Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
abinci bansan gulma" Ta bud'e fuska tana dariya tare da miqewa tace "Ammi me muka samu" "Abinda kika ce d'ana na kwad'ayi" "Cowleg" ta furta ido waje har da d'an tsallenta ta mara mata baya. *** Tun da yayi sallar asubahi ya nufi cafe din cikin hotel d'in cikin qoqarin tura saqo ta yanar gizo wato mail amma firr yaqi tafiya, wayar hashim ya kira bugun farko kuwa ya d'aga "Duk wani d'an iska ya biyo bayanka" "Tun da ka same ni a tsakiyar 'yan kan titi ba" ya bashi amsa, dariya hashim yayi suka gaisa cike da annashuwa yana tambayar jikinsa, Yace "Ya akayi kasan nine" "A halin da ake ciki yanzu duk baquwar number", Girgiza kai yayi yace "doctor wani taimako nake so kayi min" "Me kake so dani?" "Zan turo maka saqo ta mail da inda zaka tura min yanzu pls" "That is only if you tell me your whereabouts?" Gashin kansa ya shafo had'e da murza goshinsa yace "sai ka jini" ya katse wayar cike da tunaninka, ya san hashim for a lifetime, baze ta'ba barin ko quda ya cutar dashi ba se de a yanayin da ake ciki yanzu idan aka cire Ammi da bello bayajin akwai wanda ze yarda dashi. Qarar da wayarsa tayi yasa shi dawowa daga duniyar tunanin daya fad'a _Reply "done" from doctor_ Murmusawa yayi, ya tashi ya shiga restaurants d'in kusa dashi ya kar'bo breakfast d'in da yayi musu order, knocking yayi bisa door, "Waye" munu ta tambaya Cike da jin dad'in yacce ta tambayar yace"nine" bud'ewa tayi fuskarta d'auke da fara'a "ina kwana Bro A" "Lafiya" yace tare da handing mata leather bag d'in ya juya, har yayi taku biyu ya juyo zata rufe yace "wait, ina d'ayar take?" "Sallah take" tace a duburburce, gyad'a kai yayi badan ya yarda ba ta kuma cewa "sallar walaha" "Uhumm" kawai yace tare da d'aga girar sama ya tafi. Rufe qofar tayi tana me hamdala da be gano taba, ta ajiye ledar bisa table cikin d'aga murya tace "se ki fito dodon naki ya tafi" Sam dake bayan curtains ta fito hannu a saman qirji tana maida numfashi tamkar wacce tayi tsere "Ke lafiyarki" munu ta tambayeta "Baki ga abinda ya faru bane??" Munu ta kyabe baki tana fad'in "eh naga de kin 'buya bayan curtains sbda kar bro A ya ganki... sbda yana cinye mutane..ko?" Guntun tsuka tayi "ke dalla nifa tsoron wannan manyan idanun nasa nake bawai...." Dariya munu tayi "ke da shi maga wanda yafi wani ido" Turo baki tayi "tabb wlh gara nawa kina ganin nashi kamar na mujiya gashi yayi ta wani lumshe su kamar me jin bacci" "Ehhh lallai har kin manta warning d'in daya kafa miki jiya ko, maza ya jiki, ni dai taho muci abinci dan yinwa nake ji" Dad'a cuno bakin tayi ba tare da tace komai ba ta hau bud'e pack din abincin. Anwar da ke tsaye jikin qofar ya ji duk dramer da suke ya girgiza kai wato 'buyar mishi tayi, sbda idanunsa irin na mujiya ko? Zaki sani ne ya furta a fili. 3 weeks later Dawowar Ammi kenan daga raka mom hajar airport ko parking mota batayi ba wayar ta ta shiga qara alamun kira, d'agawa tayi had'e da yin sallama, aka ansa "Ann! Kaine? Inaka shiga hakane na dena samunka " tace a rikice "Ammi na lafiya ta qalau, inason fad'a miki ne ma in 3 days time zaki ganni, idan nazo zan fad'a miki duk abinda kike son ji, we wil talk later i love you" Tun kan ta samu sukunin amsa shi ya katse wayar se qarar message taji _reply "ammi kar ki sanar da kowa ina hanya, ki d'auki kayanki kije quarters d'in AB machinery zan same ki a can. Take care_ Tunani kala kala ta tsinci kanta dayi se de ta barwa kanta cewa anything has a reason baze ta'ba yin abu haka kurum ba. Ranar wata laraba misalin 3:30pm tayi musu cikin tafkeken kamfanin AB machinery ginin da idan ka shige shi zaka zata sace ka akayi, katangar sa kad'ai abar kallo ce me tsayin gaske ce ainun, ko ina cikin wurin zagaye yake da qayatattun flowers masu fidda qamshin dad'i ko ina ka kalla mutane ne birjik sanye da kaya kala d'aya wato blue colur daga bayan su tamfkeken A da B ne a had'e, duk inda motar da suke ciki ta wuce se kaga ana tafi fuskokin mutanen da kallo d'aya zakayi musu kasan turawa ne manne da murmushi wasu kuma dariya kai kan gani kasan farinciki suke, Maida idonta tayi inda yake tare da waro ido waje, dama yana fara'a haka? Hannu tasa ta dad'a murza ido wai kode mafarki take ganin tabbas d'in hakane yasa ta kuma leqawa ta kusurwar kujera inda har ta iya hango lotsawar man pride d'insa, Iska ce me d'umi ta doki spot d'in wuyansa har besan lokacin daya lumshe ido ya bud'e a hankali ba, jin abin na neman kashe masa ga'bo'bin jiki yasa shi waigowa a hankali sede tsayawar da motar tayi yayi daidai da komawar ta jikin window dan qarasa kashe kwarkwatar idonta "Sir mun qaraso" maganar driver ya d'au hankalinsa, daidai lokacin da yake shaqar wani ni'imtaccen qamshi, umartar sa yayi daya shigo da kayan shi kuma ya sauka ya tafi, ganin haka ta bud'e qofa tare da kamo hannun munu suka fito duk da son kalle kallen su basu samu daman yin hakan ba gudun kada ya 'bacewa ganinsu Gaban wata tafkekiyar wooden door suka tarar dashi tsaye yana danna door bell, wata baqar fata ce ta bud'e qofar tare da rissinawa "Welcome back sir" Be amsa ta ba ya wuce bayan tayi gaggawar kaucewa, suma suka bi bayan nashi tamkar jela, "Ammi na" ya furta cikin d'aga murya a lokacin daya dudduba d'akunan gidan Cikin gigin bacci ta daddafa ta fito, sama ta nufa kasancewar tana underground apartment, kiran sunanta da ya kuma yi ne yasa ta yin saurin haura benan "Ann my son" ta furta in a shaky voice wanda tuni hawaye suka hau ziraro mata, waigowar da zeyi ya hango ta tsaye da sauri ya isa gareta ya rungumeta dan yayi kewar Ammin nasa sosai "Ammi na" ya furta a hankali, sun jima a haka kan munu tayi gyaran murya game da fad'in "ina wuni", share hawayen tayi da hannu ta d'ago kai a hankali, ta amsa musu tare da qare musu kallo A nutse ta tako zuwa inda suke tana me dad'a fad'ad'a fara'arta tasa hannayenta ta shafo kawunan su dake sakaye cikin hijabi tace "sannun ku da zuwa yara na" hannu tasa ta d'ago ha'bar Sam tana kallon cikin qwayar idanunta, a hankali tace "Samira" Game da fashewa da kuka me tsanani wanda ya rud'asu duka, "Ammi ammi na lafiya me ya faru" Ita kuwa samira baya tayi had'e da sakin kuka wurjanjan, munu ta shiga bata baki yayin da Anwar ke lalla'ba mahaifiyarsa Hajjo wato Ammi ta d'ago tare da janyo samira ta rungume, idonta cikin na Anwar take cewa "She's her mothers child, she looks exactly like her, she's mariya's photocopy" ta qarashe maganar cikin hawaye had'e da fara'a "K..in..sa..n mummy na?" Lumshe ido Ammi tayi "'yar uwa tace ta jini.." *** A can gida nigeria kuwa uncle ya rasa gane kan bro B, gashi baya barin d'akinsa a bud'e , motar sa kuwa ta jima da barin gidan, kamar ko yaushe dawowarsa daga office kenan ya tararda gwaggo zaune a falo tana kallon labarai "A a barrister kaine haka da rana tsaka" "Wullahi fa yau Alhamdulillh aikin namu da sauqi" ya zauna saman kujera suka gaisa tace, " to madalla sannu bari na samo maka ruwa kan a qarasa abincin yau munyi ranar abinci" "Ai barshi gwaggo nagode, yanzu wani abokina da matarsa suka matsa seda naci a gidan su" "Ai kuwa yau abincin ka tayi tuwo da miyar agushi me tantaqwashi" "Atoh a ajiye min da dare ta dumama zanci" Hanyar kitchen ta nufa, "to bari na shaida mata kuwa" shi kuma ya haye sama. *** Tsaye yake bayan wata takekiyar daf dake ajiye gefen titi, seda ya gama qarewa samarin kallon tsaf kan ya danna Bluetooth dake maqale cikin kunnen sa, "na gama survey d'in" Daga can akace "Bello mutanen nan na da mutuqar hatsari, lallai ka kula" "Doctor insha'Allah zan kula, go and pamper Rayya not me" Daga ciki yana iya jiyo sautin murmushinsa, "to naji, ka gyara settings d'in glasses d'in?" "Eh" "Then you are good to go, take care" Kai ya d'aga, kan ya tsallaka titin zuwa gurin samarin dake zaune saman dakali. ©️Kdeey😊 DABAIBAYI 👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊 ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (22) Barka yace dasu game da d'aga musu hannu, kallons sukayi duka a kaikice cike da mamakin qarfin gwiwa irin tashi kul da yanda kowa ke shayin zuwa kusa dasu Cikin kakkausar murya d'ay cikinsu wato oga Nafi'u yace "kai yane?", shafa kansa yayi had'e da kunna Bluetooth dake maqale cikin kunnensa ta yacce ze iya jin maganar da dr ke mishi, Ya kada baki yace, "ahh sannunku fa, sunana buhari me dabaibayi nazo bautar qasa ne nan makarantar gomnati" "To se aka yi yaya.." cewar wani cikin zafin rai, hannu oga nafi'u ya d'aga masa, idonshi saman na bello "se aka yaya d'an bautar qasa" "Ina so ne idan babu damuwa nake zama cikin ku idan ina gida" Kallon juna sukayi, can d'ayan yace " me ze hana, sede idan ka yarda amma za mu rinqa qaruwa da kai ta wani fannin ko ya" Kai ya gyad'a "well inhar wannan ne me sauqi ne ai ina d kayan abinci, kayan kallo impact wancan shagon jikin makarantar can nawa ne" Nan d'ayannan daya d'au zafi ya washe baki da cewa "kai wancan kwftareren shagon, ah lallai mun samu mafaka, ni sunana rody" Ni kuma "aqilu" Cikin fara'a d'ayan yace "barka ni sunana salihu" Jinjina kai yayi, "da fatan zaku riqe ni da hannu biyu ku bani dukkan amanar ku" Dariya suka kwashe da ita tun qarfi kan wanda aka kira da salihu ya dafa kafad'arshi yace "zo muje abokina" Ba tare da wani tunani ba ya mara masa baya,suka nufi wani layi, "ina zamuje haka" "Gidan mu, inaso na nuna wa baba ta yau na samu kalar abokin da take fatan nake huld'a dasu" _kar ka bishi_ daga cikin Bluetooth doctor ya nemi dakatar dashi, gyaran murya yayi a wayance kan yace "salihu bari naje masallaci wani lokaci maje na gaishesu" 'Dan jimm yayi alamun beji dad'i ba, yace "shikenan ni bari na watso ruwa se mu had'u a can shagon" jinjina kai yayi ya juya ya nufi masallaci, Bayan an idar da sallah yace da salihu ya jira bari ya zaga band'aki, bayan wani incompleted building ya fake tare da danna wabi button jikin glasses dinsa wanda duk qura idonka baka isa ka gane akwai shi, fuskar hasheem t bayyana ta ciki, "Buhari me dabaibayi" ya bushe da dariya, dariyar shima yayi, "kayi scanning fuskokin su?" "Eh, gashinan computer na neman su" "Aha, bari naje" "Okay I'll keep you updated" Direct d'akinsa suka wuce daidai qofar shiga suka had'u dasu, oga nafi'u yace "abokin zamu fita aiki da Allah kad'an sama mana me maiqo odan mun dawo akwai naka kason" Rody yace "ahh oga kace yau akwai zuwa duniyar sama" "Wajibul manzil aboki naa" cewar aqilu cikin muryarsa ta riqeqqen d'an daba, gira ya d'aga da cewa dafatan ba zaku wuce goman dare ba dan ina kwanciya da wuri sboda zuwa aiki" Girgiza kai oga nafi'u yayi had'e da jinjina masa yace "se mun dawo" suka juya a tare, salihu dake baya ya d'ago masa hannu tare da sakar masa murmushi me kama da yaqe jiki a sanyaye, numfashi ya sauke bayan ya rufe qofar da key ya fad'a saman tamusashshiyar katifar dake qasan d'akin yana kuma qarewa shagon kallo game da jinjina kai yana mamakin ta yanda ake mutane ke iya rayuwa a irin wannan area, Seda ya tabbatar sunyi nisa da anguwar ya fito, ta wata boyeyyiyar hanya yabi dan zuwa gida can ya jangi driver zaune cikin mota ya shiga suka tafi yana shiga ya ciccire kayan jikinsa had'e da qullewa cikin leda, ya kishingid'a jikin leather seat tunanin Sam ya maye gurbin tunaninsa. *** Hawaye yaci gaba da zuba a idon Ammi yayin d take rungume da Sam a qirjinta, d'ayan hannunta kuma cikin na Anwar, saman kujera ta zauna tare da kuma kwanto da Sam kan cinyarta, shiru tayi kan ta fara magana da cewa " Alhaji muhammadu ningi shine sunan mahaifin mu ni da qanwata mariya tun ina shekara sha hud'u mariya na sha biyu mahaifiyarmu umma indo Allah yayi mata rasuwa hakan yasa jama'a matsantawa mahaifinmu qarin aure har yakai aka had'ashi da yarinyar kawunsa a cewarsu baze yiwu ya zauna hakanan da yara mata ba, Ina da kusanci sosai da mariya dan ta d'aukeni ne tamkar umma komai se ta tambaye ni ta keyi har wata ran hakan ke 'bata ran y Umma ramatu wato matar mahaifin mu, kula da hakan yasa nake takatsantsan, umma ramatu irin mutanen nan ne masu nunawa duniya tamkar su had'iye ka dan so a baya kuma sunfi kowa qinka , sauqin abun d'aya umma ramatu bata fiye zaman gida ba dan se yamma liqis take dawowa daga office inda take aiki a office d'in matar mataimakin governor, A shekarar dana gama secondary d'an abokin mahaifina ya ganni yace yana so, ba a d'au wani lokaci ba aka aurar dani gareshi ba tare da an duba wai ya kusan haihuwata ba duk da umma ramatu taso cusa wa babanmu ra'ayin hakan 'yan uwansa suka qi kuma Alhamdulillah naci ribar hakan duk da Allah da ya fini sonshi ya kar'bi abinshi se ya barni da gwarazan mazan da zasu sharen hawaye na, (ta shafo sumar Anwar) Mariya tayi aure a lokacin bello yana da shekara sha biyu a duniya, lokacin Alhaji amin alfalla ya zama Ambassador of nigeria to turkey dan gaba d'aya can muka koma da zama yayin da yara n kawo su nan garin karatu. Akwai wata rana da bazan manta ba mariya nada shekari goma da aure ta kira ni da daddare take shaida min gobe zataje ningi kamar yacce ta saba tana kai sadakar abinci da suturu ga mabuqata amma tanaji tamkar kada taje, meyasa na tambayeta, tace wullahi yaya inaji tamkar zanyi wani nisan zango ne, dariya nayi mata dan a tunani na shirmenta ne kurum, na kuma ce kada ta sake ta fasa zuwan, to dama gskya tun aurenta nada watanni ta fara fuskantar qalubale daga dangin mijinta har takai wani lokacin ta nemi tahowa turkey na bata baki, Barrister usman kuwa qanin mijina ne ubansu d'aya, nice na had'asu da maiqasa ganin yana neman lawyer da ze danqawa amanar wills d'inshi, Ranar da mariya ta 'bace a ranar na dira a nigeria dan duba mahaifina Allah barshi n qarasa kano na duba qanwata se mugun labari ya riske ni, gidan da ban samu zuw kenan ba na tafi kano, tun muna saka ran Allah ze bayyana ta har kwanaki suka shura aka tafi wata uku, Labarin rashin lafiyar me gidana yasa ni koma wa turkey inda isata asibiti keda wuya na tarar da gawar mijina wanda akayi poisoning a abinci, ranar nayi kuka tamkar zan mutu har ta kaini ga kwanciya a asibitin tsawon wata guda Duk abinnan dake faruwa ban yarda an sanar wa da yara ba, ni da kaina dana samu lafiya na tattara komai nawa na komo nan se da na tabbatar sunzo gurina hutu na fad'a musu zancen da har yau idan na tuna nake jin ba dad'i dan ni da kaina nasan ban kyauta musu ba ko ba komai zasu so ganin gawar mahaifin su. (Nan ma girgiza mata kai Anwar yayi tare da sa hannu ya share mata hawaye) Wannan shine gskyar labarin mu ni da 'yar uwata mariya, rasuwar mahaifinki kuwa barrister ne firr ya hanani zuwa, wanda bana ce ga dalilin hakan ba se de abinda na sani baze ta'ba yin abin da yasan be kamace ni ba" _kuyi manage da wannan insha'Allah zuwa anjima zaku sake jina_ son so🥰 ©️Kdeey😊 DABAIBAYI 👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊 ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (23) _this whole page is for you my wattpadians_ 💖 _jiddatul khair😍 thanks for your immense support_ 😘 ✨ ..hannu tasa ta share hawayen dake fita a idon sam ta d'ora da cewa "samira yanzu da Allah ya kawo ki garemu bazan kuma yarda ki bar ni ba, kece zaki maye min gurbin 'yaruwa ta a fuskarki zan rinqa ganin mariya ta, taja hanci tare da kamo hannun Anwar, insha'Allah bazaki kuma shedding tears ba while we are alive, Anwar is your brother and bello ma haka wic is younger to Anwar, Sam i never thought kece wacce suke kulawa da ita, but daga yanda naji labarin ki a bakin barrister yasa ni tausaya miki na kuma sa yarana lallai su taya uncle d'insu fighting dan wannan case d'in is not just for his carrier is a big goal in his own life and theirs, Ta kalli Anwar kan a kuma maida idonta kan Sam, "kiyi hakuri da maganganu na, na sani sunyi miki tsauri da nauyi a yanayin shekarun ki, but i know my baby has a deep understanding, kar ki ta'ba bari wani abu daga maganata ya ta'ba ki, kada ki damu kwatakwata i'm with you, your brothers are, uhm?" Ta qarashe da sigar tambaya, Jijjiga kai Sam tayi tare da dad'a ruqunqume Ammi cikin sanyin muryar kuka tace "i'm so happy Ammi, yau is one of the best days in my whole life, yanzu saura abu biyu buri na ya cika" "Abu biyu" suka kalli juna Ammi da Anwar Jinjina kai tayi "na farko Ammi inason mummy na ta dawo gare ni cox inaji a jiki na she's alive somewhere else in the world, na biyu kuma akwai haske na da nake kwana ina tashi dashi cikin zuciya ta, kullum daddy used to tell me kada na bari yayi nisa da ni" "What is that?" Ammi ta tambaya cikin bata hankalinta baki d'aya, "i don't know, since when daddy passed away na kasance cikin mafarki..." nan ta kwashe labarin tsaf ta basu cikin zubar hawaye, "Shushh...insha'Allah hasken nan naki ze bayyana gareki soon, ki kwantar da hankalin ki kinji,.." ta dad'a janta jikinta tana rarrashinta, Gyaran muryar da yay ne yasa su d'agowa cikin ciccin magani yace "Ammi bafa ita kad'aice a gabanki ba, gani ga munubiya but duk kinyi focusing kanta, how ridiculous" Hararar wasa Ammi ta mishi jin yana nuna kishinsa a fili, munu dake gefe tad'an dara a hankali kan ta kada baki tace "bro A are you jealous" Saurin shan mur yayi " am whaaat? N..no never da wannan yarinyar, malama tashi jikinta kuje kuyi sallah kuyi wanka se ku fito" Dariya reaction d'insa ya basu, Ammi ta d'ago kanta with a smile on her face tace "maza kuje wancan way d'in there is a room by your right hand side nan ne masaukin ku," tayi pecking forehead d'inta, "Ammi.." yace cikin ciccije lips, murmusawa sukayi duka sannan suka wuce yayin da shi kuma ya maye gurbinta, "ah ah kai ba masallaci zaka wuce bane" Tashi yayi "inason naji d'umin Ammina tukunna" Karan hancinsa taja, "bazaka ta'ba girma ba" "Not until i give you grandchildren" yayi winking eyes d'insa kan ya fita a guje, dariya tayi ta juya bedroom itama cike da farin ciki, bayan ta leqa kitchen ta shaida wa cook ya maza ya shirya table for four. Lokacin dinner Ammi ke tambayar sa school din da ze kaisu nan ya sanar mata boarding school ze kaisu kuma gobe, fork and table knife dake hannunta ta ajiye "Why boarding school?" Se da ya sauke numfashi, ya saci kallon su duk sun tsura masa ido yace "ku tashi ku bamu wuri" bayan sun tafi tace "Ann meke faruwa ne? Ko uncle ne yace kayi hakan?" Girgiza kai yay, cikin rawar murya yace "Ammi i'm afraid dont know who to trust" nan ya kwashe duk abinda ke faruwa kama da wannan motar dake kawo musu ziyara and basu san ko wane daga cikin gidan nasu ke huld'a dasu ba har zuwa neman halaka su da akayi, ya d'ora da cewa "na sani uncle will never do such thing but canjin makaranta daga wacce uncle yasa na kaisu d'in is the only way for their safety, na riga da nayi wa miss chloe magana kuma mun gama komai gobe zan kai su, in 2years time they will be graduates" yayi winking eyes d'insa tare da miqewa dan barin wurin Ammi da jikinta ke a mace dan sosai maganar tasa ta firgitar da ita, taja salati had'e da girgiza kai tace "yanzu cikin wannan yanayin kabaro min bello" Tsayawa yayi tare da waiwayo wa, "kar ki damu na bawa gwaggon munubiya amanar shi, she will look after him, hasheem too is with him all the time, and akwai SS kewaye da gidan, duk moves d'in kowa za a ke sanar dani, bara nayi sallah nazo yau kusa da Ammi na zan kwana" yace had'e da daga gira yana mata warm smile ya fice, Numfashi ta sauke tare da saurin maida hawayen dake qoqarin zubo mata, wannan wace irin rayuwa ce cike da qalubale who want to brings them them down, shin meye ribar ruguza farincikin marayun Allah, da wannan tunani Ammi ta qarasa d'akinta ta tada sallar magriba, A ranar kusan kwana sukayi hira ita da anwar dan tun 8 ya kora Sam da munu d'aki da cewar kada su kasa tashi gobe da safe, a zuciyarsa kuwa har da kishin yacce Ammi ke bawa Sam kulawa sama dashi😆. Washegari Tun 6 suka hallara saman table sede har yanzu basu fara cin breakfast ba sanadiyyar al'adar su ce sai kowa yazo ake fara cin abinci, hakan ya faru ne ta dalilin Sam da bata fito ba, "Anya kuwa Samira lafiya tun d'azu da kika kira ta tace gatanan amma shiru" Munu tace "Ammi haka take bata son cin abinci ko a gida haka gwaggo ke fama da ita" "To Ammi lets just start kafin tazo before na fad'i muku anan" ya qarashe had'e da turo baki, "Je ka kira ta" tace dashi "Me.." ya nuna kanshi da yatsa, ganin kallon da tayi mishi yasa shi miqewa ya nufi downstairs cike da qafuluwa ya shiga knocking bisa door, qofar ce ta bud'e alamun ba'a rufe take ba ya taka cikin d'akin daddad'an qamshi ne ya bigi hancinsa har be san sa'ilin da ya lumshe ido ba, d'akin neat yake tamkar ba'a ta'ba kwana cikin sa ba, tsintar kansa yayi da qarema d'akin kallo, numfashi ya sauke game da juyawa ze fita idonsa ya sauka bisa curtains da yaga suna motsi maida idonsa yayi view d'in d'akin ko alama be hango flowers na motsi ba bare yace iska ake, idonsa da sukayi qasa yasa shi gano sam'baleliyar farar qafa me d'auke da zara zaran fararen yatsu se mutsu mutsu suke, murmushi yayi me sauti ganin yacce take d'age qafafu ita a dole bata so a ganta, "Yaro yaro ne" ya furta a hankali, takawa yayi har gabanta yasa hannu ya yaye curtains d'in, tun daga idonta dake runtse ya shiga qare mata kallo zuwa kyakkyawar fuskarta dake sakaye da baqar talha zuwa shining pink lips d'inta ya gangaro saman qirjinta da tsabar bugu da yake har sama da qasa yake yi, wanda ya bada qaimi wajen tona albarkatun qirjinta da suka d'an girma, riga ce fara qarama daga ciki wacce tayi fitting dinta ainun akayi stalking cikin baqin wandon palazo, sosai shigar tayi mata kyau dan duk da girman wandon seda ya tona asirin dirin da Allah yayi mata, Ga sassanyan qamshin dake tashi cikin jikinta me d'ankaran dad'i wanda bawai turare bane kad'ai sabulu ne da toners masu d'ankaren tsada, lumshe ido yayi ya kuma bud'e saman fuskar tata wanda yayi daidai da bud'e idonta Cikin rawar murya take furta "ni banson zuwa boarding school,..." "Meyasa?" Ya tsinci kanshi da tambayar ta, idanunsa stick to her lips dake motsawa a hankali, "Banson na bar kusa da Ammi.." "She's mine Sssamm" ya qarashe da in-ina, "Nima ai tawa...cc.." Be bata damar qarasa maganar ba, cikin zare ido da qoqarin qwatar kanta ta shiga dukan qirjinshi tun qarfi, tsawon wasu sa'oi har ta fara yin laushi, oga Anwar kuwa hannu yasa had'e da tallafota jikin shi yana sakin numfarfashi

Chapter 7 of 13