stand for yourself kinga fa ya habibii is so mean”
“Don’t worry mubi May be bayason zamana gidansu ne, afterall nan da kwanaki kad’an ze tafi, and I will be back to my normal self “
“Uhm, zo muje muyi game”
“Wanne?”
“X and O”
Da fara’a ta girgiza kai suka nufi d’aki
****
*Birmingham, London UK*
Tsananin azaba da hucin sanyi yasa kowa ka gani sanye yake da cardigan babba da hular kai har dasu safar hannu dana ‘kafa, hakan take ga magidancin dake driving motor d’insa yana kuma ansa kira at thesame time
Daga can ‘bangaren aka ce “uncle please kataimaka min na dawo ko da na wata d’aya ne AB machinaries need me, kaga nan tunda bro B yana nan....”
Tun kan ya kai aya ya katse shi “hey mr Man oh let me call you with your name, Anwar bana san kame kame ka zama babban kwabo kenan tunda har ‘kaninka ze iya abu amma kai baza kayi ba, wannan ne taimakon da kake ta ikirarin zaka yi? Ko kuwa ka manta al’kawarin da kayi na DABAIBAYAR al’amuran nan, ka manta da Ammin ka...”
“Uncle na kasa samun nutsuwata I don’t know what to do, amma Insha’Allah ko dan al’kawarin da na d’auka sai na cimma burina ko da zai zama aikina na ‘karshe a doron ‘kasa, but before that uncle inason hutawa inason ganin ammi na i missed her...”
“...and AB machinaries ko?, kai wannan yaron da ace ba a nigeria aka haife ka ba da bansan yanda zakayi ba, zaka zo hutu amma na 2weeks kawai ka tattara komai ka barshi a hannun qaninka”
“Yesss that’s my super uncle, I love you muah” ya manna wa wayar kiss ya shige gida.
©️Kdeey😊
DABAIBAYI👄
©️Khadija Ahmad (Kdeey😊)
®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)
(5)
Bayan wasu kwanaki...
Firgigit ta tashi jin yadda ake buga ‘kofar d’akinta kamar za’a ‘balle, a iya ‘kiyasinta yanzu sha biyun dare ta wuce tabbacin kowa na gidan ya jima da kwanciya to wane haka? Ko de horror ne yazo cinye ni tunanin daya kuma rud’ata kenan har takai ga zubda hawaye jiki na makyarkyata, can ‘kuryar gado ta ma’kure kanta kira take
“Daddy...wayyo umma na...um...” kan ta’karasa aka banko ‘kofar tun ‘karfi wanda yayi daidai da d’aukewar numfashin ta.
Washegari
Kwala mata kira ta ke tun ‘karfi amma shiru kakeji wai malam yaci shirwa, “kai yarinyar nan kuwa Anya lafiya?
Baffa ya sauke jaridar dake hannunsa yace “kinsan fa yau saturday qila bata farka ba”
“Haba Abban yara sha d’aya fa ta gota ri’ke min yarinyar nan kaga bara na dubo ta”
Fad’owa yayi d’akin kamar wanda aka wurgo kallon sama da ‘kasa ta masa
“Kai lafiya naganka a firgice?”
Sana’ar tasa yayi ta susar kai yace “ko d’aya uwarmu kawai de...”
“Kawai de me?, kai gafara da Allah naje gun d’iyata” fuu ta wuce sa, fuska a cakud’e ya isa gaban Abba ya zauna yana faman kukkumbura “ya dai yayana?”
“Abba wai meyasa umma kullum take son min fad’a ni idan batason ganina ne ba se nayi komawa ta ba”
Murmushinsu irin na manya yayi kan ya Kada baki yace “yayana kenan ka ta’bajin inda uwa ta guji d’anta?...”
“To amma Abba baka ganin kullum kullum...”
“Kayi haquri kasan umman taku gidan gargajiya ta taso har da kunya irin ta d’an fari yasa take maka haka bawai intentionaly bane,um?”
“Abba shekarar ta nawa a birni nazata duk qauyencin mutum idan ya shekara arba’in ze dena amma...”
A tsawace Abba yace “kai da Allah can banson sakarci mahaifiyar taka kake fad’ar haka a kanta, To lallai yau na kuma tabbatar da kanka yana da matsala dole mahaifiyarka take complain a kanka tashi ka bani wuri” ya ja tsaki rai a ‘bace, cikin tafiyar bouncing ya nufi hanyar waje
“Ka kintsa dan jirgin ‘karfi biyar zaku bi”
Wani qululu ya tokare mishi wuya a zuciye ya nufi waje dede lokacin da ihun umma Salamatu ya iske kunnansu
A kusan tare suka fad’a d’akin, Amir ya tsugunna gabanta yana jijjiga ta “Sam Sam ki tashi! Sam wake up please”
Umma salamatu dake a firgice ta nufi kawu “Abban yara Sam..Sam bata motsi” rasa abinyi yay kawai ya ciro hular kansa yana firfitu dan duk da AC dake d’akin d’igar gumi yake.
Amir ne ya shiga girgiza sa “Abba muje hospital, Abba banson wani abu ya samu Sam”
Aljihu ya shiga laluba fad’i yake “ina kake ina na ajiye “ ya d’ago kai yana kallon habibii “kai maza d’auko key “ ya cicci’be ta suka nufi parking lots inns salamatu na sa’be da safiyya kafad’a .
*one hour later*
Likita ya kalli Alhaji kabiru a fusace “malam anya kuwa yarinyar nan ‘yar kace kamar yanda ka fad’a yarinya qarama ace tana d’auke da hawan jini?”
Murya na rawa umma salamatu tace “Ha..w..an jini likita?” Tare da dafe qirji
“Kwarai kuwa hajiya, am sorry to say amma a gaskiya ku kiyaye dan bugun zuciyarta am ba daidai yake ba, ko zaku iya tuna wani abu daya faru da ita jiyan?”
Umma tace “umm to gskya bama ce ba dan lafiya qalau muka rabu da ita ta shige d’aki ta kwanta”
“Basu samu matsala ba, kuma ba wanda sukayi fad’a dashi cikin yara” ya nuna su Ameer da ya hannu, habibii kuma se dad’a had’e rai yake, umma ya kaikace tana duban sashen habibii
“Umma” ameer ya furta yana kallonta yana girgiza kai ta juya gun doctor “babu”
“Well To gskya de zan baku shawara ku rinqa bincikar a wani hali ‘yarku take ciki dan tabbas firgici ne yasata a wannan halin and again zan riqeta ta kwana biyu zuwa ta warware,
“To bari muje mu dawo Ameer Kai se ka....”
“Amm hajiya karki damu kanki, anan asibitin mutanen waje basa jinya munada wadatattun ma’aikatan da zasu kula da ita”,
“Amma ta yaya...”
Yana sakin murmushi yace “karki damu she’s safe with us”
Kallon kawu tayi ya girgiza mata kai tace “To shikenan ma iya ganinta kan mu tafi”
“Sure! Munirat munirat “
Wata matashiyar nurse ta shigo da sauri ya nunata “wannan ce zata zauna muku da ita zuwa lokacin da zata dawo daidai, ya kalleta take them to room no.18 VIP,
“Yes sir” ya furta ta na me russunawa
Kan tayi gaba su mara mata baya.
Daidai shiga d’akin wasu matasan maza biyu suka fito daga ciki kasancewar bayan su a juye yasa Amir saurin cewa “who are those guys??”
Nurse munirat tace “am.. ss..tudent ne suna bin rooms dan duba patient”
“Students a private hospital?” Cewar habibii
Duburburcewa tayi “am..a..”
“Haba mana habibii kar ka rud’ata mana ba kaji me tace bane d’aliban lafiya ne, muje da Allah, kuyi tafiyar ku” ta qarashe zancen idonta a bayan matasan, gaba sukayi batare dako waiwaye ba.
Kafad’a habibii ya d’aga irin ko a jikina, yayinda Amir ya riga kowa shigewa d’akin
Kwance take sam’bal saman gado doguwar rigar baccin mark&spencer kalar pink tabi jikin nan ta lafe har kana iya gano ‘yan qananun boobs d’inta, gashinta dake barbaje saman pillow nurse munirat tabi ta kame gu d’aya tare da Jan farin quilt ya sakaya mata jiki, fuskar nan tayi kuyat takoma pink zirr abinka da farin mutum idanta dake luhu luhu har yanzu da d’igo d’igon busassun hawaye
Hannunta d’aya an ma’kala drip yayin da d’ayan hannun ke manne cikin na Amir
“Allah ya baki lafiya, Sam”
“Amen, nifa Abban yara abin nan ya d’aure min kai shin me ya razana Sam har ya shiga wannan halin”
“Ko dai mugun mafarkai take umma”
“Banajin Amir, na fi ta’allaqa abin ga d’an uwanka Anya habibii ba kaine ka jef...”
“Haba umman su, fisabilillahi ya kamata ki kawo maganar nan a nan, kai ku tashi mu tafi ma”
“Abban yar...”
“Kinga tashi muje kinsan halin da take ciki yanzu bata son hayaniya”
Mi’kewa tayi tana fad’in “uhm yaushe ka zama likita kuma bansani ba?”
Bece uffan ba ya nufi ‘kofa, yayin da umma ta matsa bakin gadon ta shafo sumar Sam, “Allah ya tashi kafad’unki” saman goshi ta sumbace ta, safiyya dake hannunta ta rinqa zillo tana son sauka gurin Sam.
Nurse munirat dake gefe tsaye tace “hold on beauty yayarki bata da lafiya”
Umma tayi dariya “ai akwai shaquwa tsakaninsu, nurse ga ‘yata nan a kula min da ita sosai dan Allah I can even give you some extra cash”
“Kai haba hajiya bakomai ai aikinmu ne kuma ana biyanmu isassun albashi. Nagode”
“Shikenan ya amanarta nan” ta fita
Nurse munirat ta kalli gadon a fili ta furta “yacce kike me kyau am very sure haka zuciyar ki take”
“Stop admiring her and do your work,”
Saurin sunkuyar da kai tayi tana Sosa gefen wuya “am sorry sir” tayi saurin bi ta gefenshi ta fice, daidai lokacin akayi knocking bisa ‘kofar
“Yes come in”
“‘Daliban lafiya” ya furta cikin dariya
Kanne masa ido babban yayi, suka tafa da likitan
“Maza how far now? Kun ganta ba?”
“Yeah...”
“Ah ah fa Bro A wancan mutanen basu bari mun ganta sosai ba..”
“Ha’a to gatanan ai se kaci gaba, doctor let’s go, meet me down there idan ka gama scanning d’in” ya furta cikin wata deep voice, suka fice
Wanda aka kira da Bro B ya maida hankalin sa kan wayarsa dake hahhaska Sam tamkar me yin video, daya gama ya mayar aljihu ya Mara musu baya.
Fitowa tayi daga inda take la’be tana tapping gefen bakinta da manuniya tana jinjina kai cike da tunani
©️Kdeey😊
DABAIBAYI👄
©️Khadija Ahmad (Kdeey😊)
®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)
(6)
Tayi saurin juyawa ta koma office d’inta,
GET WELL HOSPITAL, asibiti ne da babban d’an kasuwa Alhaji Ammani ya ginawa babban d’ansa Hasheem bayan dawowar sa daga UK inda ya karanci gynecology wato likitan mata, asibitin be tsaya anan kad’ai ba akwai ‘kwararrun likitoci daga ‘bangarori da dama dake aiki cinkinsa tsaftataccen asibiti ne wanda ya gaji da had’uwa ta fannoni da dama kama ga ma’aikatan kiwon lafiyar, masu gyare gyare, wadatattun magunguna da dai sauran su
Saboda sau’kin da asibitin ke da shi da kuma kwararrun likitoci ga kyakkyawar kulawa da ake baiwa majinyata yasa mutane ke tururuwa cikinsa. Wannan kenan,
Alhaji ammani abokin Alhaji Ibrahim ne sosai hakan yasa alhaji kabiru ya bud’e family file a GET WELL gashi basu da nisa sosai.
***
Tun kafin motar takai ya tsayawa ya dira yayi cikin gida direct d’aki ya shiga yana tattara kayan sa ya na tura su cikin akwati ya d’auko passport d’insa ya zira cikin Jakar dake goye a bayansa wayarsa dake hannunsa ya sa gaban aljihu ya nufi hanyar fita
“Yayana ya haka?”
“Abba zan wuce airport ne “
Ya kalli agogon hannunsa “airport by this time?”
“Abba remain 2hrs fa”
Umma tace “To ai ka jira abokin tafiyar taka yazo ko?”
“Ya sameni a can” yayi gaba
Baki, hanci, ido ta saki tana binshi dasu,
A tsawace Abba yace “Yayana haka ya kamata kayi wa mahaifiyar ka magana?! Tamkar wata sa’arka!, ka dawo nan ko kuwa!”
Cak ya tsaya, har seda Abba ya kuma cewa “ba da kai nake bane?”
Dawowa yayi yana faman hura hanci, daf dasu ya tsaya, “idan har ka tafi ba tare da ka bawa mahaifiyar ka ha’kuri ba kai fa Allah!” Ya juya zuwa cikin gida.
***
Dr Hasheem ya kallesu murmushi bisa fuskar shi “gaskiya you are a lazy being Anwar”
Lumshe ido yayi kan ya bud’e su a kan hasheem “think whatever you want, bazan damu ba” ya cigaba da daddanna mini laptop d’in dake bisa stool,
Girgiza kai Bro B yayi sanin cewar d’an uwan nasa baze kuma furta wata kalmar ba, ya kalli Dr yace “Allah da ace bansan Bro A ba zan iya ko bin hanyar da yake ba talkless of na mishi magana, kaga fa da muka shiga d’akin can ko kusa da gadon qin zuwa yayi, kamar wanda yaga trash”
“Ai wallahi da zan samu uncle zance masa ne kai ya kamata kaje hutu shi ya zauna ya cigaba da aikin”
Wani kallon karka fasa ya watsawa hasheem, hasheem ya kwashe da dariya yana fad’in “Allah kuwa kai da qasar haihuwar ka amma kabi ka tsane ta,”
“Ka fad’awa wanda aka Haifa anan ba de Anwar ba!”
Bro B yace “naji d’in and I’m proud to be a Nigerian”
Harara daya watsa masa ne yasa shi saurin d’aga hannuwa “I’m sorry big Bro”
Wayar dr hasheem ce ta katse su inda tashiga qara alamun kira dannawa yayi muryar wata nurse ya doki kunnuwansu “Dr room no.18” katse wayar yayi suka mi’ke a tare banda Anwar dake cigaba da latse latsen system,
Hasheem ya kalli Bro B “ i think you should stay here gara naje naga halin da take ciki tukunna,”
Nodding yayi shi kuma ya fice xua d’akin.
Maida hankali yay kan d’an uwan nasa yace “Bro A do you think is a good idea ka tafi ka barni ni kad’ai anan?”
Murmusawa yayi “kar ka damu I’ll soon be back afterall kasan hankali na baze ta’ba kwanciya ba matsawar kana cikin mugayen mutanen nan, so chill dana kwana biyu zan juyo, kar ka manta you are my only family now”
Forming line yayi da baki, Bro A ya bashi assuring look tare da tapping kafad’ar shi , kiran dr hasheem ne ya shigo wayar Anwar, yace dasu suzo su same shi, tare suka jera zuwa d’akin
Bro B ne ya fara sallama ya shiga, tayi waal da ido
“Mu...Mu’allim Bello”
Murmushi ya sakar mata sam ya jikin ki?”
Gaza ansa shi tayi, tayi waal tana bin Bro A da ido ‘O’ shape tayi forming da bakinta, “Mu’allim is he your brother?”
“Yeah...big brother”
“Hello Mu’allim’s bro” ta d’aga mishi hannu.
Blank look ya bata without saying a word ya maida hankalinsa kan waya.
©️Kdeey😊
DABAIBAYI👄
©️Khadija Ahmad (Kdeey😊)
®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)
(7)
Sam da bata lura ba ta cigaba da cewa “doctor dama ka san mu’allim B?”
Kai ya d’aga, “he is nice right? U know what....”
“Kaii!!...hasheem r u sure wannan ce yarinyar da bata da lafiya?”
“Iya sani na idanunka garau suke so kar ka sa ni tantama” cewar hasheem a qafule dan zuwa yanzu ya fara jin haushin sabbin attitude d’in Anwar,
Bro B yace “kana tunanin set up ne ko ya?”
“Bro can’t you see tun shigowarmu take hayaniya ko mu bamu yi surutan da take yi ba, habaa make her stop or barshi am, bari na jira ku a office” fita yayi suka bishi da ido,
Qasa qasa ya kalleta ganin yacce tayi kicin kicin da fuska yasa shi matsawa kusa da gadon tallafe da kafad’ar hasheem yace “Sam doctor hasheem aboki na ne, nazo gurin sa ne naga file d’inki shine na nemi alfarmar ganinki dan na tabbatar ke d’in ce”
Murmusawa tayi had’e da lumshe idanu ta bud’esu saman nasa “nagode mu’allim, doctor hasheem is nice too just like you kasan me, he often give me some chocolates whenever muka zo nan and I share it with Ameer kamar yanda ka koya mana, kuma inace mishi thank you”
Fad’ad’a murmushinsa yayi “that’s very good Sam keep it up”
Gyaran murya hasheem yayi wanda yaja hankalin Bello ya girgiza masa kai, shi kuma ya amsa masa ta hanyar lumshe idanu,
Saman kujerar dake kallon gadonta ya zauna
“Sam how are you feeling now?”
“Fine mu’allim”
“Good, inaso ki nutsu ki zan miki wani tambaya but you have to promise me first zaki bani gamsashshiyar amsa”
Da sauri tayi nodding “Anything for you mu’allim,”
“Good, I want to know what exactly happens before you fainted?”
‘Dago kai tayi a firgice, hawaye suka hau shatatowa tamkar an bud’e fanfo,
“U’ve already promised and kinsan lefin wanda ya karya alqawari”
*
Karkad’e rigan ta hau yi tare da gyara zaman talhar dake nad’e a wuyanta tana ganin fitowar sa ta mara mishi baya,
Qare mishi kallo ta shiga yi daga baya, Ba’kin takalmin hamez sau ciki daya sakaye doguwar farar qafarsa ta fara kalla shigar baqaqen kayan sunyi mugun tafiya da imaninta baqin jeans da baqar riga me qaramin hannu shi ya kuma fito da haibarsa, kansa dake cike da baqar suma data dabaibaye fuskar had’e da saisayeyyen sajensa ya kuma dilmiyata a kogin begensa har tana jin inama ace yana mata kallo d’aya ya fad’a tarkon soyayyar ta kamar yanda ta kamu farat d’aya daga kallo d’aya.
Jin taku daf dashi har ana neman ta’ba sahun sa yasa shi saurin waiwayo wa qiris ya rage goshinsu ya bigi na juna, direct idonta ya fad’a cikin nasa wanda yayi sanadiyyar tsayawar numfashinta na wasu sakanni, ga qamshin sassanyan turaren Ricci wanda ya had’u da versace da sauransu suka bugota har cikin qoqon hancin ta lumshe ido tayi ta bud’e cikin nasa tare da tallafar fuska da hannunta na hagu.
***’Baby ni dai ni dai se na bika um um”, kuka take har da su bubbuga qafa tamkar d’iyar goye, “habibty rayya ki bar ni naje bazan jima ba zan dawo kinji”, “To promise me ba zaka kalli kowace kucakar mace ba,” “na miki alqawari” “ba wani goodbye kiss,” “Kai baby baka da dama, To matso na baka”’***
Ba zato tasa hannu ta tallafo fuskarshi tana qoqarin manna bakinta saman nasa qiris ya rage su manne ya sakar mata lafiyayyun mari saman luntsuma luntsuman kumatun ta, zube wa tayi a qasa ba tare da ya kalle ta ba ya fad’a office d’in hasheem tare da bugo ‘Kofa da ‘karfi.
*
“Ya..yace idan na fad’a ze yimin irin yanda sukayi ma mummy nah...”
Kallon juna sukayi da hasheem kan ya kalle ta “Sam kin manta yanda nayi punishing adnan da ya cilla wa sholey ball?”
‘Daga kai tayi yaci gaba, “I will deal with whom so ever he is kinji, feel free and tell me,” kula da yacce take a tsorace yasa shi cewa “trust me”
Hanci ta ja ta fara da cewa “ bansan wane ba kullum dare idan su umma da kowa sun kwanta se yazo yayi ta buga min qofa to shine yau ma yazo”
Kukan da yaci qarfin tane ya hanata wata sa magana,
“Sam me yake miki?”
“Yana ta’ba min jikina ku...kuma da zafi..”
“Innalillahi....”
Tashi yayi ya matso gabanta ya tsugunna idanunsa sun kad’a jazur muryarsa har bata fita sosai yace” Sam who is he?”
“I don’t know, he cover his face with a lion mask” ta kuma fashewa da kuka, saurin kiran munirat hasheem yayi yace ta zauna gurinta su kuma suka yo waje “mu’allim umma na..ka kaini gurin umma na”
Yana jinta ya share tare da fita daga d’akin da sauri. Jikin qofar ya jin gina qirjinsa na masa wani irin zafi...
Hasheem ya ri’ko hannunsa yana bashi baki suka nufi office tun daga nesa ya hango mutum a yashe can bakin ‘kofa da sauri suka qarasa ya sa hannu jikin wuyanta da hannunta jin pulse d’inta na bugawa ya danna emergency button dai dai lokacin nurses biyu suka iso suka cicci’beta aka d’orata bisa gadon suka nufi wani d’aki dan bata taimkon gaggawa.
Zaune yake yayi crossing qafafunsa bisa table yayi baya da kansa idanunsa a rufe sosai yayi nisa cikin tunani ba komai ke damunsa ba se waccan ficiciyar yarinyar da duk ta rud’a shi, a tunanin sa masifar daya zazzaga mata ze sa yaji sau’kin abinda ke damunsa se dai tamkar ya hurara ta cikin zuciyar sa ne, To shin damuwar ta meye? Bansan ta ba, hasali ma uncle aiki ya bamu a kanta and her stupid family, wait who the hell is she, what is so special about her da har uncle yasa muke wasting precious time d’inmu a kanta?! All this answers are to be answered by Bro B, jin zuciyarsa na tsananta bugawa tamkar zata ‘ballo mishi qirji ya dafe da sauri yana rintse ido “please wacece ke? Meyasa zaki min haka?”..numfarfashi ya shiga saukewa yana jin qirjinsa har ciwo ya fara saurin miqewa yayi dai dai lokacin suka turo qofar
Neman fad’uwa yake Bro B yayi saurin riqosa “Anwar lafiya?”
Girgiza kai yayi yana faman sauke numfashi batare daya furta ko kalma d’aya ba ya koma da baya ya zube saman kujera Bro B ya zo Yana gyara masa kwanciyar ya ri’ko hannunsa
“Wacece ita?”
“Wa kenan?”
Fuska a murtuke hasheem yace “wacce ka wullar a bakin qofa?, wullahi baka da kirki Anwar....”
Rufe ido yayi yanaji hasheem yana masa fad’a be hanashi ba har se da yaji shiru ya bud’e ido, yana me kallon Bro B yace “I need to know her more bro, yarinyar da uncle ya bamu aiki kanta”
Baki ya bud’e ze fara magana ya katse shi “tashi muje gida, ba tare
Daya kalli sashen da hasheem yake ba yace “se mun dawo!” Ya fice Bro B na biye dashi bayan sunyi musabaha da hasheem, batare da ya bawa asibitin 2nd glance ba ya figi motar qiris ya rage ya bigi security man din dake gate.
Ranar duk samarin uku haka suka wuni sukuku
Anwar Sam ce damuwar sa meyasa a duk sanda ya tuna da ita se gaban sa ya fad’i gashi Bro B yana ciwon kai be samu bashi labarin Sam ba!
Bello a.k.a Bro B a.k.a mu’allim bello, yace da Anwar yana ciwon kaine kad’ai dan ya barshi ya sama damar tunanin yanda ze fidda Sam daga cikin wayan nan mutane ya yadda zata bar cikin su baki d’aya! Dan a yacce yake ji baze ta’ba samun kwanciyar hankali ba matswar tana rayuwa cikin iyalin Alhaji kabiru, after all ciwon da ake zargin wasu cikinsu sukayi still suna neman gurgunta rayuwanta, mene aibunta dan ta kasance cikinsu, mene aibunta dan ta aminta dasu d’ari bisa d’ari ya Allah wannan wace irin jarabawa kake yiwa baiwar ka, ubangiji ka tsare ta daga sharrinsu dan tsarewar ka. Da wannan addu’ar ya lumshe ido nannauyan bacci yayi awon gaba da shi.
Can bangaren hasheem kuwa hankalinsa tashe yake dan yarinyar da suka samu sa’bani da Anwar ta’ki farfad’owa se bakinta dake furta Bro A wanda yake da tabbacin ji tayi Bello ya ambata, ba komai ke dugunzuma masa lissafi ba se tunanin cewar yau sukayi alqawari da iyalan me girma governor cewar ze sallami yarinyar su, gumin daya shatato masa ne yasa shi zaro handky daga gaban rigarsa ya share iska ya fursar ya nufi ‘kofa da niyyar zuwa d’akin rayya ya kuma bincikar halin da take ciki, sa hannunsa bisa handle kenan yaji an turo ‘kofar
Wani kakkauran yawu ya had’iya a lokacin da sukayi ido biyu da firstlady hajiya maryam mainasara gefenta governor ne his excellency dr jamilu mainasara ne wanda suka rakiyar commissioners ne da S.A’s, har ‘kasa ya sunkuya dan basu girmamawa, tun kan ya furta wata kalma maganar firstlady ta doki dodon kunnensa
“Dr hasheem don’t stress yourself please, zan fi so mu qarasa d’akin rayya tukunna, dan kaga taron nan duk nata ne.
Yatsa yasa ya sharce zufar dake tsiyayo masa ta gefen kunne a zuciyarsa kuwa ba abinda yake se fad’in Anwar ka sakani yin qarya, ka sani jin kunyar dubbanin jama’a, na tabbata yacce sukayi gangamin nan to tabbas zan rasa kujerata a yau, ya kalli qanin mahaifinsa Commisioner of health Dr sufyan yana ta sakin fara’a, na tabbata fara’ar nan is going to be replaced by disappointment,
Allahumma la sahla..ya shiga karanta wa a zuciyar sa har suka isa bakin qofar, bismillah yace da gov. Mainasara, yatsa ya girgiza masa da cewa “ah ah anan kaine jagaba doctor kai zaka fara shiga,
Dariya yayi mai kama da yaqe kan ya wangale ‘kofar inda sukayi ido hud’u da d’iyar su kwance tayi male male mara lafiya Zam! Runtse ido yayi a zuciyar sa fad’i yake ta faru ta qare tun bare da ya bud’e ido sukayi ido hud’u da firstlady da ta kafa masa dara daran idanunta
‘Kasa yayi da kansa yayin da yaji mahaifan nata na ta qoqarin tashin ta, amma shiru maqatau kake ji wai maye yayi amarya.
A d’an rud’e yaji muryar dr sufyan “hasheem ya haka?”
Cijewa yayi ya d’ago kai “uncle b.....”
“Suprise..”
Sak ya tsaya da maganar da yake baki bud’e, tacigaba “mummy na” ta rungume ta ‘kaqam nan fa d’akin ya cika da shewa kowa na tofa albarkacin bakinsa,
Hamdala hasheem yayi tare da kuma jingina jikin bango idonsa kafe bisa fuskar yarinyar dake ta faman zabgawa mahaifanta shagwa’ba su kuma suna biyeta ko dan itace ‘yarsu guda d’aya tal da Allah ya basu.
“Alhamdulillah “itace kalmar data su’buce daga bakin hasheem, Dr sufyan dake gefen sa ya dafo kafad’ar shi tare da furta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 13