Reading SIRRIN YA'MACE COMPLT BY MRS ALKALI Chapter 14 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waje daya ne dan tunda suka shirya da Mujaheed ta daina fita office."

"Kallon Mujaheed tayi tace kun dawo lafiya ya mai jikin cike da farin ciki ya ce jiki alhmdullah, ashe juna biyu ne da Mufeedah, cike da murna Marwat ta ce Masha Allahu, congratulations Allah ya inganta ya sauke ta lafiya, da ameen Mujaheed ya amsa dan yaji dadin addu'an da Marwat ta masa."

"A hankali ya zauna a gefen ta dan rungumar ta yayi cike da kulawa ya ce ina addu'a Allah ya albarka ce ni da samun zuri'a ta tsatson ki, hawaye ne suka shiga sau ko mata a hankali Mujaheed ya shiga goge mata su, cike da raunin Murya Marwat ta ce ameen Zauji nah nima ina son inga na haihu da kai mucigaba da addu'a Insha Allahu Allah maji rikon bawa ne , murmushin karfin hali tayi tace finally dai Jaheed zai zama father dariya sukayi gaba dayan su."

"Mujaheed da kan sa ya sanar wa dasu Hajiya da Yaya Aisha duk dangi ba wanda baisan Mufeedah tana da juna biyu ba murna kuwa ba a cewa komai don Mujaheed har kyautar kujeran makkha ya raba wa dangi, ciki kuwa har da iyayen Mufeedah ya bawa baba da ummah sai baba zuwaira rannan ba irin kukan da baba zuwaira batayi ba sai neman gafarar su ummah takeyi, Mufeedah kuma yace sai ta haihu zataje."

"Tun da cikin Mufeedah ya baiyana sai laulayi yasako ta a gaba bata iya cin duk wani abu da zata girka, ganin haka ne yasa Marwat ta karba girkin ita take musu komai da kanta ta ke kaiwa Mufeedah abincin watara suci tare, a hankali Marwat tafara sakewa da Mufeedah ganin yarinyar bata da matsala tana bata girman ta, kusan yanzu a part din Mufeedah take wuni dan bakaramin gara ta cikin yakeyi ba duk tabi ta fita daga haiyyacin ta, yanda Marwat ta sauko take kula da Mufeedah hakan bakaramin dadi yayi wa Mujaheed ba Wani irin matsayi yasake bawa Marwat acikin zuciyar sa yana ganin kima da darajar ta."

"Mujaheed ne ya ke konce Marwat na rungume ajikin sa, sungama making love habeebty nah wlh kin chanza gaba daya ke baki gani ba ne kin danyi kiba ga shi fatarki ta kara yin fresh kuma dandanon ki ya chanza gawani ruwan ni'ima na musamman da yake gigita kwakwalwata, me sirrin ne kam, dariya Marwat tayi tace Kai Zauji nah banda tsokana mana bawani sirri kawai dai santi kakeyi dariya sukayi gaba dayan su."

"Haka rayuwa ya cigaba da kasan cewa alhmdullah hankalin Mujaheed ya kwanta dan a yanzu bayi da matsala da matan shi , Marwat tana kokari wajen ganin an zauna lafiya a gidan haka itama Mufeedah tana kiyayewa, su baba sunje makkha sun sauke farali, har sun dawo , Mufeedah da Marwat sunje sun marabce su a sabon gidan da Mujaheed ya saya musu, hakan bakaramin dadi yayi wa su ummah ba ganin babu wata matsala a tsakanin su haka sukayi ta nunawa Marwat kauna kamar ita suka haifa."

"Cikin Mufeedah na da wata takwas , yau daren litinin misalin qarfe 1 30pm na dare Mujaheed yana kwance a dakin Marwat daomin kuwa kwanan ta ne, Wani irin matsanancin ciwon mara ne ya tada ta, tun tana daurewa har ta gagara Mujaheed ne yata shi ganin halin da Marwat ta ke ciki ne yasa hankalin sa tashi duddah in wata ya zo karshe tana yin ciwon mara amma ya tsorata da wannan, ganin abun yana cigaba ne yasa ya dauke ta ya"

"saka a mota , private hospital ya kai ta cikin gaggawa suka shiga emergency da ita dan daman anan take ganin likita idan ciwon maran ya tasar mata, cikin kankanin lokaci suka rufu akanta domin bata agajin gaggawa."

"Ganin ta na Wani irin nishi da bankarewa ne yasa doctor yace anya ba haihuwa ba ce kuwa , nurse din ce ta ce kuma mijin ta yace ciwon al'adana kasan tasaba yinsa duk wata ,kuma da alama bata da wani shigan ciki, doctor ne ya bude cikin ta dan danna maran yayi yaji da tauri gawani malalacin kara da ta sake kallon nurse din yayi yace wannan haihu wa ce , ai bai karasa maganarba sukaji kukan baby inyeeh inyeeh, da sauri nurse din tasa hannunta ta dauki babyn tana kokarin yanke cibiya sai ga wani sabon nishin kafin kace me Wani babyn ya fado, haka suka yanke cibiyan suka jara Marwat tsaff tare da jariren ta guda biyu daya mace daya na miji, dake ba su san da haihuwar ba acikin zani kawai aka sanya su, wani daki mai kyau na musamman a ka kai Marwat tare da babies dinta, bacci takeyi dan anmata allurai ."

"Mujaheed ne yake ta sintiri abakin emergency doctor ne ya fito yace BISSIMILLAH alhaji zaka iya ganin ta duddah ma tana bacci, da sauri Mujaheed yabi bayan doctor duk hankalin sa atashe, dakin da Marwat ta ke konce ya shiga, ganin ta tana sharan bacci ne yasa ya sauke ajiyar zuciya doctor ne ya mika masa hannu yace congratulations ansamu twins boy and girl duk suna cikin kishin lafiya Mujaheed bai gane me doctor yake nufiba san da yasake nanata masa, da sauri Mujaheed ya nufi inda doctor ya nuna masa bude zanin daya gani a lullube yayi, ya Allah wasu cute babies yagani sun mannu da juna, ai baisan sanda ya saka hannun sa ya shiga taba fiskar su ba, wasu irin hawayen farin ciki ne ya suka shiga zubo masa bakin sa na rawa yace doctor how is this happen, tayaya yaushe Marwat ta samu ciki kodai mafarki nakeyi ne , doctor ne ya dafa kafa darsa yace ba mafarki bane alhaji ana iya samun haka May be cikin yabi jikin ta ne kuma bata da laulayi nan doctor yashiga masa bayanin wasu matan hakan na iya kasan cewa da su batare da sun saniba don duk karshen wata suna period, Mujaheed ya gamsu da bayanin doctor, bai san san da ya zube yana yiwa Allah sujjada ba sai kirari yake jero masa ."

"Zuwa wayewar gari asibitin yacika makill da Yan uwa da abokan arziki kowa mamaki yakeyi yaushe Marwat ta samu cikin sai gashi cikin ikon Allah ta riga Mufeedah ma haihuwa, murna awajen hajiya da iyayen Marwat ba a magana, bare kuma uban gayyan, Mufeedah ma ba a barta a baya ba itama a asibitin ta wuni duddah tayi nauyi haka ta wuni tana rike da babies din kyawa kamar uban su yayi kakiya tofar dake identical twins ne, don harcikin ranta takejin son yaran, ai dolene ma taso Jinin Mujaheed, yagama mata komai a rayuwar ta ba a bunda zata ce da Allah sai godiya."

"Mujaheed ne yabawa doctor kyautar kujeran makkha sannan yace yaje company ya zabi motar da yake so, sannan duk wani mara lafiya za a basa magani kyau ta zuwa karshen wata, bakaramin murna doctor yayi ba , shikam yaga farar haihuwa, haka a ka sallame Marwat suka koma gida ita da yaranta, hajiya ce ta zauna da ita, iyayen Mufeedah ma sunzo sun mata barka bakaramin dadi hakan yamata ba."

"Ranar suna yara suka ci sunan hajiya da mahaifin Mujaheed wato Mas'oud amma ana cemusu mubeen da mubeenah, haka suka cigaba da renon yaran su cike da kulawa, bayan haihuwar Marwat da wata daya, Mufeedah ma ta tashi da nakuda, kafin ace za aje asibiti ma ta haihu a gida, ta samu babyn ta kato, zo kaga murna awajen familyn ,shidai Mujaheed ba abunda zai ce da Allah sai godiya, ranar suna yaro yaci sunan mahaifin Mufeedah wato Muniru amma ana ce masa ""abeey""."

"Haka masu jego suka gama wankan su lafiya kalau, suna zaune lafiya kalau sun hada kansu suna kula da mijin su da Yayan su, inkaga yanda suke kula da yaran bazaka iya banbance yaran ba dan zaka ce ma triplets ne, Mujaheed hankalin sa ya kwanta harwani kiba yayi, rayuwa tayi albarka sai dai yace alhmdullah."

"Mujaheed ne suke zaune a main parlour yana zaune akan sofa Marwat da Mufeedah sun saka shi a tsakiya yaran sune suke wasa a tsakiyar parlourn kayan wasa ne ta ko ina yanzu twins suna da 4 months yayin da abeey yake da 3month , suna zama yanzu sai dan kiri niya na yara, Mujaheed ne ya kalle su fiskar sa dauke da murmushi yace alhmdullah Allah ya karawa rayuwa albarka ina son ku iyali na yan da Allah ya hadamu anan duniya ina rokon Allah da ya hada fiskokin mu acikin aljanatul Firdausi da ameen su ka amsa suna murmushi."

Akarshe dai Mujaheed yagane bawai kungiyar SIRRIN YA'MACE ce matsalar ba niyar mai amfani da ita ce komai.

ALHMDULLAH! ALHMDULLAH!! ALHMDULLAH!!!

END

ANAN NAKAWO KARSHEN WANNAN LITTAFIN NAWA MAI SUNA SIRRIN YA'MACE KUSKUREN DANAYI ACIKI ALLAH YA YAFE MINI ALLAH YA SA MU AMFANA DA SAKON DA LITTAFIN YA KE DAUKE DA SHI.

"MASOYANA INA MATUKAR GODIYA A GAREKU, ALKHAIRIIN ALLAH YA KAI MUKU A DUK INDA KUKE , NAGODE DA ADDU'OIN KU AGARENI ALLAH YA HADA FISKOKIN MU A CIKIN ALJANNAH INA MATUKAR ALFAHARI DA KU SON SO NAKE MUKU."

"SAI MUN HADU A SABON BOOK DINA MAI SUNA BAZAWARA BAZANCE MUKU KOMAI BA DON WANNAN KARON SALON NA DABAN NE HAKAMA TAFIYAR TA MUSAMMAN CE TA BANBANTA DA WANDA KUKA SABA GANI, KAI DAGAJIN SUNAN KUNSAN NA MUSAMMAN NE NIKAI NA NA KOSA INGA MUNFARA POSTING DIN LITTAFIN KARKUBARI ABAKU LABARI, KUDAI KU NUNA MIN KAUNA KAMAR YANDA KUKA NUNAMIN A WANNAN LITTAFIN."

KARKUMANTA.....

MRS ALKALI CE

ALKALAMI YAFI TAKOBI


Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment