cuci zuciyansa, yajima a ciki yana nemarwa kansa mafita dason gano gaskiya amma abin ya gagareshi haka yafito sam yarasa walwala dukda abokansu dasuka hallara sam hankalinshi baya gunsu,
Koda daddare bayan sallan ishah suna bedroom yanajin mujaheed yadda suke waya da mimi yashaida masa cewar su hadu da garden yana zaune mujaheed din yay wanka yashirya yafita, muhammad yanata zagaye dakin yarasa nutsuwa tunda mujaheed din yafita, kasa jurewa yayi shima yanufi garden din kallo daya yamusu yasan sunyi nisa a love amma kuma mimi tana hangoshi annurin fuskarta yadauke zujiyanta tafara lugude, yana karasowa yazauna gefenta yana kallonta yay smile yace mujaheed pls dan bamu guri muyi magana ta fahimta nida,mujaheed be kawo komaeba sema dadi dayaji don bayason abinda muhammad kewa mimi, fitsarine kawae mimi bataiba don tsoro wani irin gumine yasoma tsatstsafo mata mujaheed yana mikewa ta mike itama zata bishi ya rike mata hannu yadawo da ita mazauninta kuma yaki sakar mata hannu kanta akasa shima yana yimata kallon kurrillah yana nazartarta, meenal yakira sunanta, tayi masa shiru yakara kiran sunan nata muryanta narawa tace na am, dago ki kalleni mana mimi daurewa tayi tayi tamaza tadago sedae takasa kallon kwayar idanunsa menene a tsakaninki da mujaheed?tayi masa shiru, badake nakeba, yana sonane, ke kumafa?kanta a sunkuye tace inasonshi nima ina kaunarsa dayawa, muhammad ya jinjina kae yace good, ina ajiyata dana baki bafin natafi China?sosae yake ganin gumi yadda yake fimata wuya daga cikin gashinta saboda yadda yake magana ba alamun wasa afuskarsa, idanunta nazubar hawaye tace tananan,koda yaji haka seya saki murmushin mugunta yace maganar dakikace zaki gayaminfa sena idan nadawo ina saurarenki yanzu,mimi tadanyi shiru sannan tace dama maganar ya mujaheed ne zangaya maka muna soyayyane,ok yanzu ke kin iya soyayyane kinsan yadda take? dukda halinda mimi take ciki furucinsa seda yasa tasaki murmushi hakan kuwa yawa muhammad dadi yakara ganin wata shedar,batae tsammaniba taji yarike mata hannuwa yana murzawa cikin nashi cikin jin tsoro tadago tana kallonsa se sannan yaji yadda jikinta yake rawa, kasa jurewa kallonsa tayi tasunkuyar dakae tana hawaye, yasauke ajiyan zuciya yakara matse hannunta cikin kakkausar murya yace banason raininin hanakli zaki iya rainawa kowa hankali amma bandani kafin kowa yafahimci wacece ke inason yanzu kifadamin asalinki kifadamin abinda yake faruwa kuma shin ina kika kaemin meenal ditane kamar kowa yamakance kowa yaki fahimtar bake bace meenal banason muyi rigima dake yanzu kifadamin ko waceceke,mimi ji take kamar kasa tabude tashige ciki, murya tana rawa tace nice meen.....
yatsansa yadora akan bakinta yace karmuyi haka kada kiyimin gaddama wannan al amarin yadauremin kae, zakiyimin bayani tasauki ko kuwa,kukan da mimi takerikewa ne yakufce mata tamike zata ruga ya kuma fincikota ta dawo tazauna cikin shashhseka tace wae meyasa yaya kakemin haka kawae saboda nacanza kace bani bace mimi banason haka karabu dani, sosae muhammad ransa yabaci daganin raenin hankalinda ake shirin yimasa, kafansa yasa yatake mata yatsun kafarta tasaki kara cikin zare idanu yace shut off malama kifadamin gaskiya konayi miki abinda yafi haka, cikin dakiya mimi tashare hawayenta tace nice meenal! muhammad yay murmushi yace ok tunda kece meenal inason gobe kafin su daddy mujaheed sutafi agaban kowa ki shaida musu cewar kinason mujaheed da aure idan dae kina sonsa tokiyi haka gobe, cikin sauri taga masa ya jinjina kae gud gal tashi kishiga ciki semun hadu goben koh! da gudunta nabara mimi tae cikin gida yabita da kallon mamaki al amarin nan yana matukar daure masa kae zuciyansa a cunkushe yarasa meyasa kowa yaki fahimtar abinda yake faruwa ne....
TAKU A KULLUM NANA BMB.
08147110349
[7/28, 8:20 AM] Nana BMB: 💝💖💝💖
RABON KWADO....
BOOK 2
NA NANA BMB.
page 45
Abinda muhammad yace tayine tasa mujaheed yayi cewar yasanarwa su daddy yana sonta se aureta,mujaheed yayi mamaki dajin wannan furucin daga bakinta haka da wuri beyi mata musuba ya amsa mata zeyi domin baya shakkar tunkarar kowa indae akantane, to haka yadawo parlour yanata tunani yakasa aiwatarwa don kalamin yamasa nauyi kusada muhammad yakarasa yazauna yafada masa abinda mimi tace yakuwa saki kayatatccen murmushi yana kallon mujaheed yaname kara mamakin yadda idanuwan mujaheed suka rufe haka daya kasa fahimtar abinda yake faruwa koda yake kauna dole yamasa uzuri tarufe masa idanuwa, gyaran murya yay yace tome kazauna jira kaje ka aiwatarmana time yana tafiya,mujaheed yarike hannunsa yace pls muje karakani nagaya masa cikin shan kunu yace indae sedani ne to kafasa bama son abin kakeyi bah kenan,mujaheed gajiya yayi yatashi yanufi gurinsu daddy suna zaune da nashi daddyn sunata fira tunda ya tashi muhammad yake kallon ikon allah sosae yakejin zuciyansa tana dancing, koda ya karasa yazauna agabansu kamar me neman gafara yasunkuyar dakansa kasa zuciyansa tana wani irin bugu haka meenal shikawae tazubawa idanu,haka suma su daddy shi suka gubawa idanu ganin irin usmanda yayi agabansu cikin ladabk yace daddy dama inada maganane, kallon juna sukayi su daddy don basu san cikinsu dawa yakeba dagowa yay yakalli daddy sannan yakuma sunkuyar dakansa hakanne yasa yatabbar dashi yake,seya gyara zamansa yace to mujaheed ina saurarenka kaf dakin yadauki shiru kuwa aka zubawa mujaheed idanu, Dama maganace....Mujaheed yay shiru secan yakuma cewa dama maganace akan meenal daddy, tunda yaji ya ambaci meenal yarintse idanunsa cikin wani irin yanayi don yasan meze furta ayanzu,
Dama ina sontane daddy kuma itama tana sona iname rokonka daddy kabani auren meenal tazememin abokiyar rayuwa ta har abada,
Wani krin takaecine yacikawa auntie zuciya jitake kamar ta harbe mujaheed kallon kuma seya koma kan daddy ana tsumayin hukuncin daze zartar, muhammad jiyay kamaryashige huciyan daddy yaga wani hukunci zeyanke ne?bude idanunsa yayi sannan yay gyaran murya yace
Mujaheed!
Na am daddy
Mujaheed inason kasani yadda nadauki muhammad haka kake agurina babu bambamci komene ne kakeso agareni indae dayiwuwarsa to bashakka sena yimaka, to amma batu akan meenal inason daga yauma kasoma kokarin cireta azucinka saboda abinda kukeda muradi bame yiwuwa bane....
TO ME KARATU MUHADU A BOOK 3 INME DUKA YAKAEMU DONJIN YADDA ZATA KASANCE!
SHIN MEYASA DADDY YAHANA MUJAHEED AUREN MEENAL?
TAKU A KULLUM NANA BMB.
MASOYANA INA MIKA DUNBIN GAISUWATA AGAREKU DA GODIYA TA MUSAMMAN.
08147110349
[7/28, 8:20 AM] Nana BMB: 💝💖💝💖
RABON KWADO....
BOOK 2
NA NANA BMB
page 43-44
Meenal ce kwance a kan bed tayi lamo inbanda tunani babu abinda takeyi abin duniya gaba daya ya isheta tarasa mafita kullum cikin damuwa take harta soma ramewa, tayj zurfi cikin tunaninta tajee ana knocking seda ta gyara kwanciyarta sannan tabada izinin shigowa, hasana tashigo dauke da cup ahannanunta tana murmushi tazauna gefenta tana cewa yayarmu tunda kika gama school damuwanki takaru kullum bakida sukuni kuma ummanmu tace ki kwantar da hankalinki akan aurennan naku keda ya bassam nasan bakya sonsa kawae kinawa abbanmu biyayyane kuma baze taba canza maganaba kinsani so kiyi hakuri kada kisa damuwa aranki tadameki ko bakomae ya bassam yana matukar kaunarki zakiji dadin zama dashi kema kuma nan gaba zaki soshi,
Hawaye meenal tafara don yanzu ba abinda tafi tsana samada ai mata maganar aurennan danasani kullum tanayinta dabata yimusu bayani tunfarko kota wani hali kuwa bazata bari ta auri ya bassam be kome zefaru sedae yafaru yayanta kawae yake fado mata arae tasan yanzu yadawo gida saboda bata taba bata a lissafintaba tunda yatafi,hannun hasana tariko tace hasana ina cikin wani hali bazaki ganeba nasa yadda zanyi da rayuwata, jikin hasana a sanyaye tace kiyi hakuri yayarmu ki fawwalawa allah komae tamika mata cup din tace gashi ummi tace kisha akae mata cup din,ran meenal yakara baci saboda bata kaunar irin abubuwan nan da ummi take bata tunda aurensu yakusa fuska adaure ta anshi abin cikin cup din tshanye tabata cup din, hasans tafito cike da tausayin yayar tasu kods tasauko tasami bassam azaune suna hira da twins da ummi cikin cukurkude fuska tanemi gu tazauna cikin ko in kula yace ke jeki kiramin yayarku, hasana ta tabe baki itama tace yayarmu tayi bacci,
Bai kukalataba yadauka wayansa yacilla mata yace jeki kaemata inason muyi magana ne nakira ta ta wayan akashe cikin tura baki tadauki wayan kuwa takoma gun yayar tasu sam itama bataji dadin kawo wayanba don sabodashi takashe wayanta seda suka gama wayan tabawa hasana wayar tamayar masa koda tasauko twins kawae tasamu a apalour din ummi tana dakinta shikuma yafita answer waya da dayan wayan nashi hakanne yabata damar zama tasoma bincieke awayan tana shiga inda ranta yamata tana cikin kallon pictures a wayan taganowa kanta abinda yadaga mata hankali tamike dasauri tashige dakinta tacigaba da kallon hotunan jikinta har bari yake saboda tsoro duk rabin hotunan bassam ne shida mata fitsararru babu kayan mutumci ajikinsu wanda dasuma gara babu wasu sun makale masa ajiki hawaye kawae taji yana bimata ido,
Koda bassam yadawo yace wae twins hakasan bata sauko bane haryanzu suduka sukace tasauko mana tundazu tashige bedroom, jiyay wani daram kirjinshi yaharba inibin dayake shirin kaewa baki ya saki tsam yamike ya nufi daki, kallonta kawae take tana hawaye tana cewa allah ya isa ya bassam wlh yau allah ya toni asirinka bazaka taba auren yayarmuba ashe kae dan iskane dama tokuwa sena kaimata taga abinda kake aikatawa yaudararta kakeyi tanata masa ibar albarka, tadagowar dazatayi taganshi jingine a kofanta yana kallonta saboda firgita tamike batasanma tasaki wayanba tasaka kuka tana cewa kuma wlh kome zakayimin sena gayawa yayarmu don bazan bari ta auri dan iskaba hakanne yasa yasoma nufuta ahankali tanaja baya fuskarsa babu alamar rahamar annuri atare da ita seyanzu yake danasanin bawa hasana wayarshi dayay don yamanta ba security, harseda tadangane da jikin bango yazo dafda ita ya nunata da yatsa yace kewacece dazaki hanani auren my meems yarinya duk duniyar nan babushi sannan kuma wayace kiyimin bincike awaya?cikin zafin rae tadago btace saboda allah yatoni asirinka wayanka tazo hannuna yau tasss bassam yadauketa damari tasa hannu biyu kuwa tadafe fuskannata tana kuka cikin bakin ciki yace ke wace irin dakikiyace saboda kinganni da mata zaki kirani dan iska saboda bakida kwakwalwa mekyau kisake gangancin cemin dan iska kiga abinda zanwa shegen bakinnan naki mara kunya, hasana takuma kulewa cikin rashin tsoro tadago tace ayba karya naiba anfada din yayarmuce kuma daga yau kasa aranka bakae ba ita donsena tonama asiri katafi can kasamo matarka amma ba ah gidanmuba,
Cikeda mamaki bassam yake kallon hasana yarasa meyasa hasana batajin tsoronsa koda kuwa meze mata bata shakkar yimasa rashin kunya tunani yayi tabbas yakyale yarinyar nsn wlh seta ballo masa ruwa yanagani burinshi yakusa cika so dole yadauki mataki, murmushi keta yasaki sanan yakara matseta abango yay mata rumfa ko kyallinta ba ah hange yarufeta seda suka kwashi mintina ahaka ba umm ba um umm sannan yadago fuskarsa daukeda kaya tatccen murmushi yajuya yadauki wayanshi data yar yatafi seda yabude kofa zefita yajuyo yace no problem ayanzu zaki iya fadin abinda kikeso nima nasami nawa abin fadan so ki gwada kiga meze faru, yay ficewarsa yabarta ajiki bango hawaye shabe shabe zuciyarsa kuna kawae takeyi tafada kan bed tasoma kuka me cin rae,
WASHE GARI
Tunda su mummy suka tashi suka soma shirin tafiya mimi kuwa tunda ta tashi tarasa sukuni har sukae breakfast mujaheed yana kula da halinda take ciki sam muhammad ko inda takema be kallaba hakanne yakara tabbatarwa daddy da akwae matsala bayan gamawarsune suna parlour nana ta dafata tace meenal wae meyake damunkine nigaba daya natasa gane kanki yanzu wlh, zuciyan mimi bugawa kawae take tarasa ta ina zata fara tana cikin tsaka me wuya tanason mujaheed matuka kuma ayanzu idan tafurta to nana tasmmu abinyi zata kwacewa meenal youseep "NIKUWA NACE HMMMM" ganin tarasa mafitane yasata hayewa sama takira mujaheed koda yaga haka yasan akwae magana mikewa yay yabar palour din don answer wayan muhammad nakula dasu yana murmushi kawae soyake kafinsu daddynshi sutafi ayi komae yau ayita takare yau zefadima kowa yasan cewa wanann ba ita bace meenal....
TAKU A KULLUM NANA BMB.
08147110349 Downloaded from GNOVELS.COM.NG
This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/gnovels
Twitter : https://twitter.com/gnovels
Telegram : https://t.me/gnovels
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: 🤍💞🤍💞
RABON KWADO....
BOOK 3
💕💕💕💕💕
NA NANA BMB.
💞💞💞💞
BISMILLAHIRRAHMANIR RAHIM.
🤍❤️🤍❤️
page 1 -2
Shirune yakasance a parlour din domin kowa dahalinda yashiga cikin yanayi me tsanani mummy tace shin yaya menene wannan dalili dazesa kahana mujaheed auren meenal?
Shiru be tankataba,
Muhammad cikin wani yanayi yataso shima yazauna gefen mujaheed wanda yakejinshi kamar ba aduniyaba saboda tsananin tashin hankalinda yashiga,murya a raunane muhammad yace daddy kayi hakuri katallafawa farin cikinsu kada kayi musu haka suna kaunar juna daddy tunda yafara maganar daddy yake zuba masa wata muguwan harara.
Ganin daddy bazeyi magana bane yasashi kama hannuwansa yana cewa ina rokonka daddy kada kayi haka na tabbatar mujaheed zebata farin ciki har karshen rayuwarta,
Cikin tsawa daddy yace, MUHAMMAD KAENE MIJIN MEENAL!karigada kazamo miji agareta mijibincinta arayuwa!
To me karatu kowa poster yay a cikin parlour dinnan nepa din kowa seda tadauki, shikuwa mujaheed hannu biyu yasa yadafe kirjinsa saitin heart dinsa yana kallon daddy cikin firgita,
Galala da baki muhammad yace daddy kamar yaya? banganeba kamanta ni yayan meenal ne?
No muhammad yau komae zezo karshe tunda haka tafaru kacire wannan aranka daga yau domin kae mijine agareta,
Wata irin mikewa auntie tayi cikin firgici tace " WHAT" daddyn muhammad kasan mekakeson aikatawa kuwa? daddy beko kalletaba, Inna tafara salati tana sallallami yanzu dannan saboda danka zaka hana mujaheed yarinyar nan wani irin haline wannan kuma kake shirin daukarwa kanka?
Mikewa yayi yacewa da inna ina zuwa yanzu,
Koda yahaura sama befi yan mintinaba yasauko daukeda wani dan box me kyau yazo yazauna zuciyan auntie jitake kamar zata faso waje saboda tsananin bugun datakeyi mata,
Yar akwatun yabude yaciri wato farar takadda aciki yabudeta koda zefara karantawa seda yadago yakalli kowa yaga yadda suka maidashi TV kae tsaye yasoma cewa..
SHEKARA TA DUBU BIYU DA SHA UKU GA WATAN BAKWAI RANAR JUMA AH DUNMIN AL UMMAH SUKA SHAIDA DAURIN AUREN MUHAMMAD DA AMINA BISA SADAKI DUBU HAMSIN A BABBAN MASALLACIN JUMA AH, LIMAMIN MASALLACIN MALAM SHEHU IBRAHIM SHINE YAJAGORANCI WANNAN AUREN, ALLAH UBANGIJI YASANYA ALBARKA ARAYUWAR AURENSU.
Jisukae yaraf mimi tayanke jiki tafadi asume itakuwa auntie tundaga zsaye tayi zaman dabaro saboda tashin hankali mummy ce tayi gun mimi tana salati itada innah itakuwa nana saboda rudu batabi takan mimin bah ta isa gaban daddy tana cewa yanzu daddy duk wannan shekarun meenal tanada aure kenan?
Daddy be kulataba sema ruwa daya dauka ya guntsa abakinsa yaje yasoma fesawa mimi ahankali kuwa taja wani dogon numfashi tasoma bude idanunta tana wani marayan kuka mikar da ita daddy yayi yakamata yaje yazaunar da ita gefen muhammad wanda shida mujaheed dukansu sunyi suman zaune, kudi yaciri cikin akwatun yadanka mata yace meenal ga sadakinki nan daga rana irin ta yau muhammad mijine agareki wanda badon komae nahada auren nan nakuba sedan nawanke zargin da wasu mutane sukemin akanki.
jada baya mujaheed yafara yana girgiza kae yana karanto duk addu ah datazo bakinsa ba abinda yake tunawa se abinda ya aikatawa mimi a garden din gidansu, mimi na kuka tace daddy taya aure ze hallata tsakanina da yayana meyake shirin faruwane? kafin tarufe baki shima mujaheed yasome ya mimmike akayi kanshi shima se ruwa ake antaya masa amma ba alamun motsi atare dashi daddy yace sukamashi atafi hospital muhammad dukda jikinshi yana rawa haka yatemaka akasa mujaheed a mota mummy tanata kuka haka mimi a sukwane muhammad yaja motan suka tafi,
auntie tana zaune takasa ko motsi se nanace takula da halinda take ciki ta isa gareta tariketa tana girgizata auntie menene yasameki sam bata fahimtar me nana kematama,
Kallonsh mimi kawae take gaba daya al amarinnan ya cukwi kwiye mata kwanya hawayene keta ambaliya a idanunta tabbas tana cikin tsaka me wuya gaskiya takusa yin halinta cikin zuciyanta tana cemewa meenal kina cikin wani hali kina kaunar yousep sedae ayanzu kedashi sedae kallo daga nesa, koda muhammad yafado mata arae kukanta yakara kwacewa cikin zuci tana cewa nashiga ukuna ni mimi yazanyi da wannan bawan allah wata zuciyan tana cemata kawae ki gudu gidanku kome ze faru yafaru....
TAKU A KULLUM NANA BMB.
08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: 🤍💞🤍💞
RABON KWADO....
BOOK 3
💕💕💕💕💕
NA NANA BMB.
🤍❤️🤍❤️
page 3-4
Suna zuwa hospital aka soma bawa mujaheed temakon gaggawa seda awanni biyu suka shide tukunna yafarka yasoma kuka kamar karamin yaro muhammad yana gefenshi yarike masa hannu nujaheed cewa yake meyasa allah ze jarabceni da aikata laifi ya ubangiji kaga zuciyata kagafarceni, muhammad kayi hakuri kayafemin dumin matarka dana faraji kayi hakuri kallonshi kawae muhammad yake yarasa gane inda magan ganun mujaheed suka dosa dob basosae yake iya ganewa ahalinda yake ciki yanzu, hawaye yasoma share masa yana cewa babu laefinda da ka aikata my sweet broda kadena kuka ka kwntar da hankalinka indae masoyiyar kace zaka sameta saurin girgisaamasa kae yayi yace no muhammad kada ka kuma farta wannan maganar ko bayanraena kasaki meenak ban yafe makaba abinda daddy yayi yay daedae kuma ina goyon bayanshi,
Shiru muhammad yay masa akan maganar yanata rarrashinsa shikuwa inya tuna da abinda ya aikatawa mini a garden seya rintse ido zuciyanshi tana masa zafi yanzu matar muhammad ya lalube gaskiya kam yay asara,
Se aka sallameshi suma tafi gida mummy koda taga lokaci daya yadda dan nata yakoma inaga nan gaba tasoma zubar hawaye tana matukar tausayin dan nata, dama yau bamagar dinner kowa takae takae seda aka dawo sallar ishah ne baba yace kowa ya hallara a parlour zeyi magana, auntie taci kukanta takoshi tana ganin kuma takama ranar tonin asirintace sam bata taba tsammanin daddy zeyi mata hakaba arayuwa, seda kowa ya hallara a parlour baba yay gyaran murya yadora dacewa...
Ita rayuwa dum ayadda tazowa mumini hakuri yake ya ansheta duk wannan abun daya faru makkadarine daga allah shekara kusan shidda kenan da auren muhammad da amina zuwa bakwai dalilin yin wannan aure kuwa shine, zariginda mutane sukeyi masa akan amina wasu suna ganin amina 'yarsace tacikinsa shiyasa ya yanke wannan hukunci cikin masu zarginsa kuwa harda matarsa maryam mun boye batun aurenne smse muhammad yakara mallakar hankalin kanshi ya isa rike iyalanshi tukunna kuma ALHAMDULILLAH, Yanzu anyi abu akan gaba komae yau yazo karshe,dubanshi yakae kan mimi yace amina nasan zuciyanki ciki take da rudani to amma kiyi hakuri ki fawwalawa allah duka lamarinki maganar gaskiya marainiyaceke abubakar rikonki yayi kuma kigodewa allah daya hadaki da marika nagari kicire komae azuciyanki kiringumi mijinki kibisi sauda kafa, allah ne kadae yasan nufinshi yasaka kaunarki azuciyan mujaheed, inaso kaima mujaheed kayi hakuri karumgumi kaddara dadage da addua ah allah ya saukaka maka abinda kakeji azuciyanka sannan ga kanwar kanan nana indae zuciyanka ta aminta da ita munkaba ita sedae bazamuyi maka auren doleba, wata zabura mimi tayi zata mike caraf suka hada ido da muhammad yana mata wani irin kallo dole tagyara zamanta dama yana facing dinta sabida haka taki dagowa seyanzu hawaye kawae ke bimata fuska yanzu tanaji tanagani ua ah rabata da mujaheed abin kaunarta wanda saboda shine taki furta gaskiya akan kowacece ita,
Itama nana a kidime tamike jin furucin kakan nasu datayi daddy kuwa yadaga mata hannu takoma tazauna tana hawayen takaeci mujaheed kansa a sunkuye tunda suka zauna yace duk hukuncinda kuka yanke akaena daedaene banida zabi ayanzun baba yay murmushi yace yayi kyau allah yazaba maka mafi alkhairi arayuwarka suduma sukace ameen,nasihohi yashiga yiwa mimi da muhammad mussamman shi kan cewar yarike marainiyar allah tsakaninshi da allah kada yabasu kunya yakuma amince, tambaysrsu yay inda wanda yakeda abin cewa se a lokacin mummy tabawa daddy hakuri akan haushinsa data faraji ayanzu kuma tafahimceshi,shima mujaheed haka yabashi hakuri yace abinda yay daedae ne yana goyon bayan hakan kuma yaywa muhammad addu ah zaman lpy shida matarsa, sosae daddy yaji dadin hakan da mujaheed ye fuskanceshi ,
Hka taron yawatse kowa yanufi makwanci yana sake sake azuciyansa kotakan auntie daddy bebiba yaje yasama kofansa key don karma tashigo tamasa shirme,
Mujaheed yakasa bacci haka muhammad kowa da abinda kemasa ciwo a zuci to bangarensu mimi hakan take kowacce tana matsar kwalla taya zasuga samu suka rashi koma meze faru mimi taci alwashin bazata bari a rabata da mujaheed bah, to wannan kenan
WASHE GARI
Duka gidan babu wanda yatashi dawuri da alamu daren jiya babu wanda yadamu ishasshen bacci,.
Koda karfe 1 taharba su mummy sungama shirinsu tsaf natafiya bauchi mimi taki fitowa tace batada lpy harsu ka tafi bata saukoba muhammad bekuma bi takantaba yacigaba da sabgarshi da la asar shima yakae daddy airport don yaune zewuce dubae shima, jiki na tsuma nana takira mardiyya tasanar mata duk abinda yake faruwa tasoma rabka salati tasa kuka daga tsaye tasaki wayan saboda dimuwa ta tawarwatse,nana wayan meenal tasoma bincike acikinta daedar nan kuma mimi tafito awanka nana tae saurin aje wayan takwanta da ido mimi kawae tabita,
Da daddare mimi tana kwance abin duniya ya isheta nana tace yanzu meenal yazakiyi da yousep kenan? mimi bata ko kalletaba bare ta tankata zuwa yanzu tasoma sabawa ma da wannan iskancin na mimi seda takuma tambayarta anan tace mata nabar mikishi,nana tai shiru batae tsammanin jin haka daga bakintaba basarwa tayi tace to wae ayaushene kuka fara soyayya da ya mujaheed bamu saniba?mimi tagaji da tambayoyin nan na nana ga halinda take ciki cikin jinhaushi tace nafara sonsane asanda nagono kina son ya yousep cikin cikin jin haushi nana tace to ubanwayace miki ni inasonshine?dukda halinda mimike ciki behana tayin murmushi ba tace am sorry yaya namanta ay kincewa su daddy kinada wanda kikeso shikenan shizan zaba masa mata wadda ta dace,
Nana tayi murmushin bakin ciki tace to matar ya muhammad yazakiyi da mardiyya masoyiyarsa natabbatar yanzu tana hospital bayadda banyi dakeba kidena biyewa mardy komae nashi kina gaya mata ashe sirrin mijinkine kike barbada mata kinyi kunnen uwasshegu da abinda nake gaya miki aihmga irin tanan harda cemin kinyi alkawarin seya aureta inzuba ido insha kallo ido yanzu nasoma zubawa ma, sam mimi taki tankata don takasa gane inda maganarta tata ta dosama, wayar nana ce tayi ringin koda taga mekiran nata kuwa tasaki dariyar mugunta tana dagawa yace turomin yarinyar nan tasameni a garden kit ya yanke wayanshi, nana tace sabon salo yaukuma sweetien ce tadawo yarinya kallon mimi tayi tana dariya tace to ke gareki mijinki yace kisameshi a garden cikin kidima mimi tamike tasaki kukan tausayi tace narokeki yaya kice masa nayi bacci,
Nana takuma bushewa da dariya tace narasa yaushe ya muhammad yazama dodonki dabaki kaunar zuwa inda yake mimi takuma cewa narokeki yaya mikewa itama nana tayi tace wlh bazan gaya masaba kinsan yanzu zeshigo yakama zazzaga masifa kitashi kawae kitafi abinki yarinya garama kiriki mijinki shene mafi a ala agareki,mimi jitake kamar taringa falla mata mari suna cikin jayay yakuma kiran wayan tana dagawa yace bata wayan, takuwa saka mata akunne don tasan bazata amsaba cikin hassala yace shin zaki zone ko kuwa inzo in sameki dakaena? koda taji hakan bata jira komaeba tasuri hijab tafice,.
Ayanayinda tahango muhammad ne yakara sawa zuciyanta ta karaya tajuma a tsaye sannan yace zamanne bazaki iyabane?haka dae tasamu tadan dosana agefenshi kasa yay da voice dinsa yace kinason mujaheed? tayi saurin daga masa kae
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 27