out of control,
Jin shiru yasa Ammi mara musu baya tunkan ta qarasa ta hango qofar a wangale amma ba alamunsa to ina Anwar yayi ta ayyana hakan se de sautin da take jiyo wa daga ciki yasa ta d'aga qafa tsugunnewa tayi a bakin qofa cike da tashin hankali dakyar ta iya d'aga murya
Tace "Ann!!"
_yanzun ma dai ba yawa pls bear with me, a tunani na da babu gara ko kad'an nake tsakuro muku, insha'Allah next update will be 10 read more💪🏻😉_
©️Kdeey😊
DABAIBAYI 👄
©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊
®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)
_ina dad'a neman afuwa na jina shiru da kukayi hakan ya faru ne a bisa tafiya da nayi, nagode_
(24)
Tamkar sukar aradu muryar tata ta doki kunnuwansa, daqyar ta tattara courage dinta t angije shi gefe tare da fad'awa jikin ammi had'e da sakin wani marayan kuka, a kid'ime Ammi ta d'ago kanta ta shiga duba ta tamkar me nemo wani abu, kan ta kada baki tace "maza share hawayenki yar albarka, ba abinda ze same ki kinji, makarantar da zaki ta qawata ce duk lokacin da kike kewata zansa a baku waya se mu rinqa jin lafiyar juna uhm?" Ta d'aga kai, "good, maza kuje nasa eliza tayi miki packing abincin cikin flask dan bazan so 'yata daga zuwa ta fara da abincin makaranta ba ko ya?" Nan ma kuma d'aga kai tayi , Ammi tasa thumbs d'inta biyu taja kumatunta, "oya give me that one in million dollar smile"
Murmusawa tayi, had'e da kuma shigewa jikin Ammi, "wuce ka d'auko kud'i kuje ka saya musu suturu kafin kayi dropping d'insu" Ammi ta furta ba tare da ta kalli sashin da yake ba,
Jiki a mace ya ja qafa tare da ra'bewa ya fita ta wani hanyar, saman sitiyari ya kwantar da kai, idanunsa a lumshe ya san cewa yana da yawan buqata amma be ta'ba expecting qaramar yarinya irin Sam zata iya jan ra'ayinsa har haka ba, shin meke faruwa ne?
The feeling is so weirdo that he can't even imagine yanda akayi har ya isa gareta ya kuma mallaka mata bakinsa da ko kimberly da take fad'i tashi wajen ganin ta samu matsayin sumbata ba tayi nasara ba se kwailar yarinyar da bata yi wata cikakkiyar balaga ba, fursar da iska yayi lokacin daya jiyo sautin taku
Dag can ya hangota kwance gefen kafad'ar Ammi munu na gefe suna murmusawa farinciki lullu'be da kowannen su, knocking da akayi bisa window yasa shi saurin sa hannu ya bud'e,
"Maza ka sauke su ka dawo" tace game da juyawa ta koma,
Forming line yayi da baki had'e da cije ha'koransa har ana iya hango yanda gefen goshinsa ke lo'bawa, shiru ne ya ratsa motar, munu dake a gaba tafi maida hankali wajen qarewa garin kallo yayin da Sam ke raku'be a kujerar baya,
Sosai yayi musu siyayya kan ya je ya damqa amanarsu a hannun miss chloe inda aka wuce dasu d'akin kwanan su direct me d'auke da gadaje biyu gefe da gefe
"Ya Allah" Sam ta furta ido waje munu kuma tace "Masha'Allah", rungume juna sukayi , idanunsu suka shiga roaming around d'akin bangon d'akin manne yake da stickers d'in sophia the first yayin da ko wani gado ke had'e da reading table se toilet madaidaici, kalar d'akin pink ne haka ma kalar curtains da carpet d'in duka, knocking da akayi bisa door ne yasa su dawo wa daga duniyar kallon da suke
"Yes" suka furta a tare, wata dattijuwar baturiya ce ta leqo d'akin with a smile plastered on her face,
"Wellcome to saint teresa college"
Nodding sukayi game da fad'in "thank you"
"I'm miss patricia, dafatan zakuji dad'in kasancewar ku a nan, ni ce shugabar d'akunan hostel d'inku hope you will cooperate with me"
"Sure" suka ce tayi musu thumbs up ta tafi had'e da rufe musu qofa"
"Saint teresa" munu ta furta cikin rolling eyes kan ta fad'a saman gado, dariya tayi ta juya ta nufi bathroom ta dauraye hannu ta fito gefen gadon ta zauna ta shiga bud'e flask dan kauda yinwar dake qwaqularta.
~
"Care to explain yourself?"
Hannu sa daya d'ora saman handle ya janye game da waiwayo zaune take medicated glass maqale saman idonta tana duba jarida, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kan ya taka ya isa gabanta
Daidai qafarta ya gurfana kansa a qasa tunda yake be ta'ba jin kunyar Ammi kamar ta yau ba,
"Ina saurarenka"
Muryarta ta katse sa, lumshe ido yayi game da bud'esu saman qafarta ya d'ora hannayensa a kai ya shiga mata matsa, ga mamakinsa se ta janye qafar cikin had'ewar fuska
Tace "Ann kar ka maida ni babbar kurum mana , taya kake neman fito da sabbin d'abiu wanda ko a yahudu mara kunya ke yin hakan, kar ka bari na kuma tambayar ka"
Rufe ido yayi, yace "...mata tace..."
Cikin rawar murya tace "Ma..mata kace??"
'Daga kai yayi idonshi a qasa "Ammi banso kika yi pushing d'ina na fad'a miki ba, this is not the right time..."
"..right time? Is this what you are suppose to say to me? Wait Anwar taya akayi Samira ta zama matar ka da yawun wa? Wane ya baka ita?"
"...kawun tane, kawu kabiru," yace idonsa a lumshe,
"Anwar yaushe ka fara qarya? Na zata kawunta an nemeshi an rasa, wait..don't tell me you are behind all this"
"Not all Ammi.."
"Ya isa.." ta d'aga masa hannu, tare da juy masa baya, rarrafawa yayi ya riqo qafarta jin tana sheshsheqar kuka,
"Na rantse miki da Allah Ammi nayi hakan ne saboda farautar ransa da aka fara"
Ta juyo hawaye na bin fuskarta "kanaso kace shima ana neman rayuwar sa ne?"
"Hakane, ciki harda matar sa da yaronta"
Cike da mamaki tace " ban fahimce ka ba"
Gyara zama yayi, ya fara da cewa
" wata rana na fita zagayen gari dai dai wani lungu a amadu bello way na hango wani saurayi na leqe hakan yasa naja gefe nayi parking dan ganin abinda zeyi bisa mamakina da yaga babu kowa se ya fito game d yafito wata babbar mace tazo suka fad'a wani d'an qaramin gida se da na tabbatar sun shige na fito , ta bayan wani window na tsaya dan naji meke faruwa a gefe guda kuma inason ne naji inhar barayi ne ko wasu masu tada zaune tsaye na kira 'yan sanda cikin ikon Allah se naji maganar mace na fad'in
"Nace muku ki ida kashe shi kunqi wai shin ba kunyi min alqawarin kashe kabiru bane ko dai bakwa son kud'in ne! Kun kuwa san alqawari, dakanku kuka dafa qur'ani kuka kuma rantse zaku kashe mana shi, kai kuma Amir ina zancen fyad'en da zaka yi mata!
Wai ku wasu irin daqiqai ne to billahillazi na baku kwanaki uku rak ku aiwatar da abinda nace muku in ba haka ba mu zamuyi da kanmu idan yaso kuyi biyu babu, haka itama uwar yarinyar mu kasheta dan mun gaji da ajiyar kayan da ba mamora.."
Baya naja da jin haka, a take na bar wurin jiki na rawa na nufi makarantar da Bro B yake kula da Sam, na shaida masa duk abinda naji mummy wlh kuka nake daqyar na iya sanar dashi labarin tun daga wannan ranar muka saka ido kan shige da ficen su kwatsam a kwana na biyu sega shi an kawo Samira asibitin hasheem ganin haka nasa Dss bashari ya tura aka kama kafatanin gidan with d exception of shi uncle dinta da babban yaron ta na tura su nijar qarqashin kulawar aboki na shugaban qasar garin,
Aurena da Sam kuwa ya faru ne dalilin ajiyeta a wurina da nace zanyi, kawu ya nemi tayina a kanta da farko naqi aminta sedai tsoron abinda ya faru da ita da Amir kada ya kuma faruwa da ita tunda ga habiibii yasa na yarda a ranar mutawakkilu ya amsa walicci na aka d'aura aurenmu bisa sadaki millon d'aya, wanda na bud'e acct da sunanta na ajiye a ciki da alqawarin duk sanda tasan gaskiyar lamarin zan mallaka mata haqqinta, sa'annan a tambayi ra'ayinta a kaina,
Ba iya nan na tsaya ba dan nayi tattaki har turkey na damqa kamfanin dake can a hannun gomnati da taci gaba da kula dashi tare da basu 2 % na riba, a yanzu haka habibii wato d'an kawu kabiru na tura shi karatu singapore shi kuma kawu yana gidan mutawakkilu wato shugaban qasar nijar"
Ammi durqushewa tayi hawaye nabin fuskarta, tace " Ann cikin labarinan wace uwar yarinya da aka gaji da ajiya",
Murmushin da yafi kuka ciwo yayi yace "Ammi na mummyn Sam na raye..."
Qirji ta dafe da hannh cikin kufcewar kuka take fad'in "um um um um Ann kada kayi min qarya! Ka fad'a min gaskiya dan yin hakan baze kwantar min da hankali ba sede ya tada min"
Hannuwanta ya kamo cikin nasa "Ammi ki nutsu ki saurare ni yi miki qarya da wannan maganar babu riba a gareni mahaifiyata ki sani duk wannan fad'i tashin da nake saboda farincikin ki nake"
Hannu tasa ta share hawayen fuskarta "Ann zan had'a ka da chief of army staff na nigeria madu Aliyu lallai inaso a kamo min matar kabiru dan tabbas tana da masaniyar inda mariya take" waya ta d'auka da niyyar kira yayi saurin cewa
"Ammi zan fiso mubi komai a sannu, idan muka ce zamu bi abin sama ta ka abin baze zo mana da sauki ba, yanzu haka Bro B yana can kan binciken wanda suka kawo mana hari a hanya wanda nake kyautata zaton hakan will lead us to mutanen dake riqe dasu aunty mariya"
Jimm tayi,can tace "Ann all this years ace mariya na raye? Shin wani irin hali take tsayin shekaru sha wani abu ba tare da taga wani nata ba?" Ta qarashe cikin tsananin kuka.
Kwantar da kanshi yayi a qafarta shima yana zubda hawaye yace "Ammi na inaso kiyi min wani alqawari" yayi rigingine idonsa a kanta yace "you will never let Sam knows about this ciki harda zancen aure na dake kanta"
Girgiza kai tayi cikin dashewar murya tace "meyasa.."
"Hankalin ta baze d'auka ba, and nafison ta kammala makaranta tukunna"
"Se idan ka iya d'auke idonka a kanta, dan idan har abinda ka aikata d'azun ya kuma faruwa to kuwa lallai ita da kanta zata kawo wani abu koda be danganci igiyar ka dake kanta ba"
Nannauyan ajiyar zuciya ya sauke had'e da jinjina kai cike da tunani bacci yayi awon gaba dashi , murmushi tayi cikin zubar hawaye ta d'aga hannuwa sama tana dad'a godewa Allah da kuma roqon Allah ya bayyana 'yaruwarta ya kuma kawo musu komai cikin sauqi, pillow ta janyo ta d'ora kanshi a kai ta d'auko blanket ta lullu'be shi, ta shige d'aki ta kwanta hawaye na zubo mata cike da tausaya wa rayuwar su, su duka,
Bello ko a wani hali yake ciki? Tunanin hakan yasa tayi saurin kiran wayar bello,
***
Cikin wani babban gida suka shiga bayan sun tabbatar da ba wanda ke ganin su, wata mata ta fito jikinta sanye da tsadadden leshi wuyanta da hannunta cike da gwalagwalai se d'aukan ido suke shigowarta cikin haske yasa hasheem da bello dake kallonsu tamkar a TV ta cikin camera da suka manna jikin salihu ba tare da sanin sa ba suka miqe a firgice...
"Haj..iya mar...yam..mainasar" suka furta cikin rawar murya kallon juna sukayi a rud'e zuciyoyinsu na tsananta bugu, qurawa mini TV d'in ido,
_Tafa hannu tayi "you guys did a very good job, you deserve a medal you know, tayi dariya kan ta hakimce saman kujera tayi musu alama da hannu cewar su zauna,_
_"Nafi'u kunyi qoqari mutuqa se dai naso ace ku da kanku kuka qarasa su, dake Allah na sona se ya kawo min komai cikin sauqi" ta kwashe da wata arniyar dariya lokaci d'aya kuma ta gimtse tamkar ba ita ba_
_Tace "naji ance baquwar fuska ta shigo unguwar ku" jimm sukayi cana rody yace "eh madam wani corper ne yazo serving anan makarantar arean mu"_
_"You know i hate new faces so ku iya takun ku" kai suka jinjina,_
_"Madam have u heard from lawalin nijar kuwa?" Cewar aqilu,_
_"Har yanzu ba wani labari, amma akwai tabbacin be fita daga garin ba"_
_"Partaining hajiya ya ake ciki akwai wani improvement?" Cewar salihu_
_Kafad'a ta d'aga "talking about waccan matar je kazo min da d'an iskan dattijon nan" ta furta hakan idonta saman wani qaton gardi dake tsaye a gefenta_
Sulalewa su bello sukayi , ganin an _shigo da wani dattijo hannunsa da qafafunsa maqale da ankwa jan qafa yake dan tafiyar ma ta gagare shi, shi da qashi marabar su qalilance se fata, janshi akayi har gabanta aka tunkud'ashi kansa se gilu gilu yake ko d'aga kai wannan ya kasa, qur suka zuba mishi ido sai salihu daya sadda kai,_
_"namadi" ta kira sunan sa tun qarfi, na rantse da wanda raina ke hannunsa idan baka fad'i inda diamond d'in nan yake ba, da kai da hajiya a yau kwanan ku ze qare"_
_dattijon da ta kira da namadi ya d'ago kai jiki ba qarfi cikin inda inda tamkar me koyon magana yace na rantse da Allah baki na baze ta'ba furta sirrin ubangida na ba koda zaku rinqa yankar nama na kuna zubar wa"_
_Miqewa tayi a fusace ta fisgo kulkin dake hannun nafi'u ji kake gamm! Ta buga masa a kai nan da nan kuwa jini ya hau zuba, saurin riqota akayi wani saurayi ne yace "mami ki barni dashi" cikin yaqunar fuska ya kalli namadi "na baka awa hud'u idan baka fad'i inda yake ba da kaina zan qarar da kwanakin ka da kai da ita so called hajiyar taka, ku d'auke shi_
_waiwayowa yayi yace "nayi magana da garwashi idan basuyi magana ba , da dare zamu kaisu baqin daji a harbe su duka, kukuma anan zaku tsaya har a qare aikin dan na gaji da magana d'aya kullum_
_ya kallo mahaifiyar tasa mami lets go kada daddy ya zama suspicious ya kama hannuta suka fice_
Tsakanin bello da hasheem rasa wanda ze tashi tsaye akayi duk idanunsu sun kad'a tamkar gauta ko wayanda suka shekara kuka, amma tsabar tashin hankali ne daya afka musu, bello ne yayi qoqarin sanar da dss bashari a kan plan din su hajiyar inda ya basu goyon baya hade da nema musu sojoji aqalla mota biyu zuwa uku,
Hasheem kuwa kai ya sadda qasa cikin rud'ewa ba komai ke damunsa ba se tunanin halin da rayya zata tsinci kanta if she finds out about what her mothers doings,
Ana cikin haka ne wayar bello tayi qara
"Ammi" ya furta idonsa stick to hasheem's
Daga can tace "my son ya kake?"
Sama yayi da qwayar idonsa trying to maida hawayen dake neman zubo masa yace "am good ammin mu dafatan kina nan lafiya,"
Jinjina kai tayi cikin jan hanci tace " lafiya qalau ina tare da d'an uwanka with your cousin sis Samira"
"Cous..in sis? Samira?.."
Jinjina kai tayi tamkar yana kallonta tace "yes my son, ita d'in 'yar qanwata ce da ta 'bata mariya"
Cikin zare ido yace "da..namadi?"
"Yeah..shine amintaccen driver dinsu tare suka 'bata..." ta shiga yin kuka me cin rai,
Numfashi ya sauke a zuciyarsa yana tunanin kenan itace ake cewa za a kashe tare da namadi anjima, wani kuzari yaji a jikinsa a fili yace "Ammi na ki tayani da addu'a dan 'yar uwarki ta kusa fita daga hannun mugayen nan, zata yi magana yace " Ammi zan kira ki anjima ki kular min da kanki, kice ma bro A i love him and tell Sam that i miss her"
D'it wayar ta katse ido ya lumshe had'e da sakin murmushi, tsintar kansa yayi da farin ciki wanda be san dalili ba, tapping kafad'ar hasheem da ya zuba masa na mujiya yayi,
"Lets go"
Ya furta kawai ya nufi wane, cikin mota suka shiga basu tsaya ko ina ba se ofishin babban sona wato col. Kamal ibrahim (labarin aurena) inda suka zauna suna masu cigaba da kallon duk wani moves d'in jama'ar gidan through camera d'in jikin salihu.
A can gefe guda kuma ss ke zagaye da ciki da wajen gidan governor dan kula da duk motsin hajiya maryam,.
***
A can Birmingham cikin college Sam tun bayan zuwansu ke kwance ta gaza yin komai sa'ilin da munu ke kai kawo wajen shirya musu kayan su cikin wardrobe
Kallon Sam tayi jin shirun nata yayi yawa tace "wai nikam meke damunki a tunanina dai tun ranar da muka baro kano kika gama kukan rabuwa d gwaggo, to yanzu kuma ko zan iya sanin abinda ke ja miki zubda hawaye?"
Idanunta dake a lumshe ta bud'e tare da qoqarin zama cikin sanyin ta tace "munu bansan yanda zansa abinda nakeji into words ba, i can take the feeling away.."
"Uhumm" munu tayi making sound with a questionable look
Saukowa tayi daga gadon ta tsugunna a gaban munu "ina tsoron kada na saka zuciyata cikin hatsari" ta furta cikin damuwa
"Subhanallahi hatsari fa, hatsari wani iri?"
Cikin rawar murya tace "i have never been through this before, the only feeling da zan miki bayani ki fahimta is that of litattafen hausa da kike bani labari.."
Kwashewa munu tayi da dariya pointing at Sam tace "Sam are you in love?"
Jinjina kai tayi "deeply in love if i might say"
Ihu munu tayi tana rawa tace "this is amazing sweetheart kinsan nima fa hakan ne ya faru dani na gaza furta wa ne dan kada kice am too young for it, kinsan dawa?..ko dake live it fara fad'a min naki? Tace sounding excited
Sam ta girgiza kai, se na fara jin naki tukunna"
"Tabb ai baki isa ba bayan kece kika fara yin zancen, dan Allah ki fad'a min kinji"
A shagwa'be tace "munu manaaa"
Hannu tasa ta kare idonta irin wai tanajin kunyar nan tace "Bro..B"
Cakk duniyar ta tsaya wa Sam gabanta yayi wani irin bugu har seda ta dafe da hannu, tashi tayi da baya baya ta fad'a toilet, had'e da fashewa da kuka a hankali..
Can kum munu ta bud'e idonta se taga wayam Sam tashiga qwalawa kira
"Shine kika gudu ko, zaki sameni ne inanan ina jiranki kizo ki fad'a min who the lucky champ is"
Sosai ta jima cikin band'akin ko da ta fito ma sallah ta tayar da ta idar kuma ta rungume munu ta baya trying to act normal tace "nayi miki wayo, dama na kula tunda muka baro kano kike 'boyemin wani abu shiyasa nayi miki wayo"
Ta juya a guje ta fita munu ta biyota suna dariya direct assembly hall suka shiga inda shugabar makarantar ke ma d'alibai barka da dawowa sabon term da kuma murnar zagayowa sabuwar shekara.
To nima de kdeey ina taya dukkan masoya littafina dama kafatanin al'umma murnar sabuwar shekara
*Happy new year 2020🥳🤸🏻♀💃🏻*
©️Kdeey😊
DABAIBAYI 👄
©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊
®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)
(25)
Iface ifacene ya maye gurbin maganar shugabar bayan data gama rattabo bayanai tare da kuma introducing malamai ga sabbin d'alubai,
Haniyar da ta cika hall d'inne yasa taja gefen shiga corridor ta tsaya, kad'aici yasa ta tunanin abinda ya faru mintuna da suka shud'e "Bro..B" muryar munu ke mata yawo akai, taya akayi all this while bata fahimci inda 'yaruwar tata ta dosa ba? Hakan na nufin namiji d'aya suke so kenan, shin ya akayi na amincewa soyayyarka..bayan ni d'in banta'ba soyayyaba..,ido ta lumshe hawaye na cigaba da zuba,
Gyaran muryar da akayi ne yasa ta bud'e idon a hankali, "handky" wata kyakkyawar yarinyar ta furta fuskarta d'auke da fara'a, kuma bud'e ido tayi dan kuma tabbatar da abinda take gani d'in shin dagaske ne?
"Sholey" ta furta cike da mamaki da farinciki mixed together, jinjina kai tayi had'e da bud'e hannu tace "surprise"
Fad'awa tayi jikinta cike da farinciki nan kuma kukan ya sauya zuwa na farincikin ganin qawartata.
***
Bisa gadon ta suka zauna hannunsu a sarqe bayan fitar munu daga d'akin ta zayyana mata halin da take ciki, shiru sholey tayi kan tace "zaki yarda idan nace miki cikin labarin ki ba komai se zallar tausayawa da ganin qima? Sam you are just sixteen for goodness sake, kar ki bari wannan shirmummukan su kanainaye ki su tauyeki, yanzu ba lokacin soyayya bane, kiyi amfani da quruciyar ki kan tsufa yazo miki, nasani you are a human dole ki so opposite gender d'inki, amma b yanzu ba,
Kuma ni duk cikin zantukan ki ba komai se zallar tausaya masa da kike saboda yanayin hidimar da yake dake, look we are in this environment to gain knowledge pn how to build our world nan da shekara biyu you will be freed up so lets use our time before its too late" ta qarashe da d'aga mata gira
Kai ta d'aga a sanyaye kan ta sulale ta kwanta saman pillow, tabbas Bro B ya mata halacci a rayuwa tun da har ze iya kashe aikinsa ya koma kula da ita shin dagaske tausayinsa ne yayi rinjaye a gareta? Da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita.
Sautin kiran sallar dake tashi a wayarsa ne ya tada shi daga nannauyan baccin da yake miqa yayi had'e salati idonsa ya sauka saman agogo dake maqale jikin bango, 2:00pm tashi yayi ya nufi d'aki yayi alwala yayi sallah sannan ya waiwayi office,
***
Cikin ikon Allah suka isa gida sede shigar su keda wuya sukayi kici'bis da ita, ganin suna muzurai yasa tace dasu "mami, yaya kune yau a tare qarqashin inuwa d'aya, lallai za'ayi ruwa da qanqara"
Hannu ya kai mata "ke dan ubanki ni sa'anki ne ko mami tsarar wasanki ce da zaki tsare mu da tambayoyi"
Cuno baki tayi, "to ba gskiya bane abinda kullum fad'a kuke" hannu ya kuma kai mata da niyyar mangareta tayi saurin 'buya a bayan mami,
Ya nunata da yatsa zan kamaki ne"
Hararar sa tayi daga bayan mami bayan ya fice ta fito tare da zama kusa da mami tamkar zata shige jikinta,
Tace "mami daga ina kuke haka jikin ki sanyi?" ta d'an d'ago tana kallon ta, d'auke kai hajiya maryam tayi cikin qoqarin kauda zancen tace "Rayya bansan tambayar kurum da Allah, daddyn ku ya shigo daga office?"
Gyara zama tayi had'e da d'aga kafad'a "yeah...amma yana shigowa CP ya kirasa naga ya fita"
"Ya fita? Shi da wa?" Tace cikin son ji,
"Oh mami nifa ban sani ba, call and ask him" t tashi har ta fara tafiya ta waiwayo "yawwa i forgot mahaifan hasheem are coming"
"Duk wani abu me muhimmaci is stick in here" ta nuna kanta da yatsa kan ta cigaba da cewa "so i see no reason da zan manta da neman auren 'ya ta" ta qarashe tana me d'aukar jaka ta shige d'aki.
Halim ta kira tana kuma jaddada masa kan fitar su ta anjima da cewa ya shirya ta a sirrance, bayan ta ajiye wayar ta shiga to and fro a ranta tana ayyana cewa lallai ne su qarasa hajiya mariya da namadi a yau dinnan kan su maida hankali gun kabiru da yaronsa tun kan dss su gano she's behind all this, murmushi tayi me sauti a fili ta furta "lallai nasara na tare dani" ta bushe da wata iriyar dariya.
Ita kuwa RayyaLumshe ido tayi game da kya'be baki ta wuce d'aki da niyyar kiran hasheem.
☆
Dss bashari, col. Najib (labarin aurena), tare da bello ne ke zaune a office d'in Najib suna shirya yanda operation d'in ze kasance, knocking a kayi bisa door
"Yes" najib ya amsa, wata budurwa me matsakaicin kyau ta leqo "sir me girma governor ke neman iso"
"Let him in×2"
Suka miqe a tare dan girmamawa a daidai lokacin da jamilu mainasara ya shigo, sara wa najib yayi fuskarsa d'auke da murmushi,
"your excellency sir" auka furta hakan a tare , da hannu ya nuna musu
"pls have a seat"
Sabuwar gaisuwa suka kuma yi, yace "Anwar right?" Yace idonsa kan fuskar bello,
Hasheem ne ya amshe da cewa "qaninsa ne bello"
"Uhum? Yeah se yanzu na kula wancan be kai wannan haske ba"
"Yes sir " bello yace in a low voice.
"Hasheem ya wajen manya"
"Lafiya qalau sir" yace cikin shafar kai cike da kunya, jinjina kai yayi kan ya tattara hankalinsa kan col Najib,
Yace "colonel akwai labari ne, dan daga ni had'uwar nan taku waje d'aya akwai magana"
Dariya col najib yayi "we all went
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 13