yana kallonsu,
tsananin tausayinsu ya gallabi zuciyarsa.
A hankali yae ya durkusa a gaban ihsan ya shafa
kanta, ta dago ta ganshi, ta fada jikinsa tana
dariya
Abba na ina ka tafi ka bani?
Ya rungumeta sosai yarinya ta rinka ajiyar zuciya
ya rinka shafa kanta.
Tayi lamo a jikinsa har tayi bacci ya shimfideta
ya dawo wajen zainab.
Yace yanzu zainab haka zakiyi min kiki sakin
ranki ku rinka shiga kunci keda ihsan.
Keda zaki rarrasheta amma ke kina kuka ita
tanayi, a haka kike so na tafi na barku, taya
zuciyata zata samu nutsuwa, bayan nasan bakwa
cikin kwanciyar hankali.
Kayi hakuri yaya wlh ni ba haka bne, ni abunda
ya daga min hankali naga har sha dayan dare
baka dawo bane, yaya ba dole na damu ba?
Yaya ina kaje ka kai sha daya baka dawo ba?
Yayi murmushi yace ina zanje kuwa, ai kinsan
bazan iya fita wani waje a wannan lokacin ba, ina
falon saukar baki muna lissafi da su sadik yanzu
nan suka tafi.
Tayi murmushi ya kamo hannunta zo muje na
kwanta kada na makara.
Da safe ya fito falo shida zainab yana dauke da
ihsan, sunci kwalliya kamar masu shirin zuwa fati,
sunata murmushi da fara'a ke ba kyace da wani
kunci a ransu ba
mansura suka shigo falon ita da Ahmada sunci
kwalliya tana taunar cingam, Ahmad yayo wajen
zainab yana cewa aunty mami mu tafi gaba daya.
Ta shafa kansa kada ka damu yarona idan mun
gama shirinmu zamu biyoku, inkaje ka kula da
karatunka, kaga za a canja maka makaranta
saika kula sosai.
Yace to aunty mami naji.
Mansura ta kallesu ta tabe baki, takaicinsu da
bakin cikinsu ya isheta, wato du yanda taso ta
kuntatawa zainab donta ga bacin ranta, yarinyar
taki nuna damuwarta.
Har mota ta rakosu, Aliyu ya mikowa zainab
ihsan ta karbeta, ya shiga motar suna daga musu
hannu, direba ya fara jan motar tana tafiya, Ihsan
ta kwala wata gigitaccen kuka tana zamewa daga
jikin zainab.
Motar tana kokarin fita daga get Aliyu yacewa
direba ya tsaya, ya fito da sauri ya karbi ihsan ya
rungumeta, ta rinka cewa Abba jani.
Yaya to ku tafi da talatu, ta taho da ita.
To shikenan turo talatun.
So kuyi hkr wllh banda lpia ne
[8:08AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**12
To shikenn turo talatun. Ta shige gida da sauri
talatu ta fito ta shige gaban mota kusa da direba,
ihsan na kwance jikin babanta, yana lallashinta
Ahmad yana tsunkuninta suna dariya.
Mansura takaici ya cikata, wai me zainab take
yiwa Aliyu ne da yake musu irin wannan kauna?
Kafin su karasa airprt Ihsan har tayi bacci. Suna
fitowa daga mota talatu ta karbeta, ta koma
motar direba yasu suka tafi.
Mansura kanta ya kwance da ganin gidansu na
abuja, du da dai na kano da suke ciki yafi shi
girma da kyau, amma tsarin wannan din ya
burgeta sosai, kamar gidan turawa.
Tuni Aliyu ya fice cikin sauri ya nufi ofis. Mansura
da Ahmad sun zagaye ko ina, bangare daya ne a
kulle, ta tabbatar wajen zainab ne, tunda bai bude
musu ba.
Sai dare Aliyu ya dawo abun haushi ga yunwa ga
wahala, amma yana zuwa ya tarar da mansura da
Ahmad du sunyi yaushi, wai yunwa suke ji basu
ci komai ba.
Ya hauta da fada dan me ga kayan abinci nan
bata girka ba? Tace ai babu gas kuma ta masa
waya taji ta a rufe.
Yace baki bude jakunan da akwatina da muka zo
dasu kin jere kayan ba?
Tace ai bata yi komaiba, yayi tsaki matsalarki
kenan har yau baki san yanda zaki kula dani ba.
Ya tashi da kanshi ya bude kayan ya fito da
soye-soyen da zeey ta musu, dambun nama, kec,
meat fy, samosa, cin-cin da wainar shinkafa, da
sinasir da fukasau da soyayyen miya.
Kawai sai mansura tayi turus, lallai zainab tayi
nisa wajen siye zuciyar Aliyu, ita yaushe tayi
tunanin haka ma bare tayi, abu daya tasan tana
da yaji.
Aliyu yasa Ahmad ya shiga kicin ya dauko filet da
cokala, ya bawa Ahmad shima ya diba. Yaja gefe
ya fara ci, yace wa mansura ki debi abunda zaki
iya ci, ki zuba ragowar a firij. Ki debo mana ruwa
da lemu tunda komai sai ance kiyi.
Ta zumbura baki, ta tashi tayi yanda yace, ta
zuba nata abincin ta zauna tana ci.
**** ***** ****
zainab ta shiga damuwa sosai, na rashin
tafiyarta, tana son zaman kano saboda iyayensu
da 'yan uwansu.
Amma gaskiya tafi son zaman abuja, saboda tafi
kusa da mijinta, tasan halinshi tasan damuwarsa.
Tasan yayanta mai son a kula dashine wajen
cikinsa da biya masa bukatarsa to tasan
auntynta tun tana ita kadai ta riga tayi sakaci da
hakan.
Ta kalli Ihsan data gama rigimar neman abbanta
tayi bacci. Ta mike ta shiga toilet ta dauro alwala
tazo ta kama nafila tana musu addu'ar neman
zaman lafiya a tsakaninsu da cikawa da imani.
Tana shafa taji nutsuwa ta saukar mata, taji
zuciyarta wasai, babu kunci ko damuwa.
Tahau gadonta ta kwanta, wayarta kamar jira
take tahau burari, ta dauka da murmushinta, tace
"hello gudan raina, ya kake? Ina auntyna da
dana?
Yayi wata irin sanyanyar ajiyar zuciya, yace
rayuwata ina Ihsan dina tayi bacci kota nata
rigimar nemana?
Um-um ta hakura tayi bacci.
To saka min naji munsharinta don na tabbatar da
lafiyanta.
Tasa a wayar a hancin Ihsan, yaji numfashinta
yana sauka a hankalo, tasa a kunanta kaji ko?
Um Alhdllh naji bebyna kalau take. To ya dan
bebyna baya tare da matsala ko?
Kinsan tunda nayo miki waya mun sauka, to tun
daga lokacin ban samu kaina ba sai bay isha
inata aiki.
Cikin tausayawa tace, wayyo yayana, ka wahala,
sannu yayana, koda yake ai ka huce gajiyar yanzu
dan nasa aunty ta gasa ma jikinka da ruwan zafi,
kuma tayi maka tausa, nasan gajiya ta gudu sai
wacce zaka sake dauka yanzu ko yaya?
Yace, don kinga bana kusa kika samu bakin gaya
min haka ko?
To bashi du ranar dana dawo na ware gajiyar
akanki.
Tasa dariya tace yaya kayi hakuri bazan kuma ba
kaji?
Yace nasan ranki ya baci sosai rashin tahowarmu
tare.
Amma don ki kwantar min da hankali kika dake,
kika nuna min bakomai kina goyon bayan nayi
adalci a tsakaninku, don kina so ranar lahira na
tashi cikin maza salihai, masu adalci a tsakanin
matayensu, baki nuna son zuciya ba.
Tace yaya dare fa yayi, kada mu shiga hakkin
auntyna, yaya saida safe. To Allah ya tashemu
zeeyta.
Kwana hudu ranar jumma'a da azahar ya baro
ofis ya taho yayi shiri, ya taho kano.
Zainab kuwa tana cike da doki anata yi masa
girke-girke da soye2 da lemuka.
Taci kwalliyarta ita da Ihsan.
Ihsan tana cikin 'yar shimin riga ruwan hoda me
adon les, a kirjin da hannun rigar sai dan jeans ga
dan takalminta me madauri kasansa na glass,
yarinyar tayi kyau matuka.
Tanata tsalle2 ta acikin motarta a harabar gidan,
motar Aliyu ta shigo yana ganin Ihsan yaji
zuciyarsa ta cika da farin ciki da annashuwa
direban bai gama tsayawaba da motar ya bude
ya fito da saurinsa Ihsan tana ganinsa ta kama
dariya, tana dago masa hannu da cewar Abbana!
Abbana ya dauketa ya kankame yana murna, ya
jiyo da daddan kamshi sahibar tasa ya daga kai
yana kallonta tana masa murmushi, ya dago
mata hannu ta taho ta shige jikinsa, suna dariya
yayi mata kyakyawar runguma yasa hannunsa a
mararta, ya rada mata a kunanta ya bebyna?
Ta rangwadar da kai lafiyarsa lau sai maraicin
Abbansa da yayi.
Ya rada mata ai gani nazo zamu kasance dashi
na tsawon awa biyar.
Ta kwace jikinta tana dariya, "a nifa yaya ba haka
nake nufi ba.
Yace ai kin manta da bashina da kika ci ta waya?
Tasa dariya niba ruwana.
[8:09AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**13
Tasa dariya nidai ba ruwan ga 'yarka nan me
shegen wayo tana jinka.
Ya sumbaceta yace Ihsan din Abba
yarinyar tayi dariyarta tace Abban Ihsan, gaba
daya suka sa dariya suka fada cikin gida yana
rungume da iyalansa.
Suka zube a falo,
ina Amadina.
Yana can ya fara zuwa makaranta yau.
Ta rinka cire zare masa kayn jikinsa ta barshi
daga shi sai gjrn wando taja hannunshi zuwa
toile inda ta hada masa ruwan wanka.
Yana fitowa ta tareshi da tawul ta goge masa
ruwan jikinsa, ta shiryashi kamar karamin yaro, ta
rikoshi zuwa tebir.
Yana cin abincin yana zuba mata santi, zainab
kici gaba da tallafin rayuwata, kina min tattalin
so, kada ki barni naje kasa don kece farin cikin
rayuwata.
Ta taso da sauri ta rungumeshi, ta hada bakinta
da nasa, tana yi masa hot kiss da ya rikitashi,
yake kokarin mantar dashi a wacce jiha yake.
Ta cika shi tasa bakinta daidai kunnensa, i luv u
yayana, i care 4 u, life iz gud.
Ta rikitashi da kalamanta inda ita kuma ya
rikitata da soyayyarsa, tuni ya manta da batun
cewar abinci fa yake ci a falo.
Sai da ya samu nutsuwa shi kadai ya rinka yiwa
kansa dariya, zainab kuma abun ya bata kunya.
Ta fada dakinta ta shiga toilet, shima dakinsa ya
shiga ya fada toilet.
*** *** *****
Rayuwa mai dadi zainab tana zamanta cikin
kwanciyar hankali, bata da damuwar komai tana
cikin danginta da 'yan uwanta, kowa yaso ganinta
zai zo gidanta su wuni suna hira, amma ita bata
fita ko ina, sai dai in fitar ce ta kama dole.
Sai dai in Aliyu yazo du inda take son zuwa zasu
je tare.
Mansura kuma tana abuja, amma du abun duniya
ya isheta, saboda bata saba da zaman kadaici
ba.
Ahmad in ya fice tun safe ya tafi makaranta sai
yamma zai dawo.
Haka Aliyu tun safe zai fice ofis sai dare zai dawo
da ya gama abunda yake yi bacci zaiyi don
gudun kada ya makara.
Bata da lokaci na samun hira dashi
ko magana dashi, gashi ba wanda ta sani, kuma
baya barinta fita ko ina.
Kokari me aiki tazo tayi mata gama abunda take
yi ta fice.
Abun duniya ya isheta, bata da wani aikin yi sai
kallo, sai dai idan ta gaji ta kwanta ta dauki waya
ta bugawa iyayenta da 'yan uwanta.
Da abokanan arziki suyi ta hira dasu.
Take gayawa yayarta saratu matsalarta dake
damunta, kawai inba babu dama kice ya dawo
dake gida, ba gwanda zaman ki acikin dangi da
'yan uwa ba.
Ko wani abune ma ai inkin ga danginki kyaji
sauki.
Tce to bari inya dawo daga ofis nayi masa
maganar zuwana tunda gobe jumma'a zai zo to
sai anjima kya bugo naji yanda kuka yi dashi
sukayi sallama kowacce ta ajiye.
Karfe takwas na dare Aliyu ya shigo saida ya
kammala du abunda zaiyi ya zauna.
Tace Aliyu.
Yace um hum, inajinki.
Tace gobe inaso in bika naje gida.
Yayi mata wani irin kallo, yace zancen ne baki
gaji dayi ba.
Na gaya miki keda gida ba yanzu ba.
Tasa kuka, wannan wane irin al'amarine, kai baka
da lokacin da zaka zauna a gida Ahmad sai
yamm yake dawowa,
ana biki ana suna da mutuwa amma bazaka kaini
naga gida ba?
Yace itama wacce kike kishi da ita tana nan din
kika bambareta ke kika dawo, itama haka take
zaune.
Kuma baki ga ina yawan kaita gida ba, saita
shekara, don haka wlh kema saikin shekara
sannan zakije gida.
Ta dora masa hannu aka ta kurma masa ihu
wayyo na shiga uku, baya son jin kukan dan haka
ya tashi daga falon ya koma daki ya kwanta.
Ta zauna a falo taci kuka saida ta gaji dan kanta
tayi shiru.
Ta tashi ta koma dakin ta rabe kusa dashi ta
kwanta, tana ajiyar zuciya ya jawota jikinsa, baki
daina kukan nan kina so kanki yazo yana ciwo
ko?
Tace ko meye ai kaika jawo min, nagane bansan
abunda yasa baka kaunta ba, iya bakin kokari dai
inayi maka don na kyautata maka, kuma kai baka
so kasani farin ciki, kafi so kaita ganin raina a
bace.
Yace mansura inkika fadi haka bakimi adalci ba,
tun kafi na auri zainab naso na mayar dake
kaduna wajen aikina, kika nuna min baki da
ra'ayi, ashe don na dawo da zainab wajen da
nake aiki har kyace nayi miki rashin adalci?
Kika je kika hadani da kawuna, wanda shine
mahaifin yarinyar nan, ya rinka min fada akan
bana miki adalci. Yasa aka bar jikarsa da 'yarsa
aka taho daku.
Makarantar Ahmad mai tsada yaron nan yana
ganewa, kika sa aka rabashi da makarantar, aka
canja masa wata, gashi nan saida suka maidashi
baya, saboda karatun nasu ba iri daya bane.
Sannan yanzu kuma kice min zaki koma kano ki
rinka min wasa da makarantar yaro, ni da ke
waye mijin? Ko ina tsoronki ne, bare a fara cemin
mijinta ce?
Don haka keda zuwa gida saikin shekara, anwa
suma Ahmad hutun shekara. Se kuje.
*** *** ***
Ranar wata jumma'a yake ce mata mansura zan
kai tsawon sati uku fa a gida ban dawo ba.
Ta dafe kirji saboda me?
Yace. Lokacin da sakanni din cikin zainab ya
nuna ya kusa, kinga dole na zauna kusa da ita,
don kada haihuwar tazo mata bakowa
tayi masa wani irin kallo saboda in haihuwar tazo
kai zaka cire mata ciwon?
To wllh bazan dauki wannan rashin adalcin ba.
Ko mu tafi tare ko kuwa kayi kwana ukun ka ka
dawo.
Ya daka mata tsawa, ki rinka sanin irin kalmar da
zaki fadamin, ko kuma zan bar matana da tsohon
ciki ne kullum ina farga bar halin data..
[8:09AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**14
Kina tunanin zan bar matana ne da tsohon ciki,
nazo na zauna anan kullum ina fargabar halin
data ke ciki? Kinyi kuskure nasan darajar da, da
haihuwa, bazan iya kwatanta miki yanda nake
kaunar 'ya'ya ba, ya'ya na daban suke a
zuciyata. Ki kiyaye abunda kika san zai tabamin
'ya'yana, koda harara ce wllh saina dauki
mummunan mataki akai, ya fice ya barta.
*** **** ****
Ranar talata, ranar kwanan Aliyu hudu a kano,
cikin dare zainab tana rungume a jikin Aliyu yana
lallabata.
Cikin baccin taji an mintsineta, ta farka firgigit,
tana salati Aliyu ya mike a rude, yana tayata
salatin, saida suka kai karshe sannan yace mata
menene zainab?
Yaya ciwo, Abban Ihsan wayyo ka taimakamin, ya
rungumeta yana rarrashinta, tare da lailaya mata
bayanta, tare da busa iska kadan2 a kunnenta har
bacci ya dauketa, ya shimfideta yasa kayansa da
sauri ya fito mata da nata kayan.
Ya dauki Ihsan ya kaiwa talatu ita.
Yana dawowa dakin ya samu zainab ta farka da
wani azababben ciwo tana ta murkususu.
Yayi saurin rungumeta sannu zeeyta, ya salube
mata rigar baccin yasa mata kayanta, ya dauketa
zuwa mota.
Da kyar suka karasa asibiti, tana ta salati tana
murkususu, gashi tana jikinsa ya lafe da hannu
daya.
Suna isa asibiti likitoci suka karbeta, mintuna
goma sha biyar da shiganta dakin kukan beby ya
cikawa Aliyu kunne, wani farin ciki da murna suka
baibaye shi.
Ya daga hannu sama yana tayiwa Allah godiya,
saiya ga hakan ma baiyi masa ba, yayi alwala ya
shiga masallacin asibitin yayi nafila raka'a biyu ta
nuna godiyarsa ga ubangiji.
Ya nufi dakin da zainab take, sun gama gyarata
ita da jaririn fes dasu, kamar ba ita ta haihu ba.
Ya karaso da fara'arsa, sannu zeeyta Allah yayi
miki albarka, nagode zainab, ya dauki jaririn fari
sol dashi ya rungume dan yana jin wata irin
kaunarsa tana ratsa shi.
Yace zainab yanzu wannan yaron ma nawa ne?
Zainab nagode, kin kawomin Alheri cikin gida, kin
sadani da farin ciki mara yankewa
zainab 'ya'ya rahama ne, inason 'ya'ya da yawa,
zeeyta ki daure kita haifo min kinji?
Ya shafi kanta.
Tace yaya haihu ta uku, amma sai sambatu kake
yi, kamar wanda bai taba yi ba?
Yace, zeeyta kin san kuwa yanda nake son
haihuwa? Inaso naga na tara 'ya'ya da yawa,
naga na hada family kamar mutum guda arba'in
ace du nawa ne.
Ta bude baki, A yaya arba'in fa kace kana
sha'awar kara aure kenan?
Yace um-um du ke zaki haifamin da auntynki.
Tayi dariya yaya ai sunyi yawa, ba zamu iyaba.
Zaku iya tunda kuna tare da gwarzon namiji.
Ya dauki waya ya buga gida, karfe uku na dare ya
fada musu albishir din haihuwa.
Da sha daya na safe aka sallamo su ta taho gida
da tawagar 'yan uwanta.
Saida suka dawo gida Aliyu yayiwa mansura
waya, yake gaya mata zainab ta haihu a daren
jiya
tace "me kuma ta haifa?
Yace kyakyawan , sankacecen dana fari kal dashi
me kama dani sak dana miji.
Gabanta yayi wata irin mummunan faduwa,
dakyar ta iya cewa Allah ya raya.
Suna gama wayar, ta bugara yayarta saratu, take
gaya mata abunda ya faru, tace kin gani kin cuci
kanki da yanzu kina da 'ya'ya hudu ko biyar dole
du abunda zata haifa a bayan naki suke, yanzu
kuwa fa ba gashi harta fiki ba?
Tace na shiga uku yanzu ni ya zanyi, kina gani a
abujan ma nayi ziyartar asibiti yafi guda nawa,
likita yace mahaifata normal ba abunda ya
sameta, a shirye take ko yaushe zan iya daukan
ciki.
Amma har yanzu shiru babu labari.
Kedai ki samu ki lallaba shi ya barki zuwa sunan
nan, sai musan abunda za muyi akai, don dole
sai an hada da rokon Allah.
Ranar kwana biyu da haihuwar tayiwa Aliyu waya
tace zasu zo wajen suna.
Yace a'a aina gaya miki sai kun shekara zaku zo
dan bazan yarda ki cutar min da ki rinka yi masa
wasa da karatu ba.
Tasa masa kuka, ni gaskiya ba yarda da abinda
ka shirya yi wanda ba kaso in gani shiyasa kawai
zaka hanani zuwa.
Du abunda naga damar yi kin isa ki hanani ne?
Karki manta fa da na samu, zan iya kyautar da
abunda na mallaka don nuna bajinta, da godiyar
Allah bisa kyautar mutum da yayi min.
Kema ga key din mota sabuwar kira, ta yayi na
baki, ki hada da dayar sun zama biyu, albarkacin
wannan haihuwa da akayi min.
Tasa kuka banaso bana farin ciki da kyautar da
kayi min, ka barni ni kawai nazo naga abunda xa
ayi.
Ya kashe wayar yayi murmushi kawai ya girgirza
kai.
An sha shali ranar suna, a ranar kuma aka aiko
masa da takardar karin girma, a ranar Aliyu
yayiwa 'yan uwansa bajinta kanansa su hamza
dasu sadik da faruk yayun zainab, ya basu gidajr
guda hudu a jere da aka gama ginasu, yace su
nemo matan aure, ya fito da keys na gidaje
kanana ya bawa sadiya da ni'ima, yace gashi
kuma kwasa 'yan haya.
Ya bawa Abba da daddyn zainab mukullayn
gidansu da aka gama.
Tsawon wata uku basa cikin gidansu suna na
gidan zainab data zauna aciki.
Haka ya rinka bin 'yan uwa da dangi yana musu
alheri, aka radawa jariri sunan Abbansa, suna
kiransa Arfat.
Aliyu yaje da kansa ya bawa maihaifin mansura
key din gida mai kyau.
Du abunda akeyi mansura tana samun labari ta
waya, hankalinta atashe yake don ita gani takeyi
bari da dukiyarsa yake yi kamar zata kare.
via #Justice_Hamzat
[8:10AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**15
Rayuwa ta mike, jin dadi da kwanciyar hankali
sun saukar musu, basu da matsalar komai
Arfat yayi bul-bul dashi, fari sol kyakyawa.
Watan arfat hudu dai-dai wannan lokacin ne
kuma mansura suka cika shekara a Abuja.
Ranar litinin da yamma mansura, tayi masa
maganar zuwansu gida, yace su fara shiri saura
kwana shidda su tafi.
Tace kayi mana alfarma mu tafi jibi, kaga saura
kwana bakwai bikin yaya saratu, ma fara shirye-
shiryen da zamuyi.
Ya girgiza kai kwana shidda na fada miki in kinje
kwayi shirin da zaku yi.
Taso tayi magana ganin ba fuska ta zumbura
baki ta bar wajen.
Da dare suna cin abinci da Ahmad mansura tana
gefe daya tana kallo
Ahmad yace, Abba dazu fa da ina waya da Ihsan
cikin maganarta tace min arfat bashida lafiya.
Cikin sauri Aliyu yace, um-uhum?
Har yana kwarewa, yace dazu da mangariba fa
munyi waya da zainab, amma bata gaya min ba.
Ya dauki wayansa ya kira zainab ringin daya ta
dauka, yace zeeyta me yake damun babana?
Wallahi yaya zazzabine, inaga dai awon hakorine,
don yanata amai
ya daka mata tsawa da gaske bashida lafiya
kenan, amma baki gaya min ba?
Yanzu me kika yi masa ina kika kaishi?
Tace ba ko ina?
Ya doka mata tsawa kina haukane ki barmin yaro
da ciwo?
Dif ya kashe wayar ya bugawa hamza, "hamza
maza kaje gidana ka dauki arfat ka kaishi asibiti.
Yanzu nan zanyiwa doctor waya.
Yana kashewa ya mike yana zagaye falon,
hannunsa goye a bayansa, yanata busar da huci.
Ya sake buga wayar yauwa doctor za a kawo
maka yarona.
Ai gashima sun iso.
Yauwa dr ka kulamin dashi sosai
likita yace kada ka damu, zan kula sosai.
Yauwa nagode.
Yana kashe wayar ya kalli mansura ke ki hada
abunda zaki hada, da asuba zamu tafi.
Ta kalleshi cikin mamaki ba cewa kayi sai nanda
kwana shidda ba?
Ya girgiza kai bazan iya ba, bansan wane hali
yarona yake cikiba.
Karfe tara na safe suka shigo gidan ba wanda
yasan da zuwan su.
Gidan a gyare, mansura tayi bangarenta, Ahmad
ya biyo Aliyu bangaren zainab.
Zainab tana zaune cikin kwalliyarta tana ta
kamshi.
Umma da mama da ummi sunzo tun bakwai na
safe duba arfat, yana hannun ummi tana bashi
magani ta dabara, Aliyu yayi sallama, zainab ta
bude baki cikin mamaki a ranta tace jiya da
sassafe ya tafi.
Kallo daya yayi mata ya dauke kai,
tace yaya sannu da zuwa.
Ya daga mata hannu kawai, Ihsan ta taho da
gudu ta rukunkumeshi
ya dauketa yana sumbatarta.
Ya durkusa yana gaida iyayensa, ya ajiye Ihsan
ya dauki arfat, yana duddubashi yayi tsaki, yaro
jikinsa du ya saki, babu kuzari, babu wani karfi.
Ummi tace sharrin amai ai yafi ga haka, ya dauki
maganganun yana dubawa ya fice dashi a kafada.
Yace musu, umma bari na maidashi wani asibitin.
Ihsan ta biyo shi a guje, Abba zanje, ya riko
hannunta suka fita
Ahmad ya shiga da gudu ya fada kan cinya
zainab, ta rungumeshi
amadina tare kuka taho da aunty?
Umma tace me gidan saukar yaushe?
Sannan ya kula dasu, ya nufi wajensu yana
dariya, ya gaishesu ya fice da gudu ya nufi
bangaren mansura, yana gaya mata su umma
suna nan dole tazo ta gaishesu, tayi musu barkar
haihuwar zainab.
Tare da tambayar ya mai jikin? Suka ce da sauki.
Zainab ta dan rissina aunty ina kwana?
Ta dago ta kalleta, a zuciyarta tace wai wani irin
kyau da kullum kamar kara mata sabuwar halitta
ake. Ashe ba rayuwar abuja ce tasa ta wannan
kyaun ba? Ko ina take kyan nan bazai gushe ba.
Zainab ta sake maimaitawa aunty ina kwana?
Firgigit tayi ta amsa lafiya lau.
Ta ttashi ta fita daga dakin.
Ummi ta bugawa Aliyu waya, lafiya kuwa mukaji
shiru?
Aliyu yace bakomai ummi sun canja masa magani
ne, sun kuma sa masa karin ruwa, yana karewa
zamu taho.
Tace to shikenan yanzu mu zamu biya muga jikin
nasa, sai mu wuce gida.
Suka yiwa zainab sallama suka tafi
zainab ta mike ta shiga kicin ta dafa musu
wannan, ta soya wacan wai duk kokarinta ta
faranta masa
taga yayan nata yana fushi da ita.
Sha biyu dai-dai suka shigo, abun mamaki Arfat
ya ware, yanata wasansa da dariya.
Zainab tayi kwalliya ta daukan hankali, tana ta
zuba kamshinan nata mai dadi, ta tareshi yaya
sannu da zuwa.
Ya kauce ya barta a tsaye ya wuce ciki, ya
shimfide arfat ya shiga wanka, ta dauki arfat
tanayi masa wasa yanata dariya, tasa masa nono
a bakinsa yasha ya koshi.
Ahmad ya shigo aunty mami naga sun dawo,
Ihsan tana gurin mama kawo arfat din.
Tace gashinan Amadina.
Ya daukeshi, kai aunty mami kin iya haihuwar
turawa, masu kyau, ni dadi nakeji naga kannena
masu kyau haka.
Tayi dariya, Allah Amadina, zoka kaiwa mama
abinci kazo kuci kaida Abbanku.
Yace to aunty mami rikemin kanina yanzu zan
dawo.
Ya dauki ya tafi, ta saka arfat a ruwa, ta sake
masa wanka, ta canja mishi kaya yanata kamshin
hoda ta sashi cikin kekensa na zama.
Aliyu ya fito ya nufi arfat, ya daukeshi, Abbana ya
jikin? I luv u Abbana, ta zauna kusa dashi, yaya
barka da dawowa ga abincinka.
Bana ci.
Haba yaya don Allah kayi hakuri
meyasa bazaka ciba?
Ki kyaleni kawai zeey kin batamin rai, ki barmin
yaro da ciwo ki ki yimin waya, to da ya mutu
saidai na tarar da gawa kenan?
Ya tsaya bakin taga yana kallon Ahmad da ihsan
suna ball.
Via #Justice_Hamzat
[8:13AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4***16
Ya tsaya bakin taga yana kallon Ihsan da Ahmad suna ball
a harabar gida.
Yaji dadi a ransa, zainab ta taso ta daura kanta abayansa
tana magana, cikin sanyinta.
Kayi hakuri yayana ka gafartamin
naga baka dade da tafiya ba, kuma ka barshi lafiya lau,
saina kasa gaya maka, ina gudun tashin hankalinka.
Saina rasa ya zanyi da yaron, ga talatu ta tafi duba jikarta
ba lafiya, na rasa ya zanyi dashi, ni nasan bazan iya fita
bada izninka ba, shiyasa kawai nasa yaron a gaba ina
kuka.
Yaya ka yafe min, bada niyya nayi hakan ba.
Ya juyo ya rungumeta yana share mata hawayen, yaji
tausayinta, ya juyo da ita ya rungumeta yana rarrashinta.
Shikenan naji, ya isa daina kukan, na hakura muje ki bani
abincin.
**** *** ******
da yaje gida yake cewa Alh yana so zai rubuta takardar
neman alfarma a dawo masa da ofis dinsa kano, saboda ya
zauna cikin danginsa da iyalansa.
Alh yace wannan shawara tayi daidai, tunda ka fara tara
iyali dole ka zauna a waje daya, ko don kulawa da ilimin
'ya'yanka ma.
Hakan akayi kuwa baisha wata wahala ba, wajen amince
masa, aka bashi ofis a kano.
Ga harkokin kamfaninsa komai yana garawa yanda yake
so.
Zaman mansura da zainab babu irin kyara da wulakanci da
cin mutunci da mansura bata yiwa zainab, amma zainab
saita kwantar mata da kai tana binta a sannu, bata kuma
bari Aliyu ya sani, bare yayiwa mansura fada, ita dai zainab
ta dage da gayawa Allah basu zaman lafiya.
Cikin hukuncin ubangiji kuwa, Allah ya amsa addu'arta.
Ta shiga falon mansura arfat na biye da ita, watansa sha
biyar yanata yawonsa ko ina, amma bata yaye shi ba.
Tace aunty zanje dubo jikin hajiya, ga arfat nan kafin
Ahmad da Ihsan su dawo islamiyya.
Har zata fita, mansura tace ke dawo ki dauki danki.
Zainab tayi murmushi tace dana ko danki aunty? Ai kin fini
karfi akan 'ya'an nan dani dasu du mallakarki ne.
Mansura tace wai 'ya'yanki da kike turowa su wuni a
bangarena ke kina naki bakya tunanin na cutar miki dasu,
kona dakesu, ko nayi musu wani mugun abu?
Zainab tace haba aunty na dade fa da sanin halinki, tun ina
'yar shekara takwas nake hannunki, da kina da mugun abu
dani zaki fara yiwa.
Aunty kina da kirki da hakuri kullum dauriya nake yi, har
nake iya hada ido dake. Amma ina mai jin nauyi da kunyar
aure miki miji danayi. Tasa kuka.
Mansura ta taso ta rungumeta, kada ki damu zainab na
dade dayin nadaman irin abubuwan da na rinka yi miki, don
kin auri Aliyu
wanda wauta nayi da son zuciya, tun fil-azal Allah ya rubuta
ke matarsa ce, to ya zanyi da wannan rabon?
Tunda kika haifi Ihsan Allah ya cusa min kaunarta a raina,
haka arfat gani daya nayi masa naji kaunarsa ta ratsani.
Kiyi hakuri zainab da abunda nayi miki.
Ta rungumeta, wayyo aunty dan Allah ki bari ban taba
rikonki da komai a raina ba, na yafe miki aunty nima ki yafe
min.
Na yafe miki zainab.
Aliyu ya fito daga daki yana yi musu tafi, yace nagodewa
Allah da kuka hade kanku, ga cek na milyan biyar-biyar kuja
jari.
Suka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 14