Reading SIRRIN YA'MACE COMPLT BY MRS ALKALI Chapter 4 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da bazarta ne ake taka rawa acikin gidan, shiyasa yanzu take hurawa hajiya shuwa hanci."

"Ita kuwa hajiya shuwa, bata taba nuna wa zuwaira ta fahimce ta ba domin kuwa gani takeyi jahilci da rashin sanin ciwon kai ne yasata take wannan abubuwan, shiyasa ma bata taba kallon zuwaira amatsayin kishiya ba, irin wannan hali na hajiya shuwa,na nuna ko inkula da take musu shiyasa suke ganinta a matsayin mace mai girman kai da wulakanci."

"Hakan baitaba damun hajiya shuwa ba don ita acewar ta tunda lafiya kalau take zau ne da mijin ta hakan ya wadatar da ita, shiyasa harkokin gabanta kawai takeyi acikin gidan."

"Mufeedah yarinya ce mai nitsu, ga shegen kyau kamar ita tayi kanta, ""mufeedah baka ce ba fara ba sai dai ba inda ta baro kamannin hajiya shuwa sai dai ita hajiya shuwa ba baka bace sabanin mufeedah da take dauke da kalar fatan babanta don malam Muniru bakin bafulatani ne irin baki mai shegen kyau dinnan wanda in kakalli mutum sai ka sake."

"""Mufeedah doguwa ce amma ba sosai ba, kuma yar duma duma ce, baza ace mata katuwa ko kuma siririya ba, fatanta baki ne mai sheki gawani irin laushi da fatarta take da shi, tana da manyan idanu masu dan kauri kadan, cikin su farare ne tass kamar nono, lebbanta suna da kauri sannan suna dauke da launin ja ja ja ja, tana da gashin gira irin mai cike cunkus dinnan, baki ne sosai, zaka ce zana mata akayi, tana da bakin gashi sosai mai tsawo sai dai a nannade yake sabida laushin dayake da shi."

"Ayanzu haka tagama secondary school, bata ci gaba da karatuba sabida baba yace aure zai mata inya so tafara karatun a dakin mijin ta."

Dudda hajiya shuwa tana son mufeedah tayi ilimin boko mai zurfi hakan baisa ta musawa baba maganar sa ba .

"Ganin irin yanda mufeedah take da kira na cikar mace, don duk inda suran mace da kyan diri yakai tofa mufeedah ta wuce wajan."

"Ganin hakanne yasaka ummah tayi na'amm da zancen baba, a yanzu haka mufeedah ba zuwa ko'ina sai islamiya, kullum zaka ganta da babban hijabi har kasa, ga nikab da safa har da na hannu."

"Hakan baya damunta dan ya zama mata jiki, tun tana karama umman ta ta hore ta da suturta mata jikin ta, sabi da haka sai yabi jinin jikinta, duddah kawaye da yan anguwa suna mata isgili da cewa , wai matar ustazz , hakan baya damunta don tafi jin dadin rayuwan ta a haka."

"Hajiya shuwa batayi sake da tarbiyan mufeedah ba duddah ita kadai Allah ya ba ta ,ta tsaya ta jajir ce akanta, ta inda tazama ita ce babbar kawarta, ayanzu haka ma da wayan ummah ta bude account da sunan ta , kuma duk wani abu da takeyi ummah ta sani , yawanci ita netake bata shawara acikin group din SIRRIN YA'MACE in mufeedah tabata labarin posting din da akayi."

"Anyanzu haka auren mufeedah ya kusa, nan da wata daya, wani cousin din ta zata aura mai suna Kamal auren zumunci za amata, dan kaka wato mahaifiyar baban ta ita ce ta hada auren."

"Mufeedah bata jin son kamal, har cikin zuciyar ta sai dai tayi tunanin a hankali zata fara sonshi, dan kamal mutum ne mai kirki da sanin ya kamata, ayanzu haka yana teaching a private school ne yagama NCE nshi."

"Ummah bata wani damu ba ganin kamal yana da nagarta, sannan kuma mufeedah ta nuna ta karbeshi shiyasa take bin su da addu'a."

"Abangaren baba zuwaira kuma murna takeyi ganin duk wannan uban kyau da qualities da mufeedah take dashi na cikar ya mace, itama a malamin makaranta zata kare kamar mahaifiyar ta, shiya sa take kara zuga baba akan ai mufeedah sun dace da kamal."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Mujaheed bai shigo gida ba sai karfe 1 00pm, ko takan abincin da Marwat ta ajiye masa a dinning table baibi don dama san da yabi restaurant ya cika cikin shi, bai saba cin abinci a waje ba a yau sai gashi a dalilin rashin hankali irin na Marwat tasa shi yaje yaci haka yawuce bedroom din sa don bakaramin fishi yakeyi da ita ba, ya dauki alkawari sai ta zo tanemi sulhu da kanta."

"Bayan yan ya yi wanka yayi shirin kwanciya ne, amaimakon bacci ya dauke shi, sai mufeedah Munir ta fado masa arai , baisan sanda ya dauki wayar sa ba."

"Online ya hau amma kuma yaga tajima da sauka, wani irin siririn tsaki ne ya kubuce masa, haka kawai kalaman yarinyar da irin shawarwarin daya ga tana bayar wa acikin group din SIRRIN YA'MACE yani ta kwanta masa arai."

"Wayan ya kashe ya ajiye ta agefe addu'an bacci yayi ya shafa, zuciyar sa tana cigaba da nazartan irin kalamai na hikima da mufeedah ta ke amfani da su wajen bawa group din SIRRIN YA'MACE shawarwarin da suka da ce, bacci barawo ne yayi awungaba da shi."

"Misalin qarfe 8 00am nasafe Mujaheed yafito cikin shirin sa , sai dai ayau ba suit bane ajikin sa, jamfa da hula ne yasaka, bakaramin kyau yayi acikin kayan ba, sabida yawanci yafi sanya kananan kaya sabida yanayin aikin sa."

"Ayau Saturday ba office zai jeba , sabida fishi da yakeyi da Marwat ne yasa ya tsiri kaiwa wani aminin sa ziyara a anguwar tudun wada , sabi da so yakeyi ya saitawa Marwat zama, so yake sai ta gane kuren ta na bin shawarwarin bara gurbin kawar da bata san tushen ta ba, yayi alkawarin sai ya nuna mata kuskurenta."

"Kamar bazai shiga bedroom din Marwat ba, tuno da cewa jiyama da ya dawo bai nemeta bane ,dole ne yaleka yaga lafiyan ta koda kuwa bazata kula shi ba."

"Kofar bedroom din ta ya bude, akonce ya sameta akan gado jikin ta na lullube da wani blanket mai shegen taushi, da alama ko tashi batayi ba, dan gajikin ta sanye da pyjamas, sannan gashin ta duk a hargitse, wayar ta ce a hannunta sai dannawa ta keyi, da alama abu mai muhimmanci takeyi acikin wayan, dan kuwa kallo daya tamasa ta watsar dashi taci gaba da abunda takeyi."

"Bakaramin zafi abun yayi wa Mujaheed ba, shi kanshi yasan wannan ba Marwat din sa bace, dan da abaya ne bazata taba zama haka ba, dan kafin ya dawo daga masallaci tagama shirya masa break fast itama ta jara jikin ta sabanin yau da ta nuna masa ko inkula akansa abun yamasa zafi duddah haka ya danne zuciyar sa cikin kunar rai, yace mata good morning, kamar bazata amsa ba cikin yatsine fiska, tace masa how are you, tsabar ta kaici Mujaheed baisan sanda ya juya ba yana shirin barin dakin."

"Don yaga rainin wayon nata ya fara yawa, saukar muryanta yaji tana cewa, bayan time din ka da kabata jiya, yanzun ma wajen ta zakayi sammako kaje ko, ai da kasani da kwana kayi achan, nidai wlh bazan yafe ba in an chuce ni."

"Cikin kakkausan muryan da ta gaji da bacin rai yace Marwat stop this nonsense how many times dazan cemiki duk abun da zaki fadamin kar ki kuskura kisaka zargi acikin zaman auren mu, ni zaki ce inje in kwana a waje."

"Cikin ko inkula tace toh sai me zargi ai yazama dole tunda kai kabada kofar da zan zargeka wani irin aikin office ne da zai sa ka kakai karfe 1 00pm a waje, sannan kafara nunamin halin ko inkula, shine zaka cemin kada inyi magana akai, sabida kasaba tauyemin hakki na, waya sanima ko karuwa ka ajiye."

"Marwatttt, yawani kira sunanta da karfi cikin bacin rai mai tsananin gaske, idanunsa ne suka kada sukayi jajawur sabida bacin rai ga jijiyoyin kansa sunfito boro boro tsaban ransa ya baci, dunkule hannunsa na dama yayi cikin kunar rai da wata irin kakkausan muryan sa yace this is the first and last time da zaki fadamin duk wani rubbish da ya fito daga bakin ki."

"Baikara jiran mai zata ce ba ya juya yafita cikin sassarfa, harwani irin jiriniri yake gani cikin matsanancin bacin rai ya shiga motarsa kirar Roll Royce yajata da mugun gudu, cikin hanzari security ya bude masa kofa, ganin wani irin tuki da baitaba ganin ubangidan nasa yanayi ba, da mugun gudu ya cillah hancin motar sa kan titi."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Bayan fitar Mujaheed wani irin wawan ajiyar zuciya Marwat ta sauke, a hankali ta sake jikin blanket da ta mugun damkeshi da hannunta."

Dan tunda Mujaheed ya fara magana cikin bacin rai ta damke blanket din.

Dan bakaramin tsoron yanayin da yashiga tajiba dan tasan shi mutum ne mai saukin kai da dadin zama amma kuma bai iya bacin rai ba.

A hankali ta sauka daga kan gadon toilet ta wuce domin ji takeyi mararta kamar zai fashe tsabaragen fitsarin da ya taru mata dan ba karamin kokarin rike fitsarin tayi ba lokacin da Mujaheed ya ke mata tsawa ba.

Bayan ta fito daga toilet din ta koma kan gado tayi kwanciyar ta wayanta tacigaba da dannawa.

"Aranta kuwa tagama cin alwashin sai ta sai tawa Mujaheed zana, dakan sa zai zo ya amince da bukatunta, tayi shirin gasa masa aya a hannu, shiya sa ma ayanzu ko yimasa girki bai dame ta ba bare jaran gidan, ko jaran jikin ta tarage yi acewar ta ai sabida shi takeyi yanzu kuma tana fishi da shi."

"Aganinta daukan wannan matakin shine hanyar da zai samarmata mafita a wajen Mujaheed, shiyasa ayanzu bata da wani aikin da ya wuce daga konciya sa i Danna wayar ta tashiga group din SIRRIN YA'MACE taga gwaramar da akeyi, inta ji yunwa ta nemi snacks da drinks ko kuma tayi ordern takeaway akawo mata har gida."

"Hakan bakaramin dadi yakemata ba ganin tanacin gashin kanta, acewar ta huta roro ne domin ba dawainiyar kowa akanta,sai take jinta Free tana enjoying din mood din da take ciki a yanzu."

"""Mujaheed yayi tafiya mai nisan gaske, sanda yaga yana kokarin fita daga cikin garin zariya sannan ya yi parking a bakin hanya."

"A hankali ya kifa kansa a kan siterin motar, wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga gangaroma sa."

Shi kansa bazai iya tuna yaushe rabon da yaji saukan hawaye akan fiskar sa ba.

Sai ga shi a yau Marwat tasa masa wani irin bakin cikin daya kasa mantawa.

Allah ya gani ba karamin so yakeyiwa Marwat ba shiya sa yazabi fita yabar ta don gudun kada ya dauki mummunan mataki akanta daga karshe yadawo yana da nasani.

Yajima a wajen yana karanto duk wata addu'a data zo bakinsa.

"A hankali ya kejin sanyi acikin zuciyar sa, wayarsa ce tafara ringing."

"Sanda ta kusan katsewa sannan ya sa hannun sa ya dauka, picking call din yayi tare da kara wayar a kunnen sa."

"Muryan Brr. Imam ne ya karrade kunnen sa, cikin muryan wasa yace haba MJ tun dazu fa ka shanya ni kace gakanan kana zuwa tun dazu nake duba hanyar ka shiru, ko dai Hajiya Marwat tarike maka wuta ne dan nasan ka ba sauki a wannan harkar ya karasa maganar cikin dariyar shekiyan ci."

Jin yanda ya karasa maganar cike da sheganta ka neya saka Mujaheed yin murmushin da bai shirya ba.

Cikin husky voice dinsa yace on My Way insha Allah.

"Yana fadan haka ya hanging din kiran, Wani irin dariya Imam yayi yace shegen kaya kenan ,miskili kafi mahau kaci ban haushi."

Matar sa ramlart ya kallah yace ina fatan dai break fast is ready.

Murmushi tayi tace karka damu komai yakammala.

Kace yau muna da babban bako kenan.

"""Kamar zai ajiye wayar, bai san meyasa zuciyar sa take son sanin cewa ko mufeedah ta hau online ba."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Yana hawa yaganta online, massage ya turamata kamar haka."

"""Barkan ki da safiya"" ""Barkanki dai sister ykk"""

"Wani murmushi Mujaheed yayi ganin cewa itakam bilhakki ta dauka da mace take charting, ammasa tabasa."

"""Lpy qlu alhmdullah """

Jiya na dubaki around 1:00pm bakya online.

Emoji mai alamar ta turomasa tace chap wayar ummah ce kuma bata bari na hawa online in dare yayi.

Ayyah hakan yana da kyau ai ummah ta kyauta cewar Mujaheed.

Nan dai suka dan taba tadi inda Mujaheed ya ce mata yanazu haka yana hanyar anguwar tudun wada zaije sada zumun ci.

Mufeedah tace tace aikuwa anguwar mu daya kinga saiki kara so gidan mu musa da zumunci.

Baisan meyasa zuciyar sa ta amince da maagnar mufeedah ba.

"Haka kawai shima yakejin yana son yaganta, duddah ita a zatonta da mace yar uwar ta take tare."

"Haka mufeedah ta shiga masa kwatancen layin su, in da yaga bawani nisa da gidan aminin sa Imam."

Nan yamata sallama tare da alkawarin zuwa bayan ta turomasa da numbern wayar ummah in ya zo zai kirata.

"Kashe wayar yayi, a fili ya furta, yaukam idanu na zasuga wace ce mufeedah, Wani irin cute smile ya sake , shikam bai san dalilin da yasa yakejin ta aran sa ba , gashi dai baitaba ganin ta ba charting kawai sukeyi, amma haka kawai yakejin wani irin abu game da ita akasar zuciyar sa, kon ceccen sajen sa ya dan shafa ,kai kace bashi ne ya fito cikin bacin rai ba."

Motar ya tayar yayi reverse cikin nitsuwa yake tukin sa kamar ko yaushe.

Yadan yi tafiya mai nisa kafin nan yashiga cikin gari.

Titin da zai kaishi cikin anguwar tudun wada ya dauka.

"A kofar wani tafkeken gate yayi Horn nan danan aka wangale masa gate din,da alama maigadin ansanar da shi zuwan sa."

"Parking yayi a cikin parking space, fitowa yayi daga cikin motar sai baza kamshi yakeyi."

Ganin wanda ya fito acikin motar ne yasa mai gadi bazowa aguje dan ya san kakar sa ta yanke saka zubewa yayi akasa yafara kwasar gaisuwa.

"Cikin sakin fiska Mujaheed ya amsa masa dagani akoi sabo a tsakanin su, hannunsa ya saka a cikin aljihun wondon sa bunch na 1k ya ciro ya mikawa maigadin, jiki na rawa yasaka hannunsa biyu ya karba, sai rattabo addu'o i yakeyi, cikin sakin fiska Mujaheed ya nufi kofar main parlour na cikin gidan dama shi ba bakon gidan ba ne, yanzu ne dai da aiyuka suka masa yawa a office bai fiye zuwa wajen imam din ba."

"Imam da Mujaheed aminai ne tun na yaranta, sunta so anguwa daya kuma makwabtan junane gida jen iyayen su."

Akoi good understanding a tsakanin familyn su zumunci sukeyi mai tsafta.

"Tare su Mujaheed sukayi karatu da Imam sai dai kowa da course din da ya dauka, inda shi Mujaheed ya zabi business administration, shikuma Imam inda ya karanci common and Islamic law."

"Ayanzu haka lawyer ne mai zaman kansa, in da shikuma Mujaheed yake da companies na motoci a jahohi daban daban, sabida bakaramin arziki yatara ba ga shi kuma ya gada awajen mahaifin sa, wannan ne yasa zumuncin su yadan ja baya, amma basuyi kasa a guiwa ba wajen sada zumunci in suna Free ba."

Imam yana da mata mai suna ramlart inda suke da yaya biyu daya mace daya na miji. Macen ce babba sunanta hanifa inda namijin suke kiran sa da hanif.

"Nocking din kofar yayi, nan danan aka bude masa kofar ,inda imam ya wani irin rungumeshi irin one side dinnan."

"Tureshi Mujaheed ya shiga yi, dariya imam yayi yace miskili kafi mahaukaci ban haushi , kaga angon Marwat masu MJ plaza the whole CEO of Jaheed group companies."

Mujaheed ne ya dan bugi kafadar Imam gocewa yayi yana dariya yace ya haka daga fadar gaskiya sai cin zali.

"Dariya Mujaheed yayi yace naga kamar ba a maraba da zuwa nane, naga ka tare ni daga bakin kofane kanata faman mini surutu."

"Aww kace ma surutun banza nayi kenan duk wannan washin dana maka ya tashi abanza kenan,to gaskiya ban yarda ba yakamata inji alert, cewar imam cikin raha."

Baka da matsala cewar Mujaheed yana dariya.

Ramlart ne ta fito tana cewa kaga manyan baki angon Marwat.

"Maraba ka iso mana kunwani tsaya abakin kofa da alama amintakar ce ta motsa ta fada tana dan murmushin zolaya, dan tasan karfin amintakar da take tsakanin su."

Nan Mujaheed ya karaso cikin parlourn zama yayi acikin daya daga cikin sofa nan suka shiga gaisawa da ramlart.

"Bayan sun gaisane yake tambayar ta ina yaran sa, nan tace masa sunje islamiyar safe na asabar da lahdi , cikin dan zolaya tace kawata kam har yanzu shiru , dan sosa kai yayi yace Allah bai kawo ba tukunnah, murmushi tayi tace to Allah ya kawo nagari da ameen suka amsa dukan su."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

Ramlart ne ta musu iso wajen dinning table nan tashiga saving din su bayan ta kammala ne taba su waje don suji dadin sakewa tasan yaukam tunda suka hadu ai sai Allah.

Mujaheed ne yace kamar kasan yau banyi break fast ba.

Kallon sa Imam yayi yace chap yau wacce rana kenan wait yaushe ma kafara wasa da abinci ban sani ba.

Murmushi Mujaheed yayi yace sabida nazama acici ko.

"Ah toh nidai nasan sanin da na maka baka wasa da abinci, maybe yau din ma Marwat bata da lafiya ne yasa kafi to bakayi break fast ba."

"Ajiye spoon din hannunsa yayi, yace uhuummm kodaya wlh lafiyan ta kalau."

"Kawai dai 2 days bana gane kanta ne, nan Mujaheed yashiga labarta wa imam abunda yake faruwa a tsakanin sa da Marwat."

Bakaramin mamaki bane ya kama Imam ganin duk irin son da Mujaheed yakeyiwa Marwat sai gashi a yau ta kureshi tasa yana fadan laifin ta dakan sa abunda bai taba gani ba a tsakanin su.

Kallon Mujaheed yayi yace to kai yanzu Wani mataki kadau ka.

Uhuummm wani mataki kuma kasan ina matukar son Marwat bazan iya dogon fishi da ita ba.

"Yanzuma karkaji yanda nake ta yaki da Zuciya ta akan fishin da nayi mata, dole na hakura na ajiye son agefe don naga matukar naci gaba da biye mata, bazata taba fahimtar kuskuren ta ba, nasan nan da dan lokaci zatayi apologize sabi da nasan bazata iya yin fishi ni ba."

"Mujaheed ne ya kwashe da dariyan shekiyan ci yace uhuummm kaga fadan masoya, kowa ya shiga tsakanin mata da miji zaiji kunya."

"Shima Mujaheed din dariya yayi ganin yanda Imam yake jansa da raha, Allah ya gani yana matukar kaunar aminin sa , shiyasa bayi da wani aboki ko aminin da yawu ce Imam ."

"Nan suka shiga hiran yaushe gamo, sundauki lokaci suna tattaunawa."

"Mujaheed ne ya dubi a gogon hannunsa yaga time yatafi sosai, mufeedah ce ta fado masa arai."

"Tashi yayi yace kira madam namata sallama nikam zan wuce , nan Imam ya nufi bedroom domin kiran ramlart."

Bayan tafito ne Mujaheed yamata sallama tare da ajiye mata bunch din 1k guda biyu yace asayawa yaran sa sweet duddah ya so haduwa da su amma basu dawo ba.

"Nan ramlart ta shiga masa godiya shiyasa Mujaheed ya ke bala'in burge ta dan ya iya kyautar ban mamaki, abun hannunsa sa bai rufe masa ido ba."

Sallama sukayi da Imam ya shiga motar sa ya wuce.

"Parking yayi abakin wani ShopRite bayan ya shiga ciki ne yafara tunanin me yaka mata yasaya wa mufeedah a matsayin gift, don shi rabonshi da yazo shopping da kansa har ya manta."

"Tunawa yayi da lokacin da yake soyayyah da Marwat tare suke zuwa shopping,nan fa yashiga daukan su turare masu uban tsada, bayan yagama ne yaje ya dauko su chocolate da su biscuit masu bala'in tsada duk wani kayan kamshi da na zaki sanda yasaya, kamar wanda bai san ciwon kudin saba bayan yagama ne yaba su ATM suka cire kudin su."

"A bayan mota ya saka kayan,nan yata da motar ya nufi address din da mufeedah ta fada masa."

"Sanda yazo dedai inda ta kwatanta masa sannan yayi parking, layin yashiga karewa kallo duk gida jen bawasu hadeddu bane sai dai dagani akoi rufin asiri da godiyar Allah."

"Wayan sa ya dauko ya dialling numbern ummah da mufeedah ta tura masa, cikin sauri ya katse kiran tunowa da yayi amatsayin Maman Sadiq suke charting da ita."

"Massage yashiga typing nan ya sanar mata da cewa,,"

"""Maman Sadiq ce na iso ina waje kifito mugaisa."""

"Wayar ta na hannun ummah message din Mujaheed ya shi go ,"

Ummah ce ta kwalawa mufeedah kira tace gachan ba kuwar ki ta iso yanzu tamiki text eh maza kije ki shigo da ita.

"Mufeedah ce tace toh ummah don tun dazu ta sanarwa da ummah ce wa maman sadiq wacce suka hadu a group din SIRRIN YA'MACE zata kawo mata ziyara,nan ummah ta nuna jin dadin ta tace ai ba duka aka hadu aka zama daya ba, ai SIRRIN YA'MACE alkhairii ne ga wanda yagane, gashi nan sai Allah ya sa ku kullah zumunci tun bakusan juna ba har Allah ya sa ku hadu watarana asanadin group din SIRRIN YA'MACE."

"Murmushi mufeedah tayi ita kam tarasa wace irin kauna umman ta takeyiwa wannan group din SIRRIN YA'MACE, da yardar ummah take cikin group din kuma ummah ce take bata shawarwari tana rubutawa acikin comment section."

"Zumbulelen hijabin ta ta dauko sakawa tayi tace ummah bari in mata iso, ummah ce tace toh kiyi sauri kar tagaji da jiranki."

"Mufeedah ce ta juya zata fita jin muryan ummah tayi tana cewa yau kuma babu nikab ne , dan tura baki tayi tace ummah yau fa zamu fara haduwa da ita kuma kinga cikin gida zamu shigo, ai bawani matsala tun da mace ce yar'uwa ta."

Ummah ce ta yi dan murmushi tare da cewa to maza hanzarta .

"Wani irin dogon tsaki baba zuwaira taja, tace ayi dai mugani idon tusa zata fura wuta,sai wani iyeyin saka katon hijabi, andai ji kunya wlh, anyi kyawun dan maciji."

Duk uban kyawun da ake tinkaho da shi an kare a auren malamin makaran wasu kuma haka kaddaran su take daga uwar har yar.

"Ko kallon inda take ummah bata yiba don inda sabo tasaba da halin zuwaira tun ba yau ba, ita bata mata kallon mai cikekken hankali ma shiya sa bata taba tamka mata ba in tana shirmenta."

Sanin cewa ummah baza ta tamka mata bane yasa ta shigewa dakinta tana ta faman sababi ita kadai sai kace mara hankali.

"Muhadu gobe insha Allah don jin yanda haduwar Mujaheed (MAMAN SADIQ) da mufeedah zata kasan ce, ba a fara wasan ba yanzu ne ya mu tsunduma cikin littafin."

SIRRIN YA'MACE

Mrs Alkali

Page

"Mufeedah ce ta fita kofar gidan su , amma wayam bata ga Maman Sadiq ba."

Hakan ne yasa ta yi dialling numbern da aka turo message da shi dazu.

Mujaheed yana zaune a cikin mota yaga wata black beauty ta fito daga cikin wani matsakaicin gida .

"Baya iya ganin fiskar ta so sai, sanye take da zumbulelen hijabin ta."

Ganin sai dube dube takeyi ne yasa zuciyar sa ta raya masa cewa ita ce mufeedah.

"Wayarsa ce tafara ringing, duba wa yayi yaga numbern ta ne, baiyi picking call din ba."

"Tunani yakeyi anya bazai tafi ba kuwa, toh yan zu in yaje yace mata shi ne Maman Sadiq, haba ai abun da kunya."

Yana son

Please Login or Register in order to submit comment