajiye tiren abincin tayi, a hankali tace Zauji ga lunch, juyowa yayi yana jara zamar hulansa , yace har angama kenan karamin murmushi tayi tace ehh noddles na dafamaka nasan fita zakayi gashi kana jin yunwa, don dai baka son sayan abinci a wajene shiyasa nace barin maka dafa maka noddles sabi da yafi saurin dahuwa."

"Wajen abincin ya nufa, zama yayi ya bude plate din fork ya dauka ya ibo abincin cikin nitsuwa yakai abincin bakin sa taunawa daya ya furzo abincin waje."

"Subhanallahi Zauji are you okay cewar Marwat, ruwa ya dauka ya sha sosai sannan ya sauke ajiyar zuciya, yace habeebty anya kin dandana abincin nan kuwa, no Zauji kasan noddles bai dameni ba, bai sake cemata komai ba ya tashi ya nufi hanyar fita, ya na cemata sai nadawo, zanje gaida su hajiya, toh agaishe ta cewar Marwat."

"Bayan fitar Mujaheed ne Marwat ta dau fork din ta ibo abincin, ta kai bakin ta wani irin watso shi waje tayi da karfi, wani irin kauri kaurin wuta yakeyi ga uban borko no da tacika, no wonder Jaheed yaki cin abincin sabi da tasan bai son acika masa borko no a cikin abincin sa, tiren tashiga tattarewa, jara wajen tayi tsaff."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Mujaheed anya baza kuga likita ba kai da Marwat kuwa, cewar Hajiya data zubawa dannata ido, don ita harga Allah rashin haihuwar Marwat tafara damunta."

"Ajiye spoon din hannunsa yayi, yace nafara tunanin haka nima, Insha Allah zamuje muga doctor akan matsalar, toh da dai yafi kam cewar hajiya,"

"Kudi masu yawa Mujaheed ya ajiyewa hajiya,yace ga wannan babu yawa, toh Mujaheed Allah yayi albarka, agaidah mutanen gidan, zasuji hajiya mu kwana lafiya, yafada yana kokarin fita daga parlourn."

"Gun masu suyan kaji ya tsaya, gashesun kaji ya saya akasaka masa a leda, direct gida ya nufo."

"Misalin qarfe 8 30pm yashi go gidan , a parlour yasamu Marwat tana zaune, wayan ta ne rike a hannunta, kallo daya tamasa ta dauke kanta taci gaba da dannawayar ta, cikin nitsuwa ya kara so ajiye ledan hannunsa yayi, sai a lokacin ta ce hmm yaukam kadawo da wuri kenan da alama yau baka biya wajen budurwar taka ba."

"Dan murmushi Mujaheed yayi, yace uhuummm habeebty kenan dama nace miki wajen budurwa nake zuwa ne, kema kinsan aikin office ne yakemin yawa, kinga yau weekend shiyasa na dawo da wuri, uhuummm dama"

"haka zaka ce mana, ai yanzu maza ba abun yarda bane, cewar Marwat da take danna wayar ta, Mujaheed ne ya dan girgiza kai ganin yanda ta dage wai wajen budurwa yake zuwa."

"Kallon ta yayi yace kinsan dai in auren nake son yi baki isa ki hanaba ko, zuciyar ta ce ta buga da karfin gaske wani irin dagowa tayi tace bangane me kake nufiba,kenan ma dagaske gun budurwa kake zuwa , bai sake tamka mata ba, yadauki ledan ya nufi kitchen ganin bata da niyan tashi, shi yarasa yaushe Marwat tafara chanzawa haka, amma zaiyiwa tufkar hanci, dan bazai lamunci hakan ba."

"Kajin da ya sayo ya juye a plate, yogurt ya dauka a cikin freezer parlourn ya fito, dauke da tiren a hannunsa ajiyewa yayi ,a kasa, zama yayi ya tankwashe kafafunsa Bismillah yayi yafara cin naman cike da nitsuwa."

"Ganin bashi da niyar kulata ne yasa ta sauko ta zauna a gefen sa Bismillah tayi tasa hannunta tashiga cin naman, duk cikin su ba mai magana shi naman yake ci ita kuma Marwat tana ci tana danna wayarta."

"Hannunsa ya cire a hankali yace alhmdullah, tashi yayi yace mata habeebty ina jiranki a sama in kin tattare kizo kimin wanka, bata amsa shi ba tacigaba da safgarta, sanin taji sane yasa shi wucewa bedroom abun sa."

"""Zulaiha ce ta mata massage kamar haka"""

Sister ykk ya oga

"Lpy qlu alhmdullah hmmm oga yana lafiya ai yau ya dawo gida da wuri, kinsan tunda nafita a safgarsa ya sha ruwan jikinsa."

Hmmm dama nafa damiki maza zuma ne sai da wuta wlh inkin kuskura kin sake masa kinaji kina gani zaije ya auro miki wata tazo kuma ta nuna ta fiki iko da gidan cewar zulaiha.

"Chap ai wlh bai isa ba ke nifa bana son kishiya don haka mijina bai isa ya kara aure ba, bare kuma shima nasan baya ra'ayin mata biyu."

"Hahaaha hala yamiki zakin baki irin na maza kenan , to ai kina ruwa wlh tunda kika yarda da maganar sa nidai shawarwarin da zan baki, wlh karki sake kiyar da dazancen sa kuma ki nuna masa kina da yancin yin duk wani abu da ya shafeki, gara kiyi wa kanki fada sister karki ce komi na rayuwar ki sai kinjira namiji ya yanke miki hukunci , alhalin shi yana da rayuwar sa a waje shin kin san shi me yake aikatawa ne in yafita, shawarwa ne nabaki kin san an ce ciwon ya mace na ya mace ne."

Ba komai sister nagode zanyi nazari akan maganganunki.

"Da haka Marwat ta kashe datan wayan ta, tashi tayi ta nufi bedroom, tura kofan tayi tashiga, Mujaheed ta samu yana zau ne yana jiran ta kamar yadda tayi tsammani sai dai ta kudura acikin zuciyar ta, ta dai na wannan wahalan, ina dalili ace wanka wannan sai ta masa kamar wani lude."

"Kallon ta Mujaheed yayi yace tun dazu nake ta jiranki, yatsine fiska Marwat tayi tace sai yanzu na kammala cin abincin."

Kallon ta yayi yace to ai sai muje kimin wankan kinsan dai ke nake ta jira.

Sorry Jaheed wlh duk nabi na gaji kaje kayi kawai.

Kallon ta yakeyi a tsanake yake nazarin ta kana yace toh ke bazakiyi wankan bane.

"Ehhh tace masa, tare da kunna wayan ta tashiga chart hankali konce."

"Habeebty ko dai namiki wani laifi ne, cewar Mujaheed da ya zuba mata narkekkun idanunsa."

"Hmm Jaheed kenan sai yanzu ne kake tambayan ko kamin laifi, bawani laifi da kamin kawai dai bana jin dadi ne."

"Baisake ce mata komai ba ya juya yashi ga bathroom, amma zuciyar cike take fall da tunanin sababbin halayen da Marwat ta tsiro da su, yafi kowa sanin ta sabida haka zancen bata da lafiya ma bai taso ba."

Bayan wasu mintuna Mujaheed ne yafito daga bathroom daure da towel a kunkumin sa hannun sa rike da karamin towel yana goge kansa dake jike.

"Marwat ce ta taso tawuce bathroom, abunta kamar ba ita tace masa bazatayi wankan ba."

"Da ido Jaheed yabi bayan ta da kallo, zuciyar sa ce take raya masa tabbas akoi wanda yake shirin tarwatsa musu zaman takewar auren su, kuma zuciyar sa tana zargin koma waye ne tabbas ta waya suke magana dan ya lura a yan kwanakinnan tafiye bawa wayar ta muhimmanci, Amma ba komai zai yi bincike akai, dan bazai zuba mata ido taci gaba da yin duk wani abu da yaga damaba."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

WAYE MUJAHEED..?

"Mujaheed Mas'oud Raji, shi ne asalin sunan sa, da ne a wajen marigayi Alhaji Mas'oud Raji tsohon commissioner n kudi na jahar kaduna, kuma babban dan kasuwa ne a wanchan lokacin, kafin Allah ya masa rasuwa ya rike mukamai da dama acikin gomnati na wanchan lokacin, yana da mata daya wato Hajiya Sarah sai yayan su guda biyu Hajiya Aisha ita ce babba sai Mujaheed me bimata sai dai akoi rata sosai a tsakanin su."

"Hajiya Aisha tana auren wani babban attajiri ne a halin yanzu ma basa Nigeria, suna Dubai da zama ita da mijin ta da yaran ta biyu Sameer da sameerah."

"Mujaheed ya tashi cikin gata da kulawa yayi karatun sa a kasar waje , inda ya karanta business administration, Mujaheed yayi karatu mai zurfi sosai, a halin yanzu yana da company n motoci daya bude, duddah suna da branches da dama a sauran garuruwa, Amma shi yake kula da wannan company nnasa mai suna JAHEED MOTORS ,,"

"Mujaheed da Marwat auren soyayyah sukayi, bakaramin so Mujaheed yakeyiwa Marwat ba, wanda hakan yasanya suke zaman lafiya a tsakanin su."

"Marwat yace ga Alhaji Ibrahim Wakili , babban abokin Alhaji Mas'oud Raji ne tare aka sha gwagwarmayan siyasa a wanchan lokacin, shiyasa da soyayyah tashi ga tsakanin Mujaheed da Marwat ba karamin farin ciki iyayen su sukayi ba."

Marwat tare sukayi karatu da Mujaheed itama business administration ta karanta.

"Marwat taso tayi aikin gwamnati sai dai Mujaheed yaki lamunce mata, yace yafison takasan ce full house wife, badon ranta yaso ba haka ta hakura sabi da tsananin son da takeyiwa Mujaheed."

"Ganin hakan ne yasa Mujaheed ya bude mata babban plaza mai suna MJ plaza a cikin gari sannan ya zuba mata ma aikata sosai suke kula mata da komai, takan zuwa ta duba time by time, duddah sauran aikin a gida take yinsu a cikin system dinta."

"Kawayen Marwat sun sha fadamata cewa wlh tarage nunawa Mujaheed so sabida namiji ba dan goya da zaniba ne akan me zata zauna a gida ya hanata fita aiki da karatunta da komai, amma ta zauna agida sai kace matar kulle."

"Marwat bata taba yarda da maganganun su ba sabida tana matukar son mijin ta, kuma ba abunda Mujaheed ya rageta da shi, shiya sa hakan bai taba damunta ba."

""" Monday tushen aiki , Mujaheed ne yafito cikin shirin sa na fita, wasu irin suit ne masu shegen tsada a jikin sa, dinning table ya nufa inda ya hango Marwat ta na zaune da alama shi take jira."

"Saving din sa tayi , toested bread ne da tea, Mujaheed ne ya kalli cup din data zuba masa tea din yace me wannan habeebty, kallon sa tayi tace kamar yaya Jaheed break fast ne mana, kinsan dai office zan fita kuma kinsan nafi son abu mai dan nauyi."

"Haba Zauji kasan yau din na makara ne, kasan jiya bansamu bacci da wuri ba."

"Bai sake cemata uffan ba sabida bai san mekuma zai ce mata ba, gaskiya hakurin sa yafara karewa akan lamarin Marwat, haka yayi break din a gaggau ce, bayan ya kammala ne yace habeebty yakamata muje muga doctor jiya ma Hajiya tamin magana akai."

"Marwat ce ta ce haba Zauji ai haihuwa ta Allah ce , shi ke bada ita san da yaso ,ko dai kaima kafara gajiya da Rashin haihuwa na ne."

"No ba haka bane kawai dai naga yakamata muje muga doctor ne, yau kimanin shekara goma da auren mu , amma ko batan wata baki taba yiba, kuma bamutaba ganin doctor akan matsalar ba, kinga gara muje a duba mu asan inda matsalar take kuma kunga Hajiya har tafara magana akai."

"Marwat ce ta ce toh shikenan Allah ya sa muji alkhairii, da ameen ya amsa."

"Mujaheed ne da Marwat zau ne a gaban doctor, bayan yagama duba results din su da akagama yimusu gwaje gwajen da ya kamata."

"Kallon Mujaheed yayi yace yallaboi, result din Hajiya ya nuna bata dauke da wata matsala ."

Wani irin ajiyar zuciya Marwat ta sauke tare da cewa alhmdullah.

"Doctor ne ya kalli Mujaheed yace yallaboi matsalar a wajen ka take , kana da matsalar tsinkewar maniyi wanda hakan shi ya sa baza ka iya bawa mace ciki ba, sabida kafin sparm din ka ya shiga mahaifarta ya riga da ya tsinke."

Sai dai akoi magungunan da zamu dauraka akai Insha Allahu za a dace dan ba abun da muwa bane wannan.

"Mujaheed ne ya sauke ajiyar zuciya, mikawa doctor hannu yayi sukayi musabaha, yace thank you doctor Allah ya sa a dace ameen doctor yace."

"Basu koma gida ba sai da Mujaheed ya bita pharmacy yasayi magungunan da doctor ya rubuta musu, nan suka wuce gidan hajiya."

"Bayan Mujaheed ya sanar da hajiya abun da doctor yafa dane , jikin ta yayi sanyi, sosai ita da take saka ran ganin jikokin ta ta wajen Mujaheed sai ga shi an samu matsalar a wajen sa take."

"Cikin damuwa Hajiya ta shiga musu nasiha da nuna musu komai na Allah ne, ya jarraba maganin Insha Allahu za a dace, basu bar gidan Hajiya ba san da ta tabbatar da tarage musu damuwa sosai sannan ta musu nasiha mai ratsa zuciya, sallama suka mata suka wuce gidan su kowa ransa cike fall da tunani da damuwa, kafin wannan rana Marwat bata taba tunanin cewa bazata haihu da Mujaheed ba amma a yau tunanin ta yafara sauyawa."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Bayan kwana biyu da zuwan su Marwat asibiti, posting tayi a group din SIRRIN YA'MACE, kamar haka,,"

"Asslm sister's barkanmu da warhaka, ina cikin damuwa , yau shekara goma da auren mu Allah bai bamu haihu wa ba, munje asibiti an ce miji na ne yake da matsar tsinkewar maniyi dan Allah matan sirri kubani shawara ina cikin damuwa."

Nan fa akashiga mata comment wasu suna cemata ta hakura ta cigaba da addu'a haihuwa ai na Allah ne.

"Yayin da wasu suke cemata wlh karta yarda ai da ita ce take da matsalar da bazai zauna da ita ba, haka dai tayi tabin comment tana ta karantawa."

Massage tagani anturo ta inbox din ta dubawa tayi taga zulaiha ce.

Haba sister sai kace baki san halin maza ba yanzu naga posting din ki a group din SIRRIN YA'MACE shiya sa nabiyo ki ta private.

"Ai wlh karki taba yadda haba kituna in dake aka samu da wata matsala da wlh sai ya rabu da ke kokuma ya kara aure, don bazai yadda ya zauna da juya ba, amma ke kin tsaya neman shawara, gara ma tun wuri kiyiwa kanki fada, haka zakici gaba da zama da shi kenan ke bazaki so kiga jinin ki ba kenan, amma yakamata kiyi tunani akai."

"Ajiyar zuciya Marwat ta sauke bayan tagama karanta sakon da zulaiha ta turamata, tunani tashiga yi a zuciyarta , tabbas zulaiha gaskiya ta fada, toh amma haryanzu tana son Mujaheed, wata zuciyar ce tace to kenan haka zakici gaba da zama da shi baya haihuwa, nan dai tashiga sake a ranta, shaidan sai bijiro mata da"

"munanan abubuwa yakeyi, tabbas yakamata tayi magana da Mujaheed dan a yanzu ta tabbatar da tana bukatar haihuwa."

"Tashi tayi tanufi kitchen domin shirya masa dinner, tuwon shinkafa miyar taushe ta masa don tasan yana matukar son tuwo musamman in ya samu miyar taushe, haka tagama komai tsaff tajera akan dinning table, bedroom tawu ce domin yin wanka."

"Bayan ta fito ne daga bathroom din tayi sallan magariba, wajen mirror ta nufa , mayukanta masu bala'in tsada ta hau shafawa san da tagama sannan ta dau ko humra ta shafa, clouseset ta bude wata arniyar sleeping dress ta ciro, bakaramin kyau rigar ta mata ba, rigar transfered ne red in colour, jara gashin kanta tayi ,tasa masa ribbon red ta daure shi zamatayi tana jiran dawowansa."

"Karfe 9:30pm Mujaheed ya shigo gidan duk agajiye yake, ganin ba kowa ne a parlourn yasa ya nufi bedroom din sa dan yasan warhaka Marwat tana chan, duddah ma kwana biyun nan yaga ta chanza masa sabi da ta daina zuwa bedroom din sa sai dai shi yaje nata, kuma in yaje ma da fada suke rabuwa, ga mamakin sa kuwa ya same ta acikin dakin, tattausan murmushi ya sake mata, itama tashi tayi ta nufo shi cikin yanga da yauki, jakan shi ta karba, kiss ya mannamata a gefen kumatunta, cikin nitsuwa tafara rage masa kayan jikin sa bayan tagama ne ta wuce bathroom ta hada masa ruwan wanka, ita ta taima ka masa yayi wankan, bayan yagama shiryawa ne, suka sauko parlour domin cin abinci."

"Cikin santi da so da

Please Login or Register in order to submit comment