Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shi ba se ma duka da ya Kaiwa faffad’an qirjinsa tana kuma shigar da fuskar ta jikinsa, ajiyar zuciya ya sauke he know hakan ze faru dama, tana d’aya daga cikin dalilin da yasa yake son dawowa, Be kuma furta ko kalma d’aya ba se hannu da yasa saman sumar kanta yana shafawa a hankali, Se da tayi kuka me isarta sannan ta d’ago idonnan nata yayi jaga jaga duk maskara ta ‘bata mata fuskar, powder tayi dabbare dabbare, janbaki kuwa duk ta goge saman ash rigar sa. “Mine ba zan kuma yarda kayi nisa dani ba ko da hakan na nufin rasa rayuwata ne , do you know d hell I went through duk sanadiyyar rashinka, mine yaushe zaka gane irin soyayyar da nake maka dukkan numfashi na yana fita ne da sunanka dan Allah kar ka kuma yin nisa dani idan ba haka ba zan kashe kaina” ta qarashe a marairaice Iska ya fursar daga bakinsa without saying a word ya d’auko tissue ya share mata fuska ya ja hannunta suka fita, a motar ta qirar Bentley dai dai gidan da ke street 11, average avenue suka tsaya, Sarqafe da qugun juna suka nufi cikin gidan kai kana ganin su kaga masoyan da suka jima cikin begen juna. *** Qarfe 6:35pm daidai agogon Nigeria aka idar da sallah a masallacin asibitin GET WELL, hasheem da bello suka jero a tare, qasan bishiyar zaitun suka tsaya bello ya kalli hasheem Yace “doctor muna stressing d’inka da yawa gaskiya” “Hmm..a da ba, amma yanzu inajin yarinyar nan tamkar wata ta jikina” Jinjina kai bello yayi “amma Doctor what’s your view akan case d’in nan? Kuma me kake ganin ya kamata muyi? Tsaya ma tukunna har yanzu securities basu samu wanda ya yiwa nurse d’inka illa ba?” “Well yace basu samu kowa ba, amma sun kuma tightening security, amm kagane ba ni a nawa tunanin babu yacce za’ayi ba wani notice nothing nothing mutanen nan suyi vanishing lokaci d’aya, kuma bayan sun san cewar yarinyar su na nan...” “Baka ganin suna gudun kar a ga gazawar su wurin kulawa da ita duba ga barazanar da ake wa rayuwarta a gidan?” “Well hakane, amma fa kar ka manta he’s d’an ‘kasa’s brother ...” Dariyar ‘keta bello yayi, “a naka tunanin baze iya cutar da ita ba” Ya d’aga kafad’a “it’s up to them all I know ni dai, we have to get justice for this young girl “ Wayar sa dake qara ya d’auko a aljihu, uncle U ya bayansa a screen d’in, a kunne ya saka “my one and only uncle” Daga can ‘bangaren ya amsa shi, ya jima beyi magana ba zuwa can yace “I’ll call him right away “ Hasheem da tuni mood d’insa ya canja yace “ni nasan dole se ya fara zuwa wurin baturiyar nan kan ya qarasa gida , Allah ya kyauta” ya ja tsaki ya bar gurin. Bello da ransa yayi mugun ‘baci ya shiga tattauna lips d’insa na qasa idonsa ya kad’a yay Jajir bango ya kai wa duka “Why Bro meyasa? Meyasa kake son lalata tarbiyyar da Ammi ta jima tana bamu, irin kalar sakayyar da zaka yi mata kenan???” *** “Wayyo umma na..ze kash..e..n...” tun qarfi gwaggo ta girgiza ta, ta farka, kalle kalle ta shiga yi zuwa can ta sauke ajiyar zuciya ta ruqunqume gwaggo hannunta cikin na munu fad’i take “Gwaggo kar ku bari yayi min, ze tsikara min allurar jikinsa, yaji wa nurse ciwo, yana ji min ciwo a jiki na wayyo qafana” munu da ta dafa qafar tayi saurin janye hannunta dai dai lokacin hasheem ya fad’o d’akin gwaggo na qoqarin gyara mata kwanciyar suka hango jini na biyo cinyar ta zuwa ‘kafar ta “Innalillahi wa Ina ilaihir raji’un” cewar hasheem wanda idonsa ya sauka kan jinin dake zuba... ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) WATTPAD @Deejaht ahmad ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (12) *NOT EDITED * Wata nurse ya qwalawa kira aka ja gadon da take kai zuwa wani d’akin inda aka shiga bata taimakon gaggawa salati da salallami gwaggo ta shiga yi fad’i take “shikenan sun lalata mana ‘ya na shiga uku ni haule me zan ce ma ibrahim da mariya “ kuka tashiga yi bil haqqi munu dake gefenta itama nayi dakyar suka yi shiru. Wucewar awa d’aya da rabi doctor hasheem ya fito jiki a sanyaye ko d’ago kai ba yayi yazo wuce wa ta kusa dasu munu ta tare shi “Doctor ya jikin Sam?” A hankali ya d’ago kwayar idonsa ya sauke cikin nata dake cike da qwalla “ta..na nan lafiya bacci take” da haka yaja wata zuwa office, gwaggo tayi saurin zuwa qofar d’akin tana le’kawa ta wata ‘yar ‘bula, d’an guntun murmushi ta saki “dagaske yake bacci take munu” Murmusawa tayi hawaye suka biyo kuncinta tace “Alhamdulillah, gwaggo to muje mu ganta ko?”, girgiza kai tayi “aa munu I think zefi mu barta ta huta tukunna, zo mu jira a can” tayi pointing wasu kujerun qarfe. ~ Bello guri ya samu ya zauna har aka kira sallar isha bayan ya shiga yayi sallah ya fito ya zauna kan d’aya daga cikin kujerun shan iska dake harabar asibitin waya yake jujjuyawa a hannunsa amma zuciyarsa ta jima a duniyar tunani _Kimberly wata hatsabibiyar yarinya ce da tayi wa rayuwar Anwar shigar bazata, a lokacin da suke jami’a Anwar ya kasance d’aya daga cikin kwarin aji ma’ana wayan da kwakwalarwarsu tafi ta kowa ja hakan yasa da yawa d’alibai suke yawan zuwa gurinshi dan ‘karin haske, had’uwar su da Kimberly ya samo asali ne wani lokaci suna shekara ta biyu a jami’a inda tayi differing semester kuma ta kasance bata d’auka summer course ba da ta dawo, so da semester ta zagayo ne hasheem ya had’a ta da Anwar dan yake koya mata karatu, Sam Anwar be so hakan ba dan da farko ‘ki yayi se da yaga ran aminin nasa ya ‘baci ya amince, from the very first time da suka fara karatu Kimberly taji itafa ko da zata tafi tsirara se ta Mallaki Anwar tun daga nan fa tun Anwar na yakice ta har ya kyale inda ta kuma shiga jikinsa kai qarshema Allah kad’ai yasan iya abinda ke wakana tsakaninsu _ Iska ya fursar idanunsa a runtse yana jujjuya kai mafita kawai yake nema a gefe d’aya kuma yana mamakin abinda Anwar d’in yayi, wato dalilin komawar sa kenan?, hannu yasa ya cakud’a curly hair d’inshi, there’s only one way out ya ayyana hakan a zuciyar sa. Wata number yayi dialing “check your inbox” ya kashe wayar ya shige cikin asibitin, cikin reception ya hango su zaune gwaggo ta kafa tagumi munu kuma ta kwantar da kanta saman cinyarta, kai ya girgiza cike da tausayin su, ya nufi office d’in hasheem Handle d’in ya murd’a, daga ciki hasheem ya leqo ganin waye ya sashi bud’ewa, shiga yayi jiki ba ‘kwari ya shiga, saman doguwar kujera ya zube, shiru ya biyo baya ko wannen su da abinda yake qissimawa, hannu yasa ya shafo fuskarsa a hankali ya shiga karantowa bello abinda ya faru, Lumshe ido kawai yayi cike da tausayawa yarinyar kan ya miqe ya fita, wurin su gwaggo ya nufa ya tsugunna cike da ladabi “Hajiya kuyi haquri komai yayi zafi maganin sa Allah” d’aga kai tayi, ya cigaba “..amm hajiya nace idan babu damuwa zanso sanin alaqarki da Samira” Numfasawa tayi idonta quri a waje d’aya, ta shiga fad’a masa tsakanin su, cikin gamsuwa da bayanin nata yace “hajiya ni sunana bello Alfalla ni kuma malami ne a makarantar su samira haka kuma aboki ne ga likitan dake kula da lafiyar ta, ni Lauya ne me zaman kaina...ahh ya sosa kwantaccen sajen sa, ina miki wannan bayanan ne bisa wasu dalilai wanda na bar wa kaina sani which with time zaki sani Insha’Allah” Gwaggo dake jinjina kai tace “Allah sarki mungode da kulawa, Allah ya bada lada” “Amen, idan ba damuwa ko zan iya samun address ko dan gaba” “Anan muke sultan road Gidan alhaji Aminu” Noted, ya tafi bayan yayi musu sallama. Tashi gwaggo tayi zuwa d’akin Sam biye da munu, a lokacin wata nurse ta shigo ta duddubata murmushi d’auke a fuskarta tace “hajiya ‘yar nan taki is a fighter jikin ta yayi sauqi sosai zuwa gobe Insha’Allah zaku iya tafiya gida, let me go and give doctor hasheem the good news,” ta fita da sauri. Da azama Gwaggo ta nufi bakin gadon daidai lokacin Sam ta fara tari tun qarfi, munu ta taro ruwa a dispenser ta bawa gwaggo ta bata, a hankali ta shiga bud’e ido har ta wangale su duka “Gwaggo na” ta furta cikin rawar murya tare da fad’awa jikinta. *** “You mean sunyi qoqarin yi mata fyad’e?” Hasheem ya girgiza kai “haka ne, dan duk alamu sun nuna hakan” “Innalillahi...she need a very tights security, Bari na fad’a wa uncle” *** *8:00am Birmingham U.K* “Ammi na” ya shagwargwa’be mata tamkar yaron goye, duk ya kanainaye ta, shafa hannunsa ta cigaba da yi wanda suke sar’ke cikin nata , gyaran muryar uncle ce ta d’auki hankulansu inda ya tura kujerar da yake zaune baya, yana share bakinsa da tissue, wayarsa dake haske yayi picking yana duba saqo Yace “Anwar yaushe ka iso garin nan??” ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) WATTPAD @Deejaht ahmad ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (13) Tari ne ya sarqe shi tun qarfi, Ammi da mom hajar suka tashi da sauri ko wa na qoqarin nema masa ruwa, cike da takaici uncle ke kallon su duka, guntun tsaki yaja ya tashi ya hau sama, kallon juna sukayi Ammi tayi wa mom hajar Alama da ido ta bishi, gyad’a kai tayi fuskarta d’auke da tausayin Anwar da take ta faman shafa bayan sa, hannunsa dafe da ‘kirji, da’kyar ya iya yiwa ruwan kur’ba biyu ya nemi Ammi ta rakashi d’aki dan hutawa. _Mom_hajar_ Zaune ta same shi bisa reading reading table yana gyara medical glasses dake maqale a idonshi, be ko waiwayo ba, yaci gaba da duba littafin Human values, lumshe ido tayi had’e da karya wuya gefe ta taka a nutse zuwa gabanshi, hannuwanta ta sa saman shoulder d’insa a hankali ta shiga massaging, lumshe ido yayi dan sakon ya isa inda ake buqata sosai tasan lagwan sa, she knows the right thing to do. Cikin kwantar da murya take fad’in “Ni dai nasan yalla’bai d’ina mutum ne me kula da nasa, baya ta’ba ganin wanin sa cikin wani hali ya yi ko oho dashi” ta sunkuyo dai dai kunnen shi “Ko zan san wanda ya ta’bo min soft heart d’ina?” Forming line yayi da baki, ya d’ora hannunsa saman nata dake kai komo saman ‘kirjinsa , zare glasses yayi ya d’ora saman littafin “Mata yaron ku d’innan yana caza min kai , na rasa ya zanyi, kina gani ke kika sa baki lallai na barshi ya taho amma daga zuwanshi kiga abinda yayi, ni nasan dama dalilin shed’aniyar yarinyar nan yasa shi cewa lallai ze zo har da yimin qarya! Wai ze zo ne inspecting company!” Gyara zaman ta tayi saman cinyar sa tare da kwantar da kanta saman kafad’ar sa hucin numfashinta na dukan dokin wuyansa ta furta “afuwa...afuwa yalla’bai na sani Ann be kyauta ba amma be kamata a halin da yake ciki ka tafi ba tare da nuna damuwar ka ba, a halin da ake ciki yanzu addu’ar mu yafi buqata” Ta d’ago kai, “um kaje ka duba shi idan jikin nasa da sauki ka nusar shi har fad’a ban hana kayi mishi ba, amma banda fushi kaji yalla’bai d’ina” Ido ya lumshe tare da bata peck saman goshi, har bakin qofa ta raka shi sannan ta zauna saman kujerar daya tashi ta shiga dialling number Bro B. ‘Dakin samarin ya nufa inda ya tarar dashi ya fito daga band’aki d’aure da towel a ‘kugu, tsayawa yayi fuskar nan a had’e, da sauri ya iso gabanshi ya tsugunna a qasa “Uncle...” hannu ya d’aga masa cikin Kausasa lafazi yace “Anwar komai kake yi kasani ubangiji yana kallon ka, kuma kowa yayi daidai lahirar sa ya gyara.” har ya juya ze fita ya tsaya “kar ka manta wata d’aya kawai na baka mu juya Nigeria tare” Ido ya wangale “uncle nige..ria?” “Yes...zan je da kaina wannan lokacin dan da alama abin ya fara fin qarfin ku” da haka ya fita daga d’akin inda ya bar Anwar da tunani. *** Washegari misalin qarfe sha biyu da rabi aka basu sallama direct gidan gwaggo suka nufa abinka da yaro tuni ta manta da abin da ya faru dan had’uwarsu da munu yasa ta shiga sabgar ta, da dare misalin takwas mu’allim bello ya kawo mata ziyara har da rakiyar sholey da yaje takanas har gida ya d’auko ta duk dan yasa Sam farinciki aikuwa ji tayi tamkar tafi kowa sa’a a duniya yau gata ga munu da gwaggo ga kuma sholey se wuraren tara mu’allim da sholey suka tafi bayan yayo musu shopping da dama. Bayan wata d’aya Hasheem ke zaune gaban firstlady Yana prescribing magunguna for Rayya bayan ya gama ya nemi izinin tafiya, har ya tashi tsaye ta fad’o falon kamar wacce aka jefo se haki take “W..ai..t doctor” Waiwayo wa yayi ya sauke idonshi saman nata, baki ta turo gaba“kai meyesa ne kullum kullum kake tafiya da wuri” bambarakwai yaji maganar, kallon firstlady yayi ya kuma maida idonsa kanta Taci gaba “ni ni Allah ka tsaya muyi hira tukunna ” ta shiga sharar qwalla, a fusace firstlady ta daka mata tsawa “ke! Ray...” Hannu ya d’aga mata ta gefe still idanunsa kan Rayya yace “I’m sorry ma, kina son yauma muyi hirar aboki na ba”ya nuna mata kujera bismillah, diddira qafa ta hau yi, “ni Allah ka dena min hirar wani da ban sani ba, I only knows you and you alone I want to spend the rest of my life with” saurin kallon ta yayi cikin fad’uwar gaba Sum sum sum ya nemi guri ya zauna without saying a word, hakan yasa firstlady hajiya maryam da muqarrabanta barin falon, Murmushi me kama da yaqe ya saki had’e dayin qasa qasa da idonsa yace “I’m at your service ma” Kunya taji ta kare idanunta daga mugun kallon da yake harba mata, yayin da reaction d’inta ke saka hasheem cikin wata duniyar ta daban. *Bayan wata d’aya* Malam aminu kano airport ya samu baquncin uncle usman da Anwar, inda Bro B ya taryo su a motar sa zuwa gidansu dake kwairanga road, shigar su befi da awa d’aya ba uncle ya yi shirin fita inda ya nemi rakiyar Bro B. 2:00pm Ringing d’in da wayar shi ce ta farkar dashi, hannu ya miqa yayi ya d’auki wayar ya qaga a kunne, cikin sleepy voice yace “inaji” “Tashi kaje sweet heaven high ka d’auko Samira, zan tura maka address d’in da zaka kaita” Kafin yace wani abu d’if wayar ta mutu, bud’e ido yayi ya kuma duba wayar ganin tabbas uncle d’inne yasa shi tashi ya shiga wanka. Farar top yasa mara hannu had’e da black three quarter ya feshe jikinsa da turaruka masu tsada sumar kansa da take kwance ya gyara ya d’auka car keys ya fice. Wayar bello ya kira yana d’agawa yace “Bro B kasa a fad’a ma yarinyar nan kalar mota Ina school premises kar ta wuce 2mins u know I hate waiting” ya katse wayar tare da gyara tsayuwar motar ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) WATTPAD @Deejaht ahmad ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (14) *NOT EDITED * Tunda security man ya sanar da ita saqon mu’allim bello gabanta ke fad’uwa, tare suka taho da sholey har ta isa jikin motar sannan su kayi sallama, knocking window tayi jin qofar a rufe, shiru ba’a bud’e ba kuma qwanqwasawa tayi jin ba’a bud’e d’in ba yasa ta kara fuskar ta jikin window wai ko zata gano ciki, wur wur take da ido, jiki na rawa jin wani mugun fitsari daya cika mata mara gashi bata son shiga toilet d’in makaranta idonta ya cika da kwalla jin yana neman zubowa , kallon motar ta kuma yi gata dai se huci take amma ba alamun mutum cikin ta, juya wa tayi da niyyar nufar waje dan neman abun hawa, taku biyu zuwa uku taji ance “ke!” Banza tayi dan a tunaninta mazan makarantar ne jin ana ta cewa ke! har sau ba adadi had’e dayin horn yasa ta waiwayo a fusace tana faman matse ‘kafafu Wani irin bugu qirjinta yayi bazata ta’ba mance wannan fuskar ba ko da cikin mafarki wani nannauyan yawu ta had’iye a qafule ta watsa masa daradaran idanunta dake ta tsiyayar hawaye, komawa yayi cikin motar ya zauna yana qare mata kallo ta side mirrow badan tanaso ba se dan taimakon kanta kar tayi fitsarin wando yasa tayi saurin zuwa ta shiga tun kan ta qarasa rufe qofar ya figi motar su gateman da tsalle aka sha. Ido ta runtse tun qarfi hannunta bisa handle d’in qofa ta ruqunqume duk tabi ta firgita jin yacce yake manna gudu bisa shimfid’ed’iyar kwaltar sokoto road, qafar nan tata gam take dan qiris take jira fitsarin ya zubo, wani irin giya yaja aiko sam ta qwala qara tun qarfi tare da fad’owa jikinsa ta ruqunqume shi, ita duk a tunanin ta accident su kayi, a hankali ta shiga bud’e ido jin shiru ba ko motsi Idanunta suka fad’a cikin nashi hancinta dake bisa nashi ta janye da sauri kanta a qasa, “d’agani” Sassanyar muryarsa ta doki kunnenta, saurin kallon kanta tayi cikin zare idanu ta koma bisa seat d’inta, “Ke!!!! Fitsari kikayi min!!!!!” Wani irin bugu qirjinta yayi tamkar ze ‘ballo waje ta shiga kuka wiwi tana sheshsheqa tabbas fitsari tayi kuma a jikin sa innalillahi wa innalillahir raji’un, yau kam tasan wannan mutumin se ya kusan kasheta, Ji tayi ya ja motar ya kuma tsaya lokaci qanqani ta rikice ganin da tayi sun shigo wani gida murya na rawa tace “dan girman Allah kayi haquri kar kayi min komai wullahi zanyi duk abinda kace” kula da rud’ewar da tayi yasa shi sassauta abinda yayi niyyar yi mata, bud’e qofa yayi ya fita tare da fad’in “biyo ni” Ciki ba qwari ta bi shi a baya har zuwa wani tafkeken falo me d’auke da kujeru seti biyu, wata qofa ya nuna May da yatsa “shiga ki gyara jikin ki, akwai aerial cikin toilet yanzu zan kawo miki kayannan ki wanke min tass!” “Uhum” Yaja tsaki “dirty human being” ~~~~ 2 hours later Parking Bello yayi suka fito se fara’a suke shida uncle, “kaga abinda nake fad’a maka ko?” “Sosai uncle, nifa abin nan ya d’auren kai kana ganin zata yarda da maganar mu kuwa duba da ta manta abinda ya faru shekara ashirin baya?” Dariya uncle yayi “yaro yaro ne kai dai zuba ido ka gani,” “Su kuma su alhaji kabiru fa?...” Murmushi yayi “they are trapped” “Ban fahimce ka ba...” Shigowarsu falon ke da wuya wayar bello tayi qara “gwaggon samira ce” ya furta idonsa bisa uncle, “‘Daga muji” Answer wa yayi, suka gaisa tace “dama nace yau ko su sam nayin wani abu ne a school shiru bata dawo ba” Saurin kallon juna sukayi da uncle, cikin dabur dabur yace “ahh..ahh” uncle ya d’aga masa kai yace “eh nace ta jira na gama aiki ne se nayi dropping d’inta” “Ayya to shikenan, na yarda da kai bazaka ta’ba barin wani abu ya kusance ta ba” Girgiza kai yayi hannu a ka yace “insha’Allah nama gama yanzu zan kawo ta” “Allah ya kawo ku lafiya” ta ajiye, a fusace ya juya zuwa window yaga ali driver na wankin mota, d’akin Anwar suka nufa se de daidai shiga d’akin suka ji an yi atishawa cak suka tsaya, kuma yi akayi har sau uku, da sauri suka fad’a d’akin da suke kyautata zaton anan ne. Me zasu gani? Sam!!! Suka furta a tare, “mu...muallimmm sanyiiii” ta fashe da wani irin kuka me cin rai, juyawa yayi ya d’auko bargo cikin wardrobe ya lullu’beta fad’i yake “Shii shiii, babu abinda ze same ki kinji, trust me Sam, open your eyes please, ya kalli uncle, uncle kar ka bari ta rufe ido pls pls pls Sam say something,” tallafo ta yayi jikinsa yaji taja wani dogon numfashi har sau uku jikinta ya saki ‘Dora ta saman gado, wayar hasheem ya kira yana d’agawa ya fad’a masa tare da ce masa maza yazo yanzu. ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) WATTPAD @Deejaht ahmad ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (15) *NOT EDITED* _afuwa na rashin jina on time_ 🙏 A fusace fad’a d’akin inda ya tarar da Anwar kwance yana bacci kashir’ban, hannu yasa ya yaye bargon ya cillar gefe, “Wullahi na rantse duk abinda ya samu amanata ka sani se na d’aure ka, d’aurewar da se ka gwammace mutuwar ka da rayuwar ka” ya qarashe maganar cikin qunar rai, Zaune ya tashi yana jinjina maganganun uncle, me yake nufi da yarinya? Wace yarinya? Ido ya zare da sauri ya miqe tsaye ya nufi falo, cikin tashin hankali ya nufi inda take kwance, “Malam kar ka qaraso mana nan!!!” Kallon bello yayi cike da mamaki jin yacce ya daka masa tsawa, “ni kake ma ha..ka!?” Gaza kallonshi bello yayi se ma juya baya da yayi, ya had’a kai da bango. Uncle ya kalla shima ya d’auke kai, sallamar hasheem ce ta sa su duka waiwayo wa, Goshin ya ya ta’ba da wuyanta, ya kara yatsansa a hancinta, “I think firgici be kawai de ko sanyi daya ta’bata,” warware bargon jikinta yayi, “we need to change this clothes, a kunna mata heater” “Ok ammm please ko zaki iya taimaka mana ki canza mata kaya” Rayya ta fito da ido waje, “waye ni?” Ta kalli hasheem cikin yatsinar fuska, d’aga mata kai yayi, turo baki tayi “ inane d’akin?” Nuna mata yayi bayan ya d’auko wasu riga da wando d’an daidai gwiwa sababbi ya bata. “Amma wullahi ka bani mamaki, qaramar yarinya me ta sani da zakayi mata wannan hukuncin dan kawai tayi maka fitsari?” Uncle yace “ai hasheem na rasa a ina yaron nan ya d’auko wannan mugun halin dan Sam ba haka nasan halin d’ana ba” Anwar dai bece komai ba se ido daya zubawa d’an uwansa jin yacce ya gasa masa magana d’azu abinda be ta’ba yi ba” Bello da hankalinsa kacokan ke d’akin da Sam ke ciki be san abinda suke tattaunawa ba, all he knows baze ta’ba yafe wa Anwar ba idan wani abu ya samu Sam” Wucewar mintuna talatin, Rayya ta fito a guje da qarfi take shaida musu ta farka, a tare suka nufi d’akin su bello tsabar sauri kamar ze kifa, Anwar jiki a sanyaye ya bisu a baya yana zulumin abinda ze gani. “Alhamdulillah jiki yayi kyau, sannu Samira” kallon rashin sani ta bishi dashi kan a hankali ta maida idonta saman na bello “mu’allim “ ta furta cikin sanyin sauti, tsugunnawa yayi a gabanta “Yes Sam ya kike jin jikin ki yanzu?” Bata bashi amsa ba hawaye suka gangaro “inason zuwa gurin gwaggo da munu” ‘Daga kai yayi, “yanzu zan kaiki kinji wipe away that tears, uhm!” Waiwaya wa yayi gun hasheem “Doctor yaya?” Matsowa yayi ya ta’ba kanta “well zafin jikin ya ragu zaka iya kaita gida idan yaso zan d’ora ta a kan magunguna , idan jikin yaqi kwana biyu se a kawo ta ko allura na bata” Kafad’a ta maqale “uhm uhm banaso mu’allim “ dariya sukayi duka, Rayya da duk ta qulu a tunaninta kan meyasa wannan yarinyar zata rinqa yiwa hasheem shagwa’ba se ciccin magani take Anwar da tun tuni yake jingine jikin qofa kuwa idonsa stick to Sam wacce ke sanye da oversized shirt and threequarter, ajiyar zuciya ya sauke lokacin daya ji bayanin hasheem yayi wa Allah godiya da babu abinda ya same ya, dan har ga Allah ba ze so ace ta sanadiyyar sa wani abu ya sameta ba, juyawa yayi jiki a sanyaye daga can yaji muryarta na furta “sorry..” kamar ya tafi se dai ya tsaya had’e da lumshe ido kan ya bud’e yacigaba da tafiya dai dai fita waje ya jiyo

Chapter 4 of 13