Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
“Allah ya biya ka da gidan aljanna, she’s there source of happiness” Murmushi yayi tare da sosa qeya dan tabbas ya sani Allah ne ya cece shi se de me? Maganar da rayya ke fad’a ce ta sanya shi cikin wani d’an qaramin tashin hankali. “Mummy he is so handsome, ni dai Allah ina son shi idan ban same shi ba zan kashe kaina na mutu” “Doctor waye haka?!” Nannauyan numfashi ya sauke idonsa cikin na uncle d’insa ya furta “Anwar” Dr sufyan ya maimaita sunan cike da mamaki, “CEO AB MACHINARIES??, me yazo yi naija” “Whaat!!! Kana nufin yaron da na jima Ina nema wanda ya rinqa decline d’in requests d’ina, shine ya shigo garina?!” Maganar da ta fito daga bakin me girma governor kenan Bugun zuciyar sa ne ya tsananta, Anwar you are in hot pepper.... (Qarin haske😆 by next page qulle kan ya isa haka🤣, lol) ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (8) *NOT EDITED * Waiwaye~ Marigayi Amin Alfalla d’an asalin jihar kano ne qaramar hukumar dala , cikin unguwar lamido crescent GRA area gidan shi yake ya rasu a shekara ta dubu biyu da sha hud’u inda ya bar yara biyu uku tal a duniya tare da mata biyu duk da hajjo uwargidansa sunan ya aure tane kawai amma a UK take rayuwar ta dan can mahaifanta suke befi sau biyu ta ta’ba zuwa naija ba wic ko ‘yan uwanta dake maiduguri ba wani kyakkyawan sani tayi musu ba, gaskiyar sunan hajjo maryam yaranta biyu da marigayi alfalla Anwar da basheer se d’ayar matar sa sadiya wacce take yaren ibra ce, sun had’u da Marigayi ne sanadiyyar zuwan ta office d’insa na naija dake kano matsayin secretary d’insa inda ya d’auketa aiki har ta kai su ga qulla soyayya bayan auren su Allah ya azurta su da yarinya mace taci suna bilkisu , bayan rasuwar Marigayi ta d’auke d’iyarta suka tafi wanda har yau babu ita babu dalilinta, duk kuwa da duban da Barrister qanin marigayi alfalla yayi mata. Marigayi ya fad’i ya barwa yaransa d’inbin dukiya hakan yasa suke business ba kama hannun yaro inda sukayi naming businesses d’in nasu da AB....ma’ana Anwar bashir. AB MACHINARIES kamfani ne da yayi suna gun producing qualitative kaya hakan yasa qasashe da dama ke kwad’ayin yin business dasu se de qalubalen da suke fuskanta shine sam mamallakin kamfanin bawai da kowa yake mu’amala ba, za’a iya cewa kamar selecting yake. Game da maganar su da me girma gov. Kuwa akan wasu injina ne daya keso ya siya gurin su dan gyara shinkafar mu ta gida kamar yacce shugaban qasa yace akoma yi, se dai qiri qiri Anwar yayi ko oho da maganar daga baya ma se ya aika wa me girma governor cewa ya nema a wani wurin daban. Wannan kenan Dawo wa labari, “Doctor inason had’uwa da yaron nan within 48hrs, bawai Ina neman yardar sa bane, this is an order from me” cewar me girma governor ya juya ga P.A d’insa “ka samun cikin schedules, idonsa kan rayya yaci gaba, na miki alqawari ko ta halin qaqa se kin same shi kinji” Girgiza kai tayi cike da farinciki, “Amma your excellency..” “Kar ki damu kome ze zo mana da sauqi Insha’Allah “ ya qarashe a hankali zuwa can ya d’ago kai yana kallan dr sufyan yace “babban likita yaushe zaku sallame mu?” Waiwaya wa dr sufyan yayi zuwa sashen da hasheem yake yayi yace “Doctor yaushe zaka sallami patient Dinka?” “Yanzu am zata iya is wucewa gida zan aiko da magunguna zuwa anjima Insha’Allah” “Allah ya kaimu” cewar First Lady, bayan yan hirarraki da yan jaridu suka tafi, inda suka tafi suka bari hasheem da tunanin yacce zeyi ya kai Anwar wurin me girma governor yar dariya ce ta su’buce masa daya tuna yanda me girma governor ya rinqa alqawarin mallakawa yarinyar sa Anwar Mutumin da lafiyayyiyar mace ma ba ko wacce yake kulawa ba talkless of mara lafiya kamar Rayya. Lallai be san waye Anwar ba, mutumin da yake murd’ad’d’e, mutumin da idan kayi dama hagu yake yi, mutumin da yake wa fari kallon baqi. *Bayan wasu awanni* Anwar Alfalla shine sunan da yayi typing cikin system d’insa nan da nan ta bud’u yaci gaba da tura saqonni tare da acceptn wasu kwankwasa qofar da ake ne ya tsaida shi ba tare da ya d’auke idonsa daga kan computer ba ya bada izinin shigowa Babban mutum ne ya shigo, kallo d’aya zakayi masa kasan he’s in his early 60’s yana tafe yana gyaran babban riga, sallama yayi tare da jan kujera ya zauna. *Five minutes later* Duk inda quluwa takai ya gama quluwa alhaji me babura kenan wanda yayi tattaki takanas yazo wajen Anwar dan tattaunawa ta musamman, dad’a karkacewa yayi bisa kujerar yana hararar shi qasa qasa, ‘Dago kai yayi a nutse murmushi maqale a bakin shi, “barka da zuwa alhaji hope u didn’t find any difficulty coming in here?” Tambayar tazo mishi kamar da rainin hankali, basarwa yayi “ah Alhamdulillah, ya aiki naga kamar kana aikine ma” “Aa no karka damu nagama ai, if to say ban gama ba da zan sallame ka ne zuwa wani lokaci “ Jinjina kai Alhaji yay yaci gaba, “ko akwai wani abu da kake buqata?” “Sir Anwar kan maganar nan ce da mukayi a waya kan fitulun babura” Jimm yayi zuwa can ya sauke numfashi yace, “alhaji me babura ko?” “Eh eh ni ne” “Na tuna, amm bari muga..” Wasu takaddu ya janyo ya bashi yace gashi ya cike yayu transfer yanzu” Haka suka ci gaba da tattaunawa har Allah yasa aka dace suka rabu. *** Sam ta tashi a firgice tana qwala kiran Abbanta da umma har ma da Ameer nurse munirat ta fad’o d’akin a guje “Shhh calm down fine baby, menene ya sameki, gashi doctor hasheem ya fita wayyo” Marairaice wa Sam tayi “please ki kaini gurin umma na da Amir kinji kar su tafi su barni” kuka take bil haqqi, har da su majina “Okay ok kiyi shiru bari naje na d’auko waya na kira doctor” Girgiza kai tayi a tsorace, tunanin ta d’aya wannan mafarkin da tayi wai sun tafi sun Bart’s gashi tana ta neman su bata gan su ba” Wani sabon kukan ne ya su’buce mata, zuwa can bacci me nauyi yayi nasarar d’auketa. Munirat dake bakin qofa ta le’ko da farantin silver a hannunta me d’auke da allura ta shigo tayi mata. Tajima a tsaye tana kallon ta ba abinda take se qiyasta kyawu irin na Sam, zuwa can ta sauke ajiyar zuci ta fita tana gunaguni saboda wayar Doctor da taqi shiga *** Qarar bell ce ta tashe shi jin se dannawa ake ba qaqqautawa salati yayi tare da miqewa ya zauna hannu yasa ya murza idanu, ya kai hannu ya kunna bedside lamp idansa ya kai kan agogo 5:10am wane haka? Tashi yayi yana gyara zaman boxers d’insa ya nufi qofa, fridge ya tsaya yasha ruwa sannan ya nufi qofa ya bud’e, saurin juyawa yayi ya kalli time kan ya waiwayo ya kalle shi “Hasheem?!” Winking ya masa ya ra’be ta gefensa ya shige ciki, rufe qofar yayi ya biyo shi saman kujera ya zube yace “lafiya dai na ganka da asuba haka?” Dariya yayi, “ina neman rakiyar ka ne” “Rakiya yanzu?” “Taimaka min zakayi, nayi maka alqawarin daga yau bazan kuma takura ka ba bare ma tafiya zakayi zamu jima bamu had’u ba” Numfashi ya sauke yace “amma kasan yau by eleven jirgina ze tashi right?” “I promise you ba zamu jima ba” “What’s so important da gurin da zamu je kuma inane?” “Kasan dai ni ba d’an yankan kai bane” “Kana fad’a min magana ne? Zan fasa wullahi” Hannu ya had’e gu d’aya “yi hakuri yalla’bai ka shirya mu tafi” Hararan wasa ya yi masa ya shige d’aki . Se gurin 6:30am suka kama hanya, banda hamma ba abinda suke bugawa daidai wani tamfatsetsen gate yayi horn gate d’in ya bud’e ya nausa hancin motar ciki a harabar yayi parking suka fito wani matashin saurayi yayi musu sallama tare da yi musu iso zuwa bakin wani pool cikin wata bukka. Zaman su ke da wuya ya fito sanye da jallabiya hannunsa riqe da mug sallama yayi musu suka amsa, kiran sunansa da yayi ne yasa shi d’ago kai ko ba’a fad’a ba yasan wanene numfashi ya fusar tare da watsawa hasheem wani killer look. ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (9) *NOT EDITED* Sipping shayin yayi kan ya kada baki yace “Anwar Amin Alfalla, the young talented billionaire nasan za kayi mamakin ganina ko, well to clear your doubt ba abin mamaki bane duba da nan jihata ce, nakan san duk wani shige da fice da akeyi cikin ta” ya numfasa “well kuyi haquri na cika ku da surutu ban baku abin sha ba, duba da weather d’in garin nasan zaku fi buqatar me d’an d’umi” Basu kai ga yin magana ba ya bada order a kawo musu abun ta’bawa, maida idonsa yayi kan fuskar Anwar wearing a smile yace “Anwar ko kana da abin cewa?” Forming line yayi da bakinsa still idanunsa maqale kan hasheem kan yayi faking smile yace “ranka ya dad’e sir bani da abin fad’i, se abinda kace” Jinjina kai mainasara yayi “ok I think duba ga lokaci let’s just get straight to the point but kafin nan Anwar ko meye dalilinka na qin yin aiki dani? Ma’ana qin yimin abinda nayi requesting duk da cewar na had’a maka da deposit ne?” Murmusawa yayi yana me kuma sadda kai qasa yace “I’m sorry ranka ya dad’e amma inaga zefi cancanta muje kan maganar data kawo mu nan daga baya se muyi wannan” “Ko zan iya sanin dalilin da yasa kasan cewa ba maganar kenan data zaunar damu a nan ba” “Ranka ya dad’e akwai different companies da suke qwararru ta wannan fannin wanda suka dame ni ta ko ina kan meyasa akan ni kad’ai zaka damu?” Gyad’a kai mainasara yayi yana mamakin courage irin na Anwar ya d’age gira “maganar ka gaskiya ce, amma inaso ko dan gaba ka kiyaye, maganar mu ta gaba kuma..ko ka sanar dashi?” Ya karashe maganar idonsa kan hasheem “Aa ranka ya dad’e abinda ka aika ni yi kad’ai na aiwatar wannan hurumin ka ne” “Anwar! Ina neman alfarma a gurin ka” Mamaki ya cika shi cikin sanyin sauti yace “alfarma? A wurina kuma” Mainasara ya jinjina kai, daidai lokacin aka kawo musu abin ta’bawa aka zuba wa hasheem anwar kuma tea kawai ya kar‘ a shima d’in kad’an ya kur’ba “Anwar inason ka nemi auren yarinya ta Rayya..” maganar da me girma governor ya sashi wata muguwar qwarewa Tun qarfi hasheem ya shiga taping bayansa, bayan ya kar’bi gorar sassanyar ruwan sanyi ya tuttula masa a baki, sunkuyar da kai yayi na wasu sakanni kan yaja hanci ya mi’ke tsaye da sauri yana d’an sadda kai yace “with due respect ur excellency, I’m sorry for what I did a baya, amma idan kana son hukuntani ne dan Allah kayi ta wani hanya ba wannan ba” Dariya mainasara yayi “Anwar kenan” ya dafo kafad’ar shi “a kan wani dalili zan nema hukunta ka, kan rights d’inka? Aa bana haka, kuma hukunci da ‘yata how ridiculous! “ ya maida idonsa kan hasheem “dr ko zaka iya yiwa abokin ka bayanin rayya! I mean inda ta Ganshi” Gyaran murya yayi bayan ya kora ruwa ya kalli Anwar dake masa wani d’an banzan kallo “yarinyar da ta fad’i a bakin office d’azu” Kya’be baki yayi, ta ya suke expecting ze iya tuna wata yarinya! Wacce take asibiti ma mara lafiya, shirun da yayi yasa me girma governor dad’a watso masa tambaya, “ka tuna ta?” Girgiza kai yayi a qafule yace “I can’t remember her” “Whatever de Anwar wannan be maqasudin zaman nan namu, Ina neman alfarmarka da ka taimaka min, Rayya bata ta’ba neman abu ta rasa ba ko da kuwa Nisan sa yakai birnin sin, ga qoqon bara ta nan Anwar dan darajar Allah ka taimaka min” Kallon mamaki yabi governor dashi, soyayya? Shi ya so wata? Kuma wai da aure!” “Silence didn’t speak Anwar so zan baka dama kayi tunani amma kafin nan zanso ka ganta kan ka tafi dan abokin ka yace za kaje ganin gida” “Ye...yea..h, a zuciyarsa kuwa banda tafarfasa ba abinda take, shi yaso wata da zancen aure Ina yake da time ma, gskya ma he’s not ready kwata kwata, to speeds things up ya amsa da to, Nan da nan kuwa fara’ar me girma governor ta fad’ad’a inda yasa ayi ma firstlady magana ta sa Rayya ta kintsa, shiru be ya biyo baya har na wani d’an lokaci kan wayar dake gefen me girma governor ta d’au qara yana d’agawa ya sauke ya qwalawa wani magana inda ya umarceshi yaje government house ya d’auko Rayya, Tattaunawa suka cigaba dayi tsakanin me girma governor da hasheem inda nan take me girma governor yayi ma hasheem alqawarin alkhairi masu yawa saboda kawo mishi Anwar da yayi. Can gefen Anwar kuwa daddanna waya kawai yake amma hankalinsa kwacakon yana kan lokaci dan Allah Allah yake su tafi yaje ya fara shiri ya kuma ci mutuncin hasheem for bringing him to this hell To hell mana kai shifa ji yake kamar yana zaune a waya, horn d’in da suka ji ne yasa shi d’ago kai a nutse waze gani? Wannan fat mango d’ince, wacce ta nemi kissing virgin lips d’inshi, Idan be manta ba itace wacce ya hankad’e jiya, itace dama governor yake magana?, lallai dole yayi pleading dan Allah ne kad’ai yasan maza nawa taso raping, saurin kauda tunanin yayi jin maganar hasheem a kunnenshi “Look how breathtaking beautiful she is” Girar sama data qasa ya had’e ya watsa masa hararar kana da hankali kuwa, iska yaji fuuu ta doko shi before he knows se ganinta yayi tsugunne gabanshi ta tallafo chubby kumatunta ta tsare shi da ido, “Hey bro A meyasa kullum kake dad’a kyau ne” Saurin d’aga kai yayi yaga me girma governor bayanan ya maida hankalin shi kan hasheem ido waje Yana pointing d’inta da hannu alamun “is she d one?” Kai hasheem ya d’aga masa yayi baya yayi relaxing yana sakacen Haqori... (Ayimin afuwa yau ban samu damar typing da yawa ba. Tnc u) ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) WATTPAD @Deejaht ahmad ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) Assalamu alaikum Ina neman afuwar jina shiru da ku kayi hakan ya faru sanadiyyar kakata da Allah yayi wa rasuwa, Ina barar addu’ar duk wanda ya karanta post d’in 🙏 nagode. (10) A nutse ya sauke kwayar idanunsa saman nata wanda hakan ya haddasa wa Rayya fad’a wa cikin shauqin bege, cike da izza yace “tashi a gaba na!” Ko d’ar bata yi ba sema koma wa da tayi saman side table ya zauna still idonta stick to him, numfashi ya sauke cike da rashin sanin yanda zeyi da fat mango (in anwar’s language 😆) kallon hasheem yayi yanda ya wani bararraje yana niqar abinci bayan ya jaju’bo masa wannan aikin, ‘kwafa yay tare da d’an sakin fuska ya kalleta ji yake kamar ya ham’bareta amma ya basar yana me faking smile “Hi beautifullll” ya wani ja word d’in, dariya ya sar’ke hasheem har be san lokacin daya fursar da ruwan bakin shi ba ya d’aga musu hannu “Sorry sorry pls” inda sukayi parking ya nufa yana dariya wanda sautin ta ke isa har kunnen Anwar, Fuska a d’an cunkushe ta juyo da kanta inda yake “wane wannan yake qoqarin spoiling mana special moments d’inmu, ko be ta’ba jin an fad’i haka bane” Mamaki maganar ta bashi, sosai ya fara doubting lafiyar yarinyar cikin kwantar da murya yace “baki san shi bane?...” ‘Dan jimm tayi alamun tunani, can ta d’aga kafad’a “not at all..” “Likitan ki ne..” “Likita? No! This is d first time I’m seeing this guy” “Is she suffering from..” “Alzheimer’s yes” Jinjina kai yayi idonsa a kan hasheem, tausayin yarinyar ya cikashi, a tausashe yace “Rayya wannan doctor d’inki ne, shine yake kula da ke kinji” Turo baki tayi “To amma ni ai lafiya ta qalau fa” Tsintar kansa yayi da murmusawa ya kalli agogon dake maqale a hannunsa a hankali ya furta I need to save a life, a fili kuma yace “Rayya will you like to join me for a ride?” Farinciki fal ranta ta yi nodding har da saurin miqewa, tsaye shima ya tashi ya kalli hasheem da ya ke kallonsa tamkar wani baqonsa ya kashe masa ido ya juya suka nufi mota, Hasheem tsabar mamaki ya gaza furta ko ‘A’ mamakin hali irin na Anwar yake, jin ana laluba masa aljihu yasa ya dawo present time Anwar ke neman key “Thank you” ya furta yana nuna masa muqullin ya koma motar a guje inda Rayya ke jingine tana jiransa... Wayar hasheem dake bisa table ne ta shiga ringing ya d’aga lokaci d’aya annurin fuskarshi ta gushe ya maida wayan cikin aljihu ba tare daya nemi sallama da me girma governor ba ya rubuta wani short notes ya bada a bashi ya fita ya shiga napep. *** Gwaggo ke ta kai kawo waya a kunne minti d’aya biyu taja tsaki, munu na zaune saman cushion ta shar’bar kuka cikin sheshsheqar kuka tace “gwaggo har yanzu bata shiga ba” Numfashi ta sauke “hmm, munu je d’aki ki d’auko min gyale mu kuma koma wa ko Allah ze sa sun dawo” “To gwaggo” ta shiga d’aki da sauri ta fito riqe da mayafin jikinta sanye da hijab ta mi’ka mata ta yafa suka rufe gidan suka fice *** A qagauce ya sauka a napep d’in ya fad’a asibitin straight d’akin ya nufa, bakin gado ya sameta tana ta gursheqan kuka bakin gadon ya tarar da ita zaune duk ta ciccizge carnula d’in hannunta tana ganin shi ta mi’ke tsaye “Doctor dan Allah ka kaini gurin umma na please doc..” Jirin daya kwasheta ne ya Hana ya ‘karasa maganar nurse munirat tayi saurin taro ta, riqe kanta tayi hawaye na bin kumatunta, gyara mata kwanciyar yayi tare da bata taimakon da tafi buqata nan da nan kuwa wani baccin ya d’auketa. Gefe ya matsa yana dialling number Alhaji kabiru, sake kira yayi for d 101 times amma shiru hakan yasa ya yanke hukuncin nufar gidansu yaji ko lafiya dan dole ya sallami yarinyar nan dan baze juri ganinta cikin wannan halin ba Motar sa qirar Honda 2008 wacce ke ajiye cikin garage din asibiti ya d’auka ya nufi gidan Alhaji kabiru *** Zaune yake gefen cashier yana kallon duk wani moves d’inta ta cikin mini TV we libgar kaya take da masu amfani da marasa amfani mutane se kallonta suke wasu ta danqara musu harara wasu ta ja musu tsaki ganin yadda lokaci ke ja yasa shi dakatar da ita hakanan, Marairaice fuska tayi “Bro A ice cream fa?” Iska ya fursar ya tsaya riqe da qugu “oya hurry up kar nayi latti kinji” Girgiza kai tayi ta juya ta d’auko cikin freezer har da dad’in chocolate shi dai yana ta bin kayan da ido mamakin inda zata kai uban kayayyakin yake wanda kwata da rabinsu kayan maqulashe ne Gida ya kai ta har qofar falon mahaifinta ta kira hadimin gida ya shiga da kayan agogon hannunsa ya kalla yace “To baqo zeyi halinsa ‘yammata na” Wal tayi da ido “ni nice ‘yammatan ka?” Kallon yacce take farinciki yayi yace “yes, and you are also my sister..” Ta katseshi “and..?” Ya gane abinda take nufi amma se yace “d’aya matsayin se idan kin min alqawarin kafin mu kuma had’uwa zaki rame” Kwa’be fuska tayi “why?” “‘Yammata na qiba is not good to your health” Shiru tayi kanta a qasa ya cigaba “in dai yammata na ta rage qiba I’ll surprise her” Da fara’ar ta tace “With what?” “Zan fad’a miki amma ba yanzu ba” Ta girgiza kai “Zan rage kaga dama mummy na bata so itama” “Very good yammata na, yanzu bari na tafi saura 2hrs jirgina ya tashi” ‘Kwal ‘kwal idonta ya kawo ruwa kula da haka yasa shi cewa “kinga bari naje na shirya se nazo muyi sallama ko” “To kayi sauri kaji” Ya d’aga kai “to shikenan” a hankali ta sauka a motar ya ja ya tafi, yana fita a gidan ya sauke relief sighs ya nufi gida. Qarfe 10:30 ya tura wa d’an uwansa text ya shiga jirgi suka lula gajimare. *** Lokacin da hasheem ya isa gidan Alhaji kabiru yayi daidai da isowar gwaggo daidai bayanshi ta tsaya lokacin da yake juyowa cike da tunanin mafita sukayi ido hud’u “Sannu bawan Allah, “ Kallonta shima yayi “sannu ina wuni” Cikin rawar murya tace “lafiya qalau, kai ma neman masu gidan kake yi ko?” “Eh amm nazo na tarar basa nan...” Wayarshi data shiga qara ne ta katse sa “Eh nazo gidan su yarinyar basa nan bello what’s happening?, Hello hello...mtsw poor network” ya maida wayar aljihu Gwaggo ta matso kusa dashi “Yaro ko kasan wani abu game da inda masu gidan nan suke ke?” Kallonta yayi ganin resemblance d’in yarinyar da Sam ya sa shi gyad’a mata kai. ©️Kdeey😊 DABAIBAYI👄 ©️Khadija Ahmad (Kdeey😊) WATTPAD @Deejaht ahmad ®️Haske writers association 💡 (Home of expert and perfect writers) (11) *NOT EDITED * “Ina suka tafi, Ina d’an uwana ya tafi ka taimake ni ka bani amsa d’annan shi kad’ai ne dangina kaf fad’in duniyar nan ka taimake ni ka had’a ni dashi...” Tausayinta matar ya cika masa zuciya hakan yasa shi lumshe ido ya bud’e yace hajiya ni kaina tunanin inda mutumin nan ya tafi nake dan a jiya da safe ya kai yarinyar sa asibiti na da zummar a duba masa lafiyar ta se dai tun bayan barin su can ban kuma jin shi ba, ko wayar sa, hasalima da na kira ake rejecting daga baya kuma wayar a kashe na keji shiyasa nayi tattaki zuwa nan” “Samira kake fad’i? Samira na wurinka?” Ya d’aga kai “tabbas dan yanzu haka rigima take kan lallai se na kawo ta gurin umman ta, sai da nayi mata allura saboda ta samu nutsua sannan na samu na fito” “‘Dannan taimake ni ka kai ni gurin ta idan wani abu ya sameta bazan ta’ba yafe wa kaina ba..” Jikin hasheem yayi sanyi jin kalamin gwaggo hakan yasa shi saurin tare musu napep suka tafi, tare suka iso da bello wanda shima yayi parking motar sa kenan. gwaggo ya gaisar a tsatstsaye suka fad’a cikin asibitin duk irin gaisuwar da ake wa hasheem be tsaya ba se hannu kawai da yake d’aga musu, kai da ka gan su kasan suna cikin wani yanayi na tashin hankali, dai dai shiga d’akin suka jiyo ihu daga ciki, a qagauce suka fad’a nan suka ga an fice ta window da gudu se labulaye da iska ke kad’awa Maida ido sukayi kan Sam wacce ta ke a qaqqafe tamkar gawa baki bud’e ido a wawwangale kanta suka yi a rud’e su na jijjigata motsin da bakin ta ke yi Doctor ya bi, jin abinda tace yasa shi saurin waiwayawa baya daga lungun gado ya hango nurse munirat yashe cikin jini munu ta saki wani irin ihu tare da fashewa da kuka... *** *Birmingham, London UK* Zaune yake cikin wani tsadadden restaurants dake fidda wani tsadadden qamshin rose flower da ke tashi ta ko wani lungu da saqo na wurin, mata ne da maza baibaye da wurin ko wa na harkar sa, da yawan su masoya ne dan daga masu sarqafe da hannun juna se masu sumbatar juna wasu kam a rungume suke, kasancewar rayuwa irin ta waje ba wanda ya damu da abinda wani ke yi, Yayin da kowa ke harkar sa shi yana gefe ne rungume da magazine, duk da qarar takalmin da ta nufo shi, be hanashi qarasa abinda yake ba se ma d’aukar qaramin kofin whiskey dake bisa table yayi ya kur’ba, qamshin turaren Nina ricci daya bugo sa ne yasa shi sakin wani lallausan murmushin da ya fidda sirrin kyawun fuskar shi, a hankali ya d’ago ‘kwayar idonsa ya sauke saman kyakkyawar fuskar ta, “Kimberly” ya furta cikin sanyin sauti, tashi tayi da sauri ta fad’a jikin sa tare da sakin siririn kuka, “shhiiii ya isa haka kim pls ki bar kuka kar hankalin jama’a ya dawo kan mu” Bata kula

Chapter 3 of 13