Reading SIRRIN YA'MACE COMPLT BY MRS ALKALI Chapter 6 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kara sa maganar cikin zafin rai daganin yan da take rusa kuka kai kasan maganar ba karamin zafi tamata arai ba.

"Ummah ce ta jawo ta jikin ta cikin hikima irin ta uwa tafara mata nasiha da kontar mata da hankali, ganin irin yanayin da Mufeedah ta shiga ne yasa tayi ta kalleshin ta kanta na bisa kan cinyar ummah baccin wahala yayi awun gaba da ita."

"Ummah ce ta sauke ajiyar zuciya ganin Mufeedah tayi bacci kontar da ita tayi a hankali, tunani tashiga yi hanyar da zatabi ta takawa abun birki dan idan tace abun bai dame ta ba tayi karya kawai dai daurewa takeyi bata son Mufeedah taga ta karaya shiya sa take nuna mata abun bai dameta ba, amma yazama dole tayiwa tufkar hanci."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

Misalin qarfe 5:30pm na yamma motar Mujaheed ne tayi parking a kofar gidan su Mufeedah.

Yaji ma yana zaune a cikin motar sai saka da warwara yakeyi a cikin zuciyar sa.

"Cikin karfin hali ya dauki wayar sa numbern Mufeedah ya kira amma har ta katse ba a daga kiran ba, sake kira yayi a karo na biyu namma ba ayi picking call din ba, ajiyar zuciya ya sauke tare da fitowa daga cikin motar."

"Wani yaro ne ya zo wucewa tabakin layin , kiran sa Mujaheed yayi yace shiga gidannan kace ana sallama da Mufeedah."

Ummah tana tankada garin tuwo a tsakar gida taji sallamar yaro.

"Wai ana sallama da Mufeedah inji wani a waje, cewar yaron da aka aiko."

Ummah ce ta ce je kace inji waye..?

"Ba afi minti daya ba yasake dawowa, wai inji Mujaheed, shiru ummah tayi tana nazari, chan tace kaje kace masa bata nan , fita yayi dan isar da sakon sa."

Baba zuwaira ce tafito daga dakin tace uhuummm sabon salo kenan kiran sallah da wisirrr.

Ko kulata ummah batayi ba taci gaba da aikin ta.

"Mujaheed ne ya Ciro gudan 1k yaba wa yaron , godiya yaron yashiga masa nan yawuce yana yan tsalle tsallen sa."

"Duddah ance masa batanan haka kawai zuciyar sa take rayamasa ba gaskiya bane , May be tananan fishi tayi sabida zagin da Marwat ta mata."

"Yana tsaye a kofar gidan ya jingina da jikin motar sa, wani dan dattijo ne yanufo kofar gidan akan keken sa irin na tsofi."

"Ganin bakuwar fiska ne yasa malam Muniru ya yi parking din keken nasa , sauka yayi yanufi mutumin dake tsaye a kofar gidan ya jingi na da jikin motar, gawani irin kwarjini da haiba da ke tattare bisa fiskar sa."

"Ganin dattijon ya na nufo sane yasa Mujaheed cikin sassarfa ya tinkaro malam Muniru, sallama ya masa tare da mika masa hannu cikin wani irin nauyi da Mujaheed bai san daga ina yake jinsaba ya mikawa malam Muniru hannunsa musabaha sukayi tare da gaisawa."

"Malam Muniru ne yace hala kayi batan kai ne kake tambaya, dan sosa kai Mujaheed yayi yace a'a baba nazo gidan nan ne yakara sa maganar tare da nuna kofar gidan."

"Cike da mamaki baba yake kallon sa, toh waya zo nema agidannan kuma, asanin sa dai wannan ba dangin hajiya shuwa bane, bare yace wajen ta yazo."

Dan kaf cikin gidan yasan dangin ummah ce kawai zasu iya kama da wannan bawan Allah.

Cikin karfin hali baba yace to Allah dai yasa lafiya nine maigidan sunana malam Muniru.

Sake sunkuyar da kansa kasa yayi jin shi ne mahaifin Mufeedah cike da nauyi da kunya yace nazo wajen Mufeedah ne.

"Cike da matsanancin mamaki baba ya kalli Mujaheed, toh ina Mufeedah tasan wannan attajirin mutumin kuma me hadinta da shi."

Cikin karfin hali baba yace to ince dai ko lafiya kake neman ta Allah dai yasa bawani abun bane yafaru.

"Cikin nitsuwa ya ce lafiya kalau baba, dama nazo mugaisa ne."

"Cikin zuciyar baba tunani yakeyi ko dai sabon saurayi Mufeedah tayi ita da auren ta saura sati biyu, kuma yaushe Mufeedah take fita waje da zata hadu da wannan attajirin."

"Cikin sanyin jiki baba yace toh barin shiga cikin gidan, cike da kunya Mujaheed ya jinjina kai."

"Cikin gidan baba ya nufa , zuciyar sa cike da sake sake , wlh da ba don wannan mutumin yayi masa korjini ba ai da yajima da koran sa a kofar gidan, amma hausawa sun ce wata fiskar tafi gaban mari, ko da yake kaifin ummah da mufeedah ne amma bakomai zaiyiwa tufkar hanci da wannan tunanin baba ya shiga cikin gidan."

"A tsakar gida ya samu ummah tana aikin tuwon dare, jin sallaman baba ne yasa baba zuwaira fitowa daga cikin dakin ta."

"Ummah ce ta masa sannu da dawowa cikin sakin fiska ya amsa mata, yana mata sannu da gida."

"Baba zuwaira ce tace malam andawo lafiya, amsa mata yayi tare da cewa ina Mufeedah ne."

"Ummah ce ta ce tana daki , bacci takeyi, ran baba ne ya baci yace haba wani irin bacci kuma da wannan yammacin."

Cikin dan fada fada yace to ai sai ki taso ta kice mata tayi bako yana kofar gida yana jiran ta.

"Wani irin faduwa gaban ummah yayi, tabbas ba kamal bane dan idan Kamal ne yazo hira shi harcikin gidan yake shigowa, to kuwa waye ne da baba dakan sa yake masa iso, zuciyar ta ce ta ce kodai Mujaheed din ne bai tafi ba, cikin rashin mafita ta nufi dakin dan cika umarnin baba."

"Cikin dakin tashiga, Mufeedah taga ni a konce har yanzu."

Zuwa tayi domin tashin ta a bacci saitaga ashe ma tariga da ta farka kawai dai tana konce ne ummah ce ta taba jikin ta zafi taji kamar wuta.

"Cikin tashin hankali tace haba Mufeedah kinga irin abun da nake gudu ko, shiyasa nace kisawa ranki salama, amma kinki gashi kinjawo wa kanki zazzabi."

"Cikin azabar zazzabi Mufeedah tace ummah ki lullubani sanyi nakeji da sauri ummah ta dauko wani blanket dinta mai taushi ta rufa mata, tashi tayi tana cewa barinje infada wa malam gaskiya baikamata abarki a haka ba inyaso ko asibiti ne ma kaiki."

"Ummah ce ta samu baba a turakan sa , sanar dashi halin da Mufeedah take ciki tayi, ba bata lokaci ya tashi yabi bayan ta dan baya wasa da duk wani abu da yashafi yayan sa musamman ma Mufeedah da ta kasan ce rauninsa dan kuwa ita kadai ce diya mace."

"Dakin da Mufeedah take baba yashiga , ganin irin halin da Mufeedah take ciki ne yasa ka baba shiga tashin hankali domin kuwa jikin ta kakkarwa yakeyi da alama sanyin zazzabi ne ya rufeta duddah blanket din da ummah ta lulluba mata hakan bai hanata shiga cikin yanayin ba."

"Akidime baba ya cewa ummah barin fita innemo abun hawa sai mukaita asibiti ki kimtsa mata jiki kafin na samo abun hawan, bai jira amsar ummah ba haka yajuya cikin sauri domin fita nemo abun hawan da zai kai su asibitin."

"Kofar gida ya fita cikin sauri, Mujaheed ne ya nufo baba ganin yanda ya taho a kidime cikin nitsuwa Mujaheed ya ce baba lafiya kuwa."

"Babu lafiya dana jikin Mufeedah ce ya tsananta yanzuma abun hawa zan nemo domin kaita asibiti kayi hakuri kaje kawai daga baya ka dawo kugai sa intaji lafiya, cewar baba dakeyiwa Mujaheed baya ni ."

Cikin nitsuwa Mujaheed ya ce subhanallahi Allah ya bata lafiya in ba damuwa baba mezai hana in sauke ku a asibitin naga samun abun hawa zaiyi wahala a layin nan.

"Cikin tashin hankali baba yace haka ne dana , sai dai kar musaka ka dawainiya."

"Dan murmushi Mujaheed yayi yace uhuummm bawani da wainiya baba ai yiwa kaine ciwo yasha gaban komai, Allah dai yabata lafiya da ameen baba ya amsa, yace to barin je in fito da ita."

A shirye yasamu ummah da Mufeedah ummah ta saka mata zumbulelen hijabin ta baba ne yace to BISSIMILLAHn ku muje .

"Ummah ce ta kalleshi tace malam har ansamu abun hawa da sauri haka, cikin hanzari baba yace wlh wannan mutumin ne dan albarka ashe bai tafiba shine yace zai rage mana hanya ."

"Cikin hanzari baba yace kamata muje, zuwa lokacin mufeedah ta gama fita a haiyacinta dan kuwa bakaramin shiganta zazzabin yayi ba har irin sambatun nan takeyi."

"Kofar gida suka fito, Mujaheed ne ya bude musu kofar back sit baba ne ya taimakawa ummah suka saka Mufeedah cikin motar Mujaheed ne ya tsuguna har kasa yana gaida ummah cikin sakin fiska ta amsa masa cikin zuciyar ta tana yabawa da kamalan sa."

"Front sit baba ya zauna, wani irin sassanyan kamshi ne da sanyin AC yake tashi a cikin motar tun da baba yake bai taba shiga mota mai numfashi irin wannan ba, gara gara ummah amma ita ma bata kai wannan ba, ganin komai ya dai dai tane yasa Mujaheed ya tada motar cikin nitsuwa ya shiga tuka su ."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Wani irin hadedden private hospital Mujaheed ya kai su baba, acikin harabar asibitin yayi parking."

"Baba ne ya kalleshi cikin sanyin jiki yace kayi hakuri dannan amma ba wannan asibitin muke zuwa ba, daga ni asibitin kudi ne wannan mukuma na gomnati muke zuwa."

"Mujaheed ne ya sunkuyar da kansa kasa yace ba damuwa baba , bai jira cewar baba ba ya bude kofar ya shiga cikin reception din asibitin bai wani jima ba ya fito tare da nurse's mata guda biyu ."

"Daukan Mufeedah sukayi daura ta akan gadon tura marassa lafiya sukayi zuwa lokacin bata ma san waye akanta ba sai sambatun zazzabi ta keyi, cikin sauri suka shiga turata."

"Su baba da Mujaheed ne suka bisu ba wani bata lokaci aka karbi Mufeedah abunka da private hospital nan dana doctor ya dubata, su baba suna zaune a reception suna jiran doctor."

"Kusan 30min doctor yafito, wajen su baba ya nufa ai da sauri baba ya tashi."

Ganin yanda baba yake rude ne yasa ka doctorn kwantar masa da hankali.

"Bawata matsala ba ce fever ne sai typhoid daya ke damunta da alama ta sha matsanancin kuka ne shi ne ya haifarmata da fever mai tsanani, zaku iya shiga ku ganta an samata drip da sauran allurai, yanzu haka tana bacci zuwa anjima zata farka."

Baba ne ya sauke ajiyar zuciya yace likita mun gode.

Baba da ummah ne suka wuce dakin da aka nuna musu inda Mufeedah take konce.

"Mujaheed ne yabi doctor n office din sa , don yana bukatar karin baya ni, kuma bazai iya tambayar doctor n agaban su baba ba."

"A kwance suka sameta a wani daki mai shegen kyau bazaka ce a cikin hospital dakin yake ba , ummah ce ta zauna a gefen gadon da Mufeedah ta ke kwance ."

"Hannunta ta daura akan goshinta ajiyar zuciya ta sauke jin zazzabin ya fara sauka, kallon baba dake tsaye tayi tace malam kazauna mana jikin nata da sauki, sai a lokacin baba yayi hamdala zama yayi a daya daga cikin kujerun da aka ajiye a dakin domin duba marar lafiya."

"Baba ne ya kalli ummah yace uhuummm Allah da iko yake , wannan yaron dan albarka ne ."

"Ummah ce ta ce uhumm ai na Allah basa karewa, don a waya suka hadu da Mufeedah, nan fa ummah ta labartawa baba komai bata boye masa ba, sai dai bata fada masa kiran da Mufeedah tayiwa Mujaheed har matar sa ta dauka tamata zagin kare dangi ba wanda shine musabbabin ciwon Mufeedah, haka kawai takejin mutumin ya kwanta mata arai, dan taga yana da dattaku kuma gasanin yakamata tunda ba yaro bane ."

Ajiyar zuciya baba ya sauke yace Allah sarki dagani mutumin kirki ne Allah ya saka masa da alkhairii da ameen ummah ta amsa masa .

"Doctor so nakeyi ka karamin bayanin me yake damunta ne, kallon sa doctor yayi nan yashiga yimasa baya ni yanda zai fahimta sosai."

"Sauke ajiyar zuciya Mujaheed yayi jin cewa matsalar ba wata babba bace sai dai akasan zuciyar sa yana tunanin me ya sa Mufeedah kukan da zai hadda sa mata mummunan fever haka, ganin bashi da amsar tambayar sa ne yasa yayiwa doctor sallama yafita daga office din."

"Cikin nitsuwa ya turo kofar dakin bakin sa dauke da sallama, su baba ne suka amsa cike da sakin fiska kan gadon da take kwance ya kallah."

"Tana kwance sambal kamar wanda babu rai ajikin ta bacci takeyi amma dakaga yanayin baccin kasan na wahala ne, a hankali ya janye idanunsa tare da cewa su baba ya mai jikin."

"Cike da fara'a baba da ummah suka amsa da sauki da alama ma har zazzabin yafara sauka, a hankali ya furta alhmdullah Allah ya kara afuwa, da ameen su ka amsa."

"Baba ne ya kalle shi yace duddah ban san waye Kai ba hakika nagode sosai nagode da temakon daka mana, Allah ya jikan magabata."

"Cike da kunya ya amsa da ameen baba, baba ne ya mike ya cewa ummah to zan wuce gida zanje na sanar da zuwaira anka maku a gado inya so daganan sai a hado muku abun da zaku bukata sai inta ho muku da shi, cike da so Ummah ta ce toh malam adawo lafiya, Allah ya sa cewar baba."

"Mujaheed ne ya ce baba muje in maida kai, haba dannan anya bamu saka ka dawainiya da yawa ba kuwa ."

Bakomai baba cewar Mujaheed da ya nufi kofar fita baba ne yabi bayan sa yanata jera masa addu'o i.

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Marwat ta gama cika tayi fammm kamar zata fashe , akan idanun ta Mujaheed ya ci wanka ya fita duk tana kallon sa ta window."

Wani irin bakin cikene ya turnike zuciyar ta ji takeyi kamar numfashinta yazo karshe.

"A yau ta tabbatar namiji ba dan Goyo da zani ba ne ita Mujaheed zaiyiwa haka, wannan shine tukuicin so da kaunar da take masa, lallai yau ya nuna mata matsayin ta a wajen sa tun da ya zabi karuwar sa akanta, wato ita bata ma gabansa shiyasa yaci wanka yatafi wajen karuwar sa sabida ta bata mata rai."

A hankali take jin wani irin tsanar sa na da da mamaye mata zuciya.

Wayar ta ta dauka online ta hau nan fa tashiga yiwa zulaiha typing din abunda ya faru tsakanin ta da Mujaheed.

"Bayan 5 minutes taga zulaiha ta mata reply kamar haka,,"

""" Hmmm dana ai duk wacce ta dauki namiji uba to wlh zata mutu marainiya, waya fadamiki miji goma ai ba uba goma bane, dama na fadamiki watakila karuwa ya ajiye a waje shiya sa yake miki haka ,sai ga shi ayau kin tabbatar, to wlh gara kisan inda dare yamiki, bayan kin cemin kunje asibiti antabbatar da yana dauke da matsalar tsinkewar maniyi amma ai bai hana shi bin matan bariki ba,sai kece zaki kashe zuciyar ki kizauna dashi ba da ba jika ayau in yafadi ya mutu kece da asara, toh ayanzu dai dabara tarage gareki."

Wasu hawayen bakinciki ne suka sauko a kumatunta tabbas maganar zulaiha haka take a yau Mujaheed ya tabbatar mata miji goma ba uba goma bane duk irin sadaukar wa da tamasa amma ya rasa da me zai saka mata sai da bin karuwai a titi.

"Nan tashiga saka da warwara acikin zuciyar ta, tabbas ko da Mujaheed baya so dole tafara fita office sannan kuma ko sha'awar sa zata kashe ta wlh bazata taba yarda ya kusan ce ta babu kariya ba dan bazata taba yarda ya kwaso mata cuta ba, dole ne a yanzu ta koyi jajir cewa ta tsaya da kafafun ta a yanzu bata bukatar neman izinin Mujaheed wajen tafiyar da rayuwar ta ,jitakeyi ta zama mace mai yanci da cin gashin kanta."

"Misalin qarfe 7:30pm na dare Mujaheed ne yayi parking motar sa a kofar gidan su, mai gadine ya leka yana kokarin bude masa kofar, dakatar da shi yayi yace kabari kawai ba jimawa zanyi ba."

"Cikin gidan ya shiga a parlour yasamu Hajiya tana zaune tana kazumin ta, ganin yashigo ya zauna ne ya sata dakata da lazumin."

"Bata cemasa uffan ba sanda tagama nazartar sa, cikin nitsuwa da hikima tace hala baka da lafiya ne Mujaheed."

"Dan Sosa kai yayi yace anyini lafiya hajiya, lafiyan mu qlu baba na dake sunan baban ta yaci shiya sa mafi yawanci take kiran sa da baba na."

"Baka da lafiya ne tasake jeho masa tambayar akaro na biyu, a hanakali yace Hajiya lafiya na kalau kawai dai stress ne na office kwana biyu bana samun zama sosai shi yasa."

"Duddah bawani yadda tayi da bayanin nasa ba cewa tayi toh Allah ya kyauta adai dinga rage aiyukan kasan ance rai dangin goro, ya Marwat tasake jefo masa tambayar da tasa shi tuna wani irin bakin ciki dayake ta kokarin dannewa acikin zuciyar sa."

"Lafiyar ta qlu cewar Mujaheed, hajiya ce ta kwalawa mai aikin ta kira."

"Wata mata ce tafito da sauri , zubewa tayi a kasa tana kwasar gai suwa awajen Mujaheed."

"Hajiya ce tace a kawo masa abinci talatu, da sauri tace to hajiya, tashi tayi domin cika umarnin hajiya."

Talatu ne ta kawo abinci ta jera agaban Mujaheed sanin da tayimasa baya son cin abinci a dinning table shiya sa ta shumfuda masa ledar cin abinci a kasa saving din sa tayi bayan ta kammala ne ta wuce.

"Cikin nitsuwa ya zauna a kasa a hankali ya fara cin abincin da talatu ta jera masa tuwon shinkafa miyar taushe tasha gyada da tantakwashi ga manshanu da aka zuba akai, sabida favorite food dinsa ne yasa yaci abincin sosai bayan ya kammala ne yayi hamdala tissue yadauka ya goge bakinsa."

"Anya kuwa baba na yau kaci abinci ma kuwa cike da kunya yace naci hajiya kawai dai kinsan ina son tuwon shinkafa miyar taushe ne , uhuummm aikuwa kam cewar Hajiya daba wani yarda da maganar sa tayi ba ita ta haifeshi shiya sa take gane duk wani yanayi dayake ciki."

A gogon hannunsa ya duba yaga karfe 9:00pm na dare dan Sosa kai yayi yace uhuummm Hajiya nace ko akoi sauran abincin nan ne asaka min ina son inci dumame gobe ya kara sa maganar cikin inda inda.

Murmushin manya Hajiya tayi tace toh barin sa talatu ta hadamaka.

Kwalawa talatu kira tayi tace maza je ki hadawa baba na abinci a flaks toh hajiya cewar talatu da ta juya da sauri ta nufi kitchen din.

Ganin yayi shiru ne alamar bazai kuma sake cewa komai ba dan sarai ta san halin miskilanci irin na Mujaheed yasa tace kana shan maganin ka kuwa.

"Cikin sanyin jiki yace ehh Hajiya karshen wata ma zan koma asibitin mugana me Allah zaiyi , ajiyar zuciya ta sauke tace to Allah ya sa ada ce da ameen ya amsa."

"Talatu ne ta fito daga cikin kitchen din ta hada masa abincin a cikin wani basket mai shegen kyau da tsada gawasu uban flak ma su kyau data jera aciki, a gaban sa ta ajiye basket din tare da cewa yallaboi anhada abincin cikin taushin Murya yace yauwa talatu nagode, tashi tayi tawuce kitchen din din karasa sauran aiyukan ta."

Tashi yayi yana daukan basket din yace Hajiya zan wuce .

"Toh baba na Allah bamu alkhairii kai gaishemin da Marwat din, zataji yace tare da fita daga parlourn hannunsa dauke da basket din."

"Bude bayan motar yayi ya saka basket din, rufewa yayi ya zagaya mazaunin driver ya shiga dake a waje yayi parking cillah hancin motar sa yayi akan titi, bai tsaya ko ina ba sai bakin wani ShopRite."

"Kayan tea da su drinks ya saya da sauran abun da maras lafiya zai buka ta kai kace wani shagon za a bude bayan ya gamane ya biya kudin komai aka saka masa a mota, wajen ALQASIM SUYA ya tsaya lafiyayyun gashesun kaji ya saya bai tsaya ko ina ba ya dauki hanyar asibiti."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Parking Mujaheed yayi acikin parking space na cikin harabar asibitin yakai kusan 3min kafin ya fito bude back sit yayi ya dauko basket da ledojin shopping din, cikin asibitin ya shiga."

Su baba ne yasamu zaune a kan kujerun da aka jera a bakin ward din.

Cikin nitsuwa da girma mawa ya tsuguna ya gaishe su tare da tambayar me jiki.

Baba ne yace ka isa dakin tana ciki jiki kam alhmdullahi mun gode Allah.

Cikin dakin ya nufa hannunsa dauke da Basket din.

Cikin nitsuwa da Kasai ta daya zama jinin jikin sa ya tura kofar Murya kasa kasa yayi sallama sanin cewa ita kadai ce acikin dakin tunda ya wuce su baba a waje.

"Mufeedah tana kwance a kan gadon sanye take da wani baby pink colour hijab dayayiwa fiskar ta matsanancin kyau ga fiskar ta yi fayau da ita, tun kafin ya shigo hancinta ya ke shakomata wani irin sassanyan kamshin turaren da ajikin mutum daya ta taba jin sa, jin anbude kofar ne yasa ta kallon wajen ganin sa tayi dauke da basket da wasu manyan ledoji, gaban ta ne ya fadi, a hankali ta shiga sauke ajiyar zuciya, tun tashinta ummah ta sanar da ita cewa Mujaheed ne ya kawo su asibitin."

Kamal ne dake zaune a gefe akan kujeran da ke cikin dakin ya amsa sallamar da akayi dan dakin ya kasan ce shiru shiyasa ma yaji sallamar da akayi.

"Wani kamilallen mutum ne mai dauke da korjini ga wani shegen kyau dayake da shi kallo daya kamal ya masa yasan cewa wannan ba karamin mutum bane don a girme ya girme shi nesa ba kusa ba, ga kudi da suka boye ainihin shekarun sa, haka kawai kamal yaji gaban sa ya yanke kauda idanunsa yayi daga kan mutumin da yaga kai tsaye ya nufi gadon da Mufeedah take kwance."

"Basket din hannunsa ya ajiye a gefe tare da ledojin, kallon Kamal yayi tare da mika masa hannu badon ran Kamal ya so ba sai don korjini dayaga mutumin ya masa haka yamika masa hannu suka yi musabaha, Mujaheed ne yace ya me jiki dan azaton sa Yayan Mufeedah ne."

"Cikin dakiya Kamal yace da sauki alhmdullah ta samu bacci ne, dan shi haka kawai yaji Mujaheed bai biya masa a rai ba."

Mujaheed ne ya zubawa Mufeedah dake kwance ido ganin idanun ta suna dan motsi ne ya tabbatar masa da cewa ba bacci takeyi ba likimo tayi.

Cikin nitsuwa da izza ya dan matsa kusa da gadon a koi dan space a bakin gadon hakan ne yasa

Please Login or Register in order to submit comment