tana cewa “zan baka chocolates d’in da goggo ta siyo min kaji”
One sided murmushi ya tsinci kansa da yi, kan ya waiwayo a hankali ya bata thank you look, ya sakai ya tafi, qasa mu’allim bello yayi da kanshi yana sakin murmushi wannan yarinyar wani irin zuciya take da, Samira halayyar ki na burge ni, ya ayyana hakan can qasan zuciyar sa.
***
Munu dake zaune a qofar kitchen tana gyaran kayan miya ta kalli gwaggo tayi murmushi “gwaggo baki yarda da mu’allim bane?”
“Ba haka bane munubiya, yarinyar nan amana ce a gareni taya kike expecting hankalina ze kwanta bayan bata tare dani”
“Gwaggo nayi imani tunda tana tare da mu’allim she is safe, so ki kwantar da hankalin ki ‘yar ki zata dawo lafiya”
Sauke tagumi tayi “Allah ya bi bakin ki”
“Amee..”
“Assalamu alaikum,” ta fad’o gidan tamkar wacce aka cillo
“‘Yar halak”
Gwaggo ta washe baki, “Sam yaki taho nan” ta janyo ta jikinta, rungume juna sukayi su gwaggo har da ‘kwalla,
Munu ta tashi tana d’auraye hannu a gindin famfo tana fad’in “tabb aikuwa nima Allah dani za’ayi family hug d’innan” ta tafi a guje ta fad’a kansu
“‘Yammata yi a hankali kar ki ‘balla mana gwaggon mu”
Juyawa tayi ganin me maganar ta kare fuskarta da hannu “laah..haba mu’allim ni d’in nawa nake”
“Ga ki nan duk qasusuwa “ Sam ta qarashe da yin gwalo
Kwakkwa’be fuska munu tayi tana kallon gwaggo tace “wai gwaggo bana girmi yarinyar nan da kwana shida ba, Allah kice ta dena tsokana ta, ‘bakutu kawai”
Ai Sam na jin haka se ta kwakka’be fuska ta saki kukan shagwa’ba, har da tashi a guje ta fad’a d’aki, dariya ya bisu dashi kan ya dawo da kallonsa gurin gwaggo dake sharar qwalla
Cikin sadda kai tace “ina tausayawa rayuwar samira ba uwa ba uba, Allah ka bani ikon kyautata rayuwar ta”
Numfashi ya sauke “Amen gwaggo, ni zan koma”
“To madallah , Mun gode qwarai, yawwa bello niko nace ko za a iya samar wa munubiya gurbin karatu a makarantar ku?”
“Eh me ze Hana sede yanzu kinga saura befi kwanaki ba su fara zana jarabawar shiga ajin gaba, amma wani aji take”
“Aji d’aya suke da Sam”
“To ba matsala se de nake ga idan babu damuwa ko a bari ta shiga bayan jarabawar kamar zefi”
“Hakan yayi dama dan walwalar Sam nakeson su kasance tare”
“Tom Insha’Allah zan fara processing “
“Nagode Allah yayi albarka”
Sallama yayi mata, ta tashi “bari na d’ora girkin nan dan nasan tunda kuka had’u se ta Allah, fitowar ku ba yanzu ba.
***
A can quryar d’aki kuwa Sam ce ta zage take ta bawa munu labarin abinda ya faru
“Mutumin nan is so scary Sam, meyasa baki fad’awa gwaggo ba?”
Ta girgiza kai “um um munu nice da lefi, pls kar ki fad’a mata”
“What about this medicine??”
“Wani magani ku ke magana ?” Cewar gwaggo data shigo d’aukan abu
Kallon juna sukayi kan Sam tace “dama gwaggo bani da lafiya shine school doctor ya bani magani”
Jin yacce maganar kefita daqyar yasa tace “meke damun ki” ta sa hannu a wuyanta da goshinta
“Is just a minor headache and cold”
“Minor? You are calling rashin lafiya minor ke ni bani medicines na kira hasheem ya tabbatar min da ingancin su” ta d’auki ledar maganin ta fita.
Murmushi sukayi , a hankali munu ta d’ora hannuwanta saman na Sam “mu’allim na kula mana dake”
Lumshe ido tayi had’e da jinjina kai
Ta qarashe da cewa “Nima Allah yasa yake bani kulawa haka”
Murmusawa su kayi a tare, ta kuma cewa “ba fa wani abu nake nufi ba, don’t think nagative “
Yanuwane face tayi had’e da d’aga kafad’a ta bud’e hannuwa, ta tashi ta shiga toilet dan d’auro alwalar magriba
©️Kdeey😊
DABAIBAYI👄
©️Khadija Ahmad (Kdeey😊)
WATTPAD @Deejaht ahmad
®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)
(16)
*NOT EDITED *
Da ya dawo daga masallaci be zarce ko ina ba se bakin shagon dake daura da gidan su, hira wasu Samaria biyu keyi da wasu daga ma’aikatan shagon hirar dai ta ball ce shi dai daga ya murmusa se ya d’aga musu kai idan an tambayesa abu dan Sam shi ba ma’abocin kallon kwallon qafa bane, wayar sa dake aljihu ya zaro ya shiga yanar gizo ba komai yana duba nasarorin da kamfanin sa ke samu a can qasar ta UK.
Kewar kimberly ta tsargo masa, tsam ya miqe tare da zagawa bayan shagon dan kiranta sosai yake son jin muryar ta,
Ilai kuwa tana d’agawa ta fashe masa da kuka, se dai tun kan ya samu damar rarrashin ta wata mota ta d’au hankalinsa wacce tayi parking daidai qofar gidan su, duk da irin kalar hello da take sirfa mishi be samu damar kulata ba, ya kashe wayar tare da seta wayar shi ya d’auki hoton plate number d’in,
Tsayuwar shi ya gyara , ya shiga dialling number bello ringing d’aya tayi ya d’aga “kana ina”
“‘Daki doing what suits me best”
“Ok duba cikin wayar na turo maka saqo ka turawa dss bashari ya duba min”
“Yes broseee”
Kashe wayar yayi, ya cigaba da karantar motar zuwa can yaga anja an tafi, numfasawa yayi a hankali kan ya ja qafa ya koma cikin gida dan ji yayi komai ya sare mishi, me ke shirin faruwa kuma? Tambayar datayi crossing mind d’insa kenan.
*
Misalin 7:45 am zaune suke bisa dining table suna breakfast shiru ya ratsa, gyaran muryar uncle ce taja hankulan su duka, inaso wani cikin ku yaje gidan su Sam ya shaidawa gwaggo Ina willing kai yaranta boarding school saboda wasu dalilai nawa and bana so taqi aminta so kuyi duk abinda kuka san zaku iya saboda ta aminta” ya miqe dai dai lokacin shima anwar ya miqe
“Uncle ni zanje na qarasa processing visa d’inka”
Kallonshi yayi “Luke gidan tare idan ka dawo kayi wannan d’in daga baya” ya wuce ya barsu dariyar data kamo bello ya guntse ta dan yasan hanya hanya Anwar keyi dan kar su had’u da gwaggo domino uncle ya fad’a masa cewa ya shaida wa gwaggo abinda yayi wa ‘yar ta.
***
Tafe suke a hanyar su ta dawo wa daga aiken da gwaggo tayi musu , munu ta dage se bawa Sam labarin da wani littafin hausa da wata ‘yar ajinsu ta basu take daf zasu tsallaka kwaltar titin gidan kawu kabiru ta hango wani mutumi ya shiga gidan, nuna wa munu tayi, “zo muje mu ga wane munu, kar ayi wa su umma sata”
Bin ta munu tayi suka tafi a hankali suka karkata suka shige gidan sad’af sad’af yacce baza a ji takunsu ba falon farko suka shiga ba kowa nan suka lelleqa ko ina ba alamun mutum d’akin amir suka fad’a jin kamar takun mutum, can suka jiyo wata murya na waya
“It’s cleared ma!”
Daga cikin wayar suka jiyo ance “I am very sure zasu dawo ko ba dad’e ko ba jima just don’t forget to keep an eye”
“Yes ma! Amma ya batun samira fa?”
Dariya aka kyakyace da ita “wannan ka barta har zuwa lokacin da zata mallaki hankalinta shine take me amfani, yanzu ita da hoto basu da maraba”
Firgici me sunan firgici ya kama Sam da munu suka ruqunqume juna har basu sani ba suka bigi wani flower vase ya fad’i qasa ai a guje suka maqale jikin bango se dai jinginar su ke da wuya bango ya juya dasu se gasu cikin wani tamfatsetsen closet wanda yasa lokaci d’aya Sam ta kurma wani uban ihu me tada hankali
Munu dake a firgice tayi saurin d’ora hannunta a bakin Sam “shii shii...k...iy..I shi..ru kar ..a ji mu Sam”
Ta fashe da kuka qasa qasa, hannun da Sam ke pointing tabi da ido bata san lokacin da ta fad’a baya ba har ta bige da bango,
“Shish..shine...”
Yawu munu ta had’iye da qyar idanunta kafe kan fuskar zakin dake kallo su, numfashi ta shiga saukewa a hankali ta taka a hankula zuwa wurin fuskar ta yaye saurin ja baya tayi ganin hoton ya habiibii,
Saurin kallon juna sukayi cike da mamaki Sam cikin raunanniyar murya tace “dama shi..ne “ munu ta matsa kusa da ita tare da jan hannunta suka nufi wata qofa a hankali suka murd’a key d’in jiki se gasu a waje,wajen ma dai dai layin gidan gwaggo fita sukayi da sauri ba kowa se tsirarun mutane juyawa sukayi suna kallon qofar data rufe bazaka ta’ba cewa akwai wata qofa a wurin ba a kid’ime suka shiga zabga sauri zasu shiga gida kenan su mu’allim bello suka iso.
A tsakar gida suka tarar da gwaggo suka fad’a mata suna kuka, duk suka rikita ta, menene? Me ya faru? Me ya same ku? Amma shiru ba wanda ya kulata, sallamar su Anwar ce ta sa su sassautawa
“Yawwa ai gara da kuka zo, kun gansu sun tisa ni gaba se tambayar su nake ba wanda ya kulani, dan Allah kuntayani tambayar su, oh ni haulatu”
Mu’allim bello yace “Sam, munu what’s wrong? Meke damunku?” Nan ma shiru ba amsa carpet d’in dake ajiye a gefe ya shimfid’a yana me kallon Anwar.
Anwar da duk suka qular dashi jin yanda ake faman tambayar su basu amsa ba ya ce “Idan baku had’iye kukan nan ba, ni da ku ne” cikin kakausar murya,
‘Dif kake ji wai malam yaci shirwa, ashe wargi ma wuri ya samo “ku samu wuri” sum sum sum suka zauna kusa da gwaggo yaci gaba before the count of 3 ku fad’i abinda ke damun ku.
Tar tar tar suka zayyano abinda ya faru hawaye na biyo baya tun bare Sam, hankali tashe gwaggo ta rinqa salati tana sallallami fad’i take “shikenan zaman mu a garin nan ya qare oh ni Allah ka bani ikon cin jarabawar nan taka, yanzu ace habibii ne dama ke qoqarin lalata miki rayuwa, kai duniya ina zaki damu” ta fashe da wani marayan kuka ta rungumo su jikinta
“Ba kuka zaki yi ba gwaggo”
“Me kake so nayi, bani da kowa bani da komai d’an uwana ya gujeni wannan yaran kawai nake gani naji dad’i to suma ana neman fara farautar su ina zanso kaina ni haulatu”
Qwallar data ciko idanunsa ya share “gwaggo ku tashi mu tafi”
Bello yayi saurin kallonsa, “ina?”
Gidan mu “zaman su a nan ya qare”
Ta girgiza kai “um um d’an nan wahalar se tayi yawa, ka bari zuwa gobe se mu koma can garin mu, inda muka fi wayo”
“Gwaggo dan darajar Allah ki tashi mu tafi in yaso Mayi deciding step to take next”
Kallonshi tayi ido a kod’e “kuj’e d’aki ku d’auko mana hijabai”
Qulle gidan su kayi, suka d’unguma zuwa kwairanga road.
©️Kdeey😊
DABAIBAYI👄
©️Khadija Ahmad (Kdeey😊)
WATTPAD @Deejaht ahmad
®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)
(17)
Tun daga nesa ya hango motar rannan a qofar gida, daga can baya ya tsayar da motar had’e da sauke wani gauron numfashi , “ya dai?” Bello ya tambaye shi, “ku sauka ku bi ta gate d’in baya” bello ya maida idonsa inda yaga Anwar d’in na kallo, wata baqar mota ya gani a qofar gidan wani mutumi jingine jikinta bayansa a juye, jikinsa ne ya bashi cewa ba lafiya ba, “su waye wad’ancan?” Ya furta a hankali, “abinda nake son sani kenan, har yanzu ba wani feedback daga wurin bashari ne ?”, “a a nasan da ya kira” girgiza kai Anwar yayi ya kalli su Sam ta cikin mirror had’e da sauke ajiyar zuciya a hankali yace “shiga dasu, zan bi bayan motar can” d’aga kai bello yayi ya juya baya “gwaggo bismillah muje mun iso ”
Hanci taja, ta kama hannuwansu suka bi bayansa, tsawon mintuna sha biyar sannan mutumin ya matsa ya shige gida, motar taja.
Ta wata kwana ya bi ya cimma motar a hankali yake binsu har zuwa commissioner road cikin wani tafkeken gida aka shiga, waige waige yayi unguwar shiru ba’a ji komai se kukan tsuntsaye, daga can baya kad’an ya hango wani me trader zaune yana quqqulla leda, parking yayi ya sauka zuwa wurin mutumin,
Sallama yayi had’e da fad’in “Washh Allah baya na, na gaji” buzun dattijo ya d’ago da kanshi da hausa shi da bata fita dakyau yace “sannu bawan Allah”
“Yawwa baba, dan Allah taimaka min da ruwa mana tun safiyar yau bansa komai a ciki na ba”
“Kash se de fa kayi sa’a duk masu zafi ne “ ya miqa masa sachet d’in pure water
Dariya Anwar yayi “nagode, amma baba daman talaka na samun abu me sanyi ne, rabo na da ganin ko qanqara na manta”
Kallon sama da qasa mutumin ya mishi, “kai kuwa daga ina kake haka dan shigar ka da kamanninka sun nuna kai d’in babban mutum ne”
Baki ya bud’e har da riqe ha’ba “wa d’in ni, tab lallai kace oga yayi aiki”
“Kamar yaya ban fahimce ka ba”
Gyara zama yayi, “ni sunana lawali nazo ne daga qaramar hukumar ajingi”
“To to ko kai ne sabon direban hajiya”
Jimm yayi zuwa can yace”..eh nine”
Kallon da tsohon ya masa yasa shi shan ruwan jikinsa, “...amma..”
“Uhm...riqe maganar ka inde gidannan ne wata biyu na baka zaka gudu kaima da qafarka”
Ido ya waro waje “ko zan san meyasa kace haka?”
“..kaje ka gani..” ya miqe tsaye bari na kewaya
Binsa yayi da ido yana juya maganar, tashi yayi da zummar barin wurin ya hango wani ya leqo daga cikin gidan da motar nan ta shiga , bayan wata bishiyar darbejiya ya la’be, bisa mamaki sa se ganin wannan tsohon yayi ya fito shima yana waige waige har yana d’aga wa mutumin hannu
Cikin d’aga murya mutumin yace “ina yake?”
Dattijon dake leqe leqen neman Anwar yace “yanzu na barshi anan fa, wataqila gudu yayi”
Cikin d’aga murya mutumin yace “dalla ware, ni dama nasan duk qarya ka shirya son shigowa kake, To hajiya tace ka cire wannan tsimman ka shigo ciki”
Cikin d’aga murya dattijon yace “Kai dalla malam kasan yacce zaka rinqa min magana, ni ba sa’an ka bane” ya ja tsaki, hannu yasa ya cisge farin gashin bakin sa da na jikin gashin girar sa,
“Ahhh yau tun a nan zaka tu’be, lallai kana had’uwar ka da hajiya ba zata yi kyau ba” saurayin da ada yake dattijo ya ja tsaki
ya miqe tsaye tangar tamkar ba tsohon nan ba dake dunqufe se da ya kuma wawwaigawa gefe da gefe sannan yayi wuf ya fad’a gidan suka rufe.
“Innalillahi wa inna’ilaihir raji’un” ya furta out of his breath, su wane wad’annan mutanen?, kuma wacece wannan hajiyar? Sad’ad’awa yayi ya fad’a mota ya tafi jiki a mace
***
“Gwaggo ba wai uncle ze raba ki da su bane, kina ganin dai abinda ke faruwa boarding school d’in ita tafi dacewa da su”
“Amma..”
“Kar ki damu hajiya yaran nan tamkar yaran cikina suke, saboda gudun haka yasa na yanke hukuncin tura su can UK inda Iyalina suke tare da Anwar dan qarasa karatun su, Allah barshi ke kuma se ki zauna a nan tare da bello da kuma ni har Allah yasa mu warware wannan dabaibayin se mu koma can baki d’aya”
Baki bud’e tace “barrister kaine?...”
Ya murmusa “Ni ne gwaggo, na dawo da qarfina dan nemawa Samira haqqinta da ake qoqarin qwace mata”
Gwaggo ta fashe da kuka “barrister ina cikin wani hali, a yanzu yaran nan sune kad’ai nake gani naji sanyi, idan sukayi nisa da ni ya...”
“Gwaggo nima d’anki ne, Insha’Allah bazaki ta’ba maraicin rashin su ba” cewar bello
Murmushi uncle yayi yace “nayi miki alqawari duk hutu zasu rinqa zuwar miki”
Numfashi ta sauke “shikenan na amince nasan ba zaka ta’ba cutar damu ba, you are my last hope”
Jinjina kai yayi, ta share hawayen fuskarta “Amma meye had’inka da su bello”
Kafad’ar bello ya rungumo “ya’yan wa nane marigayi”
“Allah sarki ‘yan albarka, Allah ya jiqan mahaifan ku”
“Amen gwaggo”
“kukan ya isa haka” suka jiyo muryar shi daga bakin qofa
Kallon shi sukayi duka, gyara tsayuwarsa yayi tare da takowa jiki a mace ya zube saman kujera idonsa saman nasu Sam, “ku tashi ku bamu wuri, ya nuna musu qofar d’aki
Bayan sun shige ya gyara zama had’e da tallafo fukarsa da hannayenshi,
“Anwar lafiya” cewar uncle, girgiza kai yayi tare da miqewa ya rurrufe qofa da windows, suna binshi da ido kafin ya zauna ya zayyane musu duk abinda yafaru tun ganinsa na farko da motar,
Cikin qunar rai uncle yace “yanzu kana nufin cikin yaran gidannan akwai wanda ke bada information a kanmu”
“Yeah, akwai yaron su cikin mu”
Bello ya kalli uncle “I think gara bro A ya tafi da yaran nan abuja gobe idan yaso suyi passport da visa kawai su wuce daga can”
Jinjina kai uncle yayi idonshi kan Anwar “hakane ka shirya gobe ku tafe da safe tun kan garin Allah ya gama washewa”
“Ni kuma..amma...”
Barrister yace “uhm uhm ka koma bakin aikin ka se ka rinqa kular mana dasu, nayi magana da mss chloe kan makarantar da ka sauka ka je ka same ta” ya kalli bello “Kai kuma ka shirya dan muma da safe zamu tafi garin damagaran dake jamhuriyar nijar “
“Barrister ni kuma fa?”
“Kar ki damu , bazan bar gidan nan ba face na bar miki yan sanda wanda zasu kula da lafiyarki ”
Ta girgiza kai, “shikenan kai ni gurin yarana na kintsa su tunda fitar wuri zasu yi,”
Bello ya taka mata, Anwar da uncle kua , kusan raba dare sukayi suna tattaunawa.
3:00am
‘Kishin ruwa ya farkar da Anwar, kasancewar dare ya tsala ba abinda kake ji se qarar haushin karnuka, qafafunsa ya fara s’aukarwa qasa daga bisani ya miqe tsaye seda ya duba fridge d’in d’akinsa babu ya nufi frdge d’in kitchen,
“Gwaggo yinwa muke ji” muryar su Sam ta bigi kunnen sa,
“To ya kuke so nayi muku, dan Allah ku daure zuwa gobe da safe se na bada a samo muku qosai da asuba”
“Ni...ni dai Allah kinsan fa ba za’a samu da asuba ba, wayyo zan mutu”
“Ke samira, kul kul na kuma jin kin ambaci mutuwa maza ku tashi ku d’auro alwala kuyi ta sallah yinwar zata ragu “
“What” ya furta a hankali bud’e warmers d’in dake saman dining yayi, ganin akwai abincin da cook ta dafa, tun na dare yasa shi yin hamdala saman trey ya jera har da plates da spoons ya nufi d’akin
knocking yayi, daga ciki kallon kallo sukayi, gwaggo addu’a d’auke da bakin ta ta nufi qofar
“Au Anwar kana tsaye dama, abin hannunsa ta kalla, “har da hidima haka da dare ai da ka barshi ma” a zuciyarta cewa take kar de yaji maganar da muke
Murmushi yayi yana jinjina Kawaci irin na matar yace “aa bakomai”
Hannu tasa zata kar‘ba yace “aa gwaggo barshi, kai maza kuzo ku kar‘ba kun tsare mutane da ido, munu ce ta fara zuwa ta kar‘ba, ita kuwa Sam dad’a sunkuyar dakai tayi tana dad’ matse cinyoyinta a qirji duk kunya ta kamata saboda rashin mayafi
Kamar daga sama taji yace “Ke mara jin magana bazaki taso ba” rau rau tayi da ido idonta akan hijabinta dake jikin munu ta taso, a hankali ta isa gabanshi ido a runtse ta miqa hannu ta amsa plates d’in ta juya nan ma tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki, qofar yaja ya rufe ya jingina jikin bango ido lumshe
Daqyar ya ‘bam’bare daga jikin bangon ya koma d’aki, fad’awa yayi saman gado had’e da ruqunqume pillow, ido ya rufe ba komai yake gani ba illa tafiyar Sam wacce duk takun da tayi yammatan qirjin ta ke motsawa kasancewar rigar baccin jikinta ce kawai tayi musu sutura, tsaki ya ja had’e da sakin guntuwar dariya yace “lemun tsami kenan” tashi yayi ya fad’a band’aki ya d’auro alwala ya shiga yin nafila
©️Kdeey😊
DABAIBAYI👄
©️Khadija Ahmad (Kdeey😊)
WATTPAD @Deejaht ahmad
®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)
(18)
Abinci cike da baki ta watsa wa munu hararar qasan ido, tana fad’in “wlh tunda kika sa namiji ya ganni a haka se na rama,”
a hankali munu tace, “To ba kece da gwaggo tace mu tashi muyi nafila ba, baki tashi ba, me kike dashi da zaki ‘boye masa..” ta qarashe da dariya
Takaici ya cika Sam tayi qwafa, “To wayace ki d’aukar min hijabi ko bani da komai ai mu’allim bello yace duk namijin da ba baban ka ko qaninka ba ba muharraminka bane ka kasance me killace kanka...” qwarewar da tayi ne ya hanata qarasa maganar gwaggo data kishingid’a ta tashi a firgice tana shafa mata baya, munu kuma ta bud’e fridge ta d’auko mata ruwa, daqyar ta dawo daidai, abincin da bata qarasa ci ba kenan bacci yayi awon gaba da ita.
Misalin 5:30, zaune suke suna hira Anwar yayi sallama, cikin qasaitaccen takun sa ya qarasa cikin falon daidai kujerar da gwaggo take ya tsugunna yana gaida ta, gaishe shi suma su kayi, ya amsa ba tare da ya kalla inda suke ba yace “Gwaggo akwai saqo na ajiye miki a d’aki,”
jinjina kai tayi cike da tunanin ko menene? tace “To madallah angode Anwar”
“Ku tashi muje ko” ya furta a hankali, gwaggo suka nufa ko wacce cikinsu ido ya kawo ruwa, amma ba damar kuka ganin yacce Anwar ke tsare gida,
“Allah yayi muku albarka, kuji tsoron Allah, ku kuma riqe addinin ku, kar kuga bama tare bazan kwa’be ku ba, Allah na kallon ku kuma ku ze hukunta ku gwargwadon lefin da kukayi masa” ta kalli Anwar “a yanzu ragamar kula da ku su na hannunka, gasu nan amana” ta qarashe cikin rawar murya kallonsu tayi ganin yacce suke qiqqifta ido yasa ta shige d’aki da sauri, “Allah ya sauke ku lafiya” ta fad’a daga ciki.
Da hannu ya nuna musu hanya, jiki a sanyaye suka nufi waje ko wacce na qunshe kukanta kar Anwar yayi musu fad’a, cikin wata golden d’in jibgegiyar motar Lexus Jeep suka shiga inda ya umarci d’aya cikinsu ta shiga gaba, munu tayi saurin shigewa baya ta bar Sam tsaye wacce kukan ta ya koma da biyu ga na rabuwa da gwaggo ga kuma na zama kusa da dodon ta, dan ita har firgita take idan taji koda motsin sa ne , inaga yau gashi gata?,
“Ke ba zaki shigo bane,”
Girgiza kai tayi ta bud’e ‘kofar a hankali zata rufe kenan se ga bello kamar wanda aka cillo yana haki alamun yasha gudu yace “hold on, taya zaku tafi ba sallama, ya miqa musu wasu manyan ledoji ga kaya nan idan kuka je abuja Bro A ze kai ku a d’inka muku kafin ku tafi, munu dake baya ta amsa su kayi Godiya, da baya ya koma yana Sarawa Anwar
“Drive safely bro”
Murmushi ya masa kan ya harba motar.
***
Kusan minti biyar yana duba takaddar ba dan be fahimci abinda ke rubuce ba, se dan son tabbatar da abinda ke jiki shin ya take me?, wayar Anwar ya kuma trying for the fifth time in taqi shiga, bello ya fad’o masa a rai dialling wayarshi yayi ringing biyu ya d’aga
“Babban likita na Rayya bada kanka a sare..”
One sided murmushi yayi “Abokina Ina Yayanka?”
Bello yace “yana daf da shiga Abuja”
Duka ya kaiwa bango, yana to and Fro yace “ ya Allahu I really need to see him why did he left ba tare da sallama ba, when is he coming back?”
“Well May be in a year or two”
Da qarfi hasheem yace “what! Ze wuce UK ne, uncle ya sani?”
“Yeah shi yace ya tafi da su Sam”
“Sam kuma?! Ahhm ahh...is all right ina zuwa” yatsunsa biyu yasa saman goshi yana murzawa, kan ya zube hannuwansa saman table yana girgiza kai ya kalla agogo 11:45am key ya d’auka da wayoyinsa ya fita bayan ya barwa sakatarensa sallahun kowa yazo ace ya fita a dawo da yamma.
***
Driving yake amma hankalinsa baki d’aya na kan wayar sa dake haske ba damar dauka.
Juyawa tayi cikin lafiyayyen baccin da ya d’auketa tun barinsu kano, Mafarki take gata kwance saman gadon ta gefen ta daddy ne kwance yana kallonta a hankali tashiga bud’e ido
“Morning daddy” ta furta murmushi d’auke a fuskarta,
Gyara zaman medicated glasses din idonshi yayi
Yace “morning mami” yayi pecking goshinta, hannu tasa ta maida cincinrindon gashin kanta baya, ta matsa kusa da shi tare da d’ora kanta saman kafad’arsa ta rungume hannunsa a jikinta,
“Have you saw him?”
‘Daga ido tayi tana kallon fuskar daddyn tace “who?..”
Murmushi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 13