Reading SIRRIN YA'MACE COMPLT BY MRS ALKALI Chapter 5 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya juya yatafi amma zuciyar sa taki basa hadin kai.

"Yanajin wayan sa ta katse, daga cikin motar sa yana hango yadda yarinyar take ta dube dube da alama tana duba Maman Sadiq ne."

"Cikin karfin hali ya bude motar, kafafun sa ya zuro cikin nitsuwa ya fito daga cikin motar."

Mufeedah tana ta dube duben ta tun fitowar ta daga cikin gida taga wata hadeddiyar mota tana parke a chan gefe .

Da alama babu kowa acikin motar tunda taga andauki lokaci babu wanda yafito aciki.

Ganin an bude marfin motan ne yasa hankalin ta ya koma chan .

Zuciyar ta ce ta buga ganin wani kyakkyawan mutumi mai kama da larabawa ya fito daga cikin motar.

Hancinta ne yashiga shakomata wani irin sassanyan kamshin da bata taba jin irin sa ba a tsawon rayuwarta.

Ganin kamar ita ya nufa ne yasa gudun zuciyar ta yakara tsanan ta.

Cikin sauri ta juya da niyar shigewa cikin gidan su.

"""Assalamualaikum """

Taji saukan wata dadda dan murya ya sauka mata acikin kunnen ta.

"Numfashinta ne ya tsaya na wucen gadi, a hankali ta sauke ajiyar zuciya."

"Juyowa tayi a hankali cike da nitsuwa, ya Allahu shine abun da mufeedah ta ke ambata acikin zuciyar ta."

"Tun da take bata taba ganin kyakkyawan mutum mai korji ni da cikar kamala kamar wannan mutumin da yake tseye agabanta ba, ashe dazu don yana dan nisa da ita ne, ayanzu da yake daf da ita sai ta kejin kamar notikan kanta zasu kwance."

Jarumta ta aro cikin sanyin murya da nitsuwa ta ce .

"""Wa'amin alaikumussalam"""

"Kallon ta Mujaheed yakeyi cike da nitsuwa, yace mufeedah Munir right, yakara sa maganar cikin dan sakin fiska."

Cike da mamaki mufeedah ta jinjina masa kai tare da ce masa ehh.

"Kafin ma ya sake magana ta shiga gaishe shi cikin kunya, duddah bata san shi ba, amma jin yakira full name dinta yasa taji kunyan sa don haka ta sunkuyar da kanta kasa."

"Rabon da Mujaheed ya tsinci kan sa acikin irin wannan yanayin har ya manta sai gashi from no Ware yaji yana enjoying din yanayin da ya tsinci, kan sa aciki."

"Zuba mata ido yayi, ganin ta sunkuyar da kanta kasa cike da kunya ne yasa shi sakin murmushi mai dan sauti, wanda hakan ya sa mufeedah dan daga kanta , faduwa gabanta yayi."

"Anya wannan mutum ne kuwa zuciyar ta ta raya mata cikin hanzari ta juya, zata shiga gida."

Amma me muryan wannan mutumin taji yace kinfito neman Maman Sadiq ne ko.

"Wani birki ta ja jin ya ambaci sunan Maman Sadiq, to ya akayi ya sani ko dai shi yakawo ta a motar chan to in haka ne ina take."

Tunanin ta ne yakatse Jin yace sunana Mujaheed nine wanda kike jira.

Cikin mamaki mufeedah ta kalleshi cikin sigar tsokana Mujaheed ya ce nine Maman Sadiq da kike jira.

"Zaremasa kyawawan katti idanun ta, Mujaheed ne yaji wani irin faduwar gaba."

"Kina mamaki ne cewar Mujaheed, dan murmushin da ya baiyana kyawawan hakwaran ta tayi."

Tunda Mujaheed ya ke bai taba ganin mace black beauty kamar mufeedah ba.

"Cikin nitsuwa yashiga mata introducing kan shi, bai boye mata yadda akayi ya shiga cikin group din SIRRIN YA'MACE ba sai dai ya boye mata laifukan Marwat cike da hikima ya mata bayani."

Ajiyar zuciya ta sauke tace bakomai amma hakan da kayi ba daidai bane shiga group din mata da sunan Mace.

"Kasani yin hakan laifi ne, murmushi Mujaheed yayi jin yadda take masa magana cikin nitsuwa da sanyin murya."

Uhuummm hakane nima nasan nayi kuskure amma insha Allahu a yau zanfita a group din.

"Murmushi tayi jin cikin sauki ya fahim ce ta, cikin nitsuwa tace ummah najirana barin wuce kartamin fada na gode da ziyara."

Harta juya taji saukan muryarsa cikin husky voice.

"""Mufee"" ya fada cikin wani irin sigan da yasaka gaban mufeedah faduwa."

"Tsayawa tayi bata juyo ba, kusan minti 2 taji kamshin jikin sa na kara kusan to ta."

"Kodai angaji da bakon ne in tafi, taji saukan muryarsa cikin nitsuwa ta juyo tare da rufe fiskanta da hannayenta."

Murmushi yayi Allah ya gani yana son mace mai kunya.

"Mika mata ledojin hannunsa yayi yace ga wannan gift ne na kawo miki, kuma naji dadin yanda kike bawa mata shawarwari masu kyau a group din SIRRIN YA'MACE."

Kin karban ledan tayi tace ai ummah ce take taimaka min akan hakan.

"Gaskiya ummah ta kyauta, agaishemin da ita, cewar Mujaheed."

Dan zaro masa idanu tayi tace toh inji waye zance mata .

Inji Maman Sadiq mana cewar Mujaheed yakarasa fada yana dan shafa sajen fiskar sa.

"Dariya yaba wa mufeedah wanda hakan yasata ta murmusa, shagala yayi da kallon ta."

Jin kamar idanu na yawo akanta ne yasa ta dago fiskar ta .

Charaf suka hada ido dashi da sauri ta janye nata idanun jin wani irin faduwar gaba.

Ajiye mata ledojin hannunsa yayi yace kyauta ne daga Yayan ki.

Da sauri ta dago kanta jin ya ambaci kan sa da yayan ta.

Kodai bakya son sabon dan uwa ne cikin jin kunya tarufe idanunta tace uhuummm ina so.

"Murmushi yayi yace good girl kinga bani da kanwa yanzu kuma nasamu, ki gaishe min da ummah da Abba, next time zan shigo mu gaisa."

"Toh tace masa tare da yimasa godiya, sallama ya mata."

"Cikin nitsuwa da Kasai ta ya juya yanufi motar sa, jin ya juya ne yasa mufeedah zuba ma bayan sa idanu."

Zuciyar ta ce take bugawa da karfi ta rasa dalilin jin hakan tunda ba yau ta saba tsayuwa da na miji ba .

"Amma kuma ko kamal in yazo hira bata taba jin abu makamancin haka a tattare da shiba, zuciyar ta ce tace May be don wannan din yafisa shekaru ne shiya sa take jin haka akan sa ."

"Jin kamar ana kallon sa ne ya sa Mujaheed ya tsaya juyowa yayi a hankali , bazato ba tsammani mufeedah taga ya juyo."

"Kunya ne ya kamata ganin ya kamata tana kallon sa, da sauri ta dauki ledojin da ya ajiye mata ta juya da dan sauri cikin sassarfa."

"Wani irin cute smile Mujaheed ya sake tare da shafa lallausan gashin kan sa, ganin ta dauki ledojin ta shiga gidane ya sa shi sauke ajiyan zuciya, motar sa ya shiga ,zama yayi acikin motar wani irin Nishadi yake ji acikin zuciyar sa."

"A zahiri ya furta what's wrong with me, ta da motar sa yayi reverse yayi ya juya cike da Nishadi yake tukin sa cike da nitsuwa."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

A tsakar gida mufeedah ta samu ummah da baba zuwaira.

Ummah ce ta zuba mata idanu ganin ta da wasu manyan ledoji na ShopRite.

"Ganin irin kallon tuhuman da ummah take mata ne yasa ta cewa, ummah shi yabani wai kyauta ne."

Cike da tuhuma ummah ta ce shi waye.?

Inda inda mufeedah ta fara tarasa ma ta ina zata fara yiwa ummah bayanin cewa Maman Sadiq ba mace bane namiji ne.

"Ganin irin daburcewar da Mufeedah tayi ne yasa ummah ce mata maza wuce daki kinjira ni, cikin sauri ta wuce dan batasan kuma me zata cewa ummah game da wadannan kayan ba."

"Ganin ta wuce ne yasa baba zuwaira yin kwafa tace uhuummm ayi dai mugani in tusa zata hura wuta, nasan da Kamal ba shi da kudin da zai mata uban wannan sayaiyan, Allah sarki Kamal bawan Allah za'a cuceka a hadaka da kara da kiyashi."

Ko inda baba zuwaira take ummah bata kallah ba bare tasan da su takeyi.

"Tashi tayi tanufi dakin ta dan itama hankalin ta bazai taba konciya ba idan bataji a ina mufeedah tasamo wa dannan kayan masu uban tasadan ba, don daga ganin kedan tasan kayan ciki ba laga laga bane, dan ita ma daga gidan arziki ta fito tasan ire iren kayaiyakin nan."

"A zaune ta samu mufeedah sai tafka da warwara takeyi, cikin nitsuwa ummah tace ."

""" A ina kika samu kayannan"""

Cikin sanyin jiki mufeedah ta fara labartawa ummah yan da su kayi da Mujaheed ba abunda ta boye mata.

"Ummah ce ta sauke ajiyar zuciya ta kalli mufeedah ta ce, kinsan dai yau saura two weeks auren ki bana son ki jawo abunda malam zai zo yayi ta miki fada kin san dai idanun babar ku zuwaira suna kanmu dan Allah ki kiyaye, sannan ki kira mutumin kimasa godiya kuma bana son kisa ke karbar abun hannunsa."

Cikin nitsuwa da sanyin jiki ta ce insha Allahu ummah zanyi yan da kika ce.

"Mujaheed bai koma gida ba sai bayan sallahn Isha, duk wunin da yayi bai dawo gida ba daga gidan su mufeedah office ya wuce duddah yau Saturday ne amma yace gara ya rage wasu aiyukan akan ya koma gida Marwat ta kunsa masa wani bakin cikin, duk wannan wunin dayayi baya nan Marwat bata daga waya takira sa ko sau daya ba, abun bakaramin bata masa rai yasake yi ba, shi yasan da a ce da ne data kira sa yafi sau goma da wannan tunanin ya shigo gidan, misalin qarfe 9:00pm na dare."

"Kamar yanda yayi tsammani ba bu kowa a parlourn sai TV dayake ta aiki shi kadai, parlourn yashiga karewa kallo, duk yafara fita daga haiyyacin sa ya lura tun da Marwat ta yi fishi da shi akan maganar komawarta aiki da batun sama mata yan aiki yaga ta dai na kula da gidan da alama yauma bata jara parlourn ba ,dan ga ledojin sweet da biscuit nan a war watse a parlourn har da goran drinks da aka sha da alama tayi baki ne ganin yanda akayi scatting parlourn sosai."

"Bai san san da wani tsaki ya kubce masa ba , dan arayuwar sa ya tsani kazan ta, zai iya jure komai daga wajen Marwat sai dai bazai juri kazantar da zata lalata masa gida ba koma bayajin zuciyar sa zata taba amincewa da bukatar ta dole ne ma gobe ya zauna da ita yamata magana yakamata ta fiskanci rayuwar ta, dan bakaramin danne zuciyar sa yakeyi ba wajen yin fishi da ita ba."

"Bedroom din sa ya wuce direct key yasa ya bude, yanda yabar dakin haka ya same shi ba jara ba komai."

Ajiyar zuciya ya sauke kayan jikin sa ya rage nan yashiga tattare abun da yaga zai iya a dakin bayan yagama ne ya shiga bathroom yayi wanka.

"Fitowa yayi ya shirya cikin pyjamas din sa masu mugun taushi, konciya yayi da tunanin gobe da safe zai zauna da Marwat domin ganin yakawo karshen wannan rashin fahimtar da take tsakanin su."

"Addu'ar bacci yayi, yana rufe idanunsa a maimakon bacci ya dauke sa, sai yaga fiskar mufeedah ta na masa gezau, yanayin shigarta da yanda take da kunya ne ya fado masa bude idanunsa yayi, Wani irin lumshe idanunsa yayi tare da shafa gashin kansa, wai me yake shirin faruwa da nine, zuciyar sa ce ta raya masa sabida kyawawan dabi'un ta ne yasa."

"Wayarsa ya dauka alamar shigowan message yagani, dubawa yayi yaga numbern da yakira Mufeedah da shine, anturo message din tun karfe 5:00pm Amma baigani ba sai yanzu."

"Bude message din yayi kamar haka,,"

"""Barka da wannan lokacin Yaya dafatan kakoma gida lpy, nagode da ziyara Allah ya saka da alkhairii, Allah ya kare gabanka da bayan ka , ka gaida mutanen gida, bissalam."""

"Wani irin sanyi ne yake mamaye zuciyar sa a hankali yashiga shafa sajen fiskar sa, fuskar Mufeedah ce ta fado masa tana murmushi wani irin yarrrrrrr yaji ajikin sa , cikin sauri ya fara ambatar sunan Allah da neman tsari."

"Time ya duba yaga karfe 11:00pm yasan May be tayi bacci da yakira ta , baiga message din ta bane sai yanzu, kashe wayar yayi da niyan gobe insha Allahu zai kirata, haka kawai ya yaba da hankali da nitsuwar yarinyar sai yakejin ta kamar kanwar sa ,haka zuciyar sa taci gaba damasa sake sake har bacci barawo yayi awun gaba da shi."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Marwat ce zaune a akan sofa a cikin parlourn ta Hakim ce tunani takeyi, ita fa wannan fishin da Mujaheed ya keyi da ita yafara isan."

"Tayi zaton zai lallabata ya amin ce da bukatar ta sai gashi taga alamar bilhakki yake fishin da ita, sai dai tanajin a wannan karon baza ta taba yarda yaci galaba akan ta ba duk yan da zatayi sai ta kwatarwa kanta yanci."

"Tana cikin wannan tunanin ne taji kamshin turaren sa, basarwa tayi kamar bata san da wan zuwar sa a cikin parlourn ba."

"Cikin nitsuwa da kasaita ya zo ya zauna a gefen ta dan konta wa yayi ajikin ta ta gefe daya, ture shi Marwat ta yi ta turo baki gaba alamar har yanzu fishi takeyi da shi."

"Cikin sanin weak point din ta yafara shafa lallausan gashin kan ta, a hankali ya matso da fiskar sa daf da nata harshen sa ya zura a cikin bakin ta cikin kwarewa ya fara kissing dinta."

Cikin kankanin lokaci Marwat tafara sakin layi dan baka ramin missing din sa tayi ba.

"Ita ma dauriya ce kawai da son kwatarwa kan ta yanci, Mujaheed ne yaci gaba da aikamata da sakonninsa masu wuyar fassarawa, san da ya tabbatar da sakon sa yakai inda yake bukatar yakai."

"A hankali ya fara janye jikin sa daga nata,cikin sauri Marwat ta bude idanunta da suka gama rinewa , ba abunda take bukata sai mijin ta a wannan lokacin."

Ganin irin halin da tashiga ne yasa Mujaheed ya tashi ya nufi bedroom din sa bai ce mata uffan ba.

"Shima daure wa kawai yakeyi amma so yakeyi ya nuna mata kuskuren ta,yayi alkawarin ko sha'awar ta zai ka she shi bazai sake kusantar ta ba sai tagane kuskuren da ta aikata masa na hanasa kanta da tayi 3 time."

"Yana shiga bedroom din toilet ya wuce ruwan sanyi ya sakewa kansa, a hankali yafara sauke a jiyar zuciya jin yanda sanyin ruwan yake ratsa bargo da jijiyar jikin sa ."

"Sai da ya tabbatar da ya samu nitsuwa sannan ya fito , goge jikinsa yayi da towel, mayukansa masu tsada ya shafa tsaf yagama ya shirya kan sa a cikin t-shirt da 3 quater masu shegen tsada da taushi, dan yau Sunday ne so yakeyi ya huta a gida."

Bayan ya kammala ne ya dau wayan sa konciya yayi akan makeken gadon sa.

"Mufeedah ce tafa domasa arai tunowa da bai mata reply na message din da ta turo masa ba ne yasa yayi dialling din numbern ta Ringing tayi harta katse ba a dauka ba, ajiye wayar yayi a gefe dan bacci yake ji, konciya yayi, nan take bacci mai shegen nauyi yayi awungaba da shi."

"""Mufeedah, Mufeedah"" haka ummah ta ke kwalawa mufeedah kira."

Mufeedah ce ta shigo dakin tana goge hannunta da dan wani tsummah da alama wanke wanke tagama.

"Ummah gani cewar mufeedah dake faman ajiye tsumman hannunta, ummah ce ta ce kin gama wanke wanke ne, Kai tajin jina mata."

Mika mata wayar ummah tayi tace dazu ankira da numbern Maman Sadiq.

Haka kawai mufeedah ta ji Wani irin duummm gabanta ya shiga faduwa ita dai bata san meya sa takejin irin wannan yanayin ba in ta tuno da wannan mutumin.

"Ganin ta sunkuyar da kanta kasa ne kuma batada niyar karban wayar ya sa ummah ta ce ungo nasan mutumin da yazo niya ne ki kira sa ,kuma ki sanar da shi ansa miki ranar aure da wani, dan banga dalilin kiran ba,dama nazaci mace ce shiyasa ma na barki kika fita wajen sa, bana son abun magana kinga baba zuwaira har tafara magana akai ,dan har malam ta fadawa jiyama san da ya tuhume ni akai, da kyar ya yarda da cewa ba saurayin ki ba ne dan da alama wani abun ta kitsamasa ."

"Jinjina kai Mufeedah tayi wayar hannun ummah ta karba, dialling call ta shiga nana taga Miss call din sa kiran wayar sa tayi back."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

Yan da Mujaheed ya kunna Marwat haka ya tafi yabar ta acikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa.

"Taso ta yi controlling din kanta amma abun yafi karfin ta bedroom din ta ta wuce, wanka tayi da ruwan sanyi ko zataji saukin yanayin ."

"Amma me kamar ma kara motsa abun tayi ganin zata cutu da yawa ne yasa kawai ta yanke shawarin gara ta ajiye fishin a gefe in komai ya kammala sai ta dora daga in da a ka tsaya, dan ba karamin kunnata Mujaheed yayi ba."

"Tashi tayi ta dan kimtsa,fitowa tayi ta nufi dakin Mujaheed, tura kofar tayi a konce ta hango sa yana ta baccin sa cikin nitsuwa da konciyar hankali."

"Tsaki taja wato ita ya mayar birin wasan sa ko, tunda gashi yazo yana baccin sa hankali kon ce ita kuma yabaro ta cikin bala'i, tsaki taja a karo na biyu, itama ji takeyi da tana da yadda zatayi da ta hakura da niman shi sai dai sashi na jikin ta bazai barta ba."

"Cikin class ta shiga takawa cikin dakin , wayarsa ce ta fara ringing bata kalli in da wayar take ba har taji wayar ta katse, ganin bai motsaba ne ya tabbatar mata da cewa bacci me nauyin gaske ne ya dauke shi."

"Tazo zata hau kan gadon nasa ne taji wayar ta sake daukan kara, siririn tsaki taja, fasa hawa gadon tayi."

"Juyawa tayi ta dauki wayar May be important call ne, ganin numbern ba suna yasa tayi picking call din."

"Wani murya mai zaki cike da nitsuwa taji, tace assalamualaikum,,"

Zuciyar Marwat ce ta buga da mugun karfi wanda hakan yasa ka sanda ta danne saitin zuciyarta da hannunta haka kawai ta tsinci kanta cikin faduwar gaba.

Zare wayar tayi a kunnenta numbern ta kurawa idanu ganin haryanzu ba a yanke kiran bane yasa ta sake mayar da wayar kunnen ta.

"Cikin wata irin murya, mai cike da kishi da bacin rai tace wake magana ."

Cikin nitsuwa Mufeedah tace barka da warhaka aunty dama na kira ne inyiwa Yaya godiya .

"Ai Marwat batajira ta karasa jin abunda Mufeedah zata cemata ba,cikin wani irin kishi da zafin zuciyar da bata ma san tana da shi ba, ta lailayo wani ashar din da ita kanta bata san ya akayi ta koye shi ba."

"Tace yar iska kawai karuwar banza wato kinga yau baizo wajen ki ba wato shi ne zaki kirasa, harda wani wai godiya zaki masa, godiyar ubanki, nace toh wlh inkina son ranki da lafiyan ki ki gaggauta rabuwa da mijina, jaka kawai karuwa wacce bata san darajar kanta ba, ai bata karasa fadaba taji anwani fizge wayar."

Mujaheed ne tun san da Marwat tafara zagin Mufeedah ya farka daga farko bai fahimci da wa take wayaba ne sai daga baya.

Cikin huci da zafin kishin da yagama makantar da idanun Marwat tace dole ka kwace wayar ashe da gaske abun da kake aikatawa kenan haba Mujaheed shiya sa ka chanza mini a cikin gidannan danayi magana kace office ne ya rike ka.

"Ashe karuwa ka ajiye a waje kana cutata,gashi ni ka gagara kabani hakkina wlh bazab yafe maka ba Mujaheed Allah ya isa tsakanina da kai."

"Wani irin bakin ciki ne ya tokare wa Mujaheed wuya ganin Marwat taki basa dama yamata bayani, gawasu bakaken magana da take tafaman jifan sa dasu."

Cikin yanayi na bacin rai yace karki kuskura bakin ki yasake jifana da irin wadannan kalamen ki iya bakinki.

"Cikin kuka da kunar zuciya Marwat tace ai dole ka fadi haka sabida karuwar ka tafini daraja a idanun ka, wlh kaji kunya Mujaheed me na rageka da shi a gidannan, in banda jaraba irin taka, mene bana maka, shine zaka sakamin da wannan , nagode Mujaheed amma kasani wlh bazan ci gaba da zama da kai ba, a yau sai ka sakeni inya so kaje ja auri karuwar ta ka, nima nagaji mutum ba da'ba ba jika ba wlh sai ka sakeni bazan cigaba da zama da mazina ci fasiki ba ta karasa maganar cikin matsanancin kuka."

"Wani irin rawa jikin Mujaheed yakeyi kallo daya zaka fahimci yana cikin mugun yanayi, damke hannun sa yayi da karfi, cikin wata irin murya mai tsawa yace stoppp it Marwatttt get out of My side,ya kara sa naganar cikin daga murya."

"Ba shiri Marwat ta juya da gudu ta fita kuka takeyi mai tsuma zuciya, cike takeyi da nadama da dana sani na auren Mujaheed sai ayau ta sake gane babbar kuskuren da ta aikata na yarda da Mujaheed data yi, bedroom din ta tashiga ta rufo kofar da karfin gaske."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Zama yayi a bakin gadon kama kansa yayi da hannunsa biyu, ji yakeyi kamar kan sa zai fashe tsabaragen yanda yake jin yana masa ciwo."

"Shin yaushe Marwat ta dawo haka ne ya takeyin abu kamar wata jahila wacce batayi kara tuba, daga ganin kira kawai sai ki hau zagin yar muta ne ba bincike, jin kan nasa yana barazanar fashewa ne yasa shi tashi ya nufi bathroom so yake ya watsa ruwa ko zai samu sassauci acikin ransa, ayau Marwat ta gama kai shi makura, shi take kira da mazinaci fasiki har da masa gorin haihuwa wani irin kullutun abu ne ya zo ya tokare masa makoshin sa dakyar ya samu ya wuce toilet din."

"Wanka yayi a daddafe alwala ya daura ganin cewa Ana kiran sallan la'asar, fitowa yayi ya shirya tsaff cikin manyan kaya haka kawai yaji yana son saka manyan kaya harda babbar riga, abunda bai dame shi ba kenan amma a ayau yaji yana bukatar saka su."

"Bakaramin kyau yayi ba a cikin kayan sai dai kallo daya zakayiwa fuskar sa kasan baya cikin walwala, don ya hadeta tsaff ba wani alamar annuri akan fiskar."

"Key din motar sa ya dau ka wannan karon SUV zai fita da ita don ya kwana biyu bai fita da ita ba, so yakeyi in yayi sallan la'asar ya wuce gidan su Mufeedah don so yakeyi yabata hakuri duk zagi da cin mutunci da Marwat ta mata akan kunnen sa."

Fitowa yayi daga bedroom din kota kan dakin Marwat baibi ba duddah yan da yakejin tana ta sheshsheqan kuka a cikin dakin.

"Parking space ya nufa wata jibgegiyar mota kirar SUV ya nufa sai shekin sabonta ka takeyi, kai daganinta kasan anzuba nera wajen sayanta, shiga yayi yatayar reverse yayi security ne ya bude masa kofa cikin nitsuwa ya cillah hancin motar bisa ga titi dudda yana cikin matsanancin bacin rai, amma yayi kokarin danne fishin ."

"""Mufeedah ce zaune a gefen ummah kuka takeyi bilhakki,tun da ummah ta haife ta ba'ataba zaginta kokuma cimata mutunci ba kamar yau."

"Ita ce ake kira da karuwa yar iska mai bin maza, wani kukan ne tasake fashewa da shi."

"Cikin muryan lallashi ummah tace haba Mufeedah kiyi hakuri da wannan kukan haka ko so kikeyi ciwo ya kamaki, ita wacce ta zagekin tasan kinayi ne, shiyasa nace ki yanke alaka da shi banga dalilin da zaisa ya kulla mutunci da keba nan da sati biyu ke matar wani ne."

Cikin wani irin bakin ciki Mufeedah tace ummah kinji irin zagin da matar sa tamin kuwa har da cemini karuwa yar iska fa ta

Please Login or Register in order to submit comment