"perfect" yace, qafafuns ya raba game da hawa samanta ba tare da ya ta'bata ba har seda fuskarsa ta daidaita da tata ya sakar ma kyawawan lips d'inta sumba kafin ya zira hannuwansa ta bayanta ya tallafo ta jikinsa, shiru ne ya biyo baya kan a hankali yace "nazo shirya amarya ta"
Wal tayi da ido, ya kanne mata idonsa, dariya tayi tace "ina su mummy?"
"Nace dasu su huta ni zan shirya abata"
"Mene?" Yanda ta waro ido ya sa shi dariya, daidai lokacin suka ji knocking, " maza tashi ta qaraso"
"Wa kenan"
Miss dee from abuja na taso ta takanas saboda ta shirya min ke, qofa ya bud'e matar ta shigo kallo d'aya zaka mata kasan ta jiqu da naira ga uban gayu da take dashi cikin daddad'an muryarta data tsumu da turanci suka gaisa da Anwar kan ta maida idonta kan Sam game da furta kalmar "tubarkallah, amaryarka tamkar ita tayi kanta, she is the real definition of beautiful,"
Murmushi ya saki yana jin tamkar duk duniya ba wanda ya kai shi sa'a, miss dee ta kuma cewa "we are running out of time, oga sir ka bani aron amaryarka for just 3hours"
Kai ya d'aga kan ya matsa jikin Sam ya bata peck a goshi "take care" ya furta cikin kunnenta da haka ya fita mutan gida ana tayi masa tsiya wai dududu awa nawa ya rage a kai masa ita, be kulasu ba se murmushi da yake saki har ya bar musu gidan baki d'aya,
***
Few hour later
Hawaye ne masu d'umi suka gangaro bisa fuskarta, "shiii kada ki 'bata mana shirin mu ango ya kasa biyana in ponds kamar yanda ya alqawarta" cewar mss dee
Murmushi ya su'buce mata, still idonta bisa mirrow gani take kamar ba ita ba, sanye take da royal blue gown wacce take fitted se de ta bud'e daga qasa sosai har ta mamaye kusan rabin d'akin, sosi rigar tabi duk wani curve na jikinta ta kwanta showing her real figure 8 shape, fuskar nan tasha nude make up yayin da sumar kanta aka killace ta cikin royal blue head wuyanta da kunnenta se kyallin gold suke haka hannunta cike yake da kambunan gold, an sakaye qafarta cikin heel d'in dune yayin da clutch d'in hannunta ta zama ta kamfanin dune itama, duk inda ta motsa qamshin turaren khumra da tsadaddun designer turaruka ke tashi, wasu hawayen ne suka kuma yanko mata mss dee tasa tissue ta d'auke mata su, "wai su hawayen nan bazasu dena zuba bane"
"I wish daddy na is alive to see this day" tace cikin muryar kuka
"I'm sure he is watching from heaven"
Murmusawa tayi kawai jin abinda matar ta fad'a daidai lokacin akayi knocking sholey ta shigo itama cikin ubansun kwalliya,
"Hello besfrenn" tace cikin juyawa dan Sam taga kwalliyarta, a hankali ta karkato haba ai sholey daka tsalle tayi tana ihu "wow babe kinyi kyauuuu..."taja kalmar kan ta fad'a jikinta suka rungume juna ta d'auko wayarta qirar iphone 11pro ta d'add'ana mata pictures sannan ta fita dan kiran motar da zata d'auki amarya ta matso bakin qofar falon,
Da taimakon mss dee ta tako d'as d'as zuwa waje sholey ta bud'e mata qofar baya ta shiga kan ta juya itama ta shige motar dake gaba,
Hannu taji an zira cikin nata wanda ko ba'a fad'a ba tasan mamallakin su kasancewar motar da duhu yasa bata ganin fuskarshi sosai, daf da ita ya matso game da zira fuskarshi cikin wuyanta yayi kissing sannan ya miqa hannu ya kunna fitila, seda yayi blinking eyes sannan ya juyo da fuskarta setin da yake, "tubarkallah Masha'Allah" yace game da kashe wutar ya janyo ta jikinsa ya rungume haka suka zauna har seda suka isa harabar da zasu sauka wanda shima kan su saukan seda paparazzi suka gama buga musu hotuna har dai suka isa cikin hall inda tuni amare da angwaye sun hallara sune a tsakiya daga gefen hagu bello da munu ne daga dama kuma hasheem da Rayya dukkan ninsu sun sha kyau abun dai se Masha'Allah.
Anci ansha an gintse, direct daga nan angwaye suka kwashi amarensu zuwa gidajensu kamar yanda gomna jamilu mainasara ya umarta.
A gurguje🤸🏻‍♀
Yau watansu uku cif da tariya, wanda yayi dai dai da rasuwar hajiya maryam mahaifiyar Rayya,
"Baby please mana..." cewar Ann dake zaune saman dining table yana cin gasashen naman rago"
Sam dake tsaye gaban cooking gas tana juye irish a plate jikinta sanye da oversized shirt wacce ta sakkomata har rabin cinya , kallo d'aya zaka mata kasan ta Anwar ce tace "baby ni Allah se ka jira mun gama cia nutse sannan za muyi wanka baza mu fita da yunwa ba"
"Baby cikina is full, kalla kiga yanda tumbi na ya girma" yace a shagwa'be
"Ka bani minti kad'an kaji yanzu zan gama"
Tagumi yayi with a pout on his face ya zura mata ido yana mamakin yacce kwana biyu kullum se tayi breakfast da irish take jin dad'i shekaran jiya daya hanata har da kukan ta, jira yayi har ta gama ya sa'bi abarsa zuwa band'aki inda suka sullu'bo wanka bayan ya nad'o ta cikin towel ya ajiye ta, suka mulke jikinsu da tsadaddun mayuka masu gyara fata sannan suka kimtsa suka fita zuwa gidan gomna.
A tare suka jera zuw cikin falon kowa ya hallara su kad'ai ake jira, kallon juna sukayi sannin cewar sunyi laifi bayan sun gaida kowa taja jiki ta zauna tsakiyar munu da rayya shima gurin d'an uwansa da amininsa ya zauna , nan daddy ya kalli rayya yace "daughter bismillah yau zaman kinsan naki ne"
Murmushi tayi wanda ya fallasa 'yan tageyen kumatun da tayi bayan sallama irin ta addinin musulunci ta kalli mummyn sam tace "mummy, nazo da qoqon bara ta da fatan zaki tallafa min?"
Murmusawa mariya tayi " idan har ina da abin tallafa miki insha'Allah zanyi da dukkan qarfi na"
Kai ta jinjina "daddy yau watan mummy 5 cif da rasuwa idan baka manta ba kayi min alqawari kuma yau nake son ka cika min"
Kai ya d'aga, seda ta kalli mutan falon tsaf kan ta sauke idonta kan fuskar mijinta ya jinjina mata kai ta sauke ajiyar zuciya
Tace"inason kayi replacing gurbin mummy da mummyn Sam"
A birkice mummyn sam tace "what?!"
Yayin da Sam ta miqe tsaye a firgice, Ammi kuwa hawaye game da murmushi ne suka maye fuskarta, kowa na falon ya cika da mamakin qarfin hali irin na Rayya,
Sam ce ta fita daga falon a guje, mummynta ta bita, Anwar da Ammi ma bin bayansu sukayi, shiru falon yayi, hawaye suka ziraro a idon Rayya tana kallon mijinta tace"ka gani ko dama nasan baza su aminta ba"
"Doctor jikin nata ya tashi ne?" Cewar mainasara,
"Daddy...lafiyata qalau i know what i'm doing, na tabbata deep down inside you kanaso dan Allah kar kace aa i know mummyn sam too zata amince kar ka manta she's your first love inaso ka cika burin da ka jima kana mafarkin samu, this is d only way i can repay you kan 'bata maka rai da nayi lokacin rasuwar mummy please don't say no kaji.."
"He won't say know.." waiwaya wa tayi ta kalli Ammi cike da mamaki, Ammi ta riqo hannun mariya tace "jamilu for the second time zan baka amanar 'yaruwa ta"
Miqewa yayi game da d'an duqawa irin na girmamawa yace "nayi miki alqawari ko quda baze sauka saman fatarta ba without my permission"
Sam dake tsaye ta bayansu tace "na yarda, Allah ya sanya alkhairi" ta qarashe cikin rawar murya sosai take jin kishin wani ze kasance da mahaifiyarta.
A take me girma gomna yasa a nema masa zama da me martaba inda basu wani d'auki lokaci ba cikin satin aka d'aura aure, inda mummyn Sam ta tare a gidan gomnati matsayin firstlady,
Bayan sati biyu, Ammi da iyalanta suka koma Birmingham inda zasu cigaba da zama lokaci lokaci zasu rinqa ziyartar qasarsu wanda Anwar yaci alwashin da ya gama ginin reshen AB machinries zasu dawo dun dun dun se ko idan ziyara, wanda hakan ba qaramin dad'i yayi wa Ammi ba,
A gefe guda kuma a kullum jamilu mainasara cikin shiwa Rayya albarka yake, ganin tun lokacin daya auri Mariya yake samun cigaba ta ko ina,
Bayan shekara hud'u
"Kai ku d'agashi before nazo kan ku" Sam tace a tsawace, a firgice yaran suka fashe da kuka har suna sheshsheqa,
Fuska shaye da toka yace "baby wai meke damun ki ne jiya mafa seda kika saka su kuka"
"Oh shikenan kuma ban isa nayi ma yarana fad'a ba se ace meke damuna" fashewa tayi da kuka game da juyawa ta fad'a d'aki,
"Innalilllahi" ya furta kan ya sa'bi twins d'in a hannunsa suka bi bayanta, kusa da kanta suka zauna ganin yaran na kya'be baki alamun suma zasu yi kukan yasa shi saurin dakatar dasu yace "heyys kuce we are sorry mami"
Cikin gwaracinsu kuwa suka fad'a, tashi tayi zaune tana tura baki gaba ta janyo su duka jikinta tana kissing, jan jiki yayi zuwa gareta cikin kunnenta yace "nifa?" Hararar wasa tayi masa kan ta kwantar da kai saman qirjinsa tace "I'm pregnant"
"Alhamdulillah" yace game da dira a qasa yayi sujjada, tayi rau rau da ido "are you happy?"
Kallon ta yayi game da kallon twins dake lafe a jikinta bacci ya kwashesu ya amshe su d'aya bayan d'aya ya kwantar dasu a gadonsu kan ya zo ya jata jikinsa su kwanta hannunsa d'aya saman cikinta yana shafawa d'ayan kuma saman kanta yana mata susa,
"I'm excited baby, kyautar mutum fa? Kinsan kullum addu'a ta itace Allah yasa na kasance cikin d'aya daga cikin wanda annabi zeyi alfahari dasu, baby Allah yasa yanzu ma ki haifar min twins"
Dukan qirjinsa tayi, yace "yes kinga Afif da Affan sun cika 3years.."
"Saboda kullum ku isheni da qiriniya ba uma su rinqa tumurmusheka"
"Shine damuwar ki, shiyasa kike musu fad'a wlh baby idan ina tare dasu Allah kad'ai yasan irin farincikin da nake ace wai dukkan su jinina ne? Huh Allah is great"
Jin da yayi tayi shiru ya leqa fuskarta yaga ashe she's fast asleep, a fili yace "wannan da rikici da kuma bacci kazo kenan" kissing d'in cikinta yayi tare da tofa musu addu'a duka shima ya shige jikinta lokaci d'aya bacci ya d'auke shi.
_Tammat bi hamdulillah_
Na sadaukar da wannan littafin nawa ga duk wani masoyin rubutu na, sai kun jini cikin sabon littafina me suna ...DA CIWO A ZUCIYA TA
Whatsapp only; 08148700538
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 13