Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
min rayuwa har haka, kuma meye laifin mijina a ciki?" A fusace hajiya maryam tace "Kasancewar sa me kud'i, k..ku..ma taya kike tunanin zan jure ganin kinyi aure kin barni ni da na girme miki da shekara kusan uku!..kinsan baqincikin hakan ne yasa ranar d'aurin aurenki na gudu bq d'in gidan kaka na 'buya ina kuka ashe a d'akin aka sauki baqin da suka zo d'aurin aure daga kano...daga cikin ma'boyata mahaifin namadi yaron Alhaji d'anqasa yana d'aya daga cikin wayanda aka sauka, daga ma'boyata na hangi shigowarsa ya shige band'aki fitowarsa tayi daidai da tashina zan fita naji ya janyoni na fad'a kansa a lokacin ya lalata min rayuwa...,tun daga wannan ranar na ci alwashin rama gi'bin da yayi min, a lokacin dana bincika naji labarin rasuwar sa yasa na maida hukuncin kan d'ansa namadi..shine dalilin da yasa na aikata haka..." Dariya jamilu mainasara yayi "to Alhamdulillah tunda har kin iya fad'ar dalilin ki amma ki sani ba wai mun yarda bane, na sani asiri gaskiya ne tunda har ya kama Annabin mu, amma maryam komai yana tafiya da hali ni kuma a gaskiya na gaji bazan iya zama da macen da take iya kisa ba saboda hak na yanke igiyar aure na biyu daga kanki kije su tafi dake ..." Rayya ta yanke jiki ta fad'i duk suka yo kanta harda hajiya maryam se de tun kan ta qaraso me girma gomna ya umarci CP ya shigo da mutanensa ya tafi da ita, Ihu hajiya maryam ta rinqa yi fad'i take abarta ta ga lafiyar 'yarta amma ko kallonta gomna beyi ba, sema barin d'akin da yayi. *** Haka rayuwa ta kasance yau dad'i gobe akasin haka, yau sati biyu kenan da fitowar su mummyn sam ba laifi ta samu lafiya se rashin qwarin jiki wanda hasheem ya tabbatar musu idan ta juri cin kayan gina jiki zata dawo daidai bada jimawa ba already yau kwanakin su biyu a gidan kawu kabiru wanda daqyar me girma gomna ya aminta suka tafi a cewarsa ai shima he is part of the family, sede tafiyar data kamashi zuwa france ne yasa ya yarda su tafi har ya damqa musu ragamar kula da Rayya dake kwance a asibitin hasheem dan sam jikin nata yaqi dad'i, duk wannan dramar da aka sha su Sam basu san abinda ke wakana kenan ba, kamar ko yaushe tafe suke su uku zuwa hostel ko wannen su da abinda yake tunani, numfashi sholey ta sauke bayan ta juya ta kallesu duka Tace "kunsan me?" Girgiza kai Sam tayi, munu tace "se kin fad'a" "'Dazu mami na ke fad'a min shatima ya kira ta wai zasu kawo lefe" "Ya fad'a mata ba ma ke ba?" Munu tace cike da mamaki, "Hmm, ance miki kunyarta yake wannan ta'b, ai yacce kika san ba yayar sa ba ko dan first cousins suke da ita, kuma kinsan yau sati d'aya bana picking call d'insa" Kafad'a munu ta d'aga "oho dai yaje tunda dai munayin sa ai shikenan" "Ke de bari qawata" cewar sholey suka tafa suna dariya, murmushi Sam tayi tace "congrats sweetheart" Rugumeta sholey tayi, "All thanks to you, tunda kece kika fargar dani na hango the Angel within him" "Group hug" munu tace tare da fad'awa kansu cikin dariya suka ce "wayyo zata karya mu" *** _Can't you call kiji ya muke silly girl_ Karanta message d'in ta kuma yi _silly girl_ mutum d'aya ke ya'ba mata kalmar nan, zaune ta tashi da sauri tana kuma maimaita kalmar bro A sunan yayi ringing cikin kanta, All this while dama shi ke tura mata saqo har yake kiran kansa da husband d'inta! unbelievable, baki bud'e ta koma tun farkon saqon daya fara tura mata tana karantawa. Saurin dialling number munu tayi dake sun fita shopping da sholey, tana ta ringing bata d'aga ba haushi yasa ta wurga wayar kan pillow game da kwantawa ta rungume qafafunta a qirji gabanta na wani irin bugawa "me bro A yake nufi...ya Allah kasa ba gaske bane na shiga uku na samu na cire bro B a raina kuma ga wannan! Innalilllahi, hawaye masu zafi suka siraro mata Thinking of him alone yana sa zuciyarta wani irin bugu, kenan shiyasa yake mata iskanci, ta waro ido waje game da fad'in wayyo! Ta jima a kwance zuwa can tasa hannu ta d'auko wayarta, ta shiga kiran layin Ammi a lokacin suna tare da mummyn Sam suna hira, Ammi na bata labarin auren Sam da Anwar, mummyn Sam tana kuka wanda kallo d'aya za kayi mata kasan kukan farinciki ne saboda murmushin dake manne saman fuskarta, Ringing d'in wayar yasa ta tsaya da cewa "Samira is calling.." Cikin rawar murya tace "Pls put it on speaker" Kai ta d'aga, "hello Ammi na" Zirrrr hawaye suka zubo wa mariya, "Samira na nayu fushi se yau kika tuna da ni" Cikin shagwa'be murya tace "Allah Ammi ba haka bane, mss paticia ce tasa mu kashe wayar dan kar tayi distracting d'in mu daga karatun exams" "Oh samira na wasa nake miki, how have you been, ya exams d'in?" "Alhamdulillah, nan da 4days zamu yi hutu gashi bakwanan" "Yea, Ann yace ba zaku zo gida ba har se kun gama session d'in baki d'aya," "Ammi.. yanzu..yaushe zaku dawo to?" Ta qarashe a shagwa'be kukan mummyn Sam ya d'an kufce dan har Sam se da ta jiyo, A rud'e tace "Ammi is everything okay?" Saurin riqo hannunta mariya tayi game da girgiza mata kai alamun kada ta fad'a mata,...jinjina kai tayi cikie da tausayin 'yaruwar tata tace "Lafiya, kin ga canjin weather yasa mura ke neman kama ni" "Ayyah sorry, yanzu when are you coming back" "Insha'Allah in two weeks time, akwai matar uncle d'in su Ann da muke zaune anan, ta haihu yau da safe so inaso ta samu qarfin jikinta sosai sa'annan mu dawo" "Okay Ammi, bara na barki" "Okay dear, ina 'yanuwanki" "They went for shopping" "Meyasa baki je ba?" "Period pain yasa ni gaba Ammi" "Have you take a medic?" "Miss patricia tace wai ba'ason ake shan magani" "Or sannu kinji make sure you relaxed kada kiyi motsi da yawa and drink some fruits uhm?" "Ok Ammi take care, i love you" "Bazaki ce na gaishe da brothers d'inki ba?" "..send my greatings to mu'allim bello" da fad'in haka tayi saurin ajiye wayar dan haka kurum taji fad'uwar gaba tun kan ta ambaci sunan Bro A. *** "Meyasa kika hanani fad'a mata, do you know how joyous she will be?" Cewar Ammi tana qoqarin ajiye wayar bisa bedside drawer, "..bana son ta shiga wani state ne, baki ji ba Sam d'ina ta girma har tana yin period" ta qarashe cikin dariya me had'e da kuka Kai Ammi tayi nodding, Muryar umma salamatu wacce shigowarta kenan ta doki kunnuwan su, "..she will be more than happy idan ta ganki a raye, she always says she misses you kullum dare se tayi kukan rashinku a gareta..nayi hasara rashin bata soyayyar uwa dan Allah ki yafeni mariya wullahi banyi hakan a sanina ba..Ameer yau satinsa guda baya ci baya sha duk ya fita hayyacinsa, yace lallai na nemo masa Samira ya nemi afuwar ta idan har ina son ya koma yanda yake, dan Allah ku agaza min" ta durqushe a gabansu cikin zubar hawaye, Kallon kallo sukayi tsakanin su, kan Mariya tace "muje na ganshi" Umma salamatu tayi leading d'insu har d'akin sa, inda yake kwance rigingine idonsa bisa sealing hawaye na zubo masa, babu me cewa shine Ameer d'in Sam d'innan me wasa da dariya, ya rame duk ya fita a hayyacinsa, Zama mariya tayi kusa da kanshi game da d'ora hannunta saman sumar shi, "Ameer d'an lukuti me qaton tumbi me kama da bulun boti..." d'ago kai yayi game da fashewa da kuka bayan ya kwanta saman cinyar mariya, "Itace waqar da take yi maka a duk lokacin da kazo gida back then can you remember? You are morethan a brother to her Ameer, duk abinda kayi wa Sam zata yafe maka, duk abinda ya faru kayi ba'a cikin hayyacinka ba, dole zata yafe maka uhm? Ka cire damuwa a ranka, inaji a jikina zata yafe maka" Cikin kuka yace "mummy kin tabbatar?" Kai ta d'aga "insha'Allah, maza zauna muci abinci kaji, yinwa nake ji and dont say no" ta nuna shi da yatsa in a playful way, Kallon ummasalamatu yayi kan yace "zanci nima" Nan suka zauna suka ci abincin ana ta'ba hira wacce take tun tada ce da haka har ya qoshi suka tafi suka barshi zeyi wanka ya fito falo, *** Bello da Anwar ke zaune suna hirar bayan saduwa cikin office d'in hasheem wanda ya tafi dubo lafiyar Rayya, "Kana son ce min first cousins muke da Sam all this while bamu sani ba?, Allah is great♡" cewar bello cike da farinciki mara misaltuwa Numfashi ya fursar tare da gyara zama ya had'e hannuwansa wuri d'aya bayan ya kuma kallonshi ya d'anyi one sided murmushi "Yeah, and Rayya too" "Alhamdulillah..you know what? Yanzu komai zaizo min cikin sauqi insha'Allah.." 'Daga gira Anwar yayi, "mene?" Ya tsugunna gabanshi "Bro A amanata, she's going to be mine, i'm willing to make her mine officially.." Duniyar yaji ta tsaya mishi cakk babu abinda yake iya jiyowa se sautin dariyar Bello game da hamdalar da yake...amanar sa??? Ya ayyana a ransa, kan ya jiyo shi yana fad'in "Yes Samira..i love her so very much..." ©️Kdeey😊 DABAIBAYI 👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊 ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (31) ..hawaye masu d'umi suka ciko idanunsa, yayi saurin sharesu da hannu kada bello ya gani, yayi saurin miqewa ya fice da sauri har suna neman yin karo da hasheem "Bro A" Yana iya jiyo muryar bello na kiransa but bashi da courage d'in fuskantar sa a halin da yake yanzu! There is only one way out! Bello be ta'ba neman abu ya rasa a wurina ba face nayi masa, se idan bani da halin yi, wu'ka da nama duk a hannuna suke, dole nasan abin yi, ya ayyana hakan a ranshi, Key yay ma motar sa ya nausa bisa kwalta, yana tafe yana zubda qwalla besan haka soyayyar Sam tayi mishi mugun kamu ba se yau da waninsa ya furta kalmar so a gareta, wanin ma d'an uwansa, steering wheel ya doka tun qarfi tare da fashewa da kuka hannunsa saman qirji yana duka fad'i yake "why why meyasa ki kai mana haka she's my heart and bello is my own blood" ya sauke ajiyar zuciya, da taimakon Allah ya isa gidan kawu kabiru. Cikin jerin motocin kawu ya ajiye tasa, da d'an saurinsa ya qarasa cikin gidan, ba me cewa ga halin da yake ciki saboda toshe idonsa da yayi da baqin gilashi, A falo ya had'u da umma salamatu da mummyn Sam cike da wani tsananin kunyar su ya sunkuyar da kai, har qasa ya tsugunna ya gaida su, cike da fara'a suka amsa masa umma salamatu na tsokanar shi "Haba Anwar a 21st century muke fa, surukuntaka is now old model, kai da za kazo mu zauna mu sha hirar mu " Key d'in hannunshi ya cusa cikin sumar kanshi yana susa game da kuma sadda kai yana murmushi, "Ammi fa?" Yace murya qasa "Au ja'iri bazaka kulani ba kenan, to kaje tana d'akin ciki daka hagu" Kai ya d'aga sum sum sum ya shige ciki, saman sallaya ya sameta zaune ta d'aga hannu sama tana addu'a, da azama ya isa gareta saman cinyarta ya kwantar da kanshi tare da sakin wani silent kuka wanda danshin ruwan da taji ne yasa data idar da addu'ar ta leqa fuskar sa, "Subhanallahi, Ann lafiya?" Kai ya girgiza "Ammi bro b.." A rud'e tace "Bello? Meya faru dashi?..d'agani muje na gani a ina yake?" Girgiza mata kai yayi a hankali ya tashi zaune fuskar nan tayi jaga jaga da ruwan hawaye "he..saidd..." gaza furta qarshen zancen yayi , A firgice tace "sunyi masa wani abu ne shima?" Ta tambaya "Ko d'aya Ammi,...Ammi kinsan cewar inason bro B sosai ko? Inason shi sama da yanda nake qaunar kai na..i can even sacrifice my own life in har tasa zata inganta," Cikin rawar murya tace "naji...naji fad'a min abinda ke faruwa mana" "...he is my only blood Ammi, i see Abbi when ever i look at him...Ammi soyayya batayi mana halacci ba" "Ka fahimtar dani Ann, ni-nifa bangane inda maganarka ta dosa ba" "Ammi zan iya bar mishi kowa, komai amma banda nan" ya nuna heart d'inshi da yatsa, ya cigaba da fad'in "...ita d'in zuciyata ce, rabuwa da ita tamkar rasa rayuwata ne,...meyasa ze ce yana son matata ta sunna!" Ji tayi d'if duniyar ta tsaya mata idanunta kan qofa inda bello ke tsaye tamkar ruwa ya cinyeshi. "Bel..lo!!!" Ta qwala kiransa on top of her voice, 'Dago kai yayi kan ya furta komai suka jiyo qugin mota tun qarfi, ai rasa me bawa wani hanya akayi tsakanin Ammi, umma salamatu da mummyn Sam, "Shin meke faruwa ne?" Suka furta kusan a tare idonsu bisa fuskarta, "Innalilllahi wa inn'ilaihir rajiun" ta furta a fili kan ta juya ta koma cikin gida suka mara mata baya, A daddafe ya fito falon, ya zube a gabansu, cikin sambatu yake fad'in bazan iya rabuwa da matata ba kuyi min rai, haka ya rinqa maimaita kalmar har bacci nannauya yayi awon gaba dashi, Cirko cirko sukayi a kanshi cike da tausaya masa, mummyn Sam ce tayi qarfin halin d'aukar waya ta kira bello, Wani irin rough driving yake cikin fitar hankali, yayin da a gefe guda kuma 'yan sanda ke biye dashi sedai duk qoqarin su basu cimma shi ba, yayi gaba ya barsu da cizon yatsa🤣. Shagon unguwar su salihu ya nufa dan yasan can ne ba wanda ya sani idan ka d'auke hasheem, wayarsa dake haske ya kashe ya kuma rufe kansa a d'akin, ruf da ciki yayi rungume da pillow yana kuka me cin rai, A fusace ya tashi zaune yana maganganu, "wallahi a a bayan na gama shukata qiris ya rage na girbe, Sam batayi deserving heartless miji irin ka ba, baka sonta lallai se ka datse igiyar auren nan ka bani ita domin ita d'in tawa ce, Nasha ganin soyayyata kwance cikin idonta, Sam bazata ta'ba amincewa da kai ba after dukkanin cin mutumcin da kayi mata, se yanzu da kaga ta isa ban ruwa...bazan ta'ba yarda ka mallaki abinda yake nawa ba, Sam Amanata ce, she's mine and i'm going to make her mine officially, dole ka sake ta na aura...!" Da haka ya silale bacci yayi awon gaba dashi. *** "Hasheem ya kake ganin lafiyar tashi" "Mummy damuwar da yake ciki na neman ta'ba mishi zuciya dan yanzu haka yana cikin maxim.." "Um um um um sam yarona lafiyarshi qalau..." "Only if you give him abinda ya ke so Am..." "Zo muje daga waje" tace dashi living mummyn Sam and umma salamatu behind. """ Tagumi ya kafa bayan gama sauraron abinda Ammi tace, "Ammi her love change d demon in him" "Pardon?" Jinjina kai yayi da cewa "tun sa'ada kuka zo na kula bai cika son magana ba kullum cikin kallon wayarsa which i definately know hotonta ne, he even day dream about her,..Anwar often smile amma yanzu his lips are always parted and spread kamar zasu ta'bo walls d'in kunnensa har hakwaransa ana gani yanzu" "...you observe all this ba tare da kasan da maganar nan ba? Dr kasan yarana sosai, cikinsu who deserve to be with Sam?" "Ammi Sam matar Anwar sunanta, kuma ba'a ta'ba canja wa tuwo suna Allah kad'ai yasan alkhairin da ya shirya cikin auren nan" "Bello fa?.." Gira ya d'aga game da cewa "well! Bello In my own observation tausayin Sam yafi rinjaye a zuciyarsa sama da soyayyar da yake ikirarin yana mata..." "Kamar yaya?" "Ina nufin tausayinta yake ji, be sani bane, but i'll make him understand" ya miqe tsaye, "Ina zaka je?" "Zanje na taho dashi" "..bazaka iya samun shi ba, wayarsa a kashe take.." One sided murmushi yayi "zan zo miki dashi yanzu Ammi" Cike da damuwa ta d'aga kai, da ido ta bishi har ya 'bace wa ganin ta. *** Abinci suke ci hakan yasa banda qarar spoon ba abinda ake ji, "kim" Saurin waiwayawa sukayi jin an qwala kiran hatsabibiyar yarinyar mss chloe kamar yanda suke kiranta dashi saboda rashin jin maganar ta. Daga wata qofa ta fito, tana girgiza tamkar bishiya idan ana iska, dama gata kamar ta karye tsabar rama, ido biyu suka yi da munu ai kuwa ta galla mata harara, Da turanci tace "ke wakike ma kallon banza" Munu tace "ke da wani idon kika ga na kalle ki?" Qwafa tayi cike da takaici can cikin zuciyarta kuwa haushi take ji da ba Sam bace, dan haka kurum taji batason yarinyar, yarinya tamkar ita ta halicci kanta, duk wani features da Anwar d'inta ke so na 'ya mace yarinyar nan me qwala qwalan ido tana dasu, abin takaicin kuma shine mom d'inta tace cousin sister d'in Anwar ce, Numfarfashi take tamkar wacce tayi tsere idanunta na faman harararsu, sede hausawa sunce harara a duhu...dan ita samira ko d'ago kai bata yi ba kanta a qasa tana cigaba da cin abincinta. Tsaki taja ta nufi wurin sakatariyar mahaifiyarta ta bata wata paper kan ta juya ta bar wurin cike da takaicin Anwar d'an uwan Samira ne. Nannauyan ajiyar zuciya Sam ta sauke bayan ta waiga taga fitarta, ta dawo da idonta kan munu, "Wai meyasa bakya shayin tsokanar matar nan ne? Bakya gudun ta fad'awa mamanta.." "Ta fad'a mana se me ai itama mss chloe tasan halin nata, kuma inada tabbacin mu zata mara wa baya" "Kinga kallon da tayi mana kuwa, Allah dakyar nake tura abincin nan dan qiris nake jira naga tayo kan mu nasa gudu" Dariya Munu ta kwashe da ita, "kice dama sadda kan da kikayi idonki na kanta?" "Ba dole ba kinga yanda take numfarfashi kamar tsohuwar guzuma" Dariya suka kwashe da ita, daidai lokacin suka jiyo ihun mss chloe tana masifar wa yace sakatariyar ta ta bari Kim ta tafi California ba tare da saninta ba, Kallon juna sukayi sum sum sum suka bar wurin zuwa sport complex. *** Daqyar ya iya cire jiki daga katifa ya nufi qofa jin yadda ake bugu, "Waye?" Ya tambaya in a sleepy yet cracky voice "Bello bud'e nine" Kamar ya share sede ya bud'e ya juya ciki, girgiza kai hasheem yayi bayan ya tura qofar, Komawa yay ya kwanta idonsa a lumshe, yayin da hasheem ke tsaye a kanshi hannunsa cikin aljihu yana karantar yanayin shi, Numfasawa yayi a hankali yace "Bello tashi muyi magana" "Ina saurarenka" yace ba tare da ya motsa ba, "Ka tashi ka zauna nace!" Yace in a commanding voice, Bello ya tashi zaune game da fursar da iska me zafi daga bakinshi, yace "ina jinka" "Menene dalilin da yasa baka ta'ba fad'amin labarin soyayyar da kake yiwa Sam ba, afterall ni da kai muke aikin nan tun farko, uhm?" "A lokacin she's such a baby and at that time i have no feelings for her,..." "Yaushe ka fara jin soyayyar a zuciyarka?" "The day Anwar punished her" "Uhumm?" "Tana kuka...helplessly... kallo d'aya nayi mata naga yarinyar need a shoulder to lean on, amma kaga yanda yayi treating d'inta idan ta zama under his custody me kake tunanin ze faru, shin waye ya bashi ita da har yake ikirarin matar shi ce?!" "Kawu kabiru, and it's official,..." "Official my foot! Doctor nasan Anwar abokin k..." "Anwar? Bello a kan mace kake kiran sunan d'anuwanka da raini? ka nutsu ka dawo hayyacinka fa, how sure are you ita yarinyar bata son auren? Or do you think 'yar qanqanuwar soyayyyar da kake ikirarin kanayi mata zata aminta da kai! Look idan rai ya 'baci be kamata hankali ya gushe ba, aure ba abun wasa bane kada na kuma jin kana cursing d'in shi in ba haka ba wullahi zaka gamu da fushin ubangiji, gara ka san abinda kake idan kuma kaqi tam! A yanzu haka mahaifiyarka na can hankali tashe kar ka bari ta dalilinka wani abu ya faru da lafiyar ta kamar yanda kayi sanadin ta d'an uwanka!" Da fad'in haka Hasheem ya fita a fusace cike da 'bacin rai. ©️ Kdeey😊 DABAIBAYI 👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊 ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (32) Qirjinsa ya tsananta bugu tsabar kad'uwa da firgicin abinda hasheem yace, mukullin mota ya d'auka ya fice da sauri daqyar ya iya tsayawa rufe qofar d'akin. Bumper to bumper suke tafiya dan ta side mirrow ya hango motar bellon, one sided smile yayi, bello will never choose anybody over d'anuwansa da mahaifiyarsa ya ayyana hakan, cike da farinciki ya juya akalar motarsa zuwa asibiti dan gano rigimammiyar tasa da taqi yarda ta koma gida, Da taimakon ubangiji ya isa gida, sede yana zuwa umma salamatu ke shaida masa sun tafi gidan barrister yanzu, can ya nufa zuciyarsa cike da tararradin a wani hali Ammi da Ann suke, A falo ya tarar da mom hajar zaune saman carpet tana pleading wa barrister, kallonsu yay cike da mamaki, "whats going on here?" Yace cikin rawar murya, Tasowa tayi da sauri ta kama hannun bello " B please taimake ni ka taya ni bashi hakuri yaqi saurara na tun ranar da abin nan ya faru, I'm fed up with his new attitude!" Ta qarashe maganar da kuka, Salati yayi game da dafe kansa, tamkar me koyon tafiya ya ja qafa zuwa kujerar da barrister yake, "Uncle..." "Shiiii.." yace game da d'ora yatsa saman lips, "But unclee.." "Wullahi na rantse da Allah na yafe mata, wannan halin tunanin da nake yi ba komai bane face tuna yanda na yarda da ita amma ta yaudare ni ta hanyar kwasar sirrika na ta yad'a a waje not thinking amanar da na d'auka na kula da dukiyar marainiyar Allah" "But uncle ka duba halin da take ciki she just gave birth, and..." Kai ya jinjina "bello kai yaro ne do you know what it takes to love a woman and to be betrayed by the same woman?, na yafe mata but dole tayi hakuri da sabbin halayen nan nawa dan baza su tafi lokaci guda ba" da fad'in haka ya bar falon zuwa sama, Idonshi ya maida kanta da ke qasa tana zabga kuka lokaci guda duk ta sauya mom hajar din da take 'yar gayu da 'kwalisa yanzu zaune take da riga da zani dabam dabam gashin kanta yayi buyu buyu, lallai tashin hankali bashi da rana! Daqyar ya samu ya lalla'bata game da bata baki kan komai me wucewa ne, nan ta shaida masa su Ammi sun tafi asibiti dan jikin Anwar yaqi dad'i, da haka ya bar gidan zuwa asibitin, room no 2 ya nufa kamar yanda nurse munirat ta sanar masa, Kwance ya hango shi saman gado, Ammi na gefen kansa ta kafa uban tagumi, yayin d gwaggo ke sallah saman sallaya, a hankali ya taka zuwa gaban gadon hawaye suka yanke masa cikin kukan zuci ya sumbaci goshin d'anuwan nasa dake kwance lokaci d'aya duk ya canza kamanni, duk ta dalili na? Ya tambayi kanshi, ganin dakyar numfashi ke fitar masa bakinsa a bud'e, da sassarfa ya qarasa gaban Ammi ya tsugunna game da kwantar da kansa saman cinyarta ya riqo hannuwanta cikin nashi tare da fashewa da wani marayan kuka yace "Ammi dan Allah ki yafe min, wullahi sharrin shaid'an ne banyi niyyar saka ku cikin qunci da tunani ba, hasalima bansan cewa Samira mata take ga Anwar ba, i'm just saying my mind out, dan Allah Ammi ki bashi haquri kice ya tashi ni na hakura bana sonta, i just come to realize that tausayinta nake ba so bane, Ammi kice wani abu pleaseee" Dafa kafad'arsa da akayi ne yasa shi d'ago kai ya rungume qafar mummyn Sam yana me cigaba da zubda qwalla "pls mummy talk to her taqi kulani kinji.." Kanshi ta shafo tan girgiza kai tace "ba qin kulaka tayi ba, ever since Anwar ya shiga wannan halin taqi yin magana kwata kwata" Cikin tashin hankali ya juyo gareta se gani yayi tana kallonsa idonta na tsiyayar hawaye, rarrafawa yayi gabanta, ta tallafo fuskarsa tana me share masa hawayen da hannunta game da girgiza masa kai a hankali ta furta "Allah ze baka wata mafi alkhairi kaji, kayi hakuri" Kai ya gyad'a a hankali yace "insha'Allah Ammi, Allah ya bawa Bro A lafiya" "Ameen" suka furta baki d'aya, nan dai suka had'u suka rinqa bashi baki har ya sauko suka shiga hira wace akasari ta Anwar ce da yanda auren su ya qullu. Satin Anwar d'aya ya samu lafiya, bello ya nemi yafiyarsa kan maganganun daya fad'a masa marasa dad'i, haka rayuwa ta kasance musu suna da wata biyar a nigeria suka fara shirin komawa dan Ammi tace hankalinta yayi kan su Sam da yanzu suke ajin

Chapter 11 of 13