aunty
gaya masa." tace kinsan in ni na gaya masa cewa
zaiyi inason koya miki yawo.
Ta mike bari naje, aunty kiyi min addu'a
Allah yasa ya barni." tace "to Amin."
yana shirin fita mansura ta kawo masa
jakarsa, zainab ta fito ta durkusa tace
"yayana. Bai kulata ba yace "uhm! Ya akayi?
Yaya dan Allah zanje gidan aunty
sadiya? Me akeyi a gidan?
Bikin kanwar mijinta ake yasira, shine
nake neman alfarma dan Allah yaya
kabarni naje. Ya daga kai kada ki dade. Tace to
yaya
nagode." yana fita ta tafi gidan sadiya,
direba ya kaita. A can ta tarar da ni'ima
suka rugume juna suna murna. Kinyi sa'a
'yar uwa ya barki."
kinganni dai, yayan namu ne sai a hankali. Amma
yau ba laifi fuskar tasa a
sake take. Hu! Aunty wannan material din
fa? Tana daga su tana yaba kyansu.
Tace Abban yasir ne ya kawomin su
tsaraba, amma naga sun zo akaya zan
sai muku. Yauwa auntyn mu kina burgemu fa.
Suka
gama tsra shirinsu na zuwa fati, wani
hadadden material ne da aka sake fito da
kyansa da wani dinki mai kyau.
Gaba daya su ukun sunyi kyau amma ba
kamar zeey da kamar don ita aka yoshi. Suna
bayan motar sadiya da mijinta suna
gaba. A gidan fatin suka bi bayan amarya
da ango suka rakata har mazauninta.
Yaron sa'adu bori yanata kida da waka
'yan mata sunata rawa daga baya aka
tsaya da kidan, babban kawar amarya tazo ta yi
addu'a tareda yiwa bakin da
suka zo barka da zuwa. Daga nan ango
da marya suka tashi suka ja zugar
kawaye da abokai suna biye da bayansu
har wajen masu sabis. Kowa shiyake
sabis din kansa. Zainab duk inda tyi idon mutane
ne akanta, ita kallon ya isheta,
don bata saba da irin wannan shiga ba,
ta saba kullum tana hijabi, to ita abunda
yafi damunta ma sha daya har tayi, tana
jin soron yaya fa.
Amma yaya sadiya da mijinta sunce har dakinta
zasu rakata su bawa yaya
hakuri.. Wata kawarta tazo taja
hannunta, dole saita yi rawa. A hankali
take juyawa, kusan maza hudu ne suka
rufa kanta suna mata liki.
Kamar daga sama yaya Aliyu ya diro wajen, saiji
tayi an damki hannunta. Ta
juyo a tsorace dan ta razana, ganin
yayanta ya hade rai kamar wanda bai
taba dariya, saita firgice ta tsorata. Ya
funciki hannunta yayi waje da ita, ya
bude mota ya turata ciki shima ya shiga. Ta
takure a tsorace take, saboda tasan
halin yayanta sarai, akwai zafin zuciya.
Aliyu ransa ya baci sosai ganin maza
suna yiwa zainab liki, ba dai sonta suke yi
ba? Wani abu ya soki kirjinsa, ya rinka
ganin bibbiyu a idonsa, yayin da motar ta fara
tangal-tangal kamar zata kifa.
Zainab ta fara salati ta baro kujerarta ta
rungume Aliyu tana ihu tana salati.
Tirkashi! Mu hadu a littafi na biyu,
waishin menene ya soki zuciyar Aliyu?
via #Justice_Hamzat
[9:14AM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 2**1 & 2**2
A hankali ya dawo hayyacinsa,
yaci gaba da maimaita salatin daya ji zainab tanayi. Saida
taji ya samu nutsuwa sannan itama tafita daga tsoron data
shiga, tayi saurin komawa
wajenta. Yaci gaba da tukin a hankali cikin nutsuwa, zainab
ta fashe da kuka tace, "don Allah yaya kayi hakuri bazan
kuma ba. Don Allah ka yafe min." da kyar ya iya bude
bakinsa yace,
zainab meya hadaki da wa 'yannan maza da suka
rufu suna yi miki liki? Tace "wallahi yaya ban san su ba, ban
taba ganinsu ba sai yau. Kuma ko magana bata hadamu
dasu ba, wallahi ina zaune
wata kawata tajani gurin rawar, kawai sai gani nayi anamin
liki. Kayi hakuri kaji yaya bazan kuma ba. Ya daga kai, yace
shikenan ya wuce."
da sassafe aunty sadiya tayo mata waya tana tambayarta,
"ince kodai yaya bai dake kiba? Tace
baiyi min komaiba." ta bata labarin abunda ya
faru, suka yi dariya gaba daya. Bayan sun gama
hirarsu, ni'ima ta bugo ta tambayi abunda yaya
yayi mata. Itama ta bata labarn yanda suka yi.
Ni'ima tace, "dadina da yaya akwai zafin zuciya,
amma inka bashi hakuri shikenan komai ya wuce.
** ** ** ** *** ni'ima ce ta shigo, suka rungume
juna, suka zauna talatuwa ta shigo musu da
abinci, ni'ima tace, aunty sadiya fa tace muje
goben ta sai mana material din, kala uku ta dibar
mana. Zainab tace sai auntynmu, gaskiya mun
gode, kawai daga can sai mu wuce gurin dinki.
Ni'ima tace daman mama ma zata karba mana
kudin dinki awajen Abba." ta mike, tafiya zanyi."
haba yaya ni'ima tun yanzu? Wallahi inkin zo
bana so ki tafi." ta dafa kafadarta, kiyi hakuri
zainab, na baro yaya a gida, kinsan yanzu zai
taho, idan ya sameni anan, gobe inkin tambaye
shi zuwa gidan aunty sadiya cewa zaiy ni nake
zuwa nake saki yawo. To shikenan yaya ni'ima
sai goben." sha biyun dare ta tashi tayi na filla,
tai ta addu'o'inta tayiwa mahaifiyarta addu'a tare
da mahaifinta, da fatan Allah ya bashi zaman
lafiya da matar da ya sake aura. Ta gama
shirinta, ta gama tofa addu'o'inta ta kwanta, taja
bargonta zata rufa. Yayinda ta jawo wayarta zata
kashe, dai-dai lokacin da zata kashe, sakkonni
suka shigo. Mamaki ya sake kamata, ta fara
budewa ga abunda yake ciki. "wah! Zeeytah
tsananin sonki da kaunarki kullum yakan hanani
bacci. Zeeytah yaushe zaki ban dama na
bayyana gareki, na matsu na aureki. Na jini
manne a kirjinki ina bacci kona ji sauki da
radadin sonki. Wayyo zeey kece rayuwata."
subhanallahi, waye wannan? Na shiga uku! Allah
yasa dai ba aljani bane. Ta sake bude sakon ga
yanda yake. "zeeytah kaunarki takai makura a
zuciyata, dab nake da rasa rayuwa saboda zugin
sonki. Wai yaushe mafarkina zai zamo
gaskiyane? Na jiki kan kirjina ina lallaminki ina
riritaki, na dameki da soyayyata mai hanani
bacci. Ta cillar da wayan tana cewa na shiga
uku! Waye wannan? Waya ke son rikitamin
zuciya? Mutumne ko aljan? Allah gani gareka,
Allah ka kawomin sauki. Dakyar tunani ya barta
tayi barci. Ranar alhamis da yamma bakonta
yazo, saurayin da suka hadu a kofar wajen salon.
Ahmad ne ya shigo da gudunsa yana cewa,
"aunty mami kizo inji wani dan gayu a mota mai
kyau. Tace "dan gayu a mota mai kyau? Yace ka
kirawo ni? Eh, aunty mami, yace nace wai
mutumin da muka hadu dashi ranan." mansura
tace mutumin da kikace kin bawa katine. Saiga
talatuwa ta shigo tana dariya, tace "don Allah
aunty mami. Yanda Ahmad yake gaya mata, tace
don Allah yau dai kije kada ki kori wannan, ki
taimaka kije. Mansura tace kai mata kujera
farare guda biyu harabar gida, yanzu zata zo.
Mansura tace kije ki shirya, ba kyau fa
wulakanci." ta mike ta shiga dakinta ta sako
hijabinta ta fito. Mansura ta kalleta tayi tsaki,
meye haka? Yanzu zance ma saida hijabi zakije?
Wallahi kedai gidahuma ce kije ki yafo karamin
mayafi." tace don Allah aunty ki kyaleni, yaushe
zanje gaban wani kato da dan karamin mayafi ya
karewa halitta na kallo ya cuce ni? Mansura tace
saiki tayi 'yar kauye kawai." tayi murmushi ta
wuce ta tafi harabar gidan. Yana zaune akan
kujera, ya rinka sakin murmushi dan yaga ta taho
gareshi. Ta zauna tace barka da zuwa." ya amsa
"yauwa zainab ya gida, kun dawo? Ta amsa da
"lafiya lau. Yace "to dama gaskiyar abunda yake
tafe dani, na ganki kuma gaskiya naji ina sonki,
ina kaunarki, ina matukar son na aureki. Shiyasa
nake neman amincewarki, daki amince ki aureni
dan mu zamo abokanan rayuwan juna nan gaba."
tace mishi, bakomai Allah ya zaba mana mafi
Alkahiri. Yace Amin. Kin amince naci gaba da
zuwa kenan? Ta daga masa kai. Yace naji dadi,
ubangiji Allah ya tabbatar mana da alkahairi."
talatuwa ta kawo mishi ruwa da lemo, zainab ta
zuba masa ruwa da lemon a kofuna, tace masa
bisimillah mana, kasha." ya dauka yana sha suna
ci gaba da hirarsu, yayi mata bayanin kansa.
"nidan garin nan ne, muna zaune a unguwar
gandu. Mahaifina Alh sani yana da mata biyu da 'ya'ya
tara, nine na uku a gidanmu sunana nura.
Nayi karatu na firame da sakandare a garin nan, inda nayi
jami'a a dubai. Ina kan harkokin mahaifina na bangaren
kamfanin motoci." ta jinjina kai, tace naji labarinka, Allah
yayi mana jagoranci na Alheri.
ALLAH yayi mana jagoranci
na Alheri, sukayi sallama zai tafi ya bata rafar kudi taki
karba. Yaita mata magiya data karba, tace don Allah yayi.
Hakuri bazata karba ba. Ta wuce gida. Tes ne ya kuma
shigowa wayarta, ta
bude ta karanta kamar haka. " i luv u zeey, luv is like d
music of the nature the note 're heard by the loving heart
that is tender nd pure, i care 4 u,
i miss u, na i luv u." ina sonki, ina sonki, na dade cikin
sonki. Ki soni zeey shine samun kwanciyar
hankalina. Zeey yaushe zaki amince dani na
bayyana gareki." ranta ya kuma dagulewa, wai
waye wannan ne yake damunta da kalamai?
Maye nufinsa? Ta mayar masa da amsa kamar
haka. "dan Allah waye kai? Me kake nufi da
rayuwata? Don me zaka boyemin kanka? Nifa
marainiyace dan Allah ka rabu dani kada ka cuci
rayuwata. Tana tura tes din mintuna biyu da
tafiya waya ta shigo ta kama ringin, tana dubawa
lambar da ake yo mata tes da itace. Tsoro da
fargaba suka kamata, ta kasa daga wayar harta
katse. Aka sake bugowa ta sake katsewa, sai
akaro na uku sannan ta iya dagawa, muryanta
can kasan makogoro tace hello! Wake magana?
Cikin taushin murya da kyakyawan lafazi yace,
"salamu alaiki ya hasken ruhina. Sanin
muhimmacin sallama shiyasa ta amsa, amma a
zuciyarta tana cike da tsoro da fargaba. Ya ce,
"haba zeey, kada ki taba mugun tunani akaina,
zainab ni masoyinki ne na usuli mai burin gina
miki ingantacciyar rayuwa. Zeey ta na dade cikin
tafarkin kaunarki, tun kina kankanuwa zainab
Allah ya jarabceni da azababbiyar sonki. Zainab
ki amince da soyayyana kona samu dadadden
burina ya tabbata, wato ya zamo na aureki." to
waye kai? Aina kake? Ya sunanka? "to ni sunana
haidar, kuma ni haifaffen garin nan ne, sai dai
aikina daya sa bana zaune anan din dindindin."
to taya akai ka sanni, kuma waya baka lambar
waya ta? to nasanki ne idan nazo garin ina ganin
sanda ake wucewa dake a mota zuwa makaranta
da safe, ina ganin sanda direbaku yake daukoki
shidda na yamma. Lambar wayarki kuma wata
rana na tsaya zan sai kati a wajen wani me dan
kes din katuna waya da wayoyi, saina ga wata
mata, ina ganin mai aikinku ce tazo da wayarki
wajen. Saina ji tace bari taje ta dawo kafin yasa
mata katin. To tanan na samu dama na dauki
lambarki. Shikenan bayanin da kike sonji? Tace
a'a meyasa ba zaka fito na gankaba kake yomin
tes? Yace haba zeey ina yo miki tes ne danki san
dani kada nazo miki gaba gadi ba tare da saninki
ba, shiyasa nake yo miki tes dan nasamu
amincewarki tukunna kafin nazo. Da fatan kin
gane? tace na gane. Sannu a hankali soyayya da
shakuwa ta shiga tsakaninsu, don yanzu zainab
ta saba da soyayyarsa, sai sukai sha biyu na
dare suna hirar soyayya, amma har yau basu ga
junansu ba, daga waya sai tes ke hadasu. Saidai
har yau ta kasa gayawa yayanta Aliyu maganan
saurayinta haidar da yake neman amincewarsa
daya fara zuwa zance wajenta, sai dai har yanzu
suna tare da saurayinta nura, du sati ranar
Alhamis yake zuwa wajenta, basu taba haduwa
da yayanta Aliyu ba. Yau ma nura ne yazo, ta fita
harabar gidan, yana zaune kan farar kujera da
tebur fari zagaye a gabanshi, dayar kujerar tana
kallonshi. Zainab tayi masa sallama ya amsa da
fara'arsa, taja kujera ta zauna suka gaisa fara
tambayar ya bayan rabuwa. Talatuwa ta kawo
masa lemo da cin-cin da meatfay yana ci yana yi
mata hira, har yanzu bata wani sakewa dashi ba,
amsarta daga um sai a'a sai dai kuma tayi
murmurshi. Wayarta tayi kara tana dubawa tayi
ta amsa da hello! Mazaje ya akayi ne? Zeey ta
inakan hanya yau na taho gida, na gaji da
tunaninki, inaso zan zo muga juna." kai amma fa
naji dadi mazan jiya." yauwa zeeytah, nagode,
shigowar safe zan miki dan ki ganni sosai."
bakwai da rabi zanzo gidanku, nizan kaiki
makaranta muna tafe muna hirarmu mai dadi, na
jira tunda jumma'a ce ba dadewa ba zakuyi a
tasoku, mu sake tahowa tare muzo gida mu wuni
muna hirar soyayya." Allah mazan jiya? Allah
zeeyta, saina iso. Ok mazaje, bey." nura ya
kalleta yace dama kina hira haka? Ko donni
bakya sona ne, naji har sunaye kika rada masa
mazaje dan mazan jiya. Tayi murmushi tace ba
haka bane, bazan iya fadar sunan sa bane
saboda sunasu daya da yayana, shiyasa nake ce
masa mazaje. Inace masa mazan jiya ne saboda
yanayin aikinsa. Ta tsiyayo lemo ta miko masa
ungo yi hakuri karbi kasha. Yace saidai ki bani
abaki in kina so nasha. Tace "a gaskiya baza
iyaba, ka karba kasha da hannunka kawai." ta
miko mishi. Shikuma ya kawo baki yana so ya
kurbi lemon. Dai-dai lokacin Aliyu ya shigo get
din gidan idonsa ya gano mashi. Yayi wani irin
kogi da motar. Tsoro yasa zainab ta saki kofin
lemo ya fadi. Aliyu ya bude motar ya fito kamar
namijin zaki, ransa abace fuskarshi a daure
kamar bai taba dariya ba, da kakinsa ajikinsa na
soja ajikinsa. Yana taku cikin kasaita ya nufo
inda suke, tuni zainab ta hankade tebir din
gabanta tayi cikin gida a guje. Cikin kakkausar
murya ya nunawa nura dan yatsa yace "waya
baka iznin kula kanwata? Zoka fice kada na sake
ganinka da ita. Zoka fice. Nura yana so yayi masa bayani
ya daka masa tsawa tareda
[9:14AM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 2**3 & 2**4
NURA yaba so yayi masa bayani ya daka masa tswa tare da
nuna masa kofa, da sauri nura ya fice ya shiga motarsa
yaja. A fusace ya
shiga
gidan, zainab duta gigice ta rukunkume
mansura
tana cewa "aunty ki ceceni, ki ceceni aunty. Mansura tana
ta tambayarta meye? Ta kasa gaya
mata saboda rudewa da gigita da take ciki. Cikin takunsa ya
shigo, ta saki mansura tai daki da gudu ta turo kofar, da
kafa ya daki kofar
dakin ta bude, ya zari wayar radio, ta rude, tana
bashi
hakuri yace "uban waye ya baki iznin zance
da
wani?
Harda bashi lemo a baki. Dama abunda
kikeyi
kenan in ba na nan? Ya tsula mata wayar, ta
gigice ta rukukume mansura. Mansura ta
tareshi tana masa magiya yayi hakuri. Ya hankade ta,
yace ina nan zuwa kanki, zaki san kinsata
zance. Mansura tayi saurin barin gurin danta san
halinsa. Ya sake tsulawa zainab, ta
rukunkumeshi
tana ihu, "don Allah yaya kayi hakuri, wallahi
bazan sake ba kaji yaya, kayi hakuri yayana, wallahi dukan
da zafi. Allah zankiyaye bazan sake
ba." ya cillar da wayan, tayi saurin cikashi,
yayi dakinsa. Zainab ta zauna tana kuka. Mansura ta
dagota tayi dakinta da'ita tana rarrashinta.
Wallahi bansan zai dawo yau ba, shida baya dawowa sai
jumma'a da mangariba, to me ya kawoshi gida yau
Alhamis?
Ya kwalawa mansura kira, ta fito da saurinta.
Ya rinka gaya mata maganganu, yaci mata mutunci.
Yace wallahi wannan shine na karshe, du
sanda
ta sake barinta ta fita zance wajen wani sai ranta yayi
mummunan baci.
Ya fice ya bar gidan, mansura tace,
masifaffe,
kada ka barta tayi zance ta samu mijin aure, saika
kwadantata kaci." zainab tana daki tana sheshekar kukanta
taji wayanta na ringing.
Ta duba, saita daga tace hello! Mazaje. Yace a'a zeeyta
yana ji haka? Du yanda akayi akwai
damuwa, gaya min zeeyta meyake faruwa?
Cikin sanyinta tace lafiya lau mazan jiya ba komai.
A'a daga jin muryar nan ba kalau ba, bazan
iya hakurin zuwa gobenba, bari yanzu nazo naji
ko meye." tayi saurin cewa a'a mazaje kada kazo ka bari
tukunna saina gayawa yayana.
Haba zeeyta ki bari nazo mana muga juna, yanzu du donki
da nake bazaki bari nazo ba?
Tace, "kabari sai wani lokacin.
Yace don bakya sona baki damu dani bako? Ya kashe
wayar tasa.
Ta dafe kanta, "ya Allah sharrin soyayyar kenan, da da bata
kula kowa tayi zamanta lafiya, yanzu
kuwa daka fara soyayyar tata gashi ta fara cin karo da
matsaloli." ita dai gaskiya tana son
haidar, don bata taba ganinshi ba amma yanda take jin
muryarsa da lafazinsa tasan cikakken
mutum ne me mutunci da kamala
baza taso ace ta rabu dashi ba dan bata san wa zata hadu
dashi agaba ba.
Ta dauki wayarta ta buga masa, ringin daya ya dauka, yayi
shiru. Cikin sanyinta da marairaita tace "mazaje fushi kake
yi? Yayi mata shiru
cikin shagwaba tace, "mazan jiya, kada kayi fushi
dani, baka sani bane wallahi ina cikin matsala shiyasa."
cikin sanyi rai yayi ajiyar zuciya, yace wacce irin
matsalace? Ki gaya min mana." dazu yayana
yazo ya sameni ina zance, baka ga yanda ransa ya baci ba.
Yaita mana fada nida aunty na.
To idan kazo ya ganka kaga bansan abunda zai kuma
faruwa ba.
Wallahi bana so naga ran yaya abace,
ballantana kuma ace nina bata masa, wallahi raina yaki dadi
duk nadamu da fushin da ya keyi, don ni
yaya shine uwata.
Haidar yace gaskiyane na gane, tunda ina sonki dole na
tayaki biyayya ga iyayenki da 'yan
uwanki, zan nemi yayan naki na gaya masa ina
sonki, ina so ya amincemin na fara zuwa zance
gurinki kina ganin hakan yayi?
Tace, yauwa mazaje nagode.
Yace kada ki damu na gaya miki, i care 4 u, i miss u, i luv
u."
tace, "nima haka" tayi saurin kashe wayar tana dariya.
Shima daga can dariyar yayi yana mai farin ciki yanda ya
samu karbu awajen yarinyar.
Sai goma na dare sannan Aliyu ya koma gida, yana zaune a
falo, Ahmad yazo ya zauna a jikinsa
yana dan lallbashi har yayi bacci. Mansura tana
jin shi bata fito ba, ita a dole fushi takeyi
akan fadan da yayi mata akan zainab.
Zainab tana sanye da kayan bacci kwance akan
gado ta kasa bacci, tunaninta yana kan
yayanta da yake fushi da ita.
Ta mike ta daura zani tasa hijabinta akanta, ta
rufe jikinta. Ta bude dakinta ta fita falon, tayi
sallama cikin sanyinta da yanayi na tausayi aciki,
ya amsa sallamar, ta zauna akasa kusa da kafarshi, tace
yaya don Allah kayi hakuri, Allah ya
huci zuciyarka, don Allah yaya ka yafe min bata maka
danayi.
Yace, zainab kin batamin rai, daman inba na
nan zance kikeyi? Meyasa kike kula samari?
Don Allah kayi hakuri yaya bazan kuma ba. Yace, "gaya min
da mutum nawa kike yin zance.
Wallahi yaya shikadai ne yake zuwa." to
kuma suwa kike waya dasu? Wallahi yaya shima shikadai
ne." gaya min sunansa?
Tayi murmushi sunkuyar da kai. Yace kina sonshi? Ta rufe
idonta bata ce komaiba. Yace "nida burina naga kinyi digiri,
ashe hakan bazata
samu ba, samari bazasu barki kiyi karatu ba, ko auren za
ayi ne?
Yace ga maganin na dauki kisha kada jikinki yayi ciwo.
Tace to yaya nagode. Ta dauka tayi dakinta. Ya bita da
kallo yana kissima abu a zuciyarshi, yayi murmushi ya
lumshe ido yana tunani abunda yake tabo ranshi. A daure
ayi like da comments don hakan ke kara mana kwarin
gwiwa
ZAINAB sunyi candy, ita dai bata samu hutu ba ta fada
kacaniyar bikin ni'ima. Ranar Alhamis akayi
kamu, kuma dije ya cashe musu da kida, ranar
zainab ta ajiye ustazancinta tasha rawa. Da
daddare yunwa ta isheta, gata ba gwanar cin
abinci, daman ga abun ya hade ma da hidimar
biki. Tana cikin kawayen ni'ima da zasuyi kwanan
biki anata hira da ita, kowa sonta yake yi, suna
son hira da ita, don sha'awa take basu. Gata fara
kal kyakyawa, gata da fara'a ga ladabi, don
kowacce aunty take ce mata. Tace yaya ni'ima
nifa yunwa nake ji." tace baga tuwon shinkafa ba
da zafinsa? Tace tuwo yaya ni'ima, ai ba zan iya
ci ba." ta dauki wayarta ta buga, "hello, yayana
yunwa nakeji." ya hauta da fada, "don me zaki
zauna da yunwa? Cikin shagwaba tace, "to yaya
su basuda komai sai tuwo."
mintuna kadan sai gashi a gidan da youghot da
ice-cream, da kaji uku manya ya kawo mata. Ta
bude tana ci, ni'ima tace 'yar gatan yaya kenan."
sakina cikin kawayen ni'ima tace, yarinyar nan
kinaji da gata, irin wannan cima da kikeyi dole
kiyi ta faman kyalli, baki da matsala."
zainab tayi dariyarta mai ban sha'awa tace,
yayana ai shine babata, baya barina cikin
damuwa, suna cin nama da youghot da ice-cream
tana basu labarin yayanta da yanda take tsoron
shi da gudun bacin ransa. Da safe ta shiga gurin
babanta ya bata rubutun tsari da magani a dame
da kindirmo, da tsumi da zuma. Tun tana 'yar
shekara sha uku babanta yake tsumata da
magani, shi tausayinta yake ji, yana ganin tunda
ta rasa uwa ba mai kula da ita ta wannan
bangaren.
Kullum addu'arsa Alah ya bata miji na gari wanda
zai kula da ita, ya tallafi maraicinta. Washe gari
suka tafi gyaran amare, akayi musu dilka da
halwa, jikinsu ya rinka tsantsi da sheki.
Suna gidan kunshi haidar yayo mata waya, "hello
mazaje ya akayi ne? Nifa na matsu zeeytah so
nake kawai na aureki, zainab kaunarki tayi min
yawa, zainab yaushe zamu hadune? Yaushe zamu
ga juna?
Karka damu mazan jiya gobe kazo daurin auren
yayata saimu ga juna." yauwa zeeytah zan zo
miki cikin farar shadda da bakar dara, da farin
takalmi. Zansa babbar riga, zansa farin agogo na
azurfa da farin gilas. Tara da rabi zanzo, sannan
saura rabin awa a daura auren kenan, tunda
goma za a daura.
To naji dadi wallahi sai goben.
Ranar daurin aure zainab tagama tsara
kwalliyarta cikin wata dakakkiyar shadda mai
tsadar gaske da yayanta yayi mata biki, ta nada
dan kwalin kamar nadin gwaggwaro, tayi kyau
sosai.
Haidar yayo mata waya cewar ya iso yana dakin
saukar baki na gidansu, ta kara feshe jikinta da
turare ta fice tayi dakin baki. Tayi sallama cikin
sanyinta, ta hango bayanshi cikakken mutum mai
zati dakyan kira, irin mazan nan masu wahalar
samu. Kamar yanda ya gaya mata zaiyi shigarsa
haka ta gani. Tayi sallama tare da cewa hello,
haidar barka da zuwa.
Yana juyowa hanjin cikinta ya hautsina, nan da
nan ta dabarbarce ta nemi nutsuwarta ta rasa,
bakinta ya dabarbarce. Dakyar ta iya hada
sunansa ta fada, tace, yaya Aliyu!"
ta juya cikin gida aguje ta fada daki tasa kuka
tana jimamin meyake shirin faruwa da ita? Karfe
goma dai-dai taji an daura auren ni'ima da
hamza saurayinta. Dai-dai lokacin da aka sake
daura auren Aliyu da zainab.
Zainab bata karasa jiba ta yanke jiki ta fadi, inda
mansura ta sheko da gudu dakin data ga zainab
ta shiga tana cewa, "ni zaku yaudara ku ciwa
Amana? Yau zainab koni ko ke, saina kasheki
nayi maganin maciya amana." inda ta shaki zainab.
Zainab ta rinka kakari. Sadiya da ni'ima suka yo
dakin da gudu, suka cakumi mansura suka cillar
da ita gefe suna cewa, ke kada kiyi mana hauka,
'yar uwar tamu zaki shaka kina kokarin kashewa?
Umma ta shigo a guje ta dago zainab ta
rungumeta tayi dakin da ita. Mansura ta rinka zage-zage,
"ni za ayiwa rashin mutunci da tozarta na rike yarinya tun
tana 'yar shekara
takwas, sirrina babu wanda bata saniba, na riketa
kamar 'yar cikina, amma cin amanar da zai biyo
baya kenan ku aurawa mijina ita?
Ta rinka deban kayan wajen tana watsi dasu.
Sadiya tace mudai kiyi mana shiru kada ki bata
mana taro." ta kawowa sadiya duka, mutane
suka tare suna bata hakuri, amma tijara take tana
zuba ruwan rashin mutunci. Saida ummi tayi
waya gidansu babarta da yayarta suka shigo
suna tambayar meya faru? Mansura ta fada jikin
babarta tana kuka, tana cewa hajiya kinga
abunda suka yi min, kina kallon irin sakayyar da
sukayi min, du kyakyawan rikon dana ma zainab
yau sunga ta mike ta zama mutum, shine suka
aurawa Aliyu ita." ta karasa tana kuka. Hajiya da
saratu suka saka salati tare da cewar, amma
Aliyu da zainab sunci amanarki sun tozarta ki, sun
wulakantaki, amma kansu sukayi wa, yanda
sukayi miki Allah ya tozartasu, taho mu tafi, aure
ne bakya yi su rike dansu. Bayan zainab su kara
aura masa mata uku su zama hudu.
Daman munafunci daya sa aka kai miki zainab
din don ta gama ganin sirrin gidan, ta riketa
Amana tamkar uwarta, amma sakayyar da zakuyi
mata kenan. Don kanku ku rike Aliyu, Allah ya
bata wanda ya fishi, suka jata suka nufi nasu gidan sunata
sababi.
Tofa Littafi ya canja salo
[9:15AM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 2**5 & 2**6
SUKUWA maza 'yan daurin aure, ana gama daurin
aure suka nufu daula hotel, don cin abincin daurin
aure, wato walima ta zama kadai 'yan daurin
aure.
Aliyu ba abunda ya dame shi sai washe baki
yake, yana ta gaisawa da mutane. Da yawa
mutane sunata mamaki, don sun san miskilanci
da rashin yawan dariya irin na Aliyu, amma yanzu
ya kasa rufe bakinsa saboda fara'a da amsa
gaisuwar jama'a da masu sanyawa auren nasu
albarka.
Cikin gida kuw, masu gidan yaransu da manyansu
cikin farin ciki suke da wannan aure na Aliyu da
zainab, saboda kawunan su a hade yake.
Su sadiya dasu ni'ima kuwa sai murna suke suna
zuba shewa da tafi.
Zainab kuwa tana dakin umma kudundune cikin
bacin rai, duniyar tayi mata zafi, ta rasa mai yake
mata dadi. Ita bata ga laifin auntyn ta ba, dole
tace taci amanarta. Mai auntyn ta rage ta dashi?
Ta dauketa kamar 'yar cikinta, amma yau
sakayyar da zata yi mata kenan ta aure mata
miji? Ta sake fashewa da kuka.
Meyasa haka? Meyasa yaya Aliyu mata haka?
Tana ganin yaya Aliyu mai rikon gaskiya da
amana, ashe shima zai iyabin son zuciyarsa. Ya
aureta yaci amanar matarsa? Wayyo ni Allah!
Kaico da wannan rayuwar, ranta ya rinka kuna,
makogwaronta ya rinka daci, ta rinka jin wani
yuuu a kanta. Ta dafe kan tana jin wani sara
mata da yake yi, wasu duhu suka gifta ta idonta,
idanuwanta suka rufe tayi baya ta fadi
numfashinta ya dauke.
Umma da ummi suka shigo dakin a lokaci daya,
suka ganta a wannan halin. Gaba daya sukayo
kanta suka dagota suna salati, umma ta
rungumeta tana salati tare da nanata kalmar
innalillahi wa'inna ilaihi raji'un."
yayin da ummi tayi falo da sauri tana salati,
mutane suka yo caa akanta suna tambayarta
lafiya? Ta rude sai fadi take ku kirawo mana
direba, zainab ce ta suma."
sadiya da ni'ima suka saka ihu suka yi cikin
dakin. Dakyar aka samu direban aunty sadiya a
waya, don duka direbobin sun kwashi mutane
suna can daula hotel.
Aka dauki zainab bata san inda kanta yake ba,
suka tafi asibiti. Sunata neman wayar Aliyu gaba
daya wayoyinsa a kulle suke saboda jama'a.
Haka ta Abba da daddy ma du ba'a samu.
A asibiti kuwa gaba daya matan sun cika daki
sunata koke koke, su umma da ummi kuwa da
mama matar baban su zainab, sunyi jugum-
jugum sai salati suke suna hailala a zuciyarsu,
tare da nemawa zainab lafiya cikin zukatansu.
'yan nurse din duk suka korasu falon asibitin,
sannan likita ya fara yiwa zainab taimakon
gaggawa.
Cikin ikon Allah ta farfado, sai likitan yayi mata
allurar bacci donta samu nutsuwa.
Sai sha biyu aka tashi daga walima, sannan aka
samu lambar wayar Abba da daddy. Suna jin
zainab a asibiti suka ce
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 14