bakin kofa tace to yayana nayarda kafita nashirya sedae gani tayi yakara matsota sosae harsunajin numfashin juna yace kinutsu meenal bawani abu zanyi mikiba bazan kara aikata abinda nayimiki a garden bah nasan ban kyautaba kiyi hakuri kawae yajanyeta gefe yabude kofan yafita suna paulour suduka suna jiranta sauri sauri tashirya takwaso kayanta tafito suka kaemata mota suka nufi gidansu su innan sukayi musu sallama sannan suka dauki hanya kuma mimi ansami abinyi abinda take so kallon duniya idanunta nakan hanya,
GOMBE
Meenal ce kwance kan gadon asibiti gefenta kuma wata matace azaune tazuba mata ido ba tsammani taga meenal din tasoma bude idanunta tanadan motsi harta bude idanunta tangaran matar kuwa tadurkusa ta rungume meenal tana kukan dadi tasoma magana sedae me? sam bahausa matar takeyiba fulatanci take yarawa tana mika godiyarta ga ubangiji daya tashi kafadun yarinyarta,tamkar zuciyar meenal zata fito waje haka takeji duk abinda yafarune yashiga dawo mata sedae tunaninta yatsayane atime din da mutuminnan yake bata ruwa sedae tafarka taganta anan yanzu matar tana dagata tajuya suka hada idanu komae na na tunaninta yatsaya saboda tsorata ita kanta matar seda tafuskanci hakan karkashin zuciyan meenal addu ah take sosae saboda wannan matar tarike fuskanta itace take yawon zuwa mata a mafarki tana kuka tana mika mata hannuwa rintse idanunta tayi tana cewa dama mutuwa nayi kenan gashi naga wannan matar shikenan nabar gidamu har abada tana wannan tunanin ne muryar wata yarinya tadoki kunnenta wadda tashigo yanzu bazata wuce shekara shadaya da rabiba sewasu twins yara maza dasuka biyota abaya kyawawa dasu masha allah sukuma bazasu wuce shekara 7 bah zuwa 8 yarinyar tana cewa UMMI! wae haryanzu yayarmu bata farkaba jin yarinyar tayi hausa yasa meenal saurin bude idanu tana kallonsu ganin hakanne yasa yarinyar farin ciki mara misaltuwa taje takwanta akanta tana murna kamar me yaryarmu munyi kewanki kullum cikin kuka muke munrasa inda zamu tsoma rayuwarmu ina fata babu abinda azzulam can sukayi miki koh, shiru meenal tayi musu taki tankawa kowa sedae ido kawae datake binsu dashi jikinta asabule tamike tsaye tana kallon yayar tasu kamar tayi kuka takalli matar tace UMMI meyasamu yayar mune bata magana hannunta tariko tace hasana kiyiwa yayarku uzuri bata gama dawowa dae daeba bata juma da farkawaba twins suna gefe sunzuba mata idanu suma, idonta tafda kwalla tace allah sarki yayarmu allah yasaka miki yabaki lpy kokarin mikewa zaune take ummin ta temaka mata ta tashi tasa mata pillow abayanta tazuba mata idanu ko kiftawa batayi hasana takalla tace kira abbanku kisanar masa yayarku ta tashi bamusu kuwa tadauko waya cikin jaka, ummin mamaki take yadda meenal take kallonta haka hannunta tariko sosae tana cewa kiyi hakuri MIMI kinji kinriga kindawo gida kiwantar da hankalinki babu abinda zesameki,wata faduwar gabace tasami meenal jin an ambaci mimi seyanzu komae yadawo mata tuni tafara ambaliyan hawaye tana girgizawa matan kae ita yanzu taya zata ganar dasu ba ita bace mimi seyanzu ta tuna itace matar datakejin kukanta awaya yanzunkam mamakinta yakare ta tabbatarda ba mutuwa tayiba to amma wacece wannan matar rarrashinta ummin tasu tashigayi dakalami da dada masu kwantar da hankali itama hassana gefenta tazo tazauna tace sorry kinjee yayarmu nakira abbanmu yanzu zezo kidena kuka kinji tasa hannu tana share mata hawaye haka twins kafafunta suka rike suna cewa pls yayarmu karkiyi kuka, tunda meenal take bata tabajin nutsuwar zuciya da farinciki irin wannan bah ganin ita kadae sukema wannan rarrashin ga nuna kauna da kalawa hakanne yasa hawayenta kin tyayawa duksetake ganin abin wani iri yau ana mata irin wannan rarrashin bandaki tace musu zata shiga don haka ummin tasu ta rakata bakin bayan tatsaya daga kofa tana jiranta,
Tana cikin bandakin abban nasu yashigo da sallamarsa kana ganinshi kasan yana cikin farin ciki suduka sukayi kanshi cikin fillacin yasoma magana shima cayake ina mimin take ummin tanadaga bakin bayin tayi masa nuni da hannu alamun tana ciki hasana tace abbanmu yayarmu ay bata magana,itama fulatancin tayi masa magana,meenal tana daga cikin bayin tana jiyo yadda suke magana sedae sam ko kalma daya bazatace ga abinda suke tattaunawaba don sun juye harshensu tuni idanunta yadinga tsiyayar hawaye tagama abinda takeyi amma takasa fitowa kamar tasa kuka catake ya allah wani irin mutanene wadan dan ka kawoni cikinsu bansan mesuke cewaba ganin batada mafitane yasata dole bude kofa tafito, ummin takamota har kan gadon tazaunar da ita, sannan tayi mata hausa tace mimi inane yakemiki ciwo yanzu,girgiza mata kae tayi alamun bakomae, abban nasu yace to alhmdlh 'yata tadawo gida lpy makiya kuma sedae suji kunya ankusa kama wadanda sukeda sa hannu a saceki mimi alkawari nayi bazan taba kyale kosuwa sukayi mana hakaba wlh, kuma tunda allah yanufa kin farka ayau zamu koma gida bazaki kara kwanan hospital dinnan bah duka gaba daya gari yadauka 'ya ta tadawo so nan babu wani tsaro gara mutafi gida acan hankalina zefi kwanciya sam umminsu batayi masa musuba yana maganar tana hadawa meenal tea mekauri a cup tabata tasha takoshi sosae taji kwarin jikinta dama ga drip ansa mata ba iyaka,
GARIN KANO
koda suka isa janbulo gidan alhj abubakar horn biyu gateman yabude musu gate suka shiga gidan bayan sungaisa da megadin, nana tana kwance tadora kanta akan cinyar auntien tasu ita kuma auntien tana karatun jarida,koda suka shiga parlour din nana tamike cike da mamaki tana kallonsu sunshigo bawani hayaniya, aduk sanda meenal tayi dawowa irin wannan tunkan motansu ta tsaya zata fita aguje tayi ciki tana kwala musu kira sallamar dasukayima kasa amsawa nana tayi saboda mamaki se auntie ce ta aje jaridar ta amsa musu,koda suka hada idanu da mimi zuciyar tace tawani irin jarbawa saboda yadda tayi mata kwarjini ga girman dataga takara dakuma cika ido babu fuskar data fado mata seta safiyya,hakadae ta daure aka gaggaisa mujaheed yana dariya yace nana yadae meenal din taki tacanza mikine kikayi poster haka kina kallonta da mamaki nana tace sosae makuwa tacanza ya mujaheed wannan ba halin meenal bane akwaedae wani abu ganima nake kamar ba itaba shida mummy sukasa dariya kana yace lallae nana abinnaki aziminne toke meenal kinji mimi nazaune tadanyi guntun murmushi don ita tunda suka shigo tajee mutanen basuyi mataba duk zuciyanta acunkushe yake mussam irin kallonda dataga auntien nayimata, nandanan aka cikasu dakayan ciye ciye mimi ruwa kawae ta iyasha saboda bata yanayi me dadi nana kuwa takasa dena kallon mimi saboda mamaki auntie duk wannan baragadar babu komae kasa jurewa nana tayi tace waike meenal lafiyanki kalau kuwa suduka kallo seya koma kanta murmushi tayi mata again tace lafiya kalau fah ba abunda kedamuna tafiyan nance tasa kaina yana ciwo ko magana banasonyi amma bawani abu mekika gani,wlh ban yardaba shine abinda nana tace kawae, sosae auntie take mamaki yadda mimi take magana da aji cikin yauki amma saboda abindake cimata zuciya ko kulata takiyi hirarsu suke da mummy ita kuma nana sunayi da mujaheed hakanne yasa mimi juyawa takwanta akan kujera ta lullube fuskanta da mayafinta,
Suna cikin fira munaheed yakira muhammad vidio call yana shaida masa aysun iso aje wayan yayi yadda zega kowa suna gaisawa mummy ce tafara tsokanarshi tana cewa kadae zama dan can can ho dae ko muhammad kememe kodan hotunma kaki zuwa kamana,mujaheed yana dariya yace lallae mummy ina zedawo bakisan yadda kasar nan take gara masabane kilama acan zesamo muku sirika yajuya ya kannewa muhammad ido yana dariya,mummy tace a ah wlh allah karya biye bakinka bakada kirki allah yatsaremu duka takae masa yagoce, auntie ma tayi dariya tace tomeye aciki kae muhammad kataho tasu inyaso shima mujaheed kataho masa datasa kuyi anko bashikenanba, yakuwa gimtse dariyarsa yace haba auntie wlh allah yakiyaye ni inada wadda zan aura,ay nana kamar an mintseleta tamike tazauna gefenshi tana cewa wow ya mujaheed wacece wannan fadeta naji don allah,hararnta yayi yace to uwar gulma bangayawa su mummy bah seke muhammad yace aikin banza to kada kafada mana,mummy tace shakuriminka muhammad aynama santa ko ince munma santa, dasauri mujaheed yace pls mummy kiyi shiru mana, muhammad yace aishikenan kuma munma dena damun kanmu tunda munsanta abinda zamu ganta meye nadamuwa kada kafada kila bata azziki bace kake hana musani mudae indae batayi manaba dole acanza, dariya sosae mujaheed yayi yace bakasan kowaceceba zaka fara yimata rashin ta ido inda kuma kanwar kacefa? nepar kan muhammad ne yadauke haka itama auntie dakyar yatattaro nutsuwarsa muhammad yace banganeba,
Zaka gane nan gaba kadan cewar mujaheed.
Tambayarsa yayi yace ina meenal ne nibanjita tunda muka fara waya, tana kwance mimi tana kunshe dariyarta don bakaramin dadi hirar tasu takeyimataba, kallonta mujaheed yay yana murmushi yace kaganta tana hutawa takwaso gajiya murmushi muhammad yay metarin ma ano ni dayawa yace to nunamin ita nagani waca irin gajiyace haka dazatasata shareni,
Wayan yadauka ya isa inda take kwance tanajinshi tarufe idanunta ya yaye mayafin fuskanta tabayyana kafansa yadora kan tata yada yatsansa babbashi yana mata susa a tafin kafan nata tanata mamar mamar da idanunta kana gani kasan ba bacci takeyiba dariya take shirinyi saboda abinda yakeyi mata tasaki murmushi har dan dimple dinta ya lotsa abinda muhammad yakeson tabbatarwa dama kenan wani irin gumine yake tsatstsafo mishi mikewa tayi tari kafan nashi tace kae yayana kaga katasheni ina bacci tayi maganar cikin shagwaba shikuma yarankwafo saetin kunnenta yace baki gaisheda yayankiba yay maganar harda dan cizar mata kunne muhammad ya lumshe idanunsa time din tadago tace yaya ina wuni, bekara bari yaji mezata ceba yakashe wayan....
TAKU A KULLUM NANA BMB.
08147110349
[7/28, 8:20 AM] Nana BMB: 💝💖💝💖
RABON KWADO....
BOOK 2
NA NANA BMB
page 23-24
Muhammad jiyayi karatun yafice mishi a rayuwa gida kawae yakeson komawa domin tabbatar da raenin hankalin da wannan mimi din keshirin yimasa shin ya akayi meenal zata koma haka tabbas ba ita bace to ina takaemin meenal dita ya akayi koea yakasa ganewane kodae nine bana gani dakyau kae ina baze yiwuba sam kasa nutsuwa yayi yanata zagaye a room dinsa zuciyarsa na azalzalarsa yakoma Nigeria,koda yakashe wayan mimi kallon mujaheed tayi da mamaki shikuma yadan tabe baki yace yayi fushi seki kirashi kibashi hakuri,duk abinda sukeyi auntie nakallonsu tagefen ido rabin hankalinta nagun mummy rabi nagunsu mimi, nana ma matsawa tayi kusa dashi tace wae ya mujaheed son meenal kakeyine shiyasa tayi wannan nutsuwar dabata taba yiba,murmushi yayi yadungure mata kae yace ina ruwanki ne,mummy tace kyaleshi nana intayi tsami fah kowa seyaji rabi dasu abinki,wani irin tukukine yake tasowa auntie amma tana dannewa hab da magrib shima daddy yadawo gida ko sama behauba sabuwar hira tasake barkewa sedae kasan zuciyanshi fal take da mamaki ganin mimi shiru shiru tunda suka gaisa bata kara maganaba ga girman dayaga takara, inda taga dazu sunshiga dominyin alwala itada nana yasata ganewa nanne dakinsu sunata zuba ta silale tanufi dakin tana tafiya kamar bataso jitake kamar za a cemata ina zaki,
Koda tashiga tatsaya tanata bin dakin dakallo kana ganin tsarin dakin zakasan na mutum biyune kae tsaya wanka tashiga tayo koda tafito setarasa wacce ce wardrob din meenal koda tabude ta tan taci karo da teddy guda manya daga kasa wannan ne ya tabbatar mata itace ta meenal kuma ga rubutun dataga anyiyyi an manne a wardrob din duka tabisu tana karanta tana murmushi rabin rubutun akan ya muhammad dintane se nana seyanzun tasoma fahimtar irin shakuwar dake tsakaninsu da muhammad simple kaya bacci tadauko tadan murza mae da dan turare tasa kayan seda tagama zagayenta adakin sannan takwanta bacci,
Sedare Dr yasallami meenal suka fito dakanta take iya takawa abban nasu yarike mata hannu abinda yabawa meenal mamaki shine ganin motaci datayi birjik abakin hospital din ga bodyguards sun zagayesu kallo daya zaka musu kasan nera na aiki gurin motocinnan biyu ta bodyguard sebiyu tasu atsakiya sekuma biyu again abaya ta guards din aka bude musu suka shiga ummin tasu da mimi dakuma abban nasu su hassana kuma suka shiga tagaba motan guards din suka antaya motocin suka soma tafiya nan danan meenal tatsure ganin tsaron da ake musu meenal azuciyanta cewa take ya allah waca irin rayuwace wannan kuma allah sarki iyayena yanzu nayi muku nisa taya zan kubuta a hannun mutanen nan dole nagaya musu gaskiya life dinta kawae take tunani tabaya yadda taketa ikirarin intabar kano bazata dawoba ashe tayi maganar bakin bakin mala iku shiyasa allah yacanza mata rayuwa,lumshe idanunta tayi tanadan cizar lips dinta nakasa don kuka keshirin kwace mata jitayi ummin tarungumota jikinta tana da da rarrashinta don taga halinda tashiga taji dadin hakan sosae meenal shiyasa takara shige mata koda suka isa gidan ko ince estate seda meenal tamike daga jikin umman tasu securities ne tako ina daga sama an kafe wani symbol an rubuta WELCOME TO GIDAN FULANI! se walwalin haske rubutun yake abin kayatarwa, wangamemen gate din securities suka bude musu suka shiga tunda meenal take bata taba ganin gida irin wannanba anshiga gidan amma haryanzu tafiya ake ga bene wani kan wani hakanne yasata rintse hannayenta zuciyanta na tsananta bugawa kodae gidan 'yan yankan kae allah yakawoni ne? tunani take kala kala harsuka isa parking space sukayi parking suka fito ko ina haske take gani tunda suka shigo amma sedae inda suke tunkarane babu haske ko kadan kam kuwa takara rike hannun ummin tasu tanata raba idanu koda suka inda duhun yake kamar walkiya taga haske yakawo jama ar gurinne yasata firgicewa tana shirin guduwa rikon da ummin tasu tamata yasata kasa matsawa daga inda take,duka jama ar gurin suka dauka da tafi suna fillaci cikin nishadi da farin ciki daya bayan daya kowa yake zuwa yana welcoming dinta ido kawae take bin kowannensu dashi mutanen abin burgewa kana gani base angaya makaba kasan family dayane hardasu ummin da abban nasu sukayi welcoming dinta baki saro take kallonsu sunata mata murna da dawowa mutanen sun burgeta matuka har smile takeyi sedae sam batajin abinda suke cewa, haka ummim tasu takama hannunta suka nufi part dinsu 'yar kauye meenal tazama ganin haduwan gidan nasu mimi sekace a London tsarin gidan nasu har dakin mimi takaeta tace zauna na hada miki ruwa kigasa jikinki sosae gefen makeken bed din mimi tazauna wani sanyin kamshi nadukan hancinta dakin ya tsaru komae nadakin peach colour ne da butter milk tasau baki tanata kallon dakin ummi tafito daga bathroom din tatsaya tana karantarta seda takare mata kallo sannan tace meenal kitashi kishaga wankan koh saurin juyowa tayi ganin irin kallonda takeyi matane yasata sunkuyar dakanta tace to, fita daga dakin tayi tace kiyi kishirya kikwanta kisamu isasshen bacci don kinsan gobe hardare baki bakarewa zasuyiba, da kallon mamaki meenal tarakata harta fice taja mata kofan koda tashiga wankan tajuma acikin kwamin wankan don sosae tajee dadin ruwan sannan tafito kods tabide wardrob din tsarin kayan yaburgeta ga kamshin dake tashi tadauki sleeping dressed tasaka kana tayi sallah gurin aje sallayama zamanshi yake seda tagama addu inta sannan taje tamurza lotion me kamshi takwanta tunani kala kala ne a zuciyanta tagaza yaddanma kanta ita meenal itace awannan life din wani irin sanyin ni imane yake ratsata har bargon jikinta tana wannan tunanin bacci yadauketa,
WASHE GARI
Su mimi suna kwance kana gani zakasan baccin baya wani yimata dadi saboda ta takure gure daya haka auntie tashigo tasamesu da asuba akayi sa ah kuwa fuskar mimi itace awaje takarasa harda sandarta kuwa tazabga mata mari ta tashi firgigit tana kallon auntien hawaye na ambaliya a idonta don bakaramin zafi tajiba,nana ma afirgicen ta tashi ganin abinda yafarune yasa cewa haba auntie metayi miki kuma daga dawowarta cikin fushi tace zaku tashi kuyi sallah ko yaya tayi maganar tana huci suduka shiru sukayi tafita tanata masifa ita kadae abin sosae yadaurewa mimi kae tomeyasa tamareta haka?
TAKU A KULLUM NANA BMB.
08147110349
[7/28, 8:20 AM] Nana BMB: 💝💖💝💖
RABON KWADO....
BOOK 2
NA NANA BMB
page 25-26
Tunda meenal tayi sallah asuba bata koma bacci bah tanata azkar har gari yasoma yin haske sannan tashafa tamike tacire hijab din tazauna gefen bed tana ganin komae yazame mata nadaban a arayuwarta iskace taketa daga labulaye ga sanyin asuba daya ratsa bedroom din hakanne yasata mikewa tabude labulayen haske ya gauraye dakin cike da annushuwa tabude kofan bayan inda aka aje furanni masu kyau dasuka zagaye gurin abin sha awa iska nata fificeta tana sauke ajiyan zuciya se daga mata gashi take seda tagama kallon furannin sannan tasoma kallon tsarin gidan tana hangen ragowar benayen abin sha awa komae cikin tsari tana murmushi tace ya allah wani irin gidane haka ka kawoni me abin me abin birgewa da mamaki tashagalta da kalle kalle taji ana jifanta da wani abu hakanne yasata saurin kallon kasa domin ganin menene taga wasu furannin ne ake jifanta dashi peach colour da alamu dae kalan da mimi kekauna kenan ganin hakanne yasata saurin karasawa tarike glasses dinda yazagaye gurin tahangi wani saurayi kuwa yana kan mota atsaye yana rikeda wani dogon basket dayake zuba furannin yana watsa matasu dukda tazararsu hakan behanata ganin haduwar guy dinba black beauty sunkuyawa tayi tana kwasar furannin tana shaka kamshinsu sosae yaymata dadi,
Muryarshice takatseta dataji yana WELL COME BACK MY SWEET MEEMS! dakarfi yake maganar yadda zata jiyoshi aykuwa se yashe baki take tanan tsaye taji anriko mata hannu dasauri tajuya taga ashe ummi ce zuwa tayi ta leka tawatsawa saurayin dakuwa tace anshi naka "BASSAM" hannun nata tarike tace muje kishirya nazaci zanganki kinshirya kinbiyewa bassam, cikin jin kunya tagaisheta ta amsa tace kishiga kiyi wanka kishirya kinji koh, batare da musuba tace to ummi, seda tashiga wankan sannan tabude wardrob dinta tadauko mata wani tsadadden less fari tass dashi
se shekin kyau yake sannan ta ajiye mata akan bed tafita, bawani bata time tafito tazauna gaban dressing mirror kayan shafan kawae take kallo nagurin da turaruka tama rasa wadda zatayi amfani dasu su " su meenal an zama 'yan kauye hhhhh" tajuma tana shafe shafenta sannan tasoma fesa spray kala kala tasaka kayan na mimi sedae rigan bata kamata yadda ake soba taso tayi mata yawa, tana gama saka kayan taji anayi mata knorking seda tazauna tabada izinin shigowa, hassana ce tashigo hannunta dauke da tray nakayan breakfast murmushinta ta fadada tace hasana kece, cikin jin dadi takaraso ta aje tray din gefe tace morning my besty, morning my love sis ykk ina twins, zama hasana tayi gefenta tace wow yayarmu kinga yadda kike walwali nakyau kuwa gaskiya kinfi dakyau tabdi kinganki kamar amarya tubar kallah, lallae suya bassam akwae zuba shirme yau dama najishi yafara ay, kiyi kiyi break din yayanmu yanzu yaya zara zata hawo yimiki kwalliya fah! meenal haka tafara tunanin waca irin kwalliya kuma za ayi mata abinda tunda take arayuwarta ba ah taba yimataba hannu takae tafara daukan kofin tea hasana tarike hannunta tace a ah kifara shanye madarar shanun cikin dayan cup din tukun da dumintama tunkan tayi saunyi dama ummi tace bazaki kula madarar bah kifara da ita tukunna, bansan meyasa bakisan shan madarar nan yayarmu?galala meenal takebin glass cup din madarar da kallo batace kalaba tadauka tashanyeta,kadan taci abin karin shima tea din iya rabi tasha cup din ta ajiye da mamaki hasana tace badai koshi kikaeba, meenal tace haba hasana aynamaci dayawa bakiganiba,
Hasana tayi dariya tace kae yayarmu ahakane kikaci dayawa kallifa ko rabi bakiyi bah, itadae meenal kishigida tayi akan pillow tana kallon hasana tana zuba mata murmushi najin dadi tanason hasana sosae wani farin cikine takejin ya mamayeta ganin irin gatanta tan dasukeyi abin yana mata dadi, itakuwa hasana mamakine yakamata ganin yadda yayar tasu tacanza semagana take mata cikin faran faran da fara ah sabanin da dako magana ma batasonyi,
Tasauke ajiyan zuciya tace to yayarmu bari nafita da abinci sena turo miki yaya zarah din nasan ketake jira tamike tadau tray din tafita tanamejin dadin sauyawar yayar tasu tana fita meenal tayi wani irin birgima a kan bed din tana cewa ya allah wani irin gatane wannan nake gani arayuwata nagode maka daka sauyimin rayuwa me dadi " to me karatu lamarin meenal aziminne tamantama da yayanta da masoyinta" koda hasana tasoma saukowa daga steps din benen tana fara ah, hango bassam datayine yasata daure fuska yana zaune a parlour yaharde kafa sunata hira da yaya zara,
Tunda tasoma saukowa daga steps din yake kallonta tana sanye da jeans blue yakamata se riganta pink tazo mata gwiwa tayi kyau sosae tadan kamata rigan hakanne yasa dan kirjinta daya soma tasawa bayyana ga hulan kanta ma pink tayi kyau sosae tana tafiya cikin takamarta da nutsuwa ita alan dole kada a raenata jiyake kamar yaje yarufeta da duka batasanma yanayiba seda ta ane tray din kan dining sannan ta dawo tazauna itama taharde kafa zara da bassam hira suke cikin fulatanci gefe gefe suke saka turanci sam basa hausarma, cikin shan kamshi tace yaya zara yayarmu tagama, ta amsa mata da to seda suka gama tattaunawarsu tadauki jakarta tahaura saman, ita kuwa hasana batasan ma me akeba buga game dinta take a tap dinta kawae sejin tsawar data razanata tayi dasauri tamike zata gudu kuwa yace lallae yarinyar baki iya gaisuwaba koh? jin hakanne yasata dawowa cikin tura baki tace ina kwana kawae yaja tsaki yace stupid girl dallani kawomin breakfast tunkan nazo na anshi wayan na faffasata inga ta maitar game, idonta tafda kwalla ta aje wayan nata tanamejin haushin zaginta dayayi taje kan dining din tadauko masa ragowan da meenal tarage tazo ta aje masa tunkan takarasa mikewa yakuma zuba mata wata tsawar ashema kin raenani har haka nizaki kawowa saura nayi miki kama damecin saura almajiri kika maidani kome,
Cikin zucuciyar hasana tana cewa ba almajiri bane kae kuma wlh sekaci, arazane takarasa dagowa tana kallonshi alamun maganar tasa ta tsorata ta ta dafe kirji tace ya bassam yanzu ragowan yayarmune bazakaciba kyamarta kakeyi kenan to wlh sena gaya mata galala bassam yake kallon makirci irinna hasana tajuya dasauri tasoma hawa steps din,dagudu yakarasa yafisgota saura kadan tafadi yariketa ya wancakalata kan kujera yana cewa uban wayace miki nace bazan ciba,da hannu ya nunata yace wlh kika haura samannan sena lahira yafikijin dadi, yajuya cikin takaeci yazauna yasoma tura abin karin yana nadamar sata takawo mata abin kari dayayi ga tea din ya huce kuma gashi rabi haka yashanye hasana zuciyanta kal dafarin ciki ta kuntata masa kuma taki tafiya saboda kada yatashi yagudu yakici hka ya cuccusa yanamejin zafinta a zuciyanshi yadauki wayoyinsa yafice daga gidan hasana don dariya harda kifawa da tsallen murnarta tanufi dakin twins donyi musu wanka tasan yanzu sun tashi suna zuba rashinji....
TAKU A KULLUM NANA BMB.
08147110349
KUYI HAKURI MUTANE NAH KUNJINI SHIRU KWANA BIYU INA BUSY DAYAWA NE.
[7/28, 8:20 AM] Nana BMB: 💝💖💝💖
RABON KWADO....
BOOK 2
NA NANA BMB
page 27-28
Fitowar mimi daga wanka kenan wayarta tasoma ruri ita tamantama dawata waya a jaka batabi takan wayarba tazauna kan sofa tana fuskantar mirror kome ta tuna kuma tamime taje ta dauka wayan a time din ma kiran yayanke kawae taje tajonata a charged nana binta da idanu kawae take cikin mamaki tace waya kirakine? mimi bata tanka mataba illah zubawa fuskanta idanu datayi cikin mirror tana shafa inda auntie tamareta haryanzu abin mamaki yake bata,tana nan zaune wayar tata takuma ringing nana nazaune tayi fushi dama saboda taimata magana taimata banza,tahanzarta zuwa tadauki wayar don ganin mekira nana ganin mekiranne yasata tasau baki tace yanzu nadiyace take kiranki dama shine kikaki daga wayan itadae mimi kallonta kawae take ta mirror harta daga wayan suka gaisa taji tana cewa jiya sukazo ay wlh nadiya ba wayanku kadae tadena dagawaba harda tamu hatta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 27