Reading SIRRIN YA'MACE COMPLT BY MRS ALKALI Chapter 7 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya zauna awajen ta saitin inda kanta yake.

"Wani irin kululun takaici ne ya tokarewa Kamal wuya shidai baisan wannan mutumin daga ina ya fito ba, don daga ni ba dangin ummah ba ne gashi harda wasu uban ledoji da basket ya shigo da shi, wani irin kishin Mufeedah ne yake taso masa duddah kaka ce ta hada auren su Amma Allah ya gani bakaramin so yakeyiwa Mufeedah ba dan gani yakeyi ya tsinci dami a kaleh, don Mufeedah tana da qualities da ba ko wacce mace ce take da shiba."

"Jin kamshin turaren ya kara kusanto ta ne gashi tanajin alamar idanu na yawo akan ta ne yasa a hankali ta dan bude idanunta, karaff idanunta yafada acikin na Mujaheed dake zaune a gefen ta ya zuba mata narkekkun idanunsa."

"Ai dawani irin sauri, ta maida su zata rufe cikin husky voice dinsa kamar mai yin rada cikin wata irin sassanyan muryan da ba kowa ne zai iya jin sa ba yace upon your eyes bana son gulma."

"Cike da kunya ta bude idanunta ganin ya kamata tana satar kallon sa cikin muryan marassa lafiya tace barka da dere, cikin nitsuwa a hankali yace how are you feeling now, a hankali ta ce da sauki, Wani irin ajiyar zuciya ya sauke ahankali ya ce alhmdullah, dan kallon sa Mufeedah tayi jin irin hamdalan da yakeyi, aranta ta ke jinjina kirkin sa , tunowa da irin zagin kare dangi da matar sa ta mata dazu ne yasa ta turo baki tare da kawar da kanta gefe tunowa da tayi akan sa akamata iban albarkan nan duddah tawani bangaren zuciyar ta tana fada mata ai dole ne ma matar sa tayi haka irin wannan gallelen mijin da Allah ya bata."

"Duk abunda ya faru akan idanun Kamal yau yana ganin ikon Allah shikuma wannan daga ina, tun dazu da suka gaisa da Mufeedah ta rufe idanun ta tace masa bacci takeji sai gashi daga zuwan wannan mutumin tabude idanunta har hira sukeyi kasa kasa gaskiya shi bai fahimci wannan lamarin ba."

Cike da kishi Kamal ya ta so daga kan kujerar da yake zaune wajen Mufeedah ya nufa zama yayi a ta inda kafofinta suke sai yazama kamar sun sata a tsakiyar su ne.

"Wani irin kallon love Kamal ya mata tare da cewa beb kin tashi ne sannu ya jikin naki, cike da kunyan abunda kamal yayi Mufeedah ta amsa tace da sauki."

"Ko inda Kamal yake Mujaheed bai kalla ba duddah yana sane da abun da yafaru, kuma ya fahimci boyfriend din ta ne , shi abun ma dariya ya basa ganin yaranta ne yake damun sa, in da soyayyah yakeyi da Mufeedah ai Kamal bai isa ma ya matso kusa da ita ba, amma duddah haka sai ya koya masa darasi."

"Mujaheed ne ya zuba mata narkekkun idanunsa, duk atakure takejin kanta ganin yanda suka sakata a tsakiya ga Wani irin narkeken kallon da Mujaheed yake jifanta da shi duk tara sa sukuni."

"Mujaheed ne ya tashi wajen basket din daya kawo ya nufa plate ya dauka yayi saving din ta tuwon shinkafa miyar taushe dawo wa yayi da plate din a hannunsa zama yayi tare da zuba mata idanu cikin wata irin karamar murya, yace wake up ba yanda ta iya dole tabi umarnin sa ganin ba wasa akan fuskarshi."

"Shi dai Kamal yaga bakin sa ya motsa amma kuma baiji mai yace ba kuma ga Mufeedah ta tashi zaune shifa baigane me mutumin nan yake nufiba, ga wani irin kallon da yaga yake mata wanda yakasa fassara kallon ga plate din da ya rike shake da tuwo sai kamshi ne yake ta faman tashi."

"Ganin ta zauna ne yasa ya mika mata plate din a hankali ta saka hannayenta zata karba by mistake taji saukan hannun sa cikin nata, da sauri ta janye hannun ta jin wani irin shocking, cike da basarwa Mujaheed ya ajiye mata plate din a kan cinyar ta, dan rankwafo wa yayi cikin sanyin murya yace eat."

"Ba musu kamar wadda yayiwa bita zaizai duddah bata da apatite din cin abincin amma haka ta tsinci kanta da daukan spoon din , a hankali tayi BISSIMILLAH tafara tsakuran abincin cike da nitsuwa."

Ganin ta fara cin abincin ne yasa Mujaheed ya ciro wayar sa yafara dannawa

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Tsakuran tuwon Mufeedah tayi duddah tuwon yamata dadi amma bazata iya cin saba dan jinta takeyi a mugun takure, a hankali ta ajiye spoon din."

"Ganin ta ajiye spoon din ne ya sa Mujaheed dagowa dan yana kallon ta ta kasan idanunsa, ganin bata ci wani abincin kirki bane yasa shi kallon ta sauke kanta kasa tayi ganin irin kallon tuhuman daya kemata."

"Wayarsa ya mayar cikin aljihun sa spoon din ya dau ka plate din ya daura a cinyar shi, tuwon ya ibo a spoon a hankali ya nufo bakinta da shi, fiska ba wasa yace mata haaaa irin yanda akeyiwa yara."

"Satar kallon inda Kamal yake zaune tayi gani tayi yacika yayi famm sai huci yakeyi kamar wani tsohon kumurci, jikin ta ne yayi sanyi."

"Sake tamke fiska Mujaheed yayi ganin position din da take kallo fiskar nan ba wani annuri yasake cewa haaa, ganin yanda ya tamke fiska babu alamar sassauci ne ya sa batama san ta bude dan karamin bakin ta ba, cikin nitsuwa ya shiga bata abincin a baki sai kace wata baby."

Kamal ne ya tashi jin zuciyar sa tana barazanar fitowa ga uban korjini da mutumin ya masa da ba haka ba wlh sai yayi maganin sa hanyar fita ya nufa ko sallama baiyiwa Mufeedah ba sai ji sukayi an bugo kofar da wani irin karfi.

"Mufeedah ce ta dan razana jin yanda kofar tayi kara kamar zata karye, Mujaheed ne ya dan kalle ta yace uhuummm matsoraciya kawai kifadawa boyfriend din ki nan ba government hospital bane idan ya karya musu kofa securities din su zasuyi maganin sa."

Kanta ta sunkuyar kasa sabida kunyar abunda Kamal yayi.

"Yanda su baba sukaga yanayin Kamal sunsan da akoi matsala, don tun dazu suke jiran fitowar Mujaheed amma shiru, sai kuma gashi yanzu Kamal yafito ransa abace, sallama yayi musu tare da addu'ar samun lafiya wa Mufeedah wucewa yayi, ganin a asibiti ne yasa baba bai masa bayanin waye Mujaheed ba dan gara yamasa bayani da alama kishin maza ya motsa, amma sai sun koma gida zai masa bayani."

Haka Mujaheed yayi ta feeding din Mufeedah kamar wata baby duddah ta koshi bai barta haka ba sanda yakara mata da naman da ya sayomata awajen ALQASIM SUYA.

"Bayan da Mufeedah ta iya san da yayi ra'ayin sa sannan ya kyaleta haka, maida plate din yayi a cikin basket din."

Tazaci tafiya zaiyi sai taga ya dawo ya zauna yacigaba da danna wayarsa da alama wani abu mai muhimmanci yakeyi aciki.

"Ganin hankalin sa baya kanta ne yasa tasamu damar zuba masa idanu, Mujaheed yana duba wasu takkadu na office a wayarsa jin kamar ana kallon sa ne yasa ya dakata da abunda yakeyi."

"Ba zato ba tsammani taga ya dago kansa hada idanu sukayi a karo na biyu, da sauri ta sa hannun ta ta rufe fiskanta ganin ya kamata akaro na biyu tana satan kallon sa."

"Dan murmushi yayi, cikin sigan tsokana yace hala nafi gajeren boyfriend din ki kyau shiyasa kike kallo na, yarinya taga dan saurayi mai kyau ta rikice ."

"Ai batasan sanda tawani zabura ba tare da cukuikuyewa acikin hijabinta ba, shikam yana nan sai kace hawainiya yanzu zakaga yana fara'a anjima kuma kaga ya daure maka fiska."

Agogon hannunsa ya duba ganin time ya tafi ne yasa shi ya tashi dan bai taba tunanin zai kai wannan time din a cikin asibitin ba.

"A hankali ya ce zan tafi, Jin abun da yace ne yasa ta dan sassauta wa fiskar ta ta, amma duddah haka bata ciro ta sosai ba."

Ba zato taji saukan muryarsa kukan me kikayi ya saukar miki da fever haka.

Jin tambayan a bazata ne yasa ta tayi shiru don bazata iya cemasa matar sa ce ta zage ta ba.

"Ganin bazata ce masa komai bane yasa a cikin murya mai taushi yace waya ce miki mace tana yiwa yar'uwar ta mace kuka, ashe ma ke din raguwa ce tunda gashi kinyi kukan da ya haifar miki da fever."

"Turo masa baki tayi, cikin shagwaban da bata masan tayi ba, tace fa uhuummm uhuumm cemin tayi wai wai wai sai takasa karasa maganar dan tanajin nauyin tace masa tace mata yar iska , karuwa."

Dariya tabasa ganin taki kara sa maganar kuma yariga da yasan me zata fada tunda yaji komai agaban sa Marwat ta zage ta .

Dan murmushin gefen baki yayi yace to wayace ki kira mata miji kin san tana bala'in sona shiyasa tazaci ke din budurwa tace.

"Cikin sauri ta rufe fiskanta jin abunda Mujaheed ya ke fada, cikin sanyin Murya taji yace i apologize on be half of her bata fahimce ki bane shiya sa kuka samu miss understanding amma Marwat is a Nice person , sorry."

"Wani irin sanyi taji a cikin ranta tabbas taji zafin zagin da matar sa ta mata amma yanzu da yafadama wadannan kalamen sun waken laifin matar sa ko da ita ne May be haka zatayi cikin zuciyar ta take jinjina irin son da yakeyiwa matar sa, sake maimaita sunan da taji ya ambata tayi, cikin ranta tace Marwat uhmm daga ji Sunan yan gayu ne wannan."

"Saukar muryansa taji yana cewa gud night Allah ya kara afuwa, a hankali tace ameen."

"Bayan sa tabi da kallo ganin yan da yake tafiya cikin nitsuwa da kasaita, haka kawai taji wani abu acikin ranta."

"Harzai bude kofar yaji zazzakar muryan ta cikin sanyi, yayaaaa ta dan ja karshen sunan Wani irin faduwa gaban sa yayi wanda shi kansa bai san dalili ba."

"Juyowa yayi ya zuba mata ido, sunkuyar da kanta tayi tana wasa da zuben azurfan da yake dan yatsan ta, kamar bazata yi magana ba har zai bude kofar yaji tace nagode Allah ya saka da alkhairii Allah ya kare gabanka da bayanka, Allah ya biya bukata."

"Wannan shi ne karo na biyu da tamasa irin addu'ar nan, wani irin sanyi ne yake ratsa kasar zuciyar sa, bazai iya tuna yaushe rabon da Marwat tama sa irin wannan addu'ar ba cikin wani irin annuri yace thank you, bude kofar yayi yafita."

"Su baba ya samu suna zaune a inda yabar su sai yanzu yakejin kunyan zaman dayayi acikin dakin daga shiga dubiya, cikin kunya yamusu bankwana ya tafi domin dare yafara yi ."

"Ahankali Mufeedah ta zame ta kwanta, rufe idanunta tayi hancinta nakara shakomata sassanyan kamshin turaren sa,kai kace yana cikin dakin wani irin Nishadi takeji, ga bugun zuciyarta da ya karu, Wani irin yanayi take jin kanta aciki, a haka su ummah suka shigo suka sameta."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Misalin qarfe 1 1:30pm Mujaheed ya shiga gidan , a hargitse yatarar da parlourn, bakin cikin sane yadawo sabo ganin yanda Marwat tabar parlourn a lalace, tunani ya fara a zuciyarsa ko dai zaije ya fadawa gidan su ne inyaso amata fada, wata zuciyar ce tace masa hakan bai kamataba yau shekara goma da auren su bai taba kai ta kara ba sai yanzu ajiyar zuciya ya sauke a kasar zuciyar sa yace Insha Allah zanyi kokari infahimtar da ke kuskuren ki."

Bedroom din sa ya wuce dan ba karamin gajiya yayi ba yau tun da safe bai huta ba sai zirga zirga yakeyi ga bacin ran da Marwat ta sakashi duddah yana kokarin danne abun aransa.

"Ganin kofar bedroom din sa a bude ne yasa shi dan mamaki da alama akoi mutum aciki, yasan kuma Marwat ta daina zuwa bedroom din sa tunda ta dauki fishi da shi, a hankali ya tura kofar wani sassanyan kamshi ne ya bugo hancin sa."

Cikin nitsuwa ya shiga cikin dakin Marwat yagani kwance akan makeken gadon sa tana sake da wani irin sexy dress.

Kallo daya yama ta ya dauke kansa dan haryanzu yanajin haushin ta ganin ta a hakan ba karamin birki ta masa lissafi yayi ba amma kokari yakeyi ya danne hakan dan alkawari yayi wa kan sa cewa idan har ba ita ta bukaci ya kusance ta ba toh bazai taba nemanta ba sai tanemi afuwarsa kuma tagane kuskurenta.

"Jin anbude kofar ne ya tabbatar mata da cewa Mujaheed ne ya dawo, dama zaman jiran sa takeyi duddah tana cikin fishi da shi Amma kuma bazata iya kaucewa halin da take cikiba a yanzu dan bakaramin bukatar mijin ta takeyi ba shiyasa ma ta daure ta kawo kanta in komai ya kammala sai ta daura da fishin ta."

"Marwat ce ta tashi daga kan gadon cikin yanga ta nufo Mujaheed shidai baice mata uffan ba yazubawa sarautar Allah ido, bathroom din ta wuce ruwan wanka ta hada masa."

Fitowa tayi dakanta ta ta shiga rage masa kayan jikin sa Mujaheed bai hana ta ba dan shima a bukace yake da ita.

"Bayan ta rage masa kayanne taja shi cikin bathroom din, juyawa tayi zata fita, ba tsammani taji ya jawo ta jikin sa cikin abun wankan suka fada nan fa suka shiga aikawa da juna sakonne."

Ba karamin missing din juna sukayi ba dan kowannen su cikin zafin nama yake kokarin isar da sakon sa.

Nikam nace uhumm dama tsakanin mata da miji sai Allah

"Sanda suka gama jagwal gwala juna sannan suka yi wankan atare, bayan sun fito daga bathroom din ne bawani bata lokaci Mujaheed ya daura mata daga inda ya tsaya dan ba karamin bukatar ta yakeyi ba a hankali ya kwantar da ita akan gadon , bakinsa ya saka acikin nata a tare suka sauke ajiyar zuciya dan ba karamin missing din juna sukayi ba ."

"Cike da kwarewa Mujaheed yake sarrafa Marwat duk sunbi sun fita a hayyacin su, kowa burin sa kasan cewa tare da dan'uwan sa, jin Mujaheed ya karan to addu'ar saduwa da iyali ne yasa Marwat dawowa cikin hayyacinta."

Daga koncen da take Mujaheed ya rankwafa kanta haka ta zura hannunta taja bedside drower ta ciro wani kwalin condoms cikin muryan bukatuwa tace Zauji tsaya.

"Chak Mujaheed ya dakata da abunda yakeyi jin muryan Marwat dago jajayen idanunsa yayi zuba mata su yayi, ganin ya daka tane yasa ta bude dan kwalin dayake hannunta kororon roba guda daya taciro ta mika masa."

"Mujaheed ne ya karba tare da sake zubamata idanunsa alamar wannan fa, cikin karfin hali Marwat ta ce kasaka kasan bazan yadda kasake kusanta ta ba sai munje asibiti an tabbatar mini da lafiyar ka."

"Wani irin dukan kirjinsa kalaman Marwat suka masa, domin kuwa a bazata suka taho masa , bai zaci zargi da kyamar da Marwat take masa yakai haka ba."

Yau shi akebawa kororon roba dan zai sadu da matar sa ta sunna shida yake neman haihuwa shine kuma zata saka yayi amfani da condom akan wani dalilin ta marar tushe.

Kallon ta yayi yanayin fiskar sa na chanzawa cikin wata irin murya da tagama gauraya da sha'awa dakuma bacin rai yace Marwat kinyi kadan kisa ba kusance ki da kororon roba akan wani banzab dalilin ki marar tushe.

Wlh a yau kuma a yanzu zan kusance ki batare da kororon roba ba ina so inga karshen iskancin ki a yau.

Jin abunda Mujaheed din yake fada ne yasa gaban Marwat faduwa dan wlh bata shirya mutuwa ba ina dalili ya je ya dauko cuta ya yaba mata tana zaman zaman ta ita ba da ba ba jika ba inta mutu ai ita ne da asara.

"Cike da karfin hali ta tattaro sauran karfin ta ta yunkura tana kokarin ture Mujaheed, amma ina ya saka mata karfin shi gaba daya ."

"Cikin bakin ciki da dana sani Marwat tashiga ture shi tana dukan kirjinsa, Mujaheed, kar ka tabani wlh bazan yarda ba mazinaci kawai ni zaka yabawa ciwo kaje jagama bin karuwar ka sannan kace zaka sadu dani ba kororon roba Allah ya tsinewa wannan sha'awar da tasa nakawo kaina gare ka ."

"Jin irin kalamen da Marwat take jifan sa dasune ya kara tsananta bacin ransa cikin fishi yace zakiga yanda zan sadu dake ayanzu ba sai anjima ba zan saka miki ciwon da kike gudun, ai bai jira mezata sake cewa ba kawai ya shigeta da mugun karfi Wani irin ihuu Marwat ta sake kai kace wannan ne first night dinta."

Jin Mujaheed ya gama shiganta ne yasa takara fashewa da kukan bakin ciki shikenan ita kam tata ta kare.

Haka Mujaheed ya murje Marwat son ransa cike da mugun ta da bacin rai bayan komai ya lafa ne ya koma gefe ya konta.

"Nan fa yaji Marwat ta kara volume din kukanta sai kace wanda aka cirewa ido wani irin takaicinta ne ya kama Mujaheed, don a hakan ma bakaramin kokarin danne zuciyar sa yakeyi ba , baya son yarasa control din sa gaba daya kar yazo yayi abunda zaiyi dana sani agaba."

"Cikin muryan tsawa da bacin rai yace"" get out!"" Of My room."

"Dawani irin sauri Marwat ta diro daga kan gadon ko takan sleeping dress din ta bata biba tanufi kofar fita daga dakin sanda taje bakin kofar ta ce Allah ya isa mugu azzalumi kawai wlh Allah sai ya sakamin kuma bazan zauna da kai ba saika sakeni, tana kaiwa nan ta fita tare da bugo masa marfin kofar da mugun karfi."

Dafe kansa yayi tunanin halayen Marwat yakeyi dole ne gobe ya dauketa suje asibiti a musu gwajin HIV duddah ya tabbatar da basu da komai amma in ba haka ba yasan Marwat bazata daina zargin sa ba.

"Ajiyar zuciya ya sauke tashi yayi yashiga bathroom ya tsaftace jikinsa, shirya wa yayi cikin pyjamas din sa haka ya kwanta suku suku jiki ba kwari in yace halin Marwat baya damun sa to yayi karya wlh, haka yacigaba da tunani har bacci barawo yayi awun gaba da shi."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Yau takama Monday, cikin Mujaheed ne yafito cikin shirin sa na fita office sai dai yana son kafin ya wuce office su je asibiti shida Marwat."

"Bedroom din ta ya shiga azaune ya same ta a gaban dressing merro da alama wanka tayi sai dai kallo daya zakayi fiskar ta kasan bakaramin kuka tayi ba, abunka da farar mace fiskar nan tata tayi jawur da ita ga kumbura da idanunta sukayi."

Kallo daya tamasa ta dauke kai dan wani irin haushi da takaicin sa ne suke taso mata.

Mujaheed bai damu da irin kallon data masa ba dama yariga da yasan za'a eina hakan.

Cikin dakekkiyar muryansa da ba yason ta kawo masa wargi yace inajiran ki parlour ki shirya zamuje hospital baijira me zata ce ba haka ya juaya ya sauka main parlour domin jiranta.

Marwat bata musa ba dan a halin yanzu itama tana son tasan matakin kafiyar ta koda kuwa Mujaheed bai ce suje hospital ba dama tayi niyan zuwa don haka batare da gardama ba tashiga shiryawa.

"Yana zaune a parlourn wayarsa ya ke dannawa jin alamar ta sauko ne yasa ya kashe wayar ya mayar aljihun sa ko inda take bai kalla ba ya fice daga cikin parlourn ganin hakan ne yasa Marwat ta bi bayan sa, fiska ba annuri."

"Zaman kurame sukayi acikin Motar babu mai cewa uffan, ahaka har suka iso haraban asibitin parking Mujaheed yayi batare da ya kulata ba ya fito itama hakan da yayi bai wani dame ta ba bayan sun fitone suka nufi cikin asibitin."

"Zaune suke a gaban doctor cike da fara'a doctor yace yallaboi har magani ya kare kenan, toh Allah ya sa andace da ameen Mujaheed ya amsa ita kam Marwat ko kallon inda suke batayi ba dan ayanzu ba batun haihuwa ce agabanta ba , sanin matakin kafiyar ta shine first."

"Mujaheed ne yadan kalli doctor cike da dan nauyi ya ce doctor so nake a mana medical checkup ina son a hada harda na HIV nida Madam ,yakara sa maganar cikin dan kunya, akasar zuciyar sa kuma wani irin turirin zafi da kuna yakeji, wai yau shine za'ayiwa gwajin kanjamau, yace a musu medical checkup ne don baya son doctorn ya zargi wani abu tun da family doctorn su ne ,ajiyar zuciya ya sauke wata zuciyar ce tace masa to ya zaiyi hakan shine maslaha dan baya son suci gaba da zama da Marwat akan zargin sa."

"Doctor ne yace ba matsala yallaboi bari mufara duba yanayin lafiyar sparm din ka muga ko maganin damuka daura ka akai yayi aiki, in mungama da wannan sai amuku medical checkup din kasan yana da matukar muhimmancin ace time to time ma'aura ta su dinga yin gwaji domin sanin matakin lafiyar su."

"Haka kuwa akayi bayan angama masa gwajin sparm din ne aka sake iban jinin su shida Marwat aka gwada, bayan results ya gama fitowa ne likita ya fara musu baya ni kamar haka."

"Sorry to say yallaboi bamuga wani chanji a cikin sparm dinka ba da alama maganin baiyi wani aiki ba dan bawani improvement da aka samu, sai dai hakan ba wata damuwa bace dama ana iya samun hakan, shiyasa muka ce kadawo after 2 month domin musan halin da kake ciki yanzu zamu chanza maka maganin Insha Allahu za a iya dace wa wannan karon."

Cikin sanyin jiki Mujaheed ya ce ba damuwa doctor kowani bawa ba ya wuce kaddarar sa.

Sake kallon su doctorn yayi yace sai kuma batun gwajin da aka muku na HIV.

"Ai wani irin tsalle zuciyar Marwat tayi ji takeyi kamar taje ta warce results din taganewa idanunta, dan ita kam tagama saddakarwa Mujaheed yagama yaba mata ciwon kanjamau."

Shikam Mujaheed hankalin sa kwance

Please Login or Register in order to submit comment