Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
abinda yake faruwa, 'yan uwan youseep suma sunzo dama su nadiya sune amarori, shikuwa gogan mom ce tasawo shi agaba ta taso keyar sa suka taho tare, ba mom ba har shi daya kalli nana seda tabashi tausayi yadda takoma, sedai ji dakai yahanashi koda kulata mah, ana tashi bejira suba yabawa motar sa wuta yay gaba, hakanne yakara sawa zuciyan nana karaya takasa dena kuka seda safiyya ta rarrasheta sosai tukunna tasamu tadan sawa cikinta wani abu tasha magani saboda ciwon da kanta yakeyi. Zukatan kowa cike yake da farin ciki da kauna a wannan gidan, murna da rawar kafa gurin angwayen biyu ba ah magana WASHE GARI Yau take lahadi! za ah mika meenal dakin mijinta tunda ta tashi takejin ta sukuku jikinta yayi sanyi sosai kiris take jira a zungureta tasoma kuka tawani lafewa safiyya ajiki, shikuwa muhammad tunda suka tashi mujaheed yasa shi a gaba da tsokana kan cewar yau yake ango. Fuskar mom dauke da murmushi tasami meenal da mimi tana shaida musu cewar ay zarah itada iyayenta suna kan hanyar zuwa donma wani uzuri ya rikeso da tuni sun nan ana shagali dasu, bakaramin farin ciki mimi tayiba saboda tasaba da zarah sosai tanata zumudi, Su muhammad sun tafi raka abokansu na nesa airport, 4 da 'yan mintuni kuma motar su zarah tayi parking a gidan na safiyya a time din kuma motocin Abban su mimi suka parker, yazo gidan domin yin sallama dasu yau ze wuce saboda uzurin da yake dashi, Mahaifiyar zarah dince tafara fitowa acikin motan, hamshakiyar mata ce meji da kudi da class tasoma takunta cikin takama da izzah, se su zarah itada inty dasuka take mata baya yanzun, inty itace taje taho dasu gidan saboda basusan shiba, baban na zarah ne yafito daga karshe a mazau nin driver, abin mamaki koda suka zo shiga ciki securities din Abban su mimi, hanasu shiga sukayi hakanne yasa maman ta zarah juyowa tanawa Abban kallon mamaki, wanda shima hakanne take, cikin wani irin yanayi yake kallon su da matukar mamaki hannun sa har rawa yake ya daga waya yakira daddy awaya, Batare da bata time bah daddy yafito, sedai koda ganin abinda yay arba dashi yasashi yin turus a tsaye yana wani irin yamutsa fuska kamar yaga kashi, zuwa wan nan lokacin maman zarah tasoma kufula cikin fushi tasoma tambayar daddy lpy ne meke faruwa? sedai sam be tanka mata bah illah iyaka ma hankalinshi yana kan mijinta bama jinta yake sosai bah, jawo kofan daddy yayi ya isa gabansa yana me yi masa wani irin kallo na kaskanci da rashin mutum ci, finger dinsa guda daya yasa ya nunasa ya ambaci sunan sa " Imam! Menene yakawo ka gidan nan? akan wani dalili mah zaka zomin gida taya yama!" daddy yana maganr ne cikin wani irin fushi da kunan zuciya, se a lokacin Abban ya karaso inda suke tsaye yace." Yazone domin yakara haddasa mana wata masifar a rayuwar mu, domin zuwan wan nan butulun gidanka sam ba alheri bane," " Inafa ze zama alheri!" Daddy yay maganar yana kallon Abban, jikin imam a mugun sanyaye yace. " Alhj Abubakar!" koda ya furta sunan daddy kukane yakwace masa yana me cewa." Tabbas kaine nashafe tsawon shekaru ina nemanka seyanzu Allah yahadani dakai, saboda nasan babu makawa kasan inda matata safiyya take.... TAKU A KULLUM NANA BMB 08147110349 [8/31, 3:39 PM] Nana BMB: ❣ RABON KWADO....!! BOOK 3 NA NANA BMB GARKUWA WRITTER'S ASSOCIATION { Marubuta masu garkuwa da alkalami domin fadakar da al'ummah } page 41 - 42 Tassss! kakejin daddy ya kwadawa imam mari, cikin karaji yace." Wannan yazama nafarko kuma nakarshe dazaka kira safiyya matarka kagane koh! Wani irin kallo imam yake watsawa daddy idonshi yakada yay jajir yace." Alhj mekake nufi dahakan?" Haba daddy kawai yake shafawa yama kasa cewa imam kala saboda takaici, " Iman kayi gaggawar tattara iyalan ka kubar gidan nan! tunkan asan abinda yake faruwa mah,inkuma bahaka bah yanzu zansa bodyguards suyi waje daku" Abbah cikin fushi shima yakewa imam maganar, kallon wulakanci imam yay masa yabudi baki zeyi magana, sega meenal da mimi sun bude kofa sun fito cikin farin ciki suka rungume zarah sam basusan abinda yake faruwa bah seyanzun dasuka kalli fuskan ko wannen su suka san ba lafiya ba, jikin meenal a sanyaye ta karasa inda su daddy suke tsaye tace." Daddy lpy kuwa muka ganku a tsaye haka meyasa basu shiga ciki bah," sam yarasa abinda ze cewa meenal mah, juwa tayi da kallonta kan imam wanda har seda ta tsorata da irin kallon da yake mata na kurillah, sauke ajiyan zuciya daddy yay yashafi kanta yace." Meenal kushiga ciki babu abinda yake faruwa yanzu zamu shigo muma" jinjina masa kanta tayi taname shirin juyawa tayi anyi ram da hannunta, hakanne yasa ta juyowa a tsorace tana kallon imam saboda irin rikon daya mata, " 'Yata ina mahaifiyar ki take?" Imam yay mata tambayar cikin wani yanayi kamar ze saka kuka gyara tsaiwar ta tayi kawai tana kallon shi da mamaki, ganin hakanne yasashi yimata murmushin karfin hali yace." Eh tabbas ke 'yata ce kuma ni mahaifin kine, koda kika kalli kwayar idona bakiga jinin kibah" Murmushi meenal tayi tace." Wai bakai bane Abban zarah?" murmushin ya mayar mata yace." Niba mahaifin ta bane, mahaifiyar ta kawai na aura, ke kadai ce "yata a duniya" Kasa motsi meenal tayi a gurin tanajin kalmar sa kamar an buga mata gudu ma akanta, jiki a sake ta juya tanama daddy wani irin kallo, cikin takaici daddy yadan ciji lips dinsa na kasa yaname lumshe ido saboda bakin ciki,bayyada ya iya dole ya kalleta yace." Meenal mahaifin kine shi yau Allah yakawo miki shi kada kiji mamaki ko shakku" Sam meenal tama rasa awani hali take ciki yanzu ko hawayen ta nemesu ta rasa kallon imam kawai takeyi shikuwa matsowa yakarasa ze rungumeta cikin wani irin firgici tayi baya tana masa wani kaskan tancen kallo, cikin sanyin jiki yatsaya yana girgiza mata kai harda magiya " Kiyi hakuri 'yata kada kiyimin haka kutemaki ni don Allah keda mahaifiyar ki ku kadaine farin ciki na wlh" " Allah yasawa kah! koda wasa ko a mafarki bazamu taba zama farin cikin kaba kada ka kuma kirana da 'yarka domin ni bansan kaba, bansan waye kaibah duk duniya banida mahaifin da yawuce daddy nah wanda yasan fadi tashi nah a rayuwa saboda haka kada ka kara danganta kanka da mahaifiyata don tafi karfin kah, kakuma tafi kabar mana gidanmu! domin kai ba alheri bane a gun kowa!" meenal takarashe maganar cikin kuka! A lokacin kuma su muhammad suka dawo gidan kasan cewar motocin Abban su mimi tacike parking space dinne yasa basusamu damar shigowa da tasu motanba sosai suna dai hangen abinda yake faruwa bude kofan motan mujaheed yay zefita muhammad ya riko masa hannu yana girgiza masa, yana cewa." Fara kiran mimi muji abinda yake faruwa naga meenal tana kuka" dawowa yayi yazauna mujaheed din yakira mimin, tsaki kawai muhammad yay yace ba lallai sun fito da waya bama kawai muje don bazan iya jurewa bah ganin meenal tana wan nan kukan" kafin ya rufe baki kuwa an daga wayan sedai be tantance muryan wayeba yace." Wai meyake faruwane awaje? suwaye sukazo?" Ba ah bashi amsa bah yaji an yanke wayan, bebi takan hakan bah suka fita a motan suka karasa inda kowa yayi dako dako a tsaye, mujaheed ne ya tsaya gefen mimi yana tambayar ta lpy? sedai kanta bashi amsa mahaifiyar zarah ta karaso gaban imam fuskarta babu alamun annurin rahama tasoma sauke masa maruka dukda haka be isheta bah seda ta cakumi kwalar rigar sa tana huci tasoma magana cikin fusata! "Tabbas yau nakara yarda da cewar kai butulu ne bakin muna fiki macuci! namaka dare dole kayimin rana, dama ance kaji tsoron wanda kafiya temakawa dayawa, ashe har mata ce dakai harda 'yah saboda muna fiki ne kai daya sa aka kamaka bacemin kayi harkallar kudi bace ta hadaku ashe karya kakeyi" Abban su mimi lokaci da yakama imam yasanar dashi yasaki safiyya. Mari lafiyayye shima imam ya sauke mata wanda yasata kara gigicewa takara shake masa wuyan riga tana cewa." Wlh yau imam taka takare a duniya sekayi nadamar abinda ka aikata min rayuwar ka ma a gidan yari zaka karasa ta" Fitowan safiyya kenan domin ganin abinda yake faruwa sabida itace ta daga wayan mujaheed,tayi mummu nan gani, ganinta da imam yayi ne yasashi dena jin abinda maman zara take cewa ma kallon ta kawai yake, Girgiza kai kawai daddy yay cikin takaici yaje yakama hannun ta suka shige ciki, tsaki Abbah yayi yaname cewa." Ay kuma shike nan tunda haka yafaru gara komai yazo karshe yau, hajiya kisake shi yanzu dai dole mushiga ciki a kashe wan nan kurar data taso sabida haka idan kuntafi kwacigaba da rigimar ku kome zakiyi masa kimasa" Dakyar imam yakwaci wuyan rigarsa a hannun ta se faman haki yakeyi don ya shaku kam ba karya rankayawa akayi parlour kuma kowa ya hallara, ummi tana ganin imam tasoma sallal lami tana cewa." Haba tunda naga daddyn ku ya haye sama da safiyya nasan ba lpy bah ashe bala ei ke kuma tunkarar mu" Dakatar da ita Abbah yayi kan tayi shiru kada takara cewa kala, haka kuwa tai gum da bakinta se uwar harara datake antaya masa haka muhammad kallon sa kawai yake, dakyar Abbah yashawo kan daddy ya fito da safiyya aka zauna gaba daya kuka kawai take tamkar numfashin ta ze fita, bayani daddy yamasa kan cewar shida safiyya yanzu shikenan har abada domin matar sace a yanzun harda yaransu ma, 'yar sace meenal gata nan sedai bashida da iko da ita sam seyanzun hassan da usain dasukaji wan nan batu sukasan ma abinda yake faruwa, saboda kululun daya tsayawa imam hawaye kawai yafara yanajin kamar yahadiye zuciya ya mutu jiyake makar yashake daddy, " Macucin banza da wofi dole mana dama kayi hawaye, mummu nan kaddara ce nima tasa na aure kah amma kasani yau taka takare bayan sakina dazakayi zakaga abinda zanyi maka" Sam bebi takan taba yamike ya tsugunna a gaban safiyya yanajin kamar ya hadiye zuciya yace." Safiyya kiyi hakuri ki gafarceni kaddarar rayuwar muce ahaka mutum baya taba gujewa kaddarar sa arayuwa" tunda yafara magana kukan nata ya tsananta nan danan numfashinta ya canza, dafe kanshi daddy kawai yayi don yasan za ayi haka dama kafin yagama tunani kuwa sejinta yayi ta fado jikinsa a sume! cikin kidi ma kuwa ya rarumeta yana jijjigata yana ambaton sunan ta, bodyguards Abbah yakira yace suzo su fitar da imam daga gidan domin anyi anyi yafita sam yaki hankalinshi nakan safiyya, su hudu suka shigo kuwa suka cukwi kwiyeshi kamar kayan wanki sukayi waje da shi, maman zarah tamike taname cewa " kusamin shi a mota mutafi kai tsaye police station zamu tafi yau duk kudina dayacimin seya biyani kuma yasakeni inba hakaba kuwa sena daureka imam" Dr bello daddy yakira a waya cikin gaggawa kuwa ya iso yaduba yanayin jikin safiyya hankalin kowa a tashe yake ba ita tafarka ba kuwa se wajan la asar tayi wani iri da ita dakyar ummi tabata tea ta amsa aka bata magun gunan ta tasha shine yasa tadanji dama dama bugun da zuciyan ta yake yadai daita yanzu, 9 tanayi nadare safiyya ta tubure musu tace a zo a mika meenal dakin mijin ta bazata kuma kwana a gidan suba se a dakin mijinta, tariga taji sauki ita saboda batada lpy baze yi wu ace za ah fasa kaita dakin tabah, Ya Allah! meenal koda tajee wan nan batu wani sabon shafin kuka tabude tanaji tana gani ummi tasata a gaba tayi wanka tafito tashirya ta tsaf tanata bazaza kamshi abinta, cikin zuciyan meenal lugude kawai take tsoro yana kara kamata da nauyin abin datake gani wai itace za ah mika gidan Ya muhammad a matsayin matar sa, a gaba suka sakata suna mata fadan tabi mijinta sauda kafa,seda suka gama aka kaita gurin daddy mah yay mata nasa nisiho hin masu ratsa zuciya hartaji zuciyan ta ta karaya sosai ta saduda saboda taga babu sarki se Allah wan nan al amarin haka yake, Dukda ga gida ga gida hakan be hana su ummi shiga motaba meenal ta rike ta sosai tanata gunjin kukan ta gefensu mimi ce se nana gaban motar kuwa inty ce itada zara se mujaheed daya jasu zuwa gidan suna fita gateman ya bude musu gate suka shiga, seda suka tsaya sukayi addu o i tukunna a bakin kofa kuma ummi tace tashiga da kafar ta ta dama, gida nata tashin kamshi gana amarya kuma seya hade har cikin bed room suka kaita kowa yazauna abinsa anata bata baki har 10 ya wuce san nan ummi tasa akaiwa meenal wayau kowa yasilale a hankali suka tafi dama mujaheed yana ajesu yakoma, koda meenal ta farga da hakan kuwa da mugun gudu tayo hanyar parlour din sedai tamakaro gam taji kofan a rufe hakanne yasata zubewa a jikin kofan tacigaba da kuka, To ango kuwa yana can yashirya abinsa yace babu katon daze rakashi dakin sa, koda mujaheed yaji haka tabe baki yayi yace." Nima naga 'yar kafarka tazomin rakiya" muhammad yay murmushi yace" kaika huta ay" yay gaba abinsa, jikin mimi sosai yayi sanyi tunda suka dawo gida take tunani tunda itace akan layi goce da wuri za ah dunguma a tafi bauchi itama akaita nata gidan, ita kuwa nana abinne ya hade mata biyu ga tunanin yousep dana auntien ta tanason sanin halin da take ciki, 11 muhammad yashiga gidan nasa yana bude kofan parlour yaji yabuge abu, hakanne yasashi zuro kai a hankali yaganta ta bingire tanata bacci, murmushi kawai yayi don yasan tunda aka fara shagalin bikin nan basu samu ishasshen bacci bah, ledojin hannun sa yaje yasaka a fridge, kana yadawo yadauke ta a kasan yaje ya shim fideta a makeken bed din, fuskanta kawai yazubawa idanu cike da shaukin so da kauna ahankali yaketa shafa gefen face dinta kasancewar baccin ta yayi nisa sam ko motsi batayi, mikewa yayi yakashe light din parlour yarufe ko ina san nan yadawo yashiga bathroom yadauro alwala yafito yasoma jero nafil fil yana me mika godiyar ga ubangiji daya cika masa wan nan buri nasa, sebayan ya idarne yasoma karatun Al kur'ani me girma seda yajima yana karatun tukunna yatashi yasoma cire kayan jikinsa dagashi se boxer ya haye bed din a hankali yasoma raba meenal da sutirar jikinta har ya rage daga ita se pant da bra ya manna ta da kirjinshi yaja musu bargo, dake shima gajiyar ke nukur kusar sa nan danan bacci yadauke sa, To asuba ta gari amarya da ango. TAKU A KULLUM NANA BMB 08147110349 [8/31, 3:39 PM] Nana BMB: ❣ RABON KWADO....!! BOOK 3 NA NANA BMB GARKUWA WRITTER'S ASSOCIATION { Marubuta masu garkuwa da alkalami domin fadakar da al'ummah } page 47 - 48 Tunda mimi ta tashi taketa kiran ummi a waya sam taki dagawa harta gaji tayi mata text akan pls kada sutafi tanason ganinta ko yaya ne kafin su tafi, nanma shiru babu amsa hakanne yasata kiran meenal tana kuwa dagawa tasa mata kuka har hankalin meenal yatashi, dakyar ta iya saita kukanta tace." Pls sister na rokeki ki kira ummi a waya tashigo part dinmu inason ganin ta kada sutafi sam taki picking call dina" ajiyan zuciya tasaki meenal tace." Insha Allah yanzu zata shigo kwantar da hankalinki,don yanzu muka gama waya da ya muhammad yace yanzu zasu taho" sake rikecewa mimi tayi takuma saka kuka tana cewa." i beg u sister ki kiramin ita yanzun" " sister na meya sami voice dinkine bata fita sosai? sorry kinji kidena kuka kina dagamin hankali sosai" turo baki mimi tayi harda harara tana cewa." wan nan mugun yayan nakine mana jiya yahanani bacci san nan yau ya hanani zuwa inyi sallama dasu ummi" murmushi meenal tayi donta fahimci abinda take nufi tace." Kai sister Allah ya shiryeki ya mujaheed dinne mugu kawai saboda ya anshi hakkinsa" tsaki mimi tayi tace "wai hakki zakiga hakki yarinya nidai ki kiramin ita" murmushi meenal kawai tayi ta kashe wayan takirawo ummin bata daga ba seta kira auntie safiyya tashida mata abinda yake faruwa,murmushi kawai tai ta nufi bangaren nasu. Tasan ummi kota wani hali bazata shigo bangaren 'yar tatabah yanzu, rarrashin ta tayi sosai takara kwantar mata da hankali takara gasata sosai a ruwa medan zafi ta lallabata tayi shiru sedai kuma ta makale ta taki saki tace ita su tafi tare tayiwa su ummi sallama, sam auntie safiyya taki yarda harseda tayi mata jan ido tukunna tana fa nuna mata aure fah tayi, jikinta asan yaye tasake ta tashige bed room tafada kan bed tasoma sabon wani kukan. 11 da wani abu suka kama hanyar kano, wajan la asar suka iso muhammad ko gidan be shigaba ya wuce nashi gidan, don zumudi kawai yake yaga iyalin nashi, Farin cikine sosai ya lullubeshi kuwa cin karo dasu dayay a parlour sam basuma san ya shigoba saboda hankalinsu yana kan game din da suke bugawa kallonsu kawai yake yana zuba murmushi, hankalin meenal ne yafara kaiwa kanshi," Ya muhammad!" ta kirashi cikin tsananin farin ciki saboda ganinsa datayi ba tsammani da gudu ta mike tayi gunshi har tana takewa hassan yatsun kafarsa, tun kan takarasa ya tareta da kyakkyawar runguma yana sauke ajiyan heart, a kunne ya soma mata magana." My angel nayi missing dinki over jiya nayi bacci mara dadi" rintse idanun ta meenal tayi don seyanzun abinda yake wakana tsakanin su yadawo mata tasoma kokarin janye jikinta amma sam babu hali sabida rikon daya mata, " Sannun ku da dawowa! babban yaya, ya hanya?" usain yana murmushi yamasa maganar ganin abindake wakana tsakanin sa da amaryar tasa, shikuwa hassan se tura baki yake don kuwa yaji zafin takun na meenal, murmushi muhammad yay yace." yawwa my brothers hope nasameku lpy" " Nidai yanzu dawowar ka matarka sabida taganka tawa kafana mugun taku kilama se ankaini gurin gyara" cewar hassan kenan, Sakinta muhammad yay yana murmushi ita kuwa a sukwane tayi bedroom don kunyace takama ta matuka, gurinshi ya zauna yana kallon kafar nasa cikin tausayawa yace." Ayya! sorry kajee batasani bah ay tayi maka" Rikeshi nabiha tayi tace "yaya kayafe mata kajee bata saniba" murmushi hassan yay yace " Tom shikenan my small nahakura saboda ke" Kuma tunta muhammad yariko yana cewa." Wow yau munci albarkacin kanwarmu Allah nagode maka, yanzu bari nafito wanka naci abinci semuje kuga mamma, nasan kinyi missing dinta sosai koh?" nabiha ta daga masa kai tana murmushi, mikewa yay yana cewa." to bari nafito tsarabar ku tana mota mah sauri yasa ban shigo muku da itaba bari nafito" sukabishi da toh, kuma suka rakashi da idanu. A kofan fita yaci karo da ita harta gama hada masa ruwan wankan zata fito, salin alin yakama hannunta suma koma bathroom din, nan danan yanayin ta yasauya kamar wadda akawa mutuwa kamar tayi kuka tace." Pls kayi hakuri ya muhammad ni nayi wankana ma fah abinci zanje na shirya maka a dining" cikin kure ta da shanyay yun eyes dinsa ya noke wuyan sa a shoulder dinsa yana tura baki gaba alamun yaki din, aikuwa yaga tana shirin saka masa kuka, hakan yasa yakarasa mannata da bango yahade bakinsu gurin daya yana kissing dinta har seda tagaji da tsaiwa tukunna yasakar mata lips din nata, Zuciyar ta taf da mamaki idanun ta arufe tasoma laluben kofa zata fita don zuwa yanzun tasoma sallama ya muhammad din nata, da mamaki shima kawai ya tsaya yana kallon ta " Meenal" Yakira sunan ta cak ta tsaya batare data juyo bah hannu yasa ya jawota kusa dashi yana kallon fuskanta na few seconds, yace." Bude idonki ki kalleni" seda yakuma mai maitawa tukunna tabude eyes din nata ahankali tasasu cikin nashi, ganin yadda nashin yakoma ne yasa takeson maida nata ta kulle ammah bata samu damar hakan bah, cikin sanyin shi yace " sweetie kina sona kuwa? tell me, kada ki boye min" takasa magana se kanta kawai data daga masa, babu abinda yagani cikin kwayar idonta se zallar tsoro, ajiyan zuciya yayi yasake ta tafice kuwa da saurin ta, kai kawai ya girgiza yana murmushi yace. " Yarinya zaki dawo kan hanyama" Ko da tafita zuwa parlour hassan harda rike baki yace. " OH! yaya kuma daga shiga daki kuma semuji ki shiru" hararar burin kunya tamasa sa ta wuce kitchen" murmushi usain yay yace." To mudai yay sauri yazo tafiya zamuyi mu baku guri" " Tab! wa ina nan ni senaga kul! uwar daka" inji hassan, galala usain yake kallon sa harda rike baki yace lallae kuwa ashe kanada babban aiki" kashe masa ido daya yayi yace "to kabari kagani kuma" meenal tanajiyo iyashegen na hassan sama sama harta fito ta aje masa abincin be wani jumaba yafito yazo yaci abin cinshi yakoshi, kana yamike yace su fito, meenal cikin azar babi aka zari hijab akai waje tanajin dadi, Suna zuwa parlour suka sami ummi azaune bata juma da idar da sallah bah, koda ta hangosu farin ciki ne sosai ya lulluneta ta mike ta tarbesu ta cafe nabiha zuwa sama tana dariya itama haka atunanin ta taga mamma dinta 😅 seda ta shilla ta sama sannan suka zauna tana cewa." kyakkyawar yarinyata nayi kewar ki dayawa" itama tana murna tace." i miss u too mamma" doss! tadan dora mata kiss a kumatu, kallon twins ummi tayi tace OH! twins ansamu sister an manta da mamma koh! ko ku kirani a waya mugaisa ma" keya usain yasoma shafawa yana murmushi shikuwa hassan dariya yayi yace." mamma sim din mu bazeyi aiki bah a nan anata hidimar biki kuma daddy besamu time bah ya canza mana, ita kuma yaya data kiraki mukace tabamu wayar tahanamu" yadda yay maganar tasa ta karshe zakasan sharota kawai yake meenal yakeso yawa sharri, takuwa soma antaya masa harara, haka ummi

Chapter 24 of 27