hankali, chan kuma Ta fara yar dube dube cikin yar jakar bako Dinta, "Momma Na kan Kujera se kallon yarinyar Takeyi, ji take yarinyar ta shigan Mata Zuciya Tana Sonta..
"AFRAH kuma daga kitchen Ta fito dauke da wani plate shinkafa da taliya da miya se manyan Namomi Kake gani a Sama _Nasan wasu har sun hadiye miyau Lolx_ karasowa tayi ta ajiye plate din agaban Xeey, Xeey ko na gani tun kan ace mata taci ta fara Ci hannu bak'a hannu kwarya, Afrah kam na gabanta kamar yanda ta Saba in tanacin abinci har se ta gama sannan zata tashi,
"Momma kam duk tausayinta ya kamata se Allah sarki take tacewa... Pallow din shuru yayi Afrah da mummy kowa se sak'a abu yakeyi a Mind Dinshi dan Tausayin *Xeey*, "Momma ce tace Afrah Tunda ta Gama Cin abinci maza ki kaita Daki ki temaka mata da wayau ta chanza kaya dan wannan dakyar zata yarda Ai mata Wanka, Haka ko Akai Xeey ce ta kamo hannunta suka Shiga Daki Tai mata dibara ta chanza mata kaya, aka fitar da na jikinta chan waje akasa a bola, D'an chanza kayan datai har tai kyau Sosai kamar ba itaba, Xeey kam ba un ba um um se kallon dakin dai take tayi abunka Da Mara magana,
__"Bangaren ismail kuwa tun randa Su musaddiq yabar school din yajishi unconfortable, dan yayi missing dinshi sosai yace inama nine naje naija da wallahi ko zan salwantar da rayuwatace Se Naga Xeey, Allah sarki Memo dinnan ya dakko Ya fara Dubawa, yana ganin tinaninta zai dameshi yai maza ya ajiye memo din ya fara wani abu daban dan kawar da hankalinshi daga tinanin Xeey, dan inba haka yayi ba to yau akwai Kasa Bacci lolx...
"Da daddarene Wani Matashin Saurayi da bazai wuce 29years ba sanye da wata Yar Polo shirt da Wando se lapcot a Rataye a kafadarsa, hannunsa rike da wasu books na doctors, Shuguwa pallow din yayi daidai Lokacin da Xeey ta Fito daga room dinsu, Hada ido sukai da wannan guy din xeey ta koma daki da gudu ta fada Kan Afrah,
"Afrah mikewa tayi ta fito pallow dan ganin waye, yayanta tagani a tsaye ya kura mata ido Yace Sist waye wanchan ta shige dakinki kamarfa mahaukaciyan da nake Gani A chan Bola, "Afrah tace Bro wlhi she's The One ni nace mummy a dakkota dan tausayi take Bani Wallahi,
"Bro din Afrah ya taba baki yace to manya, iyayen tausayi ke kin ciki iyayi wallahi, idan ba mutun bace kuma fa? "Afrah Tace seta cinyemu,
"Bro yace tab ta cinyeki dai naga har dakin ki kika sata, Yana magana yasama waje ya Zauna, ya kara da cewa Please my sist get some water for me, "Afrah tace ok, Taje frigde ta dakko mai ruwa me Sanyi ta bashi, zata tafi kenan Yace Sist Wait! "Afrah ta dawo ta zauna Yace Look Dont be a victim fa *DAGA TAIMAKO* Ki jawowa kanki bala'i *LITTAFIN SISTER SADNAF* Nan Afrah tadanyi shock dai tace na shiga Uku!
"Bro yai dariyar mugunta Yace no Ki tsayar da xuciyarki waje daya Allah zai temakeki, "Nan hankalinta Yadan kwanta suna hira Kenan sega Momma ta fito itama tai joining dinsu suka ci gaba da hira, BRO NE yace mum naga munyi bakuwa Allah Yasa alheri ne dan ni tsoron irin mutanan nan nakeyi wallahi "Momma tace uhm Ameen dai Afrah nima dazu nake tinani tayi karambani amma Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu sukace ameen nan dai Bro yaci yasha ya koshi sannan ya koma Part dinshi, Around 10 ya kwanta dan ya gaji yau sosai sunyi aiki a hospital dinsu,
"Afrah kam tun Maganar da Bro dinta Ya fada mata Kar tasama VICtim din *DAGA TAIMAKO*
Ummiey XEEY
[11/7, 6:55 AM] Ummiey Xeey Abakson💋: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛
```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson💋*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]
*LIKES AND DROP YOUR COMMENTs*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM😍*
*📄PAGE 49__50*
"Afrah Kam tun maganar da Bro dinta ya fada mata karta Zama Victim din *DAGA TAIMAKO* Yasa Data Shiga Daki Phone dinta Ta dauka ta shiga cikin Audio Tai Playing Din Suratul Baqra dan neman kariya daga sharrin mutun da Aljan, Tun tana bin karatun har bacci ya kwasheta ita ma Xeey taji d'omin bargo tuni tai bacci....
*WASHE GARI*
"Afrah ta tashi da wuri tai wanka ta maida ma y'ayanta Ruwa a kettle Din shima yayi sannan taje ta hada mai breakfast dan yace yau Sunada aiki da yawa a hospital dinsu dan haka yana gama cin breakfast Ya fita yayi Office.. "Afrah kuma bayan tafiyarshi ne Ta karasa wani ruwan a kettle Bayan yayi Zafi ne ta juye takai toilet, Sannan tazo ta lallaba Xeey har ta kaita toilet ta wanke mata kai duk a dunkule dama a tsefe yake, Tai mata wanka sosai sosai sannan ta kamo hannunta suka fito daga toilet din, nan dai Ta samu ta shafa mata Mai sannan ta gyara mata Gashi, ta sama mata wata doguwar Riga then Ta kawo mata abinci taci sannan ta rike hannunta sukai dakin mummy,
"da Shigar su mummy tace Lalle Afrah Yar albarka sannu da kokari ji yanda kika gyarata kai amma Allah ya saka miki da Alheri sweet heart tace ameen momma, Itadai Xeey ba abun da take in banda KALLON mutane....
*B*angaren Hajiya Sa'adatu kuwa yanzu da karfin Asiri mijinta ya manta da komai nashi tun daga kan dukiya, da wata xeey balle matarshi da abba, Da yan uwanshi, Tasashi a gaba se yanda tai dashi, hatta Dan fitan da yake dan dai Karta rasa na kashewane kuma Idan ya samo ita zai kawomawa amma da tuni na hanashi Yi, Yanzu duniya na mata dadi se abun da tace harta yan aiki duk ta koresu wasu ta kawo masu goya mata baya, dan Sauran Bazasu yarda da abubuwan da takeyiba sai yasa,
"Alhaji Dai Ya Zama Mijin Hajiya na Gaske dan Jan akalarshi take yanda Takeso bama yanda ya kamata ba.....
"Alhaji Ma'aruf kuma Mahaifin su Afrah ya dawo yaga Xeey bece Komai ba shima Illa tausaya mata dayai, Haka suketa rayuwa dukkansu sun dauka Xeey tamkar yar cikinsu, Dan kome Zai siyo tare yake siyo musu.... Akwana a tashi ba Wuya Wata shakuwace ta kullu tsakanin Afrah Da Xeey duk da bata Magana amma Har cikin Ran Xeey tana Son Afrah, Bro kuma Xeey ta maidashi tamkar abokin wasanta idan benan Kofar dakinshi Take Zuwa har se ya dawo ya bude mata kofar ta shiga Sometimes ma idan yana Bacci ta shugo sedai Ya barta a dakin ta karace watsawarta dan na farko ba barna zatai mai ba, Kuma ba sata zatai mai ba, dan haka be damuwa, Ko frnds dinshi idan sunzo suka ganta kowa sedai ya tausaya mata dan kana ganinta Kasan da walakin goro a miya....
"Akwai wata ranane Bro Ya dawo daga Hospital ga ba kowa a gidan Afrah na Exams momma kuma bata nan tana gidan biki, Bro.... Ne ya shugo yaga Xeey a kofar dakinshi ta kwanta yace Allah sarki, Tsallekata yayi yaje dakinshi Ya kwanta yaji yunwa, Tuni ya fito Ya shiga kitchen ya fara dafa indomie, Be ddeba ya gama Yasa a plate ya dawo daki ya zauna kenan Yaga Xeey a gabanshi har tasa hannu ta fara ci, Tsayawa yayi yaga yanda take cin indomi din da Sauri, "tausayinta ya kamashi har da yar kwallanshi, nan take ya fara tinanin Wai anyama taci abincin rana? Gashi har yamma tayi, Phone Dinshi ya dauka ya fara dialing din number Afrah... Ringing biyu ta dauka, tana gaisheshi be amsaba yace Rabonki da gida tun yaushe? Tai kasa kasa da murya tace since morning muna exams ne fa Bro,
"Daka mata tsawa yayi yace Kuna exams kinsan zaki wahalar da yarinyar mutane meye na dakkota
Kin barta da yunwa, me yasa kike hakane?
"Afrah Tace i'm sorry bro ba haka bane bansan zan dadeba ba wallahi yace shiiiii..ya kashe waya, Afrah kam gabanta se fadi yakeyi tana tashiga Uku, "Yana gama call din K'ura ma Xeey ido yayi se loma take tayi abun tausayi Indomie dakwai2 amma har ta cinyeshi befe loma ukuba, Tana gamawa Ta sama waje A dakin tai kwanciyarta, Shima Tinani ya fara Dan yunwar ma gaba daya ya nemeta Ya rasa dan tausayin Xeey....
"Yana kwance akan gado Xeey na kasa yai yar karamar tsaki yace mtsww wannan ma ba tsari bane bari na Fita dan shaidan nanan yana yawo, wata Zuciyar tace to me zakai da mahaukaciya wata zuciyan tace kayya Kaidai kawai ka fita dan haka Ya dauka phone dinshi da mukullun bike (Mashin) dinshi ya fita zaga gari yau nace BOSS ba a son fita da Mota ne Lolx.....
Wajen shakatawa ya nufa achan ya sama abu Yaci sosai but hankalinshi na wajen Xeey.. "Afrah tana hanya se tinanin fadar Bro dinta dazata tadda take tajin tsoro, tinani takeyi har ta Karasa gida, tana shiga taga Kofar Shi a bude wani tsoro taji amma ta daure ta shiga tana zuwa taga Xeey akwance, kiran yayanta tayi taji shuru, nan ta dauka waya ta kirashi tace bro gani a gida..
"Yace harkindawo ya exams din tace alhmd, yace nadan fitane tunda barin mutane da yunwa kukeyi, Tadan wayince tace no kayi hakuri, "yace is Ok. Da sauri ta nufa kitchin itama dan dafa Musu abinci gaba daya gidan, Taliya ta daura sannan taje tai wanka ta fito, time din ya daho ta zobo a plate ta kawo ma Xeey dakin Bro ta tasheta zata bata Taga xeey takice, tai tai da ita ta bata ina Xeey taki ci,
"Afrah tafara tinanin ko zatayi xuciyane, dan batasaN Bro din ta ya bata ba...
Xeey kam tak'i ci,
"Afrah kam zama tayi ta shara taliyarta me dadi nan itama ta baje a wajen se baccin Gajiya, "Bro dinta kuma yaje ya dawo ya gansu duka a dakin, Afrah ya tasa, ita kuma ta tashe xeey nan dai suka bar mai Dakin Se mamakin Afrah yake, Yace kai mata se ahankali wata sa'in da me hankalin wato Afrah da mara hankalin Wato Xeey duk Sun Wani zo sun kwanta maka a daki yanzu da da abokina nazo fa? Yace Allah ya kyauta...
Koda suka Koma part dinsu duka bacci suke tayi se gab da magrib Mummy ta dawo ta gansu duka akwance har gabanta yafadi seda ta tabasu taga suna nunfashi Sannan tace Alhamdulillah ku tashi magriba yayi nan Afrah ta tashi ta tashe xeey, ita taje tai Alwala tai Sallah xeey kam nanan Zaune ba un ba un um,
"momma da xeey basu suka tashi daga kan sallayaba har seda Akai ishai sukai addu'o insu sannan
Mummy ce tace wa Afrah ta dauko mata goran ruwa da cup
*Muje zuwa*
Ummiey XEEY
[11/12, 9:48 AM] Ummiey Xeey Abakson💋: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛
```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson💋*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]
*LIKES AND DROP YOUR COMMENTs*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM😍*
_Make a relation with someone, who is not only proud to have you but will tare every risk to be with you._
*PAGE 📄 51 52*
"Mummy ce tace wa Afrah ta dauko mata goran ruwa da cup tana kawo wa mummy ta fara karanta suratul Fatiha, Ayatul kursiyyu da ayatushshifa, sannan ta karanta aya ta 80 da ta 81 ta suratu Yunus ta lalata sihiri tana gama karantawa tace Afrah ki bata tasha sannan ki shafe mata jikin ta da sauran.da kyar Afrah ta samu *Xeey*tasha tana gama sha ta fara zare zaren ido ta sai kuma ta fashe da kuka har bacci yayi awon gaba da ita dakyar suka samu suka kaita bedroom Afrah tayi mata addu,oi ta rufe ta da blanket.
*CIKIN DARE* cikin bacci Afrah taji ana kokarin bude kofar dakinsu bude idan da zata yi taga Xeey ce keson bude dakin ta fita cikin saurin da ko ita bata san tana dashi ba ta isa bakin kofar ta sanya karfinta gaba daya ta janye *Xeey* daga jikin kofar tasa key juyowar da zata yi taga Xeey ta kwanta a kasa tana burgima tana yayyaga kayan jikinta "kuka me karfi Afrah ta saki cikin tashin hankali ta lalubi wayarta number big bros ta latsa ta gaya masa abinda yake faruwa saboda bata son ta tashi mummy a tsakar dare tace yazo ya taimaka yayi wa Xeey allurar bacci bata fi 3 minutes da ajiye wayar ba sai gashi ya iso da kyar aka samu akayi wa Xeey allurar kasancewar ta birkice tana ta buge buge bakinta yana ta motsi kamar me son fadin wani abu baifi 5 minutes dayi mata allura ba kasala ta saukar mata da wannan damar Afrah tayi amfani wajen biya mata Ayatul kursiyyu a kunnuwanta har bacci me nauyi ya dauke ta hamdala Afrah tayi ta koma ta kwanta.
__ knocking din data ji anayi shi ya farkar da ita mummy ce ke cewa Afrah kin makara fa yau har 6:00 o'clock baki yi subhi prayer ba tashi tayi gami da tattaki zuwa toilet ta daura alwala sannan tayi sallah sannan mummy ta bata ruwa Wanda aka karanta suratul bakara, fatiha,falaqi, Nasi, laqada ja,akum Wanda aka dandaqa ganyen magarya guda bakwai cikinsa tace ta shafewa Xeey jiki dashi karbar ruwan tayi ta fara shafawa Xeey kamar wadda aka mintsina haka ta tashi tana kokarin zubar da ruwan mummy ce ta rike ta tana karanta mata ayatul kursiyyu a kunnuwanta nan take kasala ta zo mata tayi luf ajikin mummy kamar ba itace take buge-buge ba bacci me nauyi ne yayi awon gaba da ita wanda ko breakfast bata samu taci ba sai around 12:00 o'clock.
*Bangaren* Isma,il kuwa kwance yake yana bacci mafarkin Xeey yayi ya ganta acikin wani katon rami mai xurfi tana ta miko masa hannu tana kiransa *isma,il Isma,il Isma,il* yayi kokarin zai jawo hannunta sai kawai duhu ya raba tsakanin su yana jin kukanta amma baya ganin ta, kuka me karfi ya saki Wanda yayi dai dai da farkawarsa fuskarsa cike da hawaye yayi sharkaf da gumi duk da AC dake kunne a dakin da sauri ya sauka kasa ya fara kuka me karfi yana kiran sunan Xeey kamar wanda aka tsikara tashi yayi ya dauro alwala ya fara nafila ya ringa yiwa Xeey addu,ar neman kariya yana rokar mata mafita a wajen Allah bayan ya kwanta bacci kaurace wa idon isma,il yayi sai juye-juye yake yana tunanin mawuyacin halin daya ga Xeey aciki kara fashewa yayi da kuka.
*H*ajiya Sa,adatu ce da daddy ke sauko wa daga step suna hira da daddy tana fari tana kasa da murya tace Alhajina da badon karka ce na fiya fitina ba dana dan nemi wani abu a wajen ka washe baki yayi tare da cewa banda abinki me zaki nema da nake dashi na hana ki kome kike so fadamin zan miki shi dama ba wani abu bane so nake ka.................
Sun kuyar da kanta tayi cikin kissa ta fara fadi ina son ka bani 50.3million ne dama zanja jari dariya Alhaji yace dama ke dan wannan kike tada hankalin ki brief case dinsa ya jawo ya rubuta mata cheque ya rubuta mata 60.5 millions ya mika mata tana gani ta gigice rungume shi tayi tare dasa tafin hannunta cikin nasa tana murza wa ta fara magana Alhajina bani da kalmar da zanyi maka godiya sai dai nace Allah ya kara mana dankon soyayya toshe mata baki da hannunsa yayi yace Menene abin godiyar wajibi na ne na kyautata wa iyali na, fari tayi da ido tace Alhaji tashi na raka ka driver na jira
Karka yi late yana mikewa ta kara narke masa tare da lumshe idon ta mai kama da bantaren mudubi lol kalmomi take furtawa kamar haka *I LUV YOU WITH OUT YOU MY LIFE IS OUT OF CONTROL* to ko na dawo dai na fasa fita ne Dan naga yau soyayya ta tashi, fari da idonta ta sake yi tace a a Alhaji yi tafiyar ka babu komai.
Ummiey XEEY
*_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛
```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson💋*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]
*LIKES AND DROP YOUR COMMENTs*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM😍*
Dedicated to *IDON MIKIYA WRITERS ASSO🦅* YOU GUY'S ARE AMAZING❤
*PAGE 📄 53__54*
*I LUV YOU WITH OUT YOU MY LIFE IS OUT OF CONTROL* "to ko na dawo dai na fasa fitar ne", A cewar Alhaji, sa'adatune ta wani sake murmushi hade da cewa" yi tafiyar ka babu komai.
yana tafiya ta kira Aminiyarta ta shaida mata abinda Alhaji ya bata shewa yalwa ta saki tace gani nan zanzo a bani rabo na, "Maganar yalwa ta b'atawa Sa,adatu rai amma saita hakura saboda yalwa zata raka ta wajen wani boka, Ba' dauki lokaci mai tsayi ba sai ga yalwa ta iso haka, Sa,adatu ta cikata da kayan kwalama da mak'ulashe sai da taci tayi Kat sannan "tace Sa,adatu dauko min rabo na, Sa'adatu ranta Adan bace tace" bari nayi miki transfer na 1million
"yalwa ta d'an bata rai tace haba ina laifin 2 million kinga wahalar dana sha wajen binne abubuwan da Boka ya bayar da wanda yace a boye inda wani bazai gani ba koya taba haba sa,a
" Sa'adatu tace To yalwa bari na baki 2 din a zuciyarta kuma tana fadin kinci na karshe don da Kaina zan rinka tafiya ko don sirri na
********
"Xeey ce kwance a bedroom tana ta sharar baccin ta mummy ce ta shigo da garwashi a hannunta ta zuba Habbatussada ta turarawa Xeey, Wani zabura XEEY tayi ta mike tana shirin kuka, mummy CE still ta r'ikota ta fara mata adduoi sannan ta samu ta lafa, abun yaba mummy mamaki sosai, tace dole mu dage da addua Dan da alama Zamu sama nasara sosai
*********
*After 4months* haka DAI aketa adduo ana samun nasara sosai sedai Xeey bata magana is like abun ya taba mata brain sosai, Afrah kam yanzu ta tafi service komai mummy ke mata se big bross yana Dan temaka mata abun da be gagaraba
__Ismail kuwa ya dawo hutu, tun da ya shugo garin yaji bemai dadi sosai Dan yasan ba ganin Xeey zaiyiba, koda ya shugo area dinsu ya shiga gidan mummy tamai oyoyo ta kawo mai abinci yaci yashiga toilet yayi wanka ya fito ya shirya yasa wani light blue shadda yayi kyau sosai..
Pallow yazo ya zauna ya dakko remote ya r'ike, mummy CE ta shugo ta sameshi taga yayi shuru da alama ya sunduma cikin tinani, "mummy CE ta kora mai ido ta tausaya mai sosai Dan tasan sure! He's thinking of Xeey..
"Dafashi tayi tace look my son, Dan Allah kayi hakuri, I told you several time's without number nace ka rage tinani ba abun da zai karama sedai cikin kai, just be praying for her, Allah ya hadata da alheri a duk inda take,
"Ismail ne yayi wani ajiyar zuciya yace Hakane mum, wallahi ADALILIN da yasa kikaga INA yawan tinata shine when I was in school INA yawan mafarkintane, kuma ba'a yanayi najin dadi nake ganin taba sai yasa,
"Tunda yake magana mummy idonta ya cika da hawaye Dan tasan Sabon da sukai da ita sai yasa take tausayamai, " tace nasani my love, nima zanci gaba da tayaka da addua, ai Xeey tamuce so please ka sake ranka insha Allah nima zan temakama wajen tayaka Neman inda take ko a Raye ko amace _Mummy ta fadamai wannan maganar ne Dan kwantar mai da hankali Dan ita Sam da za ace ta nemo inda Xeey SUKE bata saniba_
Wani murmushi Ismail yayi Dan ba karamin jin dadin maganar mahaifiyarshi yaji ba, yace thanks mum I'm proud of you, itana tai smiling tace me too Allah ya k'ara tsaremun my son "yace Ameen mum
Kwanar Ismail biyu, Kullun seyayi dialing number room mate dinshi na school, *musaddiq*
Yauma Zaune yake a pallow yana shan coffee dayar hannunsa r'ike da phone, dialing number musaddiq yayi again yaji abun da ya tsana _the number you dail Does not exist please try again letter_ yani tsaki yaja yayi da shuguwar mummy, har gabanta ya fadi tana Allah yasa ba Xeey ya tinoba,
Zuwa mummy tayi ta zauna kusa dashi tace my love meke faruwane naga kana tsaki, " Ismail yace wallahi mum number din frnd dinnan nawane na kira naji be shiga shine abun ya batamun rai, Mum tace eyyah sorry kuma bakasan address dinsuba ko?
"Ismail yace wlhi mum da na sani zuwa zanyi direct saidai ya ganni, mummy tace Hakane kaka damu please, Ismail yace lol mummy bazan damuba tunda muna gari daya sure wata rana Zamu HADU.. Tace Hakane nan DAI ya gama shan coffee dinshi ya fito wake zai zaga gari,
_yana fitowa yaga normal joint din da suke tsayawa da Xeey wani hawaye ya zubo mai nan danan yaji kanshi ya fara ciwo, be samu yaje inda zaijeba ya dawo gida ya kwanta kanshi Nata ciwo
*Ummie Xeey CE*
[1/3, 8:30 AM] UⓂmiey Xeey👄: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛
```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson💋*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]
*LIKES AND DROP YOUR COMMENTs*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM😍*
*so sorry dear fans for d delay nd long suspence,in shaa Allah it has come to an end,u will be seeing my updates regularly luv u oll.💙💚💛💗💞❤🖤*
*PAGE📄 57__58*
"kamar a mafarki ta ganta a dakin da bata san ya akayi ta shiga
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 14