subhanallhi, meya faru
kuma haka? Umma tace, "shidewa tayi ta zube a
sume." to Allah sauwake gamu nan zuwa." Abba
ya binciko Aliyu cikin abokansa yace kaifa muke
jira ka gama sallamar abokanka kazo muje wata
'yar anguwa. Aliyu ya amsa musu cikin
girmamawa, bai tsaya tambayarsu ina zasuje ba.
Aliyu yana gaba kusa da direba, Abba da daddy
suna baya. Direba ya kaisu asibiti, tunda suka
shiga gaban Aliyu yake faduwa, yake tunanin me
kuma ya faru?
Direba ya tsaya suka fito, suka nufi falon asibitin
jikin Aliyu a sanyaye,
yana hango su umma da ummi, ni'ima da sadiya
da hajiya ya fara karanto kalmar "innalillahi
wa'ina ilaihi raji'un.
Daga nan ya rinka tsintar bayanin da ummi take
musu, na abunda ya samu zainab, ran Aliyu ya
baci hankalinsa ya tashi. Bai tsaya sauraron
ummi datake gaya masa likita yace kada a shiga
inda take ba, da saurinsa ya nufi dakin da aka
kwantar da zainab din.
A hankali ya murda kofar ya shiga
da sallamarsa aciki.
Nurse din data ke gadinta tana zaune gefe daya
tana sauraron farkwanta, tana ganin Aliyu tasan
shi sarai, don haka ta mike ta fito.
Aliyu ya tasaya gaban zainab yana kallonta,
yarinyarshi zainab mai kyau da nutsuwa, lallai ta
shiga tashin hankali, yau daya kawai ta rame
haka. Yasa hannu ya shafi fuskarta, tayi fiyau da
ita. Saiya ga takara fari, dan bakinta lebenta
jajaye, siririn dogon hancinta mai tsawo, ga zara-
zaran gashin idonta, baki lafiyayyen gashin girarta
daya kwanta das kan girar.
Ya zame dan kwallin kanta, bakin gashinta mai
tsawo da sheki wanda kullum yake kasancewa
cikin gyara, yaita walwali yana sheki, shiyasa bai
taba hanata zuwa salon ba, yanzu du sati biyu
take zuwa salon, dan ya fuskanci bata damu da
kitsoba saide kalba.
A hankali ya rankwafa kanta ya hada fuskarsa da
tata, cikin kyakyawan lafazi muryansa can cikin
makogwaronsa yace "zeeyta
ki soni don Allah ki kaunaceni, bani da buri
kullum saina yanda zan mallakeki. Zainab kece
rayuwata, tun ranar da kika fado duniya ina
ganinki Allah ya dasa min kaunarki a zuciyata,
kullum kwanan duniya karamin kaunarki akeyi.
Zeeyta ba kya ceto rayuwar yayanki ba, ki
tsamoni daga cikin damuwa ba? Haba zeeyta, ke
kadaice farin cikin rayuwata." aka taba kauren
kofar ya dan ja baya. Likita ne zai shigo, yayi
saurin gyara mata dan kwalinta ya rufa mata
maya fi, wai don kada yaga jikinta.
Likitan yayi sallama, yace, ta farka ne? Yace
mishi a'a ya mika masa hannu suna gaisawa..
YACE kada ka damu idan ta farka normal zaka ganta.
Sai dai don Allah adinga kiyaye wa abunda zai bata mata
rai."Aliyu ya gyada kai, yace "insha Allahu za'a kula.
Abba da daddy suka shigo suka tsaya akanta
suna yi mata addu'a da fatan Allah ya bata lafiya.
**** *** ****
saratu da lawisa sun saka mansura a gaba
sunayi mata fanfo zuga iri-iri, lawisa tace, "don
haka nake gaya miki, ki kula da yarinyar nan,
mutum mai shiru-shiru abun tsorone, kinga yanzu
ta kaiki ta baro. Ta gama sanin sirrinki kaf gashi
yanzu ya aureta ta zamo kishiyarki, wallahi ko
kadan kada ki saurara mata, kada ki barta ta
zauna don ba gidan zama tazo ba.
Kuma wallahi ki fito da kudi mu shiga malamai ki
samo kansa, ki mallake shi tsab. Dai-dai da
uwarsa da ubansa ki rabasu dashi, ya zamo babu
wanda yake gabansa saike da yaronki.
Mansura tace, "um! Wannan uban 'yan taurin kan
zai mallaku ne, tun kwanakin baya fa na kashe
kudi akansa, amma inda kika san dutse haka
yake, kwata-kwata baya lankwasuwa. Kuma
halinsa ne bawai ni kadai yake yiwa hakan ba, ita
kanta yarinyar baki ga yanda yake takura mata
ba. Inta jin tausayinta. Ashe shidai akwai abunda
yake kullawa ransa.
Kiga mutum kullum kicin-kicin dashi ba fara'a shi
ba zai zauna ayi wata hira mai dadi dashi ba
ballantana kiga dariyarsa. Wallahi na gaya miki
sai muyi kwana biyu dashi bama magana, don
haka ma tsani naga yazo garin gwanda yana can.
In nayi magana yace wai dan Allah na rabu dashi
ban iya soyayya ba. Du wayewata yana cewa ban
iya soyayya ba, yanzu daya auri wannan
gidahumar kifin rijiyar aina ga ta yanda zasuyi
soyayyar.
Saratu yayarta tace, to inbanda ke da abunki
wannan ai du shi zai koya mata." mansura tace,
tabdijam wannan, wannan dinne zai zauna yana
koya wa mace wani abu, ai shi inbanda isa da iko
da gadara babu abunda ya iya. Shifa ason ransa
komai saide kayi masa yana daga kwance, tunda
naga sangartar tasa tayi yawa kai tsaye inya ce
inyi masa abu nake cewa bazan iya ba.
Lawisa tace wallahi na gaya miki namiji ba dan
goyo bane, ko uwarka ka yanka ka bashi inya
tashi mantawa zaiyi ya zuba ma rashin mutunci."
saratu tace to ba gashi ya mata ta gani, ta rike
'yar tamkar cikinsu don yankan kauna ya tashi ya
aureta.
Mansura tace shekara takwas ina rikon 'yar nan,
ko shekara banyi gidan miji ba ya tattaro min
rikon 'ya, karshe abunda ya sakamin dashi
kenan? Ai duk zasu ci buhun ubansu, mun saka
kafar wando daya dasu. Wallahi saina rushe
zamansu, basu bajin dadin rayuwar, mu zuba su
gani.
**** *** ****
kwanan zainab biyu a asibiti, tayi bacci ta huta
sosai, don data farka take komawa baccin
zuciyarta ta huta ta samu nutsuwa, ta manta da
abunda ya faru.
Dakin cike yake, da mutanen gidan, zainab ta
farka ta yunkura zata mike, umma ta dagota a
hankali tana yi mata sannu. Zainab tayi salati
tace, "umma meye na ganni a asibiti? Tace ishiru
bakida lafiya ne, zo muje ki wanke bakinki."
ta kamata takaita toilet ta wanke mata bakinta
da fuskarta. Ta dawo da ita ta zauna a bakin
gado 'yan uwanta da iyayenta suna mata sannu.
Ummi ta hada mata shayi mai kauri tana bata da
kofin, mama ta zubo mata farfesun kaza ana bata
tanaci, taci dayawa.
Aliyu ne ya turo kofa ya shigo da sallamarsa, tayi
kur ta zubo masa ido tana so ta tuno wani abu,
shikuwa murmushi yake yi, ya daga hannunsa
sama yana yiwa Allah godiya.
Ta kura masa ido tana kallonshi ko kiftawa
batayi, a hankali abun ya fara taro mata cikin
kwakwalwarta, tabbas abunda taji ba mafarki
bane gaskiya ne, yanzu ita matar yayanta Aliyu
ne da gaske? Hawaye ya fara zubowa a idonta,
ta mike a hankali tana takawa sannu a hankali ta
nufi inda Aliyu yake a tsaye, ta durkusa a
gabansa cikin kuka, ta rike kafafuwansa tasa
kanta ajiki tana kuka, da sheshsheka tana cewa,
yaya, haba yayana yaza kayi min haka? Haba
yaya kaine fa uwata? Yaya yaza ka rikide ka
zama mijina? Yaya du abunda uwa take yiwa
'yarta tunda na rasa mamana kai ka fansheta, ka
juye ta a wajena, ka hanani maraicin rashin uwa,
ka zama kaine uwar tawa. Ya zakayi min haka
yayana? Kaifa mijin auntyna ce, matar da na
dauketa kamar 'yar uwata da muke ciki daya, ta
rikeni da gaskiya da rikon amana, zumunci ne mai
karfi tsakanina da ita.
Yaya ya zakayi sanadiyyar rugujewar wannan
zumuncin? yaya don Allah, yaya don girman zatin
Allah ka taimake rayuwata ka sauwakemin
aurenka ka bani ko waye kaga dama."
dakin shiru yayi bakajin motsin komai sai
kukanta, mahaifinta ya taso yazo ya dagata, yace
"haba zainab ina ganinki da hankali da ilimi, ashe
sun zamo na banza tunda zaki iya cewa mijinki
ya sakeki." tace kayi hakuri daddyna
bazan iya zama da auren nan ba, naci amanar
auntyna, da wani ido zan kalli auntyna? Na
yaudareta naci amanarta, naso kaina daddy,
bazan iyaci amanar auntyna ba."
daddyn yace yau, "zainab yau zan gaya miki
abunda baki saniba, tun kafin Aliyu ya san zai
san mansura mahaifiyarki ta bawa Aliyu ke." ta
juyo a razane ta kalli mahaifinta. Ya daga mata
kai yace kwarai hakane.
Bazan taba mantawa bayan mamanki ta haifi
sadik da
banda lpia ina fatan zky hkri
[9:15AM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 2**7
Bazan taba mantawa ba bayan mamanki ta haifi sadik da
faruk, tana so ta haifi 'ya mace, ita da Aliyu har nafilan dare
sun sha yi da rokon Allah ya bata 'ya mace mai hankali da
nutsuwa da hakuri da baiwar ilimi.
Saboda tunda na auri mamanku Allah ya hada jininsu da
Aliyu, komai nasa a gurinta yake.
Shawararsu daya bakinsu daya. Lokacin da mamanki ta
samu ciki kusan tare sukayi laulayin cikin nan, idan tayi
amai shi zai kwashe ya gyara
wajen, du abunda take son ci shine dan aiken
sayowa.
Ranar da aka haifeki kuwa kiri-kiri Aliyu ya hana
daukanki wai kada asa miki datti da ciwon jiki, du
sanda akace Aliyu ya samu hutu bashida wajen
tarewa sai wajen mamanki yana rainonki. Kina da
shekara daya ya shirya miki birthday. Kina kan
kafadarsa yana yawo dake. Lokacin da ya yanka
cake din yasa miki abaki aka dau tafi, yace Allah
yasa na miki na aurenmu watarana."
mamanki tace, "haba Aliyu, yaushe zakayi jiran
karamar yarinya haka? Yace wallahi mama tun
ranar da aka haifi zainab Allah ya dasa min
kaunarta araina, ni dai dan Allah mama inaso
kimin Alkawari zaki auramin zainab inta girma."
mamanki tace na dau alkawari, in dai har Allah
yayi kai mijinta ne, to ba mai aurenta sai kai, na
baka zainab tundaga yanzu ta zama taka.
To kinji yanda mahaifiyarki ta bawa Aliyu ke, tun
kina 'yar shekara daya. Abunda ya tashi aurenku
kuwa yanzu, yazo mana ne ransa a bace yace
"shidai dan Allah a taso da alkawarin mamanki a
aura masa ke, don yana tsoron samarin da suke
yi miki tururuwa, yaga har kin fara zance. Shiyasa
ya nemi alfarma a hade aurenku data ni'ima.
To yanzu mahaifiyarki tana karkashin kasa ta
rasu, baza kiyi kokari ki cika mata alkawarin data
dauka ba, kinfi so kita barinta da nauyi akanta?
Ta dago kanta tana kuka tace, daddy ko wane
irin alkawari mamana ta dauka akaina zan iya
cika mata shi, na hakura daddy. Kayi hakuri ka
yafe min bata maka da nayi." yace bakomai
zainab, tsakanina dake kullum sai albarka."
***** ****** ****
kwananta uku a asibiti aka sallameta, don taji
sauki. Amma du shigowar da Aliyu zaiyi tana
asibiti nan bata iya dago kanta ta kalle shi bare
tace zatayi masa magana kota gaisheshi,
kunyarsa take ji sosai. Bama inta tuna haidar
shine Aliyu, du tes din kalamomin soyayyar da ya
rinka turo mata da wayar da suka rinka yi ashe
du yayanta ne Aliyu, ita ya zata yi da wannan
abun kunya?
Ita kuwa mansura data ji zainab tana asibiti,
addu'a ta rinka yi Allah isa kada taji sauki a fasa
aurenta da Aliyu.
Da Aliyu yaje dadadare gidansu mansura zai
dauketa su tafi gida, sai tace ai ita ta gama
zaman gidansa, mayaudari maci amana, Allah ya
isa tsakanina dakai! Tunda kaci amanata."
abun ya konawa Aliyu rai, yace ni kike gayawa
wannan maganar? Tace ana gaya maka din
azzalumi! Yace to ya isheki, kada ki sake bakinki
ya kuskure ki zageni, zaman gidanku kuwa kiyi
tayi, randa kika gaji kya dawo." yaja motarsa ya
tafi ya barta nan tsaye.
Saboda kwanciyar zainab a asibiti, an fasa bikin
da kaisu acikin wannan satin sai asabar mai
zuwa za'ayi wuni akaisu dakin mazajensu.
Zainab ta zamo bata da sakewa ko yawan
magana, ko yaushe ka ganta tayi shiru tana
tunane-tunane. Aliyu daya fuskanci kunyarsa take
ji sosai, saiya daina shigowa inda take. Sai dai da
safe d daddare yayo mata tes yace kici abinci fa,
kinsan bana son zama da yunwa.
Ya karashe mata tes din da kalaman soyayya
masu sanyaya zuciya. Takan girgiza kai tace, "kai
namiji, ba ruwanshi da kunyar abunda yake so.
Wai yayanta Aliyu shine yake mata irin wannan
kalaman soyayyan, baya jin nauyinta bare
kunyarta.
Yaita aiko mata da cimarta ko yaushe, abubawa
da yasan tafi so,
suna zaune a falo ita da ni'ima, wayarta tayi
kara, ta duba ta gani saita kyaleta taita burarinta
harta gaji ta tsinke don kanta, amma sai aka
sake bugowa.
Ni'ima ta dago kai ta kalleta, tace ki dauka mana
dan Allah, nasan bazai wuce yaya ba." ta girgiza
kai tace bashi bane." ni'ima tace to ki dauka
mana."
ai ban san mezan ce masa bane.
Ni'ima tace ki gaya masa abunda ya faru kawai
kada yaga kin yaudareshi."
tana daf da katsewa ta dauka, a sanyaye tace
"hello! Daga can nura yace ai dole kiki daga
wayata, kunya ma ai ta isheki.
Wato zainab ina ganinki simi-simi kamar ma
hankali, ashe azzaluma ce ke, kin yaudareni.
Kinsan saurayinki ne aurenki zaiyi kika binneni a
cewar yayanki ne a hannunsa kike, ashe
masoyinki ne.
Zainab idonta ya fara zubar da hawaye, tace ba
haka bane, don Allah nura ka saurareni kaji.
Karaf a kunnen Aliyu daya shigo dakin a yanzu,
tuni hanjin cikin zainab ya hautsina, tuni ta rikice
ta kasa cewa komai, wayar tana manne a
kunnenta tanaji nura yana gaya mata
maganganu.
Aliyu ransa ya baci, ya rinka wani huci ya karaso
inda hankalinra ya tashi, ta rintse idonta tana
jiran saukar mari. Yasa hannunsa akan nata
hannun da yake kange a kunnenta, ya zare wayar
, ya daka masa tsawa kai wawa shasha! Kana
sane da matar aure kake waya? Wallahi kayi na
farko kayi na karshe...
Bakwa comments ko likes don haka zanyi daina wahalar da kaina may be littafin bai muku bane shiyasa nayi typing kadan ma.
[9:16AM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 2**8, 2**9 & 2**10
DU sanda ka sake yiwa matata waya saina daureka bbu
beli. Kuma yanzu ma ka saurari zuwan kana nan sojoji,
zasu zo su koya maka
hankali." ya cire wayar da kunnansa yayi cilli da ita ta daki
bango ta tarwatse, ya karasa gurin ya ciro sim card din ciki
ya kakkarya shi gutsi-gutsi ya
watsar a wajen. Ya dago kansa yana mata wani
irin kallo, yace wannan ya zamo na karshe, idan
na kuma gani kina waya ko kina magana da wani
sai ranki ya baci." ya juya ya fita.
Ta dafe kanta tana kukanta. Ni'ima ta dawo
dakin da tun shigowar yaya Aliyu data ga sababin
da yake yi ta zame jikinta ta gudu, don kada ya
huce akanta."
ni'ima ta zauna kusa da ita ta dafa ta, tace meye
na kuka, ke matsalarki kenan saurin kuka."
tace, haba yaya ni'ima, kin san sarai yaya Aliyu
ya fiya saurin fushi da zafin zuciya, ni kuma bana
so naga bacin ransa balle kuma ace ni na bata
masa, taya za ayi zaman aure a haka?
Ni'ima tace haba zainab kefa mai hakuri ce zaki
iya zama da yaya Aliyu, don kinfi kowa iya gudun
bacin ransa. Ni sai yanzu ma na fahimta ashe du
tsanani da yaya yake yi miki soyayya ce da
kishinki da yake yi, ni wallahi ban taba ganin
amarya da ango da suka dace da juna ba irin ke
da yaya."
idonta yayi narai-narai hawaye ya sake zubowa
tace, "ke yaya ni'ima haka zaki rinka yi min?
Ta fashe da kukanta. Ni'ima ta rungumota tana
rarrashinta, "to shikenan kiyi hakuri na daina, ba
zan kuma ba."
du wayanci kawayen zainab ta gayyace su bikin
ni'ima, to da abun ya zamo haka ya hade da
nata, sai babbar kawarta hauwa Rabi'u ta rinka
yiwa kawayensu waya tana sanar musu tare da
basu hakuri na rashin ganin kati. Du da haka
saida Aliyu ya sanar a gidajen radio, saboda na
nesa kawayenta da basu sani ba.
Ranar jumma'a akayi mata kamu, kamun da ya
bada mamaki saboda cikar kawayenta da 'yan
uwanta suka yi, sai da aka fara saukar Qur'ani
sannan aka kamata."
daga nan wata malama ta bude filin da dan
wa'azinta (kusan hakkin miji akan matarsa ne
wa'azin kuma inaga munyi a baya basai na
maimaita ba).
Malamar nan tai ta wa'azi da fadakarwa akan
aure, wanda tunda aka fara zainab take kuka, dan
jikinta har rawa yake yi. Du da tasan hakkokin
miji akan matarsa babu abunda malamansu na
islamiya basu koya musu ba, amma wa'azin
malamar nan ya shigeta.
Yanzu taya zata hada jiki da yayanta Aliyu harta
kwanta gado daya dashi? Ya salam! Allah kaika
san abunda kake nufi da auren nan, Allah ka bani
ikon biyayya ga mijina.
Ranar asabar tun asuba akayi wa zainab da
ni'ima gyaran jiki, inda jikinsu ya fara laushi da
tsantsi, fuskarsu kuwa kamar kwan lantarki dan
kyau.
A wajen walima shiga iri daya akayi musu, wani
dankareren abu me kyalli da walwali pink, da
gwagwaro pink, dutsen da suka sa a hannu da
wuya duk pink, takalmi da jaka duk pink, sunyi
kyau sosai.
Walimar ta tara kyawawan 'yan mata gogaggu
masu takama da ayar Allah.
Domin ayau ma wani wa'azin aka kuma yi mai
shigarwa, daga nan wani babban malami yayi
lakca wadda ya ladftar da zuciyar mai saurare, ya
dasa tsoron Allah a zukatan wanda suka saurara.
Daga karshe aka rufe da addu'a, aka yiwa
angwaye da amare addu'ar Allah basu zaman
lafiya. Amaren suka rinka zagaye tebir-tebir suna
gaisawa da kawayensu, suna yi musu godiya da
damar da suka samu ta hallartar bikinsu.
Aunty sadiya tana ta raba manyan bokitai da
farantai, da kofunan shayi na tangaram. Sun so
yin kalanda, Aliyu ya hana wai baza aje a lika
masa hoton matarsa a wani waje ba, wani gardin
ya kalleta yayi sha'awarta ba.
Da mangariba daddyn zainab ya kira Aliyu ya
tambayeshi ya maganar mansura? Aliyu ya gaya
masa yanda sukayi, yace randa ta gaji da zaman
gidan nasu saita dawo.
Daddy yace, "ashsha haba Aliyu yaushe zaka
daka shirme na mata, ai hakuri zakayi ka
rarrasheta tunda kai ka tabota, kayi mata laifi
babba, don su mata wannan shine babban laifi da
zakayi wa matarka."
don haka ni yanzu zanje wajen babanta mu
tattauna na bashi hakuri kai kuma da daddare
saika je ka tafi da matarka."
Aliyu ya rissina ya amsa masa tare da yi masa
godiya.
Daddy yayi sallama gidan Alh haruna, alh ya fito
da fara'arsa, ya bude dakin saukar bakinsa suka
shiga, bayan su gaisa daddy yake cewa, "nazo
bikon mansura ne, na tambaya dazu aka cemin ai
har yanzu tana gida bata koma dakinta ba."
Alh haruna mutumin arziki, yace kasan halin mata
sai hakuri, hauka tayi masa yace tayi zamanta a
gidansu. To in banda rashin hankali ma ya za'ayi
da hukuncin ubangiji. Allah ya kaddara hakan tun
fil azal, towa ya isa yaja da hukuncin ubangiji?
Daddy yace"hakane fa don wallahi naso na sa shi
ya hakura da auren zainab ya rinka yi min
magiya dana hakura na kyaleshi, to ya za ayi da
hukuncin ubangiji. Don Allah kuyi hakuri Alh, in
ajima Aliyu zai zo ya duketa su tafi gida." Alh ya
washe baki yace, wallahi bakomai saiya zo din."
da Aliyu yazo Alh ya hadasu da mansura yayi
musu fada. Ya dauko mansura suka taho gida.
Tunda suka taho take yi masa kuka, yace "haba
mansura, kin san bana son kuka, laifi ne kince
nayi kuma na baki hakuri ba sai ki yafe minba."
LAIFI ne kince nayi kuma na baki hakuri basai ki yafeni ba."
niba wani wallhi, ai kasan ka zalinceni, haka kawai saikoyo
aure bakamin kayan fadar kishiya
ba, kuma baka canjamin kayan daki ba." yace kiyi hakuri,
idan nagama ginina wanda zan
hadeku waje daya saina canja miki, kayan fadar
kishiya kuwa ga akwatuna biyu can da kudi dubu
dari suna dakinki na ajiye miki."
sannan tayi shiru tana Allah-Allah suje gida taga
irin kayan da yake cikin akwatunan. Suna zuwa
gida shiya bubbude mata akwatunan ta gani,
kaya masu kyau da daraja da tsada, kala goma,
super, holland,leshi, shadda,ingila, diamond,
takalma uku, mayamayai da turaruka da
sauransu.
Ta zumburi baki tace ita kala nawa kayi mata?
Yace, "ba abinda ya shafeki bane wannan, tace
dama mana kace haka, kaci amanata na rike
yarinya ta gama sanin sirrina ka aureta." ya daga
mata hannu yace, "ki rinka yiwa bakinki linzami,
tun kafin nasan zan hadu dake nake son zainab,
tanada shekara daya aduniya mamanta ta bani
ita. Shiyasa lokacin da mamanta ta rasu na dawo
da ita gidana gabana don nasa ido sosai akanta
kada wani ya hure mata kunne. Yayi ficewarsa ya
barta ta dora hannunta aka tana zunduma ihu.
Ranar lahadi akayi wuni ni'ima taci kwalliyarta,
tna cikin kawayenta sunata hotuna da bidiyo.
Zainab kuwa tana cikin dakin hajiya tana
kudundune tanata aikin kukanta, sadiya ta shiga
ta dagota, "haba zainab wai miye hakane, yanzu
du kaunarku da yaya don an aura miki shi kike
kuka irin haka?
Tace, yaya sadiya aunty mansura fa marikiyata
ce, kuma saina juye na zama kishiyarta."
to meye ba haka Allah ya shirya ba. Ta lallabata
tayi wanka, ita ta shiryata ta dandasa kwalliya
cikin wata dakakkiyar galila da akayi mata dinkin
bubu, ta aikatu da surfani ta nada mata dan
kwalin shaddar kamar nadin gwaggwaro.
Tasha gwal tanata sheki, ta fito da ita zuwa
babban falo, mutane sai guda suke suna binta,
maroka kuwa sai wasata sukeyi. Sadiya ta fito da
kudi tana watsa musu, ta zaunar da ita. Ni'ima
tazo ta rungumota tana cewa, "haba my sister ko
kefe. Kawayenta du sunzo sun zagayeta ana yi
mata shekiyanci, bata iya cewa komai sai
hawaye.
Jikinta kuwa ya dumame da zazzabi, aunty
sadiya ta bugawa Aliyu waya, yana dauka tace,
"hello yaya, dama cewa nayi zainab ce ba lafiya
take fama da zazzabi, shine nace ko zaka bari a
barta a gida inta samu sauki akwota? Yace dan
Allah gafara can, inkun ajiyeta a gidan me zakuyi
mata inbanda ku dameta da sannu-sannu. Kunga
ku kawo min matata na bata kyakyawan kulawa."
tace "a yaya haka za'ayi?
Yace ku bata waje ta kwanta ta huta kada kusa
mata ciwon kai, bana so kudameta da hayaniya."
'yan wajen suka sa ihu da dariya.
Zainab kuwa ta dafe kai data ji yana sara mata.
Da daddare akayi jerin gwanon motoci, sai aka
raba jama'ar biyu, rabi zasu kai zainab da
kawayenta rabi kuma zasu kai ni'ima da
kawayenta.
Ankai ni'ima janbulo kabuga, gidanta babba mai
kyau ita kadai abunta, zainab an kaita nasarawa
G.R.A gidanta mai kyau zaman mutum daya,
fadan kyaun gidan bata lokacine. 'yan kawo
amarya sun zagaye ko ina kowa sai santin gidan
yake. Da yanda aka tsara komai, gashi ba wani
babba bane tsarin turai ne komai, 'yan kawo
amarya zasu tafi zainab ta kankame aunty sadiya
tana kuka.
Sadiya ta rasa yanda zatayi mata saboda yanda
taga jikinta yana karkarwa, yayi zafi zau, zazzabi
ne mai zafi. Sadiya tayi mata dabara tace "zauna
anan na samo miki magani da ruwa a kicin.
Ta zaunar da ita a bakin gado ta fice da sauri
tana kuka, bata ankara ba taji gidan shiru alamar
kowa ya fashe kenan. Ta dora kanta kan filo taci
gaba da zubar da hawaye, kanta yanata sara
mata, ta dora hannunta akanta ta dafe shi.
Aliyu yayi sallama cikin sanyi muryarshi, du da
tasan muhimmacin sallama amma saita kasa
amsawa, saboda wani irin rudani data shiga, itace
yau da yaya Aliyu a daki daya, daga ita saishi a
matsayin matarsa ta aure. Ko ina auntyn nata?
Yanda dai taji anata zugugun gidan tasan ba
gidan da auntyn take ya kaita ba. Yazo ya zauna
a bakin gadon, ta zame kasa tace, yaya ina wuni?
Ya dagota "lafiya lau zainab ya taro? Tayi shiru
tana sheshshekar kukanta. Yace zainab kiyi
hakuri nasan bakya sona, kada kiga na takuraki.
Zainab tsananin kaunar da nake miki bazan iya
bawa wani aurenki ba, saina ga kaman zai cutar
min dake. Kiyi hakuri zainab kidaina yawan kuka,
bana so ki jawowa kanki matsala, a sannu a
hankali wata rana zaki soni, kinki zeeyta?
Ni jininki ne dan'uwanki ne, ki daina damuwa
akaina kinji babyna."
yana dan bubbuga bayanta na rarrashi, ya shafa
cikinta, "kinga cikinki kwalam kina zama da
yunwa, bana son zamanki da yunwa kada olsa ta
kama minke.
Ya jaeo ledar kusa dashi yana zaro katon nadin
takarda, gasassun kaji ne guda uku, sai robobin
youghot da ice-cream, ya yago naman zaisa
mata abaki ta kauda kai, cikin sigar rarrashi yace
kinga, "kinsan bana son gaddama, ki karba kici."
ya rinka bata tana ci, a zuciyarta kuwa tunani
take yi, wai dama yaya Aliyu zai iya rarrashin
mutum da lallabashi haka? Yau babu wannan
fadan da hargagi na yaya,..
YAu babu fada da hargagi irin na yaya, sai wani ji
yake da ita. Lallai namiji kenan.
Ta kifa kanta a jikin gadon saboda yanda taji
yana sara mata kamar zai rabe biyu, yace zeeyta
mene ne? Ya dagota yaji jikinta zafi zau, yace, ya
ilahi. Yanzu zeeyta bazaki daina sama kanki
damuwa akaina bako? Ta rinka lumshe idonta
yana kokarin rufewa, saboda azabar ciwon da
kanta yake yi, Aliyu hankalinshi ya tashi, ya
kwantar da ita ya mike ya shiga kicin ya debo
ruwa awata a silba, ya taho da hankicif.
Ya kwantar da ita a cinyarsa ya cire mata rigar,
sai farar shimi mai kyau a jikinta, ya rinka tsoma
hankicin a ruwa yana goga mata jikinta. Sannu a
hankalin zafin jikin nata ya fara raguwa, ya bata
magani tasha, ya barta daga ita sai bes da siket,
ya shimfideta a gado ya mike ya koma kicin don
ya mayar da kayayyakin ciki, ya jere ice-cream
din da youghot din a firij, ya shiga dakinsa ya
fada toilet yayi brush, ya saka kayan bacci ya
koma dakin bayan ya rufe ko ina, ya tofe ko ina
da addu'o'i ya hawo gadon. Tuni ta dade da fara
bacci, ya dagota ya dorata akan kirjinsa ya
rungumeta, a zuciyarsa ya ringa jin wata irin
nishadi, wai yau shine rungume da zainab dinshi,
ashe zaiga wannan rana? Ashe wannan lokaci
yana nan zuwa gareshi? Yaso suyi sallah raka'a
goma sha biyu don nuna godiyarsu ga Allah, to
matsalar rashin lafiyar zeey dinshi hankalinshi ba
akwance yake ba.
Zainab ta dan motsa, ya rinka jijjiga ta yana
lallabta kamar yarinyar goye, da yake zazzabi ya
sauka baccinta take yi sosai.
Sai wajen asuba ta farka, tana jinta rungume
ajikin yayanta Aliyu du kunya ta dame ta, tana
kokarin zame jikinta daka nasa sai ji tayi ya sake
kankameta, dole ta hakura amma du kunya ta
isheta, ta kasa wani kwakkwaran numfashi.
Saida akayi assalatu sannan ya shimfideta a
gadon, ya rada mata akunnanta, "ki tashi kiyi
sallah ni zan tafi masallaci.
Ita kunyarsa take ji sosai, bata iya amsa masa
ba, ya fita ya nufi dakinsa ya shiga toilet ya
daura alwala, ya fita masallaci.
Ta mike tana mamakin yaya Aliyu, daman haka
yake? Tayi alwala tayi raka'atul fijir, ta tashi tayi
sallar asuba, ta gama laziminta ta daga hannu
sama tana addu'a, Allah ya basu zaman lafiya,
Allah ya hada kanta da kishiyarta yaya Aliyu Allah
ya kara buda masa, Allah ya bashi ikon yin adalci
a tsakaninsu. Ita kuma Allah ya bata ikon yin
biyayya ga mijinta.
Tana cikin yin addu'a yaya Aliyu ya shigo, sai ya
huce dakinsa. Tayi sauri ta shafa addu'ar ta
koma dakinta saita rufe kure kofofi, don ita a
tunaninta da wani ido zata kalli yayanta.
Daya taba kofar tata yaji ta rufe, sai yayi
murmushi kawai ya koma dayan dakin ya kwanta,
sai sannan ya samu bacci mai karfi ya daukeshi.
Karfe takwas ta tashi ta shiga wanka, ta shirya
cikin riga da siket na shadda ruwan goro dinkin
stayil ne, anyi mishi hawa-hawa kamar asabari,
an zuba dutsuna aciki yana ta walwali. Farar
fatarta tayi das aciki, ta hade kananan kalabar
kanta tasa ribon ruwan goro ta daure, ta feshe
jikinta da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 14