Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [8:06AM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO-1 PG-1 Kanal Aliyu Gwarzon jarumin soja kenan, Alhaji Yahuza shi ne mahaifinsa, matansa biyu da 'ya'ya biya. Hajiya Habiba ita ce uwargida, da 'ya'yanta uku. Aliyu shi ne babba, sai Sani da Sa'adiya. Sai Hajiya Talatu me 'ya'ya biyu, Ni'ima da Hamza. Dukkaninsu kansu a hade ya ke, da ya ke sun sami tarbiya sam babu yan ubancin nan bare nuna banbanci a junansu. Alhaji Safiyanu kanin Alhaji Yahuza ne, uwarsu daya ubansu daya, matarsa daya Hajiya Saude, da 'ya'yansu uku, maza biyu Faruq da Sadiq, sai karamar su mace mai suna zainab. Babban gida ne kowanne da bangarensa, gaba dayansu akwai kyakkyawar dangantaka da son juna a tsakaninsu. Mahaifiyarsu Hajiya Babba, ita ma a gidan ta ke bangarenta daban. Dattijuwar arziki ce me addini da ibada, ga ta da kokarin zumanci, du inda ta ji dan'uwanta wanda ko kaka dangantaka ta hada su, sai ta jawo shi jikinta ya ci arzikinta da na 'ya'yanta. Hajiya kyaftin kenan dattijuwar arziki, ko yaushe jikokinta suna tare da ita tana hada kawunansu, tana yi musu nasihohi da tattausar murya, ta rinka yi musu tarihin Annabawa da abubuwan da ta san za su karu dasu, su kara samun fahimta ko da a makaranta ne. [1:15PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**2 Yace, kai hajiya, kin matsanta min da maganan auren nan, wai ke bakya kishina ne? Tace ni ai indai akan wannan ne banayi, ka samo min abokiyar zama, idan kuma kai bazaka iya ba ni na samo maka." hajjaju kenan, za'a nemo in Allah ya yarda. Tace dakai wani ne saika samo a hadaka da 'yar uwarka sadiya, tunda kaga ansa rana data yi candy za'ayi aure insha Allahu." yace kai hajiya, kedai kina son hada sabgata da yaran nan so kike su rainani ne? Tace, "ai kaji sha'anin naka, sai son girma kamar gyambo, yo meyesa baka nemo tuni kayi ba? To bari kaji na fada maka, ko ka nemo yarinyar da kake so ayi auren kafin bikin sadiya, ko kuma ayi auren lokaci daya da sadiya." ya mike yana dariya, "hajaju kenan, kin taba ji anyiwa namiji auren dole? Tace za a fara shi kuwa daga kanka." hajiya dai da gaske take lamarinta, don ta matsu taga Aliyun yayi aure, tana so ya kara samun daraja da mutunci a gun iyayenshi, saboda Aliyu yaro ne nutsatse mai hankali da nutsuwa, yana da biyayya. Du abunda iyayensa suke so shi za yayi. Du da karancin shekarunsa yanada halin ya kamata, shiyasa ya zama abokin shawarar iyayensa. Karfe shidda na yamma direba ya kwaso 'yan makaranta tun safe. Da yake zainab a firamare take, karfe daya ake tashinsu, to saita shiga lesson na awa daya, karfe biyu take fitowa sannan antashi su sadiya da ni'ima da suke 'yan sakandare. To sai suyi sallah direba ya kawo musu abinci suci, sai kuma shiga islamiya data ke duk a cikin makarantar. Karfe hudu zasu fito sallar la'asar, suyi dan ciye-ciyensu su kuma komawa aji, sai karfe shidda za'a tashesu suyo gida. Yau direba yana tsayawa zainab ta bude ta fito tayi bangarensu, kicin ta nufa don tasan mamanta tana kicin ita da 'yan aikinsu don gudanar da girkin dare. Hajiya saude ta tari 'yarta da murna tana cewa, "sannu da zuwa auta." ta rungumeta suna dariya ta cika uwar tata ta nufi firiji tana cewa, wallahi mama yunwa nake ji." ta bude firij tace kai mama ina vanilla ice-cream dina? Mama tace a'a zeey bana son rigima, ba tun jiya kika gama shanye naki ba? Tace "to mama bana sa ragowar dayan a firij ba." tace to ai kuwa dashi sadik ya tafi makaranta da safe. Zainab tanajin haka ta yarda jaka ta hau tsalle da ihu tana kuka, "wallahi saiya biyata ice-cream. Faruk da sadik suka shigo duk da goyon jakunan su, suma nasu direban ya dauko su, don makarantar matan daban ta mazan daban aka sakasau. Tace "wai ice-cream dinta tasa a firij waye ya daukar mata a cikinku. Faruk yace "mama ai sadik ne ya tafi dashi makaranta." sadik yace ai banaki bane ragowa ne na dauka da zaki kama yiwa mutane kuka." tace "to bani nasa shi a firij ba kaje ka dauka min ba, wallahi sai biyani abuna." taci gaba da kukanta tana tsalle. Aliyu yana dakinsa ya ringa jiyo ihunta, ya shigo da sauri yana cewa lafiya? Me akayi mata mama? Tace rigimar data saba ne kawai, ice-cream ne du sunsha roba dai-dai, ragowar daya ne wai ta dauka tasa a firij shikuma dan uwan dayan abokin yin nata ya dauke ya tafi makaranta dashi ya shanye, shiya kawo wannan rikici nata." ya daka mata tsawa, "tashi zaune." ta mike a razane tayi daki da gudu. Dai-dai lokacin ni'ima take shigowa take cewa "wallahi yaya ko abinci bata ci a makaranta ba sai youghot me sanyi ta rinka siya tana sha wuni guda, yaya sadiya tai ta mata fada ta kwace youghot din ta siyo mata meat pie da yambos, saida taga zata daketa sannan taci. Aliyu yace a'a ba akai muku abinci bane? Tace, "ankai mana mana, bata cin abinci sai kayan zaki dana sanyi take sha." ya kwada mata kira da karfi, "zainab kina ina? Ta fito daga falon da sauri ta rabe a waje daya. Yace maza ni'ima shiga kicin ki zubo mata abinci ina zaune ta cinye shi. Ni'ima ta zubo mata abinci ta dire a gabanta, Aliyu ya daka mata tsawa dauki ki cinyeshi. Taja filet din ta fara cin abincin, tsoronsa take ji sosai, don tasan baya wasa. Yace ki cinye shi du idan kika rage ko kaka nida kene. Ya juya ya fita, ya sami direba a waje ya bashi dubu biyar, yace yaje bakori ya siyo masa ice-cream da youghot masu sanyi, da gashashiyar kaza guda biyu." ya wuce dakinsa. Zainab kuwa tana zaune tana kuka tana tura abincin, saida ta cinye tas sannan ta tashi tayi daki ta kuka, me aikinsu ta bita tana rarrashinta, ta hada ruwa a baho, ta cuda ta sannan ta kyaleata ta karasa wankan da kanta ta dauro alwalar sallar magariba, tana cikin shiryawa taji sallamar direba da yake kaisu makaranta. Mama ta amsa masa, ya shigo ya durkusa yace, "gashi mama inji yaya Aliyu, na zainab ne. Maman ta karba tana budawa, tace "Aliyu kenan, ai shine ma ja gaban sangartar da zainab, don daman can shiya koya mata irin wannan cimar bata damu da abinci ba, gashi ta fara girma abu yana nema ya zame mata jiki. ta kwala mata kira, ta fito da sauri tana cewa "mama me yayan ya kawomin. Ta tura ma kayan, gashinan 'yar lelen yaya. ta fito ta kama dubawa, robar yght guda shida, ice-cream guda shida, gasassun kaji guda biyu, ta dauki robar ice-cream da nono dai-dai ta saka a firij, tace wlh mama kada ki bari sukuma daukar min. surayya [1:16PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**3 MAMAN ta bata kaza daya da youghot guda uku, ice-cream guda uku, gashi nan saii tafi gidan hajiya ki hadu keda 'yan uwanki mata da mazan tunda suna can kuci, wannan kuma in na nashiga wajen su hajiya cin abinci maci acan." zainab ta dauki ledar tayi bangaren wajen hajiya, ta shiga da sallamarta, ni'ima ta tarota tana dariya tare da cewa, "sai 'yar gidan daddy, me kika samo mana. Tace, "ai bazaki ciba tunda kika sa aka sani cinye abinci." tace haba yi hakuri 'yar kanwata, kinsan tsakaninmu bata baci." sadiya ta karbo kayan tace, bawanin kunyi fada da ita dani take shiri." gaba daya suka hadu suna cin kazar da youghot din da ice-cream din. Ahaka Aliyu ya shigo ya sami kujera can nesa dasu yana duba jarida. Zainab tasa jummai mai aikinsu ta dauko mata jakarta ta islamiya tana son yin hadda, don gobe malaminsu yace su zo masa da haddan Arrahaman izu bakwai. Ta bude Qur'ani ta bawa hajiya, tace hajiya rikemin nayi hadda, gobe malam yace muzo masa da hadda, du wanda bai iya ba zai sha bulala. Hajiya ta rike mata Qur'ani ta fara karanto Arrraman cikin kwararen larabci irin wanda ake koya musu a islamiyasu, da yake tana da zakin murya, gashi ta iya fitar da kowane harafi, ta iya rera karatun da kome kake yi in kaji saika tsaya ka saurareta. Aliyu ya lumshe ido yana mai jin dadin karatun nata, a ransa kuwa fassara suran yake yi yana fasalta mata 'yan aljannan da Allah ya yiwa rahama. Tana kaiwa karshen suran tace Alhamdulillah, na haddace a kaina." hajiya tace "barakallahu fik, kin wuce dukan malam." hajiya tace shiyasa nake sara miki mutuniyata shagwabarki bata damuna tunda akwai ki da kwakwalwa mai kyau, du abunda aka gaya miki kya dauke shi a kanki. Sadik yace "iyayi dai da neman suna wai ita ace mata mai ilimi." zainab tace toh ilimi karyane? Ai ilimi shine kan gaba a rayuwar dan Adam. Ilimi lallai ne mace ya kasance tana kula dashi, ilimin addinin ta da kuma ilimin rayuwa. Misali, bari na baka misali da kowanne. Ilimin addini don tasan yadda hukunce-hukunce sallah, tsarki, jinin al'ada, jinin biki da dai sauransu. Ilimin rayuwa kuwa, don kanta ya waye ya kasance tasan abunda yake faruwa a duniya, koda ta sauraron ko radiyo, kada ace mace bata san sunan gwamnan garinsu ba, ko shugaban kasa. Kinga akwai karancin wayewa a wajenki kenan. Ilimi wani abune da yake karawa mutum daraja, Allah mai girma da daukaka yace "Allah ya shaida lallai babu abun bautawa da gaskiya sai shi." kuma mala'iku ma'abota ilimi sun shaida yana tsayar da adalci mabuwayi mai hikima. Kaga saboda muhimmacin ilimi a wannan aya, sai Allah ya ga hada shaidarsa data mala'iku da kuma ta masu ilimi. Ashe du wanda ba malami ba, ba kuma mai neman ilimi ba, toh bai cika cikakken mutum ba. Haka kuma annabi ya fada acikin wani hadisi, "duk wanda Allah yaso shi da Alkhairi, saiya fahimtar dashi Addini." haka kuma yana cewa, "neman ilimi farilla ne akan kowane musulmi namiji ko mace. Kuma Darajar farko idan ance ilimi shine ilimin addinin musulunci,sai kuma ilimi na rayuwa, kamar su ilimin likita, injiniya, siyasa, mu'amala da dai sauransu. Daraja da kimar 'ya mace tana karuwa gwargwadon yadda ta kula da iliminta, kamar kuma yanda darajar da kimarta take lalacewa a wulakance sakamakon yanda taki yin ilimi." mace ta gar itace wadda kunya bata hanata neman ilimi, ilimi na addini kona rayuwa. Ka duba ka gani, nana Aisha matar manzon Allah (S.A.W) du da yarinya ce karama, domin har annabi ya bar duniya shekarunta sha takwas ne, amma tayi gwagwarmaya da maza wajen haddace hadisan Annabi (S.A.W), domin itace ta hudu a cikin mutane bakwai da suka fi kowa haddace hadisai annabi acikin sahabbai. Kaga wannan yana nuna kulawar mata da ilimi kenan. To kada kuma yi min zargin son gwaninta ne yake sani yin karatu, a'a inason yin koyi da nana Aisha ne, don nima inaso na zama mace ma wadatatcen ilimi. Hajiya tace Allahu akbar, Allah ya baki ikon yi. 'yan'uwan suka sa mata dariya, tare da cewa sai auta. Aliyu yarinyar yaji ta burgeshi, ta kara shiga ransa sosai, yanda take da kyakyawar kwakwalwa ya kamata abarta tayi ilimi mai zurfi don ta zama wani abu gaba. Iliminta ya amfani sauran al'umma. Washe gari yaya Aliyu sammako yayi ya koma kaduna bakin aikinsa. Cikin hukuncin ubangiji sai ga mama da ciki, don ita harta fitar da ran sake haihuwa, to ta ga zainab shekara bakwai harda wata uku. Sannu a hankali hajiya tana matsawa aliyu da maganar aure, shifa ya gaya mata bashi da lokacin da zai tsaya duba matar da zai aura, ita tace "to ta nemo masa, don ita tanada lokaci. Du da akwai gidan makocinsu Alh haruna, 'yar gidan mansura ita take mutuwar son Aliyu, du sanda yazo tai ta shige da fice kenan a gidan, ayi masa soye-soye na kayan dadi akawo masa, amma baya kulawa saidai kannensa su cinye, hajiya ta zuba tukuici. Duk yanda mansura taso taja ra'ayinsa don ya sota, ya rinka sauraranta bata isa ba, ko kallonta ba yayi saboda miskili ne. Ita kuwa hajiya taga tayi tayi dashi ya samo matar da zai aura ya kasa, suka nema masa auren mansura. Surayya Abubakar [1:16PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**4 SUKA nema masa auren mansura. Alh haruna mahaifinta yaji dadi, inda yace a hade sa ranar data yaya sadiya ayi biki gaba daya." da mansura taji wannan labarin kamar ta zuba ruwa a kasa tasha don zumudi da murna. Shikuwa yaya Aliyu ya hakura ne ya yarda don bashi da yanda zaiyi, tunda iyayensa da kakansa sunfi karfinsa. Yaya sadiya sunyi candy a ranar suka yi fatin candy, kawayenta da 'yan makarantar sun shayin hotuna harda bidiyo caset don dai tarihi. Sun kakkarbi adireshin junansu da lambobin waya, don dai su rinka tunawa da juna suna sada zumunci a junansu. Satinsu biyu da candy yaya sadiya ta fara rabon katin bikinta. Inda itama mansura ta ke raba nata katin bikin ga kawayenta da 'yan uwa. Haka yaya Aliyu anbawa sani ya kai masa katunan can kaduna, yanata rabawa abokan aikinsa da abokan arziki. Ranar alhamis akayi kamun mansura, ranar jumma'a akayi kamun yaya sadiya. A ranar yaya Aliyu ya dira daga kaduna, da wasu tawagar abokanan nasa da yayi musu masauki a daya daga cikin gidajen iyayensu. Washe gari ranar asabar akayi daurin aure, gaba daya ankon galila shadda suka matsa, da hadadden dinki yi mata na aikin saa. Du ita suka sa, saida akaje gidan su mansura aka dauro auren yaya Aliyu, sannan aka daura auren yaya sadiya, daga nan maroka suka shiga busa da kade-kade, su Alh suka shiga rabon kudi ana watsawa maroka kudi. Haka abokanan yaya safiyanu mijin sadiya, sukai ta watsawa maroka kudi. Karfe hudu dai-dai aka shirya walima, kawayen yaya sadiya da kawayen mansura, abokanan yaya Aliyu da abokanan yaya safiyanu, du sun ci kwalliya ta kece raini, hadaddun 'yan mata gogaggu, wannan ta wace wannan, wannan tana wace waccan, sun sha ado da kwalliya. A harabar gidansu akayi da yake farfajiyar katuwa ce, an kafa rumfuna aciki an zuzzuba kujeru farare acikin rumfar. An ware gunda Aliyu da mansura, safiyanu da sadiya zasu zauna. Anyiwa wajen ado da fulawoyi da roba balan-balan, an wadata wajen da amare da angwaye, sunyi kyau kamar fulawa aka dasa dan kyau. Ni'ima 'yar shekara sha hudu ta fara zama budurwa, domin makerin budurci har ya fara kerata. Tayi kyau ta ratso cikin tsakiyar filin gurin da lasfika take, ta dauki lasfikar tace, "ansuturillah." ta fada sau uku, jama'ar sai kowa sukayi shiru suka zuba ido. Ni'ima ta kalli inda iyayenta suke taga daddyn zainab da Abbansu, shigarsu iri daya. Haka iyayen su mata duka su ukun shiga iri daya suka yi. Ta kalli jama'a taga kowa yayi shiru ya nutsu ya zuba mata ido. Saita ce "muyi salati ga annabi." gaba daya suka ce (s.a.w)." bayan an gama karantawa tace, "ya shafi sha biyu, Allah ya shafe du wata fitina da zata kunnowa ma'auratan nan." gaba daya akace ameen." bayan angama tace Ayatul kursiyu kafa uku, Allah ka karemu ga mugun ji, mugun gani, sharrin mutum dana Aljan, da sharrin duk wani abunki. Allah ya basu zaman lafiya, Allah ya basu zuri'a dayyiba saliha, Allah yasa anyi wannan aure a sa'a. Ta cika da fatiha, ta daga hannunta tana addu'a ana amsawa da Amin. "waman yattikillah yaja'allahu makraja, wa yarzurku min haisu lah ya tasiri, waman tawakal alallahi fa huwa hasbun, innallaha baligul amri kadija'Allahu li kulli shai'in kadira. Amin. Yayinda kowa ya shafa. Tace to Alhmdllh, jama'a muna yi muku barka da zuwa, mungode da hallartat taronmu da kuka yi don ku taya mu murnar auren 'yan uwan mu. Bari na kira muku autarmu dan tazo tayi mana 'yar fadakarwa kadan kafin malaman namu da zasu yi wa'azizzikan su gama karasowa, tace "zainab zeey daddy bismillah." zainab 'yar shekara takwas ta taso cikin nutsuwa tana murmushi daya karawa fuskarta kyau, tana sanye da dan dan datsetsen yelow les da yake ta walwali, dambara-damran dutsuna ajiki kamar madubi, tasa gwagwaro yelow, ta yafa dankwalin les din. Tasa fashion azurfa mai yalayen dutsuna wuya da kunne, da zobensu, tasa warwaraye suma yaleye. Yarinyar tayi kyau sosai, tsarin kwaliyarta kamar wata babba. Shiga iri daya sukayi da ni'ima komai da komai. Ni'ima ta mika mata lasfikar suna yiwa juna murmushi, yayinda masu hotuna suke basu flasha, masu filet din dvd da cd suke ta dauka, ni'ima ta koma wajen zamanta, zainab cikin zakin muryarta tace "Aslm 'yan uwa musulmi." gaba daya kuwa suka amsa mata da "wslm. "hakika ina taya 'yan uwana murna da wannan rana ta aurensu, Allah ya basu zaman lafiya dauwamamme, yaya sadiya da aunty mansura, yanzu Allah ya kaiku wani matsayi da rayuwarku zata canja ba kamar sanda kuna gida ba. 1- abu na farko da ake so 'ya mace ta gane ta fahimceshi shine, hakkin mijinta akanta, ta gane cewar miji shine shugabanta, ta rinka jin hakan a ranta. Saboda Allah ubangiji yace, maza masu tsayuwa ne da shugabanci a kan mata, kuma maza suna suke da fifiko wajen girma da daraja akan mata." wadanan dalilai su zasu mace ta dinga jin cewa, namij fa shugabane, kuma ta dinga jin haka a jikinta, kuma tasan yana da hakki akanta, domin tasan bazata fita ba saida izninsa, kuma duk inda zata je saita san ransa bazai baci ba. Manzon Allah (s.a.w) ya fada a cikin hadisi ingantacce [1:17PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**5 YA fada acikin hadisi ingantacce, saboda girman hakkin miji akan matarsa, "da za'a umurci wani yayi sujjada ga wani, dana umurci mace tayiwa mijinta sujjda. Koda miji zai bukaci amfani da matarsa, ita kuma tana kan sirdin rakumi, to kada ta hanashi. A wata ruwayar ta bukhari, manzo Allah (s.a.w) yace, "idan mij ya kirawo matarsa zuwa ga shimfidarsa ita kuma taki har ya kwana yana fushi da ita, to mala'iku zasuyi ta tsine mata har sai an wayi gari, bukhari ne ya ruwaito. Idan mace ta gane hakkin miji akanta, kuma tayi masa da'a akan abinda ba sabon Allah bane, to hakan zai taimaka kwarai wajen gyara zuciyarta. 2- abu na biyu shine amana, anaso mace ta zamo mai amana bata cikin abunda ya shafi dukiyarsa, kuma bata ha'ince shiba akan karan kanta. Ha'intar miji wajen dukiyarsa daukan wani abunsa batare da iznin sa ba. Ha'intar miji aka karan kanta kuwa, shine ta bada kanta ga wani namiji. Ko kuma tayi kawance da mijin da banata ba. Du matar kirki bazata yi haka ba. Toh macen kirki itace wadda bata ha'intar mijinta daga dukiyarsa ko kuma akanta. Salihan mata masu da'a ne ga mazajensu, masu tsare mutuncinsu ne da dukiyoyin mazajensu, basa ha'intar mazajensu alokacin da basa nan. Manzon Allah (s.a.w) ya fada cewa babu yanda za ayi mace ta dauki wani abu a dakin mijinta ba tare da izninsa ba, to bai halatta ba, sai sahabbai suka tambayi annabi cewa "ko abinci ne? Sai annabi yace "wannan shine mafi daraja acikin dukiyoyin mu, ba a yarda mace ta dauki abincin mijinta tayi kyauta dashi ba. Kuyi hakuri plz yau bazan samu daman pstn ba, wannan wanda nadan soma rubutawa jiyane, amma gobe insha Allahu zanyi muku 3 times pr day, kuyi hkr [1:17PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**6 BA AYARDA mace ta dauki abincin mijinta tayi kyauta dashiba saidai in dafaffe ne in tayi, gudun kada ya lalace, to sai a sadaukar dan gudun kada ya zamo almubazaranci. Shima idan miji ya dawo saiki sanar masa, ko gidanku zaki aika da abinci saiki sanar masa, bare ki bawa wani can daban. Wannan yana cikin cin amanar miji. Manya mutane suka rinka mikewa suna yiwa zainab kyautar kudi, saboda yanda yarinya karama ta burgesu, Abba da daddy sai washe baki suke yi don jin kokarin 'yar tasu da kwazonta. Mamanta kuwa tayi hamdala acikin ranta, tana mai jin dadin baiwar da Allah yayi wa 'yarta tun tana karama, kowane tebir mutum hudu ne a zagaye dashi, akayi umurni da masu sabis su fara rabon abinci, shinkafa ce fara da taliya itama haka, sai soyayyun kaji da gasashen nama, sai mitfy, samosa, sopringros, haka kowa za a tsira katon filet a dire a gabansa, mata masu wa'azi sun zo, wajen yayi shiru an nutsu ana cin abinci, yayinda aketa kwararo wa'azi akan zaman aure ga ma'aurata. Washe gari akayi yini, ranar litinin akayi fati, a ranar kuma aka kai amare dakunansu. Burin mansura ya cika, yau ta auri gwarzon namiji cikakke, wato Aliyu. Tasan sarai Aliyu miskili ne bai fiya wasa da dariya ba, shi hasalima magana wahala take masa yi masa, don inzaka daka ta tashi sai dai kuyi ta zaman kurame dashi. Aliyu mutum ne mai tsafta, dan gayu ne mai son kamshi, baya damuwa du tsadan turare zai saya indai kamshin shi yana da dadi. Aliyu yana ji da kansa, akwai iya jan aji, yana da tsananin iyayi da gwalli kamar mace, ya fiya kasaita da son girma kamar wani basarake. Washe gari ranar talata gajiyar biki bata bar ni'ima da zainab zuwa makaranta ba. Tun asuba da aka tashe su suka yi sallah, suka sake komawa gado suka nade cikin bargo suna bacci. Karfe bakwai masu aikinsu sukayi ta tashinsu don su shiry su tafi makaranta, amma du sunki tashi. Dole sai rabuwa suka yi dasu. Karfe goma dai-dai Aliyu ya shigo gidan don gaishe da iyayensa. A farfajiyar gidansu mai gadi da direbobi suna ta risinnawa suna gaisheshi. Aliyu ya cewa malam idi direba, "ina 'yan makaranta , i ce kodai basu makara bako? Malam idi yace ai basu fito ba, yau ban kaisu makaranta ba." a zuciye Aliyu ya shiga gidan, kafa kawai yasa ya daki kofar ta bude garam. Ni'ima da zainab suka tashi a firgice, suna mitsike ido. Suna dago kai suka ganshi. Kafarshi daya akan gadon, dayar tana kasa, fuskar nan tayi kirtif da ita kamar bai taba dariya ba. Zumbur suka mike suka diro kasa daga gadon, suka durkusa can nesa dashi, suka kama cewa "yaya ina kwana? Bai amsa musu gaisuwar ba, sai tambaya daya jefo musu cewar "meya hanaku zuwa makaranta? Gaba daya jikinsu ya hau bari suna in'ina da kame-kame abunda zasu ce, ya daka musu tsawa "ku tashi ku saka uniform dinku, ina jiranku a falo." suka mike da sauri kowacce ta nufi kwaba. Shikuma yayo falonsu yana tsaye. Mintuna kadan suka fito sanye da kayan makaranta da jakunkunansu a rataye, ya sasu a gaba har farfajiyar gidansu, ya kwalawa malam idi direba

Chapter 1 of 14