Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
meze ceba takashe wayan tanata zaro idanu harda guminta kamar wadda tayiwa sarki karya,koda meenal tafado mata arae se hawaye shar allah sarki meenal masoyinki yana bidarki amma sedae kinyi masa nisa allah ya tseratar dake kidawo cikin 'yan uwanki namiki alkawari zan riritamiki soyayyarki harzuwa sanda zaki dawo,jikinta asanyaye tahau kan bed takwanta zuciyanta fal da tunani kala kala, Washe gari Tunda tayi sallan asuba takwanta bata kuma sanin inda kanta yakeba tayi nisa abaccinta aunty saratu harta gama shirya musu breakfast amma shiru bata fitoba tayi mamaki tunda kullum tare suke girkin tunda tazo amma yau ko motsinta hakanne yasata shiga dakin nata taganta akwance tanata sharar baccinta ganin haka yasata yin murmushi tajuya tace lallae meenal anshawo gajiyar biki,har mujaheed yafito bata tashiba don haka sukayi breakfast dinsu sukadae, wajan karfe 12 rurin wayanta yatasheta takuwa lalubeta cikin bacci tadaga wayan batasan kowayeba jin muryan inty datayi yasata watstsakewa tamike zaune balaifi sundan taba hira sannan tashiga bathroom koda tafito seda tagama shirinta tsaf tafito parlour aunty saratu nazaune taganta tasoma murmushi tace meenal seyanzu allah yanufa kenan antashi gaisawa sukayi tanemi guri tazaun, a ah yazaki zauna kije kisamawa kanki abin kari koh,inda allah yatemaki mimi tayi mata nuni da dahannu inda kitchen din yake, Indomie kawae tadora tahada tea tana tazauna a kitchen din tana dan kurban tea din,talula tunaninda tasaba taji anmata doss akumatu,tayi saurin juyowa kuwa suka hada idanu taga ashe mujaheed ne yamata kiss a kumatu lallausan murmushi yasakar mata itama tamayar masa tace yayana ina kajene zama yayi gefenta yace ayke zanwa tambayar ina kikaje haka ina baccinki yakaekine bata cemasa komaeba sema murmushi datayi masa,ruwan indomie dinda tadorane yatafasa kamshi kuwa yacika kitchen din harda hadiyan yawunsa yace my dear mekike girka mana haka me dadi dariya tadanyi tace indomie cefa bawani abu bane jinjina kae yayi yace masha allah matata ta iya girki kenan maganarshi seta bata kunya tasunkuyar dakae tana murmishi,koda yaga seya gyara zama yace meenal arayuwata inason matata ta iya girki inaso sosae kuwa,to yayana allah yabaka wadda tafini hadawa mah,saurin girgiza mata kanshi yayi yace no ina bazan taba samun wacca tafiki agurinaba babu ita bazan gantaba kaf 'yan matan duniyar nan kekadaece wadda nake kauna kike zaune azuciyata tsawon lokaci bazan iya jure tashinki bah ayanzu meenal ina matukan kaunarki kuma inason yin rayuwa dake tahar abada muzauna matsayin miji da mata,kawae dae fatana shine bazaki kiniba meenal inason sanarwa iyayena amma inajin fargaba bansan meye azuciyanki bah bakuma nason ayimiki dole arayuwa indae bakya sona kada kikee fadamin kada kiji nauyina asoyayya babujin nauyi meenal nibazanyi miki doleba zan hakura koda kuwa hakan zezama ajalina, burina dae kullum kikasance cikin farin ciki, Sauke ajiyan heart yayi yace dukda kinada yarinta meenal amma hakan bashine zahanaki sanin so bah inason jin furicin ki abindake cikin zuciyanki kigayaminshi yanzu meenal,duk maganan dayake kan mimi yana kasa idanunta nata zuban hawaye tanaji wani irin zafi azuciyanta jitake kamar takwala ihu duk wanan kalaman nasa bada ita yakeba da meenal yake,ita kuma tun randa tafara ganinshi zuciyanta takamu dakaunarsa,sedae shikuma meenal yakeso, wata ziciyan tace mata kada kiga laefinsa tunda meenal yasani bakeba, hearty ne yafado mata arae wato yousep sosae kanta yadaure to ayga wanda meenal takeso ma bashiba, oh ya allah katemakeni wlh nakamu da kaunarsa matuka har inaji zafi idan yana furta kalaman kauna yana kiran sunan meenal yazanyine idan na amince mishi meenal tadawofa, kodae nafada mishi gaskiya ina baze yiwuba gaskiya bazan iya jure rashinkaba mujaheed koda meenal tadawo bazan iya rabuwa dakaeba, rintse idanunta tayi hawaye nafita, ya allah kaine kadai kasan nufinka na kawoni cikin wadan nan mutane allah kasa hakan shiyafi alkhairi agaremu, Hannunda tarike cup din tea dinne taji yarike danashi hannun cikin yanayin tausayi yace pls say something meenal,hawayenta tashare datago suna kallon juna tace ina kaunarka yayana ina tabbatar maka sonda nake maka yafi wanda kake yimin ina hawayen farin cikine ayanzu dajin kalamanka,kayimin alkawari koda anan gaba bazaka taba juyamin bayaba komenene zefaru anan gaba kada ka kini bazan iya jure rashinkaba arayuwata tana magana tana masa kuka,hakan kuwa bakaramin tafiya da mujaheed yay wani irin sanyi yana ratsa masa zuciya jinshi yake kamar yafi kowa sa ah,yana zuba murmushi yasa hannu yana share mata hawaye yamatsa daf da kunnenta yana cewa i promise u my dear komin wahala bazan taba barinkiba meenal kece farin cikina zan zame miki bango jigo a rayuwarki so pls stop cry am always with u,sam mimi tarasa farin ciki take ciki ko bakin ciki batajin dadi idan yana ambaton meenal,tanajin yadda yake ambatun meenal yana mata kalami masu dadi, Jiki babu kwari tamike tasoma juye indomie dinta a plate shikuma yafita zuciyanshi kal da farinciki tabare egg dinta guda uku tafito jiki babu kwari,suka zauna tare sukaci indomie din mommy di nakallonsu duk abinda suke tana ankare dasu farin ciki sosae ya lullubeta.... TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: 💝💖💝💖 RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 13-14 Mujaheed yana ankare da mimi gaba daya yanzu tasauya komae nata dasanyi takeyinshi bata wani surutu sedae murmushi inta kama to bewani damuba yana tunanin duk sabida abinda yasametane takoma haka, Koda suka kwanta bacci inty tanata latsa wayanta abinta itakuwa mimi seta juya mata kada taga hawayenda takeyi abin duniya ya isheta kamar tasoma tsala ihu,cikin zuciyanta tana cewa mekikeyi ne haka mimi kinkuwa kyautawa diyar mutane, wato "meenal" allah ne kadae yasan halinda take ciki inma tana raye kekuma gashi kina amfani da farin cikinta,rintse idanunta tayi tana dafe zuciyanta,yanzu yazanyi da rayuwata ni mimi ina komawa gidanmu meenal zasu kwashe idan tana raye sanan sudawo kaena komawata gida sam ba alheri bane gashi inason ganin mahaifiyata,zuciyata takamu da kaunar mujaheed matuka bazan iya barinshi cikin tashin hankaliba da kowama na meenal ina tausaya musu sosae dole nahakura da rayuwata nazauna inda allah yakawoni kuma shikadae yasan nufinshi nayin hakan,ya ubangiji ka kubutar da ita domin tadawo garesu nima nakoma nawa family din,tanata magana azuciyanta bacci yasaceta batare da tasaniba, WASHE GARI Tunda suka tashi inty kamar zatayi kuka duka 'yan biki suntafi se sukadae itada mimi itama kuma gashi yanzu zata tafi dawuri sameer yazo donyi sallama da aminin nashi mom tanata rarrashin inty itama mimi na nata jimamin azuci batasan wani kalar gidaba kuma yanzu zasu jitake dama suyita zamansu anan kayan azziki suka hada mata su mom sosae sannan suka tafi,suna hanyane yake cewa meenal ina wayanki ne?hankalinta nakan hanya tace tana cikin jakana,to meyasa kika kasheta meyasa kikeson rufe wayankine yanzu kowa yayta kiran wayanki akashe laifina suke gani jiya auntie ba irin fadan dabatayi minba awaya akan kin rufe wayanki kindena nemansu why?har daddyn ku tace bakya kiransa cikin damuwa take kallonsa harya gama sannan tace am sorry yayana banasonne sufahimci wani abu yasamenine amma yanzu tunda naji sauki muna zuwa zan kunna wayannawa murmushi yayi dajinjina kansa jefi jefi suna hira harsuka karasa gidan sedae mamakine yacika mimi ganin tsoffi datayi tanata tunani tasandae wadannan sunyi tsufa bazeyiwu ace iyayensabane inna tana salla se baba agefe yana lazimi yana ganinsu kuwa yasoma tafa hannuwa yana cewa oyoyo oyoyo 'yan jikokina sundawo gida sannaunku dazuwa,sosae mujaheed yaji dadin ganin kakannin nasa dayayi,yazauna gefen baba yana cewa tsoho meran karfe kaci zamaninka kanacin nawasu yana dariya yay naganar shima baban hakan yace fadi ka kara yaro naci zamanina inacin naku cakwas dani yaranka kaga nafika tsadadden jiki koh dakaene kakae shekaruna ina zaka ganu,mujaheed yay murmushi yace haba baba jifa jikin naka ai ina tunanin munkusa fara dakan gumba agidan nan,baba yay murmushi yadamki damtsen mujaheed yace tokumu gwadane innuna maka tsohon kashi ba irinna yarintaba,zafinda yajine yasashi cewa wlh naji baba nayarda amin afuwa, yakuwa sakeshi yana fara ah yace ja irin yaro allah yashiryaka mujaheed,dubansa yakae kan mimi tana zaune tanata sake sakenta yace meenal meke damunki ne kikayi shiru haka kamar ruwa yacinyeki koduk gajiyan bikinne,murmushi tayi tace a ah baba,girgiza kae yayi yace a ah dakwae abinda kedamunki ayda kalau kike dayanzu gidan nan bama jishi shiruba, zuciyan mimi kuwa tawani harba dajin furucinshi ita mezatace musune sam batasan surutu ko kadan hawan mata kaema yake inyayi yawa,kallon mujaheed baba yayi yace meke damun jikalletane se kallonta yake yana mata alamu da ido amma kanta yana kasa,dan yake yayi yace gida takeson komawa ne,se ayanzun tadago takalleshi tana yana mata inkiyi da idonshi tagane nufinshi kada tabari agane tashiga matsala,baban yace to koyau zaka maidatane ya girgiza kae yace a ah haba bayauba dae hakuri zatayi, koda inna ta idar da sallah mimi tahubawa idanu tana murmushi alamu taji ana kallonta koda tadago kuwa suka hada idanu tayi saurin sunkuyar dakanta tace ina wuni sororo da mamaki ta amsa mata wanda inda dane datuni taje ahaye mata cinya,inna tace sabon salo lallae meenal gida akeso kaga yadda tayi wani ladaf kamar wadda akayiwa mutuwa keda kikace bazaki komaba kinzo kenan sedae suyi hakuri ashe kinfasa zama gurin saratun kenan,to ay setazo takwashi kunyarta taji abinda kikeso yanzu,sosae suke hira avinsu cikin jin dadi wanda mimi nata murmushi ne kwae har tsokanarta inna takeyi sedae tayi murmushi sosae taji tsofaffin sunshiga ranta,sunkuwa yi mamakin yin shirunta kuwa haka su mummy suka karaso itama taga mimi cikin wannan yanayin nashiru mujaheed yanata zuba tabararsa yaga yadda mummy kezuba masa harara yarasa meye dalilin yin hakan, daga karshema hannun mimi takama shiga daki suka zauna tace meenal fadamun abinda yake damunki kada ki kuskura kiyimin karya meyasa kikeson komawa gida kada ki boyemin idan mujaheed yay miki wani abune just tell me duka gaba daya kincanza jikinki yayi sanyi haka zaki koma musu gidan,murmushi mimi tayi tace wlh mummy babu abinda yayimin kuma gida nakeson tafiyaba, banason maganane dayawa haka nakeyi dama indae ina menstruation gashi yace auntie ma takirashi, Seyanzu tasauke ajiyan zuciyan da harseda mimi taji tace ok yanzu nafahimci damuwan keda auntienki ne ko hakuri zakiyi meenal watarsna se labari kita mata addu ah itadae mimi amsawa take azuci kuma tana fargaban tome auntn takewa meenal?komawa parlour din sukayi aka cigaba da hira dob tayi tunanin kodae wata ayka aykar dannata yaywa 'yar mutane donba ah shedar dan yanzu,sedare suka tattara suka tafi koda suka isa dukda darene hakan behana mimi gane gidan part biyu bane ga tsaruwa iya tsaruwa gidan yatsaru kayanta da mujaheed yaketa kaewa daki yasata gane acan masaukinta yake bawanda yazauna hira sabida dare yayi kowa yanufi makwanci,ita kuwa seda takarewa dakin kallon tsaf sannan tadauko wayan meenal takunnata tazauna kan bed tazubawa wayan idanu.... TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: 💝💖💝💖 RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 19-20 Tana tafiya cikin sanda harta isa inda yake tasa hannu tarufe masa idanu tana bayanshi sedae mujaheed bakaramar tsorata yayiba addu ah yasomayi ba kakkautawa ita kuma jin yadda yake jero addu o ei yasata fashewa da dariya tajanye hannayenta dariya harda tafa hannu tana nunashi koda yabude idanunshi suman zaune yayi yana kare mata kallo ay yau ganiyay tamafi koyaushe kyau yadda take dariya kamar sakarae yake kallonta seda takare dariyar tata tace kae yayana haka kake da tsoro dama sam bemaji metake cewaba saeda takae hannu ta dungure masa kae sannan ya lumshe idanunsa tana murmushi tace kunya kakeji nabaka tsoroko, Bude idanunsa yayi dasuka soma sauyawa wayarshi yadauka yaga time har kusan biyu saurama ya jinjina kae ya aje wayan bazato taji yajawo hannunta yana daga zaune tana tsaye harseda ta dsngane daga jikinshi kirjinta yasauka akan fuskarsa yasauke ajiyan zuciya dakyar ya iya furta my dear kinbani tsoro over mekikeyi anan bakiyi bacciba shirun datayi masane yasashi dagowa yana kallonta suka hada idanu yadda nashi yacanzane bazata iya jurewa kallonshiba ta sunkuyar dakanta kasa tace nayi bacci farkawa nayi,sukayi shiru nadan lokaci sannaa taji numfashinsa awuyanta yana cewa nimafa sena rama tsoron dakika bani kishirya jinsa yanzu ato,bata fahimci meyake nufiba sema rintse idanunta datayi tana murmushi hakanne yabashi damar karewa kirjinta kallo gaba daya rigan ta zanzare dan kadan tarufe mata kirji bakin cikine yakamashi ganin karcewar datayi haryanzu akwae shatinta,hannu yasa yadan shafi gurin,habawa aykuwa kamar an tsikareta tabude idanunta tana kokarin kawcewa seyanzun ta tuna ayadda tafitoma don manni irinna mimi takasa kwacewa don riko mekyau yamata kuma yaki dena abinda yakeyi mata haushi sosae yatiketa takae baki tacizar masa hannun dole yasaketa tajuya dasauri zatabar gun tabdi tana juyowa taga yama cimmata saboda tsoro takife agurin ido kawae take kwalowa tana bashi hakuri cikin shan kunu yace tonima wayace ki tsoratani,ganin abin nashi gabama yakeyine yasata sakin kuka tana ture hannunshi tana cewa nika kyaleni banaso kukan tane yasashi tattaro hankalinshi yacire hannunshi cikin rigarta tamike asukwane kuwa tanufi cikin gida tana hawaye masu zafi koda tashiga dakin nata tasake fashewa da kuka tafada kan bed tana jin zafin mujaheed sosae azuciyanta donme zetaba mata jiki ita ba matar saba kuma ba ita yakesoba meenal yakeso ziyi mata haka, shima mujaheed kayanshi yatattara yakoma daki yanajin haushin kansa abinda yayiwa mimi,seda taci kukanta takoshi sannan bacci yadauketa, WASHE GARI Da wuri mimi ta tashi tayi wanka tashirya ta tasa kayan meenal agaba tanata kallo natafiya tana tunowa da muryar auntie takejin zuciyanta na harbawa tanajin fargaba dukda batasan gidanba amma zuciyanta bata kaunar tafiya gidan,tare sukayi breakfast dasu auntie saratu banda mujaheed donbe shigoba kallo daya sukayi mata sukasan tayi kuka sekuma basarwa take don karsu gane wani abu, daddy yana shirin fita aikine nujaheed yashigo yana waya seda yakammala sanan yagaida iyayen nashi mimi nagefe tanata zumburar baki ita ala dole anmata badae dae bah beko kulataba dasu mummy kawae yake hira har suka fita zata raka daddy din bakin gate suna fits yatashi yaje yazauna a dining yasoma breakfast dinsa beko kalli inda mimi takeba,seda daddy yashiga motan yarufe kofan sannan mummy taruza kanta tana masa magana cewar kajawa danka kunne yafaja girmansa meenal yarinyace tsaf zata rainashi kana ganidae yau kogaisawa basuyiba zuba mata ido daddy yay yana murmushi harta kare maganarta,sannan yace niba abinda zancewa dana kema idan kika gaya masa ay yayi,mujaheed yasan abinda yakeyi saedae ita meenal daganin wannan yarinya zeyi fama da ita itazakiyiwa fada kada ta lalatamin yaro,hade rae tayi tace kaedama indae akan mujaheed ne kada sonkanka dayawa goyon bayanshima kake kamar batare dakae muganshiba jiya a garden yanama 'yar mutane ayka aika,kace zata lalata wancan katon yaron duka nawa take metasani mah katseta yayi dacewa aydama ku mata haka kuke kuyi tsokana kuma kuce anmuku ba dae daeba inbanda jiya kintaba ganinsa yamata wani abu nifa bazanga laefin danaba wani kinibibinne yafito da ita daga dakinta cikin wannan dare tasameshi har inda yake kuma babu shiga ta mutumci itacefa takae kanta don dana ba dutse nahaifa bani,so kigaya mata taringa suturta jikinta harsuyi aure kada kada ta lalatamin tarbiyarr yaro da ace dakinta yabita ne wannan to zega abinda zefaru kuwa to amma yanzu laifi na 'yarkine,duka meenal matasani arayuwarta dazata iya wannan aikin,dariya yayi sosae sannan yace ki kyale zanceb kankanta duk inda mace take to macen ce so kidena yimata kallon karama aynazu akama 'yar can aure seta zauna harda murnarta kike abinki keni koyanzu my son keson yin aure yimasa zanyi donnaga 'yar takima kila setafiki iya rike miji! dama yatada motansa kafin takuma magana yaja motansa yana dariya yana cewa sekun dawo matafiya agaidasu Dr maryam sun saba mummy da daddy irin wannan drama din soyake dama yakunnota kan yafita, Seda yagama breakfast dinsa sannan yadawo kusads ita yazauna zumbur kuwa tamike cikin fushi yarike hannunta tajuyo cikin tsiwa suna hada ido tayi lakwas da ita rae abace yace baki iya gaisuwa ba koh cikin tura baki tace ina kwana yadda tayi masa maganar ne yasa ranshi yakuma baci kawae yasaki hannun nata yamike yafice daga parlour din tabishi da harara harda murguda masa baki,yana fita mummy tashigo tace meenal kingama hada kayankidae koh anjima zamu tafi kamar tayi kuma ta daga mata kae seda tazauna tace meyake damunkine kika shiga damuwa tundazu bakomae mummy, tomeya hadaki dayayanki nanma shiru batace komaeba, mummy tasauke ajiyan zuciya tace aduk sanda zakiji gurin yayanki kiringa suturta jikinki kafin kije kinga ba aure kukayiba saboda gujewa hudubar shedan, ay zuciyar mimi tsinkewa tayi tana kwalo idanu kardae mummy tagansu jiya dakyar ta iya daga mata kae alamun to don takasa dagowa, yawwa meenal allah yayi miki albarka kije kirasa kimtsa kayanki koh, tamike jiki asanyaye tanufi dakin abin duniya yaymata yawa tarasa abinda yake mata dadi tanajin wayar meenal tanata ringing amma taki kulata sotake taga mujaheed amma ko motsinshi batajiba har karfe biyu tayi narana sosae take kuka tunda tafito awanka tamakasa shirin daga ita towel tana haka taji ance kukan me kikeyi?tayi saurin dagowa suka hada ido kunyace takamata tasunkuyar dakanta kasa cikin tura baki tace to ay bakuka nakeyiba kaenane yake ciwo,betankataba yajuya zefita yace kitashi kishrya kifito mutafi kemuke jira zamu gidansu inna dagacan muwuce rintse idanunta tayi don sam tamace batasa kayaba ga towel din dukya tattare ganin zefice ne sayata saurin saukowa tazura hijab tace yayana cikin sanyinta, ay zuciyar mujaheed tawani harba jin muryar meenal dayayi tacanza wanda bakowane zefahimci hakanba takowa tayi har inda yake tazagayo tatsaya agabansa idonta tafda kwallah tace sokakeyi natafi nabarka nifa banason tafiyar nan kagayawa mummy tabarni banason tafiya nabarka nafison kasancewa dakae koda yaushe bazanyi farin cikiba indae kayarda aka maedani gida kuma sena dena yima magana, tana kuka tamatsa ta dora kanta kan kirjinshi tana kuka tana cewa pls yayana pls.... TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: 💝💖💝💖 RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 17-18 Yinin ranar tare suka kasance cikin nishadi sae bayan la asar suka tafi gidansu innah basu suka dawoba se bayan ishah suka sami auntie saratu tana zaune a parlour fuskanta daukeda damuwa suduka suka zauna gefenta kan carpet mujaheed yace menene yafaru mummy naganki cikin damuwa tayi murmushin karfin hali tasa hannu ta shafi kansa tace babu komae my son dubanta takae ga mimi wacca tazuba musu idanu tace meenal kishirya gobe insha allah nida mujaheed zamu rakaki gida Damuwa karara tabayyana afuskan mujaheed kamar yay kuka yace haba mummy abari hutun natama yakarasa karewa mana kamar mungaji da ita nasan wlh auntie ce zata kiraki tabata maki rae, batabi takan zancen nashiba tace kamantane bayan boko tana zuwa islamiyya ne gobe insha allah zamu tafi takalli mimi wadda kirjinta ke dukan uku uku tace kije kishirya kayanki kinji meenal kada karatu yadinga wuceki,kamar zatayi kuka kuwa tace don allah mummy kubarni anan nibanason komawa gidan,girgiza mata kae tayi tace kiyi hakuri meenal mahaifiyarki kebidarki shin ina kika aje wayankine seyanzunma mimi ta tuna da wata waya tunda safe dasukayi waya da inty bata karabi takan wayanba,tana daki shine abinda tace to tashi kije ki kirata jikinta asanyaye tamike tashige dakin shima mujaheed yanufi nashi guri cike da bakin ciki,aunty saratu itama tahaye sama abinta ran kowa babu dadi,koda mimi tashiga ciki jitake kamar tasa kuka itafa wlh tagaji da anje wannan gida ace za ah tafi nan gashi wannan auntien dagani bakin hali gareta tanata masifarta ita kadae tajiyo karar wayan harseda takusa tsinkewa sannan taje tana gani tasan auntien ke kira yadda meenal tayi serving number din picking call din tayi sedae tunkan tafara magana tasoma jin ruwan bala ei wlh meenal kiji tsoron haduwata dake tunda kinzama mara mutumci yanzu 'yan uwanki basuda mahimmanci agareki da iyayenki kira nawa nayi miki seyanzu zakiga daman dagamin waya sabida kinsamu guriko! sati daya mukace kiyi kidawo gida shine kika zauna dake suma basusan darajar karatun da kikeyiba gajiya dasauraren ihun mimi takatseta dacewa pls auntie kiyi hakuri bagobe zandawoba,kadama kidawo kiyi zamanki kinji duktsiya dae ay sekin dawo garemu mimi bata iya jure fadan don haka tayanke kiran ta aje wayanma tashige toilet abinta, Meenal ce akwance kotashi bata iyayi dakyar take bude idonta duk jikinta yay yaushi tawani kojale sae kace ba itaba azuci kawae take iya ambaton allah haka tayini ahaka sedare taji anshigo dakin ko daga kae takasa motsi kawae take iyaji nawanda yashigo daga bisani taji ankuma fita,sam yanzu tafidda rae da rayuwa addu ah take allah yasa intamutu anan to tamutu 'yar aljannah tadena tunanin kubuta mutuwa kawae take hange don ta sallama rayuwarta ayanzu, Wani irin kara kara takeji akunnenta kasa kasa mamakinta bekareba seda aka kuma shigowa kara take kuma shiga kunnenta tsawa da hargagi kawae take jiyowa takasa mikeww zaune donhaka tarintse adanunta tasadakar yauce ranarta takarshe aduniya, Bazato tajee an dan dora mata wani abu awuyan tsoro kuwa yakara rufar mata ta daskare akeance wata murya tajee ance yanaga kamar bata numfashi, daga kusada ita tajee ance bata mutuba numfashinnedae yake barazanar daukewa,se awannan karon tayi karfin halin bude idanunta tazubasu kan mutumin ga hasken fitilinsu duk da haka dishi dishi take gani ashe yatsunsane yasa awuyanta kuma kakin sojane ajikinshi,ba bata lokaci yadauketa cak yanufi waje da ita karar datake jine yake gigita mata kunne haryanzu batayi tunanin karar bindiga takejiba duk tafiyan dataji anayi da ita taki bude idonta sam seda taji wata san sanyan iska naratsata yasata saurin bude ido sedae duhu tagani ako ina hakan ya tabbatar mata anfito waje,seda ya isa bakin motansu sannan yashimfideta yadauko goran ruwa yabata tasoma kwankwala seda takoshi sannan tasoma maida numfashi bazato taji karar data firgitata tasaki dan guntun fitsarinta tasulale kasa saumamma! Mimi cikin baccinta taketa mutsu mutsu da alamu mafarki take firgigit kuwa tafarka tana sauke numfashi siraran hawayene ke bimata fuska tana murmushi tadaga hannayenta tana mika godiya ga ubangiji ya allah kaene abin godiya allah kasa mafarkina yazamo gaskiya meenal dinsu takuta daga hannan azzaliman cen,kasancewar tana menstruation ne yasata batayi sallaba tamike tamaida hular kanta tafito palour domin shan ruwa rigar baccine ajikinta 'yar yaloluwa gata shara shara komae breast dina kana gani saboda batasa bra bah, fridge tabude tadauki ruwan tasha abinta tanemi guri tazauna se sauke ajiyan zuciya takeyi sosae takejinta wani wasae da ita gajiya tayi dazaman parlour din ita kadae yasata mikewa sam bacci yakauracewa idanunta takuwa bude kofa tafita abinta kofan daze sadaka da dayan part din nagidan tazubawa idanu" da alamu wanan mimi din batada tsoro kamar meenal" tafiya take harta dangane da garden sedae abinda yabata mamaki shine ganin mujaheed datayi zaune kan daya daga cikin kujerun garden din yanata danna laptop dinsa duka hankalinshi nakanta sam bejitaba dagashi se gajeran wando,wani irin farin cikine ya lullubeta ganin masoyin nata datayi itakanta tarasa dalilin farin cikin dakeji tunda tafarka abacci sanda tafara ahankali tana nufar inda yake," waeshin mimi tamanta suturar dake jikintane"? TAKU A KULLUM NANA BMB. 08147110349 [7/28, 8:20 AM] Nana BMB: 💝💖💝💖 RABON KWADO.... BOOK 2 NA NANA BMB page 21-22 Sam mujaheed besanda sanda yamata kyakkyawan rumguma yanadan yasunkuya saitin kunnenta yana cewa am sorry my dear zanyi kewanki matuka but iyayenki ne suke bukatanki kusadasu bamuda iko akanki nidake seyadda sukayi damu kwaedae meenal in dae kina sona kina kaunata dayawa kina gama secondary school kibari amana aure hakan shine ze bamu damar rayuwa atare harzuwa karshen rayuwarmu,bugun zuciyartane yakaru tana tunanin taya zatayi aure bada sanin iyayentaba? Dan matsatan dayayine yadawo da ita tunanin data lula tayi saurin janye jikinta takoma

Chapter 13 of 27