Reading SIRRIN YA'MACE COMPLT BY MRS ALKALI Chapter 10 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yakeji a kasar zuciyan sa yarasa me yake damun sa, sunkuyar da kansa kasa yayi yace baba in ba damuwa ni zan auri Mufeedah."

"Kamar baba bai ji me Mujaheed ya fada ba da alama ko dai kunnuwan sa ne sukamasa karya cikin hardewar harce yace alhaji me kace, Mujaheed ne yasake kasa da kai yace baba ni zan auri Mufeedah in ba damuwa."

"Wani irin sanyi baba yaji har cikin ransa yace indai ka amince zaka auri Mufeedah ni malam Muniru nabaka auren ta halak malak, cike da jin nauyi Mujaheed ya ce na gode baba, a'a alhaji nine da godiya yanda ka fitar dani kunya kaima Allah ya hana ka jin kunyan duniya da lahira, Allah ya kara rufamaka asiri Allah ya jikan magabata, Allah ya sanya albarka a cikin auren ku ,a hankali Mujaheed ya amsa da ameen, akasan zuciyar sa yanajin kamar wani nauyi yana raguwa masa."

Cikin masallacin suka nufa nan fa baba ya wuce wajen limamin ya sanar dashi sunan angon da za a daura auren da shi .

"Mujaheed ne ya kalli Imam ya sa hannun sa a aljihun wondon sa bunch na 1k yaci ro masu yawa ya mikawa Imam, karba Imam yayi yana kallon sa alamar ya haka, a hankali Mujaheed ya ce sadakin aure ne ka matsa wajen baba ka karbamin auren Mufeedah ya kara sa maganar cike da wani irin damuwa."

Ganin irin yanayin da Mujaheed ya ke cikine yasa Imam baija zancen ba amma mamaki yakeyi to me ya faru haka ya akayi abun ya sauya bayan ajikin invitation card din sunan angon kamal bare ace soyayyah sukeyi da Mujaheed dole akoi wani abu a kasa ruwa baya tsami banza.

"Imam ne ya matsa kusa da su baba nanfa akashiga daurin auren da yabawa dubbannin jama'a mamaki kusan wadanda sukasan cewa kamal ne angon ba karamin mamakin jin ansauya sunan angon sukayi ba, nan fa yan kananan magana suka fara tashi acikin masallacin."

"Sunkuyar da kansa kasa Mujaheed yayi hada kansa yayi da guiwowin sa wani irin sanyi me hade da zazzabi zazzabi yakeji, alhmdullah aure ya dauru a tsakanin alhaji Mujaheed Mas'oud Raji da Mufeedah Muniru akan sadaki 2 million lakadan ba ajalan ba Allah ya basu zaman lafiya ameen, haka Mujaheed yaji saukan muryar mai shela tabugi cikin dodon kunnen sa."

Bayan angama daurin auren ne yan'uwa da abokan arziki aka shiga gaisawa da baba ana masa barka kowa da magana a bakin sa amma babu damar furtawa haka akayi ta gaisawa wassu kuma suna tafiya.

Bayan wani lokaci masallacin ya rage chunkoso domin mafi yawancin mutanen sun watse sabida angama daura aurarrakin.

"Imam ne ya matso kusa da Mujaheed dake sunkuye da kan sa yace kaga babban ango yadan bugi kafadarsa , a hankali Mujaheed ya dago jansa da yakejin yamasa nauyi sosai ya zubawa Imam ido cikin sanyin murya yace kaini gida kaina ne yake ciwo ganin da gaske yakeyi ne yasa Imam dena wasan ya karbi key din motar Mujaheed din dan dama da ita su ka zo."

"Fitowa harabar masallacin sukayi baba ne suka hango yana bankwana da malam liman, ganin sun fito ne yasa baba yin sallama da malam liman ya nufo su shi dai haka kawai yakejin Mujaheed harcikin ransa ashe da rabon ya fitar da shi cikin kunya ne Allah mai iko kenan."

"Sake gaisawa da baba sukayi Imam ne yamasa Allah sanya alkhairii kallon yanayin Mujaheed baba yayi yace lafiya kuwa, Imam ne yace dama yana fama da dan zazzabi tunjiya to jikin ne ya dan matsamasa shine zan kai shi gida."

"Subhanallahi cewar baba to Allah ya kara afuwa nagode maka Mujaheed Allah ya baka lafiya da ameen suka amsa , Imam ne yace wa baba zuwa anjima zasu shigo gidan domin gaishe da su ummah sannan suna son ayi maganar tarewa, baba ne yace ba komai wannan kam ai anyi mai wuyar Allah dai yaba shi lafiya, haka Mujaheed ya shiga motar gefe mai zaman banza sit din Motar ya kwantar , jingina bayan sa yayi ajikin sit din lumshe idanunsa yayi don ji yakeyi kamar kansa zai rabe biyu, gawani bakon al amari dayake ji acikin zuciyar sa dake bugawa a hankali, ba wanda yayi magana a tsakanin shi da imam duk yan da imam yaso ya tambaye sa abunda yake faruwa haka ya hakura ganin da gaske jikin Mujaheed din babu dadi, haka Imam yaja motar suka wuce gidan Mujaheed din."

SIRRIN YA'MACE

"Tun da Mujaheed ya koma gida baibi ta kan Marwat ba bedroom din sa ya wuce maganin zazzabi kawai ya sha ya konta , zuciyar sa ce ta ke bugawa da karfi, baijima da konciya ba bacci mai nauyi ya dauke sa."

Gidan su Mufeedah acike yake da mutanen biki sai kai da komowa aketayi biki ya kankama dangin ummah na maiduguri sun zo su.

"Baba zuwaira ce take ta tauna chewingam dinta har wani kass kass takeyi da shi kallon ummah tayi dake ta maraba da baki tayi tace uhuummm ayi dai mugani in tusa zata hura wuta, sai wani rawan kafa akeyi sai kace wani attajiri zata aura, ko dayake malamin makarantar ma bamu tabbatar ba, sai mun agaida daurin auren."

"Duddah ummah bata kulata ba Amma maganganun baba zuwaira sun daki zuciyar ta, Amma haka tashare tacigaba da karbar bakin ta."

"Mufeedah ce zaune a cikin dakin ummah tare da yan'uwan ta wanda suka zo daga maiduguri, sanye take da wani hadedden farin leshi da yayar ummah ta dinka mata tundaga maiduguri, kana ganin ta kaga amarya hannayenta sun sha jan lalle dan taki azana mata baki acewar ta ai fatarta tana da duhu shiyasa tafi son bakin lallen."

"Tsokanan ta sukeyi Amarya ansha kanshi warhaka dai andaura auren ku finally dai yau kinzama mrs kamal, Wani irin bugawa zuciyar Mufeedah ta yi jin abun da kawayen ta suke fada, shikenan yanzu tazama matar Kamal, duddah tana son kamal Amma haka kawai takejin wani abu akasan zuciyar ta maikama da kunci, wayar ummah ta dauka ta kira numbern kamal, amma akashe taji wayar sake train din numbern tayi yanzuma still a kashe, sauke ajiyar zuciya ta yi May be yana cikin hidima ne shiyasa yakashe wayar."

Agidan su kamal kuma alhaji garba be yake zaune da mahaifiyar kamal ga Kamal agefe ya sunkuyar da kansa kasa.

Yanzu ke zainabu me hujjarki nafasa wannan auren da kikace kar a daura cewar alhaji garba daya kafe mahaifiyar kamal da idanu don ba karamin haushin fasa auren yajiba.

"Mahaifiyar kamal ce tace Yaya kayi hakuri nima abun ya zama dole ne shiya sa baba zuwaira ce tazo gidan nan jiya da dare ita ce ta sanar mana cewa Mufeedah karuwa ce don akoi Wani alhaji dayake zuwa wajenta kuma su kawu muniru su na sane dan shi yake musu dawainiya da gidan, sannan har kudi ya bawa kawu muniru naira million 1 da sunan gudun mawa."

"Kamal ne ya dago kansa cike da damuwa da bacin rai yace kuma ni da idanuna nasha ganin sa a gidan kuma har asibiti da ta konta shi ya musu dawainiyar komai, amma kawu yace min bawani abu a tsakanin su kuma agaban idona Mufeedah ta ke nuna masa soyayyah gaskiya bazan iya auren Mufeedah a haka ba gara taje taci gaba da karuwan cin ta da shi kawai, mahaifiyar kamal ce tace amma dai wlh Mufeedah ta ji kunya in ka ganta kamar ta Allah ashe makira ce ta karshe."

Alhaji garba ne yace amma zainabu kin bani mamaki akan dan wannan abun ne yasa zaki biyewa kamal kuce afasa wannan auren .

Ya za'ayi kuyanke hukunci batare da kunyi bincike ba.

Wani bincike Kuma Yaya bayan zuwaira ce da kanta tazo tafadamana sannan shi Kamal da kansa ya tabbatar mini da hakan.

"Wannan ba hujja bace Zainab yanzu tashi zakuyi muje gidan su yarinyan gara aje ayi maganar agaban iyayen ta kinga in matsalar me jaruwa ce sai a daura auren acigaba da hidiman biki, badon umman Kamal ta so ba sai don ba ta isa ta musa alhaji garba ba yasa ta dauko hijabinta tabi bayansa ita da kamal da yakejin kan sa kamar zai fashe, ga wani zogi da yakeji acikin zuciyar sa."

"Baba ne da ummah zau ne a turakan baba na zaure, gefe guda kuma alhaji garba ne zaune ga umman Kamal a gefen sa ga kamal zaune a kasa ya sunkuyar da kansa , Mufeedah ce take zaune a kasa kusa da kafafun ummah ga baba zuwaira a zaune sai faman zare ido takeyi kamar kace mata chass ta arce a guje, wani irin bugawa zuciyar ta takeyi kallo daya zaka mata kasan ba tacikin konciyar hankalin ta."

"Alhaji garba ne yace kamar yanda na sanar da kai malam Muniru munzo ne akan batun auren yarannan da aka samu matsala , shiya sa muka zo domin a samu a warware matsalar."

Alhaji garba ne ya kalli umman Kamal yace ke Zainabu fada mana abun da yafaru da ya saka kukace adakatar da daurin auren yarannan.

"Sunkuyar da kai tayi tafara koro bayani tiryan tiryan duk abun da baba zuwaira ta fadamata sanda tafada musu, dukan su ba karamin razana sukayi ba dajin zancen umman Kamal."

"Ciki kunar zuciya baba ya kalli kamal yace haba kamalu ai aganina koda Mufeedah karuwa ce kai me rufa mata asiri sosai ne bare kuma zancen ba haka yake ba, amma ba komai aikin gama yariga da yagama Allah yayi hukuncin sa, watakila sabi da bakai ne mijin da Allah ya zabawa Mufeedah bane shiya sa hakan ta faru dan ayanzu Mufeedah andaura mata aure."

Ai ba ummah ba duka mutanen dakin sanda suka girgiza dajin magar baba ya dan ko su ummah basu san me ya faru ba dan baba bai samu damar sanar da ummah abunda ya faruba sai ga su alhaji garba.

"Baba zuwaira ce ta tashi tsaye tare da dafa kirjinta tace nashiga uku ni zuwaira yan zu duk wannan abun da ya farun sai da malam ya daura mata aure, baba ne ya kalleta cike da takaicin ta yace ba haka kika so ba ko to ta Allah batakiba, bazab sakekiba amma kisani Allah bazai barki ba dan wannan kazafi kikayiwa Mufeedah gaki ga duniyar tunda ita kika zaba, kina zaton bansan duk abun da kikeyi bane to rass nake kallon ki kinci albarkacin yan'uwan taka ne daba haka ba wlh baki isa kicigaba da zama agidan nan ba, yanzuma nabarki ki zauna zaman yayan kine kawai."

"Ummah kam bata iya furta komai ba lallai duk wanda malam ya aura wa Mufeedah ta san mutumin kirki ne malam bazai taba cutar da Mufeedah ba, kuma batayi mamakin abun da baba zuwaira tayi ba dan tasan ta zata iya yin fiyema da hakan."

"Cike da sanyin jiki alhaji garba ya tashi ya kalli su Kamal yace toh kunga ikon Allah ko matar mutum kabarin sa , Allah ya nufa ba matar Kamal ba ce dan haka sai kuta shi mutafi ai."

"Cike da sanyin jiki umman Kamal ta tashi, Kamal kam ya gagra tashi wani irin hajijiya ne yake iban shi, ganin bayida niyan tashi ne yasa alhaji garba ya zo ya dagashi yare da ingiza keyarsa waje suka musu sallama suka tafi."

"Baba zuwaira ma zamewa tayi ta nufi dakin ta, dake ayanzu mutanen bikin sun ragu sabi da dama wuni daya ne bikin inji yan garinmu kuma jollof, dan an watse sai dangin ummah ne da suka rage suma kuma zuwa gobe zasu wuce ,mutane angama tafiya da gulman cewa amarya ba ta tare ba wasu suna cewa ai auren dangi ne shiya sa May be akoi abunda ba akarasaba haka dai mutane sukayi ta mitar su har suka watse azaton su da kamal aka daura auren."

"Cikin dakin ya rage daga baba sai ummah da Mufeedah da takasa tantance me kunnuwan ta sukajima ta , tana zaune sai kace wata mutum mutumi, duddah tasan baba bazai mata zabin da zai cutar da ita ba amma tana cikin wani irin yanayi da damuwa yanzu duk soyayyah da tsara rayuwar su da sukayi da Kamal ya tashi a banza fa kenan tunda bashi ta aura ba, batasan lokacin da wasu hawaye masu zafi suka shiga saukomata ba."

"Baba ne yafara jaran murya nana yafara mata nasiha akan yarda da kaddara sannan duk wani bawa baya wuce kaddarar sa, haka kuma wani baya auren matar wani kamar yanda wata bata auren mijin wata,bayani yashiga musu ta yadda akasamu sauyin auren inda ya sanar musu da cewa Mujaheed ne ya auri Mufeedah."

Ba Mufeedah ba hatta ummah san da abun ya girgizata domin muwa taji saukar maganan a bazata ne chap in kuwa haka ne akoi aiki ja agabanta dan bata manta da irin iban albarka da matar Mujaheed tayiwa Mufeedah ba.

"Mufeedah kam ji tayi kamar baba ya kwadamata guduma a zuciya ne dan abunda bata taba tsammanin sa bane, tsananta kukan ta tayi ganin hakane yasa baba yacigaba da mata nasiha mai ratsa zuciya da nuna mata cewa tabi mijin ta tayimasa biyaiya domin kuwa shine aljannahr ta,san da baba ya tabbatar da hankalin ta ya dan kwanta sannan yacewa ummah ta dauke ta su tafi."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

Bacci sosai Mujaheed yayi sai kusan bayan la'asar ya tashi.

"Zazzabin ya sauka sabo da dana stress da damuwa ne suka masa yawa, tashi yayi ya shiga bathroom din sa wanka yayi tare da dauro alwala."

"Sallolin da su ka wuce shi ya rama bayan ya idar ne ya shirya kan sa acikin wata dakekkiyar shaddah light blue jamfa ne da wondo babu babban riga hulan da zai hau da kayan ya saka tare da agogon sa mai shegen tsada , turaren sa mai sassanyan kamshi ya shiga fesawa, kallon kansa yayi ajikin mirror, Wani cute smile ya dan sake tunowa da wani abu dayayi acikin zuciyar sa, shi kan sa yasan ba karamin kyau yayi ba, key din motar sa ya dauka ya sauka kasa, a main parlour yasamu Marwat tana zaune a kan sofa ta daura kafa daya kan daya tana ta taunar chewingam remote din TV ne a hannun ta ."

"Tunkafin Mujaheed ya karaso kamshin turaren sa ya sanar da ita fitowar sa, kafarta tafara kadawa tare da kara kaimi wajen tauna chewingam dinta."

"Ko inda take Mujaheed bai kallah ba dan a halin yanzu yagaji da halin Marwat zaman doya da manja kawai sukeyi dan bawani hakkin sa na aure da take sauke masa, shikuma ya kawo idanu ya zuba mata yana son yaga iya gudun ruwanta."

"Ganin yayi banza da ita ne kamar baigan ta ba yana shirin fita Marwat ta ce uhumm haka dai aka iya ayiwa ka a tafi wajen matan banza a haka sai kace mutumin arziki, ni dai Allah ya isa ban yafe ba wlh."

"Duk maganganun da Marwat ta fada yaji su sai dai bayi da lokacin tamka ta , a halin yanzu ma yunwa yakeji gidan Hajiya zai je yaci abinci."

Wajen Motar sa ya nufa shiga yayi security ne ya bude masa gate.

"Zaune yake a parlourn hajiya abincin da talatu ta kawo masa yakeci cike da nitsuwa, hajiya ce ta zuba masa ido tana karantar yanayin sa tabbas Mujaheed yana cikin damuwa sai dai tasan shi da shegen zurfin ciki, amma ba komai zata cigaba da masa addu'a Allah ya shiga lamuran sa."

Bayan Mujaheed ya kammala cin abincin ne ya dan kalli hajiya yace dama hajiya akoi maganar danake so in fadamiki.

"Hajiya ce ta kalleshi tace ina jinka baba na Allah dai yasa lafiya, sunkuyar da kansa kasa yayi yana jin nauyin fada mata abunda zaifito daga bakin sa sai yanzu yake ganin rashin dacewar abunda ya aikata, shima bai san me ya shiga jikin sa ba yasa ya ce zai auri yarinyar nan ba."

"Hajiya ce tace kai nake sauraro , ahankali ya ce Hajiya namiki laifi ki gafar ce ni."

"Gaban Hajiya ne ya fadi Jin abun da Mujaheed ya ke fada , Hajiya kiyi haku, na kara aure batare da nafa damiki ba ."

Kamar daga sama hajiya taji saukar kalamansa dan ba ta taba tsammanin abunda Mujaheed zai fada ba kenan.

"Kamar yaya Mujaheed ka kara aure, yaushe kayi auren ban sani ba."

Cike da kunya Mujaheed ya shiga labarta wa hajiya abun da yafaru hatta yanda akayi ya hadu da Mufeedah ta dalilin Marwat da group din SIRRIN YA'MACE san da ya fadawa hajiya.

"Hajiya ce ta sauke ajiyar zuciya, ta kalleshi tace bakamin laifi ba baba na haka Allah ya tsara maka, kasan matar mutum kabarin sa akoi wani hikima da Allah ya boye acikin wannan auren naku ina addu'a Allah ya baku zaman lafiya Insha Allahu wannan auren shi zai zama silar zaman lafiyar ka da kawo karshen matsalolin ka."

"Sai dai kasani sai ka kara hakuri da Marwat sabida ka mata laifi duk wata mace da akayiwa irin wannan abun bazata ji dadiba dan haka sai ka sake yin hakuri sannan kayi kokarin fahimtar da ita, fatana Allah ya sa tagane kuskurenta ta gyara."

"Wani irin ajiyar zuciya Mujaheed ya sauke jin abun yazo masa da sauki duddah yasan hajiya bata da wani matsala, amma yasan bai kyauta ba."

Hajiya ce tace to ya maganar tariyan nata duddah abun yazo a kurerren lokaci yakamata ace andan yi jare jare.

Mujaheed ne ya ce innafita zanyi magana da Imam.

"Toh shikenan hakan ma yayi sai ka kira yayar ka kafadamata da kanka, dan murmushi Mujaheed yayi tunowa da anty Aisha, dayayi ba karamin so yake yimata ba sabi da ita kadai ce yar uwar da ya mallaka a duniya kallon hajiya yayi yadan shafa kan sa yace toh hajiya za ayi hakan Insha Allahu."

Misalin qarfe 8 00pm Imam ne yakira wayar Mujaheed.

""" Wai ina kashiga ne kam nazo gidan ka ban same ka ba cewar Imam"""

"""Mujaheed ne ya lumshe idanunsa yace ina gidan Hajiya,,"

"""Ok to on My Way """

Baijira cewar Mujaheed din ba yakatse kiran.

"After 10minutes Imam ne yayi sallama a parlourn Hajiya amsa masa tayi bayan ya shiga sun gaisa ne , hajiya tace haba imamu idon ka kenan rabon da nasaka ka a cikin idona ai har na manta."

Dan sunkuyar da kai imam yayi yace Hajiya ayi hakuri sha'anin aikine amma za'a jara insha Allahu.

"Toh shikenan Allah ya sa, ameen cewar Imam."

Nan fa hajiya tashiga yi musu nasiha mai ratsa zuciya.

Imam ne ya tashi yace Hajiya zan wuce dama naje gida duba jikin sa ne sai akacemin yana nan.

"To imamu angode agaida mutanen gidan, zasuji Insha Allahu."

"Mujaheed ne yatashi shima yace Hajiya nima zan wuce to Allah tashe mu lafiya, wucewa sukayi tare."

Bayan fitan su ne Imam ya kalli Mujaheed Wani irin dariyar iskanci ya fara yace ango kasha kamshi kai kaga wani glowing da kakeyi kuwa tun kafin kashiga daga ciki kai mutumina kace ka tsinci dami a kale.

Mujaheed ne ya harare shi yace kaima ya kamata ka kara auren nan kasan ance mai mata daya aminin gwauro.

Chap wane ni ai gara kai nikam gara na cigaba da lallabawa da dayan uhumm wai ma kafadawa Marwat kuwa.

Shiru Mujaheed ya yi dan shima har ga Allah yana fargaban sanar mata dama gashi suna da issue yanzu kuma yakawo mata maganar auren nan ai yasan ba karamar matsala za'a samuba.

Cikin sanyin jiki yace bata sani ba har yanzu amma in nakoma zan fada mata.

Imam ne ya ce kai mutumina ammafa kataro Mach Allah dai yasa kana da yan'wasa masu bugawa.

Dariya Mujaheed yayi yace anfada maka kowa matsoraci ne irin ka.

Uhuummm kai ma zakayi bayani ne agaban Marwat yanda take bala'in son ka dinnan bana tunanin zata dauki maganar da sauki kafa san mata da kishi.

Mujaheed ne ya bude motar sa Imam ne ya kalleshi yace yanzu ina zaka je .

"Cikin gajiya Mujaheed yace gidana, Imam ne yace a'a wlh baka isa ba kasan dai a al'ada yakamata kaje gidan su yarinyar nan dazu bayan daurin aure amma anmaka uzuri sabida rashin lafiya amma yanzu kam bawani uzurin da zai hanaka zuwa, kuma kasani yanzu matar kace itama tana da hakki a wuyan ka so that zabi ya rage gareka kayi adalci ka rabauta ranar tashin alkiyama ko kuma ka tashi da shanyenyen barin jiki ."

Toh malam imamu yaushe kuma kafara wa'azi ban sani ba cewar Mujaheed da yake dariyar maganar imam.

"Ah toh gaskiya ne ai nake fada maka, yanzu abun da za'ayi muwuce tare inyaso sai inbi in ajiye mota ta agida sai muwuce da taka in maka rakiya kasan ya kamata yau inga amaryan mu."

Mujaheed ne ya harare shi yace magulmaci kawai.

Kajimin mutumi daga abun arziki to kai da haka kake nufin ba za'a maka rakiya ba dan baka da kunya.

Zaka wuce muje ne ko dai zaka tsaya surutu cewar Mujaheed daya ke kokarin rufe murfin motar sa.

"Haka imam ya shiga tasa motar yajata , Mujaheed na biye dashi a baya gidan imam sukaje ya ajiye motar sa daganan suka wuce gidan su Mufeedah tare."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

Parking din motar sukayi a kofar gidan su Mufeedah duddah dare yayi hakan bai hana hasken NEPA haska kofar gidan ba.

"Su baba ne suke zaune a kofar gida suna hira, ganin mota ta yi parking ne ya sa sauran mutanen wajen suka maida hankalin su wajen ganin wata galleliyar mota ta tsaya a kofar gidan malam Muniru."

"Su Mujaheed ne suka fito acikin Motar wajen da sukaga su baba na zaune suka nufa, sallama suka musu har kasa suka tsuguna suka gaishe da su baba, mutanen wajen sai mamaki sukeyi wannan alhajin kuma wajen waye yazo haka, muryan baba ne ta katse su inda yake tambayar Mujaheed ya jikin nasa."

Cike da girmamawa Mujaheed yace da sauki baba alhmdullahi.

"Toh masha Allahu haka ake so cewar baba da yata shi yana cemusu ku iso cikin gidan, bin bayan sa sukayi."

Da sallama su ka shiga cikin gidan baba zuwaira ce a tsakar gidan tana zaune tare da yaran ta .

"Baba ne yace BISSIMILLAH nku ku karaso ciki baba zuwaira ce ta ce malam baki mukayi ne, duddah baba yana fishi da ita hakan bai hanashi amsa mata ba yace ."

"Mijin Mufeedah ne yazo, ai wani irin rass baba zuwaira taji kanta ya saramata me zatagani haka in ba gezo idanunta sukemata ba ai wannan alhajin da ya kai su asibiti ne rannan, wato da malam ya ce an daurawa Mufeedah aure da alhaji yake nufi shine bai fadamata ba, kaichon ta da tasan haka zata kasan ce reshe zai juya da mujiya da bata je gidan su Kamal ba ai wannan shi ake kira gobarar titi a jos, yanzu tana ji tana gani Mufeedah ta zama matar alhaji kenan ina wlh bazaiyiwu ba dole ne ma ta tashi tsaye tasan abun yi."

"Muryan su Mujaheed ne ya katse mata tunanin ta bayan sun gaisa ne baba yamusu iso zuwa turakan sa ba laifi dakin a jare yake tsaff tsaff , daki ne guda daya mai dan fadi da

Please Login or Register in order to submit comment