shiga da sukai kuma sun shugo inda mutane ke yawan zuwa, Allah ka Shirya mana!!
Abincin kan table din da suka kawomai ne baiciba, ganin bakowane yace" Bari naci na banza ai ba aikensu nayiba, yaci ya koshi sosai, sannan still ya fada kogin tinanin xeey, nan danan yaji kanshi ya fara ciwo, kafin zazzabin yai zafi ya lallaba ya kai kanshi wani babban asibiti Dan dubashi.
Yana Shiga Aka nuna mai dakin da zaiga *DOCTOR*
Sallama yayi, doctor din ya amsa *(yayan Afrah)* ido hudun da suka hada tuni bro din Afrah ya m'ike yace Isma'il?
Isma'il ya amsa" da Musaddik
_Musaddiq yayan afrah ne da sukai school tare da Isma'il Wanda Isma'il ya dawo daga Egypt yana ta nemanshi...Ikon Allah yau Gashi sun hadu_
Tasowa Daga kujarar doctor yayan Afrah (musaddiq) yayi yazo, bashi hannu yayi suka gaisa hade sa rungume juna, Isma'il yace long time?
Musaddiq yace Alhamdulillah wallahi ba inda ban nemekaba I thought mafa baka dawo ba!
Ismail yace" wlhi nima nima na nema number ka na rasa, nan dai suketa hiran bayan rabuwa, gwanin sha'awa
Isma'il yace kayi aure ne? Musaddiq yace aa I'm still searching dai kaifa? Yace me too, sannan yace meke damunka? Isma'il yace wallahi ciwon kai nakeji ga zazzabi, nan Dr musaddik yama Isma'il allura sannan ya bashi magunguna, kuma yake sanar dashi anan yake aiki, Isma'il yace wow namaka Murna, Nima dai inanan INA nemane,
Musaddiq yace aiko ana Neman babban likiti irinka, I'll talk to them ansamu, Seka bani number ka, Isma'il yace wow ammafa Thanks wannan fitar nayi sa'a
Musaddik yace Lol Sosai ma kuwa, nan sukai exchanging number sannan Isma'il ya kama hanya se gida ciki da farin ciki,
Shima musaddiq yayi matukar farin cikin haduwa da amininshi na school..
Tun daga Bakin gate Mummy taji Ismail yana Kiranta mummy, Mummy, Mummy CE ta fito tana mamakin Isma'il kamar wani yaro yana kiranta, karasowa tayi tace" lafiya naga se kwalamun kira kake?
Isma'il yace" lol my Beloved mummy yau INA cikin farin ciki, mu shiga ciki, mummy girgiza kai tayi tace wannan yaron, zama sukai a pallow Sannan mummy tace'' wani farin ciki kake ko labarin Zainab ne??
Ummiey_Xeey
[1/3, 8:30 AM] Uβmiey Xeeyπ: *_ β°°β’β’~β£_πβ’β’ππβ€π
*A DALILIN MATARββββ*
*UBAββββ*
*_ β°°β’β’~~β£_πβ’β’ππβ€π
```ββββββββββββSTORY & WRITTEN BYββββββββββββ```
*ββββUmmiey_Xeey Abaksonβπβββ*
*βββββ»EXCLUSIVE WRITER'S FORUMββββ*
_[Ι¦Φ
ΚΙ Φ
Κ ΦΙaΔΙ, Ι¦Φ
ΥΌΦ
ΚΚ aΥΌΙ sΚΦΙΚ Υ‘ΚΙ¨tΙΚ's]_
*ββLIKES AND DROP YOUR COMMENTsββ*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
```βββββββββSADAUKARWA GA____βββββββββ```
*ββββMARIAM TIJJANI ADAMβπβββ*
_Dedicated this page you my dearest sisters_
```Ruqeey CE,
Nasbash
my Mareeya,```
*I love you plenty _# Ana Tare_*πππ
*PAGE 77__78*
Wani farin ciki kake? Ko labarin Xeey dinne?
Isma'il yadan yi murmushin da bekai cikiba, Dan beson ma hiran xeey hankalinshi tashi yake, yace" no mummy INA wannan friend din nan nawa da nake ta nema banda contact dinshi? Mummy tace" Aww eh na tinashi, yace" yauwa yau muka hadu dashi wlhi naji dadi har yacemun anan Neman ma'aikicin Asibiti, Mummy tace Alhamdulillah, Allah yasa a dace Yace Ameen mummy nah,
Kallo ya farayi, mummy tace" gafa abincinkanan kan dining, Isma'il yace OK mummy zanci amma yanzu Alhamdulillah, Tace shikkenan, anjuma ma babanka zai dawo, Yace" Masha Allah, Allah ya dawo dashi lafiya..mum tace" Ameen
*********
Bangaren Sa'adatu ita yanzu hankalinta a tashe, yanzu kwata kwata Alhaji be mata magana, yana bata abinci da duk hakkinta na aure, amma shi kanshi yasan he's missing something, ko yaje office a tattare da damuwa yake, A gida ma haka, shidai kawai rayuwa yakeyi amma besan mekamai dadi ba, ko zaune yake ya tsundamu cikin tinani se ya fara tinanin Matarshi, sai kuma ya hargitse yaga kamar mafarki yakeyi, Hankalin Sa'adatu ba karamin tashi yakeba, kawai k'arshe ta take jira, yanzu dukda ta chanza wajen boka amma ba abun da take gani na ci gaba, Dan ba karamin addua ake yi mata ba ta ko INA amma duk bata saniba, yanzu bata da wani power duk tayi sanyi kamar tsohuwar munafuka!!
Bangaren Mariam Tijjani kuwa, addua ba rana ba dare, kullun setayishi, kuma rana dai dai ne bata mafarkin xeey, tana yawan fadawa mai gidanta, Yace" taci gaba da adduan, shima jikinshi yana fadamai Xeey na Raye, k'ara kwantar wa Mariam da hankali yake,
*Musaddiq* ne a office bayan sun gama aikin da zasui, around 4pm ne ya koma gida! Shima tare da farin ciki a tattare dashi, da shuguwarshi, Afrah ta kalleshi tace" oyoyo yau me aka samo mana naga se smiling ake ko anyi mana aunty ne? Xeey kam kallonta tayi tana mamakin Afrah!
*Bro musaddiq* yace see you, Afrah tai dariya, yace" Sister Xeey sannu, Halan se damunki da surutu takeyi ko?
Xeey tace aa bro your welcome tace" thanks sannan ya shiga ya gaishe da mummy, ya fito ya wuce part dinshi yai wanka yasa wani Wanda 3quater da yar karamar Riga yamai kyau sosai, bayan ya kintsane yazo yai joining din su mummy a tsakar gidan under wani bishiya dake cikin gidan nanfa suka fara hira SOSAI, Har yake sanar wa mummy yau ya hadu da wani frnd dinshi amma be fada sunansaba, yace mun Dade bamu hadu ba tun muna school yau Gashi mun hadu, Mummy tace to Alhamdulillah, Allah ya barku tare ya k'ara kareku da Sharrin mak'iya yace Ameen, basu suka bar wajen ba se gab da magrib, bro ya tafi sallah, su ma sukayo daki sukai alwala sukai salla basu suka mik'e kan sallayaba seda sukai sallan ishha'i Dan haka ka'idar su take, Idan sungana magrib basa tashi, addu'o'i suke Sosai Se sunyi Ishha'i sannan su tashi,
*After one week*
Haka rayuwa taci gaba da wakana ta ko wani bangare, *Isma'il* ne kwance a daki phone dinshi yaji yana ringing dubawa yayi yaga *Dr Musaddiq* yayan afrah, picking yayi hade da Sallama, dayan bangaren aka amsa, musaddiq yace my bro congrats, kasama aikin, but yanzu inbaka komai kazo da takardunka, Wani ihu Isma'il ya sak'i yace awwn I'm speechless, Bansan mezance makaba, thanks sedai mun hadu, musaddiq yace" OK frnd!
*Isma'il* ne ya fito pallow ya tarda mum n dad dinshi, nan yake basu labarin yanzu abokinshi ya kirashi wai yakai takardunsa, Farin ciki karara ya bayyana a fuskar su, Sukace Masha Allah, Allah ya temaka yace Ameen nagode maku, INA alfari daku, kuma da bazarku nake taka rawa! Daddy shafa mai kai yayi yace Isma'il Allah yasa albarka, Allah yasa a dace yace Ameen sannan ya fita
Yana fita car dinshi wannan karon ya dauka be zarce ko inaba se Asibitin, yana Shiga, kiran Dr musaddik yayi yace" gashinan ya shugo, ba' a wani bata lokaciba Sega Musaddiq ya fito yamai kwatancen inda yake yazo ya shiga dashi!
Direct office din babban Dr din sukaje, bayan sun gaisa, ya bashi takardunshi, nan take akamai inter view yaci, babban Dr din yace CONGRATS kasamu, Isma'il godiya yamai sosai, sannan yace Zuwa Monday ya shirya ya fara zuwa aiki, sannan suka fito a office din!!
Isma'il tsayawa gun musaddiq yayi seda yagama aikinshi sannan
Isma'il yace muje nai dropping dinka a gida, musaddiq yace dako nagode, yau kasala nakeji bazan Iya driving ba sai yasa ban dakko ko da bike ba, Ismai'l ya kalleshi yace lazy guy, musaddiq yace eh naji dai....
Suna tafe suna hiransu har Sukazo kafoar gidan su musaddiq, Musaddik yai yai dashi yace ya shugo yace" Zaizo dole gaishe da mama amma ba yanzu ba, musaddik Yace" OK shikkenan ka gaishe mun da mummy nah....
Ummiey Xeey
[1/21, 10:34 PM] Β©REAL UMMIEY XEEY: *_ β°°β’β’~β£_πβ’β’ππβ€π
*A DALILIN MATARββββ*
*UBAββββ*
*_ β°°β’β’~~β£_πβ’β’ππβ€π
```ββββββββββββSTORY & WRITTEN BYββββββββββββ```
*ββββUmmiey_Xeey Abaksonβπβββ*
*βββββ»EXCLUSIVE WRITER'S FORUMββββ*
_[Ι¦Φ
ΚΙ Φ
Κ ΦΙaΔΙ, Ι¦Φ
ΥΌΦ
ΚΚ aΥΌΙ sΚΦΙΚ Υ‘ΚΙ¨tΙΚ's]_
*ββLIKES AND DROP YOUR COMMENTsββ*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
```βββββββββSADAUKARWA GA____βββββββββ```
*ββββMARIAM TIJJANI ADAMβπβββ*
Alhamdulillah I'm back again...sorry readers da jina shuru da kukai....yanzu by god grace zaku dinga samun post dina akai akai
*Dedicated to All my lovers*π
*PAGE 79__80*
*After two weeks*
Haka rayuwarsu ta kasance kullun cikin daukin juna daba juna shawara suke,
Musaddiq ne zaune akan kujera ya kalla Isma'il yace aboki let's go naga time din tashinmu yayi, nan suka harhada books dinsu na doctors suka sa a jakarsu sannan suka mike suka wuce inda musaddiq yayi parking!
Suna tafe suna hira har musaddiq yakai Isma'il gida, ya fito shima ya shiga gidan yagaishe da mum din Isma'il nan tai musu nasiha akan su rike aikinsu kuma kar su bari wani ya shiga tsakaninsu
Musaddiq yace" insha Allah hajiya, bari nazo na tafi, tace" ok ka gaishemun da hajiyarku d sauran yan gidan, Yace" ok
Isma'il ne ya rakashi har bakin gate seda yaga ya saita hanya sannan ya shugo pallow, koda ya shugo room dinshi ya wuce ya cire kaya sannan ya shiga wanka yai alwala Dan time din magrib yayi
Bangaren musaddiq kuwa Yana shiga gida shima wanka ya shiga yai alwala Ya wuce masallaci, bashi ya shugo gidan ba seda yai isha'i, Yana shugowa direct pallow ya wuce, Mummynsu Na ganinshi tace" Dan Halak kaman kasan kai su Afrah da Xeey suke jira
Musaddiq yace" to gani Allah dai yasa Lafiya, be karasa maganarsaba se gasunan sun fito daga room dinsu, Xeey na tafiya a tsanake Afrah kuma Dan murna da gudu taje ta fada jikinshi musaddiq tana cewa Bros naji dadin ganinka...!
Musaddiq binta da kallo yayi yace" ke Allah ya shiryaki, kina girma kina kara zama yarinya, Afrah tace" uhm Xeey kam dariya tayi
Hajiyarsu tace" dama gobene nakeso ka kaisu shopping kowa ya zab'a abun da yakeso harda waya zaka siyo ma Xeey ita kuma Afrah itama a chanza mata asiyo musu iri data kanaji? Musaddiq yace" eh inaji Allah ya kaimu, ya maido kallonshi ga Afrah yace see you is that why you're behaving like this in kikai wasa ba inda zaki.. Tsit Afrah tayi Dan tasan halin yayan nata sarai.
Mummy tace dama shikkenan maganar
Musaddiq yace" ba komai, nan suka ci gaba da hiransu bashi ya tafi dakinshi ba we 11pm Yana shiga yai bacci!
°°°°°
Isma'il kam tun dawowarshi hankalinshi gaba daya be tare dashi, wani mugun Son xeey yaji yana addabanshi, gado ya fada ya rungume pillow yana" magana chan kasa _INA zanga XEEY, Ya Allah ka bayyanar da ita_ be ankara ba kawai yaga kuka na nemen cin karfinsa, mikewa yayi yaje wajen madubi (mirrow) ya kalleshi wata Zuciya tace BE STRONG..
Wannan tinani tinani banaka bane, dawowa gefen gado yayi ya zauna Dan gaba daya jinshi yake like he is missing something....!
Afrah ne da Xeey Kwance akan gado se hiran su sukeyi irin na yan mata, nan Afrah take bata labarin wani *hausa novel* da aka turo, Xeey tace uhm gaskiya book din akwai dadi Idan an turo ki bani labari, Afrah tace" hahaha don't worry before a turoma I think an sai miki waya nifa duk na kosa ma gobe tayi cewar Afrah.
Xeey kam tace" uhm Hakafa Allah ya kaimu nidai seda safe! Afrah tace huh to 12 bari dai nima na kashe data nai bacci Dan gobe zamu fita, Xeey tace da dai yafi, nan kowa yai addua, yaja blankent dan Kunsan sanyi ake sosai..
*Washe Gari*
Tun wuri Afrah ta tashi sukai wanka sukai break Fast suna Zaune har 10 bro musaddiq be fito ba, gashi tana tsoro taje ta tasheshi yai mata fada, hakanan suka zauna a pallow, kwasam Sega bro ya shugo dakin binsu da kallo yayi yace" Yan matan daddy INA za'aje da wuri haka?
Afrah tace" bro don't tell me ka manta zaka kaimu shopping, zare ido yayi hade da cewa opps wlhi na manta cewar musaddiq, Afrah me zatai in ba zunburo baki ba XEEY kam dariya tayi tace"Allah sarki, Dan tinuwa da gatar da mahaifinta yake mata!
Musaddiq yaga ran Afrah ya Dan baci yace Sorry Sist ina zuwa.....
Ummiey Xeey
[1/21, 10:34 PM] Β©REAL UMMIEY XEEY: *_ β°°β’β’~β£_πβ’β’ππβ€π
*A DALILIN MATARββββ*
*UBAββββ*
*_ β°°β’β’~~β£_πβ’β’ππβ€π
```ββββββββββββSTORY & WRITTEN BYββββββββββββ```
*ββββUmmiey_Xeey Abaksonβπβββ*
*βββββ»EXCLUSIVE WRITER'S FORUMββββ*
_[Ι¦Φ
ΚΙ Φ
Κ ΦΙaΔΙ, Ι¦Φ
ΥΌΦ
ΚΚ aΥΌΙ sΚΦΙΚ Υ‘ΚΙ¨tΙΚ's]_
*ββLIKES AND DROP YOUR COMMENTsββ*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
```βββββββββSADAUKARWA GA____βββββββββ```
*ββββMARIAM TIJJANI ADAMβπβββ*
*Where is Bilkisu BK?π£* The whole page is yours
*Just wanted to say thank you for coming into my life and being my*
*TRUE FRIEND.*π....I love you
*PAGE 81__82*
"Musaddiq yaga ran Afrah ya Dan baci yace Yana zuwa, Direct room dinshi ya shiga ya cire kaya ya shiga wanka, be bata lokaciba ya fito sanye da wani light blue shirt da jeans yayi kyau sosai,
Afrah da Xeey da mum suna zaune sallamar musaddiq sukaji yace" sai kuzo mu tafi ko? Mum tace" haa! Bazaka tsaya kaci abinci ba da sauri haka?
Musaddiq yace" to sweet mum yazanyi wannan yarinyar ta matsa mun semun tafi, Afrah tace" woo waneni bro plz sit down and eat joor! Ita dai xeey binsu da kallo kawai take in abun dariyane tayi inna shuru ne tayi
Shap shap musaddiq yai having break fast dinshi, y mike ya dauka key yace musu let's go! Mikewa sukai sukai wa mummy sallama tai musu fatan alheri, da kuma Allah ya dawo dasu Lafiya sukace" Ameen
°°°°°°°°°°°
Isma'il ne zaune ya rasa meke mai dadi, phone dinshi ya dakko yai dialing numbern BABBAN AMININSHI *MUSADDIQ* ringing daya, biyu ya dauka suka gaisa!
Isma'il yace" are you at home?
Musaddiq yace" nop walhi nadan fita da sisters dinane ko zakazo ne zamu mangal plaza ne
Isma'il yace" alright sekundawo da zan zone
Musaddiq yace" Eyyah Idan nadawo zanzo ma plz regard to my mum, Isma'il yace OK agaishemun da kannan Nawa, musaddiq yace to aboki..!
Bayan sungama wayan ne Isma'il yace kai banda kirki fa yau na kusan 2months da dawowa amma banje naga Anty mariam Adam ba! (Antyn Xeey)
Mikewa yayi ya sake shiryawa sannan ya fito pallow ya gaishe da hajiyarshi, sannan ya hau kan dining yai break fast dinshi, bayan ya gama ne yace" wa mamanshi zai Dan fita! Tace" OK har ina cewa zaka kaini gidan abokinka nai musu godiya?
Isma'il yai smiling yace" I called him this morning sun fitane, mum Isma'il tace" ayyo. Isma'il yace" to zan fita mum tace" OK Allah ya tsare kar dai ka Dade please, ya matso ya rike hannun mamanshi yace" insha Allah.....!
Yana fita mum dinshi ta daga hannu tace" Ya Allah ka tsaremun yaron nan, ka bayyanar da Xeey in tana Raye, in kuma bata Raye, Ya Allah ka cirema yaron nan son Xeey... *Allah SARKI*
*ISMA'IL* ne ya fito da car daga cikin gidan, idonshi yakai ga inda suke tsayawa da xeey, Wani hawaye yaji Yana kokarin zubuwa, tuni yace" *innalillahi wa inna ilaihi rajium* ya dake zuciyarshi ya fara driving cikin natsuwa, be zarce ko inaba se gidan *MARI'AM TIJJANI ADAM* Yana zuwa Bakin gate din yai parking, ya fito ya tsaya yana tinanin taya zai fara shiga gidan, tunda gidan matar aurece be dace ya shiga kai tsayeba! Be gama tinanin nan ba Sega gate man ya fito suka gaisa, wa kake nema inji gate man"
Isma'il yace" Anty Mariam nake nema Allah yasa tananan, me gadi yace" tananan bari na shiga nai mata magana, Isma'il yace Okay...
Mariam ne zaune a hadd'andan falonta yasha kayan alatu ta ko ina, sallamar me gadi taji yace" Hajiya ana sallama dake a waje, gabantane ya fadi tace" oh ni waye toh?, kawai tace" to kace ganinan zuwa, hijab dinta ta dakko, ta fito cike da fargaban to waye wannan me nemanta?
Fitowa tayi sukai 4 eyes da Isma'il, dukansu Wani murmushi suka sake tace aww dama kaine? Maraba da zuwa ka shugo mana! Isma'il yace" wallahi kuwa, tana gaba Yana binta a baya...
Daki suka shiga ta kawo mai drinks sannan ta zaune tace" Isma'il idonka kenan dama kananan a garin nan bako ziyara, Dan yanzu ba xeey ba zumunci ko?
Isma'il yace" Anty ba haka bane wallahi ban Dade da dawowa daga school ba Alhamdulillah mun gama, ya LABARIN XEEY? GHAM gabanta ya fadi Dan taga sauyin fuskarshi, numfashi me karfi tayi tace" Isma'il wlhi har yanzu shuru ba labarinta, dukansu shuru sukai na mintoci sannan Isma'il yace" ya Salam, Mariam tace inaji a jikina zamu ganta, shidai Isma'il shuru kawai yayi Dan zuciyarshi wani tafarfasa takeyi
Yace" To Anty Allah ya amsa addu'arki tace" ameen, har ya fara fita a hayyacinsa yace mata zai tafi? Tace" Ismail ko ruwa kasha ai, yace" Hmmm Ina zan iya shan wani Abu banji labarin burin raina ba? Binshi da ido kawai tayi Dan ba karamin bata tausayi yayi ba, fita yayi da sauri yaje ya shiga motarshi da gudu yake figan motar har ya isa gida!!!
Yna shiga mum dinshi taga be cikin walwala mutuwar tsaye tayi Dan tasan meke damunshi
*Kuci gaba da biyo asannu sannu, a next page zakuji ci gaban labarin inda akaje wasu Afrah shopping*
Yours
Ummiey Xeey
[1/21, 10:34 PM] Β©REAL UMMIEY XEEY: *_ β°°β’β’~β£_πβ’β’ππβ€π
*A DALILIN MATARββββ*
*UBAββββ*
*_ β°°β’β’~β£_πβ’β’ππβ€π
```ββββββββββββSTORY & WRITTEN BYββββββββββββ```
*ββββUmmiey_Xeey Abaksonβπβββ*
*βββββ»EXCLUSIVE WRITER'S FORUMββββ*
_[Ι¦Φ
ΚΙ Φ
Κ ΦΙaΔΙ, Ι¦Φ
ΥΌΦ
ΚΚ aΥΌΙ sΚΦΙΚ Υ‘ΚΙ¨tΙΚ's]_
*ββLIKES AND DROP YOUR COMMENTsββ*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
```βββββββββSADAUKARWA GA____βββββββββ```
*ββββMARIAM TIJJANI ADAMβπβββ*
ππDedicated to All lovers of *UMAR M SHARIFF* wannan page din nakune Ku kadai.... πππ€¦
*PAGE 83...84*
Yana shiga pallow mum dinshi taga be cikin walwala mutuwar tsaye tayi Dan tasan meke damunshi, Isma'il Yana shiga daki gado ya fada yai rub da ciki ba abun da yake tinanin se Xeey, karar bude kofa yaji hade da Sallama, wai gowa yayi yace' aww mum! Wani numfashi taja tace" Isma'il bazaka cire ranka akan yarinyar nan ba ko? So kake muyi biyu babu ko?
Murmushi yayi yace" sweet mum ba komai fa, Tace" kar kaimun karya duk wani motsi ko chanji nagani a fuskarka nasan menene! Shuru yayi yace" To mum wannan ne karo na karshe da zaki k'ara mun magana muje dining inci abinci yunwa nakeji! Mum tace yauwa kokaifa..!
β’β’β’β’βͺβ’β’β’β’
Musaddiq ne yai parking a wani babban plaza dake cikin Kaduna, dukansu fitowa sukai, su Afrah ana tafiya majestically zuciyarta cike da farin ciki abun da takeso kenan, wani shago suka shiga, Suka fara dakko dogayen riguna masu kyau kala kala, bayan sun gama da nan ne ma suka shiga shagon takalma nan ma suka zab'a kala uku_Uku, sannan suka shiga shagon gyaluluka suka zab'a nan ma, Daganan shagon wayoyi suka shiga aka sai musu iPhone dukansu kala daya, bakuga murna wajensu ba ballema Afrah, haka suka gama siyayya komai masha Allah..
" Suna hanyane suka shiga ostrich suka siyo snacks suna tafe sunaci har suka dawo gida!
Suna shugowa Afrah Allah Allah, take su shiga ciki dan dadi, aiko yana parking ta dasauri ta sauka zata tafi da sauri, Musaddiq yace" kee me kike nufi waye zai daukan miki kayan? Afrah tace oh sorry bro! Yayin da Xeey ita kuma ta bude boot tana sakko da kayan, jidan kayan sukai suka shiga ciki, musaddiq bin Afrah yai da kallo yace" this girl gaba daya ta chanza but I'll fix her ass right... Lolx
Suna shiga Mum tai musu oyoyo sannan suka baje a falo nan suka fara fito da kayan, mum tace masha Allah, gaskiya kun iya zaban kaya masu kyau! Nan su Afrah Da Xeey suka k'ara mata godiya sosai Xeey harda kuka wai suna dawai niya da ita sosai, mum ta rungumeta tace" haba ai ke ta muce har abada insha Allah, sannan suka kwashe kayan suka kai cikin dakinsu suka bude phones dinsu sukai pluging a charji, sannn suka wuce kitchen Dan daura dinner!
Suna aikinsu suna dariya, Musaddiq Yana zaune yai dialing number Isma'il yake sanar dashi sun dawo ya zaizo dinne? Isma'il yace nop till we meet tomorrow akwai talk din da nakeso mui discussing, Musaddiq yace" alright sai mun hadu, Isma'il yace okay!
Misalin karfe 8 na dare time din kowa yaci abinci nan suka bude wata sabuwar hira! Musaddiq yace" mum ya ka mata wa ennan yaran su fito da miji girma suka karaya! Mum ta kalleshi tace to babban yaya ai ko kai ka musu zabi na gari, Suna maganan gaban Xeey ne yai mugun fadi tace" shikkenan i missed him cikin ranta! Nan dai suketa hira har dare yayi yace" bari na shiga room dina na kwanta gobe Monday! Mum tace gaskiyafa good night!
Su Afrah sun shiga daki, Xeey na kwance, Afrah ta dakko wayoyinsu ta mik'a wa Xeey nata tasa sim dinta, Afrah kam har ta shiga play store tai downloading whatsapp, tai installing ta fara chat! Ita kam Xeey tai shuru se tinani tinani take barkatai!
Afrah tace" what's wrong? Xeey tace" bakomai wlhi, Afrah ta ce bani wayarki nai miki sending whatsapp ki bude, Xeey tce" uhm dama kin barshi, kona bude dawa zanyi chat? Banda kowa fa! Afrah tace" karki damu zansa ai adding dinki cikin groups harda na NOVELS, Xeey tace" okay
Hope kuna enjoying? Kuci gaba da biyoni.....tnx all my lovers I heart you
Ummiey Xeey
[1/21, 10:34 PM] Β©REAL UMMIEY XEEY: *_ β°°β’β’~β£_πβ’β’ππβ€π
*A DALILIN MATARββββ*
*UBAββββ*
*_ β°°β’β’~β£_πβ’β’ππβ€π
```ββββββββββββSTORY & WRITTEN BYββββββββββββ```
*ββββUmmiey_Xeey Abaksonβπβββ*
*βββββ»EXCLUSIVE WRITER'S FORUMββββ*
_[Ι¦Φ
ΚΙ Φ
Κ ΦΙaΔΙ, Ι¦Φ
ΥΌΦ
ΚΚ aΥΌΙ sΚΦΙΚ Υ‘ΚΙ¨tΙΚ's]_
*ββLIKES AND DROP YOUR COMMENTsββ*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
```βββββββββSADAUKARWA GA____βββββββββ```
*ββββMARIAM TIJJANI ADAMβπβββ*
*Where is Juwairiyya @mrs Danja* your page is here..thanks for the love and support I hrt youπΉπΉ
*PAGE 85__86*
Xeey tace" Banda kowa fa! Afrah tace" karki damu zansa ai adding dinki cikin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 14