Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kira, ya taho jikinsa na rawa. Yace "daga yau du ranar daka kara kin kaisu makaranta abakacin aikinka." malam idi ya rikice jikinsa yana bari, yace "kayi hakuri yallabai, wallahi ba laifi na bane sune basu fito ba." yace "daga yau idan kaga basu fito ba kayi min waya kawai ka gaya min. Yace "to yallbai." suka shiga motar direban ya jasu. Shikuma Aliyu yayi cikin gida. Zainab tace, "inbanda abun yaya, daga yin aure saika fito da sassafe. "ni'ima tace, "ai gwandake bangarenku ma na 'yan firamare ne, ni 'yar sakandare nasan wallahi sai an dake ni, daya kyalemu gobe basa muzo ba." gidan Aliyu yana nan daga bayan gidansu ba nisa. Amma tunda aka kai mansura basu je gidan ba, saboda basu da wani lokaci sai dare, sukuma ba fita suka yi da dare ba. Yau alhamis ana tashi daga boko gida suka yo, dan ba islamiya. Ni'ima da zainab tuni sun gama shiri, anko sukayi na wani dandatsesen material baki, ni'ima tana rike da hannun zainab suka tafi. Suna zuwa gidan suka shiga, 'yan aikin gidan sai sannu da zuwa suke yi musu. Suka karasa babban falo inda matar gidan take, sukayi sallama, saida akayi musu izni sannan suka shiga. Mansura ta taresu da murna, a'a sai yau zaku zo, nayi fushi." suka rike hannunta suna cewa, "tuba muke aunty, kinsan kullum da makaranta. Tace, "to amma gaskiya yau anan zaku kwana." suka ce wai kwana aunty? Ai baza a barmu ba a gida." tace haba don Allah, ya ya zasu hanaku kwana a gidan babban yaya." yayinda take kwalawa mai aikinta kira talatuwa, "na'am ranki ya dade, ta amsa da saurinta, ta durkusa a gabanta, mansura tace "bakya ga munyi bai ne baki kawo musu komai ba, nifa bana son shashanci, kirinka kula da aikinki fa." talatuwa tace kiyi hakuri aunty. Ta fita da sauri ta shiga kicin ta hado musu lemuka da snacks taje ta durkusa a gbansu ta ajiye. Zata mike zainab ta bude jakarta ta dauko dari biyar ta mika mata. Talatuwa tasa hannu biyu ta karba tana godiya. Inna laraba tashigo ta durkusa a gaban mansura tana tambayarta hajiya me za'a girka? Surayya Abubakar [1:19PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**7 TA YAMUTSA fuska tana tsara mata abunda zata girka. Harta mike ta fara tafiya zainab tabita tasa mata dari biyar a hannunta, tsohuwa laraba tace, "auta me za a sayo miki? Tace a'a ki rike baki nayi. Laraba ta washe baki tana murna tana godewa zainab. Yaya Aliyu ya shigo, da sauri zainab da ni'ima suka yi masa sannu da zuwa tare da gaishe shi. Ya wuce bangarensa. Mansura ta kwalawa talatuwa kira, tazo da saurinta. Mansura tace, "ki hadawa Aliyu abinci kikai bangarensa." zainab kanta data ke yarinya tayi mamakin abun, bare ni'ima data fara zama budura. Sun san haka bai kamata ba, don ba haka ake yi a gidan su ba. Wata mata ce da goyon 'yarta ta fita da hayyacinta kamar almajira, ta durkusa tana gaida mansura. Mansura ta hade rai tana ya musta, da kyar ta amsa gaisuwan matar. Ni'ima da zainab suka gaishe da matar, zainab tace kwanto yarinyar, bata da lafiya ne? Matar tace "wallahi zazzabi ne da amai da kashi na hakori." yayinda take kokarin sakkota. Zainab ta mika hannu zata karbeta, mansura tayi karaf tace "ke zeey auta yarinyar ba lafiya kokarin daukarta kike? Saita yo miki amai ajiki." zeey tace to kije ki sai mata magani ta sha mana. Matar ta girgiza kai cikin yanayi na tausayawa, tace, "aiba kudin ne, magani har dari tara da hamsin, banida kudin dazan sai mata, kudin yayi yawa, ko dari da hamsin bani da'ita bare har dari tara da hamsin." zainab ta bude jakarsu ta zaro gudan dubu daya ta mikawa matar, "ungo kije kisai mata maganin." matar ta karba bakinta yana rawa. Mansura tace, "ke zeey kudin wa kika samu kiketa rabarwa haka? Zainab tace daddy ne ya bamu da zamu zo ko zamu sai wani abun. Mansura tace to shine kike rabar da kudi baku sai komai ba." zainab tace aunty ai muna da komai me zamu saya? Ba gwanda mu bayarba." matar nan dai tanata sawa zeey albarka harta fice ta tafi. Ni'ima ta fuzge jakar daga hannun zainab, ta bude ta leke bakomai aciki, ta harareta to kin rabar mana da kudin, to yanzu dame zamu sai ice-cream din? Ni shiyasa wallahi bana so nabar kudin mu a hannunki, du saiki rabarwa da mutane mu ki barmu haka. Nidai kawai kirinka bayar da iya naki, kada ki kuma bayarmin da nawa kudin." zainab tayi murmushi, tace "haba yaya ni'ima, abunki ai nawa ne, zan iya iko da komai naki, Allah ya bamu rai da lafiya, muna da kudi a gida, ko an bamu ma tarawa muke yi idan bamuda abun siya. To ga masu bukata saimu hanasu." ni'ima tace, "to amma ai bakya bayar du ba, ai kinsan zamu sai ice-cream." zainab tace bakomai yaya ni'ima, zaki ga Allah ya bamu wasu, don ranan malaminmu yace, "anaso mutum ya rinka ya waita sadaka, saboda tana juyar da bala'i. A zamanin annabi sulaiman (a.s) akwai wani mutum a gidansa akwai wata katuwar bishiya, tsutsuwa tayi 'ya'ya akai. Sai wata rana matar ta gaya wa mijinta cewar, ya hau kan bishiyar nan ya debo musu 'ya'yan wannan tsutsunwar zasu ci suda 'ya'yansu. Mutumin nan ya kwaso 'ya'yan, suka gashe shi, shida matarsa da 'ya'yansa suka cinye. Sai tsunsuwar nan takai karar wannan mutumin gurin annabi sulaiman (a.s), shikuma yasa aka kirawo mutumin yayi musu tsakani da wannan tsuntsuwar, mutumin yayi alkawari bazai sake ba. Ana haka sai wata rana matar nan ya kuma gayawa mijinta ya hau bishiya ya kuma debo musu 'ya'yan tsunsuwa, mutumin yaki, yace "annabi sulaiman ya hana shi ya sake dibar mata 'ya'ya." sai matar tace kana ganin annabi sulaiman zaiyi maka wani abu danka kwashe 'ya'yan tsunsuwa, alhalin shima me shagaltuwane da mulkinsa? Matar dai tai ta rudarsa har ya hau ya debo. Sai tsuntsuwar nan tasake kai kararsa wajen annabi sulaiman, annabi sulaiman yayi fushi, ya kirawo shaidanu guda biyu, daya daga gabas daya daga yamma. Yace sutafi kan bishiyar nan su zauna, idan mutumin nan ya sake zuwa wajen 'ya'yan tsunsuwar nan su rike kafafuwansa su watsoshi kasa. Shaidanu suka je kan bishiya suka zauna. Shikuma mutumin ganin ya debo wa'yancan ba ayi masa komai ba, don haka sa wannan karon ma ya sake komawa domin ya debo 'ya'yan. Har ya taka kafarsa zai hau, sai yaji almajiri yana bara a kofar gida, saiya umurci matar nan data bawa almajirin nan wani abu. Sai matar nan tace bakomai awajenta. Sai mutumin nan ya dawo ya samu lomar abinci ya bawa almajirin nan, sannan ya koma bishiya ya debo 'ya'yan tsuntsuwar nan, saita sake dwowa ta gayawa annabi sulaiman, sai yayi fushi mai tsanani, ya kirawo shadanun guda biyu daya tura kan bishiyar. Sai suka ce bamu saba maka ba, muna kan bishiyar koda yaushe, lokacin da mutumin zai hau kan bishiyar sai wani almajiri yayi bara ya koma ya bashi lomar abinci, sannan ya dawo ya hau. Zamu kama shi kenan sai ubangiji ya aiko da mala'iku guda biyu, daya ya kamani ta wuya ya jefar dani inda rana take bullowa, daya yakama abokina ya jefar dashi inda rana take faduwa. To kinga dalilin sadakar da yayi ya kubuta daga sharrin shaidanu. Aliyu yana daga dakinshi yana jinsu, ya sake jinjina hankalin autarsu, yasan hakika akwai bawar da Allah yayiwa autarsu na musamman. Ya fito daga dakinshi. Surayya abubakar [1:19PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**8 YA FITO daga dakinshi, yayi gyaran murya, ya ciro dubu biyar a Aljihunsa ya mikawa zainab, yace "zeey auta ga kudin ice-cream." ta rissana ta karba tana godiya. Yaya Aliyu ya wuce ya sake fita. Zainab tace yaya ni'ima kinga abunda nake fadamiki ba, inka bayar da kadan sai Allah ya baka mai yawa." ni'ima tace nagani, amma bani su nan kada ki sake bayar mana." ita kuwa mansura a zuciyarta cewa takeyi, "wannan yarinyar da shegen iyayi take. Wajen mangariba suka isa gida. Bangaren hajiya suka nufa sukayi sallar mangariba, zainab ta mike tayi bangarensu, saita tarar da mamanta kwance tana juyi. Ta tafi da sauri ta rikota, tana cewa menene mamana, meya sameki? Maman tace banida lafiya zaina, marata da bayana ciwo suke yi. Nan da nan sai zainab tasa kuka tana cewa, "mama tashi muje asibiti kinji? Mama don Allah tashi mu tafi asibiti ko kya samu lafiya. Maman tace da kyar, saboda ta fara galabaita "zainab asibiti babu abunda zasu iya yi min, Allah ne kadai zai bani lafiya. Ki kirawomin hajiya da umma da ummi, tayi cikin gida da sauri, du ta gaya musu gaba daya suka taho, a lokacin Aliyu yana gidan. Maman ta galabaita sosai, ko hannunta bata dagawa. Umma tana ta hado kayan haihuwar a dakin. Umma tana rike da maman, hajiya tana mata tofi a ruwa a kofi, zainab din taje ta rike maman tana jijjigata tana kuka, tana cewa mama! Mama!! Ki bude idonki kiga hajiyan fa na kirawo miki ita. Ki bude idonki kifa tofi take miki, don Allah mama ki bude idonki kiga umma da ummi., kefa kika ce nakira miki su, don Allah ki tashi." ta kama jijjigata tana gwale mata ido, tana cewa mama! Mama!!. Aliyu yace "umma ku kamata mu tafi asibiti." a lokacin Aliyu yaiwa abba da daddy waya, suka ce to suma sun wuce asibitin." a can suka tarar dasu Abban har sun riga zuwa, aka shigar da mama dakin haihuwa, zainab sai kuka take yi, ta tafi ta rungume daddynta tana kuka tana cewa daddy kana ganin mama bata da lafiya sun shigar da ita can, daddy kazo mu bita. Ya rungumota yana rarrashinta, "kiyi hakuri zainab, ki kwantar da hankalinki, mamanki haihuwa zatayi. Ko bakya so tasamar miki kanwa? Tace ina somana daddy." to kiy shiru ki daina kuka, mamanki haihuwa zatayi kinji ko? Kita yi mata addu'a kinji? Tace "to daddy zanyi mata. Abba yace, hajiya su koma da zainab gida a ar umma da ummi a gurinta. Abba ya taho da hajiya da zainab gida, zainab sai kuka take yi, suna zuwa gida suna ni'ima da sadik su ni'ima suka tare su da cewa ta haihu? Hajiya tace musu a'a ta dai kusa. Du rarrashin da hajiya take yiwa zainab ta kasa yin shiru, sai kuka take yi. Su kuwa can asibiti sun kasa samun nutsuwa, saboda jikin mama da yayi tsanani. Wajen karfe uku na dare ta haifi 'yarta mace, su umma da ummi suka ta hamdala suna yiwa Allah godiya. Karfe bakwai na safe gaba daya 'yan gidan sun hallara, ganin yanda jini ya tsinkewa mama, hankalin kowa ya tashi. Daddy mijinta yana rike da ita yana salati, yayinda likitoci suketa iya bakin kokarinsu. Sunyi mata allura jinin ya tsaya, du 'yan uwa sun zagaye ta, harda sadiya amarya da mansura, su sadik da ni'ima du suna wajen. Zainab kuwa hajiya ta janye ta suna falon dakin da aka kwantar da maman nata. Saboda kuka da zainab din take yi. Ita kuma mama jikin nata yayi tsanani, sai wasiya take bayarwa, sai cewa take cikin dakushashshiyar murya, "ina zainab autata, ki kirawo min zainab dina. Sadik ya fita da gudu yana kuka ya kira zainab, ta taho da gudu ta rike hannun maman nata ta jijjigawa, tana cewa "gani mama, tashi gaya min abunda zaki gaya min, kinji mamana? Ta kwantar da kanta akan ruwan cikin maman nata tana kuka, maman data ke fitar da nishi da kyar ta dora hannunta kan zainab din tana shafawa, a hankali ta rinka motsa bakinta tana karanto kalmar shahada 'yan uwa sunata amsa mata, tana ta shakewa. Su sadiya da ni'ima kuwa gaba daya sun rikice da kuka. Can mama tayi shiru, hamza cikin firgita yace, "ta mutu! Iyayen suka dauki salati ga daya da hawaye, yayinda yaran suka cika daki gaba daya da kururuwar kuka. Zainab kuwa tana yin baya ba'a ankara ba ta sulale ta fadi kasa ba numfashi. Aliyu ya sunkuce ta aguje ya shiga office din likitan da ita. Likitan ya karbe ta da sauri ya dorata kan gado yana kokarin ceto rayuwrta. Aka tafi da mama gida akayi mata sutura aka binneta, kowa yaji ciwon mutuwar mama. Mama mutuniyar kirki me kawaici da hakuri, daddyn zainab karfin hali kawai yake yi, domin yasan yayi rashin da da wuya ya mayar da'ita. Don rashin hajiya saude ba karamin gibi rayuwarsa tayi ba. Anata amsar gaisuwa shikuwa sai yayi jigudin yana tunani, ga 'ya'yanshi 'yan mazan faruk da sadik suna manne da jikinsa, yaran sun kasa manta mutuwar, sai dai kawai kada suna sharar hawaye. Faruk shine sa'a ni'ima mai shekara goma sha hudu, sadik kuma shekararsa sha daya. Kwana daya da rasuwar mama aka sallamo zainab suka taho, da yake ummi ce a wajenta. Yarinyar tayi wata irin rama sai kace wacce ta dade da ciwo. [1:22PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**10 ABBAN yace "toh shikenan Aliyu, Allah ya tayaka riko." Aliyu yace amin Abba, nagode, Abban yace to ka gayawa daddyn naku? Yace "eh, saida na fara zuwa nayi shawara dashi tukunna." yace, "to ai shikenan komai yayi dai-dai, Allah ya tayaka riko." ya amsa da Amin. Ya yiwa mahaifinsa godiya ya tashi ya nufi gidansu, ya gayawa kakarsu. Hajiya murna tayi takara karfafa masa gwiwa daya rike 'yar uwarsa dakyau, ta hakane zumunci zai kara karfi a tsakaninsu." don ita hajiya mace ce mai zumunci, tana so taga kan zuri'ar ta a hade, yayiwa hajiyar alheri, hajiya tanata godiya dasa masa albarka, ya fice ya nufi bangarensu. Ya tarar da umma da ummi a babban falo suna hira. Yace musu, "ku hadamin kayan zainab da daddare zan zo na tafi da ita." gaba daya suka hada baki cikin razana suka ce, "zaka tafi da ita ina? Gidana zata koma zan cigaba da rikonta. Umma ta mike ta kama yi masa fada, " wato mu ka raina irin rikon da muke yi mata, shine zaka ce zaka dauketa saboda kafi mu sanin darajarta, ko iko zaka nuna mana akanta? Yayi murmushi yace "kuyi hakuri, umma ba haka bane." iyakacin maganar kenan yayi musu shiru. Sun riga sun san bai fiya yawan magana ba, sai dai yayi atakaice. Inkin ji shi yana hira mai tsawo, to da iyayensa ne maza. Ya mike yana ce musu, "umma bari na karasa gida." umma tace "saboda maganar tamu bata da amsa ko? Yayi murmushi ya dire musu kudi a gabansu, yace ummi kwasai goro." tace "to, mungode, Allah yayi albarka." yana fita umma ta kama baki, tace, "ki gane min yaro, wai shi babba har ya fimu sanin abunda ya dace. Ummi tayi dariya tace "Aliyu kenan gadanga kusan yaki. Shifa zuwan da yayi yaga dazu bata je makaranta ba, gani yake kamar zamu kara sangartar da ita mu rika biyewa shagwabarta." Aliyu yana isa gidansa yayi fakin ya shiga, a falo ya zauna yana karkade kafa. Mansura ta fito daga daki, tace "sannu da zuwa Aliyu, ga break dinka can, koda yake rana ma tayi kaine kayi fitar safe." yace "nayi break a office din daddy bana tare da yunwa." yace kisa a share wancan dakin, zan dawo da zainab gidan nan zata zauna acikin dakin can. Ta dafe kirji tace "haba Aliyu, ya zaka ce zaka dawo da zainab? Ai zaka takurawa rayuwarta. Don Allah ka kyaleta a gidanku, wannan shagwababiyar yarinyar in zamu iya da ita anan? Ya doka mata harara yace ba shawararki nazo nema ba, idan zainab tazo kada ki barta ta zauna ki koreta." tace, "haba Aliyu kai ka fiya zafin zuciya, daga 'yar wannan maganan saika hau tari, ba nufi na haka ba, ita da gidan wanta "ai ban isa na koreta ba." yamata shiru bai sake ce mata komai ba daman tasan ba zai sake magana ba, don ya fiya miskilanci, baya son yawan magana. *** **** karfe shidda 'yan makaranta sun dawo, suna cin abinci ba dadewa akayi mangariba, suna idar da sallah hajiya ta rungumo zainab jikinta tana shafa kanta, tace "zainab yanzu fa yayanki zai zo zai tafi dake gidansa, zaki ci gaba da zama acan." zainab tasa kuka tace, nidai hajiya bazan jeba nace, yai tamin fada koma ya dokeni, hajiya tace bazai dokeki ba, kuma fada ma ya daina yi miki. Kije ki zauna kinji zainab? Ta make kafada, um-um, ni ba zanje ba." suna haka taji yo sallamarsa, da sauri ta tashi da gudu tai cikin dakin hajiya. Aliyu ya shigo ya sake gaida hajiya, hajiya tace masa "zainab dai tace baza taje ba, ka ganta can harda kuka." ya kwala mata kira ta fito a tsorace, tazo ta durkusa a gabansa yace "shine kika ce bazaki gidana ba? Ta girgiza kai alamar cewa, a'a yace to meye nayin kukan? Yi min shiru. Tasa hannunta ta toshe bakinta ta hadiye kukan. Yace ki goge hawayenki kije, kiyi wa Abba da daddy sallama." tace to, ta goge fuskarta. Ta shiga bangaren su umma ta tarar da Abba da umma da ummi suna falo, Abba yace yaki 'yata tazo ta zauna a jikinsa." yace menene naga idonki alamar kinyi kuka? Tace bakomai, Abba sallama nazo inyi muku zan koma gidan yaya." Abban yace "zainab bana son abunda zai takuraki, in bakya son zuwa ni zansa ya kyaleki kiyi zamanki." tace a'a Abba zanje." yace to shikenan zainab, Allah yayi miki Albarka, kici gaba da maida kai da kokari a makaranta, tanan ne zaku fi shiri da yayan naki kinji 'yata? Tace "to Abba nagode." ta mike ta shiga wajen daddynta, ta daura kanta akan cinyarsa tana kuka. Yasa hannunsa yana shafa kanta yace "kiyi hakuri zainab, nasan bakya son tafiya. Zainab ko yaushe kina raina, dana ganki saikin tunamin da mamanki. Zainab du ina tausaya mana ni dake na rashin mamanki. Kiyi hakuri zainab kiyi zamanki, nasan zai rikeki da amana kamar ni. Kiyi masa biyayya shida matarsa, banda rashin kunya kinji? Tace "to daddy zan kiyaye." ya bude firij ya dauko rubutu a roba ya bata, ungo shanye rubutunki maganin tsari da kariya daga shaidanu." ta karba tayi bisimilla ta shanye, ya karba yasa ruwa ya dauraye mata, ta karba tasha, ragowar ya zuba a hannunsa ya shafa mata a kanta da fuskarta. Yaita mata nasiha mai shiga jiki, yace ta daina kuka ta tashi taje su tafi." hajiya dasu ni'ima su sadik har gindin mota suka rakota suna hawaye tana hawaye. Surayya [1:23PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**11 HAJIYA tana rungume da ita tana rarrashinta suka bude mata gaban mota ta shiga, ta dunkufar da kanta akan gwiwoyinta tana ci gaba da kukanta kasa-kasa, Aliyu ya sallame su du yaraba musu kudi, yace su koma gida, suna tunanin 'yar uwarsu wai anrabata da gidansu kenan. Ya kalleta au baki daina kukan ba? Tayi saurin hadiye kukan nata, ta goge idanuwanta. Tafiya kadan suka isa gidansa, suka fito har daki ya kaita, "nan shine dakinki, talatuwa zata rinka taya ki kwana." dakin yayi kyau, a yau dinan ya sayo mata gadon silba da madubi, sai kwaba ta jikin bango, sai labuye da jan kafet, shikenan ba wani shirgi, sai toilet aciki dake gefe, tace "to yaya." ya fita ya nufi sashinsa, zainab itama ta shiga dakin aunty mansura. Zainab ta kwantar da hankalinta tana zaune a gidan yayanta, tsakaninta da abinci saita ga damar ci, ko yaushe yayan nata yana cikin siyo musu ice-cream, youghot su biskit da cakulet, da yake abinci bai dami zainab ba, ita hakan saya fiye mata dadi. Ita kuwa mansura ta fiya lalaci da sangarta, bata wani iya girki ba, shikuwa Aliyu dan gaye ne mai aji, gashi da kyankyami, don haka bazai iya cin abincin mai aiki ba. Don haka inya zo garin ma saidai yaje gida yaci abinci, don a gidansa inna laraba ita take yin girki. Babbar mace ce amma da kwarinta, don bata wuce yin aure ba, sai 'yar budurwa wato talatuwa, ita take yi mata shara dasu goge-goge da gyaran gado, inta yi baki ta kula dasu. Don wata wauta ta mansura dai-dai da mijin ma inya nason wani abu sai dai ta kira talatuwa. Don haka ma ko meye ya gwammace yayi da kansa, abinci kuwa saiya je gidansu sannan yaci. A gidansu su umma har fada suke yi masa, don me zai rinka baro girkin matarsa baya son ci. Sai dai yayi murmushi kawai yace musu bakomai. Bama yanzu da mansura take fama da laulayi. Da safe yana zaune a falo da wando iya gwiwa da farar shirt, yana lumshe idanuwarsa kamar mai jin barci. Mansura tana zaune kusa dashi tana cin wainar kwai da dankalin turawa, ta zuba shayi a kofi yana ta turiri, gashi yayi kauri da hadin madara da naskofi da dai sauransu. Zainab ta fito sanye cikin shirin makaranta, ta durkusa ta gaishe da yayan nata da mansura. Ta mike a gurguje take, dan takusa makara. Ta dauki shanyin gaban auntyn nata tadan kurba, tace "wai aunty wannan kaurin ai yayi yawa, bakya tsoron ya kulle miki ciki? Mansura tayi dariya tace, laifin babynku ne ba ruwana. Zainab tayi dariya tace ai, "ai gwanda ki dinga ci sosai don ki haifa mana katon baby in rinka daukarsa da kyar." ta nufi firij ta dauko ice-cream da youghot da cake, tazo ta wuce su da sauri saboda yayan nata, tace aunty natafi makaranta." kafin tayi magana Aliyu ya kirata "zainab." tayi saurin juyowa tare da amsawa, a sanyaye tace na'am yaya." zo nan. Ta dawo ta durkusa a gabansa. Yace haka zaki tafi makaranta baki karya ba? Tace yaya zanci cake da ice-cream da youghot a mota." yace wato har yanzu kina nan dakin cin abincin ki ko sai kayan kwadayi? Ke wace iri ce ne? Da safe ma sai kin sha sanyi bazaki ci abinda zai dumama miki ciki ba? Mansura tace wallahi haka nake fama da ita, bata son cin abinci, daga shan kayan zaki sai shan kayan sanyi." yace ina break din nata? Mansura ta kwalawa talatuwa kira, tace mata ina break din zainab? Talatuwa ta shiga dakin zainab da sauri ta dauko break din data kai mata, yanda ta ajiyeshi haka yake, ko budawa bata yiba. Ta ajiye a gaban zainab din. Aliyu ya kalleta yace to maza ki cinye shi yanzun nan." idonta yayi rau-rau alamar sonyin kuka. Shikuwa sai ya jingina da kujera ma ya lumshe shanyayyun idanuwansa kamar zaiyi barci. Ba yanda zata yi, haka ta rinka tura dankalin nan da kwai tana shan ruwan shayin. Cikinta ya cika taji kokarin yin amai take yi, tace a hankalin cikin sanyin muryanta, "yaya ya dago kai yayi mata wani kallo, bata iya fada masa komai ba, ta sake sunkuyar da kanta, ya sake lumshe idonsa. Haka taci gaba da ci tana hawaye, saida ta cinye du. Dakyar ta iya tashi tsaye, tace yaya na cinye, na tafi? Ya bude ido daya yayi mata alama da hannu wai ta tafi. Ta fice inda direba yake jiranta ta shiga ta tafi. Mansura tace gaskiya Aliyu kana matsawa yarinyar nan, da nice saika bata min rai kace ina takurawa kanwarka." ya bude ido daya yace karki manta shekaranta goma sha daya, yanzu ta shiga sakandari aji daya, har yanzu ita yarinya ce, idan bana matsamata taci abinci sai yunwa ta kamata." ta tabe baki tana gunguni, "in rashin cin abinci ne ai a wurinka ta gado, tunda kaima baka cin na gidanka." ya kwanto akan cinyarta yace, kiyi min da kanki mana, du rashin dadinsa ai zanci. Amma zaki rinka sa tsohuwar mutane wahalar girki, sannan kisa wata yarinya daban itace mai bani abinci, kallon yarinyar nan kadai tayar min da zuciya yake." ta zumburi baki bata ce komai ba, ya shafa cikinta yana cewa, "i luv u baby, yaushe zaka iso kaga daddynka? Tace ai kuwa zai jima baiga daddyn ba, sai nan da wata biyar." ya gyada kanshi, Allah kawo minshi lafiya." tadan rankwafo kanshi tace, "Aliyu dan Allah zaka danyi min tausa? Surayya [1:23PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**12 ALIYU dan Allah zaka danyi min tausa? Yace nikuma me zakiyi min? Tace bakomai." yace to kyaleni bacci nake ji." ta ture masa kansa akan kujera, tace to dagani naje na kwanta." yau alhamis karfe biyu direba ya dauko zainab daga makaranta, saboda yau basuda islamiya, shiyasa basu kai shidda ba. Ta shigo tana jan jakartata, ta zube a falo tace "wash! Aunty sannu da gida, ya bybynmu? Mansura tace gashi nan dai yana ta min zillo. Aunty ki bashi abinci yaci yunwa yake ji, inya ci zai daina yi miki zillo." ai naci abinci zeey, kin zata ni irinki ce sai anyi min dura ina kuka? Zainab tayi saurin mikewa, bari na tashi kada ya shigo ya ganni anan ya kuma sani cinye abincin daya fi karfin cikina." tayi dakinta suna dariya. Da mangariba ni'ima tazo gidan, sukayi tsalle suka rungume juna suna masu jin dadin ganin juna, kamar ba dazu suka rabu a makaranta ba. Suka zauna a falo suna dariya. Ni'ima tace auntyn mu ina wuni, ya babyn namu? Lafiyarsa kalau gashi nan yana jinki." ni'ima tace zainab kinsan gobe ne fatin zara'u yusuf shidda na yamma, ya zamuyi wajen tafiya, don yanda muke da zara'u dole ne mu fasa fatin nan? Zainab

Chapter 2 of 14