salu'be suka mara masa baya zuwa wani d'aki, da isar su jikin Ammi ya hau rawa da ta qarasa bakin gadon kuwa yanke jiki tayi ta fad'i..
©️Kdeey😊
DABAIBAYI 👄
©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊
®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)
(28)
"Ammi!" Suka yo kanta a rud'e, ruwan dispenser hasheem ya tsiyayo cimin cup Anwar ya rinqa shafa mata samn fuska zuwa wuya, cikin hikimar ubangiji ta farka bakinta d'auke da sunan "mariya.." tashi tayi ta tsugunna setin fuskar ta, tasa hannu tana shafawa had'e da fashewa da kuka,
"Yanzu wani mara imanin ne ya maida ki haka? Shine yanzu ina ribar take ? Innalilllahi wa inna'ilaihir rajiun"
Kafad'unta ya riqo cikin kwantar da murya yace "Ammi ki bar kuka dan Allah mummy zata samu lafiya insha'Allah, ai duk wanda yaci zalin wani Allah ba ya barinshi, a yanzu haka mutanen da suka yi mata haka suna hannun hukuma, yanzu haka dalilin zuwan mu garinnan me girma gwamna ya nemi presence d'inmu dan warware abinda ya jima a rufe kamar yacce yace"
With cold eyes ta kalli governor "jamilu who is behind all this?"
*
"Doctor i'm sorry to say dole zamu rufe asibitin nan har zuwa mu gama binciken mu, Alhaji kai kuma inaso kayi hakuri kje gida da jaririna nema masa abinci , ku saka mishi ankwa muje"
"Wannn shine laifin banjiba ban gani ba, nashiga uku" cewar d'aya a ciki nurses d'in asibitin,
"Ku dakata yalla'bai"
Juyowa yayi "yes"
"Amm i think i know where she is"
Kallon kallo akayi, kan ya nuna mata hanya alamun muje to, nurse da doctor suna motar yan sanda yayin da bello a motar sa shi, uncle da kuma gwaggo ne se jinjirin dake hannun gwaggo.
Tafiyar minti qalilan ya kaisu doctors quarters qwanqwasa qofa tayi daka ciki aka ansa da cewa ana zuwa,
Wata dattijuwar mace ce da bazata wuce 50-60 b ta bud'e baki ta hangame, nurse d'in ta girgiza mata kai, kaucewa tayi gefe suka shiga,
'Daki nurse d'in ta shiga zuwa can ta fito hannunta riqe da mom hajar dake ciccije baki saboda ciwon jiki,
Sairin miqewa uncle yayi ya nufo ta, "bawan Allah kada ka ta'ba ta dan kuwa kai d'in azzalumi ne!"
Maganar nurse d'in ta razana zuqatan kafatanin mutanen dake falon, "sister nasira kinsan me kike cewa kuwa?" Doctor yace a tsawace,
Idonta ta sauke bisa fuskar mom hajar tace "d'azu bayan an tafi goge baby _turo d'an teburin allura nayi zuwa bakin gadon da take, sannu nayi mata, na shiga zuqo ruwan allura d zummar nayi mata naji an riqo hannuna "kina buqatar wani taimako ne ko wani na damunki?" Girgiza kai tayi "inaso ne ki cece ni" "na cece ki" nayi mumushi kawai dan a tunani na ba'akan cikin hankalinta take ba, tsikara mata allura nayi bayan nagama dubata na juya zan fita ta riqo hannuna, "idan ban gudu daga nan ba kasheni zasu yi", "suwa?" , "mutanen da suka kawo ni, mijina d'an yankan kai ne, jira yake na haihu ya kashe ni saboda wai amfani na ya qare a wurinsa", "let me call the police", hanani tayi a cewarta megidan nata nada mutuqar hatsari na bari ta bar asibitin idan ta samu lafiya se nayi reporting, shine dalilin daya sa nayi snicking out da ita na kawo ta gidana_ wannan mahaifiyata ce dana ce tayi mata wanka kan na dawo musan abinyi,
Qasa uncle ya durqushe, baki bud'e, gwaggo kuwa salati take da sallallami nan bello yayi musu bayanin yacce suke da ita har da irin sana'ar uncle d'in haquri aka bawa juna doctor da yansanda suka tafi, gwaggo ta matsa kusa da ita
"Hajar a d'an zaman da mukayi zan iya rantsewa kina da hujjar yin wannan qaryar, sede ki sani qarya ba abar wasa bace tun bare irin wannan qazafin, bakya gudun abinda zeje yazo bare yanzu yanda duniyar take, 'barayi, kidnappers, masu garkuwa da mutane duk neman sunake ido rufe! Meyasa meye dalilin ki na yin hakan?"
Kukane ya kufce mata me cin rai kan tace "na rantse da Allah gwaggo ba nayi haka bane dan cin zarafin barrister se dan kunyar abinda na aikata masa"
Jimm gwaggo tayi kan ta kalli barrister dake tsugunne idonsa a kan hajar tace "shikenan inaga ya dace muje gida a qarasa maganar nan, ungo babyn nan kayi mata addu'a"
A salu'be yasa hannu ya kar'beta "sedai ba dabino" yace
"Kash kaga kuwa mantawa mu kayi ba mu saka ba"
"Karki damu hajiya inada zamzam bari na kawo"
"Ah zam zam? Dama ana iy amfani dashi madadin dabino?" Cewar gwaggo
Bello ya gyad'a kai "eh, a littafin fada'ilu ma'u zam zam sahafi na 29 malamai sunce annabin rahma ya d'iga zam zam a bakin yaro, ko zuma a d'ugawa yaron a bakinsa ko a d'uga a bakin musulmi ya gauraya da yawunsa sannan a d'iga wa yaro"
Gyad'a kai tayi game da cewa "akwai zumar addu'a cikin jakar ki hajar wacce na baki ki rinqa lasa ko"
Mom hajar dke shedding tears tayi nodding kanta a qasa, jakar gwaggo ta janyo ta miqa wa barrister ya saka cikin bakinsa yasa wa yaran a baki, mulai mulai kuwa ya mamule, yay masa kiran sallah a kunnenta na dama game da miqata gurin gwaggo daidai lokacin da wayar bello ta karad'e falon da qara,
Sunan Bro A yayi appearing saman screen d'in yay saurin answering,
"Gamunan qarasowa" yace game da hanging off,
"Ina ganin ya kamata mu wuce goverment house dan tuni su Ammi sun qaraso"
Barrister ya kalli sashen da mom hajar take a hankali ya taka zuwa inda take "zaki iya bin mu ko hankalinki yafi kwanciya a nan"
Girgiza kai tayi, game da d'aga kai tana kallon nurse "sister pls taimaka min da hijabi na a ciki"
Kai ta d'aga tashiga wata qofa dake falon.
Riqe da ita barrister ya zauna a baya ya kwanto da kanta saman qirjinsa zuciyarsa ciki da tunani dalilin matar tasa nayin hakan?
Yayin da gwaggo ke gaba rungume da qawarta kamar yacce tace, bello kuma na driving hankalinsa baki d'aya naga kwaltar yana juya steering wheel cike da qwarewa.
♧
Hannun Ammi cikin na mummyn Sam dake bacci sanadiyyar allurar da akayi mata, Anwar ne yaja hannun hasheem suka fita daga d'akin
"Ya dai ragowar mutuwa" hasheem ya furta cike da tsokana
'Yar qaramar dariya yayi, "bansan wulaqanci mijin fat mango" ya qarashe game da kanne masa ido d'aya, naushin wasa ya kai masa ya kauce yana fad'in
"Wlh karka kuma zagar min mata ko mu hanaka zaman garin nan"
Hannu ya had'a gu d'aya "ayi min afuwa masu gari, zo muje mu taho da baqin mu na nijar"
Da motar hasheem suka tafi basu tsaya ko ina ba se gaban gidan senator asi'u, seda akayi musu iso suka qarasa ciki cikin tangamemen falon inda Alhaji tasi'u yake basu wani jima ba suka fito biye dasu wata baqar jeep ce inda bayan sun fara tafiya suka sa'ba hanya,
Daga can kuma ss office a wata tinted mota aka sako hajiya maryam da d'anta halim ala nufo gidan gomnati dasu.
***
Ta wutsiyar ido take kallonta dan ta kula tunda su Ammi suka tafi take wani sukuku ko suna hira bata jefo baki kaman yarda ta kanyi lokxi zuwa lokaci,
Bakin gadonta munu ta zauna game da d'an jijjiga qafarta, idonta dake a lumshe ta bud'e suka sauka saman na munu,
"Tashi muyi wata magana" munu tace,
Kai ta gyad'a mata, tare da jingina bayanta jikin bango bayan tasa pillowfor support,
"Sam inaso ki fad'a min gaskiya duk tambayar da zanyi miki pls"
Sai da ta sauke numfashi tace "ina jinki,"
"Zaki iya fad'a min whats going on between ke da Bro B?"
Baki ta bud'e ta katseta, "truth..i want the truth"
"Munu is kind of weird! I don't know how to put it into words"
Dariya tayi qasa qasa "ki fad'a min Sam zan fahimta, i saw the chemistry between the two you"
"Dagaske?" Tace in a worry voice,
"Hey chill, nice fa all i know is yana yawan kallonki a sace that is tun lokacin da muka koma gidan su ga yawan yi miki fad'a wanda ni a fahimtata yanason yake jin maganar ki ko da kuwa cikin kuka ne"
Fuska ta yamutse "ke munu, ba novel kike karantawa ba all this signals..."
"Oh! Ke a tunaninki abinda nake karantawa all na wash? To tsaya kiji duk abinda qwaqwalwa ta qirqira used to happen in real life"
"Ahh" tayi making sound,
"Baki yarda ba kenan?, shikenan, yanzu dai i need my answer"
Gyara zaman Sam tayi had'e da crossing legs, nan ta zayyane mata tun first kiss d'insu har abinda ya faru ranar da suka zo yi musu sallama,
"..munu wlh forcing d'ina yake abin nata damu na, kinsan yanda nake i usually bar magana a zuciyana...and i'm also scared to say it out especially to Ammi, dan Allah ki taimaka min munu.." ta qarashe cikin kuka,
"Shiishh...is ok" tasa hannu ta goge mata hawaye tare da rungume ta, tunani ya cika kanta,
Zuciyarta na bata lallai akwai de wata a qasa dan a yacce take ganin Ammi bayan kamasu cikin intimacy will never let go of it cikin sauqi dole akwai wata a qasa, da wannan tunanin bacci ya sace su kasancewar su duka ba sallah suke ba (they are on period).
***
Tun bayan da suka isa gidan a ka bawa Ammi band'aki ta wanke mom hajar tas har da babyn ma, duk da cewa har kawo wa wannan lokacin tana zubda hawaye haka anyi anyi ta furta abinda ke zuciyarta taqi qarshema she insisted on lallai idan an zauna maganar data tara su zata fad'a idan kuma an takurata zata fasa maganar kuma she's going to live, hakan yasa aka bar yi mata maganar tun bare da suka samu ta shayar da baby teema wato fateema zahra kamar yanda barrister ya rad'a mata suna.
©️Kdeey😊
DABAIBAYI 👄
©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊
®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)
(29)
Sallamar sa ce taja hankalin bello dake hira da Ammi tsam ya miqe ya fad'a kan qirjinsa a tare suka saki wani silent kuka,
"Bro B...dafatan kana cikin qoshin lafiya?"
'Dago kai yayi game da dafa kafad'arshi
yace "yanzu kam dana ganka na tabbatar da lafiya nake, tun bayan daka tafi na kasance cikin fargaba da d'imauta, yanzu kam bazan yarda ka kuma yin nesa dani ba qafata qafarka" ya kuma rungume shi, d'an dukan bayansa Anwar yayi "nima bazan kuma yarda na barka cikin garinnan dake dabaibaye da abubuwan al'ajabi ba d'an uwana "
Knocking akayi bisa door, inda me girma gomna ya bada umarnin a shigo,
P.A d'in gomna ne,
"Ya akayi Rabi'u?"
Sai da ya sara cike da girmamawa yace
"Sir, dss bashari yace a sanar maka da zuwansa"
"Let him in" cewar jamilu mainasara
Ya juya idonsa a lumshe ba tare daya furta uffan ga mutan falon dake ta'ba hira kad'an kad'an cike da alhini ba,
Qarar qarafunan dake riqe da hannu da qafar halim ne yaja hankulansu kan masu shigowar, seda suka shigo falon sosai Ammi ta miqe tsaye sede kafin ta samu damar furta wata kalma muryar kawu kabiru ta daki kunnan gwaggo itama de miqewar tayi lokaci d'aya hawaye ya yanke mata, nan kuma isowar umma salamatu ta kuma saka falon a wani yanayin yayin da take hajiya maryam ta hau zantuttuka masu kama da sambatu cewar lallai se an fitar da umma salamatu daga falon
firr ta rikice musu tamkar sabuwar ta'bi har seda kyautar lafiyayyan mari daga hannun me girma gomna ya sauka a kuncin ta kafin a samu weather d'in d'akin ta daidaita,
nuna kanta tayi da yatsa cikin zare idanu take fad'in "Ni? Ni ka mara jamilu.."
Dariya ya d'anyi me sauti, "kwarai maryam yau sunana jamilu...to Alhamdulillah tunda ke kanki kinsan ta faru ta kuma qare, a yau ina so ki sani duk wanda ya jira ganin bacci na to kuwa ze rasa nashi, maryam kin shani na warke inaso da bakin ki a gaban kafatanin mutanen falon nan or let me say family ki fad'i gaskiyar yanda al'amarin aure ya qullu tsakanina dake bayan 'yaruwar ki mariya da na nema?"
Kallon kallo aka koma yi, cikin sauti me cike da d'imbin mamaki gwaggo tace
"Me kake shirin cewa ranka ya dad'e?"
Kai ya gyad'a idonsa saman fuskar hajiya maryam da yakejin tsanarta fiye da tunani yace "kar ki bari na fusata, dan al'amarin baze ta'ba yin kyau ba"
'Dit dit..qarar na'urar dake nuna fitar numfashin hajiya mariya ta karad'e kunnuwansu
"ta farka" shine abinda wata nurse dake kula da lafiyar ta, ta furta cikin farinciki, cikin su rasa me bawa wani hanya akayi, Ammi dake gaba turus tayi data shiga dakyar ta iya jan qafa zuwa gaban gadon cikin zubar hawaye yayinda ta toshe bakinta da hannu..
Cikin murya me fitar da iska ta marasa lafiya tace "yaya...ha.j.j..o" ta miqa mata hannu, saurin kamawa Ammi tayi game da jinjina kai, "nice..nice mari.."
Smiling hajiya mariya tayi, d'ai d'ai take binsu da ido kan fuskar jamilu mainasara ta tsaya, ta lumshe ido ta bud'e cikin qoqarin tashi,
"Tsaya na taimaka miki jikin ki ba qarfi sosai" cewar nurse bayan da ta gyara mata pillow a bayanta ta yacce zata fi jin dad'in zama, murmushi ta mayar mata, kan ta waiwaya ta kalli yaruwar tata
tace "tun bayan da labarin rasuwar daddyn Sam ya riske ni, nake mafarkin yaro me irin fuskarki yana bawa mami na kulawa yaya hajjo, se de mafarkina na jiya daban ne da sauran..shin dagaske ne Mainasara yasa an qwato ni ceto ni daga azabar da yaya maryam ke gana min na tsayin lokacin da Allah kad'ai yasan yawansu..yaya hajjo kin ta'ba jin labarin da mutum ke yiwa kansa fatan mutuwa?...to nayi wa kaina har wani lokacin nakan nemi kauce hanya,
Tsayin wannan lokacin na kasance cikin wani cage da ko cikin dabbobi mafi qasqanci ake ajiyewa ciki, ba sallah, ba wanka se bayan wata take bani sitira na sauya, abinci sau d'aya a rana, bayan gida ina yinsa ne cikin ledar da kawo min abinci, ina shan ruwa sau biyu a rana,
Bani da abin rufa cikin ko wani yanayi da ake ciki haka nake kwana, ga sauro dake addaba ta, kinsan me nake ce mata tun ina kwana d'aya a wurinta?"
Ammi ta girgiza kai "..ina ce mata ne, yaya maryam ki taimakeni ki kashe ni idan bazaki iya ba ki bawa yaran ki su qarasa ni ko ki bani guba nasha..." ta qarashe cikin hawaye,
Ammi ma cikin zubar hawaye tace "ya isa haka mari, duk ba mafarki kike yi ba, tabbas mainasara ya ceto ki daga hannun makirar can and he stands to get justice for you, ki bar zubar da hawaye kada kanki yayi ciwo.."
"Yaya hajjo already na nakasa dan bazan iya bud'e idona duka ba saboda haske, i am used to duhu"
Hannu ta d'aga sama "Allah na gode maka daka dawo dani cikin dangina"
Gyad'a kai Ammi tayi fuskarta maqale da murmushi tace "Mari ki kwanta haka, idan kika huta zuwa anjima se muyi magana"
Ido ta lumshe game da jinjina kai tace "i am thirsty.."
Ruwa Ammi ta bud'e ta tsiyaya mata cikin cup ta d'ago kanta ta bata, a hankali tace "yaya hajjo yanzu shikenan gwaggo ramatu tayi sanadiyyar bazan kuma ganin daddyn Sam ba?"
"wacece gwaggo ramatu Ammi?" Cewar Anwar,
Numfasawa tayi tare da fad'in, "kishiyar babar mu ce kuma mahaifiyar maryam"
"Amma ita d'in ai ta jima da rasuwa ko daddy?" Cewar Rayya,
"Uhm, ta rasu ne a hatsarin mota daga jos adamawa zuwa jos wanda maryam ce ta haddasa hakan"
"Daddyy?"
Kai ya d'aga "at that time baki da lafiya Rayya bazaki sani ba, amma mahaifiyarki ta jima tana cutar da rayuwata har da ma taki..., kuje ku shigo min da ita" yace idonsa saman na securities dake tsaye bakin qofa,
Ita ke gaba, halim a baya suka shigo kai a qasa, zama suka yi can gefe d'aya, bayan securities d'in sun fita ne, ya waiwayo game da zama saman kujerar dake tsakar d'akin yayi crossing legs
"Inaso ku kad'e kunnenku dakyau dan jin yacce labarina ze faro"
_tafe nake cikin garin bichi dake jihar kano se sauri nake na isa tashar jirgi dan tsaida masoyiyata da mahaifanta da zasu bar garin zuwa asalin garin mahaifinsu, duk wanda ya kalle ni se ya kuma kallo na ba dan komai ba se dan tsabagen dattin da nayi marabata da mahaukaci sabon ta'bi qalilan ce, dan dawowata daga kudu kenan na tarar da labarin tafiyar su,_
_Ranar seda na karad'e cikin jirginnan tsaf babu ko qurar su, nan na zauna cike da takaici har kusan awa uku sa'annan na koma gida, sede kafin na wuce gidan seda na tattambaya maqota ko akwai wanda yasan inda zasu daqyar na samu wata ta shaida min maiduguri suka koma inda yake asalin garin mahaifinsu,_
_Bayan qasa a gwiwa ba na shirya tafiya maiduguri bayan shan artabu da nayi da mahaifana a cewarsu tunda har kuka bar garin to kuwa lallai mahaifinku baze ta'ba yarda na zama sirikinsa ba haka suka hanani zuwa dana dage ma se mahaifina yace idan har naje ba da yawunsa ba,_
_Jin magana irin na yaran da yasa na haqura, har bayan kusan shekaru shida a lokacin na gama makaranta har ina aiki a gefe guda kuma ina siyasa, na hau jirgi zuwa maiduguri, bansha wahala wajen neman gidan ba kasancewar kakanku da yake sananne, ina isa na tarar da anyi rasuwa a gidan haka na zauna ba tare da na shaidawa mahaifinku dalilin zuwana ba daya tuntu'beni ma se cewa nayi ai nazo wani aiki ne,_
_Bayan sati biyu na lura cewa a duk sanda na shiga gida dan gaisawa da mahaifinku bana jin ko motsin mariya se gwaggo ramatu da maryam kad'ai hakan yasa nayi making up mind d'ina nayi masa magana, bud'ar bakinsa sai yace ai watan daya gabata aka d'aura auren mariya yanzu haka tana kano,_
_Kula da rud'ewar da nayi yasa ya rinqa ban baki, kwana uku bayan nan na shirya komawa gida, ana gobe zan tafi ina zaune a d'akin da aka saukeni naji yo hayaniya daga cikin gida, shiga nayi dan jiyo ihu, da isata na tarar da mahaifinku kwance rai yayi halinsa ga kuma mata na tofa albarkacin bakinsu_
_A lokacin nake jin labarin wai maryam ta haifo shege kusan shekaru biyu kenan a ranar kuma suka samu sa'bani da mariqiyar yaron shine ta tona mata asiri a gidan su har ma ta kawo yaron ta bata,_
_Wannan ne asalin yanda labarin ya faro, mahaifinku nada kwana arba'in cikin qasa kakanku ya nemi tayina kan na rufa musu asiri na auri maryam na tafi da ita,_
_A tunani na hakan kad'ai ne zesa a bar yada wa danginku magana yasa na amince, muka komo bichi tare inda nayi wa mahaifana qaryar bazawara ce na auro ta, da farko sun nuna sam basa sonta daga baya kuma suka aminta bayan shige da fice da maryam tayi ita da mahaifiyarta,_
_Idan bazan manta ba nasha kama maryam tana zuma mana magani a abinci ko tana binne abu kai har takai maryam idan mu kayi kwanciyar aure se ta lakaci ruwan maniyyi ta zuba cikin qaramar container,_
_Duk dan mu zauna lafiya ban ta'ba tambayarta dalilin hakan ba dan zuciyata na bani ba zata ta'ba cutar da ni ba, maryam ta fito da sabbin d'abiu na raini da kuma kalaman qasqanci ga mahaifana abin takaicin kuma bana iya yi mata fad'a bare kallon banza,_
_Ta ruguza soyayyar mahaifana a zuciyana haka ma 'yan uwana dan banda haihuwar Rayya, na jima ban nemi hanyar garin mu ba,_
_A wata rana muna hira da maryam muka d'auko hirar da inda nake sanar da ita cewa na gano gidan mijin mariya, nan ta nuna jin dad'inta har ma tace insha'Allah zata kai mata ziyara ashe bansani ba zuwa tayi aka binciko mata komai game da su har taci alwashin lallai se taga bayan su,_
_Ba mufi sati da maganar ba na tsinci labarin 'batan mariya, a d'aya 'bangaren kuma maryam bata nuna damuwarta game da hakan ba duk kuwa da cemin da take tana zuwa gidan har ma waya sunayi, banyi mamaki ba duk da banji dad'in yanda ta nuna ko oho ba sedai nayi shiru ne a ganina sun fi kusa,_
_A 'yan kwanakin na lura matata ta zama busy head ga wata iriyar waya da ta tsura mara amfani, hakan yasa na fara zargin akwai wata a qasa, nasa aka sa min ido akan dukkan wasu moves d'inta_
_cikin ikon Allah se muka had'u da ku (anwar, bello da hasheem) a asibitin getwell inda yarinya ta ke kwance kallo d'aya nayi muku nasan kud'in su waye duk da dama can arqalla ta ta'ba had'ani da Anwar, hakan yasa na rinqa cusawa Rayya soyayyar Anwar duk dan mu shiga jikinku dan shine abinda take lacking soyayyar 'yanuwan taka sede kasancewar rasgin lafiyarta bata fahimci hakan ba har se daga baya ta fuskanci soyayyarta naga doctor,
Muna haka bello da hasheem suka zo min da labarin nan inda na basu goyon baya dan yaqi da makaman maryam, cikin ikon Allah ga inda muka tsinci kanmu,..all way leads to pure truth,
"Na tsaneki×2 maryam"
"Na shiga uku" ta furta game da fashewa da kuka,
Adding yayi, "baki shiga uku ba tukunna dan har d'ari se kin shiga"
"Bani da laifi jamilu.."
Cikin girgiza kai Rayya ke fad'in " yanzu mummy rashin imanin naki yakai ki dauki ran d'an adam?? A gaskiya nayi takaicin kasancewar ki uwa a gare ni"
"Um um Rayya nayi miki kama da wacce zatayi kisan rai?"
Umma salamatu ta tashi tsaye a fusace tace "kwarai kuwa dan bada ban Allah ya kiyaye mu ba da tuni mun tafka babban kuskuren da kika so nayi ni da d'a na, kinsan mun zalunci yarinyar dake zaune damu tsakani da Allah, son duniya yasa kika kusa lalata wa yarona tarbiyyar sa, shin duk wannan abinda na lissafa kinaso kice duk ba yin kanki bane!"
"Ko kuwa informations d'in da kike saina munafurtan mijina ina baki suma ba yin kanki bane.." mom hajar tayi adding a tsawace,
"...you are all under gwaggo's spell !!!"
"Mene?" Suka ce a tare,
Kai ta d'aga, "mahaifiyata duk itace sila, wlh×2 ni aiwatar wace kurum tawa amma basirata bata kai nayi muku wannan DABAIBAYIn ba...na sani ba zaku yarda ba amma ko ni kai na bana sanin lokacin da nake yin wani abun har se na idar, a yanzu haka nasan bazan gaza kwana biyu a raye ba dan tasa nayi alqawari cewar duk ranar da na fasa qwai zan baqunci lahira...
©️Kdeey😊
DABAIBAYI 👄
©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊
®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)
(30)
_few pages left💃🏻🤸🏻♀_
...
Salati gwaggo tayi game da sallallami, "ke baiwar Allah amma baki ji dad'in halin ki ba sam"
Cikin zubar hawaye mom hajar taja jiki gaban barrister "kaji dalilin da yasa nayi niyyar barinka...mijina sam ban san ya akayi na amshi tayin hatsabibiyar matar nan ba, a lokacin da muka zo gaisuwar Alhaji d'anqasa idan baka manta ba muna zaune aka kira ni a waya na fita dan ansa wa, baquwar murya ce ke sanar min na yar da passport d'ina a hanya kuma wai gata a location d'ina na fito qofar gidan Alhaji ibrahim d'an'kasa, ba tare da tunanin komai ba nayi yacce tace d'in, tun kallo d'aya da nayi mata naji gabana ya fad'i haka kuma naji bazan ta'ba iya musa mata duk abinda ta umarce ni da nayi ba, tun dga wannan ranar duk wani moves d'inka ina sanar mata, dan Allah ina roqonka da ka gafarce ni, ku gafarce ni nayi hakan ne ba a cikin hayyaci na ba"
Tsam barrister ya miqe bayan ya bata baby shi kuma ya fita waje,
Jamilu mainasara yayi 'kwafa,
"Uhm kun ji ba?, yanzu me zaki ce akan wannan, kunsan Allah kada ku yarda dad'in bakinta yasa ku tausaya mata" ya waiwayo gare ta "..ko tunzurarren mahaukaci da yake mara lafiya baze ta'ba aiwatar da jahilcin kika yi ba!"
Amshewa hajiya maryam tayi da cewa "Na rantse da wanda raina yake hannunsa asiri ne yake juya ni, dan sam qin aminta nayi da tazo min da shawarar a tunanina duk inda akaje aka zo su hajjo jinina ne..."
Cikin gajiyayyiyar murya mariya tace "...idan har abinda kika fad'a ya kai zuciyarki to menayi miki da kika illata
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 13